Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maka Hanyar gaskiya, ka sani Ubangiji sai yayiwa wannan yarinyar sakayya abisa cutarwar da kake Mata, DOCTOR anya kuwa saboda matsalar iyayenku kake walaƙanta Falmata, ko dai Saboda bata haihuwa ne kake walaƙanta ta."

Ɗago kansa DOCTOR yayi da ya kaɗa yayi jajur, ya dubi SAIF tare da girgiza kai yace.

" Karka kai zarginka zuwa ga rashin haihuwar Falmata, domin kuwa bawai kwatakwata bazata taɓa haihuwa bane a rayuwarta matsalace kawai take dashi, kuma muna saka ran zata sami sauƙi kuma koda Falmata bazata haihu a rayuwarta ba ni zan iya zama da ita a haka, saboda kafi kowa sanin yanda nake son FALMATA, sai dai ƙaddara ta shiga tsakanina da Soyayyar ta, matsalar da aka samu nafi son iyayena a kanta Soyayyar su tafi ƙarfi fiye da wanda nake mata, dan Allah Saif mubar wannan maganar haka."

" Hmmm!!! Ko baka ce dama Dole zan barta tunda ba son gaskiya kake, amma ina son kasan abu wanda kowa yake kallon ka da ita, *TUN CAN DAMA BA SOYAYYAR GASKIYA KAKE MAWA FALMATA BA SHIYASA KA JUYA MATA BAYA A LOKACI GUDA*."

Ya faɗa masa maganar tare da tashi ya bar Bedroom ɗin.

DOCTOR binsa yayi da kallo cikin sanyin jiki harya fice, kwanciya yayi a bed ɗinsa tare da yin rigingine yana kallon slip muryar HABEEB ne kawai take masa yawo cikin kunnen sa, runtse idanunsa yayi yana jin wata sabuwar tsanar HABEEB cikin ransa *KA ADANA MATARKA DOMIN KUWA HAR YANZU INA SONTA* tsuka yaja still pictures ɗin Aunty Jalila yana hanunsa, rungume shi kaɗai yasan zafin da yake ji na rasa iyayen sa da yayi, tashi yayi yana sauƙe ajiyar zuciya ya ajiye pictures ɗin tare da ƙwalawa Ladiyo kira, cikin sauri kuwa ta shigo da Sallama, nuni ya mata da ta tattara kayan da ya zubar a ɗakin, da to Ladiyo ta amsa sannan shi kuma ya shige falo ya zauna zaman jiranta.

Falmata tunda ta shiga Bedroom ɗinta hawaye ya ɗauke daga idanunta, sai zafi kawai da zuciyarta ke mata ita kanta tana mamakin irin matsanancin Soyayyar da take yiwa DOCTOR Zuciyarta ta kasa hakura dashi, Soyayyar sa ji take tamkar ranta hakan yasa take jin rabuwa dashi tamkar rabuwa da rayuwarta ne, meyasa DOCTOR yake wulaƙanta ta haka, bayan shima bashi da tabbacin iyayenta suna da hanu cikin ɓatar iyayen sa, zama tayi bakin bed ɗin ta zuba tagumi, cike da damuwa, ta daɗe zaune tana cikin tunani kafin ta tashi cikin natsuwa da kuma damuwa ta nufo falo a zaune ta hangesa dama kuwa Bedroom ɗin nasa ta nufa, wajen sa ta taho, ta faɗa jikinsa tare da saka hununta ta ƙanƙamesa, sai kuma tasa kuka.

Kusan suman tsaye DOCTOR yayi jinta a jikinsa, da yayi, ajiyar zuciya ya sauƙe ya kuma kasa yakice ta daga jikinsa domin kuwa rabon dasu haɗa jiki da ita tun randa wannan mummunan lamari na iyayensa ya faru, shuru yayi kawai yana jin sautin kukan ta, cikin muryar kukan tace.

" Bansan wani irin soyayya nake maka ba, ni dai nasan bazan iya jure rasa ka ba, dan Allah kayi hkr, karka rabu dani saboda kuskuren iyayena, Wallahi ban kai ƙararka wajen Hajja ba, ban kuma ce mata komai ba, bansan dalilin da yasa ta maka haka ba, ka yafe min dan Allah karkayi fushi dani mijina."

Ta ƙarasa maganar tana kwantar da kanta a ƙirjinsa, still shuru, bai ce komai ba, itama shurun tayi tana laɓe a jikinsa, DOCTOR jin wani abu ya fara yawo tun daga tafin ƙafarsa zuwa kansa ya sashi saurin ɓareta daga jikinsa ya tashi da sauri ya bar falon duka, kallo Falmata ta bisa dashi cike da tausayin kanta harya fice, ta daɗe zaune cikin falon kafin ta koma Bedroom ɗinta.

Maji kuwa a ƙofar gidan su HABEEB ya sauƙe ta, murmushi tayi tare da cewa.

" To HABEEB na gode."

Shima HABEEB murmushi yayi tare da cewa.

" Okay ki gaishe da Mama, sai munyi waya."

"Zataji" Maji tace tare da shigewa cikin gidan.

Aunty YANA kuwa tun ɗazu zaman jiran ganin Falmata take da takaddar sakinta, amma ina shuru take ji wai Malam yaci shirwa, Yagana da ta shigo ne ta zauna Aunty YANA tace.

" Oh ni YAHANASU wai tun ɗazu fa nake zaune nake jiran naga yarinyar nan Falmata ta shigo min da takaddar sakinta amma shuru babu wani motsi."

Murmushi Yagana tayi tare da cewa.

" Wai ke tunani kike dama Hassan zai saki Falmata dan kawai wannan rashin mutunci da Hajja ta masa hmmm!!! Kin manta waye Hassan kenan, to wannan dalili yayi kaɗan yasa ya saketa, wai ma Aunty Yana meye ribarki idan Hassan ya saki Falmata meyasa kike son ya saketa."

Tsuka Aunty YANA taja tare da cewa.

" Ke Yagana baki ga dalilin ba kenan, bakya ganin yanda yake wahalar da rayuwarta kullum cikin baƙin ciki take a gidan ta, wace uwace ranta zaiyi daɗi taga ƴarta wacce ya kamata ace tana taimakon ta cikin wahala babu wannan Uwar komai lalacewar uwa tana son taga ɗanta cikin jin daɗi, duk abinda zanyi domin dawo da hankalin Hassan kan Falmata taƙi ta bani haɗin kai, naje wajen Malamai sun min aiki akansa amma abun yaƙi cinsa na karɓo wanda za'a sa masa yarinyar nan taƙi bani haɗin kai, to ya zanyi idan ba na nemi auren ya mutu, tazo ta sami wani mijin ta aura wanda zata sami kwanciyar hankali."

Jinjina kanta Yagana tayi tace.

" Tabbas kuwa Falmata bata da farin ciki a gidan Auren ta, kuma itama tana da laifi na shige taurin kai da tausayin wanda baya tausayin ta, ni dai abinda zan faɗa miki, tunda layar nan tana nan, ki ɗauka kije gidan da kanki ki saka ki kuma ja mata Allah ya isa idan ta cire, kinga kuwa idan tana neman albarka ai dole ta barsa."

" Hmmm!!! Kin kawo shawara mai kyau, zanje da kaina amma ba yanzu ba sai an kwana biyu saboda tsaro."

" Hakan yafi ya kamata kije kam, bari naje wa Hajja aika gidan Su Maji."

" Sai kin dawo" Aunty YANA tace.

" FANNA FANNA!!! Hajjo ce mai kwala mata kira amsawa Fanna tayi tare da shigowa ta zauna kusa da Hajjo tace.

" Gani Aunty."

" Ruwan wankan Umman yayi zafi ne.?"

" Eh yayi zafi daidai wanka."

" To maza tashi kije ki ɗiba ki sirka ki kai bayin sai kizo ki taimaka min mu kaita."

To Fanna tace tare da tashi taje ta ɗibi ruwan ta kai sannan ta dawo Hajjo Itace ta tayar da Umma sannan Fanna ta tallafe ta, suka Kaita bayi, fitowa Fanna tayi ta bar Hajjo, itace ta mata wanka tas sannan ta kira Fanna tace ta kawo mata kayan Umma a sip ɗin Umma Fanna ta ɗauko kayan ta kawo Hajjo ta sa mata sannan suka fito da ita suka kwantar, wannan karon idanun Umma a buɗe suke tana bin kowa da kallo sai dai bata Magana, Hajjo hayaƙin magani ta ɗauko ta turare Umma dashi, Fanna kwantar da kanta tayi jikin Umma hawaye ya zubo mata,tace.

" Zaki sami lafiya Umma da yardar Allah, zaki warke ki dawo Kamar da ummana."

Hajjo ma tausayi Umma ke bata, mata mai kazar-kazar da son ƴan UWA, mata mai kirki tana kwance cikin jinyar da ba'a gane kanta ba, suna nan zaune Hajja ta shigo, Hajjo ce ta gaishe ta, ta amsa fuskar ta a sake duban Umma tayi tace.

" Sannu Yamuram Allah ya baki lafiya, ki tashi ki tsaya akan ya'yan ki, nasan dukkan wannan abinda ke faruwa tsakanin Hassan da fatuma da kina da lafiyarki bazaki bari hakan ta faru, Allah ya yaye miki"

Da ameen hajjo suka amsa, Hajja ta juma zauna kafin ta fita tana cewa Fanna tazo zata aiketa.


Can kuwa gidan DOCTOR cikin dare kowa yayi nisa da bacci amma ita Falmata nata idanun biyu ne ta kasa bacci gashi gobe tana son zuwa school daga nan zata biya gida ta duba Umma, bata san kuma ta yaya zata sanar da DOCTOR ba, ta juma tana Nazari har bacci ya ɗauke ta.

Yayin da shima DOCTOR yake nasa Bedroom ɗin bacci ya gagaresa maganganun Hajja da HABEEB ne kawai suke masa yawo Cikin kunne, bai taɓa jin haushin Hajja irin wannan karon ba, wai shi Hajja take kira banza a banza, hmmm duk abinda aka masa bata gani ba, tafi son ya'yan kawu bukkar akansu, a cikin zuciyarsa ya furta babu komai rayuwa ce, tashi yayi ya shige tollet ya ɗauro alwala fitowa yayi ya tayar da Sallah, duk sujjadar da zaiyi sai ya roƙi Ubangiji daya bayyana masa mahaifinsa da ƴar uwarsa cikin ƙoshin lafiya, bayan ya idar da sallar ma ya juma yana musu addu'a sannan yaji zuciyarsa ta masa sanyi, bed ɗinsa ya hau ya kwanta yana bin gefen da Falmata ta saba kwanciya da kallo, lumshe idanunsa yayi tuno rayuwarsu ta baya mai cike da kwanciyar hankali da Soyayya, yau ɗaya kawai sai da yaji kewarta cikin Bedroom ɗinsa, filo ya jawo ya ƙanƙame tare da rufe idanunsa.



Naso read More ɗin yafi haka yawa amma dai ku shaƙata da wannan ɗin.

Masoya naji daɗin yanda kuka nuna min ƙauna ta hanyar siyan wannan littafin na gode sosai🤝🏻


Ki biya ki karanta cikin kunciyar hankali labari ne mai cike da Soyayya tare da ban tausayi faɗakarwa harma da nishaɗantarwa ki biya kuɗin ki ta wannan hanyar 👇🏻

*Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari*


Vote
Share
And Comment




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*




*(UMMU NASMAH CE)*
[9/3, 7:12 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤️ *Love and romantic and funny story* ❤️



*Na*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

*RIGIJI GABJI TSARƘWAI MAZAƘWAI INA KUKE MASOYA WANNAN SHAHARARREN BOOK ƊIN WATO CONEL UBAIDULLAH TO ALBISHIR YANZU MA DAI GA MOMYN AHLAN ZARAH ABDUL TA SAKE DAWO MUKU DA SABON SALO MAI SABON TAKU GAWURTACCEN SOJA CONEL UBAIDULLAH RETURN MAZA KU GARZAYA KU SAMI UWAR AHLAN DOMIN KUMA A DAMA DAKU KUMA WAƊANDA BAKU KARANTA NA FARKO BA, KU NEMA KU KARANTA KAR A BARKU A BAYA, AKAN FARASHI ƘALILAN MOMYN AHLAN TANA JIRAN MASOYANTA*


Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.





*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Book One*

*Page 19 to 20*

*____________________________________*




_______✍🏻Washe gari da safe cikin ikon Allah Falmata ta tashi cikin fara'a domin kuwa haka kawai take jin Damuwar tata ta mata sauƙi, Yau da kanta ta haɗa breakfast, Ladiyo gyaran part ɗin kawai tayi, breakfast ɗin Musa mai gadi ta bawa Ladiyo ta kai masa ita kuma ta shige Bedroom ɗinta, tollet ta shige tayi wanka ta shirya cikin wani koren atamfa wanda aka mata single style sosai atamfar tabi jikinta, ba wani makeup tayi ba sai powder kawai da lipstick da ta shafa, Bedroom ɗin DOCTOR ta shige jin shuru bai fito ba, yana kwance rungume da photo ko tashi baiyi ba da alamu yau baza shi aiki ba, ƙarasawa bakin bed ɗin Falmata tayi ta zauna tana ƙare masa kallo cikin so da ƙauna, ji take tamkar ta kwanta jikin mijinta, sai babu halin hakan saboda gujewa masifar sa, a hankali tasa hanu ta zare photon daga ƙirjinsa ta maida kallon ta zuwa ga photon "JALILA" ta furta a hankali, ajiyesa tayi a gefe tare da tashi ta shige Tollet ɗinsa, wankewa tayi tas tasa air freshener a ciki sannan ta fito daining ta ƙarasa, indomie kawai taci tare da tea ta tashi, Bedroom ɗin ta ta koma ta ɗauki Mayafinta ta saka tare da bag ɗinta, hand out ɗin ta shima ta ɗauka tare da wayarta ta fito, a falo ta tsaya ta rubuta masa a takadda, "NA TAFI SCHOOL SABODA ZAMU FARA TEXT SANNAN ZANBI GIDA NA DUBA JIKIN UMMA." sanda tazo bakin ged ɗin gidan musa ya taho da sauri yana cewa.

" Ranki ya daɗe Hajiya unguwa zaki fita ne haka da safe."

Murmushi Falmata tayi tare da cewa.

" Wallahi school zani Musa, ga wannan takaddar idan DOCTOR ya fito dan Allah ka basa bai tashi a bacci ba, ni kuma zanyi let na tsaya."

Karɓa Musa yayi yana cewa.

" Insha Allah Hajiya zan isar masa a dawo lafiya Allah ya tsare."

Da ameen Falmata ta amsa tana ficewa, sanda ta kusa nufo titi sannan ta tuna da babu kuɗin adaidaita a hanunta, "Ya Salam" ta furta hanunta tasa a jaka ta ɗauko wayarta numbern Maji ta kira, tana ɗagawa tace.

" Kina makarantar ne ko gida."?

Daga can Maji tace.

" Ina school yanzun nan na shigo, wani abune.?"

" Ehh na fito ne kuma babu kuɗin adaidaita a hanuna, akwai kuɗi a hanunki ne, idan na ƙaraso sai na karɓa na basa, nayi let ne babu halin na tsaya ko pos na cire kuɗi."

Murmushi Maji tayi dake zaune gindin wata bishiya ita da Uwani tace.

" Ki hau ki taho akwai kuɗi Amma fa kuyi sauri domin an kusa shiga lecture."

'' Insha Allah yanzu zan ƙaraso."

Ta ƙarasa maganar tana katse kiran, bata juma tsaye bama kuwa sai ga adaidaita, tare sa tayi ta hau tare da cewa University Of MAIDUGURI zaka sauƙe ni, amma zamu shiga ciki.

Ɗari biyu mai adaidaitan yace mata babu musu ta hau, har cikin jami'ar ya kaita, Maji ta kira a waya tare da faɗa mata inda suke, ba'a juma ba Maji ta ƙaraso tana cewa.

" Nawa ne kuɗin nasa."

" 200 Naira" Falmata tace, Maji 500 ta basa ya basu sanji sannan suka jera Maji ne ta dubi Falmata tare da cewa.

" Makarantar nan harta fara mantawa dake, nayi zaton ma bazaki zoba."

" Me zai hanani zuwa Maji, ai tunda nace miki zanzo to zanzo, yanzu inda matsalar take, karatun da aka wuce ni."

Numfashi Maji ta sauƙe tace.

" Gaskiya akwai matsala, amma ba damuwa akwai Allah, ke dai kawai ki dage ki fahimci darasin gaba."

" Insha Allah, ina Uwani ne ban ganku tare ba."

" Wajen ta muka nufa ai yanzu."

" Ok" tace har suka ƙarasa gindin bishiyar da Maji tabar Uwani, zama sukayi uwani tace.

" Wata sabon gani ke kuma baiwar shikenan sai kika mana hijira kika daina zuwa school."

Hararar Uwani Falmata tayi tace.

" Shine kuma baki nemeni ba, kiji ko lafiyata kekam Uwani kikayi wasa igiyar zumunci sai ta zargeki."

Uwani dariya tayi tace.

" Bani da zumunci ko bamu da zumunci ke zumuncin ne dake, ko neman mutane ke kike."?

Dariya sosai Maji tayi tana cewa.

" To kaji har kun fara faɗan naku kenan daga haɗuwar ku gaisuwar da zaku fara kenan."

Falmata cewa tayi.

" Oh mune ma kajin kenan, amma dai kin faɗa mana ba suga, KUMA bashi kikaci sai mun rama ko Uwansis"

" Ƙwarai kuwa kowa ai yaci tuwo damu miya yasha, daram zamu rama."

Dariya Maji tayi tana cewa.

" Oho haɗe min baki kuma zakuyi, shikenan sai dai ku rame ba dai ku rama ba, kinga Falmata tashi mu shiga class time ya cika gara Uwani sai 12 zata shiga lectures ɗin ta."

Tashi sukayi suka bar Uwani a wajen suka shige department ɗinsu, suna shiga class ɗin Kuma SIR AHMAD ya shigo wanda yake ɗaukar su lecture ɗin Chemistry gaishesa sukayi ya amsa yana kai dubansa ga Falmata, sosai yake kallon ta tamkar zai cinyeta, lura da hakan da Falmata tayi ya sata kawar da kanta gefe tana haɗa fuskar ta tamau, Murmushi Maji tayi yanda taga Falmata ta haɗa fuska daidai kunnen Falmata Maji ta mata raɗa.

" Maza da yawa suna bukatar shi kuma wannan shashashan mijin naki yana wulaƙanta ki."

Hararar Maji Falmata tayi tare da ce mata.

" Bana son wulaƙanci mijin nawa kike kira shasha, su dai masu bibiyar matan Auren sune shashashu."

Dariya kawai Maji tayi ta maida hankalin ta ga lectures da ya fara, duk rabin lecture ɗin da Sir Ahmad yake yi hankalinsa yana kan Falmata harya gama ya fita.

Ƙarfe 12 daidai suka fito daga lectures ɗin, a gajiye Falmata ta fito kasancewar ta kwana biyu batayi zama irin na yau ba, waje suka samu suka zauna, Falmata ranta a dagule tace.

" Maji meya kawo HABEEB gidana jiya.?"

Taɓe bakin ta Maji tayi tace.

'' Nine na turo sa?"

" Ke kika turosa akan me zaki turo min shi gidana, kinsan yanzu haka kin haddasa matsala."

Maji cike da mamaki tace.

" Matsala kuma wacce irin matsala, har akwai wata matsala wacce tafi wanda kike ciki a gidan Auren ki.?"

Falmata cikin faɗa tace.

" Hmmm Maji kenan, akwai domin kuwa Allah kaɗai yasan abinda zai faru tsakanin HABEEB da DOCTOR, Tunda yace bazai ƙyale HABEEB ya keta masa haddi, kuma DOCTOR yana da gaskiya HABEEB mahaukaci ne shi da zai shigo gidan matar Aure meye haɗina dashi, nifa nama manta sa a rayuwata, sannan ai kema bai dace ace ki turo sa cikin gida na ba."

Tunda Falmata ta fara Magana Maji take dubanta sanda ta dasa aya sannan tace.

" To uwata tashi ki dakeni akan sakaran mijinki tunda na saka ransa ya ɓaci, sai wani tayar min jijiyar wuya kike kamar wanda zaki dakeni, akan mutumin da baisan darajar ki ba, shi DOCTOR HASSAN ɗin dokar yake bi, ko shima ba sunnar Annabi yake takawa ba, kinga Malama na turo HABEEB ne domin kuwa shine kawai damar da nake dashi na hana mutuwar Auren ki, tunda nasan gabar dake tsakanin HABEEB da DOCTOR har yanzu tana nan sannan muddun DOCTOR yasan cewa har yanzu HABEEB yana sonki zai kuma iya Auren ki idan DOCTOR ya rabu dake, nasan bazai yarda ya rabu dake ba, ko dan kar HABEEB ya Aure ki, sannan DOCTOR babu abinda ya isa ya yiwa HABEEB, Tunda ranki ya ɓaci na ɓatawa ubanki rai kiyi hkr."

Maji ta karasa maganar tana tashi cikin ɓacin rai zata bar wajen, Falmata ta kamo hanunta tana cewa.

" Kiyi hkr ƙawata ki zauna."

" Me zan zauna na miki na zauna kina ɗaga min jijiyar wuya ne saboda mutumin da baisan darajar ki ba."

" Ki daiyi hkr ƙawata ki zauna ki fahimce ni."

Zama Maji tayi sannan Falmata tace.

" Kin kasa fahimta ta, Maji, kinsan yanda nake son Doctor ina gudun abinda zai jamin matsala dashi bana son rabuwa dashi, yanzu kamar wanda yake jirana ina kuskura kaɗan zai samu ƙofar da zai ce zai sakeni shiyasa nake razane da zuwan da HABEEB yayi gidana."

Maji cikin takaici da haushin Falmata tace.

" Zaki rabu dashi sanda ya kashe ki da baƙin ciki, idan aka binne ki, sai naga taya zaki dawo garesa, Falmata wai wani irin makahon so kike yiwa HASSAN meyasa bakya hango aibunsa ne, Falmata anya kuwa akwai zuciya a ƙirjinki, shi namiji girman kai garesa daga sanda ya fahimci Soyayyar da mace take masa yafi wanda yake mata, to daga wannan ranar zai fara takaki saboda yana ganin bazaki iya rabuwa dashi ba, har yanzu Falmata ke ɗalibace a soyayya naga alama ya kamata ki dinga ɓoyewa DOCTOR zalamar Soyayyar ki, ki dinga nuna masa ɓacin ranki domin nemawa kanki yanci, bawai ki tsaya namiji yana cin mutuncin iyayenki da naki ba, wannan ba daidai bane."

Numfashi Falmata ta sauƙe tare da cewa.

" Maji meyasa bakya son Doctor, tun can baya baki sona dashi, baki taɓa faɗar alkairin sa ba sai dai aibunsa, amma ai kema kinsan DOCTOR yana sona wannan al'amari ne kawai ya kawo matsala a tsakanin mu amma ke kullum kina kama hanuna akan hanyar barin rayuwar DOCTOR."

Murmushi Maji tayi tace.

" Ba son Doctor bane bana yi, dama tun baya bai dace da rayuwarki ba, makahuwar Soyayyar sane kawai yasa kika kasa fahimtar hakan, sannan ba aibunsa nake faɗa ba, halinsa nake faɗa, nifa Falmata ina kama hanunki akan hanyar gaskiya, domin inganta rayuwar ki, amma ke ƙoƙarin fisgewa kike zuwa baƙar hanya wacce bata da wajen ɓullewa."

" DOCTOR shine Wanda yafi ko wani namiji dacewa da rayuwata, wannan makahuwar Soyayyar da nake masa ita ake kira Soyayyar gaskiya tunda wahalar da nake sha bata sa na gujesa ba, Maji Hanyar da nake kai itace mai ɓulle min ba hanyar da kike kaini ba."

Murmushi kawai Maji tayi tana kaɗa kanta cike da tausayin Falmata tace.

" Ai bazaki fahimce ni ba Falmata, amma lokaci zaizo sanda zaki ce na faɗa miki amm.............."

Ƙarasowar Wata budurwa wajen da Sallama yasa Maji bata ƙarasa maganar da tayi niyya ba amsawa sukayi budurwar tace.

" Sir Ahmad ne yace wai FATUMA ABUBAKAR BUKAR tazo ta samesa a office ɗinsa."

Kallon Maji Falmata tayi tace ..

" Kije kice bazanzo ba"

Maji cewa tayi.

" Kije kice tana zuwa."

Juyawa budurwar tayi ta tafi, Falmata zatayi magana Maji ta ɗaga mata hanu.

" Ni ba jahila bace nasan ke matar Aure ce, amma ki sani shi malamin kine bai kuma furta miki yana sonki ba, kuma kin kwana biyu bakya zuwa makaranta dan haka baki san kiran da yake miki ba, kije kiji, ina jiran ki sai kizo mu wuce gida tunda kince gidan ku zaki wuce."

Falmata bata ce komai ba ta tashi ta nufi office ɗin da Sallama ta shiga amsawa yayi yana gyara zaman glass ɗin idanunsa ya mata nuni da ta zauna.

" Sir gani ance kana kira na."

Murmushi ya saki tare da cewa.

" Eh ni nayi kiran ki, me yake hanaki zuwa makaranta kwana biyu."

" Sir bani da lafiya shiyasa."

" Subabanallah sannu, ai ban sani ba da naje na duba ki."

Da sauri ta ɗago kanta ta kallesa tare da cewa.

" Sir zan iya tafiya ana jira nane."

" A'a bamuyi Maganar da yasa na kiraki ba "..


" To sir ina sauraronka sauri nake."

Murmushi ya saki tare da zare glass ɗin idanunsa yace.

" I love You fatuma, na juma ina sonki, tun sanda na fara ganinki a cikin school ɗin nan Allah ya jarabceni da sonki, kuma Auren ki nake son nayi dan Allah ki yadda ki aureni."


A razane ta ɗago kai ta kallesa zuciyarta na bugawa dam!!! Dam!!! Dam!!!!




Tirƙashi wai dama AHMAD baisan Falmata tana da Aure bane?



Ku biyoni domin jin amsar ku.



Ku biya ku karanta cikin kwanciyar hankali.


*Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari*

*Dan Allah masu turo min VTU su daina numbobin katin kawai nake buƙata ko transfer to bank account ɗina🤲🏻*


Vote
Share
And Comment



*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*



*(UMMU NASMAH CE)*
[9/4, 2:43 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤️ *Love and romantic and funny story* ❤️



*Na*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa

Please Login or Register in order to submit comment