Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dakawa Falmata, tayi shuru kafin ya fara magana cike da nutsuwa.

" Bulama wannan hukunci da kuka yanke sam baiyi daidai ba ku fahimce ni, tunda yaran nan suka nuna suna son junan su, abinda yafi sauƙi shine a barsu, saboda dukkan su ya'yan mu ne babu bare a cikin su, sannan Hassan yana gama karatunsa zai fito da aikin sa, yaran zamani ba'a musu tilas a musu Aure shine kawai abinda yafi alkairi saboda hanasu da kuke ƙoƙarin yi kar yaje ya haifar mana da ɗan da bashi da ido, ku dubi idanunsa hakan yana nuna cewa zasu aikata komai domin su mallaki junansu, Tabbas nasan zafin ran Hassan amma ina tabbacin Falmata zata Iya zama dashi tunda tana da hkr dan Allah ku duba Magana ta, ku kuma duba Zamanin da muke ciki, ba irin na da bane da ake yiwa yaro Auren dole."

Gabaki ɗaya shuru sukayi kafin Bamai yace.

" Tabbas Bulama Maganar Bukkar gaskiya ce, nima nafi son a barsu suyi Auren , idan Maganar ɗakin da zasu zauna ne kafin Allah ya hore masa ai naga ga gidan shi Bukkar wanda ya saya nan baya zai iya basu su zauna kafin Allah ya hore masa yayi nasa.''

Baba zaiyi Magana Bulama ya ɗaga masa hanu yace.

" Na fahimce ku, to naji za'a barsu suyi Auren, to ku faɗa min zamu zuba mata ido ta jirasa har shekara bakwai."?

Bamai ne yace.


" Ba haka muke nufi muna nufin ayi Auren kafin ya tafi idan yaso sai ta jirasa a cikin gidan nan harya gama karatun sa."

Shuru Bulama yayi kafin yace.


" Ban gamsu da wannan maganar taku ba dole ina bukatar nazari kafin na yanke hukunci ku tashi kuje zan sake neman ku daga baya."

Ai kuwa kafin kowa ya tashi DOCTOR ya rigasu a zuciye ya fice yana huci cike da jin haushin kakan nasa, ji yake kamar yace ya haƙura da Auren tunda ba ita kaɗai bane mace a duniya da ake neman walaƙanta sa a kanta kamar wata ƴar gwal.

Jinjina kansa Baba yayi yana binsa da kallo harya fice, dama wannan zuciyar tasa yake tsoro, da baya iya control ɗin ta a ko ina.

Gabaki ɗaya tashi sukayi suka fice daga ɗakin suka bar daga Falmata sai Bulama Falmata kusa da BULAMA ta matso Cikin sanyin jiki tace.................."






Sorry for typing error ban samu nayi Editing ba, kaina ke ciwo.

Masu cewa na ƙara yawan typing kuyi hkr insha Allah zan ƙara muku.






Ki biya kuɗin ki ta kafin ki karanta karki karanta abinda ba gumin ki ba nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya 08147537180






*ALƘALAMIN UMMU NASMAH CE*✍🏻
[9/24, 12:02 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 59 to 60*





_________✍🏻 " kaifa kamin alƙawarin cewa zaka aura min duk wanda na kawo maka a matsayin mijin Aure na, meye aibu a jikin DOCTOR, ɗan uwana ne fa Bulama, meyasa zaku ƙisa ku so bare, bayan kuma shine wanda nake so.?"

" Saboda halinsa shiyasa muka ƙisa, muna ƙin Hassan ne saboda guje miki wahala amma ke naga alamar bakya fahimtar hakan, Fatuma, dake da Hassan duka jikoki kuke a gareni, nine mutumin daya kamata ace nafi kowa farin ciki da wannan zumunci da kuke so ku haɗa, amma tunda kika ga akasin haka a tare dani to ya kamata ki duba lamarin, danke ne muke ƙin wannan auren da kuma ɓacin zumunci, Hassan ba mutum bane Normal kamar sauran mutane, yana tattare da abubuwa huɗu wanda ba'a son ɗan adam ya haɗasu duka, Zafin Rai Rashin haƙuri da kuma rashin yafiya ga kuma son kansa, taya kike tunanin zaki iya rayuwa ta Aure dashi a haka, ki fuskance mu Fatuma muna sonki ne yasa muke nema muku maslaha."

" Na fuskance ku Bulama sai dai ka sani DOCTOR bazai min duk abinda kuke zato ba, zamu zauna lafiya, mu kasance abun kwatance da sha'awa, dan Allah Bulama ka barni na auri zaɓin raina, saboda shi nake so zanyi haƙurin zama dashi a duk yanda ya kasance."

" Bazan iya ba Fatuma, ki haƙura kawai da Hassan Allah ya baki wani mijin na gari, shima Allah ya basa wata matar a can waje, Auren zumunci kam bazamu muku shi ba, tashi ki bani waje."

" Dan All.........."

Tsawa Bulama ya daka mata daya sata tashi a firgice ta fice cikin tashin hankali, Bulama tsuka yaja yace.

" Yaran Zamani marassa kunya, ta tsaya gabana sai famar magiya take min ita lalle na barta da wanda take so, mu kuma lokacin mu da aka mana Auren da babu wanda yasan wa zai aura sai da akayi auren tukunna muka san juna, ai bamu mutu ba, tunda gashi mun zauna har mun haifi iyayenku, yau naga shegan taka wajen yarinya, Soyayyar banza, zaman lafiya da kwanciyar hankali muke nema ba Soyayyar ku ba."

Ya ƙarasa maganar cikin sababi, FALMATA kuwa barowar ta wajen BULAMA ɗakin Aunty YANA ta faɗa tana kuka, Aunty YANA dake zaune ita da FANNA ne ya sata duban Falmata a tsorace tana cewa.

"Innalillahi ke meye haka kike min wannan ihun, waye ya mutu da zaki shigo min haka zaki tsinke min zuciyata."

Jikin Aunty YANA ta faɗa cikin kuka tace.

" Mama ki taimakeni, Bulama yaƙi yadda da Aure na da DOCTOR, WALLAHI Mama ina sonshi, bazan iya rayuwa babu shiba, kice karsu rabamu mama, wallahi aka rabamu dashi bazan yi Aure ba haka zan zauna har abada babu Aure.''

Tsuka Aunty YANA taja tana jin Tamkar ta tsinketa da mari, bakin ta bige tace.

" Amma dai ke Falmata anyi shashashar banza marar kunya, yanzu ke idan Banda lalacewa, shine kike tabkar wannan kukan akan ɗanamjji kamar wanda aka ce miki na mutu, aiko ni na mutu baza kiyi wannan kukan ba, to bari kiji Falmata koni nan bana son Auren ki da Hassan, sai dai idan dole ya zama babu yanda na iya sai na haƙura, saboda Hassan ba tsarin mijin da zaki Aura bane, nasan ke mutum ce mai haƙuri, dole zaki cutu da Auren Hassan, kinga shi idan ya tashi rashin mutuncin sa baya ragawa uban kowa, gashi kuma ba sana'a garesa ba, dan haka ki dakatar da zancen Aure tsakanin ku, kafin ranki ya ɓaci."

" Na shiga Uku Mama wai ina zan kai kuka na naji daɗi ne, kowa sai yace zan cutu zan cutu, na gaji da jin wannan kalmar, ni ko da yankar naman jikina kullum zai dinga yi, na yadda zan Aure sa a haka, dan haka babu ruwan ku ku barni da abinda nake so."

Ta ƙarasa maganar tana tura baki hawaye kuma na gudu saman fuskarta, Aunty YANA kallon tsoro tabi Falmata dashi da mamaki tace.

" Ni kike ɗagawa murya saboda ina nemawa rayuwarki maslaha yayi kyau, shige ki wuce ki barmin ɗaki na."

FANNA dake zaune tana sauraron sune, taji ranta yayi mungun ɓaci da furucin Aunty YANA, akan ɗan uwanta, a zuciye Fanna ta tashi ta riga Falmata ficewa, Aunty YANA ta fahimci Fanna Haushi taji, amma ita ko a jikinta iya gaskiyarta ta faɗa, tsawa ta dakawa Falmata.

" Bazaki tashi ki fice min daga cikin ɗaki bane!!!! Sai na ci ubanki yanzun nan, wawiya marar lissafi ɓace min a ɗaki!!"

Tashi tayi ta fice cikin ɓacin rai ɗakin Hajja ta shige, da Bulama taci karo yana mayarwa Hajja abinda akayi, Falmata tsayawa tayi kansu tana kuka mai cin rai tace.

" Bazan taɓa samun farin ciki ba a rayuwata muddun kuka rabani da DOCTOR, haka kuma bazan taɓa daina kuka da ku ba, saboda kune sanadiyyar rabuwa ta dashi, a ƙarshe kuma zan tattara kayana na bar gidan nan na shiga duniya tunda bakwa ƙauna ta, duk kuma abinda ya sameni kuna da alhaki ciki."

Tana gama faɗin hakan ta juya ta fice, a jikin igiyar shanya ta figi hijab ɗin ta ta fice daga cikin gidan, Hajja kallon BULAMA tayi tare da cewa.

" Baban Mala, Tunda yarinyar nan ta ambaci shiga duniya, mu zanye domin ko bata shiga duniya ba, zasu iya jawo mana abin kunya, ku barta da Hassan ga fili ga mai doki, jiki magayi, duk abinda ya faru gaba na Tabbata bazata yi kuka damu ba, saboda mun faɗa mata."

" Hmmm!!! Hakane Maganar ki Hajja Mairo, amma wallahi yaran zamani suna bani mamaki, rashin kunya ya musu yawa, Kuma idan kin lura sam yaron nan bai damu da Fatuma ba sosai, ita tafi damuwa dashi, ai kinga shi zuciya yayi ya tafi ya ƙara waiwaito wani sai ita ya bari da faɗi tashi, Tabbas ina tausayin Fatuma, domin kuwa Soyayya tana daf da kaita ta baro ta, da zanyi tsawon wata ƙila na iya zama mata g
Katangar da zan kare mata wani abun, sai dai ita rayuwa bata da Tabbas, ko na mutu wata matsala ta taso, Hajja Mairo idan kina raye, ki taimaki Fatuma."

Shuru Hajja tayi kafin ta furta.

" Ba damuwa Baban Mala Allah ya mana nisan kwana, ka sanar dasu za'a musu Auren, sannan ya kamata ace kafin yaron ya tafi India ayi Auren saboda idan har mukace ta jirasa ya dawo daga school , duniya zata zage mu saboda shekara bakwai tayi yawa da ta jirasa, saura sati biyu ya tafi ranar Monday zai tafi ko, to a ɗaura Auren jumma'a ta sama."

" Ba komai Allah ya kaimu, bari na samu na miƙe bacci nake ji"

Da to Hajja ta Amsa tare da tashi ta shige gyara masa shimfiɗa.

Ita kuwa Falmata gidan su Maji ta nufa da Sallama ta shiga Mama ta samu tana markaɗe a dutse, murmushi ta saki tace amsa sallamar tare da cewa.

" Falmata, kece tafe."

" Ehh Mama nice, ya aiki tana nan kuwa."

" Alhamdulillah tana cikin ɗaki ki shiga ki sameta."

Shigewa Falmata tayi cikin ɗakin Maji ta zauna tare da faɗawa jikin Maji ta saki kuka mai sautin gaske, a razane Maji tace.

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!!! Falmata meya faru keda waye."?

" Maji sunƙi amincewa da Soyayyar mu, sunƙi Maji sunce basu yadda ba na shiga Uku ina cikin tashin hankali."?

" Mtsss!!!! Aikin banza, ni wallahi Allah ya isa tsakanina dake, kin tsinka min zuciyata a banza nayi zaton wani babban abune ya sameki ashe akan wannan banzan kike wannan ihun kamar wanda uwarki ta mutu."

Cike da masifa cikin kuka Falmata tace wa maji.

" Kinga Maji bana son wulaƙanci damuwa ta na kawo miki idan bazaki iya mini maganinta ba, ki ƙyale ni, basai kin zagesa ba, sai kawai kice na tashi na bar miki gidan ku."

Maji ganin ƙawarta ta dau zafi ya sata sassautowa cike da rarrashi tace.

" Ki haƙuri kawata gani da nayi kin shigo cikin ihu ne kamar wanda akayi mutuwa, yanzu meke happining kinsan ni bana son ganinki cikin damuwa ƙawata."

" Maji sunƙi yadda, sunce bazan Auri DOCTOR ba, sabida wai zan cutu inji su, na rasa meyasa basa sonshi a matsayin su na iyayen sa."

Murmushi Maji ta saki tare da cewa.

" To su mahaukata ne irinki da zasu amincewa shirmen ki, nifa Falmata banga wani son da Hassan yake miki ba, kece kawai kike haukar sa akan sa, shi bai damu dake ba, sannan tunda iyayenku suka ƙi, akwai dalili ne mai ƙarfi domin kuwa bazasu ƙisa haka kawai ba, sannan ai kema sanin kanki ne Hassan akwai shegen zafin rai ga IZZAR tsiya, ni da tun farko kinbi shawarata da wallahi baki yi nisa cikin Soyayyar sa ba."

" Ni fa Maji Shawara nazo nema wajenki taya zan mallaki DOCTOR, ba cewa nayi ki bani umarni ba, dan wallahi ina sonsa bazan iya haƙura dashi ba, numfashi nane shi, taya kike tunanin mutum zai iya rayuwa babu numfashi."?

" Hmmm!!!! Tunda kin sawa kanki wahala ai shikenan, ni dai yanzu shawara ɗaya ce tak dani shine kije ki samu Hajja cikin sanyin rai da kwanciyar hankali, kuyi Magana ta fahimtar juna, ki nuna mata irin sonda kike yiwa Hassan da kuma halin da zaki shiga idan kin rasashi wataƙil ki samu ta amince harta bawa mijinta umarnin a barku kuyi Aure, tunda naga BULAMA yana jin maganar ta, tunda kin nace dole sai shi."

" Hmmm!! Maji Hajja bazata yadda ba, domin kuwa tana daga cikin waɗanda basa son wannan Auren."

" Ke dai kawai kije ki jarraba abinda na faɗa miki insha Allah zata amince, naji labarin rashin mutuncin da Hassan ya yiwa HABEEB, kota nan ma ya kamata ki fuskanci waye Hassan Domin ko ƙwarya ta fashe akwai sauran zane sam HABEEB bai kamata ya yiwa HABEEB Rashin mutunci ba, tunda dai komai tsiya ya masa alkairi, kota nan ya kamata ki gane cewa Hassan butulu ne, kuma wallahi kinyi rashin miji na gari tunda kika yadda kika kaucewa HABEEB, HABEEB shine mutumin daya fi dacewa da rayuwarki ba wannan shashan ba."

" Mtsss!!!! Kai Maji wai meyasa kika tsani doctor ne kam, kamar wanda ya kashe miki wani naki, gaskiya bana jin daɗin wannan tsanar da kike masa."

Dariya Maji tayi tace.

" Daɗin abun ma ai idan tsanar ce bani kaɗai nake masa ba harda iyayenku, bare kuma ba tsana bace kawai halinsa ne aka tsana, ki dinga dai boye wannan Soyayyar da kike masa Kafin ya fuskanta ya fara fakewa da ita yana takaki."


" Idan kuma na ƙi na ɓoye fa sai yaya."

Falmata ta yiwa Maji Maganar cike da gatsali dariya Maji tayi ta bata amsa da.

" Sai jikinki ya faɗa miki, ai kinji kalmar nan ta Malam bahaushe yace jiki magayi, wanda baiji bari kuma ai zaiji hoho."

" Mtsss!!!! Aikin banza, kawai, sai kuma kiyi insha Allah ni jikina bazai gaya min ba, ni harma na manta da wani HABEEB a cikin wannan Duniyar, ya maganar Assignment ɗin Malam musa na TAHZIF kinyi ne."

" Banyi ba sai zuwa dare, kekam ai yanzu baki da lokacin yi tunda ana ta Kai ai ba'a ta kaya."

" Ai kuwa wallahi, bani da hankalin Assignment har sai naga abinda zai turewa buzu naɗi."

" To Allah yasa kiga alkairi................"








Mu haɗu next page🤗






Ki biya kuɗin ki cikin kwanciyar hankali yafi miki sauƙi fiye da ki karanta abinda ba gumin ki ba ki nemi ni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.




Love You my FAN'S GASKIYA ina jin daɗin yanda kuke min ruwan sharhi akan BOOK ɗin nan hakan ya nuna min kuna jin daɗin novel ɗin I love You irin sosai ɗin nan🥰








*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN ✍🏻*





*(UMMU NASMAH CE)*[9/25, 11:53 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 61 to 62*





________✍🏻"kinga Malama tashi muje ke ki yiwa Hajja Magana wata ƙil ke taji naki, nikam kinsan mawuyacin abune ta fahimce ni"

" Hmmm!!! Kinga Falmata gwara ma ki kama hanyar ki kiyi tafiyarki yafi miki sauƙi nikam babu inda zani ina nan kwance bisa ƴar katifa ta."

Haɗa fuskar ta Falmata tayi cike da ɓacin rai tace.

" Haka zaki min Maji saboda na kawo miki damuwa ta ko? Ba komai na gode."

Falmata ta ƙarasa maganar tana tashi tare da ƙoƙarin ficewa, Maji saurin riƙo hanunta tayi tare da cewa.

" Karki tafi cikin fushi ƙawata, bawai naƙi zuwa miki bane, a'a akwai abinda nake dubawa ne, idan har naje Iyayenki zasu ga kamar nice nake zugaki ki bijire musu, zasu ga baƙi na, ni kuma bazan so hakan ba, ni da idan ta nine ma, Falmata da bazaki gujewa umarnin Iyayenki ba zanfi so ki musu biyayya, babu yanda na iya da zuciyarki ne, bazan iya sanja miki ita ba, kiyi hkr ƙawata."

Juyowa Falmata tayi Hawaye na zubo mata daga idanunta tace.

" Ni kaina banso kaucewa Umarnin su ba, Maji babu yanda na iya da zuciyata ne, domin kuwa itace bazata iya jure ranshin DOCTOR ba, ban san wani irin Soyayya nake masa ba, sam zuciyata bata iya control ɗin kanta, ba zuciyata tana bugawa ne tare da nasa, da zan iya tanƙwara zuciyata, to wallahi da zanbi umarnin iyayena, sai dai bazan iya juran hakan ba, ku kyautatawa auren mu zato domin na Tabbata Hassan bazai bani kunya ba, Maji na fahimce ki, Tabbas ke ƙawace ta gari wanda dukkan wani mutum zaiso ya sameki a matsayin aminiya, karki damu ƙawata, ke dai ki cigaba da min addu'a Allah ya cika min buri na."

Cike da tausayin ƙawar tata maji ta amsa da ameen, tashi Maji tayi ta raka Falmata har ƙofar gida kafin suka rabu Maji ta koma cikin gidan ita kuma Falmata ta shige nasu gidan a ƙofar gidan ta samu DOCTOR yana zaune shida Saif suna danna waya suna hira tamkar bashi da wata damuwa, Falmata gefen sa ta tsaya tare da cewa.

" DOCTOR na"

Ɗago kansa yayi a hankali tare da sakin murmushi yace.

" My dear yaushe kika ƙaraso bangan ki ba, sai kuma yayi shuru tare da zuba mata idanu, yace kuka kikayi.?"

Murmushin ƙarfin Hali Falmata tayi tace.

" A'a ba kuka nayi ba, me ka gani.?"

" Haba Dear ni fa ba yaro bane da zaki ɓoye min damuwar ki, kinyi kuka saboda su Bulama suna neman rabamu ko.?"

" DOCTOR hankalina a tashe yake ina tsoron su rabamu, idan suka rabani da kai , da rayuwata suka rabani, baka san rayuwarka rayuwata bane, mtsss, wai meyasa kayi kamar maganar bata dameka."?

Ta ƙarasa Maganar cikin rau-rau da muryar alamun zata sake wani kukan, DOCTOR murmushi yayi tare da cewa.

" To ya kike so nayi so kike na ɗaga hankali na, kinga nifa bazan iya jure walaƙanci ba, taya dan kawai nace ina sonki sai su tsaya suna neman aibata Ni, mutuwa zanyi idan ban Aure ki ba, yau ko mutuwa ɗayan mu yayi dole zamu hkr, ni fa na yanke hukunci, idan zasu bani ke su bani idan bazasu bani ba shikenan amma wallahi bazan ƙara zuwa na tunkaresu da wannan maganar ba, kuma ko Bulama ya ƙara kiran MEETING wallahi bazan jeba, kema kiyi hkr ki daina sawa kanki damuwa, idan har Allah ya ƙaddara akwai Aure a tsakanin mu, dasu so da karsu so, dole sai mun kasance ma'aurata dan haka kije ki cigaba da addu'a, ki shige cikin gida."

Saif cike da tausayi yake sauraron su, musamman Falmata yafi jin tausayin ta, Falmata zata sake magana DOCTOR ya kaɗan mata kai alamun karta kuma cewa komai, shigewa Falmata tayi cike da sanyin jiki, SAIF kansa ya dago cike da damuwa yace.

" Hassan, bai kamata ka mata wannan maganar ba, hakan yana nuna tamkar baka damu da ita ba, Hassan idan har kana sonta da gaskiya kamata yayi, ka dinga rarrashinta, ba wai ka dinga karya mata zuciya ba, koni nan yanzu banji daɗin Maganar daka faɗa mata ba Soyayya kulawa take so."

Ɗago kansa DOCTOR yayi yace.

" Bawai karya mata zuciya nake ba Saif, wallahi ina sonta, sai dai bana jin zan iya jure cin mutunci saboda kawai nace ina sonta shikenan sai ya bawa iyayena damar wulaƙanta Ni, wallahi bazan juri walaƙanci ba, na gwammace na hkr da ita idan yaso suje su bawa duk wanda suke so, tunda since ni ban cancanta ba."

" Hassan kenan anya kuwa kana sonta da gaske, da kana mata Soyayyar gaskiya, zaka iya jure duk wani wulaƙancin da za'a maka a kanta, kaga abinda iyayenka kenan suke gudu wannan zafin Zuciyar taka, domin kuwa tana rinjayar tunaninka, dan Allah ka rage wannan Zuciyar ka daure ka taka duk wani ƙayar dake kan hanyar Auren ka da Falmata koda kuwa ƙafar ka zata kasa taka ƙasa Saboda wahala, idan kayi wannan shine zai nunawa duniya zaka iya riƙeta, ya kamata ka gyara Soyayyar ka ka daina sako zafin zuciya cikin ta, idan har kana nunawa Soyayya zafin rai, to Tabbas wata rana sai ka samu Abokin takarar da zai kwace Soyayyar ka a wajen ta, muddun kuwa ta saurari wani namiji mai bawa Soyayya kulawa, zata gane cewa kai ba sonta kake, ita macen da ake so, ana riritata ne tamkar ƙwai ya kamata ka san wannan."

Ajiyar zuciya DOCTOR ya sauƙe tare da cewa.

" GASKIYA ne, SAIF zanyi ƙoƙari naga nabi shawarar ka amma gaskiya iyayena basa kyauta min, saboda bai kamata su nuna min ƙiyayya akan wannan auren ba, iyayena ne fa su, suma sun hanani auren yarsu to waye zai bani Aure.?"

" Ba ƙiyayya suke nuna maka ba Hassan, iyayenka zuciyarka suke tsoro suna gudun abinda zaije ya dawo, ya kamata ka fuskanci iyayenka, sannan kamata yayi duk sanda kuka ƙara wani zama dan Allah ka nuna musu zaka iya riƙe Falmata da kyau, ka jajurce har sai ka samu sun amince maka da Auren Falmata."

" Shikenan SAIF na gode insha Allah zan gwada na gani ko zan iya, ya Maganar tafiyar ne, next Monday ko."

" Eh next week insha Allah, jiya munyi waya da HABEEB yake sanar dani cewa jirgin 9:00am zamu bi so Abokina ya kamata ka samu ka saita hanyar Soyayyar ka, domin lokacin ka kaɗan ya rage maka."

" Mtsss!!! Hmmm!! Lokaci na ƙaɗan kam badamuwa zamu zubawa sarautar Allah Ido insha Allah komai zai tafi dai-dai."

" Hassan ya kamata kafin mubar ƙasar nan muje gidan su HABEEB mu gaishe da mahaifiyarsa, sannan mu mata godiya saboda wadannan mutanen, sun mana alkairi, kasan fa duk wanda yayi karatu a India da America da kuma Cairo zai samu aiki a kowace ƙasa a cikin duniyar nan suna best Colipication."

" Mtsss!!! Bazan jeba, kai kaje tunda kayi niya amma ni dai babu inda zani, bazan taka ƙafata a wannan gidan ba, bana buƙatar ƙara ganin fuskar sa a rayuwata."

" Hmmm!!! Abinda yake cutar ka kenan zuciyarka, tunda kace bazaka ba, nasan ban isa tilastaka dole ba, amma dai nasan duk wani matsayin da zaka taka a duniya da bazar HABEEB ne, hakan kuma bazai taɓa gogewa ba."

" Hmmm!! Saif gori kenan zaka min, Okay naji meyasa ya ƙi karɓar Vaccancy sa, sanda na dawo masa da abinsa, kaga Malam ya isa ka daina kawo min Maganar HABEEB muddun kana son mu zauna lafiya."

Murmushi Saif yayi tare da tashi yana cewa.

" Saboda ya bakane dan Allah shiyasa yaƙi karɓa, kwantar da hankalin ka, ni tafiya ma zanyi yanzu."

Yana gama faɗin haka ya juya ya hau keken sa, ya bar wajen tsuka DOCTOR yaja ya cigaba da danna wayarsa, ita kuwa Falmata sashin Umma ta shiga cike da sanyin jiki, Aunty JALILA Umma Fanna har AJIRAM suna zaune a falon Umma sai hira suke, zama tayi gefen Umma tayi shuru, AUNTY Jalala duban ta tayi tace.

" Falmata lafiya kuwa kika shigo cikin sanyin jiki."

" Babu komai Aunty.?"

Murmushi Umma tayi domin kuwa duk ta fahimci halin da Falmata take ciki, tashi Umma tayi tare da kama hanun Falmata tace.

" Tashi mu shiga ciki."

Babu musu Falmata ta miƙe tabi Umma a bakin gado suka zauna Umma ta dubeta tare da cewa.

" Karki ɓoye min damuwar ki Falmata, sanar dani meke damunki, nima mahaifiyarki ce, mai share miki hawaye, dan haka sanar dani matsalarki kinji ƴata."

Falmata kanta ta sunkuyar tare da yin shuru taƙi sanar da Umma komai murmushi Umma tayi tace.

" Kina cikin damuwa ne saboda munce bazaki Auri, Hassan ba ko.?"

Da sauri Falmata ta ɗago kanta ta kalli Umma, sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa, Umma ce ta cigaba da cewa.

" Falmata nine na haifi Hassan a ciki na, nafi ki sanin halinsa mutum ne shi mai zuciyar gaske, yana da ɗaukar zafi akan abu kaɗan, idan har ya zuciya yakan yanke hukunci koda kuwa zaiyi nadama daga baya idan kuma yayi zuciyar baya jin maganar kowa a wannan lokacin koda kuwa nice UWAR dana haifesa bazaiji nawa ba, tsoron zuciyarsa yasa muke tsoron haɗaki Aure dashi bawai dan bama sonku bane."

Falmata kanta na ƙasa tace.

" Umma ni ina son Doctor a haka zan iya juran zama dasu Umma, Please Umma dan Allah kisa baki Su barmu dan Allah Umma kar a rabamu."

Shuru Umma tayi cike da tausayin Falmata domin kuwa ta fahimci Soyayyar da take yiwa Hassan yafi

Please Login or Register in order to submit comment