Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda shi yake mata, Tabbas akwai matsala hmmm Umma ta sauƙe ajiyar zuciya tace.

" Shikenan naji zan duba lamarin, ki kwantar da hankalin ki, ki saki ranki kinji, insha Allah zanyi iya ƙoƙari na, domin ki samu cikar burinki."

Ɗan murmushi Falmata tayi tare da rufe fuskarta alamun kunya dariya Umma tayi ta tashi ta fice ta barta a Bedroom ɗin.


Washe gari kuwa da misalin 4 na yamma, Bulama ya ƙara haɗa family MEETING wannan karon harda mata su Umma da Aunty YANA, Baba shine ya fara buɗe taron da addu'a sannan Bulama ya fara magana.

" Nasan yau dukkan ku zakuyi mamaki da hukuncin dana yanke, to ban yanke wannan hukuncin ba sai da na zauna nayi dogon nazari, naga mai zai faru gaba, kafin na yanke hukunci, ba wani hukunci na yanke ba, na yanke hukuncin na yarjewa Hassan da Falmata suyi Aure a tsakanin su, kuma bana son kowa yace komai kawai ku musu addu'a da fatan alkairi, sannan wannan Auren za'ayi shine Jibi ranar juma'a kafin ya tafi India, zata zauna ta jirasa da auran ta harya dawo, dan haka gobe ayi sanarwa a masallaci idan an idar da Sallah cewa jibi akwai daurin Aure, ban Yadda ko wacce mace ta min taron biki a cikin gidan nan ba."

Shuru kowa yayi dake wajen, Baba sam baiso hukuncin da BULAMA ya yanke ba, Falmata kuwa wani ajiyan zuciya ta sauƙe cike da jin daɗi, haka wajen Hassan ma, shima sosai yaji daɗin wannan hukuncin da BULAMA ya yanke, itama dai Aunty YANA bata so wannan hukunci ba, Baba Bukkar shima yaji daɗi sosai, haka taron ya watse masu farin ciki nayi masu jin haushi da fargaba sunayi...............







Allah ya haɗa mu a next page😝😝😝😝 yasin na gaji da yawa.





Ƴar uwa biya kudin ki, cikin kwanciyar hankali yafi miki sauƙi fiye da ki karanta abinda ba gumin ki ba neme ni ta nan, domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.







*Alƙalamin RASHEEDAT USMAN ✍🏻*





*(UMMU NASMAH Ce)*
[9/26, 11:49 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 61 to 62*





________✍🏻 Falmata sosai take murmushi tare da godewa Ubangiji daya cika mata burin ta, ɗakin aunty Yana ta shige, wayar ta ta ɗauka a bedside drower, cike da farin ciki ta kira Maji bayan maji ta ɗaga ne Falmata cikin dariya tace.

" Ƙawata Albishir, kinsan su Bulama sun amince da Aure na da DOCTOR wallahi yau ina cikin farin ciki marar misaltuwa, ƙawata ranar Juma'a za'a ɗaura mana aura."

Zaro ido Maji tayi, tace.

" Kai ƙawata da wuri haka, baza'a bari sai ya dawo daga karatun ba, musha biki na kece raini."

" Hmm ƙawata Bulama yace babu wani biki da za'ayi Aure kawai za'a ɗaura, shi kuma ya tafi India Monday ni hakan ma fa alhamdullahi."

Dariya Maji tayi cikin zolaya tace.

" Saboda kin samu cikar burin ki, ko, ƙawata na tayaki murna Allah ya sanya alkairi ƙawata Allah yasa gidan zamanki kenan har abada, insha Allah da yamma zanzo mu taka rawa ƙawata kin samu cikar burinki."

Dariya Falmata tayi tace.

" Allah ya kaimu ƙawata ina jiranki."

Da ameen Maji ta amsa sannan suka kashe wayar Tana kashewa Aunty Yana tana shigowa cikin ɓacin rai fuskarta a haɗe, ta zauna kan kujera tare da wurgawa Falmata harara, kawar da kanta Falmata tayi daga kallon Aunty Yana domin kuwa ta fuskanci inda hararar Aunty Yana ya dosa, ficewa Falmata zatayi daga cikin ɗakin Aunty Yana ta dakatar da ita ta hanyar cewa.

" Dawo ki zauna munafuka."

Dawowa Falmata tayi ta zauna kujerar gefe da Aunty Yana tana tura bakin ta, Aunty Yana cewa tayi.

" Hankalin ki, ya kwanta yanzu, kin samu abinda kike so, zan miki addu'a tare da fatan alkairi Allah yasa gidan zamanki ne, sai dai tunda kin nacewa auren Hassan, to kuma dole ki koyawa zuciyarki haƙuri da kuma juriya, ki ji ƙi gani ki gani ki ƙi ji, ki dinga danne fushin ki, a duk sanda kika ga ya fusata, wannan shine kaɗai zaisa ki iya Zama da Hassan, ki tashi kije Allah miki albarka."

Ajiyar zuciya Falmata ta sauƙe domin kuwa tayi tunanin Aunty Yana, zaginta za tayi, cikin sanyin Murya tace.

" Na gode Mama insha Allah zan kasance kamar yadda kika fahimtar dani."

Ta ƙarisa maganar tana tashi tare da ficewa yau zuciyarta a wanke take jinsa duk wani damuwarta ta ya goge.

Shi kuwa DOCTOR fitarsa daga Family meeting ɗin, bedroom ɗin Umma ya shige zama yayi yana sakin murmushi Aunty Yana cike da zolaya tace masa.

" Ango kasha ƙamshi, kaga kuwa yanda ka fara haskawa, kana walwalin, angonci."

Dariya DOCTOR ya saki yana kallon Aunty Yana kafin yace.

" Kai Aunty kema dai ba dai zolaya ba, yaushe na zamo angon, bafa a ɗaura auren ba."

" Ba'a ɗaura ba, amma dai ankusa ko, kaga Malam Hassan daga yau fa sunan ka ya koma ango, kuma dole ka amsa."

Kafin DOCTOR ya bata amsa Umma tace.

" Ya isa haka, ka saurareni da kyau Hassan domin kuwa kashedi zan maka."

Hassan fuskantar Umma yayi, tare da nutsuwa yana sauraron ta, haka Aunty Jalila ma ta maida nata hankalin tana duban Umma.

" Kaga dai yanda yarinyar nan tayi ruwa tayi tsaki, bata hutawa ranta ba, har sai da Bulama ya amince da wannan auren, to wallahi ka riƙe yarinyar nan da amana da gaskiya, idan har ka ci aminarta wallahi Allah bazai barka ba, domin kuwa tana sonka da gaskiya, duk da kaima kana sonta, soyayyar da take maka yafi wanda kai kake mata, dan haka ban yadda ka ɓata mata rai ba, idan ta maka laifi ka hukunta ta, cikin ruwan sanyi bada wannan zafin ran naka ba, wallahi ka ɓata mata rai kamar ni ka ɓatawa rai ne, kuma naji labari kai mai sai na ɓata maka rai, magana ta biyu, ban yadda ka rabu da Falmata duk girman laifin data maka, sai dai kuma idan ta kaucewa shari'a ne shine ya zamo dole ka rabu da ita, amma idan bashi ba, ko bayan raina ka rabu da ita, Ban yafe maka ba, kuma sai mun tsaya da kai a gaban Ubangiji, ka riƙe Falmata da kyau domin ka samu matar rufin asiri, nasan Falmata bazata taɓa ɓata maka ba, kaji dai abinda nace ko."?

Shuru doctor yayi tare da ɗan cije laɓɓensa na sama yace.

" Umma ina mamaki idan kuna cewa wai Falmata tafi sona fiye da yanda ni nake sonta, wallahi Umma son da nake yiwa Falmata, ko kotansa bata min, kawai ita tana nuna nata soyayyar a fili ne shiyasa kuka fi ganin nata, kuma insha Allah Umma babu abinda zai rabani da Falmata sai dai mutuwa, ki daina shayi a kaina insha Allah duk sai na baku mamaki."

" Zanso hakan Hassan, Allah ya muku albarka ya sanyawa Rayuwar auren ku albarka ya kuma azurta ku da zuri'a ta gari waɗanda zata taimaki addinin Musulunci."

Da ameen duka suka amsa har Aunty Jalila, kafin suka koma firarsu ta duniya.

Da daddare Doctor ya kira Falmata a waya yace tazo ta samesa a soron gidan, bai kuma juma da kiranta ba sai gata tazo ta samesa, yana zaune bakin ƙofar ɗakinsa, kujera ta ɗauko ta zauna a gefe, murmushi doctor ya saki tare da cewa.

" Barka da isowa gimbiyar mata tauraruwar Hassan."

Murmushi ta sa cikin sanyin Murya tace.

" Har kasa naji kaina ya fara hawa gajimare, kaine tauraron rayuwata kuma hasken idanuna jagoran rayuwata, hankali na yanzu ya kwanta saboda nasan na mallaki doctor na."

Murmushi ya saki tare da cewa.

" Kamar yadda na mallaki Gimbiyata Falmata alkebbar mata, MATATA kinsan dalilin kuwa da yasa na kiraki yanzu.?"

" A'a farin ciki na, ban sani ba, amma dai nasan yanzu zan sani daga bakin Doctor na."

Cike da zolaya kuwa yace mata.

" Ya kamata kuma ace kinsani domin kuwa zuciyar Hassan taki ce."

" Zuciyarka tawa ce, sai dai ba lallai nasan ainihin karatun zuciyarba, sanar dani Farin ciki na."

" Babu abinda yafi daɗi a duniya irin ka samu mace tagari wacce zata soka koda ba ka da komai, ina alfahari dake saboda soyayyar ki ta gaskiya ne a gareni, bani da ko sisi amma a haka kika dage kina sona, hakan ya nuna min zaki iya rayuwa dani, ko a wani hali na tsinci kaina a ciki, sai dai kuma Falmata shin zaki iya haƙurin zama dani kuwa, Falmata ni kaina nasan ina da zafin rai, duk da nasan zanyi iya bakin ƙoƙari na wajen ganin na kawar da zuciyata a kan ki, bazan yadda fushina ya taɓa tasiri a kanki ba, sannan zaki iya jirana har nayi shekara bakwai a wata ƙasa na barki anan.?"

Murmushi Falmata ta saki sannan tace.

" Zan zauna da kai aduk yanda kake, Doctor zan zauna na jiraka koda kuwa shekara dubu zakayi, muddun zaka dawo gareni, to zanyi dakon jiranka har Allah ya dawo da kai lafiya."

" Tabbas Falmata, kin cika masoyiya ta gari kin samin nutsuwa a jikina, Wanda bazan iya misalta miki shiba, zan ƙara jaddada miki cewa, ina ƙaunar ki, bazan kuma daina sonki ba, har ƙarshen rayuwata."

" Na gode da soyayyar ka gareni, insha Allah zan kasance mace ta gari mai biyayya a gare ka."

Dare yayi ki koma cikin gida gobe zamu yi magana, tashi Falmata tayi tare da amsawa da Allah ya kaimu, yana Binta da kallo harta shige, murmushi ya saki shima cikin farin ciki.






***************

Juya spoon ɗin kawai yake a cikin abincin ya kasa kai koda loma ɗaya ne bakin sa, sosai yake cikin damuwa ya kasa jure rashinta a cikin zuciyarsa, bacci ma yanzu gagararsa yake yi, tsuka yaja tare da cije bakinsa, duk abinda yake momy tana kallon sa cike da tausayin ɗanta.

" *HABEEB* " Ta kira sunan sa a hankali.

Ɗago kansa yayi ya zubawa Umma idanu.

" HABEEB meyasa kwana biyun nan baka cin abinci, tun ɗazu kasa abinci a gabanka amma ko spoon ɗaya baka saka cikin bakin ka ba, sannan na lura kana yawan shiga cikin damuwa, HABEEB kana son sawa kanka ciwo saboda macen da ta maka nisa, HABEEB ka cire damuwa cikin ranka, ka dinga yawan ambaton sunan Ubangijin ka, da kuma zikiri, insha ALLAH zai yaye maka soyayyar ta, kaci abincin ka."

" Momy bana jin abincin ne a cikin raina, haɗa min tea kawai nasha, sannan momy zan koma CAIRO ranar Monday may be nafi samun nutsuwa a can."

Kaɗa kanta momy tayi tana miƙo musa tea ɗin tare da cewa.

" Okay ba damuwa Allah ya kaimu Monday, sai ka sanar da Daddyn naka insha Allah zaka samu nutsuwa cikin zuciyarka, Allah zai baka mace ta gari wacce ma tafi ita wanda kake son, sannan munyi magana da kawun ka Musa, yace insha Allah gobe zaije yaga Jalila, idan sun daidaita, shikenan."

" Okay Momy ba damuwa Allah ya daidaita tsakanin su, bari na tafi wa Daddy aikansa, GIWA BARRECK yace yana jirana a office."

Ya ƙarasa maganar yana ajiye cup ɗin tea ɗin tare da tashi, Momy Allah ya tsare ta masa, sannan ya ɗauki kay ɗinsa ya fice, Momy da kallo ta bisa tana jin tausayin sa, addu'a take masa a cikin zuciyarta, Allah ya cire masa wannan soyayyar a cikin zuciyarsa...............




Kuyi hkr ban samu nayi editing ba saboda bani da chaji a wayana.







Ki biya kudin ki, cikin kwanciyar hankali yafi miki sauƙi fiye da ki karanta abinda ba guminki ba, ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗi ki 08147537180.







*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻








*(UMMU NASMAH CE)*
[9/27, 7:55 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 65 to 66*







Sorry dan page ɗin jiya nayi mistake wajen saka number, 62 to 63 ya kamata na saka sai kuma nasa 61 to 62 kumin afuwa🤲🏻.




___________✍🏻 HABEEB motar sa ya shiga tare da dafe kansa jikin sitiyarin Motar sai kuma ga hawaye shar daga idanunsa suna zubowa, runtse idanunsa yayi yana jin ƙirjinsa yana masa suka, a kullum yakan jefawa kansa tambayar meyasa ya kasa ɓanɓare Soyayyar ta daga cikin ransa duk da ita bata sonsa tama manta dashi a cikin RAYUWARTA amma shi har yanzu tana maƙale a tasa Rayuwar, meke shirin faruwa da rayuwarsa wacce irin Soyayya ce wannan " Anya kuwa zan iya Auren wata mace kuwa? bana jin zan iya, saboda zuciyata na Falmata ne kaɗai, babu ta yadda zan iya bawa wata gurbi a cikin sa, ya kenan rayuwata zata kasance, innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, Allah kana kallon matsalar da nake ciki Allah ka tallafi zuciyata ka kawo min agaji cikin Rayuwata." Ya yiwa kansa tambaya tare da amsa kayan sa , hanunsa ya saka tare da goge hawayen fuskar sa, addu'a yayi tare da jan motar mai gadi ya wangale masa ƙofa, titi ya harba zuciyarsa cike da tunanin Falmata, yayi nisa da tafi yaji ringin ɗin wayarsa, hanunsa yasa ya amsa kiran tare da manna earpice a kunnen sa , a hankali yace.

" SHETIMA, tun ɗazu nake da niyar kiran ka sai kuma ka rigani, ya Cairo."

Ɗan murmushi SHETIMA ya saki daga can kafin yace.

" Muna lafiya amma dai school ɗin bata min daɗi tunda babu kai a cikin ta, wai dan Allah malam yashe zaka dawo ne, an fara nisa da lecture's fa."

" SHETIMA ina hanya insha Allah Monday zan shigo, jiya munyi waya da Malam Murtala yace min wai har Assignment ya bayar, amma dai muna ɗan lectures dashi ta online, so abubuwan zasu zo min da sauƙi, kunyi Magana da AA ne akan Business ɗin nan, saboda ina son zan bada contract a fara ginin Companyn nan, idan zai zauna ya jagoranci Companyn kafin mu gama karatu mu dawo, to idan kuma bazai iya ba, so zan nemi wani kafin na taho, sannan ka sanar dashi cewa, Business ɗin RIƊI zamuyi, idan zai iya fine."

" Eh munyi Magana dashi ya amince daman kasan ƙarƙashin wani Company yake so kawai ka bada contact ɗin a fara ginin Companyn."

" Okay ba damuwa zamuyi magana da Daddy sannan kuma, shima A'A ɗin zan sake magana dashi, zan nemeka zuwa dare yanzu ina dreving ne."

" Okay Allah shi kaimu daren."

Katse wayar HABEEB yayi, sannan ya cigaba da dreving ɗinsa ya kusa isa Giwa BARECK yaji shigowar text cikin wayarsa, hanu yasa ya ɗago wayar HASSAN ya gani rubuce jikin screen ɗin wayar cike da mamaki yake duban wayar " Hassan kuma?" Ya furta a zuciyar sa, buɗe text ɗin yaga an rubuta.

" _*Ina gayyatar ka ɗaurin Aure na da Falmata gobe idan Allah 1:30 a masallacin juma'a dake unguwar mu, sannan ina maka godiya da tayani bayyana Soyayyata da kayi, harta kaimu da Aure cikin gaggawa, muah 😘*_ "

HABEEB wani irin duhu ne yaji ya rufe masa ido da ƙarfi ƙirjinsa ya buga, wani suka zuciyarsa take masa, kaɗan ya hana sitiyarin motar sa ta kufce masa yayi saurin riƙe sa, runtse idanunsa yayi " shikenan na rasa ta har abada" ya furta tare ƙoƙarin maida hawayen da yake ƙoƙarin cika masa ido, tuno Maganar Momy ya sashi fara ambaton Ubangiji, a hankali kuma sai yaji nutsuwa yana sauƙa a zuciyarsa, harya iso First get ɗin BARECK ɗin.







**************

" Masha Allah ƙawata kice zaki rigani shigewa ciki, Waya ga amarya."

Dariya Falmata ta saki cikin dariyar tace.

" Badai ZULUM ya kasa ba ai kinga kuwa dole mu rigaki ta inda zaki tabbatar da cewa nawa mijin yafi naki ƘWARI."

Maji dariya ta saki sosai tace.

" Eyye!!!! To lallai dole HABIBINA ya dage tunda naga, har an fara mana gori."

Daga bayan ta taji muryar DOCTOR yana cewa.

" Babu wani gori gaskiya ne kawai My dear ta gaya miki ki, Shi dai wannan Sojan naki, kice masa ba a iya filin daga kawai ake nuna jarunta ba, har a fagen soyayya ma, dan haka ya fito ya nuna mana jarumtar sa, kafin ya samu mai tatile masa ƙafa."

Dariya Maji ta saka tare da cewa.

" Ku dai faɗi komai likitocin kune yanzu, amma dai karku manta akwai ranar Ramako, kun dai san bana barin bashi."

Murmushi Falmata ta saki tace.

" Ai kuwa sai dai ki rame ba dai ki rama ba, DOCTOR na, barni da ita na isheta riga da wando harda zanin ɗaurawa."

" Haba dai yarinya ai koshi, wannan mijin naki bai isheni ba, bare kuma ke, naga fa kanku ya fara rawa saboda kawai gobe wai za'a ɗaura muku Aure."

Dariya DOCTOR yayi yana ficewa yace.

" Munji, kema ki yi zuciya taki naki kan yayi rawar mana."

Ya ƙarasa maganar yana shigewa Maji murmushi tayi tana duban Falmata tace.

" Ƙawata, wai a ina zaki zauna bayan an ɗaura Auren ne."?

" Eh to shi dai BULAMA yace, zan zauna na jirasa a nan gidan, a ɗakin kwanana, har Allah ya dawo dashi amma jiya naji Baba Bukkar yace zai basa gidan Alh Adamu na daya saya na nan bayan gidan mu, mu zauna har sanda Allah zai basa yayi nasa muhallin, amma dai yanzu a gida zan zauna sai ya dawo tukunna mu koma can."

Ajiyar zuciya Maji ta sauƙe tare da cewa.

" Hmmm!!!! Lallai Falmata anyiwa Hassan Auren gata, shi kam ko kaɗan bai san zafin neman Aure ba, to Allah ya sanya alkairi, bari naje Mama na jirana zan karɓa mata aiki, zata fita unguwa, goben na dawo da safe."

" To shikenan Allah ya kaimu muje na rakaki, har soron gidan Falmata ta raka Maji sannan ta dawo, Bedroom ɗin Aunty YANA ta shiga ta gaishe da AUNTY LADI ƙanwar Aunty da tazo ɗazu sannan ta fita, AUNTY LADI duban AUNTY YANA tayi tace.

" YANA kinsan labarin Auren nan yazo mana a bazata, Aure haka ba zato sannan ace baza muyi biki ba, wannan fa shine Aure na farko da kika fara ɗagawa shikenan sai ayi Aure lami babu wani biki, gaskiya banji daɗin hakan ba."

" Hmmm!!! Ladi aini kaina banso hakan, babu yanda na iya ne kawai, saboda babu wanda ya isa yaja da hukuncin Bulama."

" To Allah ya kyauta, yanzu kenan bazaki mata gyara ba, haka zaki bar ta, ta tafi ɗakin mijin tamkar wacce bata da gata."?

Murmushi Aunty YANA ta saki tace

" Wai wa yace miki ɗakin miji zata ne, Auren nan fa kawai za'a ɗaura sane, bawai zama zatayi da mijin ba, idan an ɗaura juma'a shi kuma Litinin zai tafi India, ba Kuma zai dawo ba, har sai ya gama karatun sa, 7yrs anan fa zata zauna to gyaran me zan mata mutumin da zai shekara 7 ba mijin, na mata idan ya kusa dawowa."

" Au wai kina nufin ba tare zai tafi da ita aini nayi zaton tare zasu tafi.?"

" A'a ba tare zasu tafi ba, anan zai barta."

" To amma ai Aunty YANA kinsan dai yaran zamani ne su ko? To wallahi karkisha mamakin kafin ya tafi wani abu ya wakana a tsakanin su, cikin kwana biyun da kike rainawa, tun yaushe zai ɗauke ta da niyar sun fita unguwa, yaje ya maidata cikakkiyar mace kinan wangale da baki."

Murmushi Aunty YANA ta saki tare da cewa.

" Haba dai Ladi ni ɗin sai na bari hakan ya faru, ai bari kiji na faɗa, Falmata bazata fita koda suron cikin gidan nan bane har sai Hassan yabar ƙasar nan, ke na taƙaita miki zance, ɗakin nan zata dawo da kwana tunda dama shi Bukkar ba'a nan yake kwana ba."

"Sai dai kuma hakan ba"

Sun juma suna hara da Aunty Ladi har akayi kiran magarib, sannan suka tashi sallah.


Da daddare Saif ya shigo cikin gidan wajen DOCTOR a ɗakin sa ya samesa, kusa dashi Saif ya zauna tare da cewa.

" Congratulation Abokina, kawai sai kake sanar dani komai ya daidaita, gaskiya Abokina na tayaka murna Allah ya samu a dashin ka, dan kayi dacen mace ta gari, kace gobe ey warhaka mun juma da angoncewa, da ita zamu shige India ne.''

" Abokina waye zai biya mata kuɗin jirgin kasan gomnati sit ɗina kawai ta bayar, anan zan barta harsai na dawo."

Zaro ido Saif yayi yace.

" What!!!! 7years fa zakayi kana tunanin zata iya haƙurin jiranka har wannan shekarun, dutse ne ita aka faɗa maka bata da sha'awa."

" Ko tana da sha'awa, ya zan mata to, kasan dai bazan bar karatu na, dan kawai na zauna da ita ba, dole naje nayi karatu domin kuwa shine rufin asirin mu daga ni har ita, kama daina wannan maganar dole zata hkr.''

" Hmmm, to hakane amma dai lamarin akwai Abin dubawa, kasan fa yawancin mata sunfi namiji sha'awa, ni tausayin ta kawai nake ji, domin nasan zata cutu."

" Babu wani cutuwar da zatayi Malam shiyasa ma bazanyi kuskuren saninta mace ba, yanzu har sai na dawo saboda karna koya mata abinda bazata jura ba."

" Good Abokina, idan kayi hakan shine daidai abin zaizo da sauƙi, nayi zaton a hanu kake ne ai bazaka iya hkr ba, har sai ka ɗanɗani zumar kafin mu tafi shiyasa nayi wannan maganar."

Kafi kowa sanin zan iya tunda ina iya danne jarabata bana kaiwa matan banza, an faɗa maka ni irinka ne, SAIF kaji tsoron Allah ka daina lalata yaran mutane, wai ana cewa abokin ɗan iska ɗan iska ne ko, to wallahi ni ba ɗan iska bane.''

Dariya ce ta ƙwacewa Saif Sanda yayi mai isarsa Kafin yace.

" Naji ni ɗan iska ne, amma dai kasan kwana biyun nan na gyara halina ko, Allah da gaske na tuba, amma dai taba kam bazan iya daina shanta ba."

" Hmmm!!! Akwai taba babbar illa ce ga rayuwarka, zaifi maka sauƙi duka ka gyara."

Dariya Saif yayi ba tare da yace masa komai ba, sai wani zancen ya ɗauko masa daban.








Kuyi hkr banyi editing ba yau.








Ki biya kuɗin ki ta wannan numbern 08147537180 zan faɗa miki yadda zaki biya, karki karanta min LITTAFI idan kinsan baki biya.







*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN ✍🏻*






*(UMMU NASMAH CE)*
[9/28, 11:07 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 67 to 68*





__________✍🏻 Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, yau take juma'a ranar ɗaurin auren Falmata da Hassan, Hassan da babbar rigarsa ya fito, bayansa SAIF ne, shima yasha babbar riga, su Baba kuwa tuni sun juma a masallacin, DOCTOR part ɗin Umma suka shiga, tana zaune cikin yaranta AJIRAM JALILA Fanna, sai UMMAHANI ADDAR Umma wacce suke uwa ɗaya, suna ta hira, kusa da Umma ya sunkuya, idanunsa ya ɗago tare da zubasu ga Umma, cikin shauƙi da sanyin murya yace.

" Umma yau Ranar farin ciki ne a gareni, ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba, ki samin albarka Umma, domin na fita cikin Nasara ina ji a jikina, nida Falmata mutuwa ce kawai zata raba mu."

Murmushi Umma ta saki cike da ƙaunar ɗan nata, domin kuwa a duk cikin ƴaƴan ta, tafi jinsa a cikin ranta ko dan shi kaɗai take dashi namiji ne, cewa tayi.

" Kullum da Albarka ta kake tafe Hassan, Ubangiji ya albarkaci Rayuwar ka, ya tsare maka gaban ka da bayan ka, mahassada da kuma maƙiya ya kau da idanunsu a kanka, Allah yasa wannan Auren idan an ɗaurasa sai mutuwa ne zai rabaku, ka tashi kaje ɗana lokaci na ƙaratowa Allah ya albarkaci Auren nan ya haskawa Rayuwar ku."

Gabaki ɗaya falon da ameen suka amsa cike da sha'awa Saif yake binsu da kallo rayuwar Umma da ƴaƴan ta yana basa sha'awa sosai, shi kam ya rasa wannan gatan, tun yana ɗan shekara Biyu ya rasa iyayensa duka biyu daga uwa har uba, hawayen dake ƙoƙarin sauƙo masa yayi saurin saka hanu ya tare su, Umma duban ta ta kai garesa tare da saka hanu a kansa tace

" SAIFUDDEEN Allah ya maka Albarka, kaima ya fito maka da taka matar Auren ta gari, Allah ya jiƙan iyayenka."

Da ameen suka amsa har DOCTOR, UMMAHANI cikin murmushi itama ta masa addu'a, Aunty JALILA kuwa tashi tayi

Please Login or Register in order to submit comment