Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yaran ta Uku MALA shine babba sai BUKKAR ya biyo bayan sa sannan Fatuma wacce suke kira da YAGANA Mala da Bukkar zumunci ne mai ƙarfin gaske tsakanin su, mala yana da Mata mai Suna MARYAM wacce ake kira da YAMURAM suna da yara Huɗu ta farko sunanta JALILA sai HASSAN sannan A'ISHA wacce ake kira da AJIRAM sai kuma FATUMA autar Umma wacce ake kira da FANNA, a sashin Bukkar kuwa yana da matar sa ɗaya shima YAHANASU wacce suke kira da YANA suna da yara biyu rak a duniya BALARABE shine babba amma shi baya Maiduguri yana zaune ne cikin garin Abuja wajen ƙanwar Aunty YANA, sai kuma FATUMA wacce suke kira da Falmata, waɗannan Yan uwa suna bala'in son junansu, zumunci ne mai ƙarfi tsakanin su, wanda tsakanin MALA da BUKKAR babu wanda yake son ɓacin ran ɗan uwansa, haka ya kasance tsakanin ƴaƴan su, musamman HASSAN da Falmata wanda shaƙuwa mai ƙarfi take tsakanin su, wacce sam su basu taɓa zaton soyayyace a tsakaninsu, haka kuma tsakanin Hassan da JALILA suma shaƙuwace sosai tsakanin su, sam Jalila bata son ganin ɓacin ran Hassan komai taci sai ta ajiye masa.


" Umma!!! Umma!!! Umma dai kina ina"

Murmushi Aunty JALILA dake zaune gefe tana hura wutar murhu tayi tare da cewa.

" Oh Falmata irin wannan kira haka sai kace wacce ta ci miki bashi ta kasa biya."

Zama Falmata tayi tana tura baki tace.

" Ƙarar DOCTOR na kawo mata ta shiga tsakanin mu kuma Allah yau bazan yadda ba"

Ta ƙarasa maganar tana haɗa fuska, dariya sosai Aunty JALILA tasa tace

" Oh ni Jalila ina ganin sanabe, mutumin da bai riga ya zama likitan ba shine kike kiran sa Likita, hmmm su malam DOCTOR manya."

" Kai Aunty Jalila, ai dai kinsan yayana ya kusa zama likita tunda har ya fara karatun sa ni dai ina Umma na."

" Umma tana ɗaki sallah take amma ina ganin ta idar, ki shiga ki sameta."

" Aunty me kike dafa mana yunwa nake ji."

" To acici sarkin ci, shinkafa ce da wake, kuma babu rabonki a ciki."

" Lalala!!!! SECOND MOTHER karki fara ɗaukar wannan zunubin kin isa ma ki fara girkin da babu rabon mu, rabu da ita my dear na, dole a dafa a bamu muci."

Aunty JALILA taji muryar Hassan yana wannan Maganar dariya tasa tace.

" Okay wato ma zunubi zanyi, to shikenan na janye na yarda dole na baku kuci fitinannun ƴaƴan Umma."

Dariya Hassan ya sa tare da kallon Falmata yace.

" My dear ƙanwata, Ina kika shige tun ɗazu nake neman ki cikin gidan nan."

Tura baki Falmata tayi tace.

" Ni ba ruwana da kai karka sake kulani.?"

Zaro ido Hassan yayi tare da cewa.

" Na shiga Uku an fasa Aure na, laifin me kuma nayi haka my dear yaushe muka fara faɗa dake."

Dariya Aunty JALILA Tayi tace.

" Oh yau dai naji tsakanin ku, yanzu ma dai Umma ake jira a kai ƙarar ka, ina baza kunnen na naji laifin ka."

Muryar UMMA sukaji tana cewa.

" Ai kuwa gani ƴata zoki faɗa min, meya faru na ɗauka miki mataki yanzun nan."

Tahowa Falmata tayi kusa da Umma ta jingina jikin Umma tare da cewa.

" Umma na, kinga ranar asabar kina zaune a falon ki muma muna zaune DOCTOR ya min alƙawarin cewa zai kaini SUDEIS SUPER MARKET ya min siyayya shine ɗazu da safe dana masa magana yace min wai bashi da kuɗi nayi haƙuri."

Murmushi Umma tayi tare da cewa.

" Ai kuwa bai isa ba ya karya alƙawari, dan kuwa ina wajen yayi wannan alƙawarin, dan haka bai isa karyawa ba, kinga maza jeki ki shirya kizo ku tafi siyayyar."

Hassan cewa yayi " Umma banda kuɗi fa......."

Hanu Umma ta ɗaga masa tare da cewa.

" Maza jeki shirya ƴata ku tafi."

Tashi Falmata tayi da sauri ta fice tana yiwa DOCTOR gwalo, Umma duban sa tayi tace.

" Kaje cikin wadrob ɗina akwai 20k ka ɗauka kuje ka mata siyayyar, tunda ka mata alƙawari kasan dai haramun ne saɓa alƙawari ko? to daga yau karka sake yiwa wani alƙawarin abinda baka dashi, Saboda zaisa rai idan kuma bai samu ba, bazaiji daɗi ba, kaje ka shirya sai kazo ka kaita."

Dariya DOCTOR yayi tare da sunkuyawa ya mannawa Umma kiss a goshi yace.

" Thank UMMA na ina sonki."

Tare da shigewa cikin Bedroom ɗin Umma 20k ɗin ya ɗauka tare da ficewa yana cewa Aunty JALILA.

" Sai kuma asan tayi, ba dai ki jimu da my dear ƙanwata ba"

Dariya Aunty JALILA tayi tace.

" SABODA UMMA tayi belinka ba, da yanzu kuna nan kuna kwasar adashen tsiya."

" Oho dai sai kuma kiyi."

Ya ƙarasa maganar yana ficewa, Aunty JALILA duban Umma tayi tace.

" Umma, alaƙar Hassan da Falmata sai nake hango kamar akwai Soyayya a tsakanin su wanda su basu fahimci hakan ba, Umma ko ke kin hango abinda na hango kuwa.?"

Murmushi Umma tayi tare da kaɗa kai tace.

" Gaskiya ban hango ba, nafi dai hango Shaƙuwa ce ta ƴan uwan taka, to ma JALILA Hassan ya isa ya jawo Aure yanzu shi da bashi da komai da wani kuɗin zaiyi Aure ba sana'a yake dashi ba makaranta fa kawai yakeyi, ita kuwa Falmata ko yanzu za'a iya mata Aure ai kuwa kinga ko suna Soyayya Aure bazai yiwu ba saboda bashi da sana'a."

Numfashi Aunty JALILA ta sauƙe tare da furta.

" To hakane Allah ya sa mu dace."


Da ameen Umma ta amsa.

Cikin shirin ta tsaf Falmata ta fito da hijab ɗinta a tsaye ta hango DOCTOR yana tsaye ya zuba hanunsa a cikin aljihu murmushi ya saka tare da cewa.

" Wow ƙanwata tayi, kaga farar mace alkebbar mata, Kinga yanda kike haskawa kuwa tamkar farin wata, kinyi kyau my dear ƙanwata."

Dariya tasa tace DOCTOR na kaima kayi kyau sosai."


Murmushi yayi tare da cewa" Bismillah muje."


Fita sukayi suka tari adaidaita, sai sudees Super market, wani makeken shago ne mai cike da kayayyakin mure rayuwa, shiga ciki sukayi fannin takalma suka fara nufa, DOCTOR tsayuwa yayi a gefe tare da cewa.

" Bismillah kije ki zaɓi dukkan takalmin da ya miki."

Murmushi Falmata ta saka tare da nufar wajen takalman tana dubawa, hanunta ta saka zata ɗauka ɗauki wani toms wanda yayi mungun burgeta sosai ya mata kyau, yayi saurin riga ɗauka, da sauri itama ta juya taga waye ya rigata ɗauka, idanunsu ne suka sarƙe dana juna, dam ƙirjin sa ya buga, Falmata cewa tayi.


" Malam ya haka, takalmin nan fa na riga ganinsa akan me zaka rigani ɗauka.?"

Ta masa tambaya cike da jin haushi.

Murmushi ya saki tare da cewa.

" Akan bai dace da ƙafarki ba, da ƙafar budurwata ya dace dan haka ita ya kamata ta saka bake ba."

Haɗa fuska Falmata tayi cike da jin haushi tace.

" Saboda ƙafa yafi ƙafa kenan, kaga malam ka bani Takalmi na."

DOCTOR daya hango Falmata tsaye da wani ya juya baya, ji yayi zuciryasa ta tsinke da sauri ya nufosu cike da ɓacin rai.

" Bazan baki wannan takalmin ba, malama ki zaɓi wani."

Zatayi magana kenan taji muryar DOCTOR yana cewa.

" Ke da waye kike tsaye, hakane zaɓar takalmin."

Ya mata Maganar cike da tsawa, juyowa yayi yana sakin murmushi zaiyi Magana sai suka haɗa ido dashi, cike da mamaki DOCTOR yace.

" HABEEB wai dama kaine, yaushe ka shigo ƙasar, mutanen Cairo."

Murmushi HABEEB ya saki tare da cewa.

" Hassan dama tare kuke tafe da wannan ƴar ƙauyen, na kwana biyu da dawowa mun sami hutu, ya dai har yanzu kana UNIMAID ɗin ne."

Dariya DOCTOR yayi tare da cewa.

" Eh gamu nan muna ta lallaɓa karatun a haka, ƙanwar tawa kake kira da ƴar ƙauye, to kuwa kaci bashi."

Falmata cije leɓenta kawai tayi, HABEEB kuwa cewa DOCTOR yayi.

" Ina labarin SAIF."?

" Saif yana nan, yaje school yau yana da lectures."

" Ayya, kasan me zai faru, zan yiwa Daddy na Magana, naga akwai Vaccancy da governor ya basa na Mutum huɗu, wanda gomnati ta ɗauki nauyin karatun su, zuwa India, naga kai Science ka karanta, so zaifi dacewa ace a India kayi karatun ka, insha Allah zan karɓi guda biyu a hanun Daddy na baku kaida saif, insha Allah a India zakuyi karatu."

Wani irin farin ciki DOCTOR yaji tare da rungume HABEEB yana cewa.

" Alhamdulillah!!! HABEEB bansan ta yaya zan fara gode maka, amma dai Tabbas kamin alkairin da bazan taɓa mantawa ba, na gode sosai."

Falmata ma murmushi tayi tace.

" Ashe dai mutumin kirki ne kai harna fara maka kallon mutum mai son kanka."

Dariya HABEEB yayi yace.

" Oh kallon da kike min kenan akan wannan takalmi to riƙe kayanki ƴar ƙauye."

Ya miƙa mata yana sakin murmushi.............






0006064512 Rashida Usman Jaiz Bank, 200 ko mtn card ta Wannan numbern 08147537180 sai ki turo SHAIDAR BIYA ta ita numbern, yafi miki sauƙi da a baki wanda ba guminki ba, ki karanta.




*ALƘALAMIN UMMU NASMAH CE ✍🏻*
[9/17, 4:01 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 43 to 44*





_________✍🏻 " to fa ni SALAMATU yau ina jin wata rashin kunya, yaushe ka fara soyayya ban sani ba HABEEB har zaka buɗe wannan idanunka na yaran zamani kana cemin ka faɗa Soyayya Mister lover's.?"

Dariya ya saka yana kallon action ɗin Wasila ta ƙasan idon yace.

" MOMY ke dai ki bari sai mun daidaita tukunna zaki san waye ce, meye a ciki danna sanar da Momy na, ta kusa samun surka, kuma gashi Momy yarinyar macece mai kamun kai wacce tasan mutuncin kanta, ba irin matan nan bane masu maƙalewa maza su lallai sai an sosu yarinya ce mai aji."

Shuru Momy tayi jikinta yayi sanyi wannan maganar da HABEEB yayi babu shakka tasan da Wasila yake, duban sa tayi tare da cewa.

" Naji to tashi maza ka barmin falo na, kayi tafiyar ka ina buƙatar sakewa nida yarana."

Itama Wasila sosai jikinta yayi sanyi, HABEEB yana dariya domin kuwa ya fuskanci Momy ta gane da Wasila yake, ya tashi tare da cewa.

" Shikenan Momy na tafi tunda kin koreni a kawo min abinci na."

MOMY cewa tayi.

" Eh jeka na kore kan"

ajiyar zuciya Wasila ta sake, tana bin HABEEB da kallo harya fice, Momy duban Hajara da take tsume tayi tace.

" Kinga ki saki fuskarki zaifi miki sauƙi, baiyi niyya bane daya saya miki, SUPER MARKET ko anjuma ɗanjuma drever zai kaiki ki sayi takalmin, ki tashi ki ɗauki abincin sa ki kai masa."

Kafin Hajara tayi Magana wasila ta rigata da cewa.

" Ki bari Momy ni zan kai masa."

Cike da tausayin ta Momy tace " shikenan ki ɗauka yana Kitchen."

Tashi Wasila tayi, ta shiga Kitchen ta ɗauki abincin ta nufi Part ɗin HABEEB da sallama ta shiga amsawa yayi fuskarsa a sake babu yabo babu fallasa, abincin ta ajiye masa tare da zama a kujerar da take Fuskantar sa, fuskarsa ɗauke da murmushi duk da ransa baya son zaman nata a ɓangaren nasa amma sam bai nuna mata a fuskarsa ba, Saboda yasan babu kyau wulaƙanta ɗan Adam, yace.

" Hajiya Wasila akwai labari kenan naga kin zauna."

Murmushi Wasila ta saki tare da cewa.

" Babu wani labari hira kawai zan tayaka."

Still murmushi ya sake tare da cewa.

" Ai kuwa kin ƙyauta sai dai kijeki , nima ina shigowa Part ɗin momyn idan na gama, yaushe DATTI zaizo ya ɗauke kine."

Murmushi itama Wasila tayi tare da cewa.

" Ka gaji da gani nane kake tambayar sanda za'a zo a ɗauke ni."

Zaro ido HABEEB yayi yace.

" Ni na gaji da ganinki me kika tare min daga tambaya sai cibi ya zama ƙari to Allah ya baki hkr Hajiya."

" Idan ban tare maka ba na tarewa zuciyarka bisa ga dukkan alamu."

" Zuciyata kuma, meye haɗinki da zuciyata da har zaki tare mata wani abu.?"

Ya jefa mata tambayar tamkar bai san me take nufi ba, amsa ta basa da cewa.

" Saboda ina sonka, nasan ka fuskanci hakan amma kayi burus dani ka maidani mahaukaciya tamkar baka san me nake nufi ba, nasan ko karen gidan nan yasan ina sonka bare kaikuma da nake yiwa Soyayyar."

" Soyayya kuma Wasila, wacce irin Soyayya kuma akwai wata Soyayya ce da take tsakanina dake bayan ta ƴan uwan taka.?"

Ɗago kanta tayi ta zuba masa Ido na second biyu kafin tace.

" Soyayya wacce ka sani ta Aure ita nake maka ba Soyayyar ƴan uwan taka ba, Ya HABEEB ina sonka zuciyata ta kamu da Soyayyar ka mai tsanani meyasa ka kasa fuskantar hakan."

Numfashi HABEEB ya sauƙe mai nauyi cike da tausayin ta yace.

" Tabbas duk mutumin daya nuna maka Soyayya, mutum ne mai daraja a wajen ka, domin kuwa komai tsiya yafi maƙiyinka, na gode da Soyayyar da kike mini, sai dai kash ita Soyayya bata taɓa daɗi idan bata kasance a zuciyoyin mutum biyu ba, dole zuciyar mutum ɗaya zata wahala, kamar dai yanda ya kasance tsakanin zuciyata da taki, ke akwai Soyayya ta a zuciyar ki yayin da ni kuma tawa zuciyar sam babu Soyayyar ki, na riga da na bawa wata soyayyata a yau ɗin nan sorry to say kinyi let, ki rarrashi Zuciyarki ki bata hkr insha Allah zaki sami wanda ya fini, na faɗa miki hakane domin karmu wahalar da kanmu."

A firgice Wasila ta miƙe tsaye tare da cewa.

" Nayi haƙuri!!!! Nayi haƙuri fa kace, bazan iya haƙura da Soyayyar ka ba Saboda zuciyata ta kamu da ciwon Soyayyar ka, ta ya kake tunanin cire Soyayyar ka a raina abune mai sauƙi, sam bazan iya ba, ina sonka kuma ya zama dole ka soni."

Ta ƙarasa maganar cike da tsawa hankalinta a matuƙar tashe, shima HABEEB tashi yayi yace.

" Wannan ba maganar tashin hankali bane na sanar dake ne iya gaskiya ta, da take cikin Raina gudun karna yaudari zuciyarki dalilin kenan da yasa na sanar dake gaskiya, Hausawa sukace idan so cuta ne haƙuri ma magani ne, kamar yadda kikace, bazaki iya daina sona ba, haka nima zuciyata bazata iya sonki ba, kinga kuwa Soyayya bazata taɓa yiwuwa ba tsakanin so da rashin so, dole sai ya kasance akwai so da Soyayya, ki rarrashi Zuciyarki ki cire Soyayyata a ranki."

" Wannan karin magana ce kawai ta Hausawa ina sonka ina sonka ina sonka kuma bazan taɓa daina sonka ba."

" Hmmm shikenan ni dai na faɗa miki gaskiya ta wannan ruwan kine ki yarda ko karki yarda."

Hawaye ne suka gangaro daga idonta cikin shashsheƙar kuka tace.

" Wallahi dole sai ka soni dole ka Aure ni, kota halin yayane."

Murmushi HABEEB ya saki tare da cewa.

" Okay to shikenan ki gwada mu gani ko zan aureki dole, fice ki barmin Part ɗina kafin na tashi na miki abinda bazaki ji daɗin sa ba, tunda na fahimci Zuciyarki shashashar zuciyace."

" Ba sai ka kore ni ba, da ƙafata zan tafi amma ka sani dole ka Aure ni, bazan taɓa barin wata mace ta raɓeka ba, ka san wannan duk inda kaje dole ka dawo gareni."

Tana gama faɗin haka ta juya ta fice da gudu tana sakin kuka, tsuka HABEEB yaja tare da furta " shashasha marar fahimta, ana soyayya dole ne mtsss."

Wasila da gudu ta haura sama tana kuka a lokacin Momy bata nan ta yi Bedroom ɗinta, bed ta faɗa tare da sakin kuka, Hajara duban ta tayi tare da cewa.

" Lafiya Wasila kika shigo da kuka keda waye haka.?"

" Hajara Ɗan uwanki ya furta min cewa baya sona na cire Soyayyar sa a cikin raina."

" Kai haba Wasila to sai me, dan baya SONKI shi kaɗai ne namiji a duniya, ki ciresa kawai a ranki."

Girgiza kanta Wasila tayi tare da furta.

" Hajara baki san menene zafin soyayya ba, shiyasa kike faɗin haka amma ni kaɗai nasan raɗaɗin nake ji a cikin zuciyata, bazan iya cire Soyayyar sa a cikin zuciyata ba."

" Cap idan haka Soyayya take Allah ya shiga tsakanina da ita, to Allah ya miki mafita."

Wasila batace komai ba, ta cigaba da kukanta.



Da daddare kowa ya hallara a daining suna cin abinci har Daddy sai dai babu Wasila cikin su, tace ta ƙoshi, HABEEB Daddy ya duba tare da cewa

" Daddy, akwai wasu abokaina waɗanda mukayi primary school dasu, Kuma ina tunanin baka manta su ba, HASSAN MALA BULAMA wanda yake unguwar BULUNKUTU TSALLAKE, da SAIFUDDEEN KHALID."

Shuru Daddy yayi na ɗan wani lokaci kafin can yace.

" Okay na tuna su, ai harna manta dasu my son."

" Eh Daddy dama wata alfarma nake nema musu a wajen ka, sunyi karatu ne a fannin Science shine nace mai zai hana a cikin Free education da gomnati ta ba na zuwa Indiya karatu ka basu tunda ɓangaren likitanci suke karanta, kaga India suna da good Education na ɓangaren likitanci, sannan zasufi samun Salary mai kyau wanda zasu taimaki kansa harma da ƴan uwan su."

Murmushi mai sauti Daddy ya saki cikin so da ƙaunar ɗannasa yace.

" Ka wuce neman alfarma a wajena my son, kuma wannan taimako da za'a musu, basu kaɗai zamu taimaka ba har al'ummar da zasu duba lafiyar su bayan sun kammala karatun, gobe da safe kazo office ka karɓi Vaccancy ka kai musu Allah yayiwa karatun da zasuyi albarka."

Dariya HABEEB yayi tare da yiwa Daddy godiya Momy ma sosai taji daɗin alkairi da ɗanta yayi, Tabbas ta samu ɗa na gari, mai taimakon al'umma, lallai tayi dacen haihuwa domin kuwa samun mutum irin HABEEB a yanzu abune mai matukar wahala fatanta Allah ya ƙarawa rayuwarsa albarka.







Kuyi hkr dan karku ce kwana biyun nan ina muku typing kaɗan wallahi ina cikin hidima ne shiyasa kumin uzuri dan Allah🤲🏻




Idan kina buƙatar wannan littafin ki nemeni ta wannan numbern 08147537180 yafi sauƙi fiye da ki karanta abinda ba gumin ki ba.





*ALƘALAMIN UMMU NASMAH CE*✍🏻
[9/17, 4:01 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 41 to 42*




Wannan shafin sadaukarwa ne gare ku DOCTOR HASSAN FAN'S ina yinku irin sosai ɗin nan❤️🤝🏻



________✍🏻 Girgiza kanta Falmata tayi tare da cewa.

" A'a bazan karɓa ba, na bar maka ka kaiwa budurwar taka, ni zan zaɓi wani."

Cike da Zolaya HABEEB yace mata

" Wannan takalmin ya yiwa budurwa ta kaɗan 38 size ne fa ita kuma budurwata 45 size take sawa kinga kuwa ai wannan ya mata kaɗan."

Ya ƙarasa maganar yana dariya Falmata zaro ido tayi tare da cewa.

" 45 size kace, Wannan wacce Irin ƙaface da, sai kace wacce ta haɗa dangi da Aljanu, amma dai basamudiya ce ko."


Ba HABEEB harta DOCTOR sai da ya saka dariya yace.

" Kinga my dear ƙanwata karɓi takalmin ki, ki ƙyale HABEEB, tsokanar ki yake, idan kika biyewa HABEEB sai mu wuni a nan."

Dariya Falmata tayi tare da cewa.

" Oh wato duk wannan ɓata min lokacin da kayi Zolaya ta kake, to ai kuwa dole sai ka sayi wannan takalmin kuma ya kasance shine kyautar farko da zaka yiwa budurwar ka, ka samu budurwa mai size 38 domin kuwa sunfi more Takalmi sannan anfi samun daidan su da wuri."

Murmushi HABEEB yayi tare da kashe mata ido yace.

" Insha Allah kuwa wannan takalmi shine zai kasance kyautar farko da zan yiwa budurwa ta, duban DOCTOR yayi yace, zan wuce amma insha Allah zuwa gobe zan nemeka."

Musabaha sukayi da DOCTOR yana masa godiya HABEEB ta tafi tare da ɗagawa Falmata hanu, DOCTOR cewa yayi.

" Kiyi sauri ki ɗauki abinda zaki ɗauka time na tafiya, juyawa Falmata tayi ta cigaba da ɗaukar abinda ya mata sun kai wajen 4 hrs kafin suka nufo wajen payment, Doctor kayan ya miƙa musu, lissafi sukayi 50k DOCTOR cike da razana ya ɗago kansa Domin kuwa 20k kawai hanunsa muryar mutumin sukaji yace,

" Kaine Hassan Mala WANBAI."

Ɗaga masa kai DOCTOR yayi alamun shine.

" Okay to ba sai kun biya kuɗin ba, an biya wani mutum mai suna HABEEB ya biya muku, 70k mune ma zamu baku canji yanzu."

Ajiyar zuciya DOCTOR ya saki tare da yiwa Allah godiya, daya tseratar dashi, Tabbas HABEEB yayi belinsa yau, a leda suka zuba musu kayan tare da bawa DOCTOR canjin su 20k, fita sukayi suka tare a daidaita suka hau sunyi nisa da tafiya yaji muryar Falmata tana cewa.

" Wannan abokin naka yana kirki SOSAI na juma banga mutum mai kirki irinsa ba."

Murmushi DOCTOR ya saki tare da cewa.

" Kaɗan kenan daga cikin kirki Irin na HABEEB mutum ne shi mai sowa ɗan uwansa abinda ya sowa kansa, sannan shi ɗan masu akwai ne Mahaifinsa shine mistern sadarwa na ƙasa gabaki ɗaya wato Nigeria, ALHAJI MAHMUD BAMAI shiyasa kika ga yana wasa da kuɗi yanda ransa yake so, sai dai ta inda yake burgeni ko kaɗan kuɗin mahaifinsa basu damesa ba, shi dai burinsa ya tsaya da ƙafafunsa ma'ana ya nemi na kansa, yasha faɗa mana wannan maganar tun muna primary school."

Murmushi Falmata ta saki tare da cewa.

" Tabbas wannan abokine na gari, shiyasa Hausawa sukace, yin aboki da mai ture yana daɗi ko ba komai kayi ƙamshi Tabbas duk macen da ta samesa a matsayin mijin Aure ta gama dacewa."

Murmushi kawai DOCTOR yayi tare da miƙawa Falmata 20k ɗin yace.

" Gashi ki riƙe sanjin."

Girgiza kanta Falmata tayi tare da cewa.

" A'a ka rike domin kuwa ka fini buƙatar kuɗi, ni iya wannan kayan ma sun isheni."

DOCTOR zaiyi Magana Falmata ta tare sa tare da cewa.

" Dan Allah karkace komai, ka riƙe su kawai."

Shuru DOCTOR yayi tare da mayar da kuɗin aljihun sa, koda suka isa da gudu Falmata ta shige sashin su, ɗakin Hajja ta faɗa BULAMA na zaune ta shigo, Hajja hararar ta tayi tare da cewa.

" To gidan rashin nutsuwa, ɗakin arna kika shigo da bazaki mana Sallama ba."

Ta ƙarasa maganar cikin faɗa Falmata tura baki tayi tare da zuwa kusa da BULAMA ta zauna tace.

" BULAMA kana jin matarka ko, to kace ta fita harkata mena mata haka kawai zata min tsawa dan kawai na shigo ɗakin ta."

Dariya BULAMA yayi yace.

" To Hajja kinji dai abinda kishiyar ki ke cewa, to kibi a hankali domin kuwa nafi sonta fiye dake, dan haka taka a hankali."

Gabaki ɗaya dariya suka saka har Hajja, Falmata ledar hanunta ta miƙawa Hajja tace.

" Kinga abinda yayana ya saya min a SUDEIS SUPER MARKET."

Taɓe bakinta Hajja tayi tace.

" Ikon Allah su masu yaya manya, sunyi kyau Allah ya masa albarka."

Da ameen BULAMA ya amsa tare da cewa sai kije ki nunawa uwarki ko."

To Falmata tace tare da ɗaukar ledar ta shige ɗakin Aunty YANA, zama tayi kusa da ita tare da cewa.

" Mama kinga kayan da DOCTOR ya saya min a SUPER MARKET."

Aunty YANA batayi magana ba Falmata taji muryar DOCTOR dake kwance a ƙaramin gadon Aunty YANA yace.

" HABEEB dai ya saya miki ba dai DOCTOR ba."

Ya ƙarasa maganar yana sakin murmushi, Falmata cike da mamakin yaushe ya shigo take kallon sa, Aunty YANA ce tace.

" Yau dama HABEEB yana gari, shine bai shigo mana ba, kasan rabona dashi tun kuna primary school, sai kwanaki can na haɗu dashi a Ibrahim communication, amma haɗuwar tayi Shekara shine ma yake sanar dani cewa zai tafi Cairo KARATU, yace insha Allah yana dawowa zaizo mana."

Dariya DOCTOR yayi yace.

" Yace zai shigo gobe akwai alƙawarin ma da yamin amma dai sai yazo goben idan abun ya tabbata sai kuji."

Da Allah ya KAIMU Aunty YANA tace, taɗin duniya suka dinga yi, dake DOCTOR haka yake da Aunty YANA tamkar Ɗan da ta haifa.


Shi kuwa HABEEB a matuƙar gajiye ya isa cikin gidan nasu a main Falo ya zauna tare da cewa.

" Wash Momy na gaji sosai."

Murmushi wata kyakkyawar mata fara sol mai fason goshi, tayi tare da cewa.

" Oh HABEEB sarkin raki, yanzu nan

Please Login or Register in order to submit comment