Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gama breakfast ɗin ne Falmata tashi ta fita zuwa SASHIN Umma, a falo ta sameta kwance sai FANNA dake zaune.

" Ina kwana Umma"
Falmata ta furta.

Cike da murmushi Umma ta amsa da lafiya tana cewa.

" Harkin tashi, yanzu Hassan ya shigo yake sanar min zaku asibiti, ko."

" Eh Umma zamuje yanzu."

" To a dawo lafiya" Umma ta furta tashi Falmata tayi ta fita, kusan karo sukaci da DOCTOR dake ƙoƙarin shiga, murmushi ya sakar mata tare da cewa kamar kuwa kinsan ke zan shiga nema, kinga ɗauko jakarki kizo ki sameni ina waje a cikin motar Bello sauri dan Allah zamuyi ɗan biye-biye ne."

Murmushi Falmata tayi tare da shigewa da ɗan ta ɗauko mayafinta da kuma jaka, a motar ta samesa gaba ya buɗe mata ta shiga yana murmushi yaja motar tare dace mata.

" My Dear kinyi kyau sosai, wannan atamfar ta ƙarbi jikinki, yau fa da daddare zamu koma gidan mu, naso ma a ɗanyi walima, sai kuma na fasa tunda akwai walimar buɗe asibiti na ma, anyi odan magunguna gobe za'a kawo su, sai dai akwai waɗanda ba'a samu ba, kuɗin bai kai ba, zan yiwa Umma Magana ko zata sayar da filinta guda uku da suka saura sai ta bani kuɗin na haɗa, idan yaso daga baya na biyata sannan nayi sanarwar cewa zan ɗauki ma'aikata, sai dai abun farin cikin shine na samu ƙwararrun likitoci, guda goma, insha Allah idan mun fara aiki dasu, asibitin zai samu karɓuwa sosai wani sati zamu fara aiki insha Ranar Lahadi zamuyi walima Monday a fara aiki."

Falmata murmushi tayi tana wasa da zoben hanunta tace.

" Masha Allah naji daɗin wannan labarin Ubangiji yasa ku fara wannan aikin cikin Nasara, ko yanzu Alhamdulillah Allah ya maka arziki na rufin asiri, Tabbas HABEEB mutum ne wanda ya cancanci girmamawa, domin kuwa duk wani daukaka daka samu yanzu sanadinsa ne."

Haɗe ransa DOCTOR yayi jin ta ambaci sunan HABEEB, cikin tsawa yace mata.

" Ƙarya kike ba HABEEB ne sanadin samun ɗaukaka ta, Ubangiji shine ya ɗaukakani ba wani katon banza, karki kuskura na sake jin sunan HABEEB a bakin ki muddun kuwa kina neman zaman lafiya dani."

Cike da mamaki Falmata take duban DOCTOR kishi take hangowa tsantsar sa a idanunsa.

" Allah ya huci Zuciyarka insha Allah bazan sake ba, kayi hkr bansan baka son jin sunan sa ba, da ban ambato ba."

Bai kulata ba, cike da Zafin rai ya cigaba da dreving ɗin, Falmata ta basa hkr kusan sau uku amma yayi banza da ita dole yasa tayi shuru har suka shiga cikin asibitin, Darect ɗakin da Bulama yake suka nufa da Sallama suka shiga Hajja ne ta amsa tana murmushi gwanin sha'awa take kallon jikokin nata domin kuwa duk wanda ya kalli Falmata zaiga alamun jin daɗi a tattare da ita DOCTOR wani irin tsinkewa zuciyarsa tayi yanda yaga BULAMA yana kwance rai a hanun Allah, duk ya rame ga robar fitsari da aka saka masa cike da sanyin jiki ya zauna kusa da Hajja yana cewa.

" Hajja Bulama ne yake kwance haka, Hajja meyasa baki sanar dani, da nasa an ɗauko sa zuwa India, koda baya so amma fa Hajja kiga Bulama kamar bashi ba."

Numfashi Hajja ta sauƙe tare da cewa.

" Ya muka yi jarabawa ce, kuma likitocin suna kula dashi sosai kasan sauƙi yana wajen Ubangiji, tun jiya yake ambato ku, lallai sai dai kuzo ya ganku."

Share hawayen daya gangaro mata Falmata tayi ta matsa kusa dashi tare da kama hanunsa, a hankali ya buɗe idanunsa da kyar muryar sa ƙasa-ƙasa wanda sai ka nutsu sosai kaji yake cewa.

" Kira min Hassan Fatuma, kirasa kuzo kinji Fatuma."

Kuka ne ya kusa ƙwace mata duban DOCTOR Tayi tace.

" DOCTOR Bulama kazo."

Tashi yayi cike da kasala ya zo ya zauna kusa da kan Bulama.

" Sannu Bulama." Ya furta idanunsa yana ruwa, kama hanunsa Bulama yayi ya haɗa dana Falmata a hankali cikin haki yace.

" Tunda na kwanta nake roƙon Ubangiji karya ɗau raina har sai kun dawo na ganku, Hassan ka riƙe Fatuma kamar yadda na haɗa hanunku, karka yadda ka rabu da ita, matar rufin asiri ce, dan Allah Hassan karka bari ƙaddara ta shiga tsakanin ku, ka riƙeta da kyau ka min zaka riƙe Falmata bisa gaskiya da Amana."

Hawayen sa DOCTOR ya goge Yana kaɗa kansa tare da cewa.

" na maka Bulama babu wata ƙaddara da ta isa shiga tsakanina da Falmata, insha Allah itace matata har a lahira."

Kaɗa kansa Bulama yayi tare da maida duban sa wajen Falmata.

" Fatuma ki kula da mijinki ki masa biyayya, karki saɓa Umarnin sa, duk abinda ya saki masa mijinki ne kuma yayanki, bana son ki raina sa, ina sone kuyi rayuwa mai tsafta mai cike da farin ciki, dan Allah Fatuma karki zamo irin mata waɗanda basu ganin darajar mijinsu, Allah ya muku albarka."

Da ameen suka amsa cike da tausayi Hajja ma idanunta hawayen yake, domin kuwa duk wani alamu da mamaci yake nunawa haka Bulama yake nuna mata itace kawai ta fahimci hakan, DOCTOR sun juma sosai kafin suka tafi, kafin su koma gida sai da DOCTOR ya kaita taga asibitin nasa, sannan suka dawo abin mamaki suna shiga sukaji ana ihu, da sauri suka karisa ciki, AUNTY YANA ce take wannan kukan sauran matan gida kuma suna tsaye sunyi carko carko, cike da tashin hankali DOCTOR ya jawo Fanna yana cewa.

" Me yake faruwa a cikin gidan nan.?"

" Yaya BULAMA ne ya rasu yanzu Hajja ta kira ta ke faɗa su Baba Bukkar da Umma duk sun tafi."

Kusan suman tsaye DOCTOR yayi tare da furta BULAMA kuma, mutumin da muka baro wajen sa ɗazu innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un...........







Kuyi hkr da wannan insha Allah gobe zaku sami read more da ɗan yawa masu son a Dawo labari to albishir insha Allah saura 3 page kacal mu dawo labari.






KI biya kuɗin ki kafin ki karanta, karki karanta min LITTAFI ba tare da kin biya ba, idan kikayi haka, Tabbas keda Allah nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180






*KITCHEN*




*MU GYARA DOMIN IYALAN MU DA MAI GIDAN MU TUKUNYAR KI SIRRIN KI*

 

1-Gawda amfani da maggi star dan samun danɗano mai daɗi

2-Rage yawan gishiri a miya yana taimaka mana wajan rage cututtuka da hawan jini gishirin da aka saka a sulale ya wadatar a miya sai dai a kara maggi.

3-ki samu roba mai kyau ki jiƙa kanwa dan amfani yau da kullum ba sai kina zuba garinta tana ɓata abinci"¿ saboda kanwa bata rabuwa da kasa

4-idan zaki soya manja bayan kin zuba albasa tai laushi karki barta ta ƙone sai ki ɗiga kanwa a ciki yana bada danɗano mai daɗi

 

5-soya albasa da citta da garlic sama-sama suyi laushi kafin kiyi sauce ko stew, suna bada kamshi a girki.

6-ba lallai kullum sai kiyi jar miya ba,dunga bada sauyi dan iyalanki,zaki iya yin yar sauce,albasa,garlic citta,koran tattasai ,attaruhu,tumatur,
Zaki iya zaɓar yau kiyi amfani da wannan gobe ki sake wata saffur ,yau kinyi da carrot,ko cabbage ko alayyahu.ko kuma ki dan chopping potatoes dinki dasu albasa da carrot attaruhu ki haɗa sauce,barin aci da couscous ko rice duk dai abin da kike so.

7-wake da shinkafa ba lallai sai kullum kinyi da mai da yaji ba ko da miya,zaki iya soya manja kiyi chopping albasa da attaruhu ki soya sai maggi da kayan kamshi.
Ko kuma kisa gasashan kifi titus ki ɓare kisa aciki idan kina bukatar local maggi wato daddawa itama kisa kaɗan sai alayyahu !
Zaki iya ci da wake da shinkafa ko doya

8-idan kika markaɗa garlic tare da mai sai ki samu roba ko kwalba ki zuba,amma ba'a saka ruwa zata daɗe kina amfani da ita batare data lalace ba,ko garlic da black pepper da mai,ana ajiyewa ya jima bai komai ba.

9-idan lokacin ganye yazo kamar calary ko Parcely ko curry leaves ko mint ko lemon grass ,ki yanka ki shanya awaje marar rana awa kaɗan ya bushe sai ki samu mazubi mai kyau ki adana dan amfanin gaba.

 

10-masara idan aka surfa sai ajiƙa ta kwana bayan kin shanyata ta bushe sai ki haɗa da rogo ki kai niƙa







"ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*







*(UMMU NASMAH Ce)*
[10/10, 10:23 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 84 to 85*





__________✍🏻 Falmata jingunuwa tayi a jikin gini sai kuma kuka ya ƙwace mata durƙushewa tayi da gwiwwar ta, maganganun daya musu ɗazu ne kawai suke yawo a ƙwaƙwalwar ta, Tabbas ɗan adam ba komai bane, in yau kaine gobe ba kai bane Bulama ya rasu innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!! Ta furta cike da tashin hankali, DOCTOR saurin ficewa yayi daga cikin ya nufi asibiti, sosai gidan ya hargitse da tashin hankalin mutuwar Bulama, bama gidan ba har unguwar sai da ta amsa, mai unguwa mai adalci sun rasa shi, shin waye zai iya kwatanta adalci da Bulama ke yiwa talakawan sa, yawancin maganar da ƴan unguwar keyi tare da alhini.


Tun kafin a dawo da Bulama gidan ya cika da mutane masu kuka nayi masu addu'a na yi, Aunty YANA sosai idanunta yayi jajur tsabar taci kuka ta ƙoshi, Falmata kuwa tana jingine da jikin maji tayi shuru sai ajiyar zuciya kawai da take yi, Umma da Hajja tare suka dawo, kina kallon idanun Umma zaki tabbar da taci kuka, sai abin mamaki Hajja ta bawa kowa mamaki sosai tayi jarumta, bata masa kuka ba, sai addu'oi kawai dake fita daga bakin ta, kasancewar ta mace mai addini, A falon ta Hajja ta zauna ta cigaba da jan carbin ta, duk wanda yazo ya gaishe ta, sai dai ta ɗaga masa kai, ƙarfe 2 na rana aka dawo da Bulama, tsoffin unguwar sune suka masa wanka tare da sutura, yaransa kuwa babu wanda bai shiga ya masa addu'a ba, shi kansa DOCTOR ya juma a kansa yana masa addu'a, Hajja itace ta karshen shiga, ta tsugunna akan gawar tasa addu'a ta masa sosai kafin tace.

" A zamana da kai baka taɓa cutar dani ba, ka kasance mutum mai ibada da kyautatawa na ƙasa dakai, ina rokon Ubangiji yasa halinka na gari ya bika, Ubangiji ya kawo haske da salama cikin kabarin ka, Tabbas a hanu mukazo kuma a hanu zamu koma, Allah ya maka rahama, ya haskaka maka makwancinka."

Ta ƙarisa Maganar hawaye na gudu saman fuskarta, a hankali ta tashi tare da ficewa tana masa kallon bankwana ba'a juma ba, kuwa aka kaisa makwancinsa sai fatan Allah ya kai haske cikin kabarin sa.

A ƙofar gidan aka kafa rumfuna na zama makoki, Baba Sosai mutuwar ta shiga jikin sa mutane Kuwa da suka hallaci wannan jana'iza Allah yayi yawa dasu, DOCTOR suna tare da Saif tunda akayi mutuwar, shima HABEEB ya halarci wannan ɗaurin auren, a cikin gidan kuwa suma cike suke.


Kwana uku da mutuwar akayi sadakar Uku da kuma bakwai suka haɗa kasancewar haka al'adar Kanuri take sukan haɗa sadakar Uku da ta bakwai a tare, kowa ya watse babu wanda ya rage, haka kowa ya ɗauki haƙurin rashin BULAMA, Hajja sosai tayi jarumta, ta cigaba da zaman takabarta.


Randa Bulama ya cika kwana bakwai da rasuwa da daddare AUNTY Yagana da Maji sai Inno matar Ibrahim ɗan baffan Baba sai AUNTY JALILA da AJIRAM sune suka raka Falmata gidan ta dake cikin unguwar New GRA unguwa ce mai kyau ta masu kuɗi, tun daga get ɗin gidan zaka tabbatar da DOCTOR ba ƙaramin kuɗi ya kashe ba, bare kuma idan ka shiga cikin gidan Part biyu ne, kuma duka benene, sosai falon Falmata yayi kyau sosai duk da Hassan shine yayi furniture ɗin amma ya saka mata Best color ɗinta pinch da ratsin fari haka cikin falon ya kasance, daga cikin Bedroom ɗin ma haka ne komai pinch, su AUNTY Yagana basu juma ba suka koma cike da saka musu albarka.

Bayan sun watse ne Falmata take ƙarewa gidan kallo sosai ya mata kyau harma yafi gidan da suka zauna a India tsaruwa, har Kitchen sai da ta duba, sannan ta dawo cikin Bedroom ɗin ta, tollet ta shige tayi wanka sannan ta fito ɗaure da towel, dressing mirror ta tsaya ta hau mulke jikinta da mai, ƴar powder ta shafa fuskarta da lips tick sannan ta ɗauki humra mai shu'umin kanshi ta shafe lungu da saƙo na jikinta, maroun ɗin sleeping dress ta ɗauko tare da zirasa a jikinta, zama tayi bakin mirror tana sakin murmushi tare da zaro wayar ta ta buɗe data, chart take hankali kwance ita da Maji, ƙarar buɗe ƙofar Bedroom ɗin dake gefen nata taji, hakan shine ya tabbatar mata da DOCTOR ne ya shigo, murmushi kawai ta saki ba tare da ta tashi ba.

Shi kuwa DOCTOR wayarsa ya ajiye a dressing mirror, yana sauƙe ajiyar zuciya, towel ya ɗauka dake ratayi jikin bed ɗinsa kayan jikinsa ya cire tare da ɗaura towel ɗin tollet ya shige bai juma ya fito ɗaure da towel ɗin, ya rataya ɗaya kuma a wuyansa yana goge jikinsa ac ya kunna saboda yana ɗan jin zafi, sannan ya mulke jikinsa da lottion, turare ya feshe jikinsa dashi sannan ya ɗauko riga da wando na bacci na maza fari tas ya sanyawa jikinsa, wayar sa ya zaro da niyar kiran Falmata sai kuwa yaji an turo ƙofar Bedroom ɗin Falmata ce kuwa ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi gefen sa ta zauna tare da furta.

" Sannu da dawowa, yau ka ɗan juma a waje.?"

Murmushi yayi tare da cewa.

" Wallahi kedai bari, mun tsaya nida Saif ne muna tattaunawa game da sauran kayan aikin da zamu zuba a Hospital ɗin nan, kinsan babu Kudi yanzu a hanuna, da Umma naso tambaya sai kuma akayi wannan rasuwar shiyasa na dakatar da komai, so yanzu kuma ina kunyar tambayar ta gaskiya, saboda tasha hidima a kaina ina cikin tension."

Ya ƙarasa Maganar yana huro iska daga bakin sa, Falmata gyara zaman ta tayi cike da kulawa tace masa.

" DOCTOR na, babu kunya tsakaninka da Umma mahaifiyarka ne fa, babu abinda bazata iya maka ba a duniya muddun tana da halin haka, dan haka banga wani abin kunya kawai ka tambaye ta na Tabbata zata baka."

" Hmmm!!! Zata bani my dear amma sai nake gani kamar zan shiga haƙƙin ƴan uwana, zasu ga Kamar ina yiwa mahaifiyar mu wayo, bana son suji haushi na my dear."

" Kaga DOCTOR, babu mai jin haushin ka cikin ƴan uwanka Domin kuwa suma masu maka ne idan har suna dashi, kawai kaje ka tambayi Umma dan Allah karka cuci kanka."

" Hmmm!!!! Shikenan ba damuwa gobe zanje muyi Magana da ita, ɗazu na juma a gidan ana ƙoƙarin yanke hukuncin wanda zai gaji sarautar Bulama tsakanin Baba Bukkar da Baba, mutanen unguwa sunfi son Baba yayi sarautar, amma kuma Baba Bukkar shima yana son yayi, Baba kuwa yace baya son Sarautar to yanzu sunce gobe zasu yanke hukunci."

Murmushi Falmata tayi tare da cewa.

" Oh Babana, ai dama Baba shine ya dace da yayi sarautar tunda shine babba, to Allah ya zaɓar da abinda yafi alkairi, DOCTOR na gidan nan fa yayi kyau sosai komai Normal har kitchen."

Murmushi DOCTOR ya saki tare da jawo ta jikinsa yana cewa.

" Ai daman nasan dole zai miki kyau, wai ni na tambayeki mana, kawarki kam ta sallamar da Aure ne."

" Hmmm!!! Ni kaina yanzu lamarin Maji ya fara bani tsoro, kwatakwata bata son Maganar Aure yanzu kana fara mata zata ɓata ranta, sai dai kawai mu bita da addu'a."

" Amma ai hakan sam bai dace ba, ko ta manta da mutuncin mace ɗakin mijinta, zan sameta mu tattauna zancen, zanyi ƙoƙarin fahimtar da ita"

Cike da farin ciki Falmata ta rungumesa tana dariya tace.

" Wow Idan kamin haka zanyi farin ciki sosai domin kuwa ina son naga Maji a ɗakin mijinta."

Murmushi DOCTOR ya saki cike da so da ƙauna ya shafa kanta tare da cewa

" Insha nasan zata gamsu da hujjata."

Ya ƙarisa Maganar yana ƙanƙame matar sa, sun juma suna hira kafin bacci ya ɗauke Falmata blanket ya ja musu.


Washegari da safe Falmata tunda ta tashi sallar asuba bata maida bacci ba sai da ta gyara gidan ta tas sannan ta ɗaura musu breakfast, farar doya ta soya tare da sous ɗin tumatur da albarsa, sai tea data haɗa masu, sannan ta koma Bedroom ɗinta, wanka tayi ta shirya cikin riga da wando na kanta wanda suka matse jikinta, sosai suka mata kyau, a falo ta zauna kallo har 11 DOCTOR ya sauƙo cikin gajeren wando da best, zama yayi yana rungumota jikinsa tare da manna mata kiss.

" Good morning my dear love."

Murmushi Falmata tayi ta amsa masa da

" morning Doctor na, breakfast is ready."

" Sorry na manta ban sanar dake cewa akwai mai gaji ba, wanda kullum zaki dinga basa abinci dare da rana, sunansa Musa, sannan muyi Magana da Aunty JALILA tace akwai wata mai aikinta Ladiyo zata turo mana ita take tayaki aiki domin kuwa aikin gidan ya miki yawa ke ɗaya."

Cike da farin ciki Falmata take masa godiya tashi tayi ta shige cikin Kitchen sai gata da kula cike da abincin ta miƙawa DOCTOR tace.

" Gashi ka kaiwa musa mai gadin sai ka dawo muyi breakfast ɗin."

Karɓa DOCTOR yayi yana murmushi tare da tashi yace.

" Ai dole na tunda kin mayar dani ɗan aikenki, mijin tace."

Dariya sosai Falmata ta saki tare da cewa.

" Kuma dole kaje ba, ko kuma na yanke maka *ƊANYEN HUKUNCI*"

Dariya DOCTOR yasa tare da ficewa kaiwa musa nasa breakfast ɗin, a zaune ya sami Musa yana famar jin rediyo zama yayi kusa dashi ya ajiye kular a ƙasa yana cewa.

" Sarkin masu jin rediyo ba, to ga breakfast ɗinka."

Dariya Musa mai gadi yayi tare da cewa.

" Barka da fitowa Oga, an tashi lafiya, Oga ai Nigeria ce sai da jin labarai, har Hajiya ta fara girkin kenan, bari na wanko hanuna nazo na kwashi gara."

Ya ƙarasa maganar cike da nishaɗi Girgiza kansa DOCTOR yayi yana murmushi, ya miƙe yana cewa " a kwashi gara lafiya mlm Musa nima na shige."

Ya ƙarisa Maganar yana tafiya, shima musa dariya yayi ya dauki buta da sauri ya wanke hanunsa kular ya buɗe yaga doya da sous mai yawan gaske wanda zaici har ya bari, murmushi yayi tare da furta " da alama matar gidan nan zatayi kirki wannan abinci mai yawa haka ko a gidana iya wanda za'a bani kenan."

Ya ƙarisa Maganar yana kai doyar bakinsa lumshe idanunsa yayi yana jin daɗin abincin yana sawa Falmata albarka.

DOCTOR kuwa a daining ya sami Falmata har tayi seving ɗin sa, plet ɗin ya jawo ya fara cin abincin a nutse, Falmata loma ɗaya tayi ta ajiye cibin sunan DOCTOR ta kira a hankali, idanunsa ya ɗaga ya zuba mata ba tare daya amsa ba, cike da raunin murya tace.

" DOCTOR kwanan nan marata tana yawan min ciwo ga kuma jinin al'ada na ya fara min wasa, jiya har sai da na tsorata."

Ajiyar zuciya DOCTOR ya saki tare da cewa

" Tun yaushe ya fara miki."?

Yau fa wajen wata Uku Kenan, shine nace ko zaka bani izini gobe naje asibiti."

Girgiza mata kai DOCTOR yayi domin kuwa sarai ya gane abinda yake sawa jininta yake mata wasa wannan kwayar planing da take shane amma tsabar iya bariki na DOCTOR sai yace.

'' ki bari gobe zamuje asibitin Fasaha sai na dubaki da kaina, idan yaso sai ki hau adaidaita ki dawo gida."

Kaɗa kanta Falmata tayi alamun to sannan sukaci gaba da breakfast ɗin bayan sun gama DOCTOR bedroom ɗinsa yayi bai juma ba ya fito cikin shirin fita, hunging ɗin Falmata yayi tare da ficewa, FAMILY HAUSE ɗin su ya wuce, yauma a cike yaga fadar da alamun har sun shiga MEETING ɗin, fadar ya fara shiga tare da neman waje ya zauna ganin sai famar musu ake, mutanen unguwa sun dage da lallai sai dai a bawa Baba shugabancin su, yayin da shi kuma Baba Bukkar yake so a basa, ganin da Baba Bukkar yayi Yan unguwar sunfi son Baba ya sashi saka baki wajen a bawa Baba Sarautar, amma sam ransa baiso ba, shima kansa Baba baiso ba aka basa, a haka taron ya watse akan satin sama za'a naɗa Baba, shi dai DOCTOR part ɗin Umma ya shige Bayan yabar fadan, a waje ya sameta, shima yaja kujera ya zauna yana gaishe da Umma cike da fara'a ta amsa tana tambayar sa Falmata, sun ɗan juma suna hirar rayuwa kafin DOCTOR ya sosa kansa yana cewa.

" Umma dama nazo ne wajenki game da Maganar asibiti na, Umma kinsan an gama komai har ankawo wasu kayan aiki an zuba gashi next week nake son ayi walimar buɗe sa, to sai kuma kayan aikin basu gama kammaluwa ba, har yanzu akwai abubuwan da babu gashi babu kuɗi a hanuna shine nace Umma ko zaki taimakeni ki sayar da sauran filinki ki bani kuɗin n kawo sauran kayan insha Allah zan biyaki a hankali."

Murmushi Umma tayi tana kallon sa kafin tace.

" Meyasa baka sanar dani tun farko ba, ai da na sayar na baka kuɗaɗen, amma yanzu ma bata ɓaci ba, bare na gama girki sai na saka hijab ɗina naje na samu kawun ka Dauda, sai ya sayar da duka biyun ya bamu kuɗin ina ga ai zasu isheka, ka kuma daina zancen zaka biya Ni, bazaka taɓa iya biyana abinda nake maka ba, addua kawai nake buƙata a wajen ka."

Cike da jin daɗi DOCTOR ya yiwa Umma godiya kafin ya tafi.


Umma kuwa tana gama ayyukan ta da yamma lis taje gidan Kawu Dauda, Jummai matarsa kawai ta samu tsakar gida wajen bishiyar maina tana shan iska, zama Umma tayi, tana gaishe da Jummai, amsawa tayi ƙasa ƙasa tare da cewa.

" Yau kece cikin gidan namu kenan, ta ƙarin hkrn Bulama, yanzu nake jin Baban Musa yake cewa wai Baban Hassan aka bawa sarauta, gaskiya abu yayi daɗi Allah ya sanya alkairi."

" Ameen mmn Musa, Yaya Dauda yana nan kuwa nazo wajensa ne."

" Eh yana nan yana ɗaki bari na miki Magana dashi."

Ta ƙarisa Maganar tana tashi tayi ɗakin nata, sun ɗan juma kafin suka fito tare Kawu Dauda zama yayi kusa da ƴar uwar tasa, Umma cike da girmamawa ta gaishe shi ya amsa yana cewa.

" Lafiya kuwa Yamuram yanzu fa na baro ƙofar gidan ku."?.

Umma murmushi tayi tare da cewa.

" Lafiya lau babu komai, dama nazo ne game da sauran filina da suke wajen ku, dama saura Uku ne, to sai kuma kace min kana gini a ɗayan shine nace to na bar maka shi kyauta sauran biyun kuma ina son ka sayar min su duka, zan bawa Hassan kuɗin ne ya ƙara a asibitin sa, kuɗin hanunsa basu kai ba, shine zan cika masa."

Dam dam gaban Jummai ya buga filayen da ta gama saka ran cewa sun gama zama nata shine yanzu za'a mata baƙin ciki ina bazai taɓa yiwuwa ba, zatayi magana sai taji kawo Dauda ya fara.

" Wai YAMURAM baki da hankali ne, shikenan ke dukiyarki akan Hassan zata ƙare, to bazai yiwu ba, bazaki sai da gadonki akansa ba, yasan da Asibitin nasa yaje ya shera BABBAN gida bene har biyu kamar gidan gwamna, sannan kazo kace uwarka ta sayar da kadararta ta baka kuɗi, to bazan bayarba yaje ya nema a wani waje amma bazaki ƙare a kansa ba."

Umma cike da mamaki take duban Kawu Dauda, meye laifi idan ta taimaki ɗanta waye zai taimaka masa idan ita ta kasa taimakon sa, dan waye ta ajiye kadarar domin ta rufawa ƴaƴan ta asiri ne, SOSAI ran Umma ya ɓaci sai ta danne ɓacin ranta tace.

" Amma a tunanina yaya Dauda zan iya rasa komai saboda rufin asirin Hassan, wannan dukiyar tawa ce, dan haka idan bazaka sayar min ba, ka bani takadduna zan bawa MIJINA ya sayar min bance dole sai ka sayar min ba fili suna

Please Login or Register in order to submit comment