Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a dace, tunda ciwon nata ba na asibiti bane, sannan ance yana bada taimako sosai mussaman ga mutanen da suka ɓata aka nemesu aka rasa, kaga sai mu masa zancen ɓatar Baba da Jalila ko Allah Zaisa mu dace."

Shuru Doctor Hassan yayi yana kallon Umma dake kwance tana jan Numfashin ta da ƙyar, sosai yake jin tausayin Mahaifiyar tasa wani sa'in idan ciwon ya tashi mata kamar ciwon hauka haka zata dinga fisgar gashin kanta tana ƙoƙarin ciresa daga kanta ko kuma ta dinga ƙoƙarin zata cire kayan jikinta, wani sa'in kuma numfashin tane yake ɗaukewa, ajiyar Zuciya ya sauƙe yana duban AJIRAM yace.

" Okey zan tuntuɓi bellon naji yanda abun yake, idan har malamin Allah da Annabi ne bana shirka ba, to zamuje mu gwada, zamu kai Umma koma inane muddun zata samu lafiya, Allah ya baki lafiya Umma yasa ƙaffara ne, Allah ya yassare miki wannan ciwon Umma na."

Ya ƙarasa maganar cike da tausayin halin da mahaifiyar tasa take ciki sannan ya jefawa AJIRAM tambaya.

" AJIRAM yaushe zaki koma gidan ki ne, dan ya kamata ki koma kar mijinki ya ga kamar mun masa rashin adalci, zan ɗauko *HAJJO* zata zo ta zauna da Ita kafin Allah ya bata Lafiya tunda ita tana zaune a gida babu aure mijinta ya rasu ina ga hakan zaifi ko, ni dama *HAJJA MERO* ta bani izini tuni da na mayar da ita gidana, to ta hana na rasa me wannan tsohuwar take nufi.?"

AJIRAM duban ɗan uwannata tayi cike da tausayin kansu tace.

" Yaya idan banyiwa Mahaifiyata jinya ba, waye zai Mata, shima idan har ya kasa min uziri akan mahaifiyata, bai min adalci ba, mu Huɗu ne kawai ƴaƴan data haifa daga Aunty Jalila sai kai saini sai kuma FANNA kai namiji bazaka iya mata jinya ba, domin ba komai bane zaka iya mata a matsayin ka na namiji, FANNA kuma tayi ƙanƙanta ga ɗaukar ɗawainiyar jinyar mahaifiyar mu, kaga dole ne a kaina, na jinyace ta, Amma babu damuwa idan har HAJJO zata yarda domin kuwa duk ɗaya muke, tunda itama hajjo Ƴace a wajen Umma, ƴar ƙanwar Umma ne, kaje ka tuntuɓeta idan ta amince sai na koma gidan nawa amma dole kullum nazo na dinga duba umma."

Numfashi Doctor ya sauƙe yace.

" Hmmm!!! Ba damuwa insha Allah Hajjo bata da matsala zata amince, mu cigaba da addu'a Allah ya kawowa Umma sauƙi cikin gaggawa."

" Ameeen yaya, FANNA tashi ki ɗauki tsintsiya ki share cikin gidan nan."

Da to FANNA ta amsa sannan ta tashi ta ɗauki tsintsiya ta hau shara, Doctor Hassan tashi yayi tare da ciro kuɗi masu yawa ya bawa AJIRAM yace.

" Gashi ki riƙe a hanunki ko akwai Abunda zaku buƙata koda bana kusa, munyi magana da malam Sani ga wannan kuɗin kuma ki basa, yace zasuyi sauƙar ƙur'ani gobe suna so zasuyi yanka sai ki basa idan ya aiko, sannan ki tabbatar kin bata maganinta da zarar lokaci ya cika, Bari naje na gaishe da *HAJJA* daga can zan wuce Hospital insha Allah zuwa dare zanzo naga jikin nata."

" To yaya a dawo lafiya Allah ya tsareka."

" Ameeen AJIRAM."

A tsakar gidan ya tsaya tare da kamo kunnen FANNA ya murɗe, ɗan ƙara ta saki sakamakon jin zafin da tayi, cemata yayi.

" Ke ba!!! Ina baki jin magana ta ko, nace ki daina biye musu kuna hayaniya baki ji ko, to daga yau na sake jin kunyi faɗa da wani cikin gidan nan, ko ranki sai ɓaci, kinji ko bakiji ba."?

Ya mata Tambayar yana zaro mata Ido tare da sake mata kunnen, bakin ta ta tura tace.

" Naji yaya bazan sake ba."

Ficewa yayi, FANNA ta tura baki tana cewa.

" Allah bazan ƙyale duk wanda ya zagi Umma na, ba sai dai ka kasheni yaya amma duk wanda ya zageta nima sai na zagesa ehe.''


Sashin su matar tasa ya nufa wajen kakarsu mahaifiyar Baban su, wanda take zaune sashin su matar tasa, *AUNTY YANA* tana zaune ita da Mairama tana tankaɗen garin tuwo, ya shigo ko Sallama babu, kansa tsaye zai shige ko inda suke bai kalla ba, ɗago kanta Aunty yana tayi ta dubesa cike da jin haushin rainin daya mata, kamar ba Uwar matar sa ba, ɗafa tayi tare da girgiza kai ta tashi tare da tare gabansa tana cewa.

" Tsaya ƙaramin marar kunya, marar mutunci"

Tsayawa Doctor Yayi ba tare daya kalleta ba, nan ma ya tsaya ne saboda ta tari gabansa, hanu ta miƙa masa tare da cewa.

" Bani Takardar sakin ƴata, mun gaji da Auren tsiya Auren da babu mutunci Auren tarkace dan haka sakar min ƴata idan kana da zuciya nacaccen banza kawai marar zuciya."

Runtse idonsa Doctor Yayi yana jin wani irin tsanar surkar tasa yana ƙara shiga cikin zuciyarsa, gefen ta ya matsa zai raɓe ya shiga ta ƙara matsawa ta taresa tana cigaba da cewa.

" Nace ka Sakar min ƴata ko, kai wani irin marar zuciya ne kam, ka saketa, ta fara gajiya da ganin baƙin cikin ka, dan wallahi bazan tsaya na zuba ido ina kallo ka kashe min yarinya ba, Dan haka sakar min ita."

Dariya maganar ta, taso bawa Doctor, idanunsa ya ɗago da suka sauya kala ya fara mayarwa Surkar tasa magana son ransa kamar wanda yake magana da sa'arsa, wannan shine karo na farko daya fara kiranta da sunanta darect ba tare daya lulluɓe ba.

" *YANA* ya kamata zuwa yanzu ace kin fita a hanya ta, ki daina garajen tare min gabana domin kuwa daf nake dana tureki ki faɗi har ƙasa muddun baki fita cikin rayuwata ba, ƴarki kuma nace bazan saketa ba, sai randa ta yanki jiki ta faɗi hawan jini ya kayar da ita ko kuma ciwon zuciya ya kamata, a wannan ranar sai kizo zan baki takaddar ƴarki, sannan ina miki Albishir da cewa yanzu ma *FALMATA* ta fara ƙunsar baƙin ciki a cikin gida na."

AUNTY YANA sake baki da hanci tayi tana kallon Doctor, wai yau ita *HASSAN* yake kallon tsabar idonta yake faɗa mata maganar da yake so, mutumin da a baya yake mata biyayya tamkar uwar da ta haifesa yau shine yake neman zaginta haushi ne yasa ta cakwami wuyan rigarsa tana cewa.

" Idan ka fasa yasar dani a ƙasa ka raina Uwarka *YAMURAN* kuma wallahi dole sai ka sakar min ƴata ko kaƙi Allah."

Murmurshi yayi yana duban hanunta dake riƙe da rigarsa, zuciyarsa tana tunzurasa daya tankaɗeta kawai ta faɗi ƙasa, HAJJA dake cikin ɗakinta ne taji hayaniyar AUNTY YANA ya sata fitowa da sauri, tsayawa tayi tare da riƙe baki ta rafka salati tare da tafa hanu.

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!! Ni Mero yau kuma ina ganin wani baƙar lalacewa wai Surukace ta riƙe wuyar rigar Mijin ƴarta, Lallai Yana baki da ta ido, ta sakesa kafin na ɓata miki rai shashancin banza kawai."

Aunty YANA ƙin sakar masa riga tayi tana jijjiga tace.

" Allah HAJJA bazan sakar masa riga ba sai ya Bani takaddar FALMATA tunda ba ƙanwar uwarsa bane sai ya Rabu da ita ai, akan me zai zauna yana wahalar min da yarinya dan ubansa shi wayee."

Doctor leɓen bakin sa ya cije yana kallon AUNTY YANA kallo na tsana da kuma wulaƙanci, kafin ya dubi HAJJA yace.

" HAJJA idan wannan matar bata sakar min riga ba ko, to wallahi za'ayi mummunan abun kunya yau a cikin gidan nan domin kuwa zan hankaɗa matar nan hankaɗar da idan ta faɗi wallahi sai ta karye sannan ta daina zagin ubana yafi ta ita da wannan shashashan mujin nata daraja da mutunci."

HAJJA cike da haushi da kuma fara gajiya da masifar iyalan gidan nasu ta taho tana cewa...........



Tirƙashi akwai ƙura fa cikin wannan book ɗin, tare da cakwalkwalin cakwakiya ku dai ku biyoni mu jone tare⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️


*Please my fan's Share and comments*


08147537180


*ALƘALAMIN RASHEEEDAT USMAN✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce )*
[8/27, 9:30 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romance story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


*Special Gift to*

*Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku*🥰


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*BOOK ONE*
*PAGE 5 to 6*

*_____________________________________*


✍🏻__________"Sakar masa riga, wai ke meyasa sam baki da hkr ne kam yaƙi ya Saki Falmatan nace yaƙi ya Saki Falmatan ko kuma ke ki rubuta mata sakin idan kin isa marar mutunci ɓace ki bani waje kafin na ɓata miki rai."

HAJJA ta ƙarasa Maganar tana bige hanun Aunty yana dake cakwame da rigar Doctor, sakin rigar AUNTY Yana tayi ranta a matuƙar ɓace ta juya tayi ɗakin ta, tana kuma jin takaicin wulaƙanta mata ƴa da yakeyi, Doctor juyawa yayi da niyar ficewa ma daga sashin gabaki ɗaya domin kuwa ransa yayi matuƙar ɓaci, Muryar HAJJA yaji tana ce masa.

" Ina kuma zaka daka juya, ai duk baƙar zuciyar ta ka zaka tsaya mu gaisa dai ko dan ubanka, to maza ka dawo muje uwar ɗaka dama ina neman ka."

Babu musu Doctor ya juyo ya dawo, har cikin ɗakin HAJJA suka shiga a bakin gadon ta Doctor ya zauna tare da gaishe ta, ta amsa tana cewa.

" Hassan na fara gajiya da wannan masifar gabar taku ta fara yawa, Abunda ya faru ya riga ya faru, meyasa kowa bazaiyi hkr ba, duk kaima zargi kake bawai kana da tabbacin abinda kake zargi a kai ba, kana gani fa mutanen unguwa har gulmar gidan nan suke, haka bai dace ba sam gidan sarauta ne fa Babban gida amma a zauna ana abu na rashin mutunci, to na fara gajiya da wannan abun kunyar da kuke jawo mana, dole ne kowa ya ajiye gabar nan, a dawo da ZUMUNCI kamar da ko kuma duk na ci ubanku, Sannan ita MATAR KA meye laifin ta, da zaka dinga mata rashin imani, nan fa ka zauna a gabana nida Marigayi Sarki Allah ya jiƙansa ka dinga kuka da mukace bazamu baka aurenta ba, duk saboda tsoron lalacewar Zumunci, Amma kuka daka tsalle kuka dire kai da ita ku lallai kuna son junanku haka muka hkr muka yarje muku akayi Auren nan, amma shine yanzu zaka dinga wulaƙanta yarinya, kaji tsoron Allah Hassan ka kasance namiji mai kyautatawa iyalin ka, ka daina wahalar da wannan yarinyar idan ƴan iska na suka juyo kanka Hassan zanci ubanka kun sanni kaf ɗinku kun san halina bawai sanyi nayi ba ido kawai nayi shuru na zuba muku to ka kiyaye ka gyara kafin na juyo kanka."

Shuru Doctor Yayi yana sauraran HAJJA sai da ta gama maganar tukunna yace.

" HAJJA kinfi kowa sanin baƙin zaluncin da aka mana a cikin gidan nan, wannan gabar da ake yinta mu bamu da laifi dan mun ƙauracewa alaƙa tsakanin mu dasu, HAJJA ko kene a halin da muke ciki iya abinda za kiyi kenan, HAJJA sune sanadiyyar Ɓatar Babbar yarmu AUNTY JALILA, suka ƁATAR DA ABBAN MU, suka KWANTAR DA UMMAN MU, jinya duk inda muka kaita cewa ake *SAMMU AKA MATA* waye zaiyi mana wannan aikin idan basu ba, Saboda kawai tsananin son sarautar su ta tsiya haka kawai su tarwatsa mana farin ciki, sannan kuma ace a zauna lafiya wallahi HAJJA yanzu muka fara gaba dasu, ai tun farko na sanar dake cewa zan sake musu yarsu kikace baki yadda ba, dan haka FALMATA bazata ƙara samun farin ciki a gida na ba, dole itama sai ta ɗanɗani baƙin cikin da muma iyayen ta suka ɗanɗana mana, HAJJA bazan ɓoye miki ba, Ina son Falmata sai dai a yanzu nafi jin zafinta fiye da Soyayyar da nake mata, zuciyata bazata iya bawa Falmata farin ciki ba a yanzu Saboda ƙiyayyar da nakewa AHALIN TA yafi Soyayyar da nake mata tasiri a cikin Zuciyata Soyayyar ta ta fara fice min a raina ki gafarce ni HAJJA bazan iya dawo da farin cikin mu kamar daba a cikin gidana bazan iya ba, saboda ina ganin baƙin Falmata da Iyayen ta hajja koda kasheni zakiyi bazan taɓa sassautawa Falmata."

Ya ƙarasa maganar idanunsa sunyi jajajur yana kuma duban action ɗin HAJJA, HAJJA ma kallon sa take cike da tausayin sa, da kuma tausayin jikarta Falmata wanda bakin fentin da babu hanunta a ciki ya shafeta, tasan har yanzu Hassan zuciyarsa tana tafasa game da rashin Ƴar Uwar sa JALILA da yayi da kuma Ɓacewar Mahaifin sa, ita kanta HAJJA har gobe cikin tashin hankalin ɓatar ɗannata take, cikin faɗa hajja tace .

" To ita FALMATA meye laifin ta da zaka sakata a cikin wannan lamarin Hassan ka dawo hankalin ka fa.?"

" Hmmm!!! HAJJA idan ita bata da laifi, Iyayen ta ai suna dashi, dan laifin iyayenta shiya shafeta, kinga HAJJA kifa daina zare min Ido kinsan dai anmin rashin adalci ko, kinga ni na tafi domin kuwa bani da lokacin zama ina ɓata yawun bakina akan waɗannan mutanen marassa imani, Kuma HAJJA ki faɗawa wannan shashashan ɗannaki Abubakar ya fita a harkata ya daina zagi na, idan ba haka ba wata rana sai na cire masa haƙorin gaba saboda babu mutunci yanzu tsakanin mu dashi bare kuma girmamawa."


Hajja kwanon da yake gabanta ta ɗauka tare da wurgawa Hassan saurin sunkuyawa yayi kwanon ya bigi bango cewa Hajja tayi.

" Sai kazo aini ka fara zubawar haƙwaran tunda nice a gabanka, Hassan ka kiyayi duniya wallahi, komai tsiyar Abubakar dai ƙanin ubanka kuma ƙanin uba shima ubane hanu bazai goge ba haka kuma ruwa bazai wanke baa."

" to Hajja ni dai ba ubana bane shi, Allah ya kiyaye ya zamo ubana"


ya ƙarasa maganar yana ficewa daga cikin ɗakin salati HAJJA tayi tana cewa.

" Tafiya zakayi Hassan bamu gama Maganar ba, cap lallai Zumunci ya lalace wai yau ɗan ADAMU ne yake cewa Abubakar shashasha, na shiga Uku ni Maryam, Allah ka kawo min ɗauki ya daidaita min tsakanin Zuri'a ta, Allah karka bawa sheɗan damar nasara akan su."

Ta ƙarasa addu'ar tana rafka tagumi, shi kuwa doctor da ya fito a inda ya samu su Aunty YANA yanzu ma anan ya gansu wannan karon harda YAGANA a wajen, kansa ya ɗaga ya fice ba tare daya dubesu ba, AUNTY YANA tsaki taja bayan ficewar Doctor tace wa YAGANA tashi muje na baki saƙon, tashi Yagana tayi tabi bayan ta suka shige ɗaka YAGANA ne ta dubi Aunty YANA tace.

" Oh ikon Allah Aunty YANA dama haka ashe wannan yaron Hassan ya miki mungun raini, hmmm lallai abu ya girmama sai kace ba Surukarsa ba."

Aunty YANA cewa tayi.

" Kedai Yagana bari kawai, kin san tunda wannan shegiyar ƴarinyar munafuka tayi Aljanu ta tona mana asiri cewa mune muka musu Sihiri, ta dinga faɗe faɗe shikenan yaron nan ya tasomu a gaba kamar zai kashe mu kuma wallahi bai isa yaga bayan mu sai dai mu muga bayan sa."

" Hmmm!!! Aunty YANA aini yau Abunda ya miki ya bani tsoro, koda yake kina dai-dai dashi nasan zuwa kwana kaɗan ne zai dawo hanunki sai yanda kikayi dashi, ki ci ubansa iya son ranki."

Dariyar Aunty YANA tasa tare da cewa.

" Aikuwa bazan taɓa ƙyale yaron nan ba, muddun bokaye basu kare ba a duniya, sai na sashi shida kansa ya wulaƙanta uwar tasa da yake wannan gabar a kanta, kinsan yanda ake juya masa a tanda, nan gaba kaɗan haka zamu juya Hassan a hanun mu nida ƴata Falmata, kinga YAGANA yarda dake yasa nake sanar dake sirri na, kuma kema ina sanar dake ne saboda ina da naki sirrin a tafin hanuna, yanda kina fallasa nawa zan fallasa naki, dan haka ki riƙe min nawa nima sai na riƙe miki naki, yanzu ki tashi ki tafi gidan Falmata ki kai mata wannan LAYAR kina tsaye ki tabbatar kunsa a ƙarƙashin katifar sa, idan kin min haka kin gama min komai."

" To amma Aunty YANA ni Matsalar bata waje na, tana wajen Falmata domin kuwa cewa zatayi bazata yiba, kinsan ta da shegen Ustazancin tsiya, cewa fa take shirka muke aikatawa, sannan Aunty YANA Ina tsoron kar Falmata ta sanar dashi, kinsan halin sa zai iya zuwa har cikin gidan nan ya shuka min tsiya."

Shuru Aunty YANA tayi tana nazarin Maganar YAGANA domin kuwa tasan halin ƴarta sarai zata aikata Abunda yafi haka indai akan Soyayyar wannan ɗan Iskan yaron ne, duban Yagana tayi tace.

" Kijeki Yagana kice mata nine na aiko ki, idan ta miki musu ki kirani a waya dan ubanta ai ƴancin ta nake nemar mata shegiya marar zuciya kamar ba nono tasha ba.''

Yagana da to ta amsa mata sannan ta tashi ta fice.

Cikin mintuna ƙalilan Yagana ta isa gidan Doctor sanda ta ƙwanƙwasa ƙofar kafin mai gadi ya leƙo ya buɗe mata kasancewar ya san daga gidan su Uban gidan nasa take, gaishe ta yayi ta amsa babu yabo babu fallasa.

Darect Part ɗin Falmata ta shige babu kowa cikin falon sai mai aikin ta, taɓe baki tayi tare da duban mai aikin tace.

" Ke!!! Ina uwar gijiyar taki take Falmata?"

Sunkuyawa Ladiyo mai aiki tayi tare da cewa.

" Ina kwana Aunty."

Tsawa Yagana tayi mata tace.

" Keeee!!! Bana son shashancin banza, gaisuwa na tambayeki, cewa nayi ina Falmata ko kurma ce ke.?"

" Kiyi hkr Aunty, Aunty Falmatan tana ɗakin DOCTOR tun ɗazu ta shige."

Tsuka Yagana taja tare da cewa.


" Shi Hassan ɗin yana nan ne.?"

" A'a baya nan tun safe daya fice bai dawo ba."

Yagana bata sake cewa komai ba ta wuce bedroom ɗin Doctor Hassan, tana kwance idanunta biyu tayi shuru alamun tana cikin matsanancin damuwa sai bushashshen hawaye dake kwance gefen fuskar ta, tunanin da ta shiga baisa tasan da zuwan Yagana ba, harta zauna sai da ta taɓa ta tukunna, tayi firgit git ta farka cikin tsoro duk a tunaninta, DOCTOR ne ya dawo, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dafe kanta tace.

" Aunty Yagana, yaushe kika shigo."

Bakinta Yagana ta taɓe tare da cewa.

" Ina zaki ji shigowata tunda kin saka kanki a cikin duniyar tunani kina neman kashe kanki akan namiji guda ɗaya tal wanda ina da tabbacin a yau kika bar gidan sa zaki samun wanda ya fisa komai, kin zauna kina neman sawa kanki Hawan jini a banza akan wanda bai damu dake ba."

Gyara ɗaurin ɗankwalinta tayi Falmata cikin sanyin halinta tace.

"Ina son mijina Aunty Yagana bazan iya rabuwa dashi ba, kuma duk abinda yake min bana ganin laifin sa, domin kuwa iyayena sun cutar dashi da yawa, Aunty Yagana na rasa me zanyi na daidaita lamari na da mijina wlh ina sonsa amma shi ya tsaneni yanzu kwatakwata bashi da lokaci na ko kallo na baya son yi."

Tsuka Yagana taja tare da cewa.

" Ai kuwa tafe nake da yadda zaki gyara zamantakewar ki da Shi romio ɗin naki uwar marassa zuciya."

Gyara zaman ta Falmata tayi tare da matsowa kusa da Yagana tace.

" Aunty me zanyi Doctor ya daina Wulaƙanta ni."?

Layar Yagana ta ciro tare da nuna mata tace.

" Da wannan zaki dawo da hankalin mijinki kanki ."

Falmata cike da jin haushi take duban Yagana tace.

" Aunty Yagana laya ce fa wannan."

Yagana cewa tayi " eh laya ce itace maganin matsalar ki, da zarar kin saka masa a ƙarƙashin wannan katifar tasa yana kwanciya magana ta ƙare sai yanda kikayi dashi, Aunty YANA ce ta karɓo ta jiya a wajen malamin ta."

Tunda Yagana ta fara Maganar Falmata ta zuba mata ido sai da takai aya sannan Falmata tace .

" Bana buƙatar maganin matsalata daga wajen boka, ba tun yau na fara faɗa muku haka ba, a wajen Ubangiji nake neman maganin matsalata kuma insha Allah zai kawo min ƙarshen ta, Aunty Yagana na rasa me yasa kuka nacewa mushirikin Mutum keda Mama gaskiya bazan iya cutar da mijina ba, ki mayarwa mama layarta kice mata bana buƙata ta tayani kawai da addu'a Allah ya kawo min ƙarshen matsalata."

Yagana cikin jin haushin Falmata tace.

" Abinda yasa kike shan wahala kenan wannan tsoron Allahn naki, ke ga wacce kika fi kowa tsoron Allah ai kuwa kina nan kina shan wahala, an faɗa miki kowa kika gansa yana zaune a gidan sa lafiya da mijinsa to ba haka ya zauna ba, sai da ya haɗa da malami, bari na kira Aunty YANA na sanar da ita kince bazaki karɓa kiyi amfani dashi ba idan yaso sai ki mata musun ita "

" Aunty Yagana, dan Allah ba sai kin kira Mama ba, ni fa bazanyi Amfani da wannan layar ba koda na karɓa jefar da ita zanyi, kinga time dawowar DOCTOR yayi yanzu haka nayi imanin ya na hanya ki tashi ki tafi kar yazo ya sameki rai ya ɓaci kinsan halinsa."

Falmata ta faɗawa Yagana hakane kawai dan ta samu ta tafi badan Hassan zai dawo ba domin kuwa dawowarsa babu lokaci sai sanda yaga dama.

Taɓe bakinta Yagana tayi tare da miƙewa ta zari jakarta tana cewa.


" Bani kuɗin nafef ke kika sani da wahalar ki jiki magayi ai."

Falmata ɗago kanta tayi tace.

" Wallahi bani da ko sisi Aunty kiyi haƙuri dan Allah."

" Kuɗin nafef da zaki bani ma baki dashi, hmmm!!! Cap Lallai akwai matsala, to sai anjuma."


Ficewa tayi tana sababi ita dai Falmata jingunuwa tayi da jikin bed ɗin tana jinjinawa rashin tsoron Allah na mahaifiyarta ayi mutum baida tawakalli da yarda da ƙaddara shi boka ne kawai zai yi masa maganin Damuwar sa, tsuka Falmata taja tare da tashi, tollet ɗin DOCTOR ta shiga ta wanke tas sannan ta fito ta gyara masa shimfiɗar gadon nasa, ɗakin ma mopping ɗin sa tayi sannan ta fito falo, Ladiyo ƴar aikin ta ta samu zaune ta zubawa tv Ido tana kallon tashar Mbc Bollywood inda suke series mai taken *ZAUJIZ ZAUJEN* da alamu kallon yana mata daɗi, zama itama Falmata tayi tare da sakin murmushi Falmata a Kwaita da son mutane sam bata nuna ƙyama ko banbanci tsakanin ta da Ladiyo tamkar ƙanwar ta haka ta ɗauki Ladiyo Falmata cewa tayi.

" Ladiyo har kin gama aikin kenan kin zauna kallo, kedai kina son wannan series ɗin."

Murmushi itama Ladiyo tayi tare da cewa.

" Ai Aunty tun dazu shigar Aunty Yagana na gama aikina, kuma Aunty ai series ɗin yana da ƙyau fa sosai saboda akwai soyayya."

Dariya Falmata tayi tace.

" Ikon Allah Ladiyo sarkin son Soyayya, to Allah ya kawo miki miji na gari wanda zaku sha soyayya, yauwa idan kin gama kallon zan aikeki Monday market ki sayo min ganyen alayyaho, yau gwate zamu sha cikin gidan nan."

Da to Ladiyo ta amsa sannan suka mayar da hankalinsu ga tv sai dai ita Falmata sam tunanin ta yana kan matsalarta ne idanunta ne kawai suke kan tv, ajiyar zuciya ta sauƙe tana jinjinawa girman matsalar dake gabanta, haka ta kasance cikin wannan yanayin.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Shi kuwa Doctor bayan ya fito daga cikin gidan nasu Darect Asibitin sa ya wuce dake unguwar *Gwange Sabon Layi* Babban privat Hospital ne wanda akayi rubutu da manyan baƙaƙe a makeken get ɗin *AJIRAM MALA SPECIAL HOSPITAL* shigewa ciki yayi, parking yayi a gefe kafin ya fito cikin izza da isa ya nufi cikin Hospital ɗin, nurse gaishe sa suke yana ɗaga musu hanu harya ƙarasa ciki, office doctor Saif zai wuce, sai ya jiyo wani sauti mai kamar

Please Login or Register in order to submit comment