Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da SUPER MARKET ɗin da kaje ne shikenan harka gaji."

" Oh Momy waya faɗa miki SUPER MARKET kawai naje, na jewa Daddy aika fa can GIWA BARECK, daga nan na wuce masa har HAUSARI kafin fa na wuce SUPER MARKET ɗin."

Murmushi Momy ta saka tare da cewa.

" Kuma duka tafiyar ƙafa kayi ko? Kai dai HABEEB wannan son jiki naka yana damuna."

Dariya kawai HABEEB yayi, Wasila da Hajara ne suka sauƙo daga step ɗin Wasila sai bin HABEEB take da wani shu'umin kallo, HABEEB ya ganta sarai amma ya kawar da kansa gefe yayi a rayuwarsa ya tsani Wasila baya son mace wacce sam bata da kamun kai, amma sai dai sam baya ƙuntata mata, saboda duk yanda mutum yake sonka yafi maƙiyin ka, sai baya sake mata fuska, Hajara ce ta ƙaraso tare da cewa.

" Bros ina takalmin nawa."

Murmushi ya saki tare da cewa.

" Naje SUPER MARKET amma dai ban sayo miki takalmin ba, saboda banga wanda ya min kyau ba."

Tura bakinta Hajara tayi tana kallon, takalmin dake gefen sa a cikin leda tace.

" To yaya wannan takalmin fa ba gashi ba."

" Karki kuskura ki saka ranki a wannan takalmin ba naki bane."

Ƙunƙuni Hajara ta hauyi tace.

" Momy kinji Bros ko."

Momy murmushi tayi tace.

" HABEEB!!! Idan ba ita ka sayowa wannan takalmin ba, to wa ka sayawa.?"

Ta jefa masa tambayar, shima HABEEB murmushi ya saki tare da cewa.

" Budurwa ta na sayawa Momy wacce nake matuƙar sonta, shine kyautar farko da zan fara mata, amma fa sai dai bata san ina sonta ba."

Wasila wani murmushi ta saki ita duk a zaton ta itace wacce yake so ɗin, murmushi Momy ta saki tare da cewa....................."








Ki biya kuɗin ki yafi miki sauƙi da ki karanta abinda ba naki ba, idan kina buƙata ki neme ni ta wannan numbern 08147537180.


Kuyi hkr yau banyi editing ba saboda bani ishashen time.



*UMMU NASMAH CE✍🏻*
[9/17, 4:01 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 45 to 46*


*Wannan shafin naki ne Aunty na, Aunty HAUWA maman uswan, Allah ya ƙarawa zuri'a albarka ya ƙaro miki tarin farin ciki, a cikin gidan ki🤲🏻*




________ " UMMA jiya na haɗu da kawu Dauda a kasuwa yake sanar dani cewa na faɗa miki Aunty Yakura bata jin daɗin jikinta sosai."

" Subabanallah yakura jikin yaƙi daɗi kenan innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un to zan shirya naje gobe da safe yanzu dare yayi da safe insha Allah zanje Allah Ya bata lafiya."

Da ameen Aunty JALILA ta amsa sunan zaune BABA ya shigo shida DOCTOR, zama sukayi DOCTOR yace.

" Umma sannu da hutawa."

" Yauwa sannu, yaushe kuka dawo daga SUPER MARKET ɗin, banji ɗuriyar kuba dukkan ku kaida Falmatan."

" Umma tun ɗazu da la'asar muka dawo, mun shige wajen Aunty YANA ne, kuɗin ya ciro cikin aljihun sa ya miƙawa Umma 20k ɗinta yace, Umma bamuyi amfani da kuɗin naki ba, HABEEB wannan Abokin nawa wanda mukayi primary dashi, shine ya biya mana kuɗin."

Murmushi Umma ta saki tare da cewa.

" Masha Allah na tuno da Habibu, dama suna garin nan nayi zaton ai sun bar Maiduguri, ka riƙe kuɗin a hanunka zasu maka amfani."


" Eh suna nan Umma yace ma zaizo gobe da safe idan Allah ya kaimu."

Baba ne ya saki murmushi tare da cewa.

Wai ni yaushe zaka fara fita kasuwa ne, Hassan nayi nayi da kai kaƙi kasuwancin nan kai lallai sai aikin gomnati ko, kuma ba lallai bane a yanzu ka samu aikin gomnati, idan ka gama karatun tunda ba ɗaurin gindi bane da kai."

Baba ya ƙarasa maganar cikin faɗa, Umma itama cewa tayi.

" Abinda nake faɗa masa kenan kullum Baban JALILA, amma kunnen ƙashi garesa, yanzu kai ba abun kunya bane a wajen ka, kuɗin da zaka kashe ma sai ka tambaya an baka."

Haɗa fuska DOCTOR yayi yace.

" Ni Umma kubar Maganar nan kawai, ku min addu'a Allah ya bani aiki idan na gama karatu na, kuma fa Baba kaima ka sani duk wanda ya karanci likitanci to yana da aiki, kawai kumin fatan Nasara cikin karatu na."

Aunty JALILA ce tace.

" Ƙwarai kuwa Baba, likita da aikinsa yake fitowa kuma Umma ai ɗan abinda kuke basa bazai gagareku ba, na ɗan lokaci kaɗan ne, wata rana shima sai dai ya baku.''

Umma cikin faɗa take cewa Aunty JALILA.

" To uwar marassa son gaskiya, da zarar an taɓo Hassan shikenan sai ki nemo hanyar karesa koda kuwa shine marar gaskiya, Mtsss kega mai ɗan uwa ko."

Murmushi Baba yayi tare da cewa.

" Jalila kenan Baki san laifin ɗan uwanki, kullum kina cikin karesa, Ubangijin Allah ya ƙara muku son junan ku, Umma ya kalla tare da cewa, GOBE kisa Jalila taje gidan AJIRAM ta dawo min FANNA cikin gidan nan, nifa gidan nan baya min daɗi idan babu Auta na."


Sallamar kawu Dauda sukaji Aunty JALILA ce ta amsa sallamar, shigowa kawu Dauda yayi ya zauna ya miƙawa Baba hanu sukayi musabaha, Umma ce tace.

" Ya Dauda inda dabtu" ta gaishe sa da harshen kanuri amsawa yayi da.

" Dabtu beji, baki san yakura bata da lafiya bane jikin nata babu daɗi sosai fa."

" Yanzu JALILA take sanar dani, Insha Allah gobe zanje na dubata, tana gida ne ko asibiti."?

" Tana gida basu kaita asibiti ba."

Babane yace

" Allah ya bata lafiya, amma ya kamata su Kaita asibiti sabida ciwon ta kamar bana maganin gida bane."

" Hakane amma Bana ya hana su Kaita."

DOCTOR ne ya miƙa masa hanu suka gaisa kafin DOCTOR ya miƙe yace.

" Umma bari naje na kwanta sai da safe."

Da Allah ya tashe mu lafiya Umma ta amsa, sannan DOCTOR ya fice, Aunty Jalila ma ficewa tayi, ya saura daga Baba sai kawu Dauda da Umma, can Baba ma ya tashi ya basu waje ko zasuyi zancen su na ɗan uwa da ɗan uwa, bayan fitan Baba Umma tace wa Kawu Dauda.

" Ya Dauda naji labarin cewa ka saida min da gonata guda ɗaya ta gado, meyasa zaka saida min ba tare da izini na ba, dan Allah Ya Dauda me kake yi da kuɗin ne kam, ka gama ƙarar da gonakin ka da duk wani abinda ka samu na gadon mahaifin mu, sannan banga abinda kayi da kuɗin ba, komai sun lalace maka, sannan yanzu Kuma ka dawo kan nawa gaskiya bazai yiwu ba, 3million fa ka saida gonar nan, Naira biyar baka kawo min ba, gabaki ɗaya kaje ka hallakar da kuɗin daga wannan ya tsaya haka karka ƙara sai da min kadarata, Idan kuma baka daina ba zan karɓe takadduna daga hanunka na dawo dasu hanun mijina saboda darajar ƴan uwan taka yasa na danƙa maka su."

Umma ta ƙarasa maganar cikin ɓacin rai, kawu Dauda cike da jin haushi shima yace.

" Lallai Yamuram kin isa yanzu ni kike ɗagawa murya, ko kin manta ina sama dake, saboda kawai na sayar da gonarki gudu ɗaya a cikin Goma, shine kike min faɗa tamkar wata uwata, Yamuram ko kin manta baki da wani ɗan uwan daya wuce ni mu biyu fa rak uwar mu da ubanmu suka haifa a duniya yanzu ashe dama bazaki rufa min asiri ba idan bani dashi, yayi kyau na gode laifi nane dana taɓa kayanki."

" Ni fa ya Dauda ba abinda nake nufi ba kenan, gani nayi banga wani abu mai mahimmanci wanda kayi da kuɗin ba, shiyasa nayi Magana amma Allah ya baka haƙuri."

Tsuka Kawu Dauda yayi tare da tashi a zuciye ya fice, Umma a fili ta furta.

" Ikon Allah mutum da haƙƙinsa bai isa yayi magana ba, shikenan sai cibi ya zama ƙari, amma dai wallahi bazan bari ka hallakar min dukiya ba kamar yadda ka hallakar da naka."

Ta ƙarasa maganar tana tashi ta shige Bedroom ɗinta.

Kawu Dauda ransa a matuƙar ɓace ya shiga cikin gidan nasa, Jummai tana zaune a barandar gidan, zama yayi yana sakin tsaki, Jummai ɗago kanta tayi tace.

" Baban Musa mai yake faruwa ka shigo min cikin gida tamkar wanda akayiwa mutuwa."?

" Hmmm Jummai wai ni YAMURAM tasa a gaba take min faɗa tamkar zata cinye ni akan kuɗin gonar ta, alhakin ni bani na ci kuɗin gonar nan ba, ko naira biyar baki bani duka kika karɓe kuɗin nan, to wai ma me kikayi da kuɗin da kika sani na saida gonar ta."

Miƙewa tsaye Jummai tayi tare da kama kunkumin ta cike da masifa tace.

" Eye Lallai Baban Musa, ni kake tuhuma me nayi da kuɗin , yaushe ka samu wannan bakin, to bazan faɗa ba kazo ka matseni sai na faɗa maka, kuma wallahi sisi bazan baka ba a cikin kuɗin nan."

Ta ƙarisa Maganar tana daka masa harara, cike da tsoro Kawu Dauda yace.

" Allah ya baki haƙuri, dan Allah kiyi hakuri."

Tsuka taja tare da shigewa cikin ɗaki tana masifa, tashi kawu Dauda yayi yana bata hkr yabi Bayan ta tamkar wata uwarsa.




(Ai kin sihiri kenan, Jummai macece wacce bata da tsoron Allah ko kaɗan, gidan boka kuma ta mai dashi tamkar gidan uwarta, shima kansa kawu Dauda ta shanyesa sai abinda tace yake yi, duk abinda tace yayi baya mata musu haka zai aikata.)

(Kuji tsoron Allah mata, meye ribarki ƴar uwa idan kin yiwa mijinki sihiri shin bakya tsoron lahirar kine, ko kin manta wannan duniyar ba matabbata bane, kuji tsoron Allah matan zamani)


Muna hidimar biki ne, mu haɗu daku next page, i love You MASOYANA😘😘😘😘







Ki biya kuɗin ki yafi miki sauƙi fiye da ki karanta abinda ba gumin ki ba, neme ni ta nan domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180






Ummu Nasmah ce✍🏻
[9/18, 11:42 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 47 to 48*




________✍🏻 Har uwar ɗaka Kawu Dauda yabi Jummai cike da damuwa yake bata haƙuri, ai kuwa Jummai cikin ɗaga Murya tace masa.

" Naji na haƙura amma ka sani daga yau karka kuskura koda wasa ka sake tuhumata, domin kuwa ina nema mana yanda zamu rufawa kanmu ne asiri, wannan kuɗin gonar da kake gani Kabiru na bawa kuɗin yaje ya samu fili mai kyau ya saya mana gini zamuyi, mubar wannan shegen gidan gadon na laka, muma muje mu shiga bulo-da bulo, aha Tunda kai kaje ka hallakar da naka kadarorin a caca duk an cinye ka, to kuma wallahi duk wani buƙatu na daya tashi dole kaje ka kama kadarar wannan shegiyar ƙanwar taka ka sayar ka bani kuɗin haka kuma nan da ƙarshen wata ka nemo 1million ma'ana kaje ka ƙara ɗaukar gonar tata ka sayar ka kawo kuɗin zamu ɗaga gini dole muma A.c nan musha ta muci jar miya muci kaji, ka ji ko baka jiba."

Kamar wawa haka kawu Dauda yake kaɗawa Jummai kai, kafin yace.

" Naji insha Allah zan kawo miki, ina dai kin huce yanzu bana son ki dinga fushi dani."

Murmushin makirci Jummai ta saki tare da cewa.

" Yauwa ko kaifa mai gidana ai ban isa fushi da kai ba, kawai bana son abinda kake min ne, bari naje na kawo maka abincin ka."

Ficewa tayi ta nufi Kitchen ABINCIN kuwa ta kawo masa sai kuma ta zauna suna fira kaɗan kaɗan.


**************


Washe gari da safe, misalin ƙarfe 10 Falmata ta fito cikin shirin makarantar islamiyya da take zuwa huffaz fannin mahaddata, hanunta riƙe da ƙur'aninta sai kuma wayarta Nokia rakani kashi, ɗakin Hajja ta fara shiga ta samu tana lazimi shi kuma Bulama yana kwance akan doguwar kujerar Hajja yana bacci, kusa da Hajja ta ƙarasa tare da gaisheta amsawa Hajja tayi tana cewa.

" Makaranta zaki tafi ne."?

Kaɗa mata kai Falmata tayi tace.

" Ehh Hajja makaranta zanje ni, wannan tsohon ƙwaraɓaɓɓen mijin naki kam bacci yake kya gaishe sa idan ya farka."

Murmushi Hajja tayi tare da cewa

" Ai kuwa wannan tsohon yafi waɗannan samarin naku na yanzu, kina kallon tsayayyen namiji mai zati da kwarjini, adalin shugaba, ina zaki haɗa sa da lusari samarin nan naku na zamani."

Ta ƙarasa maganar tana kallon BULAMA dake baccin sa baima san suna yiba dariya sosai Falmata tasa ta nuna Bulama da yatsa tace.

" Shi wannan ɗinne tsayayyen namiji mai zati 🤣 haba dai Hajja kina kallon abu duk ya kwararraɓe ya fice hayyacin sa, kamar a ɗauka a kaisa juji a yasar, wannan ai sauran ƙasa ne, jira kawai muke ya sheƙe muci gumba da masa ranar sadakar ukun sa muyi rawa mu girgije."

Ta ƙarasa maganar tana ficewa da gudu bakin ta ɗauke da dariya, Hajja cewa tayi

" Ja'ira da ki tsaya mana kiga yanda zanci mutumci ki, kyayi rawa tunda ɗan iska ne ya mutu."

Ita dai Falmata tuni ta shige ɗakin Aunty YANA tana zaune tana shan koko da ƙosai kusa da ita Falmata ta zauna tare da saka hanu cikin ƙosan tace.

" Mama kin tashi lafiya."

" Lafiya lau Falmata, ya kika makara keda zaki tafi 9:30 kene har 10:19 kin san dai bana son wannan lattin da kike ko."

" Mama maji nake jira tun ɗazu bata ƙaraso ba, amma dai yanzu munyi waya tace gata tahowa, ina Baba Bukkar Mama."

Taɓe bakinta Aunty YANA tayi tace.

" Yana ƙofar gida suna karin kumallo shida baban Hassan."

Da to Falmata ta amsa tana kai ƙosai bakinta sallama Maji tayi ta shigo cikin ɗakin Aunty YANA, bata zauna ba ta gaishe da Aunty YANA cikin sauri, Aunty YANA tana murmushi ta amsa tare da cewa.

" Kunyi latti yau, amm maza to Falmata tashi ku tafi, kici ƙosan mana Maji."

" A'a Mama na ƙoshi, yanzu na karya."

Falmata tsumman dake gefen Aunty YANA ta ɗauka ta goge hanunta sannan ta ɗauki qur'anin ta, sallama sukayi Aunty YANA, Albarka ta saka musu tare da addu'a suka fita, Falmata ne ta dubi Maji tace.

" Ƙawata zafa mu shiga sashin su DOCTOR na gaishe da Umma sai mu wuce."

Maji da to ta amsa, suka shiga cikin part ɗin ɗakin Umma rufe da key da alamu yau tayi sammakon fita unguwa, fitowa sukayi, har sunzo zaure Falmata ta doshi ɗakin DOCTOR Maji tsuka taja tare da cewa.

" Haba Falmata wai meye haka ne kam kinfa san munyi let, amma shine kike faman karkata zuwa ɗakin wannan uban ƴan girman kan da zafin zuciya, Allah kika juma tafiyata zanyi sai dai kuma mu haɗu a school."

" Hmm zan shiga wajen maƙiyin kiba ai dole ki hasala, to kwantar da hankalin ki, yanzu zan fito."

Ta ƙarasa Maganar tana taɓe bakin ta, Falmata ɗakin ta tura tare da cewa.

" Hi Doctor na"

da murmushi saman fuskarsa ya ɗago ya zuba mata narkakkun idanunsa waɗanda suke kama da na mai bacci, hanunsa riƙe da qur'ani yana karatu murmushi ya saki tare ce mata.

" My dear na, kin tashi lafiya."

" Lafiya lau Alhamdulillah my dear na, kadai school zaki wuce."

" Eh school zan shige, naga Umma ɗakinta a rufe da key, har Aunty JALILA ma bata nan."

Murmushi DOCTOR ya saki yace.

" Umma ta tafi, gidan su unguwar mandagori."

" To Allah ya dawo da ita lafiya, bari na shige Maji tana jira na."

Falmata harta juya taji muryar DOCTOR yana mata addu'a.

" *Ina roƙon Allah ya yiwa ƙwaƙwalwar ki Albarka fiye da ƙoƙarin ki,yayi wa rayuwarki albarka fiye da hasken dake cikin rayuwarki yayi miki rahama fiye da tuban ki yaji ƙanki fiye da tunaninki ya ƙara haskaka rayuwarki fiye da hasken ki ya karɓi ibadunki fiye da ƙwazonki, Allah ya miki jalabi da jalabin dake cikin alƙur'ani, Allah ya haskaka miki hanyarki Allah ya yiwa rayuwarki albarka."

Wani irin lumshe idanunta Falmata tayi tana jin wani farin ciki na shiga ranta, wani irin ƙaunar ɗan uwan nata ne taji ya ƙara tsirga mata a cikin ranta, fuskarta ɗauke da murmushi ta juyo tare da cewa.

" Ameen DOCTOR na, Tabbas yau ka cika zuciyata da farin ciki, zan wuni cikin walwala da farin ciki, ina sonka DOCTOR na, ba iya Soyayyar ƴan uwan taka ba, soyayya nake maka wacce nake fatan na kasance a cikin ƙarƙashin inuwar Auren ka, Allah yasa ban makara ba, wajen bayyana Soyayyata gareka."

Murmushi shima DOCTOR ya saki zuciyarsa cike da nishaɗi yace.

" Tabbas Soyayyar ki karɓaɓɓiya ce a gareni, Allah ya hallici zuciyata ce saboda ke, ina ƙaunar ki fiye da yanda kike ƙaunata, ki saka a Ranki DOCTOR naki, KUMA zai kasance dake har abada."

Murmushin farin ciki Falmata ta saka tare da ficewa cikin sauri, dariya DOCTOR yayi yana jin wani irin Soyayyar ta mai ƙarfi tana ƙara bijirowa zuciyarsa, murmushin ya kara saki tare da furta.

" Ashe bani kaɗai nake dakon Soyayyar ta ba, Allah ka cika mana burin mu."


Tafe suke Falmata sai famar murmushi take, ganin murmushin da Falmata take yayi yawa yasa Maji cewa.

" Ƙawata wai farin cikin me kike haka naga sai sakin murmushi kike yiwa wacce aka yiwa kyautar zuciya."

Murmushi Falmata ta saki mai sauti tace.

" Kamar kuwa kin sani ƙawata kyautar zuciyar na, samu yau dai na daure na furtawa DOCTOR gaskiyar abinda yake zuciyata ashe bani kaɗai nake sonsa ba, shima akwai ajiyar soyayyata a zuciyarsa, yau ina cikin farin ciki DOCTOR ya amshi soyayyata."

Ta ƙarasa maganar cike da farin ciki mai yawa, Maji tsuka taja kafin tace.

" Wallahi kin bada mata, meyasa kika kasa haƙuri shi ya furta miki cewa yana sonki da bakin sa, mazan yanzu sune ma su kace suna sonka ya ka ƙare dasu bare kuma kaine ka furta musu, hmmm Falmata duk randa kika fara nunawa namiji cewa kece kike sonsa, wallahi daga baya sai kin fuskanci ƙalubale, zai miki duk abinda yaga dama saboda yana tunanin kina sonsa bazaki iya rabuwa dashi ba, bare kuma namiji Irin Hassan mai Izza da zafin zuciya ga saurin fusata, gaskiya banso ace kece kika fara furta masa soyayya ba , kinyi likin kuma zakice na faɗa miki."

Numfashi Falmata taja tare da furta.

" Hmmm, DOCTOR ba irin mazan da kike tunani bane, tun ina zanin goyo yake nuna min kulawa da Soyayya, da ƙauna da shaƙuwarsa na taso, yana nuna min kulawa da Soyayya, yau dana furta masa kalmar so bai jaba ya amsa min tare da karɓar soyayyata hanu biyu sannan karki manta DOCTOR fa ɗan uwana ne, taya kike tunanin zai juya min baya, ko kaɗan ina da tabbas akan DOCTOR bazai taɓa juyawa soyayyata baya ba , Kuma na Tabbata zan samu farin ciki mai ɗaurewa a gidan sa har ƙarshen Rayuwata."

Murmushi Maji ta saki tana duban Falmata duba na baki da hankali kafin tace

" Ba'a shaidar namiji, koda kuwa uwa ɗaya uba ɗaya kuka fito, nikam Falmata banso haɗuwar Soyayyar ki da Hassan ba, domin kuwa hakinku akwai banbanci, ina tsoron ya cutar da Rayuwar ki."

" Maji kenan, kedai na fuskanci bakya son Doctor na rasa meya tarewa rayuwarki, dan Allah Maji ki barni da abinda nake so, karki zamo silar shiga tsakanina da Soyayyata, dan Allah karki zamo silar hawaye na, ki barni da Soyayyata."

" Ni ban tsani Hassan sai dai kawai halinsa ne bana so, duk mutum mai saurin fusata da zafin zuciya bashi da daɗin zama, domin kuwa duk kuskuren da zai faru tsakanin ka dashi bazai tsaya bincike ba, hukunci kawai zai yanke cikin zafin rai, ni bazan taɓa zama silar kukan ki ba a rayuwata, sai dai na kasance miki silar dariyar ki, Allah ya tabbatar da alkairin dake cikin Soyayyar Hassan."

Murmushi Falmata ta saki Daidai lokacin da suka iso cikin makarantar.




***********



Tun ɗazu ya karbo takaddar vacancy daga hanun Daddyn nasa, Darect gidan su DOCTOR ya nufa, a ƙofar gida ya tsaya tare da ciro wayarsa zai kira DOCTOR sai ga su Umma sun dawo daga unguwa, murmushi HABEEB ya saki tare da sunkuyawa ya gaishe da Umma, cikin fara'a Umma tace.

" Ikon Allah wa nake gani kamar Habibu."

Dariya HABEEB yayi yace.

" Nine Umma."

Aunty JALILA dariya tayi tare da cewa.

" HABEEB kana duniyar nan, ka manta damu haka "

Murmushi ya saki tare da cewa.

" Aunty JALILA ai bazan taɓa mantawa dake ba a cikin rayuwata, yanda muka sha goyo da kuma kyautar kuɗin tara a hanunki."

Dukkan su dariya sukayi Umma tace.

" To mu shiga cikin gidan ko, abokin naka ina ga yana ciki."

Da to ya amsa tare da sakawa motarsa security suka shiga cikin gidan, Aunty JALILA nunawa HABEEB ɗakin DOCTOR yayi dake cikin sauron gidan, da Sallama HABEEB ya shiga ɗago kansa yayi yana murmushi ya amsa tare da cewa.

" Ka iso kenan.?"

Zama HABEEB yayi bakin katifar DOCTOR yace.

" Ehh gani kuwa, ina Saif ɗin.?"

" Saif yana hanya yanzu zai iso insha Allah, kun gaisa da Umma ne."

" Ehh mun gaisa tare ma muka shigo da ita, amma zan kara shiga na gaisheta idan muka fita......................"






Ki biya kuɗin ki kisha karatu cikin nutsuwa yafi miki sauƙi fiye da ki karanta abinda ba gumin ki ba, ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki, 08147537180.








*ALƘALAMIN UMMU NASMAH CE✍🏻*
[9/19, 10:57 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 49 to 50*






_________✍🏻 " Okay shikenan, bari na sake kiran Saif ɗin naji yana inane haka har yanzu bai ƙaraso ba."

Ya ƙarasa maganar yana ɗaukar wayarsa HABEEB cewa yayi.

" A'a barshi karka kirasa tunda yace maka ya taho kam, ai sai mu jirasa ko, yauwa HASSAN akwai tambayar da zan maka dan Allah."

" Okay ina sauraranka."

Cewar DOCTOR

" Ni kam wai Aunty JALILA har yanzun batayi Aure bane, naga sa'ar Aunty Suwaiban mune ita kuwa yanzu yaranta ma har huɗu."

Ɗan shuru DOCTOR yayi, kafin cike da damuwa yace.

" Eh batayi Aure ba, har yanzu, ni kaina rashin Auren Aunty JALILA yana sani cikin tashin hankali, babu wanda ya taɓa zuwa yace yana sonta, sai da Baba ya nemo wani ɗan amininsa ya haɗasu har an musu baiko daga baya ya dawo yace ya fasa Auren, ita kanta Aunty kullum cikin damuwa take, hmmm kwanaki cemin tayi ita ta haƙura da Aure ta ciresa cikin ranta, da ina da yanda zanyi dana nemowa Aunty JALILA miji itama tayi Auren nan, ta shiga tarihi."

Cike da tausayin ƴar uwar tasa ya ƙarasa magana, HABEEB cike da mamaki tare da al'ajabi ya furta.

" What!!!! Hassan da gaske kake min Maganar nan, Aunty JALILA ce ta rasa mijin Aure, kaico lallai maza basu san wanda zasu Aura ba, samun mace irin Aunty JALILA ai abune mai matuƙar wahala.?"

" Ƙwarai kuwa HABEEB Aunty JALILA har yanzu batayi Aure ba.?"

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati!!!! Yanzu Aunty JALILA ce ta rasa mijin Aure mace mai ilimi tarbiyya tare da cikakken zati, me Aunty JALILA ta ragu dashi tana da kyaun da namiji zai sota tana da tarbiyya, to meta gaza daahi za'a ƙita idan ba jarabawa ta Ubangiji ba kowa da yanda yake zarabtar sa, Tabbas ita kuma tata jarrabawar kenan, Hassan ina son na kawowa Aunty JALILA mijin Aure idan har zata yarda, saboda akwai wani uncle ɗina ƙanin momy na da yace Momy ta sama masa matar Aure, yayi Auren farko bai dace ba, ƙarshe ma dai sun rabu dashi da matar, suna ƴa ɗaya a tsakanin su, zamu tattauna da Momy insha Allah zaizo Wajen ta, sai dai sirri zamuyi da kai dan Allah karka sanar da Aunty JALILA nine na kawo mata miji nafi son yazo mata a shine ya ganta yake so, dan Allah ko Umma karka sanar da wannan maganar pls abokina."

Ajiyar zuciya DOCTOR ya sauƙe tare da furta, harna rasa da bakin da zan maka godiya HABEEB idan kamin haka Tabbas bazan taɓa mantawa da kai ba a cikin rayuwata."

Murmushi kawai HABEEB yayi Saif ne ya shigo da Sallama yana dariya tare da cewa HABEEB.

" Shegen gari wato dai ka samu

Please Login or Register in order to submit comment