Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shimfida musu wata taburmar tana musu sannu da hanya Fanta dake zaune gefe ne ta gaishe su tana musu sannu da zuwa, malam Gana zama yayi a gefe yana ƙarewa UMMA kallo tare da nazarin ciwon nata, sosai ya ƙare mata kallo kafin ya dubi DOCTOR yace.

" Wannan ciwon nata Asiri ne aka mata, ba ciwon Allah da Annabi bane sannan kuma asiri ne mai wuyar karyawa saboda an mata ture harda aljanu shiyasa take wani kamar na marassa hankali."

Da sauri DOCTOR ya dubi Malam cike da kiɗima yace.

" Malam duk inda mukaje karɓar magani abinda ake faɗa mana kenan, malam anya kuwa Umma zata sami lafiya."

Ya ƙarasa maganar cike da raunin murya, murmushi malam ya saki tare da cewa.

" Zata warke bi'izinillah, hanune yayi asirin ai, Kuma hanune zai karya sa, na ɗauka maka alwashi da izinin Allah sai na karya wannan sihirin, karka samu damuwa mahaifiyar ku zata warke kamar bata taɓa wani ciwo ba."

Jinjina kansa yayi tare da cewa.

" Shikenan Allah ya sa mun gode sosai, to yanzu malam nawa zamu bada kuɗin maganin."

Murmushi Malam yayi tare da cewa.

" Karka damu da kuɗin magani, bana buƙatar su, bana karbar kuɗin magani ina yine fisabilillah, zan mata magani kyauta fatan dai Allah ya mana jagora ya kuma bata lafiya."

Da ameen dukkan su suka Amsa DOCTOR yana jinjinawa karamci irin na wannan malami da abun duniya sam bai ruɗe sa ba DOCTOR duban Bello yayi tare da cewa.

" To Bello kai da AJIRAM da Fanna zaku koma gida anjuma, ni da Hajjo zamu zauna, ni ɗin ma ba zama zanyi, gobe zan dawo Hajjo ma kaɗai zatayi jinyarta idan yaso sai adinga zuwa ana dubata."

Da to suka Amsa, Fanta ne ta taho da ƙwarya a hanunta mai cike da nono wacce tasha fura damammiya ta ajiye musu a gaban su, komawa tayi ta ƙara dawowa da wata ƙwaryar tuwon BURABUSKO NE MIYAR GANYEN YAKUWA ta ajiye sannan ta samu waje ta zauna (Yasin nasan idan akwai kanuri mai karatun book ɗin nan yawunsa ya tsinke 🤣) Malam yace musu Bismillah kuci abinci.

Abincin suka ci shidai DOCTOR furar kawai yasha, saboda ransa a ɓace yake baya jin zai iya cin abinci har yanzu Maganar da yarinyar nan ta faɗa masa ne take masa yawo a kunnen sa, hanu yasa ya toshe kunnen sa tare runtse idanunsa yana jin zafin Maganar.

Da gudu Kuwa ta shigo cikin gidan tana tuntsire dariya har da sunkuyawar ta, ADDABO LUTIYA ne ta biyo ta cikin gidan da gudu itama, ƙara AI'SA ta saka sanda su Hajjo suka tsorata DOCTOR da sauri ya buɗe idanunsa yana duba wajen da ƙarar ta fito, fes ya ɗaura idanunsa akanta cike da tsana yake kallon ta, Malam ma cikin ɓacin rai ya dubeta ita kuwa ɗakin Kaka ta shige tana cewa.

" Na shiga Uku kaka, wannan ɗimemiyar mai ƙirar samudawa zata kashe ni, dan wallahi tana zama a kaina sai dai wata amma ba niba."

KAKA dake zaune tana ɓarar gyaɗa ne ta rarumo sandar ta, ta miƙe da ƙyar ta fito bakin ƙofa ta tsaya, turus ADDABO ta tsaya tana ajiyar Zuciya kallon ta kaka tayi tace.

" To Uwar marassa kunya, yanzu biyota kikayi har gidan ubanta ki daketa Saboda baki da mutunci, to ai ko mutuwa ma tana Kunyar idon uwar ɗa bare kuma ke, maza fice min daga cikin gidan nan kafin na raɗeki da sandar nan, marar Kunyar wofi "

ADDABO cike da haushi tana haki tace.

" Wallahi kaka bazan bar nan ba, sai nayiwa Ai'sa shegen duka, uban waye yace ta ce min ADDABO ƳAR LUKUTA MAI SIFFAR KWAƊI Allah bazan yadda ba sai na rama."

Ta ƙarasa maganar tamkar zata saka kuka, ai kuwa tun kafin kaka tayi magana, AI'SA ta rigata cewa.

"Ubanki ne, tunda sune suka haifeki ƴar lukuta, Kuma na faɗa ADDABO ƳAR LUKUTA MAI SIFFAR KWAƊI, ƙarya nayi ke ba mai siffar kwaɗin bane, kiga fa yanda kike dunƙule kamar kwadon."

Kaka dariya tasa tare da cewa.

" Shakka babu jikata Ai'sa batayi ƙarya ba, kamarki sak da kwaɗin, dubeki fa tsabar dunƙulewa da kikayi ko wuya baki dashi, zaki kauce min a ƙofar sauro ne ko sai naci uwarki SA'A mai koko."

DOCTOR Kaka kawai yake bi da kallo mai cike da ɗunbin mamaki, yau yaga ɗaurewa ƙarya gindi, yarinya ta nemo faɗa, ta gudo gida maimakon a hukuntata sai kuma a ɗaure mata gindi Tabbas dole wannan yarinyar tayi rashin kunya."

Girgiza kansa kawai yayi yana ƙara jin wata irin sabuwar tsanar yarinyar, idanunsa ya ɗan rufe tare da buɗesu yana cigaba da ƙarewa kaka kallo na marar adalci, Malam Gana tashi yayi ya nufesu, sanda yaje ya tsaya a gaban ADDABO cike da kulawa yace.

" ADDABO kiyi hkr kinji duk naji abinda kikace ta miki, kiyi hkr bata kyauta ba, Kuma insha Allah zan hukunta ta, bazata ƙara miki ba kinji."

ADDABO cike da jin haushi ta jinjinawa Malam kai kafin ta juya ta fita tana ƙananan magana, kaka ce tace.

" Zata sake !!! Nace sai ta sake tsokanar tata, kazo kayi abinda zakayi, har wani zaka hukunta ta, to hukunta ta mu gani, tunda kana gadarar kai ubanta ne, to bari kaji wallahi babu ruwan ka da yarinyar nan, ka fita idanunta ka barta tayi abinda take so haka kawai kunsa yarinya a gaba."

Malam Gana cike da girmamawa ya cewa mahaifiyar tasa.

" Allah ya huci Zuciyarki AMMA (dake haka yake kiranta dashi), amma AMMA baki ganin abinda *A'ISHA* take a cikin garin nan yayi yawa, ina guje mata bakin duniya ne AMMA kar bakin mutane yayi yawa a kanta bakin mutane guba ne wani bakinsa bashi da kyau, abinda nake so ki fahimta kenan, saboda ita macece wa zai yadda ya aureta da wannan rashin ɗa'ar da take dashi ni kaina uban da na haifeta zan bada shaidar rashin kunyarta dan Allah Amma ki daina biye mata na roƙeki."

Cike da faɗa kaka tace.

" Ni na auru ai ko tunda har na haifeka, tunda na auru to Itama zata auru domin kuwa na fita faɗa sanda nake kamar ta, Kuma a haka ubanka yake sona Ko ɓacin raina baya so, haka zamuyi faɗan mu, cikin dare ya rarrashe ni, mu shirya, dan haka karka kuskura ka mata mungun baki, juyawa tayi ta kalli Ai'sa tace mata, Ai'sa duk wanda ta miki a cikin garin nan kema ki masa karki raga masa ko ubansa waye ne."

Wani ɓacin rai Malam Gana yaji a cikin ransa harga Allah baya jin daɗin abinda AI'SA keyi, sannan baya son irin tarbiyyar da kaka take bata, ɗan yaune kawai ka haifesa baka haifi halinsa ba da Ai'sa ta ɗauko sa ko yatsa aka sa mata a baki bazata ciza ba, juyawa yayi ya koma ba tare da yacewa kaka komai ba, amma sam ranshi babu daɗi, kaka komawa tayi cikin ɗakin itama tana zungurin Ai'sa da sandar hanun nata tare da cewa.

" Munafukar Allah, da kika tsokanota da ta riƙeki, ta zaune a ruwan cikin ki da wannan ɗimaɗiman ɗuwaiwan nata, da sai kinyi kashin hanjin ki, gobe na sake jin kin tsokanota kiga yadda zan barki da ita ta jibgeki kamar Allah ne ya aikota"

Bakin ta Ai'sa ta tura cike da rashin mutunci tace.

" Malama daina zunguri na mana, niɗin shegiya ce zan tsaya harta dukeni, kuma wallahi ko gobe na ganta sai na tsokanota."

Ta ƙarasa maganar cike da tsiwa tana fita, wajen Mama ta wuce tana ganin su Hajjo ko kallon su batayi ba zata wuce, Malam ya kirata.

" Ke AI'SA zonan."

Tahowa tayi tana tura baki ta tsaya a kansa ba tare data risina ba tace.

" Gani Malam."

Malam ɗaga kansa yayi ya kalleta cikin ɓacin rai yace.

" Bani maganin nasha, kinji uwata tunda kin tsaya a kaina."

Bakin ta tura tare da zama tayi shuru Malam Gana faɗa ya hau mata.

" Wai yaushe zakiyi hankali ne kam, sam ke a Duniyar ki baki daraja mutane, Ai'sa ina son ki dawo hankalin ki ki nutsu kisan me kike yi bana son duniyar ta nuna miki kurenki domin kuwa baza kiji daɗi ba, jiyan nan Malam Umaru ya kawo min togaciyar ki kin zagesa, sa'anki ne shi, to wallahi ki kiyayi duniya, ki daina biyewa AMMA tana ɗauraki a turbar da ba itace gaskiya ba, ina miki faɗa ne a matsayina na mahaifinki, sannan kina kallon Mutane bazaki gaishe su ba, sai ki saka kanki ki wuce, to maza ki gaishe su."

Ƙara turo bakin tayi gaba, kafin ta kalli su Hajjo tace.

" Inda dabtu."

Ta gaishe su cikin harshen kanuri, amsawa sukayi cike da mamakin yarinyar, juyowa tayi zata ɗagawa su DOCTOR gaisuwa, karaf kuwa suka haɗa Ido dashi, zaro ido tayi tana mamakin meya kawosa gidan su, shi kuwa harara ya wurga mata, tsuka taja tare da cewa.

" Malam ya isheka harara ta, sai wani kallon banza kake min da wasu ƙananun idanunka kamar wanda ka roƙa aka sammaka, an faɗa maka gaishe ka zanyi da kake shirin nuna min IZZA, Mtsss!!!! Marar lissafi kawai."

🤣 Kuzo kuga baƙin ciki a ZUCIYAR DOCTOR ji yake kamar ya shaƙo wuyanta sai ya kaita lahira kafin ya saketa, yunƙura yayi zai tashi, Bello yayi saurin riƙesa yana girgiza masa kai, alamun ya bari baƙunta sukazo, komawa yayi ya zauna iya jin wani takaici yana hauro masa, Malam Gana cike da haushi ya yunƙura zai jawota ya mata shegen duka, ganin haka da AI'SA tayi ya sata tashi ta fice da gudu, cike da jin haushin abinda ta musu Malam yace.

" Kayi haƙuri Yaro kaji ɗan yaune ka haifesa baka haifi halinsa ba, haka nake fama da Ita, kayi hkr, ka mata addu'ar shiriya."

Tsabar takaici DOCTOR kasa amsawa Malam yayi, shi dai bai taɓa tsanar mutum ba, irin yanda ya tsani wannan yarinyar.

Awansu biyu Malam ya fara yiwa UMMA magani bayan ya bada ɗaki guda wanda za'a ajiyeta a ciki da la'asar lis DOCTOR ya bawa Bello kay ɗin mota yace su koma gida, gobe da azahar yazo ya ɗauke sa, haka kuwa akayi suka kama hanyar cikin Maiduguri har suka tafi Ai'sa bata dawo cikin gidan ba.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*MAIDUGURI*

"What!!!! Kasan kuwa mai kake faɗa min kana nufin sun tsira karka cemin sun isa cikin ƙauyen nan.!!"

Daga can Jamo yace.

" Ehh sun tsira gaskiya, nayi duk yanda zanyi dan ganin basu kwana a duniya ba, amma abun yafi ƙarfi na, saboda Yaron yana da mungun wayo."

Tsuka Jummai taja tare da kashe wayar kanta ta dafe zuciyarta sai famar tsinkewa take, a fili ta furta.

" Ina bazai yiwu ba, bazan bari YAMURAM ta dawo cikin hankalinta ba, dole sai ta bar numfashi a duniya dole ne ma, zanje wajen Malam gobe, idan har ya tabbatar min zata sami lafiya ni kuwa sai nasa an bita har cikin ƙauyen an Kaita lahira."

Ta ƙarasa maganar tana huci, sai kuma taja tsaki tare da kwanciya cikin tashin hankali.




*UNIMAID*


A matuƙar gajiye suka fito daga lectures ɗin Maji ne ta dubi Falmata tare da cewa.

" Muje Capteria yunwa nake ji sosai wallahi, tun abinci safe kinga yanzu har 3:40."

Juyawa sukayi suka nufi Capteria suna taɗi, waje suka samu suka zauna Maji ta dubi Falmata tace.

" Me za'a kawo miki, ni jalop nake bukata."?

Numfashi Falmata ta sauƙe tare da cewa.

" Babu abinda zanci ruwa kawai nake buƙata nasha magani."

Kallon ta Maji tayi tare da cewa.

" Me kikaci da zakice kin ƙoshi, Wai Falmata na lura tun ɗazu lectures ɗin da ake babu rabin hankalin ki a kansa, duk rabi ya tafi ne a tunanin mutumin da baisan darajar ki ba, a rayuwarsa ki dawo hankalin ki, ki manta da wani Hassan a cikin rayuwarki, domin kuwa shi ya juma da mantaki tunda harya sakeki dan haka ki daina ɓata lokacin wajen tunanin mutumin daya manta ki a duniyar sa, yanzu dan baki da hankali ke sai kisha magani ba tare da kinci abinci ba."

Murmushi mai ciwo Falmata tayi tare da cewa.

" Bazaki taɓa fahimtar irin Soyayyar da nake yiwa DOCTOR bane, da ana iya cire Soyayya da ƙarfi a cikin zuciya dana cire Soyayyar DOCTOR daga cikin raina, sai dai hakan bazai yiwu ba, saboda bani nake da iko da zuciyata ba, ni kaina nasan bana cikin zuciyar DOCTOR, sai dai ina mamakin yanda ni kuma yake maƙale a cikin zuciyata, kullum Soyayyar sa ƙaruwa take a zuciyata maimakon ta ragu, lissafi na yakan ƙauce min a duk sanda na gansa ina son mijina Maji bazan iya doguwar rayuwa babu shiba, taya zanyi DOCTOR ya dawo gareni, ki taya ni neman hanyar da zan koma gidan mijina ƙawata pls."

Tunda ta fara Maganar maji take kallon ta cike da haushin ta, tsuka taja tare da cewa.

" Wai ke Falmata meyasa shashasha ce ke a cikin Soyayya, meyasa kike ƙaunar mutumin da baya ƙaunar ki, meyasa kike son mutumin daya Raina iyayenki, shin kishin iyayen kine bakya yi, ko kuma kinfi sonsa ne sama da iyayen ki, wallahi Falmata ina jin haushin zuciyarki, da ana bada aron zuciya dana baki aron tawa ko Allah zaisa ki cire Soyayyar wannan ɗan iskan azzalumi wanda bashi da imani bare kuma tausayi, Falmata idan har nine kike tunanin zan share miki hanyar da zaki koma gidan Hassan to ki saka a ranki kin rasa sa kenan har abada, domin kuwa na gwammace na ɗebo ƙayoyi na watsa a hanyar domin ki rasa wajen takawa bare kuma ki shiga."

A fusace Falmata ta miƙe tsaye cikin ɓacin rai tace.

" Maji ya isa haka ki daina zagin DOCTOR, kina ƙona min zuciyata ne idan kina aibata sa, Maji, wallahi komai tsinin ƙayar dake Hanyar gidan DOCTOR zan juri takata domin ta isar dani har cikin gidan sa, na faɗa miki zuciyata bazata taɓa iya doguwar Rayuwa babu DOCTOR a tare dani ba."

Kaɗa kanta maji tayi tare da cewa.

" Lallai kina cikin masifa da jarabawa....................."





Ki biya ki karanta yar uwa, 0006064512 Rashida Usman Jaiz Bank ko kuma mtn card na 300 sannan ki turo shaidar biyan ki, yafi miki sauƙi akan a baki wanda ba gumin kiba



Alƙalamin UMMU NASMAH CE
[9/11, 4:27 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN*

_______✍🏻 " Meyasa zakice ina cikin masifa bayan kinsan Soyayyar DOCTOR da ita aka halicce Ni, na Tabbata Ubangiji bazai ɗaura min masifa ba, Maji meyasa bakya fahimtar irin Soyayyar da nake yiwa DOCTOR, kece wacce ya kamata kifi kowa yiwa soyayyata uzuri amma kin kasa Numfashi nane DOCTOR taya kike tunanin ɗan Adam zai iya rayuwa babu numfashi."?

Ta ƙarasa maganar cikin raunin murna, ajiyar zuciya Maji ta sauƙe tare da cewa.

"Lallai kuwa kina hanyar mutuwa idan har Hassan shine numfashin ki, Allah bai halitta miki Soyayyar sa ba, kece dai kika halitta wa kanki, wai ma shin na tambayeki soyayya hauka ce kam.?"

" Ƙwarai kuwa Soyayya hauka ce abu ɗaya suke tafiya dashi, wani lokacin ma gara mahaukaci baya jin zafi a cikin zuciyarsa, dan Allah Maji kiyiwa zuciyata adalci ina son Doctor na fara kasa jure rashin sa, karku bari Soyayyar sa ta kasheni."

Taɓe bakin ta Maji tayi tace.

" Tabbas idanunki sun makance yayin da kunnuwan ki suka toshe, na Tabbata yanzu bakya ji ba ƙya gani, hanyar da zuciyarki ta ɗauka ita kawai kike bi, hanya mai cike da tarin wahala da ƙalubale, Allah ya fitarki a cikin jarabawar da kika faɗa, ki tashi mu tafi na fasa ma cin abincin."

Girgiza kanta Falmata tayi tare da runtse idanunta hawaye ne ya gangaro mata ta saka hanu ta gogesu tare da cewa.

" A'a bazan hanaki cikin abincin ki ba saboda damuwa ta, ki zauna kici abinci sai mu tafi karki ƙi cin abinci saboda ni bazan ciba, hakan zai zamo kamar na cutar dake ne."

" A'a bazan iya ciba saboda kin riga kin cire min sha'awar son cin abincin, bana ƙaunar na ganki cikin damuwa, sai naji nima hankali na yana tashi, ta yaya kike tunanin zan zauna a gaban ki na iya ci na ƙoshi bayan ke cikin ki da yunwa, tashi kawai mu tafi."

Tashi Falmata tayi suka tafi, har suka fito bakin get babu wanda ya iya cewa ɗan uwansa wani abu a daidaita suka hau, sai yanzu Falmata ta dubi Maji tace.

" Da Soyayya da hauka basu da wani banbanci Maji muddun aka samu saɓani da rashin fahimta cikin Soyayya, SO yakan zautar da mai yinsa ya hanasa bacci ya hanasa ci ya hanasa sha ya kuma hanasa walwala, mafi girman muguntar so shine ya sa maka ciwo, idan akayi rashin dace ma ya kasheka *SO DANGIN MUTUWA* amma idan kikayi dace da masoyin ƙwarai babu abinda ya kai Soyayya daɗi a duniya ji zakiyi duniyar ta miki daɗi, kiji babu komai cikin zuciyarki sai farin ciki da annushuwa, shiyasa ma'abota soyayya suke ƙiranta *ZAƘI DA MAƊACI* sai dai ɗacin nata yafi zaƙin yawa, Maji ina son Doctor sai dai shi baya sona a yanzu, ta wani waje kuma zuciyata ta kasa aminta cewa DOCTOR baya sona, , ya kike tunanin rayuwata zata kasance idan babu DOCTOR a cikin ta, amsa ko ciwo ya kamani ko kuma na mutu, muddun bai dawo cikin rayuwata ba, ke wacce makoma kike hango min anya kuwa ina da hanyar da zata ɓulle min."?

Shuru Maji tayi tana kallon Falmata cike da tausayin ta, tace.

" Ai ba sai na hango miki makomarki ba, tunda kin riga kin hangowa kanki, sai dai abu ɗaya nake son na sanar dake, idan kin mutu ko kin kwanta ciwo Hassan ba zai fasa Rayuwar sa ba, ƙarshe ma dai Auren sa zaiyi ya manta da an taɓa halittar ki a duniya saboda babu komai tsakanin ku, ma'ana baku haihu tare ba, dan haka ina ƙara faɗa miki ki dawo hankalin ki."

Shuru Falmata tayi tare da runtse idanunta, ita dai tasan tana son Doctor har yanzu zuciyarta ta kasa yadda cewa DOCTOR baya sonta, ajiyar zuciya ta sauƙe, duk sukayi shuru har mai adaidaitan ya iso ƙofar gidan su Falmata, fita tayi Maji dubanta tayi tace.

" Sai na shigo."

Da to Falmata ta amsa sannan ta juya zata shiga cikin gidan, HABEEB ta gani tsaye jikin motar sa yasha ɗanyar shadda voyal ya zuba hannayensa cikin aljihu, fuskar sa ɗauke da murmushi ga sanjen daya kwanta luf luf a fuskar tasa gwanin ban sha'awa, haka gashin kansa ma yake sheƙi, Tabbas Allah ya yiwa HABEEB halittar kyau, tamkar bafulatani haka yake, Falmata haɗa fuska tayi tare da ɗaga kanta zata shige tamkar bata gansa ba.

" Ba halinki bane wulaƙanta ɗan Adam, ki juyo ki saurareni tunda nasan kin ganni, idan kuma kika wuce to Tabbas sai na biyoki har cikin gidan kin san dai gidan ba baƙo na bane ko."

Cak Falmata ta tsaya tana sauraron Maganar sa, ranta ɓace ta juyo tare da cewa.

" Ko ka manta ina da Aure ne, kake ƙoƙarin tsayar dani wai menene hujjar kane ta shiga Rayuwata."?

Murmushi HABEEB ya saki yace.

" Ya mayar da Auren naki kenan bayan ya sakeki shekaran jiya, kikace meye hujja ta ta shigo Rayuwar ki ko? To da hujja kuwa na shigo rayuwarki tunda ina da labarin sakinki da wannan lusarin mijin naki yayi."

Ƙanƙance ido Falmata tayi tare da kusanto HABEEB tace.

" Karka ƙara kira min sunan miji da lusari, domin kuwa shiba lusari bane, sannan ka adana hujjar ka domin kuwa daf nake da komawa gidan mijina, ko ka manta banyi iddaba to ka shiga nutsuwar ka, domin kuwa ina son mijina."

Dariya sosai HABEEB yayi yana karewa Falmata kallo kafin ya ce.

" To Shikenan bari muga zuwa nan da ki gama iddar ko zai maida ki ɗakin naki, sai dai fa ki sani, shifa wannan lusarin mijin naki, Ba wai yana da cikakken hankali bane domin kuwa duk namiji mai cikakken hankali bazai yi kuskuren rabuwa dake ba, Karki manta da cewa har GOBE HABEEB na sonki😉."

Yana gama faɗin haka ya juya ya shige cikin motar sa yana kanne mata ido shuru Falmata tayi ta jima tana tsaye tana nazarin maganganun HABEEB, tambayar da bata da amsar sa take yiwa kanta, shin meyasa kowa yake faɗar Magana marar daɗi akan DOCTOR, meyasa suka kasa fahimtar DOCTOR mutumin kirki ne.? Rasa amsar tambayar ta yasa ta shigewa cikin gida tana jinjinawa Maganar HABEEB.

" HABEEB wai meyasa ka kasa cire yarinyar nan a zuciyar ka, kana ta dakon Soyayyar banza, ganan Yan mata da yawa ƴaƴan manya suna binka suna cewa sonka suke meyasa bazaka zaɓi ɗaya a ciki ba? ka manta da wannan yarinyar domin kuwa ba sonka take ba."

Murmushi HABEEB ya saki yana kallon SADIQ yace.

" Bazaka fahimci girman son da nake mata bane shiyasa kake kiran na rabu da ita, a yanzu ina da ƙwarin gwiwwar cewa zan sami FALMATA a matsayin matar Aure na, na Tabbata ƙaddarar Aure na ne ya fito da ita daga gidan DR HASSAN."

Numfashi SADIQ ya sauƙe yace.

" To ikon Allah, amma kana tunanin iyayen ka zasu yarje maka ka Auri BAZAWARA a matsayin ka na saurayi wanda bai taɓa yin Aure ba.?"

Ya jefa masa tambayar yana duban action ɗin HABEEB mai makon yaga firgita daga fuskar HABEEB sai murmushi ya gani kwance cike da nutsuwa HABEEB ya basa amsa.

" Duk abinda nake so shi iyayena suke so, muddun ba abinda ya kaucewa Shari'a bane, bare kuma sun san girman son da nake yiwa Falmata, bani da matsala da iyayena domin kuwa a kullum sukan fahimce ni, matsala ɗaya ce kawai take gabana yanda zan ƙwace zuciyar Falmata daga hanun Dr Hassan."

Murmushi SADIQ ya saki tare da cewa.

" Wannan abu ne mai sauƙi, zaka iya ƙwace zuciyarta ta hanyar ƙyautata mata da kuma iyayen ta, domin kuwa ko wani rai yana son mai kyautata masa, sannan ka kasance mai yawan bata kulawa da kuma jure duk wani fushin ta a kanka kar ka bari zuciyarka tayi saurin sarewa Saboda tafi son Dr akanka, ka jure har ka samu cikar burinka, ina Tabbatar maka Abokina idan kayi haka ka gama samun zuciyarta."

" SADIQ zanbi dukkan shawarar ka, koda kuwa zan zama bawan ta ne, ina sonta Soyayyar da ban taɓa yiwa wata ƴa mace ba, Soyayyar gaskiya nake mata, SADIQ da Allah zai mallaka min Falmata a matsayin matar Aure na, na Tabbata zan bata cikakkiyar kulawar da zata manta da meye damuwa a duniya, ka sani cikin adduar ka Allah ya cika min buri na."

Dariya SADIQ yayi yana bawa HABEEB hanu suka tafa yace.

" Abokina insha Allah nasara tana tare da kai, yanzu ne zamu nunawa Dr Hassan, ya kuskure daya saki Falmata, tunda ya kasa fahimtar cewa mace kamar Falmata ADANA su ake a waje mai tsafta ba'a sakaci dasu domin kuwa kana tsayawa kallon ruwa ƙwaɗo zai maka ƙafa sai dai ka wayi gari cikin nadama da cizon yatsa."

Dariya HABEEB yayi suka ci-gaba da taɗi har HABEEB ya sauƙe SADIQ a Companyn sa, sannan shima ya shige nasa Companyn.



***********

" Garin yaya haka ta faru Jummai, ya akayi ya sake har suka kufce masa, amma wannan akwai jakin yaro, yanzu kinsan kuwa girman tashin hankalin da yake tunkaro mu, YAMURAM itace kawai tasan cewa nine na ɓatar da mijinta da ƴarta Saboda JALILA ta sanar da ita ta waya ba tare da na sani ba, sannan ta kamani ido da ido kunne da kunne ina waya cewa a kashe su sannan tasan da dukiyar da muka ƙwata a hanun mijinta muka kai ɗan mu MAHMUD ƙasar waje karatu, me kike tunanin zai faru idan har YAMURAM ta dawo cikin hankalinta.?"

Yana huci cike da tashin hankali yake Maganar Jummai ita kanta a cikin tashin

Please Login or Register in order to submit comment