Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yagana bata koma ɗakin Hajja ba tayi ɓangaren Yalwa matar baffan ta, yallaɓoi da Sallama ya shiga ɗakin mahaifiyar tasa, waje ya samu yana cewa.

" Sannu da hutawa Hajja."

Wani irin mungun kallo Hajja tayi masa tace.

" Saboda kun barni nayi hutun, nace kun barni nayi hutun ne, munafukai waɗanda sam baƙwa ƙaunar zaman lafiya a Rayuwar ku."

Ta ƙarasa maganar tana zama yanda zata fuskance sa, yallaɓoi cike da mamaki yake duban Hajja yace.

" Allah ya huci zuciyarki Hajja laifin mena miki."

" Au!!! Tambayata ma kake laifin ka, to bari kaji na faɗa maka, bazaku kashe ni da baƙin ciki ba, Bukkar duk inda ka kai ɗan uwanka MALA kayi gaggawar dawo dashi idan kuma kashesa kayi ka binnesa babu wanda ya sani, to ka sanar dani a tono sa YA'YAN sa suga gawar sa, sai a samu zaman, dole ne ku gyara zamantakewar ku dan haka faɗa min ina kakai MALA DA JALILA."

Da sauri yallaɓoi ya ɗago idanunsa a kiɗime yace.

" Wani irin Magana kike nine zan Hallaka ɗan uwana Hajja, Allah ya rufa min asiri banyi wannan lalacewar ba Hajja, taya zan Hallaka ɗan uwana wanda yafi kowa ƙaunata a duniya, wallahi wallahi wallahi ban san komai game da ɓatar Ya Mala ba, ki yadda dani Hajja."

Hmmm!!!! Kaji munafukan Asali to ban yarda da kai ba, Bukkar nasan yanda kake son sarauta babu abinda bazaka iya aikata wa dan haka na ƙara baka umarni a karo na biyu kaje ka fito min da Ɗana da Jikata, idan kuma kaƙi na tabbata Hassan bazai taɓa ƙyale ku ba, zai fara kashe ƴarku da baƙin ciki ya kawo muku gawarta ya ajiye muku, sannan ya hanaku zaman lafiya kaga daga ni kuma sai na tattara kayana na bar muku gidan na koma gurbin gidan ubana, idan yaso sai ku kashe kanku."

Hankalin yallaɓoi sosai ya tashi da kalaman mahaifiyar tasa, ya rasa ta ya zai fahimtar da ita bai san komai game da ɓatar ɗan uwansa, cike da tashin hankali yace.


" Hajja.........."

Dakatar dashi tayi tace.

" Bana son na ƙara jin komai daga bakin ka na gama baka umarni sakamako nake jira, tashi ka barmin ɗaki"

Tashi yayi ya fita cikin sanyin jiki da kuma damuwa, shi a ina yasan zai samo YaMala.........

Ɗakin matar tasa Yana ya shige ya zauna tare da riƙe kansa yayi shuru cike da damuwa, yana dake zaune ta dubesa tace.

" Abban Falmata meya sameka ka shigo haka rai ɓace."

Ɗago idanunsa da sukayi jajur yayi yace.

" Yana wai Hajja ni take zargi da ɓatan ɗan uwana, kamar yadda ƴaƴan sa suke zargina, Hajja ma tabi sawun su, wai naje na nemo mata Yamala duk inda na kaisa hmmm!!! Sunƙi su yarda cewa bani da hanu cikin wannan al'amari."

Ya ƙarasa maganar cike da ƙunar rai Aunty YANA bakin ta taɓe tare da cewa.

" To sai me tunda basu yadda ba, sai su kasheka tunda suna zargin ka, kaga karka wani saka damuwar su cikin ranka bare kuma ya dameka."

Tsuka YALLAƁOI Bukar yaja ba tare daya kuma cewa Yana komai ba domin kuwa ita ba fuskantar damuwarsa za tayi ba, ganin haka da Yana tayi itama ta watsar da zancen.


Shi kuwa DOCTOR ransa a matuƙar ɓace ya hau motar sa, ya figeta da ƙarfi, tsabar ɓacin rai idanunsa ko gani basa yi sosai, burin sa kawai shine ya gansa gashi ga Falmata, da wannan mungun tunanin yake dreving.


Allah Sarki baiwar Allah ita kuwa Falmata tun fitar Hajja daga gidan take cikin tashin hankali, tasan halin Hajja sarai yau bazata ƙyale DOCTOR ba, muddum Hajja ta sami DOCTOR ita kuma ta tabbata yau kwanan Auren ta ya ƙare, ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da kawowa take, ai kuwa kamar wanda aka tsikareta da sauri ta ɗauki wayar ta, numbern Maji tayi kira cikin Sa'a kuwa ta ɗaga Falmata cike da tashin hankali tace.

" Maji ki taimake ni kar Aure na ya mutu idan Aure na ya mutu nima mutuwa zanyi."

Maji cikin ɗaurewar kai tace.

" Auren ki ya mutu, kuma, me Kuma ya ƙara shiga tsakaninku dashi."

" Ba dashi bane Maji Hajja ne, yanzu tabar gidan nan cikin ɓacin tace lallai yau sai DOCTOR ya sake ni, na tabbata indai suka haɗu tabbas saki sai ya wajaba a kaina ki taimakeni ki dakatar da Hajja kisan yanda zaki hanata yiwa DOCTOR Magana."

Maji tsuka taja tana cewa.

" To wai ma sai me idan ya sakeki meye amfanin Auren kin nan idan banda cutuwar da kike yi, da zakiji shawarata da kin bar Hajja ta ƙwata miki ƴancin ki, ta hakane DOCTOR zai fara fahimtar mahimmancin ki daga Ranar da kika kauce masa, Soyayyar da kike nuna masa tayi yawa itace take ƙara hura masa kai wajen ganin ya wulaƙanta ki, yana ganin koma me zai miki ai bazaki iya rabuwa dashi ba, wai ina zuciyarki take ne Falmata ki tashi ki ƙwaci yancin ki mana, meye amfanin Auren mutumin da baya ganin darajar ki da na iyayen ki da suka haife ki har ya ganki ya Aura, ki dawo hankalin ki Falmata."

Cikin shashsheƙar kuka Falmata tace.

" Maji ba wannan maganar nake buƙata daga gareki ba yanzu, so nake ki dakatar da Hajja, ina son mijina bazan iya rabuwa dashi ba, koda kuwa naman jikina yake yanka kullum, zan zauna dashi a haka, ki taimakeni Maji karna rasa igiyar Aure na."

Cike da jin haushin Falmata Maji tace naji zan dakatar da Hajja amma tukunna ki kira DOCTOR SAIF ya fara raba DOCTOR da wayoyin hanunsa tukunna, gudun kar kafin na isa gidan ku Hajja ta rigani kiran sa idan har kinyi haka to Tabbas zan dakatar da Hajja."

Falmata da to ta amsa cikin sauri ta kashe kiran Maji, ta fara neman numbern SAIF sau uku tana kira zai shiga amma baza'a ɗauka ba, cikin tashin hankali Falmata ta yasar da wayar hawaye na gudu saman fuskar ta, shikenan ta shiga Uku yau zata rabu da farin cikin ta, tana cikin wannan tunanin taji wayar ta yana Ring saurin dubanta ta kai kan wayar Doctor Saif ke kira cikin sauri ta ɗaga, ko Sallama bata amsa ba tace.

" Saif kuna tare da DOCTOR ne.?"

Tambayar da ta jefa masa kenan, jin muryar ta cikin damuwa da alamun kuka yasa DOCTOR Saif cewa.

" Bama tare dashi ya fita tun ɗazu, lafiya Falmata meke damunki."

Da ƙarfi Falmata ta furta "na shiga Uku................."





????????????????????????
Tabbas akwai ayar tambaya a cikin wannan cakwakiyar family........


Shin mai zai faru, DOCTOR zai sake FALMATA?


Ina labarin AI'SA wata irin gudummawa zata bayar cikin wannan labarin ?

Shin Umma zata sami lafiya?

Shin mahaifin DOCTOR da ƴar uwarsa suna raye ko sun mutu?

Shin idan ba YALLAƁOI BUKAR bane da YANA sukayi sanadiyar rasa iyayen DOCTOR to waye ne?

Sannan su wannan family kansu ya suke rayuwarsu kafin faruwar wannan mungun al'amarin?


Amsar ku tana tattare cikin wannan littafin amma ta hanyar 👇🏻

*Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari*

*Kumin adalci dan Allah kar wacce ta zageni dama bance free book bane, idan ya miki ki saya idan bai miki ba ki barmin kayana, amma dan Allah karki zageni ina maraba daku masoyana kiyi ƙoƙarin ganin kin biya naki domin kuwa tuni har an fara biya*



Akwai waɗanda suka bani kuɗin su a cikin group ɗina na Ruɗanin Zuciya biyu so dan Allah kumin magana ta pc sai nayi adding ɗinku a paid group.

Vote
Share
And Comment




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*




*(UMMU NASMAH CE)*
[9/1, 6:24 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romance and funny story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


*Special Gift to*

*Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku*🥰


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*BOOK ONE*

*PAGE 15 to 16*

*_____________________________________*




________✍🏻 Yasar da wayar Falmata tayi cikin tashin hankali ta zauna rasa ya zatayi da kanta tayi, idan har Hajja ta sami DOCTOR bata san wani irin abu bane yau zai faru tsakanin ta da DOCTOR, hawaye ne sharshar yake zuba daga ƙwayar idanunta yayin da hankalin ta yake matuƙar tashe kafin kice me har idanunta sunyi jajur, tana nan cikin wannan halin ta jiyo dirin motar sa, wani irin tsinkewa zuciyarta, tayi da sauri ta miƙe tsaye tare da zuwa window ta ɗaga labule, a yanayin yanda taga ya fito daga cikin motar tabbas yana zuciye, runtse idanunta tayi cike da tsoro ta sake labulen jikin bango ta koma ta jingina hawaye na ƙara gudu daga idanunta.

DOCTOR kuwa da ƙarfi ya turo ƙofar falon idanunsa jawur, ya shigo ba ko Sallama, a tsakiyar falon ya tsaya cak yana ƙare mata kallo yanda take rakuɓe jikin bango sai famar zubar hawayen munafurci take, a hankali yake takawa inda take yayin da ita kuma zuciyarta take ƙara tsananta bugawa a duk takawar da yayi domin nufo ta, sanda yazo daf da ita har kamar numfashin su na haɗuwa, idanunsa da suka koma kamar gauta ya haɗa da nata yana jefa mata mungun kallo mai cike da zaki gane kurenki, saurin sunkuyar da kanta tayi ƙasa, cike da tsoro,shi kuwa DOCTOR cike da mungunta ya saka hanunsa ya fisgo gashin kanta, runtse idonta tayi cike da azaba ɗago kanta yayi tare da cewa.

" Ɗago kanki ki kalleni baƙar munafuka, uban waye ya baki shawarar ki kai ƙarata wajen Hajja, Hajjan uwata ce ita ko kuma zata hanani na miki abinda naga dama ne, bari kiji abinda baki sani ba, na tsaneki fiye da yadda na tsani mutuwa ta, bazan taɓa ƙara sonki ba a cikin Rayuwata, dan haka ki daina kai ƙarata domin kuwa bazaki ƙara samun wata kulawa daga gareni ba, dan haka kije na..............."

" Ka dakata!!!! Ka dakata!!! Karka aikata babban kuskuren da bazaka taɓa iya gyara sa ba Malam Hassan."

Daga DOCTOR har Falmata kallon su suka mayar inda sautin muryar ta fito *HABEEB* ne tsaye ya zuba hanunsa cikin aljihu kyakkyawan mutum ne fari sol tamkar bafulatani sai dai KANURI ne shi murmushi HABEEB ya saki tare da cewa.

" Abokina kayi mamakin shigowa ta cikin gidan kane akan lokaci, nazo gyara maka kuskuren kane a karo na farko, kuma na ƙarshe, kana kuskuren rabuwa da ita, ni kuma a lokacin ne zan Aure abata dama tawace ƙaddara yasa ka ƙwace ta, sam bata ma dace da miji irin ka ba damu ta dace waɗanda zamu riritata tamkar ƙawai mu bata kulawa yadda ya dace, domin Falmata matar hutu ce, ka kiyaye idan kuma baka kiyaye ba, ina nan ina jiran fitowar ta, karka manta da har yanzu akwai Soyayyar ta a zuciyar HABEEB."

Yana gama faɗin haka ya juya ya fice da murmushi ɗauke saman fuskar sa, gagara Magana DOCTOR yayi har HABEEB ya fita daga falon wani irin baƙin ciki ne ya murɗi DOCTOR HABEEB a cikin gidan sa uban waye ya basa izinin shigo masa cikin gida, Okay wato dai har yanzu bai cire Soyayyar matar sa Falmata a cikin ransa ba, ashe har yanzu yana bibiyar ta, cikin haushin ya ƙara damƙe gashin Falmata sanda tayi ƙarar azaba, haɗa kanta yayi da bango, tare da saka ƙafarsa ya mutstsike ƙafar ta, hawayen azaba sune suka gangarowa Falmata, ita kanta ta razana da shigowar HABEEB cikin gidan nan, to wa ya turo sa? sakin ta DOCTOR yayi ba tare daya ƙara furta mata komai ba ya shige Bedroom ɗinsa cikin mungun ɓacin rai, har yana jin kamar jiri, Falmata kuka tasa tana riƙe kanta dake sara mata ga yatsun ƙafarta da take jin kamar zasu fice daga jikinta riƙe ƙafar tayi cikin kukan take furta."

" Na shiga Uku wai me nayiwa Ubangiji ne yake jarabtar Rayuwata, wani irin laifi na aikata, ya Allah na tuba ka yafe min idan har akwai wani laifin dana maka kake hukuntani dashi, ya Allah ka daidaita tsakanina da mijina, Allah kana gani ina son mijina bazan iya rayuwa ba tare dashi ba, ya Allah ka dawo min hankalin mijina gareni, Allah ka kawo min sauƙi cikin wannan baƙin cikin da nake."

Ta ƙarasa addu'ar tana kuka mai cin rai.

Shi kuwa HABEEB cike da tausayin Falmata ya fito daga cikin gidan motar sa ya shiga, duban sa ya kai ga Maji dake zaune cikin motar tana jiran fitowar sa tambaya ta jefa masa.

" Ya akayi Allah yasa ba dukanta yayi ba naga ka fito kamar jikinka a sanyaye."

Ajiyar zuciya HABEEB ya sauƙe tare da cewa.

" Meyasa kika sa na dakatar da Hassan daga sakin Falmata, anya kuwa kin mata adalci, dama haka take shan wahala a gidan Auren ta, da wannan mungun zaman da Falmata take a gidan Auren ta, gaskiya ina ga mutuwar Auren ta shiyafi, tabbas Hassan ya ci amanar Falmata, Soyayyar da ta nuna masa sam bata cancanci sakamakon azabtarwa daga garesa ba, komai tsananin girman laifin da ta aikata masa, amma meyene ya jawo musu wannan zafin ƙiyayyar? Ina ku ji a jiki na kamar zuwan da nayi bai dace ba."

" Hmmm!!! HABEEB duk wanda yasan rayuwar su a baya abinda zai faɗa kenan wanda kuma bai san rayuwarsu ta baya ba, cewa zaiyi Auren ƙiyayya sukayi, duk abinda kaga DOCTOR yana yiwa Falmata bata ganin laifin sa, sai ma ƙoƙarin da take wajen ganin ta masa biyayya, sanin matsalarsu kuma wannan family essur ne, HABEEB nima dole tasa na sanya ka cikin wannan lamarin, domin samowa Ƙawata farin cikin ta, sanin kanka kaine kaɗai mutumin da DOCTOR yaƙe shayi a cikin samarin da suka nemi Falmata domin kuwa yasan kafi sa komai kuɗi matsayi da kuma iko, hakan yasa yake mungun shakkar ka tare da kishin ka, nasan koda yayi niyyar sakin Falmata, yasan cewa kana nan kana jiranta na tabbata bazaiyi gangancin rabuwa da Ita ba, na GODE daka taimaka min wajen dakatar da DOCTOR."

" To Allah ya sauwaƙa, nima nayi hakanne kawai domin Soyayyar da nake yiwa Falmata, har yanzu Zuciyata babu macen da take so sama da ita Soyayyar ta a jinina take bazan taɓa daina sonta ba har ƙarshen Rayuwata, sai dai na ɗauki ƙaddarar rashinta a yanda tazo min domin kuwa Ubangiji ya ƙaddara Falmata ba matata bace. yanzu ina kika nufa na sauƙe ki na wuce."

" Gida zaka mai dani, domin kuwa ina shiga gidan nan yanzu DOCTOR zai fuskanci nine na turo ka, na ƙara jaza mata wata matsalar muje kawai da yamma zan dawo."

Kaɗa kansa HABEEB yayi tare da jan motar suka bar ƙofar gidan.

Shikuwa DOCTOR Tunda ya shiga Bedroom ɗinsa ya kasa nutsuwa ya manta ma da zagin da Hajja ta masa, kawai yanzu tashin hankalin sa HABEEB daya shigo masa har cikin gida, sannan yake masa barazanar cewa har yanzu yana nan yana jiran matar sa, a fili ya furta, " cap lallai mace muminar kare ce mai cizo, anya kuwa Falmata basa tare da HABEEB suna Soyayyar bayan fage idan ba haka ba uban waye ya kirasa cikin gidan sa." Kwalaben da suke shirye kan dressing mirror yasa hanunsa ya watsar dasu ƙasa, hakan bai ishesa ba, sai da yasa hanunsa ya naushi mirrorn da ƙarfi, wani irin mungun yanka glass mirror ya masa tare da tarwatsewa idanunsa sunyi jajur kana ganinsu zaka hango tsantsar kishi a cikin su da ɓacin rai.

DOCTOR SAIF ne ya shigo cikin gidan shima da sauri, Falmata ya fara cin karo da ita a inda take zaune tana famar disgar kuka kamar wacce ranta zai fita, nufota yayi cikin sauri yana cewa.

" Subabanallah!!! Falmata lafiya meya sameki.?"

Bata kai ga basa amsa ba sukaji ƙarar wurgar da abubuwa da ake a cikin Bedroom ɗin Doctor, kusan tare suka nufi ɗakin da DOCTOR SAIF, doctor Saif cike da tsoro ya zaro idonsa yana bin Bedroom ɗin da kallo, ga baki ɗaya yayi kacakaca da kayan ɗakin, harta dressing mirror ma sai da wurgar sa ƙasa hanunsa kuma sai famar tsiyayar jini yake, Falmata hanu tasa a kanta ta ƙara sakin wani sabon kuka, kansa tayi da gudu zata riƙo hanunsa wanda yake zubda jinin ya dakatar da ita yana nunata da yatsa.

" 👉🏻 Karki kuskura hanunki ya taɓani macuciya maciya Amana wacce bata san darajar Aure ba da Auren ki amma kina Soyayya da wani namiji a waje ko kunya bakya ji, shine zaki turo min ƙato ya shigo min har cikin gida ko?, To karki kuskura ki taɓa ni idan kuwa kika taɓa ni sai na miki mungun illa."

Falmata a razane take kallon DOCTOR tana girgiza masa kai alamar bata da masaniya da shigowar HABEEB cikin gidan, DOCTOR Saif kuwa dariya ce taso ƙwace masa yanda yake hango kishi ƙiri-ƙiri a idanun DOCTOR Amma a hakan yake furta wai ya tsani Falmata bayan gashi yana kishin ta, Falmata ya duba tare da ce mata.

" Waye ne ya shigo cikin gidan nan.?"

Cike da tashin hankali tace.

" HABEEB ne kuma wallahi bani da masaniya akan shigowar sa rabona dashi tun Ranar Aure Na, da yazo ya min murna, ban ƙara sashi a cikin Ido na ba sai yau daya shigo cikin gidan nan."

Murmushi DOCTOR SAIF yayi, tare da ce mata.

" Okay ki share hawayen ki ki daina wannan kukan kije ki wanke fuskar, karki kanki yayi ciwo, zanyi Magana dashi.''

Falmata fita tayi tana share hawayen ta sai ajiyar zuciya take, DOCTOR Saif cikin Bedroom ɗin ya ƙarasa drowarn doctor ya ƙarasa ya buɗe, first aid box ya ɗauko ya dawo kusa da DOCTOR, zama yayi bakin bed tare da buɗe box ɗin kayan wanke ciwo ya ɗauka tare da kama hanun DOCTOR ya fara wankewa yana cewa.

" Me zai dameka dan HABEEB yazo wajen Falmata, a zatona matar da ake so ita ake kishi, ba matar da aka tsana ba ina tunanin ya fara zuwa zawarci ne, tunda ka kusa sakinta kaga kuwa ai dole shi kuma HABEEB ya fara zuwa kamun ƙafa."

DOCTOR ƙwace hanunsa yayi daga DOCTOR SAIF cikin masifa da zafin rai yace.

" Inji uban waye yace ina kishin ta, karka kuskura ka ƙara ƙiran kishi tsakanin mu naji zafin keta wa SUNNAR Annabi haddi da yayi ne, tunda duk tsiya dai akwai Aure a tsakanina da ita ko?, sannan kuma bari kaji bazan taɓa ƙyale HABEEB ba, sai na ɗauki hukunci a kansa na keta min haddi da yayi ya shigo min har cikin falo, ƙato dashi ya shigo min falo yana kalle min mata, haka addini yace ka faɗa min."

Saif bakin sa ya taɓe tare da miƙewa tsaye yace.

" Abokina meye a cikin idanunka idan ba kishi ba, meyasa kaji zafi dan HABEEB ya shigo cikin gidan ka ya kalli matar ka meyasa kaji zafin maganar sa, DOCTOR ka dawo cikin hankalinka domin kuwa kana son matar ka, matar da ake so ita ake kishi, gashi kuma naka idanun sun nuna kishin ka, ka gane cewa matar ka tana da daraja, duk wani abu mai daraja kuma adana sa ake, duk sanda ka sake matar ka ta kufce maka, abune mai matuƙar wahala ta dawo maka, babu yanda ka iya da HABEEB domin kuwa yafi ƙarfin ka, ko shara'a ne bazaka iya dashi ba, dan haka abinda ya kamata kayi shine ka dawo da farin cikin gidan ka ka riƙe matar ka da kyau, sannan ka rage wannan Zafin zuciyar taka, ka kuma cire zargi cikin zuciyarka, shine kawai abinda zaiyi katanga tsakanin matar ka da HABEEB."

Zama DOCTOR yayi tare da dafe kansa sai ajiyar Zuciya yake sauƙewa idanunsa ya kai kan hoton Abbansa da Aunty Jalila hanunsa yasa ya ɗauki pic ɗin, yana ƙare musu kallo, hawaye ne ya zubo masa daga idanunsa, ɗago kansa yayi ya dubi SAIF yace.

"SAIFUDDEEN taya kake tunanin zan iya gyara alaƙata da Falmata bayan iyayenta sun zalunce mu, sun mai damu marayun Dole, bazan Rayuwar farin ciki da Falmata ba, duk sanda na kyautata mata ji nake Tamkar na kyautatawa iyayen ta, bazan iya ba SAIF."

" DOCTOR meyasa idanunka suke rufewa kake biyewa zuciyarka take tunzura ka, kake yankewa matar ka hukuncin iyayenta a kanta, dan Allah DOCTOR ka sawa zuciyarka haƙuri ka bawa matar ka farin ciki, kasan Falmata macece ta gari sai son zuciyarka yasa ka yanke mata hukuncin da ba nata ba."

Shuru DOCTOR yayi jikinsa sosai yayi sanyi yasan dukkan maganganun da DOCTOR SAIF yake faɗa masa gaskiya ne, sai baya jin zai iya bawa Falmata farin ciki saboda yana jin zafin iyayenta............


*Ku biya domin cigaba da karanta wannan labarin mai matukar tausayi soyayya faɗakarwa tare da ban dariya ga yanda zaki biya kuɗin ki* 👇🏻

*Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari*


Vote
Share
And Comment



*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*




*(UMMU NASMAH CE)*
[9/2, 9:28 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


❤ *Love and romance and funny story* ❤


*Writing by*


*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


*Special Gift to*

*Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku*🥰


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*BOOK ONE*

*PAGE 17 to 18*

*_____________________________________*




_________✍🏻 "Zuciyata bazata iya daurewa ɗaukar haƙuri ba, *WUTAR FANSAR* mahaifina itace kawai take ruruwa a cikin zuciyata, SAIF duk sanda na kalli fuskar Falmata ji nake tamkar fuskar mahaifiyar ta na kalla, Sorry bazan iya doguwar rayuwa da Falmata ba, dole ne zan rabu da ita."

DOCTOR SAIF girgiza kansa yayi cike da haushin DOCTOR, ya rasa wani irin Mutum ne shi sam bashi da fahimta bare kuma ɗaukar shawara, abinda yasa a gaban sa shi kawai yake aikatawa duban sa SAIF yayi yace.

" Shikenan kaje ka yankewa kanka hukunci tunda kaine ka haifi kanka, babu wanda ya isa ya faɗa maka tunda kaine kafi kowa sanin gaskiya, amma ina mai tabbatar maka akwai ranar da zaka zo kana nadama kana neman taimako amma ka rasa samun mai taimaka maka, saboda masu taimakon ka ka watsa musu ƙasa a ido sanda suke taro ka suke nuna

Please Login or Register in order to submit comment