Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hayaniya a woman word, har zai shige sai kuma ya fasa ya nufi word ɗin jin hayaniyar tayi yawa, koda ya shiga turus ya tsaya yana kallon ikon Allah, domin kuwa wata ƙaramar yarinya ce ta gagari kusan nurse Biyar, sai famar magana yarinyar take da ganinta kaga cikakkiyar ƴar *ƘAUYE* ko da yanda kake jin tsantsar zallar ruwan Barbarci a bakinta babu mis ko kaɗan da Hausa haka kuma yanayin jikinta ya nuna daga ƙauye ta fito duk da babu wata ƙazanta a jikinta.

" Na rantse da Allah babu wanda ya isa a cikin ku ya min allura azzaluman banza kawai baku da aiki sai cin zalin Mutane kunsa farin kaya kamar wasu Gawawwaki sai famar allure mutane kuke saboda zalunci to wallahi nikam uwar kuturu ma tayi kaɗan ballan tana ta makaho babu ubanda ya isa ya min allura a cikin ina ji ina gani da idanuna."


Haushi da takaici ne ya cika wani tsohu dake zaune gefe da sandar sa a hanu cikin jin haushi yace.

" Ke dai *AI'SA* kin shiga Uku da wannan shegen bakin naki da baya mutuwa, baki da lafiyar ma bakin ki bai mutu ba, to ko kiyiwa mutane shuru ko na tashi naci ubanki da wannan sandar kin dai san halina yau naga tsiya a wajen yarinya, na kawo ki domin na sama miki lafiya shine xaki zo nan ɗin ma ki sai da mana da hali kina min iya shege to baki isa ba dole sai anyi wannan allurar ko zaki mutu."


Nurse ɗin gabaki ɗayan su sun jiƙe da zufa tsabar uwar kokuwar da suke da yarinyar da aka kira *AI'SA* ita kuwa bakinta yaƙi mutuwa wannan dattijon yana dasa aya ta ɗaura da mayar masa da martani.

" Ni dai wallahi *BA'KURA* ban shiga Uku ba tunda ban mutu ba nida bakina ina ruwan ka dani, Ni nace ka kawo ni wajen waɗannan azzaluman ina cewa kawai kayi magani zaka saya min a cikin garin mu koma, to wallahi Allah ko zaka kasheni bazanyi wannan allurar ba, yanzu fisabilillah shikenan sai na tsaya ina kallo a soke ni da wannan kifiyar wallahi bazan yadda ba babu ruwan ka da ciwo na ka ƙyaleni idan mutuwa ma zanyi na mutu, ai dai ba nice ƴarka ba, ya'yan ka sunan kana kallon su ni sai kaga dama kamin addu'a, eheee."

Ta ƙarasa maganar tana murguɗa masa baki DOCTOR dake tsaye ya harɗe hanu yana kallon dramar ce ya sashi murmushi mai sauti, " Lallai wannan yarinyar ba dai daru ba, sai famar magana take tsau-tsau bakinta ko gajiya bayayi" cikin zuciyarsa yake wannan zancen ƙarasawa yayi ya taka har cikin word ɗin tare da cewa nurse ɗin dake riƙe da *AI'SA* ɗin.

" Ku saketa wannan ai ta fiku lafiya ma, yanda ta gagare ku."

Sakinta sukayi Nurse Khadija tana cewa.

" DOCTOR wallahi bata da lafiya koda sukazo sanda aka musu gwajin maleria da typort kuma duk tana dasu a jikinta yanzun ma allurar typort ɗin zamu mata shine duk taƙi sakin jikinta sai famar dambe take damu."

Carap AI'SA tayi tace.

" Kaji masharranta, meye kuma materia, to aniyar ku ta biku babu ƙatuwar matar da ta isa ta min wannan allurar komai girman ta koda kuwa ta kai bishiyar kuka girma ba..........."


Tsawa DOCTOR HASSAN ya daka mata tare da cewa.

" Shut'up, karna ƙara jin maganar ki cikin word ɗin nan, shegen Surutu cau-cau ko gajiya bakya yi" kallon BA'KURA DOCTOR yayi tare da cewa.


" Baba Amma dai wannan yarinyar tana da matsalar aljanu ko, ko kuma ta taɓa samun matsalar ƙwaƙwalwa ne, naga kamar babu saiti a kanta."

" Likita Babu aljanu a jikinta ko taɓin ƙwaƙwalwa, kawai tsabar sheɗanci ne da kuma rashin kunya ya mata yawa, yanzu haka da kaji tana wannan bakin wallahi a hakan ma bata da lafiya ne da abinda zatayi sai yafi haka."

Ajiyar zuciya DOCTOR HASSAN ya sauƙe, ita kuwa sai famar murguɗa masa baki take, ficewa ma tayi daga word tana harare harare tare da riƙe ƙugu, DOCTOR HASSAN duban Khadija yayi yace

" Ki rubuta musu magani kawai ki bar allurar."

Yana faɗa musu haka ya fice abinsa, Khadija maganin ta rubuta ta bawa BA'KURA tace yaje ya duba chemist ya saya karɓa yayi tare da basu hkrn abinda AI'SA ta musu sannan ya fito, dube dube ya fara babu AI'SA a wajen sandar sa ya dogara, ya fito daga cikin asibitin a waje ya same ta zaune a bakin wani dakali sai famar kalle-kalle take, sandar sa ya ɗaga ya kwaɗa mata a bayanta, a razane ta tashi tare da rarumar dutse ta juyo a fusace zata zabgawa BA'KURA, Allah ya rufa asiri sukayi ido huɗu dashi ta sauƙe hanunta ƙasa tana huci.

" Wallahi Allah ya rufa maka asiri BA'KURA ban rufe idona wallahi da yanzu na lotsa maka kai, to wai ma me na maka da zaka ci zalina yanzu idan ban yafe maka ba fa ka mutu mai zaka cewa Ubangijin ka, ni dai Allah idan baka daina duka na da wannan sandar ba wata rana nice ajalinta sandar nan sai dai kuma ka sake nemo wanda zaka ɗingisa wannan gurguwar ƙafar taka dashi................"

Dariya BA'KURA yayi tare da ƙofa kawai suka shige cikin wani madaidaicin Chemist ya miƙa musu katin maganin suka basa kuɗin suka faɗa masa 2k ya cire ya basu sannan ya sakata a gaba suka wuce ƙauyen su.........





08147537180




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻




*(Ummu Nasmah ce)*
[8/27, 9:31 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.





*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Book One*

*Page 7 to 8*
*____________________________________*


*ƘAUYEN BINISHED*



________✍🏻 Motar da suka hau tafiyar 40 minute ne ya kaisu mashigar ƙauyen nasu, a bakin ƙauyen aka sauƙe su, sannan suka kama hanyar shiga cikin ƙauyen, ƙauye ne sosai wanda bashi da yawan mutane, jejin Allah, idan kinga gidan kara ɗaya kafin ki sake ganin wani gidan sai kinyi tafiyar minti 15 mutane ɗaɗɗaya zaki dinga haɗuwa dasu, da haka har suka ƙarasa nasu gidan *AI'SA* da gudu ta ƙarasa cikin gidan sai kuma ta fashe da kuka tana ƙwalawa *KAKA* kira.

" *KAKA KAKA KAKA* !!!!"


Kaka dake zaune cikin bukkar ta ta jiyo kiran jikar tata, amsawa ta hau yi itama tana washe jajayen haƙwaranta da ta rinasu da gwarango.

" Lale maraba da dawowa ƴar albarka yarinyar kirki shigo gani a cikin bukkata zoki sanar dani wani shegen ne ya saki kuka, yanzu na tashi muje naci ubansa."

Ƙarasowa cikin bukkar tayi tana kukan munafurci ta zauna ta hau shure-shure da ƙafa tana cewa.

" *KAKA KAKA KAKA*!!!!!"


Matsowa Kaka tayi kusa da AI'SA ta dafa mata kafaɗa tana cewa.

" *AI'SA* wai ko dai kin makance ne da kika je cikin garin nan gani ina kallon ki kina kallo na amma tsabar shashanci kita ƙwala min kira yuwa wata makahuwa me aka miki a cikin garin."?

Kuka AI'SA ta fara tana mutstsike idon ta na karya tare da gyara zama ta fara shiryo ƙarya.

" Kaka an cuceni a cikin garin nan da mukaje, BA'KURA shima ya cuceni, kaka kinsan me yacewa wani koɗaɗɗen likita, suka dinga zagina wai cewa fa suke waini nake da shafar aljanu wai mahaukaciya ce ni Allah kaka idona idon wannan koɗaɗɗen likitan sai na shuka masa tsiya wallahi, sai ya gane Ruwa ba sa'an kwando bane, kuma kaka tsabar mungunta irin ta BA'KURA ba cewa yayi zamuje ya saimin nagani ba, to wallahi kaka ƙarya ya miki, mungunta yamin ya kaini su min allura."

Salati kaka ta tafka tana tafa hanu tace.

" Haka BA'KURA zaimin, na ɗauki amanar ki na basa amma tsabar tsiya yace Ke ɗin ce mai shafar aljanu, to ƙarya suke kinfi ƙarfin aljanu, domin kuwa kina da Ni, ni ɗin nan da kike gani na san manya manyan aljanu guda bakwai, kuma yanzun nan zan baki addu'ar su, aljani ko wuta suka hura kibi ta ciki ki wuce, kuma shima BA'KURA zai san ya ci amanata, kinga *AI'SA* buɗe kunnenki na baki addu'ar aljanu karma bakin su ya kamaki kinsan wani mutum bakin sa guba ne."

Tura baki AI'SA tayi tace.

" Kaka akwai wata addu'a ne bayan wanda Baba ya bani ta surorin baƙara da Falaƙi da nasi."

Kaka cewa tayi

" Ke dallah wannan addu'ar da zan baki itace tafi komai korar aljanu su aljanun sune suka bani addu'ar da kansu, ke kinsan waye ni kuwa to bari kiji addu'ar, *SHUKURAJU MANGA GINNI, SHURƁANJO MANGA GINNI, MAHALFINI GA ALLAH GA SURATUL WALIYIL GINNI*." kinga wannan addu'ar dana baki sahihiyace sunan manya manyan aljanu ne idan kika yita to karkiji tsoron aljanu na faɗa miki ko wuta suka hura shige ta ciki ki wuce sanyi ƙalau zakiji babu zafi."

Fanta ƴar AI'SA dake kwance kan gadon kaka tana jin duk abinda suke faɗi ne, ta saka dariya dama dariyar cinta take tun sanda aka fara addu'ar cikin dariyar Fanta tace.

" 🤣lallai kuwa zaki ƙone ƙurmus babu mai ciro ki, yau naji wata addu'a a wajen kaka to waima ke kaka a ina kika gamu da aljanun har suka baki addu'ar😄"

Ta ƙarasa maganar cikin dariyar domin kuwa sosai kaka yau ta bata dariya " su SHUKURAJU MANGA GINNI manya manyan Aljanu😄 cikin zuciyarta ta yi maganar, AI'SA kuwa kallon kaka tayi ta kalli Fanta tare da dakawa fanta harara cikin rashin kunya tace.

" To ke kuma uwar gulma da saka ido waye ya saki cikin zancen mu da kakata, to wai kina nufin Kakan ƙarya ta miki, kuji ƴar shishshigin tsiya dai"

Zaro ido Fanta tayi ganin lokaci guda Ai'sa tana neman tada mata da fitina a wajen kaka to ma idan banda raini Ai'sa ce zata ce mata shegen shishshigin tsiya Fanta za tayi magana Kaka ta rigata da cewa.

" Barni da ja'ira Ai'sa to dan ubanki buɗe kunnenki kiji inda muka haɗu da MANGA GINNI ya bani wannan addu'ar"

Taɓe baki Fanta tayi tare da jefawa Ai'sa mungun kallo, kaka labari ta fara basu.

" A kwai wani lokaci munje jeji da Ba'na muna tsaka da tafiya cikin jejin nan kawai sai naji an kira sunana ance.

" Ke *YA KWALO* zoki karɓi goro, kinsan dana juya kawai sai nagan su aljanun sai bikin suna suke yanda muke bikin sunan mu suma fa haka suke nasu harda maroƙa da makiɗa , na cewa Ba'na bakaji ana kirana bane sai cemin Ba'na yayi Ke Ya KWALO ki kiyayi kanki me zakije kiyi a wajen Aljanu, nace ni sai naje yana tsaye na ƙara wajen su, suka bani goro mai yawa sannan MANGA GINNI ya bani wannan addu'ar, kinji inda na samu munafuka uwar gulma, ni nayi zaton ma bacci kike ashe shuru kikayi kina mana gulma."

Tashi Fanta tayi tana dariya har tana riƙe ciki ta fice da ga ɗakin Kaka, domin kuwa wannan ba addu'a bace surkullen kaka ne kawai da kuma gigin tsufa daya fara cimmata, Tsuka Ai'sa taja tare da cewa.

" Kaka kina kallon tana miki dariya, tana fa nuna alamun ƙarya fa kenan kike mata, hmmm bazaki tashi ki bita har wajen Maman ba ki hukunta ta shine kika zauna kina kallon ta, duk zuciyarkin nan kaka wannan fa raini ta miki."


Ai kuwa kamar wanda ta tunzura kaka ta miƙe tare da sandarta tana cewa.

" Ai kuwa gaskiyar ki ne Ai'sa tashi muje, naje har wajen Ferebuwayen naji idan itace ta sata ta dinga mai da min da zance."

Tsalle Ai'sa ta saka tare da tashi tabi bayan Kaka, Fanta suna zaune da ita da Mama da kuma wansu Kacalla, sai dariya suke fanta tana basu labarin addu'ar kaka, basu ankara ba sai ji sukayi kaka tana cewa.

" Umhum ƴar Albarka Kinji zancen ki ya dawo ko AI'SA ashe da gaske Uwar taku ce take sawa a rainani a cikin gidan nan to dake wato Ferebuwaye Ni kika raina ko to bani kika Raina ba, uwarki AI'SA Wanda kika laƙabawa wannan yarinyar sunanta ita kika Raina bani ba, sandarta ta ɗaga ta kwaɗawa Kacalla a kansa tana cewa, kaikuma munafukin Allah kana namiji kana shiga cikin mata gulma to tashi kabar wajen."

Kacalla idonsa ya ɗaga yana yiwa Ai'sa alamun zan riƙeki, kafin yace wa kaka.

" Ban tashi ba kizo ki ɗagani idan kina da ƙarfi kuma kinga wannan sandar da kika kwaɗa min akan wannan tujajjiyar mai kama da bulugari zan rama na lahira sai ya fita jin daɗi ga ta nan babbar munafuka tana biye dake kina kiran wani munafuki kaji tsohuwa da jaraba haka kawai kizo ki samu a gaba akan wannan shashsheƙar ta sakoki gaba."

Mama doge bakin Kacalla tayi tana cewa.

" Karna ƙara jin bakin ka tashi ka fice Kaltin abokiyar wasan kane (dake haka take kiran kaka dashi), ɗauki abincin marar lafiyar da aka kawo ka kai musu kafin mahaifinku ya dawo daga gona."

Tashi Kacalla yayi yana hararar kaka ya ɗauki abincin ita kuwa kaka ƙwafa tayi sanda yazo fita da gangan ya jide ƙafar AI'SA ji kake gum ta faɗi ƙasa, dariya Kacalla yasa tare da saurin shigewa yana cewa.

" Gobe ki sake munafurci ina dai-dai dake."

Kaka salati tasa tana cewa.

" Ferebuwaye kina kallon baƙar muguntar da Kacalla ya yiwa wannan yarinyar ko, kina kallo ko, bari uban nasu ya dawo zai shiga tsakaninki da waɗannan baƙaƙen mugayen tashi kinji."

Tana callara kuka ta tashi tare da riƙe kanta da ta bige, tana tsalle.

" Na rantse da Allah bazan yadda ba sai na rama wallahi bazan yadda ba, da gudu ta juya zata bi Kacalla Mama ta daka mata tsawa."

Dawo nan karki yadda ki bisa wallahi idan kuma kika bisa bayan ya dako ki nima ƙara miki zanyi, tunda baki da mutunci baki da kunya, ba yayanki bane da..........."

Kaka ce ta dakatar da Mama tana cewa.

" To ya isheki haka zaginta, sai ku daketa tunda jaka ce ita, to naga ɗan iskan da zai daketa a wannan gidan Ferebuwaye ki kiyaye ni Allah zan iya sawa BA'GAJI ya sakeki kibar gidan nan akan wannan yarinyar muddun baki fita harkarta ba."

Hanun AI'SA taja suka bar wajen tana sababi.

Mama dai shuru tayi bata kula Kaka ba amma cikin zuciyarta tana jin takaicin yanda ta lalata AI'SA yarinya duk ta zama marar kunya babu wanda ya isa ya mata faɗa daga ni har ubanta bamu isa da ita ba ya Allah ka shirya min AI'SA.

Mama tayi Maganar tana ƙwafa tare da cigaba da iza wuta, Fanta ma tashi tayi bata ce komai ta ɗauki garin tuwo ta fito waje ta fara tankaɗe itama tana jinjinawa Rashin Kunyar AI'SA.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*CIKIN MAIDUGURI*


DOCTOR shine bai dawo cikin gidan sa ba sai misalin goma na dare, lokaci ne ya ƙure masa a Hospital ko gidan nasu bai samu ya koma ya duba jikin Umman sa ba, tsap ya sami falon sai tashin ƙamshi yake ita kuwa Falmata tana zaune ɗaya daga cikin kujerun falon tasha kwalliya cikin wandon jean three cutter da kuma wata ƙaramar best wanda tasha mata jiki, gashin kanta kuwa ta ƙullesa da Ribon ko ɗan kwalo bata sa ba sosai tayi kyau, Ganinta cikin falon yasa DOCTOR ya fasa yin sallamar da yayi niya, kansa ya ɗauke tamkar bai ganta ba ya wuce Bedroom ɗinsa, wani irin tuƙuƙun baƙin ciki Falmata taji a cikin ranta duk wannan kwalliyar tayi ne ko zata samu ta burgesa amma ko arzikin kallo bata samu ba a wajensa wannan wacce irin ƙiyayya ne haka, wani irin girman laifi na masa haka "anya kuwa iya ƙiyayyar iyayena ne yasa DOCTOR yake gwada min wannan tsanar ko dai na masa wani laifi ne mai girma wanda ni ban sani ba, Allah gani gareka kana kallon halin da nake ciki Allah ka sauƙaƙa min wannan baƙin cikin dake damun Zuciyata" duk cikin zuciyarta take wannan zancen, hawaye ne ya gangaro mata daga idanunta hanu tasa ta goge tare da jingina kanta jikin kujerar ta rufe idanunta tana jin ƙirjinta yana mata ƙuna.

Shi kuwa DOCTOR wayar sa ya ajiye da kay ɗin sa a bedsite drower sannan ya hau cire kayan jikinsa towel ya ɗauka ya ɗaura a ƙugunsa sannan ya shige tollet wanka yayi, bayan ya fito daga wankan ne ya tsane ruwan jikinsa da ƙaramin towel body spray kawai ya fesawa jikinsa sannan ya ɗauki wasu blue ɗin sleeping dress ɗinsa na maza ya sanya a jikinsa, wayoyinsa ya ɗauka ya fito falo, darect daining table ta nufa, Falmata dake zaune har yanzu a inda ya barta ne ta zaro idanunta ganin DOCTOR ya nufi daining domin kuwa ko a mafarki bata taɓa tsammanin zai ci abincin gidan ba, saboda ya juma baya cin abincin ta, gashi ƙwate tayi ɗan kaɗan bata dafa dashi Bama, "yau kuma na shiga Uku ta furta a zuciyarta" cike take fal da tsoro, shi kuwa zama yayi a daining ɗin kawai ba tare daya ce mata komai ba, danne danne kawai ya hauyi da wayarsa cike da tsoro Falmata ta tashi ta nufe sa tsayawa tayi tare da cewa.

" Kayi hkr DOCTOR banyi tunanin........"

Tsuka mai ƙarfi yaja tare da ɗaga mata hanu.

" Please leave me alone, ki daina shiga rayuwata fa, wai dole ne sai kin haɗa rayuwarki da tawa, ko dole ne sai kin min Magana Mtsss!!! Duk sanda Allah ya haɗa ka rayuwa da Maye ka shiga Uku ni kuma tawa jarrabawar kenan Auren irin tsiya, mema zai hana ba za kiyi maita ba, kinsha nonon Yana mtsss!!!."

Ya ƙarasa maganar cikin tsaki, yana maida idanunsa kan wayarsa, Falmata wani irin raɗaɗi taji yanda DOCTOR yake zage mata iyayen ta babu ko kunyar idanunta, idan ba kunnenta ne suka jiye mata ƙarya ba kamar ma kiran sunan mamanta yayi babu ko sayawa, bata so magana amma dole sai tayi koda kuwa kasheta DOCTOR zaiyi.

" Kana kirana da mayya banajin zafin sa sosai, amma sai dai yau da ka danganta maitar da Mahaifiyata sai naji yamin ciwo sosai a cikin Raina, Doctor Sunan mahaifiyata ka kira fa baka saya ba, karka manta da komai lalacewar iyaye ɗansu yana sonsu, bai kamata ka ciwa iyayena mutunci a gabana ba, tunda ko ba komai surukan ka ne, baka kyautatawa zuciyata ba, DOCTOR."

Ta ƙarasa Maganar cike da rauni hawaye na zuba daga idanunta, tunda ta fara Maganar doctor yake sauraron ta ba tare daya dakatar da ita ba, sai da takai ƙarshe tukunna kafin ya ɗago ya kalleta yana sakin murmushin gefen baki kafin yace.

" Hmmm!!!! Ai daman zafin shi nakeso kiji, Idan na kira sunan mahaifiyarki sunan mahaifiyata na kira, ko kuma ni ta haifeni ne, ƙarya nayi ba YANA ake kiranta dashi ba, ko dan bakiji na kira asalin sunan nata ba, YAHANASU, komai lalacewar iyaye tabbas ƴaƴan su suna sonsu amma ba irin lalacewar iyayenki ba na rashin albarka, tir da iyaye irin naki, sannan tunda naci mutuncin iyayenki ai sai kimin hukunci, bana ɗaukar iyayenki a matsayin surukai na, ina ɗaukar sune a matsayin wanda aka zalunta da wanda yayi zaluncin ma'ana dai ina ɗaukar su ne a matsayin azzalumai maha'inta waɗanda bazasu gama da duniya lafiya ba Mtsss."

Ya Kawo ƙarshen maganar tare da buga table ɗin dake gabansa ya miƙe ya bar Falmata tsaye cikin tashin hankali da munguwar damuwa, bakinta nauyi ya mata ta kasa magana jin mugayen kalaman da DOCTOR yake faɗa mata, kuka ta saki tare da shigewa Bedroom ɗin ta da gudu ta faɗa saman bed ɗin ta tana sakin kuka mai cin zuciya, sosai take kukan tana Allah wadarai da halin iyayenta da suka ja mata tsana idan har sun aikata abinda DOCTOR yake zarginsu dashi me zatayi ta dawo da DOCTOR hayyacin sa domin ta fara zargin cewa DOCTOR baya cikin tunanin sa, anya kuwa wannan abubuwan da suke faruwa basu sashi ya fita daga hayyacin sa ba kuwa......................."?




Vote.
Share.
And comment.




08147537180




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻




*(UMMU NASMAH CE)*
[8/28, 5:34 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤️ *Love and romantic and funny story* ❤️



*Na*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.





*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Book One*

*Page 9 to 10*

*____________________________________*



_______✍🏻sosai Falmata take sambatu cikin kuka daren ranar Falmata baccin ta kaɗan ne, washe gari da ciwon kai ta tashi mai zafin gaske koda wanka ma daƙyar ta iya yinsa ta dawo ta kwanta shuru tayi tana tunanin rayuwarta ta baya har yanzu hawaye bai daina gudu a fuskar ta ba, ina ma ana tariyo Rayuwar baya tabbas da ta tariyo tata ko zataji sauƙin damuwar ta.

Shi kuwa DOCTOR ƙarfe tara ya fito daga Bedroom ɗinsa cikin shirin sa na fita aiki, breakfast ya gani jere saman table da alamu dai Ladiyo ce tayi, daining table ɗin ya nufa domin kuwa yunwa yake ji sosai jiya babu abinda yasa a bakin sa, plast ya jawo ya haɗa tea mai kauri bread ya ɗauka tare da ƙwai, ya fara ci a hankali, sanda ya gama sannan ya goge bakin sa da tissue jakarsa ya ɗauka sannan ya fice ba tare daya duba Falmata ko lafiya ba kasancewar bai ganta ba kuma ya saba kullum ta saba shigowa ta gaishe sa koda kuwa bazai amsa ba, ita kuwa tana kwance taji tashin motar sa alamun ya fita wasu hawayen ne suka ƙara sauƙa mata masu ɗumin gaske, wato ko mutuwa tayi sai dai idan ta ruɓe aji warin ta DOCTOR bazai shigo ya duba halin da take ciki ba.

Cikin wannan yanayin ta kasance, har kusan ƙarfe 12 na rana tana nan kwance cikin Bedroom ɗin ta bata fito ba Ladiyo ce ta shigo Bedroom ɗin da Sallama, amsa mata Falmata tayi muryar ta adashe kasancewar kukan da tasha, ƙarasowa Ladiyo tayi ta gaishe ta tare da cewa.

" Aunty Lafiya tun safe baki fito falo ba."

Murmushin da yafi kuka ciwo Falmata tayi tace wa Ladiyo.

" Kaina ke ciwo Ladiyo"

" Ayya sannu Aunty Allah ya baki lafiya dama baƙuwa kikayi Ƙawarki Aunty MAJI shine nace fa nazo na sanar dake."

" Kice mata ta ƙaraso."

Tashi Ladiyo tayi taje ta sanar da Maji, maji ƙarasawa tayi cikin Bedroom ɗin Falmata, a bakin bed ɗin ta zauna tana ƙarewa ƙawar tata kallo tace.

" Falmata lafiyar ki kuwa kinga yanda kika rame kikayi duhu, idanunki duk sun zurma, Zaki kashe kanki Falmata akan ɗa namiji da bashi da tabbas, ki dawo hankalin ki ki cire damuwar DOCTOR a ranki idan ba haka ba zaki sawa kanki cuta kin daina zuwa makaranta anyi lectures da yawa babu ke gashi har ana daf da fara test abinda ya kawo ni kenan na sanar dake gobe ki shiryawa zuwa school idan ba haka wallahi za kiyi rippit."



Please Login or Register in order to submit comment