Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Auren ta amma sai ya fasa, tare da kawar da kansa gefe, itama kanta Falmata taso ta gaishe da HABEEB sai dai ganin yanayin DOCTOR yasa ta fasa, Daddyn nasa kawai ta gaishe, jirgin Cairo shine ya fara tashi, HABEEB yana kallon Falmata cike da so da ƙauna ya shige, cikin jirgin, haka HABEEB ya bar ƙasar cike da Soyayyar Falmata, basu jima da tashi ba, suma DOCTOR aka kira nasu jirgin, sallama sukayi da iyayen sa, shida Saif suka shige cikin jirgin, suna ɗaga musu hanu, DOCTOR idanunsa yana kan matar sa, Falmata idanunta cikowa yayi da Hawaye, tana ji tana gani jirgin su ya ɗaga, haka suka juyo gida cike da kewarsa Falmata kuwa babu daɗi taji amma haka ya zamo mata dole tayi hkr.



Haka rayuwa ta dinga tafiya, Falmata kullum sai sunyi waya da DOCTOR safe da kuma dare, yau wata huɗu da tafiyar DOCTOR, aka saka ranar auren Maji da ZULUM wata Uku, kacal Falmata sosai ta taya ƙawarta murna, Falmata tare da Maji suka dinga hidimar hada-hadan Auren, lokaci kuwa babu wuya take lokacin Auren yazo saura sati ɗaya kacal inda za'a kai Maji unguwar BULUNKUTU AIRPORT, Ranar Alhamis akayi walima Falmata itace kan gaba a hidimar bikin, sai dai bata bawa ko wani NAMIJI fuskar mata magana ba.haka akayi hidimar bikin aka watse cikin farin ciki aka kai amarya gidan ta dake BULUNKUTU AIRPORT..................."








Kuyi hkr yau na muku a gurguje saboda naga kun matsu mu dawo cikin labari shiyasa na ɗan muku a gurguje.






Wannan littafin na kuɗi ne, idan kin gansa a waje ma ɗauko sa aka yi, ki biya kuɗin ki ki karanta yafi alkairi fiye da ki karanta Abinda ba gumin ki ba ki neme ni ta nan domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.






*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN ✍🏻*






*(UMMU NASMAH CE)*
[9/30, 10:46 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 71 to 72*




_______✍🏻 Falmata tunda ta shiga kaɗaicin rashin DOCTOR na waɗannan watannin, sai taji tana da sha'awar ta cigaba da karatun ta, zaman gidan ya isheta, tunda aka ɗaura mata Aure da DOCTOR shikenan ake mata kulle a cikin gidan babu inda take samu taje duk anbi an takura ta, ita kaɗai take wannan tunanin yayin da take kwance a ɗakin ta, wayarta ta jawo a hankali ta danna masa kira, harta yanke bai ɗaga ba, sai can kuma taga kiran sa ya shigo mata, ɗagawa tayi ta kara wayar a kunnen ta cikin sanyin Murya tace.

" Aminci Allah ya tabbata a gareka tauraro na DOCTOR na."

Murmushi DOCTOR ya saki ya lumshe idanunsa, yana jin wani sanyi da yaji muryar ta ta doki kunnensa, yana zaune harabar school ɗin nasu shida Saif da wani ba'indiyen Mutum mai suna sanskar sai Hema dake zaune gefen Saif.

" Ya akayi hasken rayuwar Hassan, tauraruwar mata da fatan kina cikin halin lafiya my dear."

Ɗan dariya Falmata ta saki mai sauti cike da farin ciki tace.

" Muddun kana cikin halin lafiya, babu makawa nima ina halin lafiya, domin kuwa bugun zuciyata ne kai kaga kuwa dole idan cutu sai kaji sautin a ƙirjin ka, DOCTOR na, alfarma na kira na roƙa ko Allah zaisa na samu."

Murmushi ya saki yana kallon Saif dake bawa Sanskar lbrn Falmata yace.

" Faɗi ko wacce irin alfarma ce, haske na, Ni kuwa insha Allah zan cika miki ita muddun batafi ƙarfi na ba."

" DOCTOR na, MAKARANTA nake so na koma University, na gaji da zaman gidan ina son na cigaba da karatu."

Ɗan shuru yayi, yana nazarin Maganar ta, kafin yace.

" University Falmata!!! Wacce makaranta kuma zaki cigaba da ita, ni gaskiya da anawa ra'ayin ne, zance ki hkr da wani karatu, kawai ki rungumi Auren ki, sai dai bazan danne miki ƴancin ki ba, kina da right ɗin da zaki nemi ilimi a matsayin ki na mace, zan barki ki cigaba da karatu, amma sai na dawo hankalina zaifi kwanciya da hakan, yanzu ina cikin school idan na koma hostel zan kira ki."

Ran Falmata baiso wannan hukuncin da DOCTOR ya yanke ba, a son ranta ya barta tayi karatun domin kuwa yanzu ne take buƙatar sa da take cikin kewa, bata son jayayya dashi yasa tace masa.

" Shikenan Allah ya dawo da kai lafiya ta furta ina son zanje gidan Maji gobe da safe na wuni ."

" Yawo dai kike son fita Dear, to Allah ya kaiki lafiya ki gaisheta ko"

Da zataji Falmata ta furta tare da katse wayar, juyi tayi daga katifar tana sakin murmushi.


***************


Malam na dawo ne game da Maganar Da mukayi na ƙanwar mij........"

Dakatar da ita yayi tare da cewa.

" Na sani ba sai kin faɗa ba, kin dawo ne game da ƙanwar mijinki ko, da kuma mijinki daya fara miki tawaye."

Kaɗa kanta tayi alamun eh, sannan ta ƙara da cewa.

" Malam ina son a ƙara dawo min da mijina tafin hanuna, sannan itama ƙanwar tasa a rufe min bakinta ta manta da dukiyar ta, da yake wajen mijina, a kawar da hankalin kowa daga kan wannan dukiyar."

Dariya bokan ya bushe dashi irin na marassa imani yace.

" Wannan abune mai matuƙar wahalar gaske rufewa wannan matar baki domin kuwa macece mai ibadar gaske dan haka ba ƙaramin aiki zamuyi akanta ba, aikinta zanyi shi amma ba yanzu ba, saboda sai mun samata tashin hankalin da zamu sa ta shagaltar da ibadar ta, a wannan lokacin ne zamu yi aiki a kanta, shi kuma mijinki, aikin sa mai sauƙi ne, ga wannan kwalbar kije ki saka a ƙarƙashin gadon da yake kwana karki kuskura wannan kwalbar ta fashe, ga wannan ƙwai ɗin da layar nan shi kuma zaki nemi tulu ki saka a ciki harda allura, sai ki tonu rami a cikin gidan ki, ki binne, yanda kika binne wannan tulun kin binne bakinsa da kuma gardamar sa gareki kenan, bazai taɓa miki musu akan duk wani umarninki ba, ita kuma zan nemeki idan buƙatar aikin nata ya taso, ajiye min numbern wayarki anan."

Cike da jin daɗi Jummai ta saka numbern ta a wayar bokan, ajiye masa kuɗin da zai kai 40k tayi a karkashin shimfiɗar sa, sannan ta ɗauki abubuwan daya bata tana murmushi tare da ja da baya harta fice, dariya bokan ya bushe dashi.

Kamar yadda bokan ya umarce ta Jummai haka tayi tun a hanya ta sayi tulun ta, bayan ta gama binnewa ne, sai kuma ta zari hijab ɗinta ta nufi gidan Umma.

Da sallama kuwa ta shiga, Umma dake zaune tsakar gida ita da JALILA sukaji sallamar ta, JALILA da gudu ta tashi ta faɗa jikinta tana cewa.

" Oyoyo Aunty Jummai!!!"

Dariya Jummai tasa tace.

" JALILA aini fushi nake dake, na zamo miki kura baki zuwa gida na ko."?

Dariya Jalila tayi Umma ce tace.

" Mu shiga daga ciki Jummai."

Cikin falon Umma suka shiga suka zauna cike da sakin fuska Umma suka gaisa da Jummai, Jummai ne tace wa Umma.

" Hassan kuma an girma, naso ai zuwa Ranar ɗaurin auren sai Baban Musa yace min babu taro shiyasa banzo ba, to naso kuma nazo bayan bikin na miki murna nan ma Allah baiyi ba, sai yanzu, Allah ya sanya alkairi."

Dariya Umma tayi tace.

" Lah babu komai fa Jummai, komai ai sai Allah ya nufa, jiya ai Musa yazo da yamma ya gaishe ni, ya labarin Yakumbo."

Yakumbo tana nan lafiya, kinsan kwanan nan ƴan boko Haram sun shiga cikin BANKI sun musu ɓarna sosai, harda jikanta magidan ci shima abin ya rutsa dashi sun kashe sa, yankan rago suka masa, abin dai babu daɗin jin."

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati, Oh ko yaushe wannan masifar ta ƴan boko Haram zata ƙare a Nigeria, abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, Allah ya mana maganin wannan musibar ita kuma Yakumbo Allah ya bata hkrn rashin sa, hmmmm!!! Allah ya jiƙansa."

Da ameen Jummai ta amsa, dai-dai lokacin Falmata ta shigo cikin falon bakin ta ɗauke da Sallama, Jummai ita ta amsa sallamar, kusa da Aunty JALILA ta zauna tace.

" AUNTY JALILA, Ga can wani yaro a tsakar gida yazo wai wani yana sallama dake a waje."

Cike da mamaki Aunty JALILA tace.

" Wani kuma waye to.?"

Umma ce tace.

" Ki tashi kije ki duba ko waye ne ma ai zaki gani idan kinje."

Tashi Aunty JALILA tayi ta ɗauki mayafinta ta fito cike da mamakin waye yake kiranta."

Falmata kuwa cike da ladabi ta gaishe da Jummai, amsawa tayi cikin fara'a tana cewa.

" Amarya, anyi biki lafiya."?

" Lafiya Alhamdulillah" Falmata ta amsa tare da cewa Umma, " zanje gidan Maji, tunda aka yi biki banje ba."

A Dawo lafiya Umma ta mata sannan Falmata ta fice.

Can kuwa ƙofar gida, Jalila ce tsaye jikin wata farar mota, tare da wani babban mutum, fuskar sa cike da haiba.

" Za kiyi mamakin ganina ko, kuma baki sanni ba."?

Ɗaga masa kai JALILA tayi alamun eh, ba tare da tayi Magana ba.

" Sunana Alhaji Ibrahim Dake ni cikakken ɗan nan MAIDUGURI ne, ina unguwar GIWA BARECK da zama nayi Aure harda yara biyu, amma Allah ya yiwa matata rasuwa na ganki ne, naga kinmin kuma ina sonki shine aka min kwatancen gidan ku, Allah yasa na miki a mijin Aure.?"

Shuru Aunty JALILA Tayi kafin tace.

" Ta waje na babu damuwa, sai dai idan har da Aure kake sona zaka iya zuwa gurin iyayena duk yanda kukayi dasu dai-dai ni a waje na "

Shikenan babu damuwa insha Allah zanyi Magana dasu gobe idan Allah ya kaimu, wayarsa ya miƙa mata, ki samin numbern ki anan duk yanda mukayi zakiji ni insha Allah, amma karki manta da ina da yara biyu kuma idan Allah ya tabbatar da Aure tsakanin mu, zaki zauna ne tare dasu."

Miƙa masa wayar Aunty JALILA tayi bayan tasa masa numbern, " Babu Allah ya tabbatar da alkairi ni zan shiga ciki."

Kuɗi ya miƙa mata yace " ga wannan ko."

" A'a na gode ka barsa."

Murmushi Alh Ibrahim ya saki tare da cewa.

" Kin san dai haramun ne mai da hanun kyauta baya ko,? Kyauta na miki dan Allah ki karɓa."

Hanu tasa ta karɓa tare da masa godiya ta shige cikin gida.



*************

Wata huɗu da Maganar Alh Ibrahim da Jalila, komai ya kankama domin kuwa Bulama sunyi bincike sosai a kansa mutumin kirki ne, sannan kuma ƙani ne ga Momy mahaifiyar HABEEB, su Bulama sunsa ranar Aure wata biyu kacal, sosai kowa yayi murna da wannan Aure na Jalila da kowa ya ke muradin gani, barin ma DOCTOR da yafi kowa son ganin Auren Yar Uwar tasa, sai dai kash bashi nan za'ayi Auren, Umma taso ta ƙara sayar da Filin ta, saboda Auren Baba yaƙi yace shine zai mata komai, Umma dole ta haƙura ta barsa.

A cikin wannan watan kuwa akayi auren Jalila, aka kaita gidan ta, ya'yan mijin nata ma yara ne masu tarbiyya sam basa raina ta, yanzu Rayuwa ta yiwa Umma daɗi, kwanciyar hankali ya ƙara zuwa mata, shima DOCTOR cikin kwanciyar hankali yake karatun sa, ko wani jarabawa shine wanda yake zuwa first class sosai malam suke ji dashi a cikin makarantar, ya samu numbern yabo sosai, a wajen HABEEB kuwa har yanzu ya kasa daina tunanin Falmata ji yake a jikinsa kamar zata dawo garesa sai dai bashi da tabbacin saƙar zucinsa.


Rayuwa tana tafiya musu cikin nutsuwa ba tare da gaggawa ba, Falmata kullum tana maƙale da DOCTOR a waya, Soyayya ce mai ƙarfi ta shiga jikinsu, yayin da ɗaya yake jin bazai taɓa iya rayuwa babu ɗaya ba.


Maji ma cike da kwanciyar hankali take a cikin gidan ta, yayin da take ɗauke da tsohon ciki, haka kuma Aure bai rabata da aminiyarta ba, sukan kawowa juna ziyara a kai akai watan Maji goma da Aure ta haihu ɗan babu rai sosai maji taji zafin rashin ɗanta amma dole tasa ta hkr ta dangana.




**************



Rayuwa tana gudu yayin da shekaru suke shuɗewa, a kwana a tashi babu wuya a wajen Ubangiji, yau shekarar DOCTOR Bakwai da tafiya India kuma a yau suke saka tsamanin dawowar sa, sosai Falmata take cikin farin ciki da dawowar mijinta..............






Ki biya kuɗin ki yafi dacewa fiye da ki karanta abinda ba gumin ki ba, ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.







*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN ✍🏻*






*(UMMU NASMAH CE)*
[10/3, 8:03 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 73 to 74*




This page Deducted to *DOCTOR HASSAN PAID GROUP* sonso nake muku ƴan uwa 😘





________✍🏻 Bello shine ya ɗauki Falmata da Umma a mota sukaje tarbar DOCTOR SOSAI Falmata tayi kyau cikin wata koriyar atamfa mai ratsin baƙi tasha ɗinkin doguwar riga fuskarta yane da baƙin mayafi sosai tayi kyau duk da fuskar ta ba makeup, karo na farko data yafa gyale kenan, sun ɗan juma zaune a wajen suna jiran isowar jirgin su DOCTOR, sai can jirgin ya sauƙa Falmata cike da nishaɗi ta zubawa jirgin ido, tana duba ta ina DOCTOR zai fito, mutane sai famar sauƙowa suke a cikin jirgin, cike da nutsuwa yake sauƙowa, zuba masa idanu Falmata tayi cike da ƙauna, sosai yayi kyau har ƙiba ya ɗan yi, fuskar sa cike da saje ya kewaye masa fuska, gashin kansa ya kwanta luf gwanin ban sha'awa har haske ya ƙara, miƙewa tsaye Falmata tayi ta fara takawa cike da nutsuwa, tana nufar sa, murmushi suka sakarwa juna, sanda suka haɗa ido, Umma idanu ta zuba musu tana kallon ikon Allah sai yanzu ta ƙara tabbatar da cewa yaran nan suna son junansu, sanda ya sauƙa daga step ɗin jirgin Falmata ta ƙarasa da gudu ta faɗa jikinsa tana sakin ajiyar zuciya mai sauti, hanunsa yasa ya riƙe bayan ta, yana jin wata nutsuwa na sauƙa masa a jikinsa, a kunne ta raɗa masa.

" Welcome DOCTOR na, yau ina cikin farin ciki da dawowar ka."

Murmushi shima ya saki tare da manna mata kiss a goshin ta cewa yayi a hankali.

" Nafi Kowa jin daɗin dawowata domin kuwa nayi missing ɗinki sosai matata, ina ga dai kin manta da Umma tana wajen nan ko.?"

Saurin sake DOCTOR tayi, cike da kunya domin kuwa zumuɗi da jin daɗin ganin mujin nata ya sata mancewa da Umma tana wajen, murmushi ta saki tare da sunkuyar da kanta, murmushi DOCTOR ya saki shima tare da kama hanunta, suka nufo Umma, Umma murmushi take musu tana jin ƙaunar su na ratsata, Sanda DOCTOR ya ƙaraso wajen mahaifiyar tasa ne ya saki Falmata tare da rungume Umma, yana dariya.

" Naji daɗin ganinki Umma na, sosai nake kewarki, Umma ina Aunty JALILA bata zo tarba ta ba."

Murmushi Umma ta saki tare da ɗago sa daga jinkita tace.

" Barka da dawowa ɗana, yanzu ba lokacin amsa tambaya bane, muje gida ka huta tukunna sai na amsa maka tambayar ka, Umma kallon Falmata tayi da kanta ke ƙasa wai ita a dole kunya murmushi ta saki tace, Oh wai ke yanzu kunya ta, kike ji, kinga ƴata, daina wannan kunyar keda yayan ki, kuzo muje gida, Oh ina Saif ne kam ban gansa ba tare da kai.?

Murmushi DOCTOR ya yi yana shafa kan Fanna dake maƙale jikinsa yace.

" Umma ai tun jiya Saif ya shigo ƙasar nan, nima sun ɗan dakatar dani ne dalilin dayasa kenan ya rigani dawowa kar dai baizo miki ba?."

" Kajika da wani zancen, ya dawo jiya ya zo min ko hutawa baiyi ba, kaga muje gida ka samu ka huta."

Cewar Umma, Bello akwatin DOCTOR ya jawo, suka shige cikin motar, suka nufi gida.

A falon Umma DOCTOR ya sauƙa yayin da mutanen gidan sai famar shigo masa sannu da dawowa suke, yayin da yake amsawa cike da farin ciki, Hajja cike da tsokana ta shigo tana dariya ta zauna kusa dashi tare saka hanu ta daki kansa.
.

" Kai kai!!! Hassan anya kuwa karatu ka tafi kaga kuwa yanda ka dawo Wani ƙato, ƙiba fa kayi, malam kai da ya kamata ka rame sai kuma ka dawo jibgege, kai ina da sake ban yarda da wannan ƙibar ba."

Dariya DOCTOR yayi tare da faɗawa jikin Hajja ya kwanta yana cewa.

" Ban rame ba, sai kizo ki ramar dani ai, kuji min tsohuwa da saka ido."

Hajja cike da dariya tace na saka idon, harna kai wannan matar taka saka Ido sauƙa min a jiki karda ka karya ni, ta ƙarasa Maganar tana nuna Falmata."

Harara Falmata ta sakar mata, tare da miƙewa tsaye tana ƙoƙarin fita ta cewa Hajja.

" Ni dai nafi ƙarfin ki nida mijina sai dai kije ki rungumi wannan tsohon."

Ta ƙarasa maganar tare da ficewa Umma dariya tayi tace,

" Kinci uwaki Hajja kike tsigalewa uwar tamu."

Daga wajen tace.

" Umma ai ku ta haifa mukam bata haife muba."

Dariya Hajja tayi cike da ƙaunar jikokin nata, sai a lokacin DOCTOR ya dubi Hajja yace.

" Hajja ina Bulama."?

" Yana can kwance cikin ɗaki zazzaɓi ke damunsa tun jiya."

" Subabanallah DOCTOR ya furta tare da cewa.

" Hajja an kaisa asibiti kuwa."?

" An kaisa sun masa allura tare da magani suka basa."

" Okay Allah ya basa lafiya zan shigo na dubasa yanzu insha Allah."

Ya ƙarisa Maganar yana tashi daga jikin Hajja, Hajja ta juma zaune kafin ta fice, ya saura daga shi sai Umma da AJIRAM sai Fanna, Falmata ce ta shigo hanunta ɗauke da, tire jere da kuloli ta ajiye gaban DOCTOR ficewa tayi daga cikin falon domin basu lokaci su gana da mahaifiyarsa, Fanna itace ta sunkuya ta zuba masa abinci, sauƙowa yayi ƙasa tare da kalmashe ƙafar sa ya jawo abincin, tuwo ne miyar ɗanyen kuɓewa best food ɗinsa kenan idanunsa ya lumshe, ko baa faɗa ba yasan wannan girkin Falmata ne tayi sa, ruwan wanke hanu ya jawo ya wanke hanunsa, abincin ya ja gabansa da Bismillah ya fara ci cike da jin dadin abincin, domin kuwa sosai yayi missing ɗin abinsu na Nigeria, sosai DOCTOR yaci abincin kafin yayi hamdala yana godewa Ubangijin sa, Umma cikin murmushi tace.

" Wannan shine kura ta gamu da abincin ta nama ai kuwa sai wawa, a ƙaro ko ka ƙoshi.?"


Murmushi ya saki yace.

" Umma nayi missing ɗin abincin ne fa sosai kinga kuwa ai dole naci na ƙoshi, na ƙoshi ma Alhamdulillah!!, Umma Baba baya nan ne naji shuru."

" Eh yaje Gombe, tun jiya amma may be ya dawo nan da kwana uku."

" Okay Allah ya dawo dashi lafiya, Umma bafa dawowa nayi Nigeria duka ba, zan koma next week, sun ɗauke ni aiki a can India sai dai gaskiya Umma naƙi yadda nayi aiki a ƙasarsu nafi son nazo na hidimtawa ƙasata Nigeria, amma sun roƙeni da nayi aiki dasu na shekara ɗaya kawai, kuma na amsa aikin, next week zan koma, sun bani gidan da zan zauna harna gama shekara ɗaya da zanyi da kuma motar hawa, shine nake son na koma da Falmata, sannan Umma asibitin da suke buƙatar nayi aiki dasu sun bani kyautar kuɗi har Naira Miliyan 6."

Shuru Umma tayi kafin tace.

" Da a son raina ne da gaskiya bazaka koma India ba, gara ka nemi aiki a Nan gida Nigeria, amma tunda ka musu alƙawarin komawa, ka koma Allah yasa kan alherin ka zakaje, sai maganar tafiya da matar ka wannan hukuncin ba'a hanuna yake ba, yana hanun iyayenka maza duk abinda suka yanke akai mu mata a wajen mu daidai ne, yanzu wannan kuɗin me zakayi dasu."

Amsa ya bata take da cewa.


" Asibiti zan bayar a gina min kafun na dawo zan nemi manyan likitoci harma da nurse domin mu raya asibitin, tunda ina da lasin ɗin da zan iya buɗe asibiti na, na kaina Umma, kinga da zarar na dawo kuma, duk abinda na samu sai muyi odan kayan aiki dasu, hakan zaifi min samun kudi sosai fiye da nayi aiki a ƙarƙashin wani, Maganar muhallin da zan zauna kuma shima insha Allah, zanyi sa, tunda yanzu Baba Bukkar ya bamu wajen zama."

Cike da gamsuwa Umma ta gyaɗa kanta alamun ta gane, fatan alheri ta masa, sannan ya ƙara tambayar ta Aunty JALILA.

" JALILA tana gidan ta, kasan cikin ta ya tsufa, tafiyar tana bata wuya, gashi dama kasan tana da matsalar ƙafa."

Murmushi DOCTOR ya saki cike da farin ciki, wai yau AUNTY JALILAN sane tayi Aure harda ciki, lallai ne duk abinda yayi farko zaiyi ƙarshe, cike da annuri yace.

" Umma, insha Allah zan kawo karshen matsalar ƙafar Aunty JALILA, bari naje nayi wanka zan ɗanyi bacci idan na tashi zanje gidan nata."

Ya ƙarasa maganar yana tashi, Kaɗa masa kai Umma tayi tace a fito lafiya, ɗakinsa na zaure ya shige, wanka yayi ya saka tree cutter da best kwanciya yayi bai juma da kwanciyar ba kuwa bacci ya kwashe sa.


Falmata kuwa AUNTY YANA ta sata cikin ɗaki, sai ɗure ɗure take mata, turaren wuta gaf-gaf na tsugunno ma, dabam na musamman tasa aka mata shi, harda haɗin wankan lalle, wani ruwan gora da Aunty YANA ta bawa Falmata tasha mai shegen bauri sai famar haɗa rai da yamutsa fuska Falmata take sha, Aunty YANA tsawa ta daka mata tace.

" Kifa shanye Falmata bana son shashancin banza!!! Dan ubanki meye abin taɓe fuska a wannan."

Tura bakinta Falmata tayi, bata ce komai ba, har ta shanye, nuni Aunty YANA ta mata da tollet tace.

" Ki tashi ki shiga, akwai ruwan lallai a cikin baho ki shiga ki zauna a ciki na 30 minute, idan kin gama karki tashi kimin Magana zan kawo miki kasko ki tsugunna."

Da to Falmata ta Amsa tana shigewa cikin tollet ɗin, duk abinda Aunty YANA ta umurce ta haka tayi, sanda ta fito gabaki ɗayan ta ƙamshi take rusunanne mai daɗin shaƙa, domin kuwa shi kanshi lallen data shiga da kuma wanka dashi, turaruka ne kala-kala masu daɗi shaƙa, zama tayi tana fuskantar Aunty YANA, Aunty YANA ce mata tayi.

" Ki ɗauki haɗin zumar nan ki shanye duka karki barmin ko kaɗan."

Tura bakinta Falmata tayi tana cewa.

" Na shiga Uku Mama nikam ki bari sai anjuma, yanzu fa nasha bauri kuma nazo sha zaƙi yanzu, kusan sati biyu fa Mama, kina bani waɗannan abubuwan."

Haɗa rai Aunty YANA tayi cikin faɗa tace.

" Kinci UBANKI nace kinci UBANKI!!!! Bana son Iskanci wallahi, ki ɗauka kishanye kafin na ɓata miki rai."

Tana tura bakin ta Falmata ta ɗauka, ta kai zumar kenan bakin ta, taji ringin ɗin wayarta, ajiye zumar tayi ta ɗaga wayar HANNA ƙanwar Maji ce tace.

" AUNTY Falmata, Mijin Aunty Maji ya rasu yanzu aka sanar damu boko haram sun kashe sa."

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati!!!! Yanzu ina Maji take, tana halin lafiya."

" A'a Aunty Falmata tun ɗazu take suma fa, mun rasa ya zamuyi."

" Ina zuwa yanzu" Falmata ta furta tare da kashe wayar tace.

" Mama mijin Maji ne ya rasu, Boko Haram, zan tafi wajen ta bansan Wani hali take ciki ba."

Salati Aunty YANA ta ɗauka cike da tausayawa Maji domin kuwa mutuwar miji akwai zafi, cike da alhini tace.

" Ki tambayi mijinki tukunna Kafin ki tafi, Allah ya jiƙansa da rahama yasa mutuwa hutu ce a garesa, wannan masifar ta Boko Haram ta addabemu."

Falmata ficewa tayi da mayafin ta a hanu cike da tashin hankali, ta faɗa ɗakin DOCTOR yana kwance sai baccin sa yake cikin kwanciyar hankali faɗawa tayi jikinsa ta saki kuka mai sauti na tausayin Maji, DOCTOR kamar a mafarki yake jin sautin kukan nata, jin abin yaƙi ƙarewa ya sashi buɗe idanunsa a hankali, sai kuma ya waresu fes a kanta cike da tsoro yana duban yanda ta dunƙule a jikin sa sai shan kukanta take a hankali cikin tashin hankali ya ambaci sunan ta.



Please Login or Register in order to submit comment