Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na Indo a Birni.


Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.





*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Book One*

*Page 21 to 22*

*____________________________________*



_______✍🏻 Falmata kamar sauƙar ruwan zafi taji Maganar sa a ranta " Wai i love You" duban sa tayi tare da cewa.

" Sorry Sir nifa matar Aure ce."

Murmushi AHMAD yayi yace

" Nima mijin Aure ne ai, serious da gaske sonki nake fatuma domin kuwa ban taɓa ganin macen da tamin domin na Aura ta ba, sai ke tun sanda na ganki nasan cewa na samu matar Aure."

Zuwa yanzu Falmata ranta ya fara barazanar ɓaci, miƙewa tayi tsaye cikin ɓacin rai tace.

" Sorry Sir kayi hkr ni ba matar Auren ka bane domin kuwa ina da nawa mijin nima ba wasa nake maka ba, dan Allah karka ƙara kira min soyayya, ina da miji kuna ina sonsa kuma kasan darajar Aure kayi hkr Allah ya baka wata matar Auren wacce ma ta fini."

Tana gama faɗin haka ta juya ta tafi har tazo bakin ƙofa taji muryar sa yana cewa.

" Idan har da gaske kina da Aure, to mijinki bai iya riƙe mace da daraja ba domin kuwa babu annurin Aure a jikinki, ki faɗa masa ya riƙeki da kyau idan bazai iya ba, ya sakar mana mu zamu iya, karki manta da ina sonki ki riƙe wannan a ranki."

Sosai Falmata taji zafin maganganun AHMAD tsuka kawai taja tare da ficewa, shi kuwa murmushi ya saki har yanzu zuciyarsa bata yadda matar Aure bace ita, " amma zanyi bincike a kanki" ya furta yana mai da hankalin sa kan takaddar dake gabansa.

Ranta a ɓace Falmata ta nufo Maji tace " mu tafi." Tafiyar sukayi sanda sukayi nisa Maji tace

" Wai ya naga kin fito ranki a ɓace meya faru."?

Numfashi Falmata ta sauƙe suna tare a daidaita sanda suka hau sannan Falmata tace.

" Mutumin nan bashi da hankali wai cewa yayi yana sona Mtsss."

" May be bai san kina da Aure bane shiyasa yace yana sonki."

Murmushi Falmata tayi tare da cewa.

" Da farko na masa wannan uzurin na sanar dashi ina da Aure, amma tsabar mutumin nan tantirin ɗan duniya ne sai bai yarda ba, cemin yayi shima mijin Aure ne kiji ɗan iska fa."

Dariya maganar ta bawa Maji kafin tace.

" Ikon kuma ya kuka ƙare dashi."?

" Ya kuwa zamu ƙare banda sanda na MAIMAITA masa da gaske ina da Aure ke kinji baƙar maganar da ya faɗa min, wai harda cewa idan har da gaske ina da Aure to mijina bai iya riƙe mace ba, domin babu annurin Aure a jikina, na sanar da mijina idan bazai iya ba, to ya sakeni su zasu iya, kiji fa wata magana marar daɗi jin sai kace a goshi ake rubuta tambarin Auren."

Dariya sosai Maji take sanda tayi dariyar ta isheta sannan tace.

" Ikon Allah Shidai Hassan ya shiga Uku da bakin al'umma wallahi baki ya masa yawa da zai gane daya gyara kafin lokaci ya ƙure masa, kinga wanda baisan zamantakewar ki da mijinki bama abinda yace, Allah dai ya kyauta."

Tsuka Falmata taja cike da jin haushin Maji tace.

" Ya Isa malama mubar zancen nan, naga kina neman shige min hanci da ƙudunduno zaki fara zage min miji dake kin tsanesa."

Dariya Maji tayi tace.

" Allah ya baki haƙuri Mrs Romio, Ke kuma baki son a zagi habibin ki ba, to Allah ya kawo miki sauƙi cikin lamuran ki ƙawata ya dawo muku da soyayyar ku shikenan abinda kike so kiji nace ko."

Murmushi Falmata tayi tare da cewa.

" Yauwa abinda ya kamata ki dinga min kenan, ba aibata min miji ba."

Dariya Maji tayi suka kama wani taɗin duniya har suka iso ƙafar gidan su Maji tare suka sauƙa Maji ta biya kuɗin, Falmata shiga gidan su Maji tayi da niyar gaishe da mamanta kafin ta fito ta wuce gidan su.


Shi kuwa DOCTOR bayan ya tashi daga bacci wanka yayi, kafin ya fito falo da jallabiya a jikin sa, kai tsaye daining ya nufa, tea da ƙwai kawai yasha sannan ya tashi ya dawo tsakiyar falon tv ya kunna ya fara kallon BBC News yafi 1hrs yana falon baiji motsin Falmata ba, kuma bai damu ya duba ta ba, sanda ya ga 12 daidai sannan ya tashi Bedroom ɗinsa ya wuce ya ɗauki kay ɗinsa da wayoyin sa ya fito, Motar sa ya buɗe ya shiga ya tayar Musa mai gadi get ya wangale da sauri, sanda DOCTOR yazo daidai get ɗin ya tsaya tare da cewa.

" Malam Musa, kana lafiya ya mai jikin dai."

Dariya musa yayi yace.

" Lafiya lau ranka ya daɗe mai jiki da sauƙi, yauwa ga wannan takardar Madam tace a baka ɗazu da safe kafin ta fita."

Cikin mamaki DOCTOR ya karɓi takaddar sai dai bai nunawa Musa wani abu a fuska ba ya buɗe takaddar karantawa yayi ya ajiye sannan yaja motar sa ya fice, Musa get ɗin ya rufe ya koma ya cigaba da jin rediyo ɗinsa, DOCTOR gidan su ya nufa wajen umman sa, bayan yayi parking ne ya shiga cikin gidan domin kuwa yau babu kowa ƙofar gidan su, Fanna da gudu ta faɗa jikin DOCTOR tace.

" Oyoyo Yayana"

Murmushi DOCTOR yayi tare da shafa kan Fanna yace.

" My dear sister har yanzu baki san kin girma ba ko, ina Hajjo naji gidan shuru."

Dariya Fanna tayi tace.

" Suna cikin ɗakin Umma malam sani ne yazo yake mata ruƙƙiya harda Kawu Dauda ma."

" Okay" ya furta tare da cire Fanna daga jikinsa ya shige cikin ɗakin baice komai ba ya zauna a gefe yana kallon yanda Umman sa take wani irin motsi sanda ake mata addu'ar sanda aka gama sannan malam Sani ya miƙawa DOCTOR hanu sukayi musabaha cewa yayi.

" Hassan jiya BELLO ya sanar dani gobe zaku kai mahaifiyar ku wajen MALAM GANA a can BINISHED, gaskiya naji daɗi sosai domin kuwa sahihin malami ne yana aikin sa da gaskiya, kuma ana dace sosai idan anje wajen sa Allah yasa aje a dace, sannan munanan muna yiwa mahaifinku addu'a insha Allah zai bayyana, idan kunje ku sanar da malam Gana maganar ɓacewar mahaifin naku ko Allah zaisa a samu wani taimako daga garesa.

DOCTOR cike da girmamawa yace.

" Insha Allah Malam zamu sanar dashi, kuma a cigaba da mana addu'a kamar yadda kuke mana kullum, na gode sosai mlm"

Kawu Dauda ne yace.

" BINISHED kuma, wajen wani malamin zakuje baku sanar dani ba, maganin da muke anan bai isa ba har sai anje BINISHED, to bazai yuwu ba, babu inda za'aje ai duk inda ya kamata aje anje ba'a samu sauƙi ba dan haka, muyi hkr mu zauna mu cigaba da neman magani a gida ba sai munje wani BINISHED ba."

Cike da mamaki DOCTOR yake bin Kawu Dauda da kallo, kafin yace.

" Kawu magani fa zamuje nema, meyasa to zaka ce karmu je, ai ba'a gajiya da neman magani, haka zamu zauna muta kallon Umma cikin ciwo, gaskiya Kawu kayi hkr zamuje BINISHED gobe bazan iya jurewa kallon Umma a halin da take ciki ba."

Mlm Sani ne yace.

" Tabbas wannan yaron yana da gaskiya Dauda ba'a gajiya da neman magani, komai nisan waje indai za'a samu magani to za'a je bare kuma shi wannan malamin mawuyacin abune aje wajen sa ba'a dace ba, sai dai kuma idan cutar mutuwa ce."

Kawu Dauda cewa yayi.

" Mlm Sani wannan ciwon na YAMURAM wani irin magani ne ba'a nema masa ba, ina ne ba'a jeba, dan haka babu inda za'a je da ita", ya faɗi maganar kamar wanda hankalin sa yake tashe ga Kuma goshin sa daya tsatstsafo da zufa.

DOCTOR cike da damuwa yace.

" But amma Kawu.........."

Ɗaga masa hanu Kawu Dauda yayi tare da cewa.

" Ni ƙanin mahaifiyar ku ce baku fini sonta ba, kuma dole kubi umarni na, babu inda za'a kaimin ƴar uwa."

Malam Sani zubawa DOCTOR Ido yayi cike da mamakin yanda ya gigice lokaci guda jin an ambaci za'aje wajen Malam Gana ko meyasa oho, Allah ya kyauta Malam sani yace tare da tashi ya fice.

DOCTOR shuru yayi kasancewar yana yiwa Kawu Dauda biyayya Kamar yadda yake yiwa Umman sa, sai dai hankalin sa yayi matuƙar tashi jin abinda Kawu Dauda yace, sai dai yana ji a cikin zuciyarsa bazai iya haƙura da zuwa BINISHED gobe, Falmata ce tayi sallama ta shigo cikin ɗakin Fanna kauda kanta gefe tayi ganin Falmata, Hajjo dake zaune gefe itace ta amsa mata sallamar, Hajjo ta gaishar cikin sakin fuska ta amsa mata.

" Aunty Hajjo ya jikin........"

Bata ƙarasa ba DOCTOR ya daka mata tsawa.

" Keeee!!!! Tashi ki fita ki bar gidan nan tunda ba ɓangaren ubanki bane, an baki wani munafurcin ne ki kawo, fita karki kuma shigowa sashin nan ficeee manaaaa!!!!"

Ya ƙarasa maganar cikin tsawa, Falmata kallo tabi DOCTOR dashi cikin zafin zuciya, tashi tayi ranta na ƙuna yayin da idanunta suke zubar da hawaye ta fita daga ɗakin, Hajjo ma sosai ranta ya ɓaci da abinda DOCTOR ya yiwa Falmata cikin ɓacin rai tace.

" Meye kayi haka Hassan, dama ashe da gaske ne abinda yake yawo a cikin unguwa cewa kana wulaƙanta matar ka, matar kace fa ta SUNNAH kake yiwa wannan cin zarafin akan gabarku ta banza wacce zargi kawai kuke baku da tabbas akai, wallahi gaji tsoron Allah ka daina wulaƙanta Aure, ko akwai laifin iyayenta ita meye laifinta, ko laifin iyayenta shine nata laifin, ka dawo hankalin ka, ka ɗauki abinda ya samu iyayenku a matsayin ƙaddarar da Allah ya ɗaura musu, kana Cutar da yarinyar da bataji ba bata gani ba, wallahi idan ka kuskura ka rabu Fatuma bazaka kuma samun mace ta kirki irinta ba, yau naga haukar banza, yanzu kai idan an hukunta ka da laifin iyayenka zakaji daɗi, to karna kuma ji karna gani ka ƙara wulaƙanta wannan yarinyar albarkar."

Shuru DOCTOR yayi kansa a sunkuye zaiyi Magana cikin zafin rai Hajjo tace.

" Karka cemin, bana son ji domin kuwa duk abinda zai fito daga bakinka akan Falmata shirme ne, ka tashi kaje ka sami Bello ku shirya tafiyar da zamuyi BINISHED gobe, ka barni da Kawu Dauda ni zanji dashi dole gobe zamu tafi."

Kaɗa KANSA kawai DOCTOR yayi tare da tashi ya ficewa, yau ko kallon part ɗin su Hajja bai ƙalla ba saboda yana jin haushin ta ya bar gidan.

Hajjo rankwashin Fanna tayi tana cewa.

" Wato kema kinbi sahun ɗan uwanki ko, kina biye masa akan zuciyarsa ta banza."

Tura bakin ta Fanna tayi bata ce komai ba ta yi shuru.

Ita kuwa Falmata sanda ta tsaya ta goge hawayen ta sannan ta shige cikin sashin su, babu Kowa tsakar gidan duk suna cikin ɗaki, ɗakin Mahaifiyarta ta shiga da Sallama Aunty YANA dake zaune ta amsa mata zama Falmata tayi tana duban Aunty YANA tace.

" Ina kwana Mama."

Aunty YANA amsawa tayi da lafiya tana hararar Falmata juyowa tayi ta fuskancesa tare da cewa.

" Wato Falmata kin raina ni, kin zaɓi sakaran mijinki a kaina ko."?

" Na raina ki kuma Mama, mena miki."

Aunty YANA cike da hasala tace.

" Ubanki kika min!!! Nace ubanki kika min dan ubanki har ni zan aiki Yagana da saƙo har gidan ki, ki saka a dawo min dashi kice wai bazaki iya Cutar da mijinki ba kega wacce kika fi kowa tsoron Allah, to aishi zai iya cutar dake, shashashar banza kin zauna namiji sai taka ki yake kamar kare."

Shuru Falmata tayi bata cewa Aunty YANA komai ba, harta gama faɗanta sanda ta gama sannan Falmata tace.

" Kiyi hkr mama Allah ya huci Zuciyaki."

Aunty YANA cewa tayi

" Yanzu me kika zoyi.?"

" UMMA na biyo na duba da jikinta."

" Okay kin shiga ne.?"

" Ehh na shiga, bari ma na shiga wajen Hajja na fito zan tafi ."

" Hajja bata nan ta fita gaisuwar mutuwa ɗazun nan, daga zuwan naki zaki tafi yanzu fa kika shigo."

" Mama ai dama ba jumawa zanyi ba, ba wuni na tambaya ba, duba jikin Umma kawai na tambaya."

Taɓe bakin ta Aunty YANA tayi tare da tashi ta buɗe drowern ta, layar nan ta ɗauko tare da miƙawa Falmata, shuru Falmata tayi tana bin layar da kallo, tsawa Aunty YANA ta mata tana cewa.

" Karɓiii!!!! Mana kina kallo na, ki saka a ƙasan katifar mijinki, wannan wulaƙanci da yake miki yazo ƙarshe, Falmata ki fahimce ni, ƙaunar ki tasa na karɓo wannan layar, zuciyata bata jin daɗin abinda mijinki yake miki, bazan cutar da rayuwarki ba, dan Allah Falmata kiyi amfani da wannan layar domin samawa kanki kwanciyar hankali cikin gidan Auren ki."

Shuru Falmata tayi tare da saka hanu ta karɓi layar cikin mutuwar jiki, tabbas tasan kalaman mahaifiyar ta gaskiya ne, babu uwar da zataji daɗi taga ana wulaƙanta mata ɗan ta a gidan Auren sa, jakarta ta buɗe ta saka layar sannan ta tashi tana cewa.............



*FREE PAGE YA KUSA ZUWA ƘARSHE SAURA 2 PAGE IDAN KINA SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN NAN BIYA KUƊIN KI TA 👇🏻*

*Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari*

Vote
Share
And comment




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻




*(UMMU NASMAH CE)*
[9/5, 9:29 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romance and funny story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


*Special Gift to*

*Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku*🥰


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*BOOK ONE*

*PAGE 23 to 24*

*_____________________________________*



________✍🏻 " Shikenan zanyi yanda kikace Mama na gode ni zan wuce."

Murmushi Aunty YANA tayi tare da cewa.

" Yauwa ƴar albarka ko ke fa, raina ɓaci yake idan ina jin labarin abinda yake miki, wallahi muddun kinyi amfani da layar nan dai dai to Tabbas, Hassan zai dawo hanun mu ke ko cewa kikayi ya miki shara wallahi sai yayi, kije ki jarraba Allah yasa mu dace."

Da to Falmata ta amsa tana cewa.

" Mama ɗari biyar nake so zanyi adaidaita idan akwai kuɗin a hanunki "

Aunty YANA cewa tayi.

" Oh Allah ya wadaran naka ya lalace, yanzu kuɗin adaidaita ma baki dashi kuma wai a haka mijinki yana da kuɗi, kai Falmata wannan Auren naki sam babu daɗi"

tsuka taja tare da ɗauko 500 ɗin ta bata, ita dai Falmata bata ce komai ba ta karɓa ta fito, da har zata shiga tayiwa Aunty Hajjo Sallama sai kuma ta fasa tuno walaƙanta ta da DOCTOR yayi, fita tayi ba tare da ta koma ba, a daidaita ta tara tace masa Gra zai kaita bayan ta haune sunyi nisa da tafiya, ta buɗe jakarta hanu tasa ta ciro layar da Aunty YANA ta bata, ƙarewa layar kallo take cikin zuciyarta take cewa ( Allah ka tsareni da saɓa maka Allah karka jarabci zuciyata da faɗawa ga hallaka saboda Soyayyar da nake yiwa DOCTOR, ko wannan layar dana karɓa wajen Mama na karɓa ne kawai saboda gujewa ɓacin ranta amma ba dan nayi amfani dashi ba) wurgar da layar tayi tana lumshe idanunta hawaye na gangaro mata, hanu tasa ta goge hawayen tare da nemawa mahaifiyar tata shiriyar Ubangiji, da wannan nazarin mai adaidaita ya sauƙeta a ƙofar gidan ta, kuɗin sa ta basa tare da buga get ɗin Musa ne ya leƙo tare da buɗewa da sauri yana cewa.

" Barka da dawowa ranki shi daɗe, na bawa Oga sakonki ai tun ɗazu ban manta ba."

Murmushi Falmata tayi tare da cewa.

" To na gode musa, Ladiyo ta kawo maka abincin rana kuwa.?"

Musa yana dariya yace.

" Eh ta kawo min jalop ɗin shinkafa kuma taji kifi ranki shi daɗe ai Ladiyo ba dai iya girki ba alƙur'an rangaɗaɗau take girki kamar kunnen mutum zai cire, idan ba karnayi ƙarya ba sai nace ma ta fiki iya girki." Sai kuma yayi saurin toshe bakin sa yace " Oh yi hkr Uwar gidan Oga aradu baki nane ya zarme."

Dariya Falmata tayi tana tafiya tare da cewa.

" Lallai kace Ladiyo ta karɓi numbern yabo na girki a gidan nan to nima Allah ya sani a danshin ta"


" Sosai ma kuwa dan har Oga yana yabon girkin ta."

Dariya kawai Falmata tayi ta shige part ɗinta a zatonta doctor gida ya dawo tana shigowa kuma sai taga baya nan Bedroom ɗinta ta shige tayi wanka, three cuttern wando tasa da best sai wata ƙaramar hula faɗawa tayi saman bed yunwa takeji haɗe da bacci, sai dai baccin yafi ci mata jiki, lumshe idanunta tayi bata kuma juma da kwanciyar ba bacci ya sace ta.

Shi kuwa DOCTOR daga, gidan su, Companyn HABEEB ya nufa, kai tsaye, sakatariyar sa ya yiwa Magana kan cewa taje tace wa ubanginta DOCTOR HASSAN ya iso, tashi kuwa tayi taje ta sanar dashi ba'a juma ba, ta fito tare da sanar dashi cewa ya shiga, DOCTOR cike da izza da kuma zafin rai ya shiga, zama yayi ba tare da HABEEB ya basa izini ba, ƙafarsa ya ɗaura ɗaya kan ɗaya fuskar sa na ɗaure tamau, murmushi HABEEB ya saki dake riƙe da biro yana ƙarewa DOCTOR kallo, hanu ya miƙa masa tare da cewa.

" Barka da zuwa masana'antar HABEEB, Likita bokan Turai *DOCTOR HASSAN A MALA*."

Taɓe bakin sa DOCTOR yayi yana cije leɓensa yace.

" Bana haɗa hanu da kare wanda bai san darajar Aure ba."

HABEEB yaji zafin kalmar kare da DOCTOR ya kirasa dashi sai dai a maimakon ya nuna masa ɓacin ransa sai murmushi mai sauti da ya saki tare da cewa.

" Ehh ai a wani lokacin gara kare akan jaki wanda shi kullum bai san abu mai mahimmanci daya kamata ya riƙe ba komai wulaƙantawa yake ciki harda abu mai mahimmanci tsabar rashin sanin darajar kai irin na jaki, shi kuwa kare ai yasan alkairi domin kuwa yana riƙe amanar uban gidansa da kuma mutanen da yake tare dasu, harda wanda ya masa alkairi, shi kuwa jaki ko kaɗan baya gane daidai yafi gane yaji duka kafin ya gyara dalilin kenan da yasa karen shigowa gidan wannan jakin domin ya masa bulala ɗaya ko zai dawo cikin hankalin sa."

Runtse idanunsa DOCTOR yayi yana jin maganar HABEEB tamkar ana caka masa mashi a cikin ƙahon zuciyarsa wato shine ma jakin, cije leɓensa yayi a fusace ya daki teburin dake gaban HABEEB yace.

" Ya Isa!!!!! Haka maci amanar Allah, kai har kana da bakin da zaka gaya min Magana, gargaɗi nazo na maka ka fita a harkar matata idan ba haka ba, wallahi sai na wulaƙanta rayuwarka, kasan halina sarai tamkar yunwar cikin ka."

Dariya HABEEB yasa har dumple ɗinsa yana lotsawa fararen wushiryarsa suka bayyana, cikin dariyar ya miƙe tsaye tare da cewa.

" Kaga banbancin mai hankali da mahaukaci shi mai hankali duk sanda aka ɓata masa rai ko aka tsokanesa baya nuna fushin sa bare kuma fusatar sa, saɓanin mahaukaci da baya iya jure tsokana, kaga kenan ko a nan ka nuna min halin ka na jakuna, malam Hassan baka iya riƙe Aure ba kaje ka koyi yanda ake kula da mace daga nan sai ka dawo ka min gargaɗin " kofa HABEEB ya nunawa DOCTOR yace " fice min daga office kafin nasa security suyi waje dakai a wulaƙance domin kuwa daga ni har kai munsan halin juna, sannan kasa a ranka ko yau nayi niyyar ƙwace Falmata a hanunka, 10 hours sunyi yawa Auren ku ya ƙare, ko ranar da naje gidan ka, naje ne kawai na ganta raina yayi sanyi saboda na juma ban ganta ba kasan dai irin son da nake mata, zaifi maka alkairi kaje ka rungumi matar ka, tunda tana sonka kafin lokaci ya ƙure maka, domin kuwa duk randa kayi sake lokaci ya ƙure maka ni kuma daga ranar nawa lokacin zai fara, tik!!! Tak!! Tik!! Tak!! Ka rabu da ita kenan, dan haka fice min a office."

Wayyo Allah kuzo kuga ɓacin rai wajen DOCTOR dama Hausawa sunce idan baki yasan mai zai faɗa baisan me za'a mayar masa ba, ga dai DOCTOR shiya fara kiran HABEEB da kare, yazo kuma yafi HABEEB jin haushi, hanu DOCTOR ya ɗaga cike da ɓacin rai zai zabgawa HABEEB mari, kafin hanunsa ya isa fuskar HABEEB tuni HABEEB yasa hanu ya riƙe hanun DOCTOR yana cewa.

" Karka kuskura ka fara wannan babban kuskuren domin kuwa fuskata tafi ƙarfin mari, ko ubanda ya haifeni bai taɓa ba bare kuma kai, ina raga makane fa HASSAN saboda bana son mutunci na ya zube a gaban ma'aikata na, fice min daga office, idan ba haka ba wallahi zan wulaƙanta ka a cikin 1hrs kasan kuma zan iya."

Wani irin huci DOCTOR yake idanunsa sunyi jawur, nuna HABEEB da yatsa yake yana ja da baya yana huci har yabar office ɗin, tsuka HABEEB yaja yana komawa ya zauna tare da dafe kansa yana jin wata sabuwar Soyayyar Falmata na bijiro masa, innalillahi ya fara furtawa yana koran sheɗan harya samu nutsuwa, aikin sa ya cigaba dayi cike da kwanciyar hankali.

Shi kuwa DOCTOR wani irin dreving yake idanunsa rufe tsabar ɓacin rai ikon Allah shine kawai ya dawo dashi gida parking yayi ya fito cike da ɓacin rai da gudu ya karasa part ɗin nasu, Ladiyo dake zaune tana kallo a falon sai da ta tsorata da ganin yanayin uban gidan nata, Bedroom ɗin Falmata ya shige yana ƙwala mata kira cike da ɓacin rai.

" *FALMATA!! FALMATA!! FALMATA!! FALMATA!!*"

Ita kuwa tayi nisa da baccin ta sam bataji kiransa ba, tsayawa yayi a kanta yana ƙare mata kallo, runtse idanunsa yayi yana jiyo kalaman HABEEB, a fusace ya saka hanunsa ya fisgo ta, da ƙarfi, ai kuwa a firgice ta farka zata danna ihu yasa hanunsa ya toshe mata baki yana saka hanu a bakin sa tare cewa.

" Shiiiiiii!!"

Shuru Falmata tayi tana zaro idanunta cike da tsoro, hanunsa yasa ya ja gashinta cike da mungunta ƙara Falmata tasa tana jin kanta na wani raɗaɗin azaba sake mata bakin yayi still yana riƙe da gashin nata yace.

" Ban taɓa ganin munafukar mace ba irin ki ballagaza wacce bata san mutuncin kanta ba, faɗa min a ina kuke haɗuwa da HABEEB, a ina kuke haɗuwa, wato ke ga jarababbiya ko saboda yanzu na daina haɗa shimfiɗa dake shine bari ki nemi HABEEB kuje ku lalace, kinyi asara wallahi, koda meye ma abun mamaki tunda kinsha nonon tsiya a wajen uwarki ai............"

Wani irin hankaɗa Falmata ta yiwa DOCTOR HASSAN idanunta sun kaɗa sunyi jajur hawaye ne kawai yake gudu a saman fuskarta tunda DOCTOR yake walaƙanta ta bata taɓa jin zafinsa irin na yau, miƙewa tayi

Please Login or Register in order to submit comment