Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duniya shikenan kuma sai ka manta da abokanka na yarinta."

Dariya HABEEB ya saki tare da cewa.

" Muka manta da juna dai, Saif kana sha'aninka fa naga sai wani gurun wuya kake, baka jin wahalar karatu fa Malam Saif."

Dariya Saif ya saki yace.

" Kai Malam ai wahalar karatu mu muke shanta kai kawai idan ana Sallah shuru ake ba'a magana Allah dai kawai ya mana jagora."

Cikin dariya DOCTOR yace.

" Kaikam ai ka mana tun farko ka ɗauki fannin business ɗinka."

Murmushi HABEEB ya saki tare d miƙawa DOCTOR takaddar vacancy yace.

" Congratulations zaku cike takaddar nan, insha Allah nan da One month jirgin ku zai ɗaga India idan kun cike sai ku maidawa Daddy dashi office zai saka hanu, Already dama shi gomna yasa nasa hanun."

Cikin murna da farin ciki, DOCTOR da Saif suke godiya, sosai sukaji daɗin abin alkairi da HABEEB ya musu, HABEEB ne yace.

" Hassan wai ina mutumiyar ne kam, ya kamata fa na ganta kafin na bar gidan nan."

DOCTOR bai kawo komai a ransa ba yace.

" Ta tafi islamiyya, amma may be kafin ka bar gidan nan zata dawo 1:00 zata kuma naga yanzu 12:30 ."

Murmushi HABEEB ya saki yace.

" Yarinyar tayi hundred pasent , ga hankali da nutsuwa uwa uba sakin fuska gata kuma kyakkyawa."

Saif dariya yayi tare da cewa.

" Wace yarinyar wai kake Magana ne."

Kallon DOCTOR HABEEB yayi yace.

" Sorry Hassan menene sunanta dan ban san sunan ba "

Dariya DOCTOR yayi yace.

" Falmata ake kiranta dashi amma dai Asalin sunan Fatuma."

Saif ne ya saki dariya mai sauti yace.

" Malam HABEEB ko dai kana ciki ne, naga kamar kana zancen tane da shauƙin Soyayya."


Dam!!!! Dam!!!! Dam!!! Dam!!!!! Ƙirjin DOCTOR ya buga, cike da tashin hankali yake duban HABEEB yaji amsar da zai bawa SAIF shi kuwa HABEEB murmushi ya saki tare da cewa.

" Bakaji dai mutuwar sarki a bakina ba, ƙanwar DOCTOR ai nima ƙanwata ne."

Wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya DOCTOR ya saki, yana godewa Allah cikin zuciyarsa, sun juma suna hira, har ƙarfe ɗaya sannan HABEEB ya tashi, tare suka shiga wajen Umma HABEEB ya sake gaishe ta DOCTOR ya sanar da ita alkairin da HABEEB ya musu na Vaccancy sosai Umma taji daɗi har sai da tayi hawaye, Aunty JALILA kuwa tafi kowa farin cikin samun cigaban ɗan uwanta.

Sun fito ƙofar gida HABEEB zai shiga mota shi da Saif zai sauƙesa a unguwar su sai shi kuma ya shige, sai ga Falmata da maji sun taho, HABEEB cike da tsokana yace.

" Hi!!! Ƴan mata."

Falmata da Maji tare suka juyo, murmushi Falmata ta saki tare da kamo hanun Maji suka taho wajen nasu, murmushi Falmata ta saki HABEEB ya cewa Maji.

" Baiwar da ajinki da girmanki kike haɗa hanya da wannan ƴar ƙauyen haba kin bada ƴan Birni."

Dariya Maji tasa tace.

" Cap amma lallai kaci bashi kuma dole sai mun rama, kana kallon ƙawara fine baby kake kiran ta da village girl, lallai taka zaƙewar tayi yawa amma ba komai akwai Ranar ƙin dillanci."

Dariya HABEEB yayi yace.

" Ai kuwa bazaku iya ramawa ba sai dai ku rame, ina fine baby ai sai dai village baby, Gaishe ni kafin raina ya ɓaci."

Gabaki ɗayan su dariya suka saka har DOCTOR Falmata kunkumi ta riƙe tace

" Naƙi na gaishe kam, ƙawata dan Allah dubi wannan baƙin baturen waini yake kira ƴar ƙauye, saboda kawai ya samu ya tafi ƙasar Cairo, to hir ɗinka malam ka dinga daidaita kalaman ka a kaina domin kana tsakiyar gata nane, idan muka so sai mu daka ka anan baka da mai tayaka."

Dariya HABEEB ya saki yace.

" To shikenan ba komai naji mai gata, samin numbern ki a nan zan wuce sauri nake."

Girgiza kanta Falmata tayi tace.

" No bazan baka ba, har sai YAYANA ya bani izini."

Dariya HABEEB yayi tare da duban DOCTOR yace.

" To yayan mu bata izini."

Dariya DOCTOR ya saki shima yace.

" My dear ƙanwata na baki izni."

Dariya Falmata ta saki sannan ta basa numbern motar HABEEB da Saif suka shiga, yaja suka tafi Falmata da Maji ma suka shige cikin gida.





**************


Kwana uku da HABEEB ya basu takaddar Vaccancy DOCTOR ya gama cike nasa da Sallama ya shiga ɗakin mahaifiyar tasa, suna zaune ita da Baba, gefen ƙafar Baba doctor ya zauna tare da miƙawa Baba takaddar yace.

" Gashi Baba na gama cikewa duka, yanzu saura a mayar dashi office ɗin Daddyn HABEEB."

Karɓa Baba yayi yace.

" Masha Allah Allah ya yi albarka, baza kaje kai ɗaya ba, dole tare zamu tafi sai na masa godiya, shima ai zaiji daɗi ai ko."

Umma ce tace.

" Gaskiya kam hanne ya kamata, saboda jin daɗin kyauta akace godiya, sai kuje tare, na sanar da Dauda ma Maganar tafiya karatun Hassan ɗin nace ya sai da min da gonata ɗaya, sai mu sami abinda zamu basa ya riƙe a hanunsa, tunda ance tafiyar tasu nan da wata ɗaya ne."

Baba cewa yayi.

" Masha Allah, naji daɗi sosai Yamuram kin ƙyauta wannan abinda kikayi nine ya kamata na masa shi a matsayina na mahaifinsa, ganin bani dashi yasa ke kika masa wallahi naji Allah ya miki albarka.


Shima kansa DOCTOR yaji daɗin hakan Tabbas yasan iyayensa suna sonsa Baba duban DOCTOR yayi yace.

" Ka tashi kaje gidan AJIRAM ka taho min da Fanna sannan ka sanar da ita alkairin daka samu."

Da to DOCTOR ya amsa sannan ya tashi ya tafi.



Kawu Dauda kuwa zaune yake gaban Jummai yana zayyano mata zancen da Umma ta masa.

" Kai!!!! Kai!!! Ina bazai yiwu ba!!!! Ni za'a rainawa hankali, ɗana bai tafi India ba kai da ka fita samun gadon a matsayin ka na namiji, naka Duk ya hallaka ya bar nata wallahi matar nan asiri ta maka dukiyarka ta kaɗe nata kuma yana nan, shine yanzu zata sayar ta tura ɗanta India, to kuwa wallahi dole nima sai ƊANA MUSA ya tafi India karatu, kuma da dukiyar tata."

Kawu Dauda ce mata yayi.

" A'a fa Jummai ba da dukiyar ta zata kaisa karatu ba, tace min baban Abokin Hassan ya basa tallafin karatu na gomnati tace wai idan ta sai da gonar zata basa abinda zai riƙe a hanunsa ne saura kuma zata bawa mijinta yayi jari."

" To karya take maka babu wani jarin da zata bawa mijinta yayi, ƙarya ne, da wannan kuɗin zata fitar da ɗanta karatu, ba dai gona ɗaya tal tace ka sayar ka bata kuɗin ba, na baka izni kaje ka sayar ka bata kuɗin, amma daga yanzu baza'a ƙara bata ko mai ba, daga yau sauran dukiyar ta ya dawo damu zamu sayar da su duka mu kai Musa karatu shima ƙasar waje, saura kuma muyi gini mu ƙaura mubar laka."

Da sauri kawu Dauda ya ɗago ya kalleta Tare da cewa.

" Taya haka zata kasance mu cinye dukiyar ta, kina tunanin zata yarda ta barmu ne."

" Dolen ta haƙura ta barmu ko tana so ko bata so zan iya aikata komai akan wannan dukiyar, dan haka ka barni kawai da ita........................."







Ki biya kuɗin kisha karatu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yafi miki sauƙi fiye da ki karanta abinda ba gumin ki ba, ki min magana ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki 08147537180.







*UMMU NASMAH ce*✍🏻
[9/20, 10:26 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 51 to 52*






___________✍🏻 " Jummai ina tsoron abinda zai shiga tsakanina da ƴar uwata, bana son mu samu saɓani da ita, tana kawar min da kai akan duk wani abinda zan mata na rashin daɗi, tana sona sosai, ya kamata mubar mata dukiyar ta haka dan Allah Jummai karmu kaita bango."

Wani irin mungun kallo Jummai take bin Kawu Dauda dashi kanta kawai ta kaɗa tare da ficewa ta bar gurin amma cikin zuciyarta ita kaɗai tasan mungun zaren da take saƙawa, Kawu Dauda tagumi ya rafka cike da damuwa cikin zuciyarsa yana jin baya son abunda Jummai take sakasa yake yiwa ƴar uwarsa sai dai yana kasa ƙin bin umarninta, ya daɗe cikin wannan nazarin Kafin daga baya ya kishingiɗe.



HABEEB a matuƙar gajiye ya shigo cikin Part ɗin Momy a kujera ya zube, babu kowa cikin falon sai Wasila, dubansa tayi ta ƙasan ido tace.

" Sannu da shigowa "

A daƙile HABEEB ya amsa mata da.

" yauwa sannu."

Murmushi Wasila ta saki tace.

" Wani abin yakan bani mamaki, yanda ɗan Adam yake gujewa mai sonsa da gaskiya, hmmm!!! Da zuciyarka tana da hangen nesa da kuma lissafi na Tabbata bazata kaucewa Soyayyata ba, domin kuwa ta sani cewa duk duniyar nan babu wanda ya kaini sonka sai dai kash Zuciyarka ta bijirewa alƙibilar ka ta gaskiya ta karkata hanyar da bata da ɓullewa, da zan baka shawara da nace ka umurci zuciyarka da tayi gaggawan dawowa zuwa ga masoyiyarta ta gaskiya domin kuwa hakan ne kawai samun salamar ka."

Duk Abinda take faɗa HABEEB yana sauraronta cike da mata kallon baki da hankali, sanda ta gama ya saki wata ƙaramar dariya kafin yace.

" Babu abin mamaki domin kuwa hakan tasha faruwa a duniya, babu amfanin tilastawa zuciya son wanda babu shi a cikinta domin kuwa shi so makaho ne, inda yake so nan kawai yake kallo, na godewa Allah da zuciyata bata zamo mai hangen taki zuciyar ba, saboda rayuwata da taki sam ba ɗaya bane bana fatan Ubangiji ya jarabceni da Auren mace Irin ki, hmmm!!! Shin kina tunanin bansan irin mugayen ayyukan da kike aikatawa bane, ko bansan ke fasiƙar ɓoye bace mai fuska biyu ki ɓoye sharrinki ki bayyana alkairin ki, to nasan komai a kanki kallon ki nake tar da waɗannan idanun nawa, dan haka ki daina alaƙanta ni da mace marar daraja da kamun kai irinki uwata gari nake nemawa ya'ya na, ba irin ki ba."

Wani irin bugawa zuciyar Wasila tayi, ta ya HABEEB yasan tana wannan harkar bayan a boye take yunsu, amma tsabar iya bariki na Wasila sai ta waske tare da cewa.

" Tabbas kayi namujin ƙoƙari wajen bibiyar lamurana, ko banza hakan ya nuna min cewa ka damu dani, na yadda ni karuwace, amma dai kana sane da cewa suma karuwan suna istibira'i a Aure su, dan haka ai kaga KARUWANCI na bai haramta Aure a tsakanin muba, Tabbas ina cikin duhu mai tsanani, Soyayyar kane kawai zata iya sauyani daga baƙi zuwa fari, cigaba da nuna min ƙiyayya kuma shi zaisa na ƙara dulmiya cikin wannan duhun da nake ciki, zan iya sauya wa na tuba na koma ga Ubangiji na muddun ka yadda da Soyayyata, ruwan kane ka ceto ni ko ka barni cikin duhu!!!."

Ta ƙarasa Maganar cikin sauti mai ƙarfi, murmushi HABEEB ya saki tare da cewa.

" Hmmm!!! Kaji wani kwaɗo wai mutum tsaftacacce ake neman dole sai ya haɗu da ƙazan ta, idan banda toshewar basira irin taki ta ina wannan zai yiwu, hmmm!!! Ai kin mankaro tunda har kika faɗa cikin hallaka Tabbas ke abin ƙyamace a cikin al'umma domin kuwa duk wata darajar ki ta zube kin gama kasa mutuncin ki a tire kin sayar maza da yawa sun kwasa waya sani ma ko kin kwaso wata cutar, taya ma kike tunanin cewa mutum mai kima da daraja zai ɗauki mace Irin ki sharar layi bular kowa, tabbas tuban da badan Allah ba ba tuba bane, shi ake kira da tuban muzuru, malama idan zaki tuba saboda Ubangiji ki tuba, karki tuba saboda wani bawansa ko dan buƙatar ki, ki cireni cikin jagorar tuban ki domin kuwa bani da hurumi a cikin sa, idan har nine wanda zanyi sanadin tuban ki, to kuwa Tabbas zaki mutu cikin baƙin duhun da ko tafin hanunki bazaki taɓa gani, ki tuba dan Allah hakan shine samun tsirarki."

Wasu hawaye ne masu ɗumin suka zubowa Wasila, cike da ɓacin rai tace.

" Tabbas na fahimci irin girmar ƙiyayyar da kake gwada min, amma kuma ka sani bazan taɓa iya cire Soyayyar ka a raina ba, dole sai ka aureni kota halin yaya."

Tana gama faɗin haka ta haura sama da gudu tana hawaye, Kusan karo ta kusa yi da Momy dake sauƙowa daga step ɗin, gefe Momy ta matsa mata tana cewa.

" Ke Wasila lafiyar ki kuwa kukan me kike haka."

Wasila bata kula Momy ba ta haura da gudu, ajiyar zuciya Momy ta sauƙe tare da sauƙowa tana bin HABEEB da kallon tuhuma, zama tayi a ɗaya daga cikin kujerun dake falon tare da jefawa HABEEB tambaya.

" Meya haɗaka da Wasila naga alamun yanzu duk sanda kuka haɗu sai ta wuni cikin damuwa, meyake faruwa a tsakanin ku."

Zaro ido HABEEB yayi tare da cewa.

" Ni Kuma Momy me zai haɗani da Wasila, nima fa yanzu haka na shigo na sameta tana wannan kukan, tambayar ta nake meya sameta shine fa ta haura sama da gudu ko amsa bata bani ba."

Taɓe bakinta Momy tayi tace.

" To sabon maƙaryaci ai kai ƙaryar ma baka iya ta ba, kaga baka taɓa min ƙarya ba, karka fara yau."

" Momy da gaske nake miki ki tambayeta mana kiji, ni Momy yunwa ina abinci na."

" Yana Part ɗinka an kai maka tun ɗazu."

" Okay Momy tunda kin kasa samawa Uncle Ɗalladi mata, ni na samo masa kuma Allah Momy macece ta gari wanda kowa zaiyi alfahari da ita idan ya sameta a matsayin mata."

Dariya Momy ta kwashe dashi tace.

" Ikon Allah, yau ga ɗa da samawa ubansa Mata, to Shikenan ina ne gidan su yarinyar, meye kuma sunanta, zan turasa yaje ya ganta idan ta masa shikenan sai muyi musu fatan alkairi."

Dariya HABEEB yayi ya tashi da gudu ya rungume Momy kiss ya manna mata a goshi ya koma ya zauna tare da faɗin.

" Thank so much Momy, Auntyn HASSAN maman su ɗaya sunanta JALILA."

" Okay yayi kyau Allah ya tabbatar da alkairi."

Da ameen HABEEB ya amsa tare da tashi ya fice zuwa Part ɗinsa, ajiyar zuciya Momy ta sauƙe bayan ficewar ɗannata, ta fuskanci Wasila son HABEEB take tun ba yau ba, sai dai a yanda ta fuskanci HABEEB kwatakwata babu Soyayyar Wasila cikin ransa, hmmm!!!! " Allah ka zaɓa musu alkairi a cikin lamarin su, idan akwai alkairi tsakanin su ka sawa HABEEB Soyayyar Wasila idan kuma babu Allah ka fitar mata da soyayyarsa a cikin ranta."

Ta ƙarasa addu'ar tana ɗaukar remote ta kunna sunnah tv.




***********

" DOCTOR na saura wata ɗaya ka tafi India, bana son ka tafi ba tare da gida ansan Soyayyar da ke tsakanin muba, kaga shekara bakwai zakayi ba lallai abarni nayi jiranka har shekara bakwai ba, gara kawai kafin ka tafi a ɗaura mana Aure ni zanyi jiran dawowarka da Auren ka a kaina."

" Hakane amma ki ɗan saurara kaɗan a gama cuku-cukun tafiyata tukunna idan mun gama insha Allah a cikin sati biyu sai mu taso da Maganar Auren namu."

" Shikenan Allah Ya kaimu."

" Ameen ki tashi ki shiga cikin gida, saboda kin juma cikin ɗakina."

Tashi Falmata tayi zata fice taji DOCTOR ya riƙo hanunta tare da cewa.

" Karki rabu dani komai tsanani komai wahala, dan Allah ki zauna dani, zan riƙe na riritaki tamkar ƙwai, koda wasa bazan taɓa barin hawaye su zuba daga cikin idanunki ba, dan Allah kimin alƙawarin zama har abada tare dani ina son mutuwa ce kawai zata shiga tsakanin mu."

Cikin sanyin Murya Falmata ba tare da ta juyo ba tace.

" Zan zauna dakai komai tsanani komai wahala, bazan taɓa guje maka ba, ko da mutuwa ce zanyi fatan ta ɗauke mu lokaci ɗaya, a sallace mu tare a binne mu a maƙwaftan juna, ga kabari na ga naka, kamin alƙawarin bazaka taɓa rabuwa dani ba, zakayi haƙuri da duk wani kuskuren da zan maka ina son ka kasance mutum mai uzuri a gareni, ni kuma nayi alƙawarin jure duk wata wahalar da zansha a dalilin ka."

" Na miki alƙawarin zan zauna dake komai tsanani komai wahala bazan taɓa guje miki ba, zan zauna dake har ƙarshen Rayuwata zan miki uzuri Kamar yadda zanyiwa kaina uzuri ina sonki Falmata ina sonki kece farin ciki na sannan kuma hasken idanuna, kece jagorata a rayuwa, i love You."

Ya furta tare da sake mata hanu yana sakin murmushi tare da tsantsar shauƙin Soyayya.

" Tabbas nayi dacen samun masoyi wanda zai kasance cikin haska min rayuwata, na Tabbata daga yau nayi bankwana da duk wani duhu a cikin rayuwata domin kuwa Ubangiji ya aiko min da haske mai haska min dukkan wasu lamurana , I love You too."


Ta ƙarasa maganar tana ficewa fuskar ta cike da annuri murmushi shima ya saki yana jin tamkar ya rungumota jikinsa, Falmata cikin gidan nasu ta shige, a tsakar gida ta samu BULAMA yana zaune, kujera ƴar tsugunne Falmata ta jawo ta zauna kusa da kakan nata.

" BULAMA iska kake shane ina kabar fadar taka.?"

Murmushi Bulama ya saki yana shafa kanta duk cikin jikokinsa yafi jin ƙaunar Falmata yarinya ce mai hankali da nutsuwa gashi kuma ko yaushe takan zuwa ta zauna dashi suyi fira.

" Fatuma yanzu zan fita, ina ɗan shan iska ne, ya naga sai murmushi kike, ko dai akwai labari ne.?"

" Eh BULAMA akwai labari, albishir nazo maka dashi, na sami mijin Aure ya kusa bayyana muku kansa kwanan insha Allah, mutumin kirki ne ɗan Asali wanda yasan darajar manya, Bulama dan Allah idan ya iso gareku ku karɓe sa ku basa aurena dan Allah Bulama kamin wannan gatan ka bani wanda nake so."

Murmushi BULAMA ya saki yace.

" Mai zai hana mu baki abinda kike so muddun ya cika sharuɗan daya kamata a basa Aure, karki damu idan har kin yadda da ɗabi'un sa."

" Na yadda da ɗabi'un sa, Bulama."

Murmushi Bulama yayi tare da tashi yana ƙoƙarin fita waje yace.

" To karki damu nama bashi ke."

Dariya Falmata ta saka cike da farin ciki ta shige Bedroom ɗin Aunty YANA.




***********


Bayan sati biyu


HABEEB da SAIF ne zaune a cikin motar HABEEB Saif duban HABEEB yayi yace.

" Yaushe zaku koma school ne, naga ka juma sosai a ƙasar nan.?"

" Mun koma ai tun Sati biyu da suka wuce nine kawai ban koma"

Cike da mamaki Saif yace.

" Meya hanaka komawa, bayan kasan yanzu ne first tearm da za'ayi karatu sosai."

" Mtsss!!! Koda na koma ba lallai na samu nutsuwar karatu ba, saboda ina da tarin damuwa a cikin raina, SAIF na kamu da Soyayya kuma na kasa furtawa wacce nake sonta soyayyata, a gefe guda kuma ga wata masifar da take neman shige min jikina, wallahi wata ƴar uwata ne, ƴar ƙanwar Momy na, ta addabeni wai ita lallai tana sona ni kuwa babu Soyayyar ta ko kaɗan a raina, amma wallahi taƙi bari na, na furta mata bana sonta, amma taƙi yadda ni wallahi tsorona kar wannan abin ya shiga tsakanin zumuncin iyayen mu."

Kaɗa kansa Saif yayi cike da jinjinawa lamarin kafin Saif yace.

" Tabbas dole ka rasa nutsuwar ka, amma ni shawarar da zan baka shine, na farko ita wannan ƴar uwar taka kayi ƙoƙarin ganin ka fahimtar da ita cikin lumana ku rabu lafiya da ita, karka mata da zafi ka bita da sanyi sai ku rabu lafiya, sannan ita wacce kake ya kamata ka cire shakka cikin ranka kaje ka furta mata Soyayyar ka, kar kayi sake wani ya riga ka shiga zuciyarta."

" Saif ba wata bace yarinyar da nake so, illa ƙanwar Hassan Falmata, wallahi Saif tun Sanda na fara ganin wannan yarinyar na saka a Raina na samu matar Aure amma ina son na fara neman izinin iyayenta kafin na furta mata Soyayyata hakan shine neman Auren daya halatta a cikin Muslunci, idan sun mata miji kuma zanyi ƙoƙarin ganin na haƙura, saboda haramunne neman Aure a cikin neman Aure, haka kuma idan tana da wanda take so nan ma zan bawa zuciyata hkr, domin kuwa bazan tilasta mata ta soni dole ba, na bakantawa zuciyarta dannawa zuciyar ta faranta, gara na barta da farin cikin ta."

" Ba'a mijin Aure ba, indai Falmata ne, kuma bana tunanin akwai wanda take tsayuwa dashi, na Tabbata Falmata zata soka domin kuwa kana da kyawawan ɗabi'un da za'a soka, daga nan babu inda zamu tsaya sai wajen BULAMA ka nemi izininsa sannan kaje ka nemi Soyayyar Falmata na Tabbata zaka samu......................"










Biya kuɗin ki Yar Uwa kafin ki karanta karki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, ki neme ni domin biyan kuɗin ki 08147537180








*UMMU NASMAH CE✍🏻*
[9/21, 1:33 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 53 to 54*






________✍🏻 " Saif wannan maganar taka ta ɗan bani ƙarfin gwiwwa amma sai dai zuciyata tana tsinkewa sai nake ji kamar Falmata tafi ƙarfi na, amma ba damuwa muje na kwatanta."

Murmushi SAIF ya. Saki tare da cewa.

" Muje Insha Allah kana tare da nasara Abokina, taya Falmata zata fi ƙarfin ka dame ta fika nasaba ko arziki, kaga ka daina shakku muje kawai angon Falmata."

Shima HABEEB dariya yasa yace.

" Harna zama angon kenan, ɗazu na kira numbern HASSAN baiyi picking ba."

" May be ko baya kusa da wayar ne, kasan fa shi mutum ne mai barin waya ma ya fice."

Jan motar HABEEB yayi suka nufi unguwar su DOCTOR, a ƙofar gidan sukayi parking, HABEEB Tunda ya tsaya a ƙofar gidan yaji zuciyarsa tana tsinkewa, amma ya daure duban Saif yayi tare da cewa.

" Saif na sake shawari, bai kamata mu fara zuwa ga iyayenta ba, har sai mun fara jin ra'ayin ta a kaina."

Girgiza Saif yayi yace.

" No HABEEB wajen iyayenta ya kamata ka fara zuwa domin shine matakin farko na neman Aure a Muslunci, su zasu baka izinin kaje ka nemi Soyayyar ta, daga nan idan kun daidaita fine."

" Shikenan muje to yanzu wajen Kakan nata zamuje kenan.?"

" Ehh wajen sa zamu may be ma yana cikin fadar sa."

Ya ƙarasa maganar suna nufar fadar, da Sallama suka shiga yau babu ko sai Baban DOCTOR, da kuma Mahaifin Falmata, murmushi saif ya saki cikin zuciyarsa yana cewa sunzo a dace, zama sukayi tare da kwasan gaisuwa BULAMA ne yace.

" SAIFUDDEEN yau kaine ka kawo min hira kenan."

Murmushi SAIF ya saki yace.

" Allah yaja da ranka BULAMA, Wannan Abokin nawa shiya kawo ni, baka ganesa ba ko."

Jinjina kansa Bulama yayi yace.

" Ƙwarai kuwa ban shaidasa ba."

" Shine wanda mahaifinsa ya bamu scholarship na karatu da zamu tafi ƙasar India."

Murmushi Baba yayi kasancewar shiya shaida HABEEB BULAMA cewa yayi.

" Masha Allah abu yayi kyau sannu samari Allah ya maka Albarka."

Murmushi shima HABEEB yayi tare da cewa.

" Ameen na gode.

Ya faɗi tare da yin shuru, Ganin HABEEB yayi shuru yasa Saif cewa.

" BULAMA abokina ya kasa Magana to bari dai na ari bakinsa na ci masa albasa"

Murmushin manya Bulama ya saki tare da cewa.

" Umhum Kai Habibu damo ne sarkin rashin magana ko, to kai kuma SAIFUDDEEN Aku sarkin Magana, ci masa albasar muji."

Gabaki ɗaya dariya fadar ta ɗauka har su Baba sai da sukayi dariya cikin dariyar Saif yace.

" Bulama HABEEB Falmata ya gani yake so, shine yace bazai fara tsayuwa da ita ba har sai ya nemi izini daga wajen ku."

Murmushi Bulama ya saki tare da cewa.

" Kaji ja'irar yarinya, ɗazun ta sanar dani cewa mijin da take so ta aura ya kusa zuwa wajena, har take roƙona da idan yazo na bashi Auren ta, ashe kaine."

Murmushi Baba ya saki tare da cewa.

" Masha Allah Habibu abu yayi kyau ai kai ba mutumin da za'a hana Auren Falmata bane idan har kun daidaita ka turo mana iyayenka kawai."

Wani murmushin farin ciki, HABEEB ya

Please Login or Register in order to submit comment