Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye cike da ɓacin rai cikin tsawa tace.

" Ni ba munafuka bace saboda babu wanda na taɓa munafurta, Zagin iyayena ya isheka haka DOCTOR!!!!! Zan iya jure dukkan wani wulaƙancin ka amma bazan lamunci cin mutuncin iyaye ba, domin kuwa duk tsiya sune suka kawo ni duniya harka ganni ka aura, wato ma zargina kake ina Zina wa'iyazubillah ban taɓa kuma yanzu ma bazanyi ba, da ni jarababbiyar ce da kake faɗi da nayi zina tun sanda ka koya min mu'amala da ɗa namiji ka tafi India ka barni tsawon shekara bakwai da zanyi zina a wannan lokacin ya kamata nayi HABEEB ba mazinaci bane ko a gaban Ubangiji zan masa wannan shaidar, wa mai da baka san da nonon tsiyar nasha ba ka auro Ni, ya isheka DOCTOR cin mutuncin iyaye ya tsaya iya dole ka mutunta iyayena tunda har ka auri yarsu."

Ta ƙarasa maganar tana kuka mai cin rai tare da jingunuwa jikin bango, DOCTOR Tunda ta fara Maganar ya saki baki yana kallon ta, yarinyar da duk sanda ya ƙuntata mata sai dai ta basa hkr yau itace take mayar masa da magana girgiza kansa yayi yana huci ya tunkaro gabanta hannayensa yasa ya dafe bangon da take jingine ya sunkuyo da kansa har suna jin numfashin juna yace.

" Kece kika fara mayar min Magana ina faɗa kina faɗa, Oh na fuskanta, kinje gida ɗazu ba, wannan uwar taki marar mutunci ta zugoki nace wannan Uwar taki marar mutunci ta zugoki ko."

Cike da ɓacin rai Falmata ta ɗauke DOCTOR da mari ta tankaɗe sa gefe, riƙe fuskarsa DOCTOR yayi yana jin zuciya na taso masa jajayen idanunsa ya ɗago cikin mungun yanayi ya nuna ta da yatsa yace.

" Ni kika sa hanu kika mara saboda shegiyar Uwar ki, da kyau da kyau Falmata tabbas kin gwada min kin kai bazan saka hanu a jikin ki ba amma zan miki abinda yafi duka zafi dan haka kije na *SAKE KI SAKI ƊAYA*"

Wani dum Falmata taji tare da wani jiri " *SAKI* ta furta tana kallon DOCTOR cike da tashin hankali sai kuma tasa kuka, lokaci ɗaya kuma tayi shuru tana sauƙe ajiyar zuciya gabansa tazo ta tsaya tare da cewa.

" Ka sake ni kace, ni ka saka DOCTOR Saboda son zuciyarka, saboda kasan ina sonka bazan iya rayuwa babu kai, gaskiyar Maji ne tana faɗa mini bana yarda sai ga zancen ya fito yanzu, dama ku maza haka kuke da zarar kunga ta tana tsananin sonku ku kuma a wannan lokacin baku da abun wulaƙantawa sai ita, meye laifi na DOCTOR dan kawai na soka shine kuskure na, na gode amma ka sani Allah ya isa tsakani na da kai ka cuceni."

Tana faɗin haka ta juya da sauri ta jawo akwatin ta, tsuka DOCTOR yaja tare da ficewa daga Bedroom ɗin, ita kuwa kayanta ta dinga zubawa a cikin akwatin, sannan ta saka kayanta, da mayafin ta, akwatin ta jawo ta fito hawaye na gudu saman fuskarta, Ladiyo dake zaune ne ta tashi da sauri tana cewa.

" Aunty Lafiya, kika fito kina kuka, ina zaki da akwatin Aunty."

Cikin muryar kuka Falmata tace.

" Gidan mu zan tafi, Aure ne ya ajiye ni a gidan nan kuma yau Auren ya ƙare, idan akwai wani abu na kuskure daya shiga tsakanin mu a zaman da mukayi ki yafe min."

Girgiza kanta Ladiyo tayi hawaye na gudu mata itama tace.

" A'a Aunty baki taɓa min laifi ba, sai ma kyauta ta min da kike, Aunty nima tafiya zanyi bazan zauna a gidan nan babu ke ba.

Ta ƙarasa maganar ta na shigewa da gudu Bedroom ɗinta, Falmata share hawayen ta tayi taja akwatin ta ta fice...............




Dan dan dan dan dan dan dan

Akwai ƙura fa cikin wannan labarin ku biyoni mu ninƙaya cikin sa domin jin yacce zata kasance amma ta hanyar 👇🏻


*Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari*




Vote
Share
And comment




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻




*(UMMU NASMAH CE)*
[9/6, 3:39 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romance and funny story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


*Special Gift to*

*Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku*🥰



*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*BOOK ONE*

*PAGE 25 to 26*

*_____________________________________*


💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 *DOLE NA MUKU GODIYA FANS DOMIN KUWA INA GANIN RUWAN MASOYA A WANNAN BOOK ƊIN I LOVE YOU UMMU NASMAH FAN'S*😘




________✍🏻 Musa mai gadi cike da mamaki yake kallon Falmata da ta fito da akwati idanunta hawaye yana gudu, da sauri musa ya ƙaraso tare da karɓar akwatin hanun nata yace.

" Ranki shi daɗe meyake faruwa, naganki kin fito haka kina hawaye, kuma yanzu kika shiga kina dariya kuma ki fito da akwati ina zaki."

Falmata hanu tasa ta goge hawayen ta, sannan tayi murmushin dole tace.

" Babu komai Musa zanje gida ne, zan dawo zuwa anjuma, Mama zan kaiwa akwatin."

Falmata ta faɗa masa hakane kawai dan bata son yawan Magana.

Kaɗa kansa Musa mai gadi yayi cikin rashin yadda yace.

" A'a ranki ya daɗe ba lafiya ba, kuka fa kike."

" Kaga Musa nace maka babu komai, bani jakata na tafi dan Allah bana son yawan tambaya."

Ajiyar zuciya Musa ya sauƙe tare da cewa.

" Shikenan kiyi hkr muje na rakaki ki hau adaidaitan"

Akwatin Musa yaja suka fice a ƙofar gidan suka tsaya jiran mai adaidaitan sun ɗan juma kaɗan kafin adaidaitan ya zo, Musa ne ya tare mai adaidaitan, Falmata ce masa tayi " UNGUWAR BULUNKUTU TSALLAKE zaka kaini amma zaka ɗan jirani na shiga na karɓo maka kuɗinka, Musa cewa yayi.

" Malam nawa ne kuɗin ta da zata biya."

" Ɗari Uku ne" mai adaidaitan ya faɗa, Musa cike da tausayin Uwar ɗakin nasa ya saka hanu a aljihun sa ya ciro Yan canjin sa, ɗari huɗu ne, ya zare ɗari Uku ya bawa mai adaidaita, sosai Falmata taji daɗin karan da Musa ya mata godiya ta masa sannan ya saka mata akwatin ta cikin adaidaitan hawa tayi Musa yana ɗaga mata hanu mai adaidaita yaja suka tafi, Musa cike da sanyin jiki ya shiga cikin gidan, zama yayi shuru yana tunanin meya fitar da Falmata cikin gidan a wannan yanayin, yana tsaka da wannan tunanin yaga Ladiyo ta fito da gana masgo ɗin ta a kanta, ware idanunsa yayi kansa ya ƙara ɗaurewa " to ita kuma Ladiyo meya fito da ita da wannan dangwalin." Sanda ta ƙaraso kusa dashi yace.

" Ke kuma ina zaki da wannan gana masgo ɗin.?"

Ajiye gana masgo ɗin tayi ta zauna a kai sai kuma ta fashe da kuka, cikin kukan tace.

" Ƙauyen mu zan koma, tunda Aunty tabar gidan nan, DOCTOR ya sake ta, ya mata walaƙanci, dan haka nima bazan zauna babu Aunty ba, tafiyata zanyi, na tsani doctor bashi da tausayi da imani, Aunty tana sonsa sosai tana masa biyayya amma baya gani tana haƙuri sosai dashi shine ya sake ta."

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati!!!! Lallai Oga ya yiwa kansa babbar asarar dan bazai taɓa samun mace tagari irin Hajiya ba, Mtsss!!! Wannan ƙaddara data faɗawa waɗannan mutanen tayi muni domin kuwa rayuwar su ta baya ba haka take ba, Rayuwa suke mai tsafta da kuma burgewa a wajen ko wani mutum, Allah ya kyauta, kina da gaskiya Ladiyo bai kamata ki zauna a gidan nan ba tunda babu mace a cikin sa, ke zaki iya tafiya, amma ni zan iya zama, Allah dai ya daidaita tsakanin su, yanzu kin sanar da Oga zaki tafi ne."?

" A'a ban sanar dashi kuma bana son sanar dashi bare kuma na ƙara kallon fuskarsa."

Musa ce mata yayi.

" Karkiyi haka Ladiyo baki san me Allah ya ƙaddara tsakanin su ba, sai kiga idan Allah ya gyara tsakanin su, ko gobe ma sai ki iya ganin Hajiya ta dawo cikin gidan nan, abinda zakiyi yanzu kije ki sanar dashi cewa zaki tafi ƙauyen ku, sai sanda Hajiya ko wata mace ta dawo cikin gidan nan zaki dawo, kije ki sanar dashi kinji."

Kaɗa kanta Ladiyo tayi alamun ta gamsu, gana masgon ta ɗauka ta koma ciki.

A kofar gidan nasu mai adaidaitan ya sauƙe ta, akwatin ta ta ja ta shige cikin gidan nasu matan gidan yawancin su suna zaune a tsakar gidan, bunta da akwatin hanunta sukayi da kallo, sallama ta musu tare da gaishe su zata wuce taji muryar Lami uwar gulma tana cewa.

" Mai kantu ya naga ƴar taku da akwati ko dai Hassan ya koreta ne."

Taɓe bakin ta mai kantu tayi tare da cewa.

" Gata nan dai kam da alamar korar, dan zai aikata tunda ba mutunci garesa ba."

Lami cike da tsurku tace.

" Hmmm idan anbi ta ɓarawo abi ta mabi sawu, suma fa idan da gaske ne zargin da Hassan yake musu to duk abinda ya yiwa Falmata yayi daidai."

Tsuka Mai kantu taja tare da cewa.

" Ke kuma lami gulma gareki, to ina ruwan ki, da wannan maganar, ke komai kika gani sai kinyi Magana Mtsss!!"

Ta ƙarasa maganar tare da tashi tabar wajen, lami taɓe bakin ta tayi, tana bin mai kantu da harara.

Falmata shigewar ta Part ɗin nasu Darect ɗakin Hajja ta shige, sallama tayi jikinta a sanyaye, Hajja dake zaune tana lazimi ne tabi Falmata da kallo, ajiye tsarbin Hajja tayi tare da tasowa tazo kusa da Falmata ta dafa ta tare da cewa.

" Fatuma lafiya na ganki da akwati, kuma ga alamun kinyi kuka a idanunki meya faru.?"

Falmata kuka tasa tare da zama ta dafe kanta cikin muryar kuka tace.

" Hajja DOCTOR ya sake ni, yaci amanata Hajja, na shiga Uku na rasa farin ciki na Hajja, bana jin zan iya rayuwa babu DOCTOR Hajja ina sonshi Hajja ina sonshi."

Kamar sauƙar aradu Hajja taji Maganar saki daga bakin Falmata, zama tayi itama Hajja cike da sanyin jiki ta dafa kafaɗar Falmata tace.

" Dama nasan dole wannan Auren naki zai mutu, alamun haka sun nuna tun sanda Hassan ya juya miki baya, bazaki mutu dan kin rasa Hassan ba, ko mutuwa yayi dole zakiyi haƙuri, Fatuma ki cire Hassan cikin ranki ki manta dashi a rayuwarki ki gina Sabuwar rayuwa karki dinga tuno Soyayyar da, ki dinga tuno walaƙantaki da yayi, ki barsa da Allah na Tabbata zai miki sakayya, Yagana dake kwance ta riƙe haɓa cike da mamaki tace yanzu naji naji muryar bukkar ya shigo jeki kira min shi harma da Yana."

Tashi Aunty Yagana Tayi tare da amsawa da to ta fice Falmata cikin kukan ta cigaba da cewa.

" Bazan iya manta DOCTOR a cikin rayuwata ba, ina sonshi sosai Hajja koda rayuwata zata cigaba da wanzuwa zata wanzu ne cikin Soyayyar DOCTOR, bazan taɓa iya daina sonshi ba hajja.''

Cike da tausayin ta Hajja ta jawo ta jikinta tare da bubbuga mata bayanta alamun rarrashi, BUKKAR ne yayi sallama shida Aunty YANA suka shigo kusa da Falmatan shima ya zauna yana cewa.

" Lafiya kuwa Hajja yaushe Falmata ta shigo gidan nan kukan me kuma take haka.?"

Hajja amsa ta basa da cewa.

" Hassan ne ya saketa."

Aunty YANA wani irin farin ciki taji a cikin ranta domin kuwa ta daɗe tana neman DOCTOR ya sakar mata ƴarta, kodan ta huta da baƙin cikin da yake shaƙa mata Baba Bukkar ne yace.

" Shikenan Allah yasa haka shi yafi alkairi, yaron nan Hassan yana min munanan abubuwa akan zargin sa na banza wanda bani da hanu a ciki, ya saketa Hajja domin ya ƙona min rai, amma insha Allah gaskiya zatayi halinta, kiyi hkr Falmata ki cigaba da addu'a Allah ya kawo miki wani mijin wanda ma yafi hassan.''

Da ameen Aunty YANA tace fuskar ta cike fam da farin ciki, Hajja cewa tayi.

" Bukkar daga kai har Yana kar wanda ya yiwa Hassan Magana akan meya sa ya saki Fatuma, kar Kuma ku nuna masa ɓacin ranku nima bazan sanja masa fuska saboda haka ba, Zuru ma ya ishi mai hankali, sannan ke kuma fatuma ki dinga control ɗin kanki duk sanda kika gansa dan Allah ko kallon sa karkiyi."

Falmata ƙyaɗa kanta tayi alamun taji, Aunty YANA tashi tayi ta fice tana jin zuciyarta wasai, shima Baba Bukkar fita yayi ya rage daga Falmata sai Hajja, kwanciya Falmata tayi a gadon Hajja tayi shuru tana tunani, Hajja kuwa cigaba tayi da lazimin ta tana jin wani irin haushin DOCTOR a cikin ranta.

A cikin mintuna kaɗan Maganar mutuwar Auren Falmata ya karaɗe cikin gidan, koda labari ya iske su Hajjo da AJIRAM da tazo, sosai hankalin su ya tashi barin ma Hajjo har wani jiri take ji, FANNA kuwa farin ciki ma taji, Hajjo tashi tayi ita da AJIRAM suka nufi sashin su Falmata, ɗakin Hajja suka shige da sallama, Hajja ce ta amsa tare da nuna musu wajen zama, zama Hajjo sukayi cikin mutuwar jiki tace.

" Maganar da mukaji a cikin gida gaskiya ne, wai Hassan ya saki Falmata."

Murmushi Hajja tayi cike da nuna rashin damuwa ta musu nuni da akwatin Falmata tace.

" Ganan Tabbas, amma yaje duniya ce ta isheshi riga da wando, ki duba yarinyar yanda take ajiyar zuciya duk son da take yiwa Hassan, ya cutar da ita sosai sai dai Allah baya barci zai mata sakayya."

Runtse idanunta Hajjo tayi cikin ɓacin rai tace.

" Abinda Hassan zai aikata kenan wacce irin zuciya ne haka dashi, Tabbas ya cutar da ita Hajja, kuyi hkr dan Allah, zan kirasa yanzu dole sai ya maida Auren nan."

Murmushi Hajja tayi tare da cewa.

" Allah ya sauwaƙa ai Falmata tabar Auren Hassan kenan har gaban abada, dan haka ku bar wannan maganar mutuwar Auren nan kwatakwata Allah yasa haka shi yafi alkairi, ni kaina idan naso dole sai ya maida Ita amma bazanyi haka saboda zaman Auren su baida wani amfani koda an mayar da Auren Cutar da ita kawai zai dinga yi, dan haka haƙura da wannan Auren shi yafi alkairi."

Jinjina kanta Hajjo tayi har yanzu ranta a ɓace yake, duban Falmata tayi da tayi shuru ta kasa Magana domin kuwa ita kaɗai tasan abinda take ji a cikin zuciyarta, ƙarasawa Hajjo tayi ta dafa ta tare da cewa.

" Kiyi hkr Falmata, insha Allah Hassan sai yayi kukan rashin ki a rayuwarsa bazai gane kurensa yanzu sai sanda komai ya kufce daga hannun sa hankalinsa ya dawo jikin sa a ranar ne zai gane kuskukuren sa lokacin da baida damar gyarawa Allah ya baki haƙurin rashin sa."

Hajjo ta faɗi tare da tashi suna ficewa cikin sanyin jiki AJIRAM kasa Magana tayi tsabar kunyar abinda ɗan uwanta ya aikata.


Wunin ranar Falmata tayi shine cikin baƙin ciki da damuwa, ko abincin dare gagara ci tayi, baccin ma kansa rabi da rabi tayi sa, haka ta kwana cikin ƙunar rai da Soyayyar mijinta.


Washe gari da sassafe DOCTOR ya tashi, ya shirya kasancewar yaune zasu je ƙauyen BINISHED, Bello ya kira ya sanar dashi cewa karya ɓata lokaci 11 zasu wuce, falo ya fito yana ɗaura agogon hanunsa, sharaf ya manta da babu mata a cikin gidan ya nufi daining, wayam ya gani babu komai, dafe kansa yayi ya manta da cewa Ladiyo ta tafi gashi ya tashi da yunwa tsuka yaja tare da ciro wayarsa ya dace kawu Dauda kira, ringin ɗaya ya ɗauka, cikin girmamawa DOCTOR ya gaishe sa tare da cewa.

" Kawu mun gama komai, anjuma zamu wuce da UMMA BINISHED."

Da ƙarfi Kawu Dauda cikin tashin hankali ya furta.

" Whatttt!!!!! Wato ban isa da kai ba kenan, dana hana zuwa BINISHED ɗin wato zaka ce sai kunje to baza'a je ba, idan kuma kuka tafi to kuwa ranku zaiyi mungun ɓaci."

Cike da ɗaurewar kai DOCTOR yace

" Kawu wai meyasa baka son muje ƙauyen nan ne kam, ka ɗagawa kanka tunda nace maka zamuje BINISHED, wai meye yake faruwa ne, ko akwai wani abune."

Kawu Dauda saurin dawowa yayi cikin hankalin sa tare da cewa.

" Babu wani abu ni gani nayi munje wajaje da yawa neman maganin nan bamu sami wani nasara ba, shiyasa kawai bana son muje BINISHED ɗin saboda karmu sha wahalar banza."

DOCTOR cewa yayi.

" Insha Allah Kawu ina ji a jikina zamu sami nasara dan haka zamu tafi anjuma ka mana fatan Nasara."

" To shikenan Allah ya bada Sa'a."

Ya faɗa a taƙaice yana kashe kiran, jikinsa kuwa ya jiƙe da gumi sharƙaf duban Jummai matar sa yayi dake gefen sa cikin tashin hankali yace.

" Mun shiga Uku asirin mu yana gaf da tonuwa, idan har muka bar yaron nan yaje BINISHED domin kuwa wannan malamin hatsabibin mutum ne, muddun YAMURAM ta dawo hankalin ta, to fa asirin mu ya tonu, domin kuwa tasan komai taji komai tasan mune muka ɓatar da mijinta da ƴarta, dole musan abinyi kafin su isa ƙauyen nan."

Jummai a matuƙar har zuƙe ta tashi tace.

" Ƙarya ne asirin mu bazai taɓa tonuwa ba, wannan ƙauyen bazasu isa lafiya, domin dole sai mun dakatar dasu, *YAMURAM BAZATA TAƁA SAMUN LAFIYA BA A HAKA ZATA ZAUNA HAR MUTUWAR TA TA RISKETA* ka kwantar da hankalinka ni nasan abinda zamuyi.



Tir ƙashi wannan shi ake ana zaton wuta a maƙera, to fa ya zata kasance ku biyo ni domin sani👇🏻


*WACCE TAKE DA INTEREST TAKE ƘAUNAR KARATUN WANNAN LITTAFIN TAYI ƘOƘARIN BIYAN KUƊIN TA DOMIN KUWA FREE FAGE YA ƘARE WANDA YA BIYA SHI ZAI SHA KARATU AKWAI WAƊANDA SUKE CEWA 300 YA MUSU YAWA TO DUK MAI SO TAMIN MAGANA RAGI BAZAI GAGARA BA*



*TABBAS NAGA RUWAN MASOYA A WANNAN BOOK ƊIN UMMU NASMAH TANA ƘAUNAR FAN'S ƊINTA SOSAI😘😘🥰🥰*👇🏻


*Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari*



Vote
Share
And comment




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻




*(UMMU NASMAH CE)*
[9/7, 5:40 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romance and funny story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


*Special Gift to*

*Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku*🥰


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*BOOK ONE*

*PAGE 27 to 28*

*_____________________________________*



_______✍🏻Me zakiyi Jammai wannan yaron yanda kika san shaiɗan haka yake taurin kai garesa, mawuyacin abune mu iya dakatar dashi daga wannan tafiyar domin kuwa idan yasa abu a gabansa sai ya kai ga cin Nasara ina mungun jin tsoron yaron"

murmushi Jummai tasa tare da cewa.

" Ka manta da cewa nima shaiɗance mai zaman kanta wallahi na fisa shaiɗanci, kasan dai zan iya aikata duk abinda nake so, ka barsu su tafi, ni kuma zan kira waya abi ta kansu da babbar mota."

Zaro idonsa Kawu Dauda yayi yace.

" Me kike nufi, kina nufin a kashe su, to ma wai waye zaki saka yayi wannan aikin, ki dai sanja wani tunanin amma banda zancen kisa dan gaskiya akwai rai da yawa a cikin tafiyar Hajjo AJIRAM Bello ga kuma Hassan ga YAMURAM bazai yiwu ba gaskiya a sanja wata mafitar ba dai wannan ta kisa ba."

Tsuka Jummai taja cikin tsawa tace.

" Ina ruwan ka da rayukan da za'a rasa, badai mutuncin mu muke nema ba, da kuma kuɗaɗen nan su tsira, to ka sani a wajen neman mutunci rai ba a bakin komai yake ba, wallahi sai naga bayan su kafin suga namu, JAMO zan saka ya min wannan aikin, dole mu dakatar dasu."

Ajiyar zuciya Kawu Dauda ya sauƙe tare da cewa.

" Shikenan ayi hakan Allah ya huci Zuciyarki, ni ma bari na shirya naje muyi sallamar ƙarshe da su, idan sun mutum ma zamu fi samun sukuni wallahi, sai yanzu na hango zancen ki."

Dariya Jummai tasa tare da cewa.

" Uhumm ko kai fa, shirya kawai kaje kuyi sallama saboda gudun zargi, karka nuna musu tsoro ko damuwa a tattare da kai na zuwan su ƙauyen kuyi komai cikin farin ciki da sakin fuska ka nuna musu kafi kowa son ganin ƴar uwarka ta samu lafiya, yanda bazasu fahimci komai a tattare da kai ba kace nima ina musu Allah ya kiyaye hanya."

Shewa suka saka, kafin Kawu Dauda ya shige tollet, taɓe bakin ta Jummai tayi tare da furta " haka kawai muna tsaka da jin daɗin mu, muna cin duniyar mu da tsinke ace za'a dakatar damu, wallahi bazai yiwu ba, duk mutumin da yace zai yanke mana jin daɗin mu wallahi sai naga bayan sa."

Ita kuwa Falmata da damuwar ta tashi daga bacci, komai cikin sanyin jiki take yinsa, Hajja duk tana kula da yanayin ta, gaishe da Hajjan tayi ta amsa tare da cewa.

" Ga nan abincin karyawar ki, ki ɗauka kici maza, ina zaki naga kin shirya kina ɗauko jaka."?

Cikin sanyin Murya tace.

" Makaranta zan tafi ina da lectures 11:30 abincin nan kuma DOCTOR ya isheni!!!"

Bakinta Falmata ta riƙe jin ta ambaci sunan DOCTOR a maimakon ta ambaci na Hajja, tana kallon Hajja cike da tsoron masifar ta, Hajja haɗa fuska tayi tamau tare da cewa.

" Wato har yanzu wannan uban yan iskan ne a cikin ranki ko, wai ke Fatuma baki da zuciya ne kam, duk wulaƙancin da Yaron nan ya miki amma yana maƙale a cikin ranki, to Allah ya yaye miki wannan jarrabawar da kike ciki, amma da zaki taimaki kanki ki cire wannan Soyayyar a cikin ranki da yafi miki sauƙi domin kuwa babu ke babu komawa gidan Hassan har abada, tashi kije kici abinci kafin na ɓata miki rai, me kikaci da zakice kin ƙoshi jiya ma haka kika kwana baki ci komai ba, shine yanzu ma zakice bazaki ci abincin ba to baki isa ba Wallahi ko zakici ki amarsa sai kin ci, kuji min ja'irar yarinya dai to Soyayyar taci uwarta Soyayyar banza Soyayyar da ba'a damu da dake ba, Soyayyar shan kwana maza ci abinci kafin raina ya ɓaci.''

Tura bakin ta Falmata tayi tana ƙunƙuni ta tashi ta ɗauko kwanon abinci tasa a gaban ta, Hajja hararar ta tayi tace.

" Ba dole kimin ƙunƙuni

Please Login or Register in order to submit comment