Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zo daf da ƙanin nata, hanunta riƙe da turare, fesawa DOCTOR ta hau yi sosai a jikin sa kota ina, tana dariya, sanda kwalbar turaren ya kusa rabi kafin ta ajiye turaren.

" Ɗan uwana, ina tayaka farin ciki yau domin kuwa rana ce wacce zaka samu farin cikin rayuwarka Kuma mace ta gari, Ubangiji Allah ya albarkaci Auren nan ya samu cikin danshin ku."

" Ameen Aunty na, sai dai har yanzu ina da sauran cikar burina a rayuwa, ina son naga Auren ki Aunty JALILA."

Hawaye ne ya zubo daga idanunta bata goge ba, tace.

" Ka cire Aure na a cikin, cikar burinka domin kuwa abune marar Tabbas, a yanzu yaci ace ina da Aure harda kusan yara uku, sai dai ƙaddara ta hanani Aure, jarabawa ta kenan Hassan, na Rashin mijin Aure, wata ƙila bana daga cikin matan zasuyi aure a duni............"

Saurin toshe mata baki DOCTOR yayi yana kaɗa mata kai cike da damuwa yace.

" Karki yanke tsammani da rahamar Ubangiji Aunty JALILA, domin kuwa bai hallici ko wace mace ba, sai da ya ƙaddara mata mijin Auren ta, sai dai jinkiri yasa muga nisan lokacin Aure yana tafiya ne da ajali idan lokacin sa yayi dole sai anyi, mutane sune suke kasa Fuskantar hakan, amma nasan insha Allah, zaki sami mijin Aure jinkirin ki zaizamo alkairi."

Kafin JALILA tayi Magana Umma ta riga cewa.

" Hassan, ku shige maza ku tafi, time na ƙurewa."

DOCTOR bai kuma cewa komai ba suka shige da Saif zuciyarsa cike da tausayin ƴar uwar tasa wanda yake jinta tamkar uwar da ta haifesa, Umma cike da tausayin Jalila ta dubeta tace.

" JALILA, bana hanaki furta mugayen kalamai ba akan wannan jarrabawar taki ta rashin miji, ni na haufeki JALILA nafiki jin zafin rashin Auren ki, amma ya muka iya da ƙaddarar Ubangiji, lokacin kine baiyi ba JALILA, da zarar lokacin ki ya cika, Allah zai fito miki da mijinki kiyi Auren ki, harma mu manta da kinyi jinkiri, addu'a shine abinda ya kamata kiyi ba mugayen kalamai ba, daga yau wannan ya zamo shine na ƙarshe da zanji wani kalma marar daɗi a bakin ki."

Hawayen Aunty JALILA ta goge tare da cewa Umma.

" Insha Allah Umma bazan sake ba.?


Can kuwa wajen ɗaurin auren cike yake da mutane, DOCTOR da SAIF harma da wasu daga cikin abokan sa, suna zaune gefe guda, ana ɗaura auren wasu kasancewar akwai layi a gaban su sai an ɗaura Aure biyar kafin nasu sune na shida, Bayan angama ɗaura nasu ne sannan aka kira su BULAMA dai-dai lokacin Kuma HABEEB ya na ƙarasowa da motar sa, duk da HABEEB yana jin zuciyarsa na tsinkewa, ga wani suka da take masa, sai dai hakan ya daurewa Zuciyarsa yayi ya hallaci ɗaurin auren, shigowa yayi ya zauna gefen DOCTOR, BABA BUKKAR shine ya bada sadakin DOCTOR dubu 30,000 lakadan, Baba kuwa shine ya bada Auren Falmata, bayan an gama ɗaurin auren ne, HABEEB cike da murmushi ya miƙawa DOCTOR hanu tare da cewa.

" Congratulation 🤝🏻 Hassan na tayaka murna ka samu mace ta gari sai dai shawara, ka riƙe ta da kyau, domin kuwa ka samu matar rufin asiri."

Murmushi DOCTOR shima yayi tare da cewa.

" Na gode, koda baka faɗa ba, nasan na samu matar rufin asiri, naji daɗi daka amshi gayyata duk da ka faɗi amma ka daure har kazo."

Ya ƙarasa maganar yana sakin murmushi cike da gatsali, shima kuwa HABEEB ɗin murmushi yayi tare da cewa.

" Ai shi HABEEB duk wanda ya gayyace shi sai yazo, koda kuwa maƙiyinsa ne, faɗuwa ba ita take nufin rashin nasara ba, wani yakan faɗi kusan sau goma amma tashi ɗaya yake samun nasarar data zarce wanda bai taɓa faɗuwa ba, ya kamata ka daina saurin cika baki, idan kaga baka san me yake gaba ba."

Yana faɗin haka ya juya tare da nufar su Baba, sosai DOCTOR yaji haushin Maganar HABEEB sai dai yaƙi basa damar mayar masa da amsa ya juya abinsa, HABEEB cike da girmamawa ya gaishe da su Bulama, dubu ɗari ya basu gudumawa duk da daƙyar Bulama ya karɓa albarka sosai ya sawa HABEEB.

" Allah ya maka Albarka Habibu, ban taɓa tunanin zaka hallaci wannan auren ba, saboda ba ka samu Falmata, sai gashi ka bani mamaki, lallai kai mutum ne na gari."

" Bulama ai kun zama iyayena koda ban Auri Falmata ba, zan shige saboda ana jirana."

Murmushi Bulama ya saki yace.

" Shikenan Allah ya maka Albarka, mun gode."

Baba ma Albarka ya masa, cikin farin ciki, HABEEB juyawa yayi ya shige cikin motar sa, Saif saurin ƙarasawa jikin motar yayi, turus ya tsaya yana duban HABEEB cike da tausayi, domin kuwa kifa kansa HABEEB yayi ya saki kuka mai cin rai Tabbas yau yasan ya rasa Falmata, ya rasa farin cikin sa, cikin sanyin jiki SAIF ya kira sunan sa.

" HABEEB!!!"

Ɗago kansa yayi a hankali idanunsa sunyi jajur.

" Nasan yanda kake son Falmata HABEEB, Amma meyasa ka kasa cireta a Zuciyarka, duk da kasan baka cikin zuciyar Falmata.?"

" SAIF nima nayiwa kaina wannan tambayar, sai dai na kasa samun amsar tambaya ta abinda na sani kawai shine itace macen dana fara so a cikin rayuwata, nasan na rasata kuma dole na haƙura, sai dai ka sani harna mutu Soyayyar Falmata yana cikin zuciyata."

Yana gama faɗin hakan ya ja motar sa ya bar wajen, cike da alheni Saif ya dawo wajen DOCTOR, cikin farin ciki suka watse daga wajen ɗaurin auren.


Yau Falmata tana cikin farin cikin da bata taɓa tsintar kanta ciki ba, haƙoran ta, sun kasa ruhuwa dariya kawai take yi, Maji murmushi ta saki tace.

" Oh ƙawata ban taɓa ganinki cikin farin ciki irin na yau ba, gaskiya kina cikin farin ciki, ina roƙon Ubangiji daya albarkaci Auren ki, Allah ya tabbatar miki da farin cikin da kike ciki har ƙarshen rayuwarki ZULUM yana hanya gobe may be asa ranar Aure idan ya zo daman kinsan dawowarsa ake jira."

Murmushi Falmata ta saka tace.

" Maji Tabbas ina cikin farin ciki ko yau na mutu na godewa Allah domin kuwa naga cikar burina, na samu abinda nafi so a cikin RAYUWATA, Ƙawata kice gobe kema kina tare da habibin ki."

" Insha Allah gobe muna tare."

AUNTY Yagana ce ta shigo cikin ɗakin tare da cewa.

" Ke Falmata ki tashi kizo, Bulama na kiran ki, suna ɗakin Hajja."

Da to Falmata ta amsa ta cewa Maji fa taje ta dawo, ɗakin Hajja ta nufa zama tayi kanta a ƙasa, bata juma da shigowa ba shima DOCTOR ya shigo kusa da Falmata ya zauna, tare da ɗan mangarinta kaɗan, ɗago kai tayi, ya kanne mata ido😉 murmushi Falmata tayi tare da mai da kanta ƙasa, muryar Hajja sukaji.

" To Alhamdulillah!!! Yau dai Allah ya tabbatar da wannan auren, hakan ya nuna mana Tabbas akwai ƙaddarar Aure a tsakanin yaran nan, to ina son kowa ya manta da cewa mun nuna rashin so a wannan auren, amatsayin mu na iyaye addu'a zamu musu Allah ya tabbatar da zaman lafiya mai ɗaurewa a tsakanin su, sannan kai Hassan abinda nake so da kai, kaji tsoron Allah ka riƙe yarinyar nan da kyau, idan ka wulaƙanta ta, wallahi sai Allah ya mata sakayya domin kuwa ta nuna maka ƙauna, sannan ina son ka rage wannan Zafin rannaka, dan Allah Hassan ka riƙe Fatuma tsakanin ka da Allah, koda bayan ranmu dan Allah karka bari rayuwarta ta shiga cikin matsala."

Ɗago kansa DOCTOR yayi ya kalli Hajja yace.

" Ki daina shakku a kaina Hajja, ina son Falmata fiye da yanda kuke zato, Falmata igiyar Rayuwata ne, tsinketa a jikina tamkar tsinkewar Rayuwata ne, taya kike zaton zan sake wannan igiyar rayuwata ta tarwatse, bazan taɓa rabuwa da ita ba."

Murmushi Bulama ya saki tare da cewa.

" Alhamdulillah naji daɗin wannan maganar taka, Hassan, Allah ya muku albarka, sannan kema Fatuma kibi mijin ki sau da ƙafa iy nayi bari na bari, ki masa biyayya, domin kuwa yanzu aljannar ki tana ƙarƙashin ƙafarsa , koda wasa kar ki yadda muji kin ɓata masa rai ko kin masa abinda ba daidai ba, idan har muka samu wannan labarin to wallahi ranki sai yayi mungun ɓaci."

Girgiza kanta Falmata tayi alamun taji, Hajja cewa tayi idan su Baba suna da abinda zasu faɗi, Umma ce tace.

" Duk abinda ya kamata mu faɗi kun faɗa hajja sai dai Magana ɗaya da zan maɗa, wanda maimaita masa shi zanyi yanzu, ku zama shaida Hajja, ban yadda Hassan ya rabu Falmata ba, muddun ba saɓawa Shari'a tayi ba, idan kuma har ya rabu da ita ba da haƙƙinta ban, ban yafe masa ko da na mutu zanci gaba da ja masa Allah ya isa ina cikin kabari na, ku zamo min shaida ban yadda ya hukunta ta cikin fushi."

Baba cewa yayi.

" Tabbas ina bayanki YAMURAM, nima kaina bazan iya yafe maka ba, muddun ka wulaƙanta min ita."

Ajiyar zuciya Hajja ta saki tare da cewa.

" Insha Allah hakan ma bazai faru tsakanin su ba, Allah ya muku albarka, YANA ke baki da abinda zaku faɗi ne keda Bukkar kunyi shuru."

Yana cewa tayi.

" Babu wani abinda zance Hajja duk abinda zan faɗa kun faɗa, Allah ya albarkaci Auren shine kawai abinda zance."

Shina Baba Bukkar cewa yayi.

" Alhamdulillah, Falmata, nasan ke macece mai haƙuri, to ina son ki ƙara haƙuri akan wanda kike dashi, domin kuwa shi Aure dole sai da hkr, saboda zakiga daɗi za kuma kiga rashin daɗi, harshe da haƙori ma suna saɓawa, bare kuma ku, dan haka ki kasance mace mai tsananin hkr shine ribar Aure, duk macen da bata da hkr to mawuyacin abune ta iya zaman Aure, ki zamo mace mai rufawa mijinki asiri, kiyi hkr da babun sa, ki kasance mace mai tsaftace muhallinta da kuma jikinta, idan kika kasance a yanda na suffato miki Tabbas zaki zauna lafiya da mijinki."

" Insha Allah Baba kamar yanda ka faɗa min haka zan kasance, bazaku taɓa samun matsala daga gare ni ba."

Bulama cike da farin ciki shima yace.

" Magana ta karshe itace, Fatuma zata zauna a tare damu har Allah ya dawo dakai, idan ka dawo sai a mata jere a nan gidan Bukkar na baya ku zauna kafin Allah ya baka naka muhallin."

Murmushi DOCTOR ya saki tare da yiwa iyayen nasa godiya, umarni BULAMA ya bawa kowa akan ya tafi DOCTOR shine ya fara fita sai Falmata ta fita itama.

Da daddare har bayan isha'i kafin Saif ya tafi, itama Maji tafiyar tayi, tana yiwa ƙawartata addu'a da fatan alkairi, haka kowa ya watse cikin farin ciki....................









Wannan littafin na kuɗi ne, idan kin gansa a waje ma na sata ne gara ki biya kuɗin ki, ki karanta guminki, yafi ki karanta abinda ba haƙƙinki ba, ki neme ni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.








*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN ✍🏻*






*(UMMU NASMAH CE)*
[9/29, 10:41 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 69 to 70*




_________✍🏻 washe gari kuwa da safe Falmata cikin farin ciki ta tashi yanzu bata da wata damuwa ko tunani tunda ta samu abinda take so, Kamar kullum yanda ta saba haka tayi ɗakin Aunty YANA ta shiga ta gaishe ta sannan tayi ɗakin Hajja ta shiga, ita kaɗai ta samu zaune a falon kusa da ita ta zauna tare da cewa.

" Hajja ina kwana"

Murmushi Hajja ta saki tana dubanta cike da tsokana tace.

" Amarsu ta ango kinsha ƙamshi sai walwal kike kina ɗauke mana ido, ja'ira da kika nace sai da kika samesa kika huta, to ai gaki gashi sai ki jiƙasa kisha ƙarshen So."

Dariya Falmata tayi tace.

" Wannan kuma ai yanzu keya dama idan ma kina jin haushi ne ke baki samesa ba, kishi ya murɗoki."

Dariya sosai Hajja tayi kafin tace.

" Allah kiyashe ne zaɓen tumun dare, ina zan kai wannan Uban Yan zuciyar tsiyar, ai sai ke da kika ga zaki iya na bar miki kuje can ku ƙarata."

Dariya Falmata ta saki ba tare data tanka Hajja ba domin kuwa ta fahimci tsokana Hajja take ji dashi, Hajja cikin serious tace.

" Kinje kin gaishe da surukar taki YAMURAM kuwa?"

" A'a Hajja banje ba."

" To maza tashi kije ki gaishe ta, daga yau duk wani wayewar gari zakije ki gaishe ta, dole ya zamo miki, idan kin ganta da wani aiki ma ki karɓa mata ki mata wannan shine ɗa'a, domin kuwa yanzu uwar mijinki ne, idan kin fito kuma shima mijin naki kije ki gaishe sa."

Da to Falmata ta amsa tare da tashi ta fice daga ɗakin Hajja ta nufi Part ɗin Umma, da Sallama ta shiga Fanna kawai ta samu a tsakar gidan tana wanke wanke.

" AUNTY Falmata ina kwana."

Fanna ta gaishe ta, tana murmushi Falmata ta amsa da lafiya tare da cewa.

" Umma tana ciki kuwa.?"

" Eh tana ciki, yanzu ma ta shiga.''

Ɗakin Falmata ta shige tare da Sallama, Umma dake zaune ta saka tv gaba tana kallon sunnah tv ta amsa tare da sakin murmushi, karo na farko da Falmata ta fara jin nauyin Umma, kusa da Umma taje zata zauna a ƙasa Umma tayi saurin cewa.

" Kul kika zauna a ƙasa, zoki zauna nan kusa dani, yaushe na dawo surikarki ban sani ba, to karma ki kuskura ki ɗaukeni a suruka, ni uwa nake gareki ba surka ba dawo nan kusa dani ki zauna."

Murmushi kawai Falmata tayi tare da zama kusa da Umman saman kujera, gaishe ta tayi cikin sakin fuska Umma ta amsa Falmata ta ɗan juma a wajen Umma, kafin ta tafi, soron gidan ta shige ɗakin DOCTOR, hanunta ta saka ta tura ƙofar da yake kare bakin ta ɗauke da Sallama, yana kwance hanunsa riƙe da waya ya amsa mata sallamar bai ɗago kansa ba yace.

" My dear, shigo mana kika tsaya daga bakin ƙofa ko kin manta nan ɗakin mijinki ne."

Murmushi Falmata tayi tare da shigowa, a gefen katifar tasa ta zauna tare da cewa.

" Oh DOCTOR na, kai dai baka gajiya da danna waya, ko yaushe idanunka suna kan waya."

Ɗan Murmushi DOCTOR ya saki, tare da mirginowa, hanunsa yasa ba tare da Falmata ta ankara ba, ya fisgo ta, ta faɗa ƙirginsa, jifa yayi da wayar gefe tare da saka hanunsa duka biyu ya kana west ɗinta, zuba mata idanu yayi yana sakin murmushi, yayin da ita kuma Falmata zuciyarta ta tsinke, karo na farko kenan da ta fara haɗa jiki da namiji tsikar jikinta ne ya zuba, gashi kuma ta kasa haɗa ido dashi, idon nata suna rufe, breaz ɗin ta ya zubawa idanu da suka ɗan leƙo masa ta cikin riga lips ɗin sa ya lashe yana haɗiyar yawu, tare da ɗan cije leɓen sa na sama a hankali yace.

" Ki buɗe idanunki ki kalle ni my dear, babu kunya a tsakanin mu yanzu, mijinki ne Ni, dan haka ki cire duk wata kunya ki fuskance ni."

Kasa buɗe idanun nata tayi, ita dai yau kam tana jin kunyarsa, ganin dai da gaske bazata buɗe ba ya sashi sakin murmushi tare da sakin west ɗin nata, zura hanunsa yayi cikin rigarta, wani zubawa tsikar jikinta yayi jin hanunsa a rigarta, yana shafa breaz ɗin ta a hankali, shima wata irin sha'awar tane ya bijiro masa, idanunta na rufe cikin sanyin muryar ta mai cike da tsoro tace.

" Stop DOCTOR pls."

Murmushi ya saki cikin hanzari kuwa ya haɗe bakinsa da nata, bayan ya cire hanunsa daga rigar tata, ƙoƙarin ƙwace kanta take amma ta kasa, tunda DOCTOR ya fara tsotsan lips ɗin ta taji wani daɗi tamkar karya daina, ƙara runtse idanunta tayi, tare da saka hanunta ta ƙanƙamesa, hanunta da DOCTOR yaji a jikinsa ya sashi gane ta fara amsar saƙon sa, harshen ta ya capka ya fara mata wani irin hot kiss mai rikitarwa, sanda yaga ta gama sake masa jikinta, har kamar tana neman ficewa a hayyacin ta, gudun karya zarme ya sashi zare bakinsa daga nata a hankali yana sauƙe ajiyar zuciya, Falmata da duk jikinta ya gama mutuwa ne ta narke masa a jikinsa, dubanta yayi tare da sakin murmushi gashin ta ya shafa cikin kunnenta mata raɗa yace.

" Haka ake gaishe da miji, good morning my dear."

Ya ƙarisa Maganar tare da hura mata iska a kunnenta, kunya ce ta Kama Falmata ta ƙara rufe idanunta tana laɓewa a ƙirjinsa tare da sakin murmushi, ta kuma kasa Magana still murmushi ya ƙara saki yace.

" Ko dai matar tawa ta zama kurma ce, Please my dear buɗe idanunki ki kalleni mana ko zanji sanyi."

A hankali ta buɗe idanun nata ta zubasu a idanun DOCTOR tana kuma kwance a ƙirjinsa, lakace mata hanci yayi yace.

" Ko ke fa, nafi samun nutsuwa idan kina kallo na, amarya ta, bani labari mai daɗi."

" A wajen ka ya kamata na samu labari DOCTOR na, zuciyata tana tsinkewa, a duk sanda na tuno zaka tafi ka barni harna tsawon wasu shekaru, ina tsoron karkaje ka gano wacce ta fini acan ta ƙwace min kai, ta warware min igiyar dana juma ina tuƙawa a kanka."

Murmushi DOCTOR yayi tare da mirginowa da ita suka fuskanci juna idanunsa ya saka cikin nata, yace.

" Igiyar ki tayi tuƙuwar da babu wata macen da ta isa ta waresa koda kuwa hurul aini ne, mace ce ta dabam ke a gareni, rayuwata ne fa ke, taya kike tunani akwai wacce ta isa rabani da rayuwata, Hassan naki ne, ke kaɗai ba tare da kishiya ba ki saka wannan a ranki, ki kwantar da hankalin ki koda shekara dubu zanyi bana tare da ke, zan tsare miki kaina, babu wanda ta isa shiga cikin rayuwarki domin kuwa rayuwata taki ce."

Murmushin jin daɗi Falmata tasa cike da ƙaunar mijin nata tace.

" Zanfi kowa farin ciki da alfaharin cewa, nafi ko mace sa'ar miji, idan har ka tsare min kanka daga wasu sheɗanun mata, Tabbas ina sonka, Soyayyar da bazan iya jure rashin ta ba, DOCTOR na, kana sona Kuwa Kamar yanda nake nake sonka."?

Ɗan dariya DOCTOR ya saki yana ƙara kallonta yace.

" Soyayyar da nake miki, tafi ƙarfi fiye da wanda ke kike min, naki kawai kika san Zafin sa, amma ni nasan duk duniya babu wata macen da zanso sama dake, ina ƙaunar ki."

Murmushin Falmata ta saki cike da jin daɗi, sun juma da DOCTOR cikin ɗakin suna hira, kafin Falmata ta fito cike da farin ciki.


Kwana biyu da ɗaurin auren Falmata da Hassan kullum cikin farin ciki suke tattare dashi domin kuwa suna bawa junansu kulawa, a cikin kwana biyun nan DOCTOR kullum sai yayi romance da Falmata sai dai bai taɓa kuskuren shigarta ba, suna dai samun nutsuwa da juna a haka.

Yau Monday itace Ranar da DOCTOR zasu tafi India, da sassafe ya shiga wajen Umma, kusa da ita ya zauna Baba ma yana zaune, gaishe su yayi cike da girmamawa yace.

" Baba Umma, jirgin 9:30am zamu hau yau."

Baba ne yace.

" Masha Allah abu yayi kyau, Allah ya kaiku lafiya ya baku nasara cikin abinda kukaje nema ya rabaku da sharrin maƙiya, kai kuma Hassan ka maida hankalin ka, kayi abinda ya kai ka, domin ka samu abinda kaje nema, a duk inda ka kasance karka manta da cewa kana da mata, Allah ya maka Albarka ya baka Sa'a cikin karatun ka."

Da ameen Umma ta amsa tare da cewa.

" Ka dage ka zamo mutum mai ƙoƙarin karatu, Hassan ina son ka zamo wani abu a rayuwa, karka biyewa abokan banza dan Allah Hassan ka dage ka zamo zakaran gwaji cikin makarantar Allah ya maka Albarka ya baka nasara ya tsare maka gaban ka da bayanka."

Da ameen doctor ya amsa tare da cewa.

" Insha Allah bazan baku kunya ba, zanyi abinda ya kaini, kuma insha Allah zan fito da sakamako mai kyau na gode sosai, ku cigaba da min addu'a."

Murmushi Umma ta saki tare da ɗauko kuɗin da Kawu Dauda ya kawo mata a kunshe cikin leda ta miƙa masa tace.

" Ga wannan dubu ɗari shida ne, ka riƙe su a hanunka saboda buƙatun yau da gobe, idan sun ƙare ka sanar dani Insha Allah zan turo maka wasu."

DOCTOR cike da ƙaunar mahaifiyar tasa yasa hanu ya karɓa yana jin tausayin ta da ƙaunar ta, a cikin ransa, kafin ya tashi ya fito, Aunty JALILA ya samu tsaye bakin ƙofa cike da ƙaunar ɗan uwan nata itama ta miƙo masa leda mai cike da donut da cake har da cincin, tace.

" Allah ya kaika lafiya ya baka Nasara insha Allah sai ka zamo likitan da sunan sa zai amsa a cikin MAIDUGURI."

Yana murmushi ya karɓa sun juma suna hira da Aunty Jalila, FANNA ma maƙale masa tayi, da ƙyar ya ɓanɓareta daga jikinsa, sannan ya shige cikin gidan, sanda yayi sallama da kowa sun juma da Bulama yana masa fatan alkairi, da nasiha, kafin ya dawo ɗakin sa, ƙofar ya tura, cike da mamaki yake dubanta da take kwance rufda ciki sai famar sharɓar kuka take, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ajiye kayan daya shigo dasu, bakin katifar ya zauna tare da saka hanu ya ɗago ta, biyo hanunsa tayi ta taso tare da faɗawa jikin sa sai kuma ta ƙara sakin kukan.

" Kukan me kike, mutuwa zanyi idan na tafi ne.?"

Da sauri ta ɗago jajayen idanunta ta kallesa, ɗaga mata kai yayi yace.

" To mesa zakiyi kuka, ko kinfi so na zauna ba karatun ne,.?"

Girgiza masa kai tayi tace.

" A'a amma zuciyata bata jin daɗin bari na da zakayi, jikina ya saba da naka jikin zan shiga cikin damuwa idan babu kai a kusa dani."

Murmushi ya saki tare da ɗago kanta ya tallafe da hanunsa, harshen sa ya zura a cikin bakin ta, wani irin hot kiss suke yiwa junan su, yayin da ɗayan hanunsa yake ciki rigarta yana murza nipples ɗinta cike da salo, a wannan lokaci, kaɗan ne ya hana DOCTOR maida Falmata cikakkiyar Mace, sake juna sukayi suna sauƙe numfashi, DOCTOR da idanunsa da suka koma jajur yake cewa.

" Ki kwantar hankalinki shekara bakwai kamar kwana bakwai ne da yardar Allah, insha Allah zan kasance dake kullum a ta waya, zan kuma dinga ziyartan mafarkin ki, kimin Addu'a fatan Nasara damuwar ki tana ɗaga min hankali."

" Shikenan DOCTOR ubangi Allah ya baka Nasara ya tsare min kai, dan Allah DOCTOR karka kalli ko wace mace a matsayin mace dan Allah."

Murmushi ya saki tare da kama kumatun ta, yana kuma sakin murmushi.

" Insha Allah kece kaɗai a cikin zuciyar Hassan."

Nocking ɗin ƙofar sukaji, da sauri Falmata ta tashi daga jikin Hassan ta koma saman kujera, Bello ne ya shigo, murmushi DOCTOR ya saki yace.

" Kardai har time ya cika."

Dariya Bello yayi yace ƙwarai kuwa 9:12 yanzu ya kamata mu fita, tunda shi Saif yanzu haka yana can filin jirgin, tashi DOCTOR yayi tare da ɗaukar cut ɗinsa ya saka akwatin ya nunawa Bello ɗauka Bello yayi yana cewa Falmata " ranki shi daɗe" tare da jan akwatin ya fice dashi, Falmata taahi tayi ta rungume DOCTOR, Kafin ta sake sa, hijab ɗin ta ta ɗauka ta saka tare da ɗaukar ledar tasa ta fito dashi shi kuma ya shige cikin gida, sallama da su Umma tare suka fito da Aunty JALILA da Baba Bukkar sai Bulama sune suka masa Rakiya filin jirgin harda Falmata ciki.

A filin jirgin sun sami SAIF suna zaune da HABEEB shima iya jiran jirgin Cairo, harda Daddyn sa, wajen dukkan su suka nufo, kasancewar wajen ake zama jiran tashin jirgin, DOCTOR cike da girmamawa ya gaishe da Daddyn HABEEB, ransa ɓace ya miƙawa HABEEB hanu sukayi musabaha, daya san zai sami HABEEB a nan da bai bari Falmata ta biyo su ba, shi kuwa HABEEB murmushi yayi ganin yanayin DOCTOR, yaso ya yiwa Falmata murnar

Please Login or Register in order to submit comment