Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gamborin gala, kuma mijina yana da ƙafar da zaije ya sayar min."

Cikin faɗa kawu Dauda yace.

" Bazan bayar ba kizo ki ƙwata idan kina da karfi karfa kimin Rashin kunya YAMURAM, ki shige ki tafi ki bani waje bana son shashancin banza."

Murmushi Umma ta saki tana dubansa, a yanzu ta fara gajiya da mulkin mallaka da Kawu Dauda yake mata akan dukiyarta dan haka yau ta gaji dole ya bata takadduna."

" Ya isheni haka Yaya Dauda, ka bani takadduna tun muna cikin girma da arziki, nayi niyyar taimakon ɗana kuma bazan fasa ba, koda kuwa zan rasa komai shiya tashi, ka bani takadduna idan ba haka ba, hukuma ce zata rabani dakai, saboda naga alamun kamar so kake na bar maka dukiyata ka cinye."

Dariya Jummai tayi, ba tare da tace komai ba ta shige Bedroom ɗinta, bata juma ba, ta fito hanunta riƙe da takaddun ta miƙawa Umma tace.

" Allah ya baki haƙuri ga takaddun ki, haƙƙinki ne ai tunda kika nema kuma ai dole a baki, Baban Musa bai kyauta ba kiyi hkr yaushe ne zaki sayar da Filin."

Umma hanu tasa ta ƙarbi takaddunta tace " gobe idan Allah ya kaimu da safe Baban Hassan zaije ya saka a kasuwa." Tayi maganar tare da ficewa a zuciye, Kawu Dauda duban Jummai yayi yace.

" Kinsan me kikayi kuwa, takaddun nan fa da kika saka a ranki shi kika bata."

" Na sani Baban Musa, zagon ƙasa na mata, kuma wallahi sai filin nan sun dawo hanuna, sai Musa ya fita ƙasar waje karatu shima da wannan dukiyar, duk wanda yaci tuwo dani miya yasha, badai gobe ne shi mijin nata zai tafi sayar mata da filin ba, kaji kaji mai zai faru lokaci yayi da zamuga bayan YAMURAM ka saka Ido kawai kayi kallo dani suke zancen nida su shege ka fasa."

DARIYA Kawu Dauda yayi tare da cewa.

" Na sani bakya Magana baki aiwatar ba, nima a yanzu ina buƙatar ganin ɗana yayi karatu domin kuwa akwai riba, ki duba kiga yanda wannan yaron Hassan yake neman yin kuɗi, duk abinda zakiyi ina bayan ki, sannan idan kina naiman taimako na, a shirye nake."

Tare suka saka dariya cike da mugunta da kuma mungun nufin su.............







Sorry for typing error not editing.







Karki KARANTA min LITTAFI ba tare da kin biya ba, ki biya kuɗin ki kafin ki karanta, neme ni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki, 08147537180.






*MU SHIGA KITCHEN MATA*





*Dambun Kwai*


 Ingredients

Kwai
Nama
Curry
Maggi
Gishiri
Albsa
Tarugu
 

*procedure*

Zaki tafasa namanki da citta da albasa magggi gishiri inyatafasu saiki sauke kizuba shi aturmi kidakashi yayi kamar zakiyi dambun nama saiki juyeshi awurimaifadi saiki zuba jajjage aciki saiki fasa kwai biyar

Kiyanka albasa kixuba curry saiki zuba maggi da gishiri kadan saiki jujjuyashi saiki. Daura mai inyayizafi saikizuba naman dakikahada inyasoyu zakiji kamshi saiki sauke

*Butter yam*

Ingredients

Doya
Butter cokali8
Albasa1
Kwai:3
Curry cokali 1
Gishiri
Mai na suya.
METHOD

Ki fere doya ki yanka ki  dauraye ki dafa ta sai ki marmasata sosai ki zuba butter ki sa maggi gishiri curry sai ki lailayata dogaye kamar girman spring rols ki sata a furji ko gurin mai sanyi tayi awa daya sai ki kada kwai ki dora mai a wuta yayi safi saiki dinga tsoma doyarki. Acikin ruwan kwai kina sawa a mai kina soyawa idanyayi ruwan kasa sai a tsame.




*PINEAPPLE,MANGO, PAW_PAW AND BANANA JUICE*


1 Pineapple
2 Banana
3 paw paw
4 mango



Da farko zaki wanke mango dinki sai ki, fere bayan sa, sai ki zuba masa ruwa ki dora akan tukunya ya dahu, idan ya dahu sai ki saukeshi, sai ki yanka banana dinki tare da sauran kayan kanana, sai ki markad'asu, amma ki markad'a yadda zaiyi laushi, shima sai ki kawo wannan mango din shima ki markad'a bayan ki gama sai ki kawo kankara ki saka a ciki,zaki iya bud'a baki dashi






*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻










*(UMMU NASMAH CE)*
[10/10, 10:23 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 86 to 89*







__________✍🏻 Umma cike da ɓacin rai ta shigo cikin gidan nata, zama tayi ranta a ɓace Baba dake zaune ne ya dubeta tare da cewa.

" Lafiya kuwa Yamuram, naga kin shigo haka cikin ɓacin rai meke faruwa."

" Baban Hassan, wai yau ni, Yaya Dauda zai wulaƙanta akan dukiyata, har yana neman zagina dan kawai zan karɓi kayana bafa taimako naje nema wajen sa ba bare kuma ya wulaƙanta ni."

" Subabanallah, Daudan meya haɗaku haka."

" Baban Hassan, kasan dai akwai gado na a wajen sa, gidaje ma biyu na gada duka ya hallakar dasu ko kai ban sanarwa ba, nayi shuru nabar maganar a ciki na, ko yarana ban sanarwa ba, gudun fitina, sannan still cikin filayen da nake dasu biyar ya hallaka biyu suma na barsa nayi shuru, ɗaya kuma na sayar na bawa Hassan kuɗin sanda zai tafi India, wai shine yanzu naje nace ya sayar min da sauran guda biyun zan bawa Hassan zai saka cikin asibitin sa, shine zai ce min wai bazan ƙare akan yarana ba, kai kaji fa wata Maganar da bata da daɗi, yau ko faɗuwa nayi na mutu bashi da gadona yaran nawa dai sune zasu gajeni, na karɓo takaddun filaye na, gasu nan zan baka, gobe kuje da kai da Hassan da JALILA ka samin fili a kasuwa, JALILA kuma abinda yasa zakaje da ita saboda akwai mai bada maganin ciwon ƙafa a wajen sai ta karɓa, gashi kuma tana da mota kaga zaku sami sauƙin tafiya."

Numfashi Baba yaja yana duban Umma yace.

" Amma banji daɗin abinda kikayi ba, ai tsakanin ƴan uwa da ɗan uwa sai Allah, idan ya huce zuwa gobe ko jibi kije ki basa hkr, insha Allah gobe kuma zamuje a sai da filin."

Da to Umma ta amsa amma dai cikin ranta tana jin haushin Kawu Dauda, Baba ne yace.

" Ɗazu mun shiga MEETING an yanke shawarar cewa nine zan karɓi sarautar Bulama, sai dai gaskiya banso hakan ba, domin kuwa shi Bukkar mutum ne mai son SARAUTA tun sanda muke yara, mtsss, amma ba yanda na iya dana bar masa sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi."

" Haka ne tunda al'umma ne suka zaɓeka Allah yasa hakan shi yafi alkairi, amm kira min Hassan a wayar ka."

Ciro wayar Baba yayi tare da neman numbern Hassan, bayan ya ɗaga ne ya miƙawa Umma karɓa tayi tana cewa.

" Ganan takardun filin nan na karɓo gobe idan Allah ya kaimu kazo kuje da Baban ka kuje ku sai da filin, zakuje harda JALILA saboda zata karɓi maganin ƙafarta acan."

Shuru Hassan yayi sai kuma yace.

" Umma bazai yiwu aje dani ba, saboda akwai abubuwan da zanyi cikin asibitin gobe, Baban ma kawai idan yaje ya wadatar, saboda zamu tantance likitocin da zasu yi aiki a asibitin ne gobe."

" To shikenan babu damuwa Allah ya taimaka, akwai wasu kuɗi a hanuna dubu ɗari, sai kazo ka karɓesu ka fara dasu kafin muga abinda Allah zaiyi."

Cike da ƙaunar mahaifiyar tasa DOCTOR ya mata godiya, domin kuwa babu wanda zaiyi faɗi tashi domin ganin cigaban ka, sai iyayen ka."

Katse wayar yayi yana duban Falmata dake kwance a doguwar kujerar falon, yace.

" Hajiya ya akayi ne kikayi shuru kamar wanda ruwa ya cinyeta."

Ɗan murmushi Falmata tayi tana cewa.

" Kai dai bari wallahi bana jin daɗin marata ne, kuma nace maka muje asibiti har yanzu Kamin shuru, ga wasa da jinina yake min."

" Zamuje gobe idan Allah ya kaimu, bari naje na watsa ruwa zafi nake ji."

" Okay sai ka fito."

Tashi DOCTOR yayi ya haura sama ita kuwa Falmata shuru tayi tana jin Damuwar wasan da jini ke mata, ta rasa wa zai faɗa mata ma'anar hakan ga yawan ciwon mara da ada bata yinsa, rashin amsar tambayar ta ya sata sakin ajiyar zuciya ta tashi ta shige Kitchen.


*****************


Jummai kuwa yau magaruba a wajen bokan ta ya mata tsugunne take gaban sa tana sanar dashi dukkan abinda ke faruwa tare da ɗaurawa da.

" Sannan abinda na yanke shine zansa a tare a hanya, a kwace takaddun sannan aje a ɓoye su inda babu mai ganinsu har sai mun gama cika burin mu."

Dariya marar daɗin sauraro bokan yayi mai haɗe da amo yace.

" Idan kika saka akayi haka to Tabbas mun samu Hanyar da asirin mu zaiyi aiki akan ta, idan kinsa an ɗauke su, ki kirata kice tazo wajen ita ɗaya idan har tazo, kinga wannan kwalbar ki fasata ki juye ruwan a jikinta, da zarar ta koma gida, shikenan zata kwanta jinya zata dinga yin abu tamkar mahaukaciya, bazata ƙara sanin waye a kanta ba, bare ta nemi tona muku asiri, amma fa dole ki sata komawa gida da wuri idan ba haka ba, a wajen zata faɗi miki, ki riƙe wannan kwalbar da kyau, samun maganin karya wannan asirin yana da matukar wahala sannan zan turo aljanu kan ƴarta Ƙaramar nasan Bukkar yana son SARAUTA to zansa Fanna ta faɗi ta bada shedar cewa su Bukkar ne sukayi asiri suka ɓatar da da Mala sannan suka kwantar da Yamuram jinya, saboda na kawar musu da zargin da suke muku."

Cike da farin ciki da kuma mamaki Jummai tace

" Boka ina kasan wannan maganar sarautar da kuma sunan su."?

Tayi tambayar cike da mamaki, dariya ya bushe dashi sannan ya daki wani ruwa dake cikin ƙwarya a gabansa, take kuwa photo Bukkar ya bayyana da kuma Fanna, yana dariyar yace."

"Ki daina mamaki akan aiki na, domin kuwa ni ba karamin hatsabibi bane, karɓi kwalbar nan ki tashi ki tafi la'ananniya!!!".

Ya mata Maganar cikin tsawa yana haɗa fuskarsa, ai kuwa da sauri Jummai ta ajiye masa kuɗi tare da ɗaukar kwalbar ta fita ta baya baya."


**************

Da daddare Falmata na kwance jikin DOCTOR, ya dubeta tare da cewa.

" Kin san me zai faru tashi ki ɗauko hijabin ki, muje Asibitin Lawan na dubaki, saboda gobe akwai abubuwan da zanyi sosai mawuyacin abune na samu lokaci."

Tashi Falmata tayi tana murmushi ta amsa da to, sama ta haura bata juma ba kuma sai gata ta fito sanye da hijabi, tashi yayi ya kama hanunta suka fita adaidaita suka hau har cikin Asibiti, Saif ya samu yana zaune a OFFICE ɗin DOCTOR Lawan, dariya DOCTOR yayi yana miƙa masa hanu suka tafa yace.

" Kaji shegen gari yau kuma nan ka ɓullo."

Dariya shima SAIF yayi yace.

" Dafa gidan ka nayi niyyar zuwa sai kuma na fasa na gangaro nan, to ya akayi na ganka da Madam ko dai kunzo fara awu ne."

Dariya DOCTOR yayi yace.

" Kaji banza idan awu ne sai kuma muzo yanzu, ina DOCTOR Lawan ɗin."

Murmushi SAIF yayi yace wa Falmata.

" To Madam Hassan, ya kk, jiya ai na kira numbern ki bakiyi picking call ɗina ba, dama cewa zanyi ki dafa abinci mai daɗin gaske ina hanya."

Dariya Falmata tasa tace.

" Ai kuwa da kazo da ka samu abinci mai daɗi, banga kiran ba, sai daga baya, na kuma nemi layin naka sai yaƙi tafiya."

DOCTOR ne yace.

" Kai dallah Uban ƴan kwaɗayi, baka bani amsar tambaya ta ba, ina DOCTOR Lawan ɗin.?"

" Kai DOCTOR Lawan fa Tunda yaga na shigo ya fita ya barni da aikin da ba nawa ba, kaje kawai kayi abinda ya kawo ka, dan bana tunanin zai dawo yanzu."

Taɓe bakin sa DOCTOR yayi tare da ɗan sunkuyawa ya ajiye wata ƙaramar kwalba mai cike da ƙananun magani ya cewa Falmata muje ko tashi tayi tabi bayan sa tunda ya fita Saif yabi kwalbar daya ajiye da kallo, kasa hkr yayi ya saka hanu tare da ɗago kwalbar buɗewa yayi tare da zaro idanunsa a fili ya furta.

" Ƙwayoyin planing kardai ace waɗannan mutanen planing suke lallai kuwa da sun cika cikakkun marassa hankali"

Ajiyar zuciya ya sauƙe yana jinjina kansa, jumawa kaɗan kuwa sai DOCTOR ya shigo shi kaɗai cikin sauri zai ɗauki kwalbar daya ajiye bisa mamakin sa wayam babu ita inda ya ajiye, cike da mamaki ya dubi SAIF yace.

" SAIF na ajiye wata kwalba anan ban ganta ba, waye ya shigo."

Numfashi Saif ya sauƙe tare da ɗauko kwalbar yace.

" Gata nan, naga kwayar planing cike cikinta, amma amatsayin ka na cikakken likita, kasan illar da wannan kwayar da take ɗauke daahi ko, wallahi kun bani mamaki daga kai har Falmata, tsarin Iyali tun yanzu bazaku bari koda yara biyu bane ku haifa idan yaso ku fara planing ɗin, zan samu Falmata zan mata Magana naji meye hujjarta na neman cutar da kanta, domin kuwa planing kafin haihuwa kasan yana jawowa mahaifa ta samu matsala wanda ko da gaba ta samu ciki, lalacewa cikin zai dinga yi, idan akayi rashin dace ma, sai a rasa haihuwar gabaki ɗaya duk kasan da wannan amma ka bari takeyi, idan bazaka iya hanata ba, ni zan hanata na mata bayanin illolinsa tun kafin ya mata yawa."

A matuƙar fusace DOCTOR yace.

" Enough Malam, babu ruwan ka cikin wannan lamarin ban aika ka kaje ka faɗa mata domin kuwa bata san ina mata wannan planing ɗin, dan haka babu ruwan ka, haihuwa ce yanzu ban shirya mata, saboda nima ta kaina nake, ban gama ɗaukar buƙatun kaina ba tukunna bare kuma na ɗauki nata dana yara, yanzu haka Umma ce zata saida filin ta, domin na samu na ƙarisa abinda babu a cikin asibiti na, Taya kake tunanin zan tara iyali a haka, babu ruwan ka, ka kau da idonka cikin wannan lamarin."

Tashi tsaye DOCTOR SAIF yayi yana yiwa DOCTOR kallon mutum mai son kansa, yace.

" Bata san kana mata planing, saboda ba kai zaka cutu, kana ganin duk sanda ka shiryawa haihuwa koda ita bazata haihu ba, zaka auro wata matar tazo ta haifa maka yara, ita kuma Falmata ka cuceta, wallahi kaji tsoron Allah ka dakata haka kabar yarinyar nan ta haifi Wanda zasu mata addu'a koda bayan mutuwar tace, bakayi talaucin da har zai sa ka kasa riƙe gidan ka ba, wannan kawai son zuciyarka ne, ka gyara idan ba haka ba, wallahi zan sanar da Falmata cutarwar da kake mata."

"Hmmm!!! Jeka sanar da ita tunda burinka ka kenan ka shiga tsakanin mu, to jeka ka faɗa maka, duk yanda zaka so Falmata baya nane tunda ƴar uwata ce kuma matata, to kai meye case ɗinka a ciki, ka daina min haka bana son muzo muna samun saɓani da kai."

" Wannan ba soyayya kake mata ba, zalunci sunan sa, Tabbas nasan ƴar uwar kane kuma bazan shiga tsakanin ku ba, amma ka sani, duk randa ta gane kana bata fill, sai tafi kowa tsanarka, kashi ma sai ya fika darajar a idanunta."

" A'a ƙarya kake Falmata bazata taɓa tsanata ba, Soyayyar da take min dole zaisa tamin uzuri.''

Ya ƙarisa Maganar tare da ɗaukar kwalbar ya sata a aljihun sa ya fice, a zaune ya samu Falmata, yace ta tashi su tafi, koda suka koma gida a falo suka zauna, DOCTOR ya dubi Falmata tare da cewa.

" Mahaifarki ne ta samu matsala, shine yake kawo miki wannan ciwon marar da kuma wasa da jinin da yake miki."

Ya faɗi maganar ne kawai domin kuwa karya yake mata so kawai yake yayi amfani da wannan damar wajen bata ƙwayar planing ɗin ta hanyar sanja mata kwalba domin ta cigaba da amfani dashi kanta.

A matuƙar tsorace Falmata tace.

" Na shiga Uku, DOCTOR bazan haihu ba kenan."

" A'a ba haka nake nufi ba, zaki haihu nan da lokaci kaɗan, hanunsa yasa cikin aljihu ya ɗauko wannan kwalbar ya miƙa mata, wannan shine maganinki idan kika cigaba da amfani dashi, zaki sami sauƙi, kullum shabiyu na rana zaki na sha, karki kauce lokaci koda kuwa da minti biyar ne, zaki sami lafiya da yardar Allah."

Kaɗa kanta Falmata tayi cikin tashin hankali ta karɓi kwalbar..................





Kuyi hkr da wannan, sannan kwanan nan bana samun damar muku editing so sorry my lovely FAN'S.







Ki biya kuɗin ki kafin ki karanta karki karanta min LITTAFI baki biya ba, ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.







*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*







*(Ummu Nasmah ce)*
[10/12, 9:57 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 90 to 91*




_________✍🏻 Washe gari da sassafe DOCTOR ya fito cikin shirin sa ko karyawa bai tsaya yayi ba, saboda yana son yaje suyi sallama da Baba kafin ya wuce, Ɗakin Falmata ya leƙa tana kwance tana bacci abinta cikin kwanciyar hankali, murmushi kawai ya saki yaja mata ƙofar ya fita a binsa, koda yazo ƙofar gidan nasu motar Aunty JALILA tana nan alamun harta sammako cike da murmushi ya shiga cikin gidan, da Sallama, AUNTY JALILA itace ta amsa tana sakin murmushi, kusa da ita ya zauna yana cewa.

" AUNTY har kin ƙaraso, ina Junior na ganki ke kaɗai kaddai har yayi girman da zaki fara barinsa."?

Murmushi Aunty JALILA tayi tace.

" Na barsa a gidan su wajen yayunsa, tunda yana cin abinci kuma yana shan kunu ai kaga nima sai na huta."

Murmushi ya saki tare da cewa.

" Okay tafiyar zata miki daɗi kenan, ina kwana Aunty bamu gaisa ba muka tsaya zance."

" Lafiya Alhamdulillah, naji Umma tace zamu tafi tare da kaine, yanzu kuma Fanna tace min wai ka fasa zuwa meyasa.?"

Numfashi ya sauƙe yace.

" AUNTY, abubuwa sun min yawa, yanzu haka yau 10am ɗin nan zamu tantance ma'aikata, ga kuma tashin hankali na sauran kayan da ban samu na ƙarisa sawa a cikin asibitin ba, gashi on Monday za'a fara aiki cikin asibitin sauran kayan yanzu haka an kawo su suna hanu, kawai baza'a bani bane sai na basu kuɗin."

Murmushi Aunty JALILA ta saki tare da cewa.

" Yanzu nawa ne kuɗin da zaka kai musu, su baka kayan.?"

" Dubu ɗari takwas fa Aunty, shine ai duk na shiga cikin tashin hankali kuɗin suna da yawa sosai."

" Dubu ɗari takwas ne suke da yawa, kaga akwai kuɗin Ahmad ƙanin mai gidana daya tura min ajiyarsu ta account ɗina, so yanzu bari na ara maka sai ka kai musu su baka kayan, idan yaso aka sayar da Filin sai a bani na maida masa kuɗin sa, bani account numbern ka na maka transfer ɗin su yanzu."

Wani irin farin ciki DOCTOR yaji tare da jin ƙaunar Yar Uwar tasa ta ƙara ninkuwa a cikin zuciyarsa cike da farin ciki yake mata godiya, account numbern ya bata take kuwa ta masa transfer ɗin.

" AUNTY wai ina Umma ne kam ban ganta ba."?

" Ta shiga ɗakin Baba yanzu zasu fito."

Jinjina kansa yayi sannan suka ci-gaba da hira da Aunty JALILA har su Umma suka fito DOCTOR Baba ya gaishe.

" Baba an tashi lafiya."

Murmushi Baba ya saki yana karewa DOCTOR kallo, haka kawai yake jin jikinsa ya mutu da tafiyar wani irin sanyin jiki yake ji mai cike da kasala, kara duban DOCTOR yayi yace.

" Lafiya lau Hassan ya iyalin naka."

" Tana lafiya Baba, da tare zamu taho sai kuma bata jin daɗin abinda yasa bamu taho tare ba."

" Ayya Allah ya bata lafiya, mu zamu wuce sai Allah yayi dawowar mu lafiya, ke JALILA tashi mu tafi."

Umma ce tace.

" A dawo lafiya Allah ya tsare ya kaiku lafiya, JALILA ki masa bayanin duk yanda ƙafar ke damunki ko, kinga wannan cikin da kikayi kinsha wahalar ƙafar."

" Insha Allah Umma zan sanar masa."

A dawo lafiya DOCTOR ya musu har wajen mota ya rakasu sanda suka tafi sannan ya koma cikin gidan.

Sanda ya karya a wajen Umma sannan ya sanar da ita Aunty JALILA ta ranta masa kuɗi zaije yanzu ya basu kuɗin ya karɓo kayan.

Umma sosai itama taji daɗin yanda JALILA take ƙaunar ɗan uwan nata, sun ɗan juma da Umma Kafin ya tafi.




**************

Falmata kuwa koda ta tashi wayam ta gani babu DOCTOR hakan ya nuna mata cewa yayi sammako ya fice, wanka tayi sannan ta fito zata shiga Kitchen bisa mamakin ta har Ladiyo da tazo jiya ta gama breakfast ɗin tana famar mopping ɗin falon cike da farin ciki Falmata tace.

" Kai Ladiyo irin wannan aiki haka baki gajiya ne, kinyi breakfast kuma yanzu kizo kina mopping, kawo na miki mopping ɗin sai ki huta ko tunda kinyi girki."

Ta mata maganar cike da kyautatawa tare da tausayi, Ladiyo murmushi tayi cikin sanyin murya tace.

" A'a Aunty ki bari zanyi, ke dai ki huta, ni ai na saba da waɗannan ayyukan."

Ɗan dariya Falmata tayi tace.

" No Ladiyo ni bazan barki ba, aiki ya miki yawa, ba ƴar aiki na ɗauke ki ba, ƙanwata ta jini na ɗauke ki, kinga kuwa ai bazan bari wahala ya miki yawa ba, dan haka ki dinga min kallon yayarki da kuka fito uwa ɗaya uba ɗaya, ba matsayin wacce kike wa aiki ba, bani kije kiyi wanka ki kwanta ki samu nutsuwa sai ki fito kiyi breakfast nasan baki maida baccin asuba ba."

Miƙa mata abin mopping ɗin Ladiyo tayi, cike da jin daɗi ruwan idanunta suna ƙoƙarin zubar da Hawaye na jin daɗi tayi aiki a gida Uku, bata taɓa gamuwa da uwar ɗaki mai kirkin Aunty Falmata ba, duk da Aunty JALILA ta kwatanta mata adalci da kauna amma Tabbas Falmata tafi ƙaunar ta, Bedroom ɗin ta ta shige cike da jin daɗi, Falmata mopping ɗin tayi, sanda ta gama ta kira numbern mijin nata three miss call bai ɗaga ba, dole ta hkr ta barsa, breakfast ɗinta tayi sannan ta dawo tsakiyar falon ta cigaba da kallo sha biyu dai-dai ta ɗauko maganin ta cikin hanzari tasha, sannan suka ci-gaba da hirarsu da Ladiyo tamkar ƙawaye.




Shi kuwa DOCTOR tuni harya biya kuɗin kaya sun kawo masa tare da DOCTOR SAIF da waɗanda suka kawo kayan suka shigar dashi cikin store, sannan suka fara gabatar da interview ɗin, cike da nutsuwa.





Da misalin ƙarfe sha biyu na rana Umma tana zaune taji kiran wayar ta, ɗaga wayar tayi taga JALILA, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ɗaga kiran tana cewa.

" Ya akayi JALILA, har kun isa ne."

Wata Irin ƙatuwar murya marar daɗin ji Umma taji ya doki kunnen ta cikin tsawa.

" Ba JALILA bace keee tsohuwar banza!!!! Ƴarki da mijinki mun sace su suna wajen mu, idan kuma har kina so mu sake su kizo yanzu da dubu ɗari, cikin ƙauyen KUKAWA, kuma karki sanar da kowa bare kuma ɗan sanda idan har kika sanar musu to wallahi gawarsu zaki samu daga nan harki karaso muna da mai bibiyar ki idan kinzo ki kira wannan numbern."

Cike da tashin hankali Umma ta miƙe tsaye tana furta innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!! Cikin tashin hankali ta zari hijabin ta ta fice ba tare da kowa ya sani ba, da ƙyar ma ta samu motar Ɗan Birni wanda daga shi mashin kawai zata hau ya shigar da ita KUKAWA, tunda suka shiga motar take Allah Allah su isa, domin kuwa ita kaɗai tasan mungun tashin hankali da take ciki, ƙarfe ɗaya suka shiga ɗan Birni sannan ta hau mashin zuwa KUKAWA tashin hankali da take ciki har ya sata mantawa da ambaton Allah, basu yi wata doguwar tafiya ba, kuwa suka shiga cikin kukawa Umma tsayawa tayi gefe tare da kiran layin Jalila sai da ta kira sau biyar ba'ayi picking call ɗin ba, sosai Umma ta shiga cikin tashin hankali tsoronta ɗaya karsu cutar dasu, hanunta na ɓari ta ƙara kiran wayar, cikin Sa'a akayi picking ɗin cike da tsawa yace."

" Ki juya bayanki zaki ga wata farar mota ki biyota, a inda tayi parking wannan gidan zaki shiga."

Cike da hanzari Umma ta juya bayan ta, tashin motar ta gani, cikin sauri mai haɗe da gudu take dumfarar motar, yayin da drever yake sauri cike da mugunta ganin da Umma tayi zai ɓace mata ya sata binsa da gudu, wani madaidaicin layi ya shiga Itama ta bisa, a kofar wani ƙaramin gida yayi parking, ba tare da ya fito ba, cikin sauri Umma ta shige cikin gidan a tsakar

Please Login or Register in order to submit comment