Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hmm!!! Haba DOCTOR halinka ne ban sani ba wannan maganar kuma ai wanda bai sanka bane zaka faɗawa, shakka babu ka mata rashin mutunci, Kuma koda bansan abinda tazo maka dashi ba, nasan gaskiya ta faɗa maka tabbas kana zaluntar matar ka DOCTOR, kuma Falmata bai kamata ta samu wannan mungun sakamakon a wajen ka ba ka mata yayi ace kana riritata kamar ƙwai, ka sani Falmata fa ta soka a lokacin da baka da komai, sisin da zaka kashe, baka dashi sai an baka, a wannan lokacin idan baka manta ba samari ne masu kuɗin gaske suke zuwa wajen ta, amma taƙi su tace lallai kai take so, duk da a lokacin kakan nunku basa son Auren zumunci saboda gurɓacewar zumunta, haka Falmata ta dage sai da aka muku Auren, sanda gomnati ta ɗauki nauyin karatun mu haka yarinyar nan tayi haƙuri tana kallo ka tafi India ta jiraka a ɗakin mahaifiyar ta har tsawon shekaru bakwai ka gama karatun DOCTOR ɗin ka, ka dawo kayi sati ɗaya rak ka koma sakamakon aikin da suka ɗauke ka acan, nan ma kayi shekara biyu sannan ne ka dawo ka ɗauke ta kuka koma tare kafin daga baya ku dawo gida Nigeria, yanzu DOCTOR wannan matar data yimaka wannan soyayyar itace abar wulaƙantawa a wajen ka, ya kamata kafin ka yanke mata hukunci ka dinga tunanin baya, wallahi kaji tsoron Allah, ka daina azabtar da baiwar Allah."

DOCTOR ɗago kansa yayi yana duban DOCTOR SAIF yace.

" Gori kake min kenan, to naji tamin halacci sai kuma akace su cuceni ko, to ban riritata kamar ƙwai ɗin ba, kaga DOCTOR SAIF dan Allah tashi ka tafi office ɗin ka, kaima idan wannan maganar zaka min na gode."

" Gaskiya ne ai baka so, shiyasa zaka koreni, Allah ya shirya ka, amm jiya ka iso kuma na fita bamu haɗu ba, Ib ya sanar dani cewa wai a mayar da matar nan opression room."

" Eh nine nace a maida ta saboda ya sanar dani cewa, sun bata ruwa tasha wai har cikin nata ya kumbura."

" Kai Ib ma dai wani lokacin shashasha ne, bafa tasha ruwan ba, sun dai ɗauko zasu bata sai Allah yasa na shigo na hana su bata, kuma matar tana da tunbi ne shiyasa ina ga zaiga kamar cikin ya kumbura."

DOCTOR cewa yayi.

" Ehh ya faɗa min jiyan dana zo, harma naje na duba ta DOCTOR SAIF bari na gudu ina son zanje na dubo jikin Umma."

Tashi DOCTOR SAIF yayi tare da cewa.

" Okay nima bari na shige office ɗina."

Tare suka fito DOCTOR SAIF ya wuce shima DOCTOR ya shige parking space ya ɗauki motar sa ya fice daga Asibitin ya shige family Hause ɗin nasu, kamar ko yaushe ƙofar gidan cike yake da mutane musamman dattawa, shi kuwa SARKIN yana zaune a tsakiyar su, taɓe bakin sa DOCTOR yayi ya ƙaraso wajen tare da sunkuyawa suka gaisa da dattawan ɗaya bayan ɗaya, sai dai Sarki ko YALLAƁOI zance bai samu kallon mutunci a wajen DOCTOR ba bare kuma gaisuwa, haka shima bai kulasa ba gudun ya tsinkasa a cikin talakawan sa, yau dai tsakar gidan babu taron gulma domin kuwa babu kowa sai yara dake famar wasansu, sashin su ya wuce da Sallama ya shiga, Hajjo dake tsaye bakin randa tana ɗibar ruwa ne ta amsa masa da.

" Ameen wa'alaikumussalam , ɗan halak kaƙi ambato, yanzu nake tambayar BULAMA kai yake cemin shima yanzu yake tambayar BELLO kai."

" Kice kamar yadda nima nake neman ki kenan, Ina kuka haɗu da Bello shima nemansa nake."

" Yana cikin ɗakin ka ƙarasa bari na kaiwa AJIRAM ruwa bayi, ina zuwa."

Shigewa DOCTOR yayi cikin ɗakin Umman, bata nan da alamu sun Kaita tollet ne wanka, zama yayi gefen katifa tare da miƙawa Bello hanu yana cewa.

" Bawan Allah jiya na kiraka shine baka ɗaga ba kuma baka biyo kira na ba."

Dariya Bello yayi tare da cewa.

" Bana kusa ka kira nazo kuma zanbi kiran taƙi shiga, ya aikin."

" Aiki Alhamdulillah, jiya AJIRAM take sanar dani cewa kunyi magana akan wani mai magani da yake ƙauyen BINISHED ko."

" Eh tabbas munyi magana, kuma gaskiya ana samun dace sosai a wajen sa, dan akwai wani mutum a bayan layin mu, shima shigen irin ciwon Umma ne, wallahi da aka kaisa can ya warke sosai."

" To amma Bello ina dai ba ɗan tsubbu bane dan gaskiya bana son muje wajen boka."

Dariya Bello yayi yace

" A'a wallahi ba ɗan tsubbu bane malami ne na gargajiya sannan kuma ruƙiyya, babu tsubbu a tattare dashi."

Numfashi DOCTOR ya sauƙe tare da cewa.

" Okay ba damuwa insha Allah zamuje, kamar Ranar asabar tunda ranar ce weekend, to amma waye zai mana jagora kasan dai ni ban taɓa shiga cikin wannan ƙauyen ba."

Bello cewa yayi.

" Zamuje tare nasan ƙauyen Saboda tare mukaje dasu, kuma malamin ya sanni sosai, wannan ba matsala fatan dai Allah yasa mu dace."

" Ameen ma je Asabar ɗin, Ina BULAMA ne kam kwana biyu bana ganin sa."

" Ai kuwa yanzu kikayi saɓani, dan bai juma da fita daga gidan nan ba ka shigo."

" Okay." Doctor ya furta a taƙaice, AJIRAM da Hajjo ne suka shigo riƙe da Umma sun mata wanka kwantar da ita sukayi, DOCTOR duban mahaifiyar tasa yayi da idanunta suke buɗe kamar zaka mata magana ta amsa sai dai ina babu baki, hanunta ya riƙe tare da cewa

" Sannu Umma Allah ya baki lafiya."

Duban Hajjo yayi yace.

" Hajjo alfarma nake nema a wajen ki, ina son zaki dawo ki karɓi AJIRAM jinyar Umma, ita ta koma gidan mijinta ta kula da yaranta, tunda kinga ke kina zaune a gida ba aure.''

Murmushi Hajjo tayi tace.

" Haba Hassan har sai ka nemi alfarma a wajena dan kawai na yiwa Umma jinya nima fa uwata ce Umma babu abinda bata minba a rayuwata, dan haka babu komai AJIRAM ta koma gidan ta, ni zanyiwa Umma jinya."

Ajiyar zuciya DOCTOR ya sauƙe cike da jin daɗi yace.

" Hakane na gode Hajjo, to ke Kuma AJIRAM, gobe zaki koma gidan ki, idan Hajjo ta ɗauko kayan ta, sannan ranar Asabar zamuje wajen mai maganin da Hajjo zamu tafi karki ce zaki zo ki zauna a gidan mijinki idan yaso daga baya sai kije ki dubata."

Nisawa AJIRAM Tayi tace.

" Shikenan yaya Allah ya kaimu goben."

Da ameen ya amsa, Hajja ce ta shigo da Sallama, amsawa sukayi DOCTOR ya ɗaga ido ya kalleta yana sakin murmushi, Hajja kusa da DOCTOR ta zauna tana sakin masa dundu a baya tace.

" Ja'iri jiya da ka gudun yanzu bamu haɗu bane."

Dariya DOCTOR yayi tare da cewa.

" Kinga Malama Hajja, ni bana son yawan Magana karki dameni."

Dariya Hajja tayi tana duban Umma tace.

" Sannu Yamuram kina fama da bautar Ubangiji, Allah ya baki lafiya Allah ya sa zakkar jiki ne" kallon DOCTOR Tayi tace.

" Hassan yanzu babu inda za'a kai Yamuram haka za'a barta a gida, nifa gaskiya bana jin daɗin zaman ta haka ba tare da annemi wani me magani an Kaita ba , duk da kuna karɓowa amma dai ya kamata a ƙara dagewa."

DOCTOR cewa yayi.

" Hajja yanzu ma maganar da muka gama kenan munji labarin wani mai magani a ƙauyen BINISHED zamuje can Ranar asabar zamu kaita."

" Yauwa to Alhamdulillah hakan yafi ai"

Hajjo ce tace.

" Sannu Hajja ina kwana."

Murmushi Hajja tayi tace.

" Hajjo lafiya lau ya uwar taki Merama"

" Lafiyan ta lau tana gaishe kuma."

" Muna ansawa da kyau,"

AJIRAM ma gaida Hajja tayi tana cewa.

" Ina zuwa haka Hajja naga kinsha sari, unguwa ne."?

" Gidan wannan ja'irin wannan wannaki zanje na dubo Falmata, kwana biyu shuru babu labarin ta, tashi ma mu tafi ka sauƙeni."

Hajja ta ƙarasa maganar tana jan kunnen DOCTOR, doctor bai kalli Hajja ba yace.

" Da banzo ba kuma waye zai kaiki.?"

Dariya Hajja tayi tace.

" Kuɗina ne zasu kaini."

DOCTOR cewa yayi.

" Yanzu ma kuwa sai kuɗin naki su kaiki domin kuwa ni ba gida na nufa ba asibiti zan koma."

Hajja cewa tayi.

" Baka isa ba wallahi dole sai ka kaini idan yaso ka juya asibitin."

Juyowa yayi ya fuskanci Hajja yana ƙare mata kallo yace.

" Zaro min idanun da kike ne zaisa naji tsoron ki na kaiki, ke dai malama bini a hankali kawai na kaiki."

Tare suka saka dariya Hajja tace

" To naji angon Hajja, ka dai san bama faɗa ko, tashi mu tafi uban masu gida."

Dariya DOCTOR yasa tare da miƙewa yana cewa AJIRAM.

" Ina FANNA taje ne ban ganta ba.?"

AJIRAM cewa tayi.

" Na aiketa gida na, amma ina ga tama kusa dawowa."

Okay ya amsa yana cewa Bello.

" Sai Asabar ɗin ka shirya zan kiraka, Hajja muje na sauƙe ki na wuce."

Tashi Hajja tayi suka fice mota DOCTOR ya buɗe mata ta shiga sannan shima ya zaga ya shiga yaja motar suka tafi.


DOCTOR hom ya danna a ƙofar gidan mai gadin ya fito da sauri ya buɗe get ɗin, a compaunt ɗin gidan DOCTOR ya tsaya tare da buɗewa Hajja yace.

" To Bismillah fita ni juyawa zanyi."

" Kai!!! Wai dama da gaske asibitin zaka koma."

Dariya DOCTOR yayi yace.

" Au dama kinyi zaton wasa nake miki, asibiti zan koma ban gama aikina ba yaushe zaki koma na turo azo a ɗaukeki."

" To Allah ya tsare a dawo lafiya, eh to ina ga zuwa ƙarfe biyar."

Ta ƙarasa maganar tana fita da Allah ya kaimu DOCTOR ya amsa sannan ya juya ita kuma Hajja ta shige cikin gidan..........





Vote
Share
And Comment




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*
[8/31, 12:50 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romance and funny story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


*Special Gift to*

*Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku*🥰


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*BOOK ONE*

*PAGE 13 to 14*

*_____________________________________*


*Sanda na faɗa nace dan Allah duk mai interest akan wannan book ɗin ya bibiya tun daga farko, shine kikayi kunnen uwar shegu dani, da zarar na buɗe data na ina samun saƙo sama da 150 mutane da kuma na group, ana tambayata DOCTOR HASSAN daga farko dan Allah da wanne zanji da typing ko da turo muku daga farko😩*




________✍🏻 Hajja a ƙofar falon ta tsaya tare da Sallama bakin ta kusan Uku tana sallama Falmata dake zaune tana dogon tunani bata jiyo ta ba, Hajja haɓa ta riƙe tana cewa " ikon Allah gida ata sallama babu mai amsawa sai kace ba gidan Musulmai ba" ƙofar Hajja ta tura ta shigo kanta tsaye turus ta tsaya tana bin Falmata da kallo, "ashe dama tana falon ina sallama shine tamin shuru tsabar iya shege" ƙarasawa Hajja tayi tana cewa.

" Wato tsabar iya Iskanci shine ina sallama kika min shuru ko."

Ta ƙarasa maganar tana zama kusa da Falmata, shuru nan ma Hajja taji Falmata bata amsa mata ba, Hajja cike da tsoron ko ta mutu ne yasata girgiza Falmata sai yanzu ta dawo hayyacin ta, cike da tsoro a firgice ta dubi Hajja sai kuma ta sauƙe ajiyar Zuciya tare da kwantar da kanta jikin kujera, tace.

" Kin tsorata ni wallahi Hajja, yaushe kika shigo banji ba."

Taɓe bakinta Hajja tayi tana cewa.

" Ina kuwa zakiji shigowata Fatuma, kin sawa kanki tunani kina neman kashe kanki, wai ma tukunna Fatuma kin dubi kanki a madubi kuwa yanda kika rame kika ƙwanjame kika fice cikin hayyacin ki, ko dai ciki ne dake Fatuma."

Ajiyar zuciya Falmata ta sauƙe cikin sanyin jiki domin kuwa Hajja yau itace ta biyu da tace ta rame, duban Hajja tayi tace.

" Hajja bani da wani ciki, kin san dai matsalar da nake fama da ita ta matsalar mahaifa kinga kuwa ai Hajja babu ni babu saka rai ga samun ciki, ku dai min addu'a Allah yasa na samu maganin da zai sa na samu sauƙi."

Cike da tausayin jikar tata Hajja tace.

" Hakane Fatuma Amma ai shi ɗan adam baya fidda rai ga rahamar Ubangiji, kiyi haƙuri Insha Allah kema zaki goya ɗanki a bayan ki, har kuyi wasa da dariya dashi."

" To Allah ya amsa wannan addu'ar taki."

Hajja ameen tace tare da cewa.

" Amma Fatuma, yanzu na fuskanci matsalar da tasa kika yi wannan bak'ar ramar wato HASSAN shine matsalar rayuwarki ya zamo miki barazana ko, yanzu Fatuma duk wanda ya kalleki tabbas yasan kina cikin tashin hankali, abinda na guda kenan a baya na ƙi yadda da ki Auri Hassan saboda shi Mutum ne mai zafin zuciya da rashin haƙuri sannan kuma bashi da fahimta, sannan shi idan ya tashi zartar da hukuncin sa idanunsa rufewa suke baya tantance fari bare kuma baƙi babu wanda ya isa ya dakatar dashi da aiwatar da nufin sa nafi ki sanin waye Hassan a hanuna ya taso tun yana ɗan yaye, ke kuma macece mai haƙuri nasan zaki cutu da Auren sa, koda wannan al'amari bai faru ba tsakanin sa da iyayen ki, dalilin kenan da yasa naƙi wannan Auren tun farko, Fatuma soyayya ta rufe miki ido kikace lallai ke shi kike so, wannan halayyar tasa ta zafin rai da rashin haƙuri yasa Hassan yake hukunta ki da laifin da babu hanunki ciki, yanzu sanar dani wani irin mungun abu Hassan yake miki yasa har kikayi wannan ramar!!!!."

Falmata duban Hajja tayi tana tuno da hanyar da Hajja ta nuna mata kafin Auren ta da DOCTOR, ajiyar zuciya ta sauƙe tace.

" Hajja babu komai tsakanina da mijina babu wani mungun abinda yake min, kawai Hajja wannan ramar da kike gani nayi, Allah ne kawai ya kawo ta bawai dan bana jin daɗin Aure na bane, mijina yana kyautata min iya ƙarfin sa bai rageni da komai ba, Hajja karki zargesa domin kuwa bai sani cikin faɗansa da iyaye na ba."

Murmushi Hajja tayi tana duban Falmata cikin faɗa da tsawa tace.

" Karki maidani shasha wacce bansan me nakeyi ba, kinsan dai ni ba yarinya bace ko na haifi ubanki na haifi Uwar ki, dan haka baki Isa ki ɓoye min matsalar Auren ki ba domin kuwa ko bakin ki da zuciyarki sun ɓoye to tabbas fuskar ki ta nuna, dan haka ki sanar dani me Hassan yake miki, dan ubanki dole auren ki yazo ƙarshe da Hassan ko yaƙi Allah, domin kuwa bazan zuba ido ina kallo ana cutar da rayuwarki ba!!!."

Cikin mungun ɓacin rai Hajja take wannan maganar, Falmata idanunta ne suka zubo da hawaye cike da tashin hankali tace.

" A'a Hajja karki shiga tsakanina da igiyar Aure na, wallahi Hajja ina son mijina bazan iya rayuwa idan babu shiba ba, Hajja kimin rai ki ƙyale wannan maganar, kije ki cigaba da min addu'a Insha Allah Ubangiji zai kawo min sauƙin lamura na kashe min Aure bashi bane masalaha a cikin wannan lamarin, tabbas DOCTOR Yana cutar dani amma Hajja ina son mijina a haka."

" Wallahi baki isa ba Fatuma bazan zuba ido rayuwarki ta lalace ba, Fatuma ki daina biyewa soyayya domin kuwa tana gabda kaiki lahira, ki dubi ya rayuwarki zata inganta ki samu farin ciki, ki tashi ki ɗauko mayafin ki mu tafi gida kinbar Auren Hassan kenan daga yau har gaban abada, zan Kuma ci ubansa yau zaisan ya wulaƙanta ki yau naga zalunci, shiyasa YANA ta dage lallai sai ya sakeki ina hanata ashe ita ta gano abinda ni ban gani ba, ki tashi ki ɗauko mayafinki mu tafi "

Falmata cike da damuwa take duban Hajja, muryar ta na rawa tace.

" Babu halin na saka ƙafa na biki Hajja ba tare da izinin mijina ba, saboda idan na biki bada izinin sa ba, zan fita ne cikin tsinuwar Mala'iku dan haka kiyi haƙuri Hajja bazan iya barin gida na ba, kije kimin Allah ya daidaita tsakanina da mijina, zanfi jin daɗin haka fiye da kashe min Aure da zakiyi, ina son HASSAN Hajja bazan iya rabuwa dashi ba ."

Hajja riƙe haɓa tayi tana tir da Soyayyar da Falmata take yiwa Hassan domin kuwa tana Soyayyar wahala ne Soyayyar da zata Kaita ta baro ta, Hajja sosai ranta ya ɓaci cewa tayi.

" Bazaki bini ba ko, kin gwammace ki zauna cikin wahala da kibini na sama miki farin ciki, wai wannan wata irin soyayya kikewa Hassan, ke fa Soyayyar ki bata da riba, anya kuwa akwai zuciya a ƙirjinki Fatuma ki zauna namiji yana taka ki amma a hakan kina nan maƙale a gidan sa kin gwammace wahalar da yake baki ta kashe ki idan yaso sai a fito da gawarki ko, to kinyi ƙarya dan uwarki da ubanki, na yadda bazaki bini yanzu ba, amma zaki taho idan ya baki takaddar ki."

Hajja tana gama faɗin haka ta juya a fusace, Falmata kuka tasa mai cin rai tana tsoron abinda zaije ya dawo domin kuwa tasan halin Hajja sarai kamar yunwar cikin ta.

Hajja kuwa adaidaita ta hau, ta shige gida cike da ƙunar rai sosai yau ranta ya ɓaci taji baƙin ciki sosai da ganin halin da Falmata take ciki, mai adaidaita yana sauƙe ta Hajja ta basa kuɗin sa, shigarta cikin gidan part ɗin su DOCTOR ɗin ta shiga AJIRAM na zaune ita da Hajjo suka ga Hajja ta shigo cikin matsanancin ɓacin rai ko sallama batayi ba, AJIRAM ce tace.

" Hajja lafiya me yake faruwa."?

Hajja bata bata amsa ba sai cewa tayi

" Ki kira min Hassan a waya, kice yazo yanzun nan ya sameni duk abinda yake ki ya barsa yazo dan ubansa."

Tana faɗin haka ta juya ta fice daga part ɗin.


Cike da mamaki AJIRAM take duban Hajja matar da suka fita tare da Hassan ɗin suna wasa suna dariya yanzu kuma ta dawo a haka, AJIRAM wayarta ta ɗauka ta dannawa DOCTOR kira ringin ɗaya ya ɗaga tare da cewa.

" Lafiya kuwa meke faruwa yanzu fa nabar gidan."?

AJIRAM ce masa tayi.

" Lafiya, Hajja ce tace kazo yanzun tana jiranka duk abinda kake wai ka ajiye kazo ka sameta."

" Hajja kuma, yanzu fa muka rabu da ita, lafiya.?"

" Wallahi yaya ban sani ba, tace dai kazo yanzun nan."

" Okay gani nan zuwa yanzun nan."

Katse kiran DOCTOR yayi cike da mamaki, tashi yayi ya ɗauki kay ɗin motar sa, ya fito daga office tare da cewa nurse fatuma ta cewa DOCTOR SAIF yazo ya rufe masa office ya ƙarasa maganar yana ficewa, motar sa ya shige ya mata kay, cike da tunani harya iso ƙofar gidan, parking yayi tare da shigewa cikin gidan part ɗin Hajja ya shige Darect, bata tsakar gidan, ɗakin ta ya shige yana cewa.

" Wai Hajja meke faruwa ne kam, har kin dawo ne wai "

Ya ƙarasa maganar yana ƙarasawa kusa da Hajja dake tsaye tana riƙe da kunkumi, mari Hajja ta ɗauke DOCTOR dashi, a firgice DOCTOR ya dafe gefen fuskar sa, bai gama dawowa hayyacin sa ba Hajja ta ƙara ɗauke sa da wani marin kafin ta fara Magana cikin ɗaga Murya


" Ubanka ne yake faruwa!!! Nace ubanka ne yake faruwa, ɗan iska marar mutunci, azzalumin banza, me kake ɗaukar kanka, nace me kake ɗaukar kanka, banza a banza, to bari kaji na faɗa maka dan ubanka bazan saka Ido ina kallon ka ka kashe Fatuma wallahi ƙarya kake, me ta maka kake neman kashe ta wani irin baƙin azzalumi ne kai, kana da tabbacin cewa iyayenta sune suka ɓatar da ubanka, waye shaidar ka, ka saka yarinya a gaba kana azabtar da ita, hmmm, yanzu idan Ubangiji shine ya ɗauki ran magaifinka aka ajiye maka gawarsa a gaban ka, zakayi gaba da Ubangiji ne ko kuma zaka daina Bauta masa saboda ya ɗauki ran ubanka, to bari kaji, idan ka fito ɗan halak a cikin uwar ka da ubanka ka bani takardar sakin Fatuma, ka saketa dan ubanka, banza azzalumi wanda baka san darajar ɗan adam ba."

Tunda Hajja ta maresa har zagin da take masa DOCTOR a tsaye yaƙe ƙyam yana duban Hajja, cikin mungun ɓacin rai idanunsa sunyi jajur kamar gauta ajiyar zuciya kawai yake sauƙewa yana jin kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu tsabar baƙin ciki, sosai zuciyarsa take tafasa tare da sake rura wutar tsanar falmata da iyayenta a cikin ransa Magana ya fara cikin ɓacin rai shima.

" Hajja marina kikayi akan Falmata, Hajja nine banza a banza kike kirana kuma azzalumi akan Falmata, Hajja duk zalunci da aka mana baki gani ba mune ma kike kira da azzalumai, kin fifita Falmata akaina Hajja."

" Na fifita a kanka!!! Nace na fifita ta akan ka dan ubanka, wawa marar lissafi da tunani, idan ka cika mai Zuciya ka saki fatuma, zuciyarka ta banza da wofi da kana da zuciyar ai bazaka zauna da ita ba baƙin mungu wand.........."

Cike da murɗar ɓacin rai da baƙin ciki DOCTOR ya dakatar da Hajja.

" Ya isa Hajja!!! Ya isa ba dai akan Falmata kike min wannan zagin ba hmmm!!!."

Ya ƙarasa maganar yana cije yatsa.

Itama Hajja cikin tsawar tace.

" Bai isa ba ubana zuwa zakayi ai ka dakeni ba tsawa zaka min cikakken tantiri marar mutunci azzalumin bawa to ko ubanka bai isa ya dakatar dani ba idan ina magana bare kuma ƙaramin ɗan iska."

DOCTOR hanunsa yasa da ƙarfi ya daki gini cike da haushi, tare da hura isa mai zafi a bakin sa wani irin mungun Sabuwar tsanar falmata ne yake ji a cikin ransa, ficewa yayi da sauri, saura kadan ya bige Aunty Yana dake tsaye tun sanda ta juyo hayaniyar su tazo wajen, Aunty YANA murmushi ta saki cikin farin ciki ta ƙara cikin ɗakin Hajja tana cewa.

" Abinda nake faɗa miki kenan kika kasa ganewa, Hajja yanda yake zaluntar yarinyar............"

Hanu Hajja ta ɗaga mata tare da cewa.

" Rufe min baki, keɗin ma kanwar lasa ce, duk abinda ya sami ƴarta ki ai laifin kune ya shafe ta, fice min daga ɗaki munafukar banza, ƙulle ƙullen ne bakya yi dukkan ku a tafin hanuna kuke, kallon ku nake tar da idanuna kuma duk na kusa maganin ku, fice bana son munafurci "

Aunty YANA fita tayi siɗi siɗi tana tura baki, tana ƙunƙuni.

" Ai kuwa baki san ina ƙulle ƙulle ba tunda ƙulle ƙullen nawa ban taɓa biyo dashi ta kanki ba, da yanzu baki da bakin zagina, ko tsintsiya na baki nace ki share tsakar gidan nan sai kin share, ayi masifaffiyar tsohuwa ta addabi mutane."

Ta ƙarasa maganar tana shigewa ɗakin ta, Hajja kallon Yagana dake kwance tayi a gefen ta tayi shuru tana kallon su tace.

" Tashi kema ƙaramar munafuka kinje kin kashe Auren ki, kinzo kin sani a gaba, kema na kusa dawowa kanki muddun baki fitar da miji kin bani waje ba, ki tashi kije ki kira min Yayanki Bukkar acan fadar."

Yagana tashi tayi ba tare da cewa Hajja komai ba gudun kar masifar ta dawo kanta, ta shige kiran YALLAƁOI wanda Hajja ke kiran sa da bukkar.

Yana zaune Yagana ta samesa, ta sanar dashi sakon Hajja, kusan tare ya tashi suka shigo da Yagana, amma ita

Please Login or Register in order to submit comment