Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

" *FALMATA*"

Idanunta da suka sauya kala zuwa red ta ɗago ta dubesa dasu hawaye na ƙara gudu mata.

" Ke da waye, me aka miki.?"

Ya jefa mata tambayar cikin sarƙewar murya tace.

" DOCTOR Maji mijinta ya rasu, tana can cikin tashin hankali bansan wani hali take ciki ba, ji nake a zuciyata ya zanyi idan akace min ka mutu, ina kwatanta Zafin da zanji idan har na rasaka, na Tabbata itama maji irin wannan Zafin take ji tana sonshi kamar yanda nake sonka, gashi yanzu ya tafi ya barta, sun kashe mata shi, shin sai yaushe ne al'ummar Borno zasu daina tsoro da zullumin rayukansu, yaushe sojojin ƙasar mu zasu sami kwanciyar hankali, amsar ɗaya ce, bamu san lokacin ba, ina tausayin aminiyata DOCTOR, na Tabbata yau tana cikin tashin hankalin da bazan iya misilta maka shiba, ka barni naje gareta."

Ajiyar zuciya DOCTOR ya sauƙe cikin sanyin jiki da tausayin Maji, miƙewa yayi ya zauna tare da jawo Falmata jikinsa ya mannata da ƙirjinsa wani laushi yaji fatar ta ta masa tare da wani ƙamshi mai daɗin shaƙa lumshe idanunsa yayi ya buɗesu cike da nutsuwa yace.

" Komai Soyayya da shaƙuwar zuciya biyu, dole sai mutuwa ta shiga tsakani, kota ɗauke ɗaya tabar ɗaya ko kuma ta ɗauke su duka lokaci guda, amma babu wanda mutuwa zata ƙyale, Falmata duk yanda zaki so masoyinki karki saka a ranki cewa bazaku taɓa rabuwa ba, akwai ƙaddara akwai kuma mutuwa, dole ne sai sun shiga tsakani, kuka ko damuwa bashi ne abinda ake yiwa masoyi ba, bayan an rabu dashi, addu'a da kuma sadaka shine babbar Soyayyar da zaki cigaba da masa bayan kin rasashi, mutuwar masoyi bashi bane yake nuna ƙarshen Rayuwar masoyiya ba, dole zata rayu koda kuwa zata kasance da ciwon sonsa, ki masa gata bayan sa da addu'a da sadaka, ki riƙe wannan a ranki, sannan ke yanzu kina nufin a haka zakije mata, kina kuka tana kuka babu mai rarrashin kowa a cikin ku, ke ya kamata ki danne damuwarki ki rarrashi ƙawarki, saboda yanzu zuciyarta rarrashi take buƙata, gatan da zaki mata shine ki ɓoye wannan damuwar taki, ki Kuma share hawayenki, sai kije kiyi ƙoƙarin share mata nata Hawayen dan Allah karki karya mata zuciya idan har kinsan bazaki iya rarrashinta ba, Please karki jeki."

Shuru Falmata tayi tana laɓe a ƙirjinsa sai famar sauƙe ajiyar zuciya take, ta kuma kasa Magana domin kuwa maganganun DOCTOR sun kashe mata jiki, ita a nata ra'ayin ta rayu dashi har ƙarshen rayuwarta, sai kuma gashi shi yana sanar da ita cewa dole sai ɗaya ya tafi yabar ɗaya, ita zata fi so koda mutuwa zata shiga tsakanin su, zatafi so ta fara ɗaukar ta, kafin shi, bata son ganin ranar da ƙaddara zata rabasu da numfashin su, domin kuwa itace ranar da zatafi ko wacce rana muni a rayuwarta, a hankali ta furta masa.

" Zan adana Hawaye na, domin ganin na rarrashi Maji, sai dai fuskata bazata taɓa ɓoye tausayi da kuma alhinin rashin da tayi ba, Zan bata kulawar data kamata ƴar uwa ta jini ta bawa ƴar uwar ta, domin kuwa tsakanina da Maji ya shige ƙawance ko aminta, jini ɗaya nake ɗaukar ta, kamin na tafi gareta."

Kanta DOCTOR ya shafa tare da manna mata kiss a dokin wuyan ta, hanunsa yasa ya jawo Briefcase ɗinsa, kuɗin Nigeria ya ɗauko 3k ya ware tafin hanunta ya danƙa mata tare da cewa.

" Na miki izini kije Allah ya jiƙansa, ki sanar dani lokacin jana'izar sa, ko ta waya ne insha zanzo."

Hawayen ta ta goge tare da kaɗa masa kai alamun to, sannan ta tashi ta tafi, cike da ƙauna ya bita da kallo harta fice, tashi yayi ya shige tollet wanka yayi, ya fito shafe shafen sa, yayi kasancewar shi mutum ne mai son gyaran jiki da ƙamshi tamkar mace, cikin Black jeans da Yellow riga ya shirya, ya fito da niyyar zuwa gidan Aunty JALILA, sashin Hajja ya nufa, kafin ya shiga wajen Hajja sai da ya shiga falon Aunty YANA da Sallama amsawa tayi tana masa maraba, ƙarasowa yayi ya zauna yana cewa.

" AUNTY sannu da hutawa mun sameku lafiya."

Murmushi Aunty YANA tayi tace.

" Alhamdulillah mutanen India kunje can kun ɓace abunku, ya karatun an gama cikin Nasara, abu yayi kyau sosai Allah ya sanya alkairi."

Murmushi DOCTOR yayi tare da cewa.

" Ameen AUNTY, bari na shiga na duba Bulama da jiki, ya labarin Ibrahim yazo kuwa.''

" Ibrahim baizo ba, amma dai yace insha Allah ya na hanya.''

"Allah ya kawo sa Aunty"

Doctor yana ficewa, ɗakin Hajja ya shiga shuru yaji falon nata babu kowa da alamu tana ɗakin Bulama fitowa yayi ya shige ɗakin Bulama, tana nan kuwa zaune harda Baba Bukkar Bulama sai famar jan numfashi yake da ƙyar, kusa dashi DOCTOR ya zauna yana cewa sannu Bulama, kai kawai ya ɗaga masa numshin dake fito masa da ƙyar shiyake hanasa Magana, duban Baba Bukkar yayi ya gaishe sa, amsawa Baba Bukkar yayi cike da fara'a yace.

" Ɗazu ai da YAHANASU take sanar dani dawowarka, naso shigowa sai kuma Allah baiyi ba, bana gusawa kusa da Bulama, saboda baya jin daɗi SOSAI."

Kaɗa kansa DOCTOR yayi yana ɗan gwale idon Bulama, yace.

" Ayya ba komai Baba Amma ya kamata Bulama a kaisa asibitin kustin, zazzaɓin fa da alamu ya fara ƙona masa jini, ayi gaggawar kaisa kafin rai yazo yana ɓaci."

" Hakane Hassan, yanzu ka tashi kaje ka ɗauko mana mai adaidaita, sai mu tafi asibitin."

Cike da nutsuwa DOCTOR yace.

" Baba ai akwai motar gida naga, me zai hana a kira BELLO sai yazo aje asibitin."

" To shikenan kirasa."

Cewar Baba Bukkar, Doctor wayarsa ya ɗaga tare cewa Bello yazo yanzu za'a kai Bulama asibiti, bayan ya gama wayar ne ya dubi Baba Bukkar yace.

" Baba na masa magana yana zuwa yanzu, ni yanzu zanje na duba Aunty JALILA bata jin daɗin ƙafar ta itama, daga can zanzo asibitin na sameku."

A dawo lafiya Baba Bukkar ya masa sannan DOCTOR ya fita yana yiwa Bulama sannu, bai juma da fita ba kuwa Bello yazo suka wuce asibitin.



*GIWA BARECK*


DOCTOR bai sha wahala ba wajen gane gidan Aunty JALILA kasancewar, mijinta babban mutum ne wanda kowa ya sanshi, bakin makeken get ɗin ya tsaya tare da ƙwanƙwasawa mai gadi ne police ya buɗe, tsayawa yayi tare da ƙare masa kallo yace.

" Wajen wa kazo ka."

Amsa DOCTOR ya basa da cewa.

" Wajen Jalila nazo matar gidan."

Mai gadin gidan cewa yayi.

" Okay to kayi haƙuri amma gaskiya nan ba'a shiga sai da ambada sanarwar cewa zaka zo, ni kuma ba'a bani izinin zuwanka ba."

Murmushi DOCTOR ya saki tare da cewa.

" Ba komai officer, jeka kawai."

Shigewa ciki yayi shi kuma DOCTOR ya zaro wayarsa, numbern AUNTY JALILA ya kira sam baiso tasan da zuwan sa ba, yafi so yayi mata suprice, muryar ta yaji ta cikin wayar tana cewa " ƙanina nayi laifi tuba nake "

Dariya DOCTOR ya saki yace.

" Tunda baki zoba aini gani a ƙofar gidan ki, Hajiya JALILA an hanani shiga gidan manyan mutane"

Cike da mamaki Aunty JALILA tace.

" Dan Allah da gaske kake ko kuma wasa kake min.?"

" Serious AUNTY Wallahi ina ƙofar gidan ki."

Katse wayar Aunty JALILA Tayi tana duban HABEEB dake zaune tace.

" Abokinka ne mutanen India wai yana waje an hanasa shigowa, dan Allah taimaka kaje ya buɗe masa get ya shigo, murmushi HABEEB ya saki tare da ɗaga Salma dake kwance jikinsa tana bacci ya kwantar da ita a kujerar, ya tashi tare da fitowa, a wajen mai gadin ya tsaya cike da Zolaya yace.

" Officer yau fa ka tabka babban laifi taya zaka hana ɗan masu gida shigowa, gidan su, Lallai yau Aunty zataci tararka, ka hana ɗan lelenta shigowa."

Ya ƙarasa maganar cike da dariya officer cewa yayi.

" To ai ban sanshi bane, shiyasa da gaske dangin kune."

" Ƙanin Aunty ne uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, ita yake bi, kuma ɗan lelenta ne, daga yau karka kuma hanasa shigowa GIDAN NAN bashi da shamaki da gidan."

" Insha Allah bazan sake ba."

Officer ya faɗa yana tashi ya buɗe ƙofar, DOCTOR dake tsaye ne yaga buɗewar get ɗin umarni ya masa daya shigo.

Shigowar yayi, HABEEB dake tsaye ne ya saki murmushi tare da cewa.

" Welcome DOCTOR HASSAN."

Yana miƙa masa hanu suyi musabaha, kau da kansa gefe DOCTOR yayi tare da shigewa yana jawa HABEEB tsaki, murmushi HABEEB ya saki yana kallon rashin hankali da raini irin na DOCTOR, sam bashi da hali mai kyau ko kaɗan........................




Kuyi hkr da wannan insha Allah gobe zaku sami read more kamar na yau..




Wannan littafin na kuɗi ne karki karanta min idan baki biyu ba, ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.








*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN ✍🏻*





*(UMMU NASMAH CE)*
[10/3, 8:04 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 75 to 76*







_________✍🏻Girgiza kansa kawai HABEEB yayi tare da ficewa daga cikin gidan gabaki ɗaya domin kuwa bazai iya komawa cikin gidan ba, Hassan yana masa kallon banza zuciyarsa bazata daurewa hakan ba ya rasa wani irin baƙar gaba Hassan yake masa yau ko wani ɗan uwan sa ya kashe masa iyakaci kenan, balle kuma akan mace hmmmm!!! Ya sauƙe ajiyar zuciya tare da ficewa, mai gadi kuwa cike da ɗaurewar kai yake duban su, idan ba saɓanin fahimta yayi ba, sai ya ga kamar wannan bakon gaba yake da Oga HABEEB sunan daya ke kiran sa dashi kenan, ajiyar zuciya ya sauƙe ganin bashi da amsar tambayar sa, shi kuwa DOCTOR cike da ɓacin ran ganin HABEEB ya shiga falon Aunty JALILA da yasan zai haɗu da HABEEB da baizo ba, tana zaune tana yanke farcenta ya shigo da Sallama, dariya tayi cikin farin ciki tace.

" Oyoyo ƙanina, ka rigani zuwa, amma dai ni naso zuwa maka sannu da zuwa kafin kai kawai saurin zuwa kayi."

Dariya DOCTOR yayi yana zama gefen da Salma ke kwance yace.

" Ke dai kawai kinga nazo ne, kunya ta isheki shiyasa zaki kare kanki, Umma ta faɗa min ƙafarki ke ciwo, AUNTY nayi farin ciki sosai yau da na ganki a cikin gidan ki na Aure gashi har na kawo miki ziyara ina zaune ɗakin ki, hmmm ko yanzu na godewa Ubangiji ya gama cika min burina, gashi yau har saka rai ake da ganin zuwan ɗanki ko ƴarki duniya, Allah ya sauƙeki lafiya AUNTY."

Murmushi Aunty JALILA tayi tana jin ƙaunar ɗan uwanta yana ratsata, cike da nishaɗi tace.

" Nima KULLUM nakan godewa Allah, daya min ni'ima ta Aure wanda a baya na fidda rai da samunsa, gashi yanzu jinkiri ya zamo min alkairi, Tabbas ba macen da zatayi jinkiri bai zamo mata alkairi ba, na samu miji na gari mai kula da iyalansa haka ma danginsa mutanen ƙwarai musamman Momy mahaifiyar HABEEB, ta riƙeni tamkar ƴar da ta haifa a cikin ta yaran mijina sun ɗauke ni tamkar mahaifiyar su, basa min raini kuma basa son ɓacin raina, bani da damuwa yanzu ina cikin fari."

" Alhamdulillah!!! Naji daɗin jin wannan labarin, Tabbas kowa ya ganki yasan kina cikin kwanciyar hankali, sai fatan Allah ya sauƙeki lafiya."

Da ameen AUNTY JALILA ta amsa tare da tambayar sa.

" Wai ina HABEEB ne ban gansa ba, ka barsa gun officer ko nasan shi idan ya haɗu da officer sun dinga calikanci kenan."?

Girgiza kansa DOCTOR yayi tare da cewa.

" No ya fita, bansan ina yaje ba gaskiya."

Yayi Maganar yana haɗe ransa.

" Ya tafi kuma, ko dai ka masa hali, kaga Hassan, abinda kake fa baya dacewa, SAIF ya sanar dani duk wani abinda yake faruwa tsakanin ka da HABEEB akan Falmata, HABEEB ba mutum bane wanda ya cancanci wulaƙanci daga gareka, mutum ne wanda ya kamata ka riƙesa riko na mutunci, domin kuwa HABEEB mutum ne shi mai alkairi da kuma daraja ɗan adam mutumin da baya ƙyamar talaka, ko yaya kake zai zauna dakai, dan Allah karka zamo mutum mai saka alkairi da sharri, komai tsiyar HABEEB, kaikam ya taimakeka ya maka rana, ba gori nake maka ba, gaskiya nake faɗa maka, domin kuwa duk wani matsayi da zaka taka a duniya shine silar hakan, koda kuwa shugaban ƙasa ka zamo, ka janye gaba tsakanin ku domin kuwa sam hakan ba daidai bane, akan mace kake wannan gabar kuma kaine kayi Nasarar auren ta, to meyasa bazaka manta komai ba, ku dawo Kamar da, ina faɗa maka gaskiya ne fa a matsayina na ƴar uwar ka Hassan wacce bazan so na barka cikin ɓata ba, dan Allah ka rage wannan Zuciyar ta ka HABEEB bai kamaci wulaƙanci ba."

" Hmmm!!! Aunty kenan, wai meyasa mutane suke min gori ne akan wannan Hanyar karatun da HABEEB yamin na tafiya India, wannan karatun fa Allah ya ƙaddara sai nayi shi, koda taimakon HABEEB ko ba taimakon sa dole sai nayi tunda Ubangiji ya hukunta hakan, sannan wannan kuɗin karatun fa, ba kuɗin ubansa bane kudi ne na gwamnati, haƙƙin mune, akan me za'a dinga min gori, ko dole ne sai nayi aminta dashi, ubanane shi waye shi, kowa yayi harkar sa mana, nace bana ƙaunar sa dole ne sai na sosa ko ana tilastawa zuciya sosai ne."

Girgiza kanta Aunty JALILA tayi cike da jin haushin bak'ar zuciyar ɗan uwan nata tace.

" Ba a tilastawa zuciya sosai amma ana tilastawa zuciya hallaci, bakaji karin maganar nan ta Hausawa ba, *ANA BARIN HALAK KO DAN KUNYA* meyasa kai zuciyarka ta kasa yiwa HABEEB uzuri, tana neman mayar dakai butulu, koda kuɗin gomnati ne, ai dai shine ya maka hanya ko? Idan bai maka Hanyar ba, a ina zaka samu haƙƙin naka da kake ambaton sa, ka dawo hankalin ka, ka fara gane mai sonka, domin kuwa ba kowa bane yake zama maƙiyi, domin kuwa HABEEB ba ƙaramin masoyinka bane, amma bak'ar zuciyar ka ta hana ka gane hakan me ka ɗauki Soyayya gaba, idan har haka taka Soyayyar take to Wallahi zuciyarka bata maka adalci ba, bai kamata Soyayya ko kishi ya rufe maka idanu daga ganin gaskiya ba, ka gyara kaje ka nemi HABEEB ku daidaita na Tabbata shi baya fushi da kai, Hassan yau na faɗa maka gaskiya koda kuwa zakaji haushi na."

Tunda ta fara Maganar yake kallon ta harta kai ƙarshe Kafin ya miƙe yana taɓe baki yace.

" AUNTY ki gafarce ni, AMMA bazan taɓa shiryawa da HABEEB ba, saboda ni ina hango abinda ku kuka kasa gani, har yanzu ina kallon Soyayyar matata a cikin idanunsa, zuciyata bazata taɓa aminta dashi ba, dan haka ku daina danganta zuciyata da wannan matsalar, idan kuma laifin zuciyartawa ne, to tayi a daidai, domin kuwa tana kishin abinda take so ne, amma ki sani har abada bazan taɓa jin haushin ki ba, koda kuwa rufeni kikayi da duka, kin kai kimin faɗa ne shiyasa kika min, na tafi dama ba zama nazo yi ba."

Ya ƙarasa maganar yana juyawa zai bar falon, Magana Aunty JALILA take masa, amma bai saurareta ba, saboda ya hau dokin zuciya yana tsoron ya tsaya zuciyarsa ta kasa jure Maganganun ta, har ya faɗa mata abinda bai dace ba, gara kawai ya tafi abinsa numfashi Aunty JALILA ta sauƙe tare da furta.

" Ikon Allah, wai mutum Zuciyarsa harta rinjayi tunanin sa, Allah ka yayewa ɗan uwana wannan Zuciyar tasa, ta ƙarasa maganar tana cigaba da yanke farcenta.



Can kuwa gidan mutuwar, Maji tana jikin Falmata har yanzu bata daina zubar da Hawaye ba, hankalinta har yanzu yana tashe Falmata cike da raunin murya tace.


" Maji dan Allah ki daina kukan nan, ko kin manta cewa, dukkan mai rai mamaci ne, Allah Shida kansa yace " KULLU NAFSIN ZA'IƘATUR MAUT" to meyasa zaki kasa haƙura da hukuncin Ubangiji, addu'a da sadaka shine gata da zaki masa bayan babu numfashin sa, domin kuwa zai iskesa har makwancinsa sa, kinga kenan kina nan kina aika masa Soyayyar ki yana kwance cikin kabarin sa, dan Allah ki daina kukan nan haka Maji babu kyau yiwa mamaci kuka."

. Sharce majinar da ta zo mata Maji tayi, tayi shuru tana sauƙe ajiyar zuciya ba tare da tayi Magana ba, sai ajiyar zuciya kawai da take famar sauƙewa, Mama mahaifiyar Maji Falmata ta kalla tare da ce mata.

" Mama yaushe ne za'ayi sallar jana'iza zan sanar da DOCTOR ne."

Mama cewa tayi.

" Sunce sai zuwa yamma ko gobe saboda sai anyi cike cike kafin a kawo su amma dai basu saka lokaci ba."

Kaɗa kanta Falmata tayi, ita kuwa Maji shuru tayi sai ambaton sunan Ubangiji take, a hankali take jin damuwar na ɗan mata sauƙi.



Tunda aka yi mutuwar Falmata bata koma gida ba, sai da akayi sadakar uku, Aunty YANA da Umma tare sukaje suka yiwa Maji ta'aziya Umma sosai ta yiwa maji nasiha tare da nuna mata girman haƙuri, shima DOCTOR tare sukaje da SAIF suka musu ta'aziya.


Bulama shima kwanan sa Uku a asibiti amma jikin nasa babu sauƙi, su kansu likitocin sun kasa gane abinda yake damunsa, sun san yana da hawan jini amma ba shine Abinda yafi damunsa ba, Baba ko da ya dawo daga Gombe sosai yasha kuka yanda yaga halin da mahaifin nasa yake ciki, DOCTOR da yaso ya fasa tafiya da Falmata ya je da Bulama can India a duba lafiyar sa, amma Bulama yaƙi yadda yace shi a barshi a masa jinya a kasarsa babu yanda suka iya dole suka haƙura suka barsa.


AUNTY YANA kuwa musamman ta ɗauki Aunty Ladi take yiwa Falmata gyaran jiki, kasancewar Aunty Ladi SOSAI ta iya gyaran jiki, ɗure ɗure kuwa sosai take mata, a cikin kwana Biyar Falmata tayi wani irin haske na ban mamaki, fatarta kuwa tamkar fulawa haka ta zama tsabar santsi, ƙamshi kuwa duk inda ta gifta sai anji sa, AUNTY YANA sosai ta saka mata Ido da zuwa ɗakin DOCTOR, rabonta da ɗakin tun sanda taje ta sanar dashi mutuwar mijin Maji, bata sake komawa ba, sakamakon warning ɗin da Aunty YANA ta mata sai dai su gaisa idan sun haɗu a ɗakin Umma ko ɗakin Hajja, DOCTOR SOSAI ransa ya ɓaci da tsakani da Aunty YANA ta musu sai dai bashi da halin Magana yasa shi haƙura Dole.

Falmata komawarta gidan Maji sau uku a cikin sati biyu, Alhamdulillah yanzu Maji ta ɗan sake har tana walwala da mutane.


Aunty LADI gyaran sati Uku ta yiwa Falmata, amma kuma ta gyaru, tayi kyau sosai jikinta gwanin ban sha'awa.




***************


Zaune yake gaban Baba Bukkar da Baba cikin fada DOCTOR ne yace.

" Baba jibi zan koma India, sai dai ina sone zamu tafi da Falmata, shekara ɗaya kawai zamuyi mu dawo."

Cike da nutsuwa Baba yace.

" Allah ya kaimu, mahaifiyarka ai ta sanar dani rashin lafiyar Bulama yasa ban samu na zauna da kai ba mun tattauna, zaka iya tafiya da ita, matarka ce ai kana da iko da ita, amma Hassan da zan baka shawara da nace gidan da suka baka ka sai dashi tunda bawai Rayuwa zakayi a can ba, ka aiko da kuɗin nan gida Nigeria, akwai fili na a New GRA na mallaka maka shi, sai a tada gini kaga kafin ka dawo an kammala komai ina tunanin hakan zaifi, can kuma sai ka kama haya."

Shuru DOCTOR yayi yana nazarin Maganar Mahaifin nasa, Tabbas hakan zaifi domin kuwa idan ya sayar da gidan ya aiko kuɗin zai masa ginin da yake so, duban Baba yayi yace.

" Hakan yayi Baba insha Allah zan turo da kuɗin idan na koma, za muyi magana da Saif yayi Magana da Usman art ya turo min zanen gida sai na zaɓa na tura masa hakan yayi Baba."

Baba Bukkar ne yace.

" Alhamdulillah!!! Masha Allah hakan ma babban arziki ne ka mallaki gidan ka na kanka, shine arziki, Maganar Falmata Kuma, ku tafi Allah shi muku albarka, zanyi Magana da Yana sai ta shirya ta zuwa jibin ku wuce."

Godiya DOCTOR ya yiwa iyayen nasa, tare da tashi ya fito cikin farin ciki.

Hakan kuwa Baba Bukkar ya sanar da Aunty YANA da Hajja Maganar tafiyar su DOCTOR, babu wanda ya hana sai ma fatan alkairi da suka musu.

Ranar Lahadi da yamma ana gobe zasu tafi, DOCTOR ya shigo shida Saif hanunsu riƙe da manyan akwati biyu sai karami a hanun wani yaro, a ɗakin Umma suka ajiye, zama DOCTOR yayi ya cewa Umma dake kallon akwatin.

" Buɗe mana Umma ki gani"

Hanu Umma tasa ta buɗe akwatin farko cike yake da atampopi dukkan su kuma an ɗinka su, sai turame uku wanda ba'a ɗinka ba, cire ukun yayi ya ajiye a gefe, Umma rufe akwatin tayi ta sake buɗe na biyu, wasu arnan sleeping dress ne da kuma dogin riguna sai riga sket da kuma wanduna, sai set ɗin bireziya da hijab, sun kai kala hamsin, shima Umma rufesa tayi ta buɗe ƙaramin kayan makeup ne cike fal, dubansa Umma tayi tace.

" Waɗannan na menene.?"


" Umma Falmata na sayawa, na bawa Babawo ya dinke mata atampopi, saboda ba'a mata kayan lefe ba, kuma kinga zamu tafi India, bazai yiwu ta tafi ba ta da wasu kaya ba, wadannan atampopi kuma naki ne guda uku na sayan miki."

Murmushi Umma ta sauƙe tare da cewa.

" Masha Allah, ka kyauta, Allah ya maka Albarka bari su Fanna su shigo sai su kaiwa Yana ko."

Da to DOCTOR ya amsa sannan saif ya gaisa da Umma sun juma a wajen umman kafin ya tafi gidan Aunty JALILA mata sallama.


Itama Falmata ranar a gidan maji ta wuni sai magarib ta dawo koda ta dawo taga kayan da DOCTOR ya kawo mata sosai taji daɗin kayan.


Washegari da misalin karfe goma jirgin su DOCTOR ya ɗaga zuwa India shida matarsa.







Kuyi hkr ban samu nayi Editing ba, yau🤗🤗🤗🤗🤗







KI biya kuɗin ki ki karanta halak ɗinki yar uwa, karki na sata, ni bazan ja miki Allah ya isa ba, amma dai kinsan hukuncin wanda yaci haƙƙin wani ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.





*Alƙalamin RASHEEDAT USMAN ✍🏻*






*(UMMU NASMAH CE)*
[10/5, 10:22 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 77 to 78*





__________✍🏻 Tunda suka sauƙa a filin airport dake cikin garin Mumbai Falmata ta fara ware Ido tana kalle kalle, ikon Allah wai itace cikin ƙasar India mutanen da take ganin su cikin tv yau kuma gata gasu, tana kallon su, DOCTOR ne ya riƙo kunkumin ta, ganin tana neman shigewa cikin jama'a ta ɓace masa, gefe guda ya matsa da ita, tare da neman kujera suka zauna, ajiyar zuciya ya sauƙe yana duban wani mutum dake ajiye musu akwatin su a gefe, kallon sa Falmata tayi tana sakin murmushi tace.

" DOCTOR na ya muka zauna a nan kuma.?"

Murmushi ya saki cike da Zolaya yace mata.

" Saboda naga kamar baki gaji da kalle kallen bane ƴar ƙauyen Nigeria."

Dariya Falmata tasa sosai har tana kwanciya kafaɗarsa ta maida masa amsa da cewa.

" Ai kuwa dole nayi ƙauyanci tunda nazo ƙasar da ban santa ba, Serious Doctor na, me muka tsaya yi anan."

Murmushi ya saki yace.

" Motar da zata zo ta ɗauke mu muke jira."

Kaɗa kanta Falmata tayi tana lumshe idanunta, basu juma ba kuwa motar ta zota, cike da fara'a kyakkyawan mutumin ya ƙaraso wajen su yana ƙarewa Falmata kallo, shima DOCTOR murmushi yayi tare da miƙa masa hanu.

" Welcome Hassan."

Mutumin ya furta, murmushi DOCTOR ya saki yace.

" Thank Sanskar, nuni ya masa da Falmata yace she is my wife."

" Murmushi Sanskar yayi tare da cewa.

" Wow Beautiful women, Black Beauty"

Ya faɗi yana ɗaga mata hanu,duka dariya sukayi, wannan mutumin Sanskar ya kira ya jidi akwatin nasu ya kai Motar suka shiga, tafiya suke Falmata tana karewa ƙasar kallo ta glass ɗin motar, wani makeken gida suka nufa, Darect kuwa aka wangale musu get ɗin, suka shige ciki, bayan sunyi parking ne,

Please Login or Register in order to submit comment