Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan taga Baba da JALILA ɗaure a cikin rana, an manne musu baki da gam, cike da tashin hankali Umma ta nufesu da gudu sai dai kafin ta ƙarisa taji an daki kanta da wata kwalba wani irin wari taji sakamakon ruwan dake bin jikinta tamkar ruwan kwata, a hankali take bin jikinta da ruwan ke bi da kallo, kafin ta juyo da sauri, Jummai dake saurin komawa kar Umma ta ganta ne suka haɗa ido biyu da Umma, cike da ruɗani tare da tsantsar mamaki Umma ke bin Jummai da kallo, " me muka mata wanda yasa zata mana wannan mummunan aikin, meyasa meye tsakanina da ita ban taɓa tashin hankali da ita ba, meyasa tamin haka" Umma ta furta cikin zuciyarta cike da tashin hankali, da hanu ta nuna Jummai tace.

" Jummai me............"

Dakatar da ita Jummai tayi cikin tsawa tace.

" Baki da lokacin tambayata, ki ajiye kuɗin da kika kawo ƴarki da mijinki zasu dawo gobe idan kuma kika mana taurin kai wallahi yanzu zansa a kashe su a gabanki sannan kema na kashe ki."

Cike da tsoro Umma jikinta na rawa ta ajiye kuɗin ta fito da sauri tana hawaye, Aunty JALILA hawaye ke gudu a fuskarta tana ƙarewa UMMA kallon tausayi yayin da take jifan Jummai da mungun kallo na tsana, Tabbas yau an tozarta mata mahaifiyarta a gabanta, ta ɗauki alƙawarin cewa, insha Allah idan ta kuɓuta daga wannan gidan sai ta nunawa Jummai kuskuren ta."

Baba kuwa babu abinda yake sai ambaton Allah cikin zuciyarsa, Jummai bata so Umma ta ganta ba, amma sai dai bata jin tsoron hakan domin kuwa ta sani nan da awa uku bakin Umma bazai ƙara Magana a duniya ba, dariya ta sheƙe dashi tare da duban jamo tace.

" A sanja musu wajen zama saboda tsaro."

Ta ƙarisa Maganar tare da ficewa da kuɗaɗen da Baba ya sai da filin a hanunta wanda Umma kuma ta kawo sai ta bar musu.

Umma kuwa harta iso gida Hawaye ne ke tsere saman fuskarta, babu kowa tsakar gidan hakanne ya bata damar shigewa ba tare da Kowa ya ganta ba, a bakin bed ɗin ta ta zauna tare da sakin kuka mai cin rai wayarta ta ɗaga zata kira DOCTOR domin sanar dashi abinda ke faruwa, jiri ya fara kwasarta komai na ɗakin ya fara koma mata bibbiyu, sake wayar tayi a ƙasa tana zubewa ƙasa itama, tun sanda Umma ta zuɓe ƙasa bata sake sanin ina take ba, ita dai gata nan kamar mahaukaciya kamar kuma macacciya.

Shi kuwa DOCTOR aikin sa kawai yake na tantance ma'aikatan da zasuyi aiki ƙarƙashin sa, ko kaɗan baida masaniyar abinda ke faruwa da ƴan uwan sa, sai misalin biyar na yamma sannan suka tashi tare da sanar dasu cewa, za'a sanar da duk wanda ya samu nasarar aiki da Asibitin ta email address ɗinsa, haka kowa y watse ana farin ciki da raha, bayan fitowar DOCTOR ne ya tari a daidaita, ya shiga tare da ciro wayarsa yana kiran numbern JALILA yaji ko sun dawo switch off yaji, cike da mamaki yace kodai cajinta ya ƙare ne, layin Baba ya kira nan ma switch off, tsuka yaja dai dai lokacin da mai adaidaitan ya sauƙe sa ƙofar gidan nasu, kuɗin sa ya basa sannan ya shiga cikin gidan babu kowa Part ɗin Umma shuru ba kowa falon nata ya shige yana " Umma Umma" shuru dai still yaji, zama yayi cikin falon yana jiranta may be, ko ta shiga tollet ne, har aka fara kiran magaruba nan shuru, cike da mamaki ya nufi Bedroom ɗinta, mai zai gani Umma ce kwance bakinta sai famar fitar da wani irin kumfa yake, cike da tashin hankali yayi kanta da gudu yana jijjigata tare da kiran sunanta.

" Umma!!! Umma!!! Umma!! Ki tashi Umma meya sameki Umma!!!?"

Shurun da yaji bata Magana sai ido kawai da take zuba masa tamkar bata taɓa ganinsa, fita DOCTOR yayi da gudu ya faɗa ɗakin Hajja yana cewa.

" Hajja!! Hajja!!! Umma na Umma na Hajja!!!"

A tsorace Hajja da AUNTY YANA ke zaune suka miƙe Hajja tana cewa.

" Subabanallah!!! Meya samu YAMURAM ɗin, ka shigo haka a ɗimauce."

Yana haki yace.

'' Tana ɗakin ta Umma zata mutu, kije karta mutu."

Sosai ya gigice a matsayin sa na likita gabaki ɗaya ƙwaƙwalwar sa ta toshe, Aunty YANA da Hajja da gudu suka nufi sashin Umma, Bedroom ɗinta suka shiga yanda DOCTOR ya barta haka sukazo suka sameta, cike da tashin hankali suma suke jijjigata, Hajja duban sa tayi tace.

" Ka nemo adaidaita muje asibiti."

Da sauri ya fice, ya dawo da Adaidaitan, shine ya ɗauko Umma a hanunsa ya sata cikin adaidaitan, Hajja da AUNTY YANA suka shiga, shima ya zauna gaban adaidaitan, asibitin Kustin suka nufa, take kuwa aka shige da ita emargency tunda aka shiga da ita cikin tashin hankali suke, Aunty YANA Baba Bukkar ta kira a waya, ba'a juma ba kuwa shima sai gashi ya zo, cikin minti talatin zancen ya karaɗe family, Kawu Dauda da Jummai ma sunzo asibitin Jummai harda kukan munafurci take yi, AJIRAM da Fanna Harda Hajjo duk sunzo su, suna tsaye suna jiran fitowar likitocin, sunan tsaye Falmata da Ladiyo suma sukazo cikin tashin hankali, kusan awan likitocin uku suka fito duk sun haɗa gumi, cikin tashin hankali sukayi kansa suna tambaya.

" DOCTOR ya jikin nata, ta farfaɗo DOCTOR."

Likitan cike da sanyin jiki yace.

" I am sorry to say, gaskiya, duk wani binciken da zamuyi munyi sa, lafiyar ta ƙalau bamuga wani abinda ke damunta ba, bare musan wani irin magani zamu mata, gaskiya wannan lamarin ya ruɗa mu sosai, shawara ɗaya zan baku kuje ku nema mata maganin gargajiya na gida, ciwon ta bana asibiti bane."

Cike da tashin hankali kowa ke kallon kowa Tabbas kowa yana cikin tashin hankali, amma shi DOCTOR HASSAN cikin zuciyarsa bai yadda ba, a daren sanda sukaje asibiti biyar duk amsa ɗaya ake basu su dawo suyi na gida, haka dole suka haƙura suka komo gida, hankalin su bai ƙara tashi ba, sai da sukaji su Baba da Aunty JALILA Basu dawo ba sannan duk layin su a kashe, cikin matsanancin tashin hankali suka kwana hatta Falmata a gidan ta kwana washe gari da safe Baba Bukkar yace DOCTOR ya tafi yaje gamborin gala ya dubo su Baba shi kuma zasu kai Umma wajen wani mai magani.

Haka kuwa akayi suka tafi da Umma shi kuma ya tafi neman su ba, mutumin daya sayi filin ne ya tabbatar masa da cewa Tabbas sunzo har sun sai da musu da filin sun juya gida, cike da matsanaciyar tashin hankali HASSAN ya dawo ya samu su Umma ma sun dawo.

Kusan kwana Biyar jikin Umma babu wani sauƙi sai ma wani irin abu take kamar mai ciwon hauka, ga su Baba anyi neman duniyar nan babu labarin su, DOCTOR da AJIRAM sosai sukayi kuka har suka godewa Allah duk wani mai magani da sukaji sai sun kai Umma babu wani sauƙi, hakanne yasa DOCTOR samun malam sani yake zuwa kullum yake mawa Umma addu'a sannan yake musu roƙon Allah ya bayyana musu Baba da Aunty JALILA, kawu Dauda KULLUM yana gidan Hanyar duba Umma bazaka taɓa tunanin cewa yana da hanu cikin tashin hankali su ba, AUNTY YANA da AJIRAM kusan kullum suke yiwa Umma, ta dawo tamkar yarinya komai sai an mata, bata taɓa ƙyamar Umma ba Aunty YANA harta tsarki take yiwa Umma da hanunta.


Yau da sassafe DOCTOR yana kwance ya saka kansa a cinyar Falmata, kana kallon fuskarsa zaka tabbatar da cewa yana cikin damuwa cike da tausayin halin da yake ciki Falmata tace.

" Mijina dan Allah ka daina saka kanka cikin damuwa, ka cigaba da yi musu addu'a insha Allah Umma zata sami lafiya, Baba kuma Allah zai bayyana su."

" Hankali na bazai taɓa kwanciya har sai Allah ya bayyana min su Aunty Jalila Naga Umma na ta sami lafiya, hakan shine kawai kwanciyar hankali na."

" Amma damuwar zata iya sa maka ciwo ai, ni dai da zakaji shawari na, daka rage yawan Damuwar."

Kafin ya bata amsa Saif ya shigo da Sallama Falmata ce ta amsa, zama yayi yana fuskantar DOCTOR yace.

" Naga alamar kamar ka jingine komai a rayuwarka saboda ƙaddara ta faɗa maka, wannan ba shi bane halin Mumini na ƙwarai yakan karɓi ƙaddara a duk yanda tazo masa, duk yanda zaka damu bazaka taɓa sanja ƙaddara ba, haka kuma bazaka iya bawa Umma lafiya ba, ko ka dawo da su AUNTY JALILA, jiya munyi walimar buɗe asibitin ka ba tare da izinin ka ba, saboda nasan ba lallai ka yadda ayi walimar ba, zaka iya cewa ka dakatar komai harsai Umma ta sami lafiya, on Monday za'a fara aiki office ɗinka na jiran ka, idan ma baka zoba zamu fara aiki mukam, daga gidan ku nake yanzu Aunty AJIRAM tace kazo yanzu Fanna tana kwance ba lafiya."

A matuƙar razane ya miƙe tare da cewa.

" Itama still innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati!!!"

Ya furta tare da ficewa da sauri, Saif tashi yayi yabi bayan sa, Falmata cike da tashin hankali itama ta haura ta ɗauki hijabin ta, tabi bayan su.

Shigarsa da sauri yayi kan Fanna dake kwance tana muƙurƙuso sai wani irin gurnanin aljanu take, hanu Aunty YANA tasa zata ɗago ta, ta bige hanunta da karfi tana cewa.

" Karki yadda ki taɓani munafuka, ba kune keda Baba Bukkar ba kuka yiwa Umma asiri ba, ta kwanta jinya kuka ɓatar dasu Baba SABODA kawai Baba Bukkar ya yi sarauta, sune suka musu asiri sune sune.!!!"

Da ƙarfi cike da wani irin murya mai amon gaske take wannan maganar idanunta duk sun jujjuya, gabaki ɗaya waɗanda suke wajen mai da dubansu sukayi ga Aunty YANA da Baba Bukkar, suma cike da mamaki tare da tashin hankali suke bin Fanna da kallo, DOCTOR gagara magana yayi, har MLM SANI ya iso ya fara yiwa Fanna ruƙiyya, still dai abu ɗaya take faɗa, da ƙyar suka samu aljanun suka bar jikinta, DOCTOR cike da tsana yake nufo Baba Bukkar, ya shaƙo wuyan sa idanunsa sunyi jajur yana cewa.

" Saboda banzar sarauta zaku hallaka min iyayena, meye Baba bai maka ba a duniya, yau Babu mai hana ban kashe ka ba a cikin gidan nan."

Sosai Baba Bukkar yake neman fita a hayyacin sa sakamakon shaƙar da DOCTOR ya masa Saif da Kawu Dauda da ƙyar suka kwace Baba a hanunsa, nuna sa yayi da yatsa yace.

" Na tsaneku na tsaneku dakai da dukkan wani abu daya fito daga jikinka, kuma wallahi kayi gaggawar fito min da mahaifina da ƴar uwata, sannan kuje ku karya asirin da kukayi, idan ba haka ba bazan taɓa barin kuba sai na zamo barazana ga rayuwarku, baƙin macuci azzalumi wallahi Abubakar na tsaneka."

Wani irin kuka mai sauti Falmata ta saki cike da tashin hankali, Baba Bukkar gagara magana yayi, kawai yana kallon su, shi kuma yaushe yayiwa ɗan uwan sa asiri, son zuciyarsa bai kai haka Hawaye ne ya zubo daga idanunsa, MLM SANI gyaran murya yayi yana cewa.

" Subabanallah!!! Haba Hassan yada hankalin ka, kake wannan irin jahilci, yanzu kai sai ka yadda da maganar aljani maƙaryaci, suna irin haka domin su haɗa, karkayi hukunci ba tare daka tabbatar ba."

Tsuka kawai yaja tare da ficewa cikin ɓacin rai da tsanar Aunty YANA da Baba Bukkar, shi dai kam ya yadda da Maganar Fanna, Falmata kuka take sosai tare da shiga cikin ruɗani da gudu itama ta juya ta fice.

A hankali ta shigo cikin falon nata, yana zaune ya haɗa kai da gwiwwa, kusa dashi ta zauna tare da dafa ƙafar sa tace.

" DOCTOR."

Bata kai ƙarshe ba ya hankaɗa ta da ƙarfi yana nunata da yatsa.

" Karki ƙara taɓa jikina, na tsaneki kamar yadda na tsani azzaluman iyayen ki, karki kuskura ki ƙara shiga cikin harkata a cikin gidan nan."

Cike da tashin hankali Falmata ta ce.

" Meyasa zaka hukuntani da laifin iyayena meyasa."

Tsuka yaja ba tare daya kulata ba, ya tashi yabar wajen, Falmata ƙasa ta sulale tana sakin kuka mai cin rai.


Wannan shine mussababin tsanar da DOCTOR ke yiwa Falmata da iyayenta, har na tsawon shekara guda, a cikin wannan halin Hajja ta bada umarnin a naɗa Baba Bukkar SARAUTA duk da itama tana cikin ruɗanin shin da gaske ya aikata abinda ake zargin sa dashi, yayin da Umma kuma sukaci gaba da nema mata magani amma har yau babu wani sauƙi haka kuma su Baba ma babu labarin su, a haka DOCTOR ya CIGABA da zuwa asibitin sa, a cikin wannan shekarar Allah ya ɗaukaka asibitin, sosai asibitin ke kawo masa kuɗi, harya sayi mota biyu, yana Kuma cigaba da nemawa Umma MAGANI.


Wannan shine dalilin gabar.


Mu tara daku gobe domin komawa Cikin labari.






Ki biya kuɗin ki kafin ki karanta karki karanta min LITTAFI baki biya kuɗin ki ba ki nemeni ta wannan numbern domin sanin yanda zaki biya kuɗin ki.
08147537180.









*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*







*(UMMU NASMAH Ce)*
[10/15, 10:12 AM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: *DR HSN 92 to 93*







*Mu koma labari yanzu aka fara kafcen masoyana DOCTOR HASSAN FAN'S ina ƙaunar ku irin sosai ɗin nan⛹🏽‍♀️⛹🏽‍♀️*





_______✍🏻 Yau Falmata sassafe ta tashi tayi duk wani aikin da zata yiwa AUNTY YANA, har breakfast itace tayi, sannan tayi wanka kasancewar ƙarfe takwas take da lecture's, breakfast ɗinta Tayi sannan ta shiga ta gaishe da Aunty YANA da Baba Bukkar ɗakin Hajja ta shiga tare da zama kusa da Hajja tana cewa.

" Ina kwana Hajja.''

Da lafiya Hajja ta amsa tana duban Falmata cike da tsokana tace.

" Wanka haka da sassafe ko dai har kin fara samo mana jawarawan ne, tun kafin ki gama idda, harda wani shafa man leɓe, lallai zawarcinki akwai kallo."

Murmushi kawai Falmata tayi tace.

" Kai Hajja sai kace wacce naci uban kwalliya, to maida gulmar ki, ni makaranta zani, kuɗi ma nake so a wajen ki Hajja, dubu Uku ina son zan sayi handout, sannan akwai ƙaramar buƙatar da nake so zanyi da dubu ɗaya."

Dariya Hajja tayi tana tashi ta nufi Uwar ɗakar ta, tare da cewa.

" Bari na duba miki, ai ba'a rasa nono a ruga."

Kaɗa Kanta Falmata tayi alamun to, Hajja bata juma ba, ta fito hanunta riƙe da kuɗin ta miƙawa Falmata tana cewa.

" To Allah ya tsare a dawo lafiya, ga wannan ɗari biyu idan kin dawo ki tsaya wajen saminu ki saya min gwarango da goro sai ki dawo min dashi."

Amsa Falmata tayi tare da ficewa, a tsakar gida ta tarar da temple ɗin matan gidan cike, gaishe su tayi ba tare da ta tsaya ba ta fice abinta kasancewar bata cika shiga harkar su ba, a ƙofar gidan su Maji suka ci karo da ita ta fito, cike da murmushi Maji tace.

" Tab bana ka taɓa ƙawata kinyi abin kirki kin fito da wuri baki samu mun kusa makaraba, muje kinsan yau lectures ɗin mutumin kine dr Ahmad, karya rigamu shiga ya hanu shiga."

Taɓe bakinta Falmata tayi tana cewa.

" Muje ni lectures ɗinsa baya ɗaga min hankali, domin kuwa haushin sa nake ji, na tsani mutumin daya cika kallon mata mtsss dan Allah ki daina min zancen sa."

" Hmmm ke Kuma daman Falmata, zancen wani NAMIJI kike so, idan ba na wannan ɗan iskan maha'incin tsohon mijin naki marar gaskiya da rashin riƙon Amana ba."

Falmata bata tankawa Maji ba domin kuwa taga alamun neman magana take, sai ma gaba da tayi ta barta tsaye, ƴar dariya Maji tayi sannan tabi bayan ta, suka tsaya bakin titi jiran adaidaita sahu, baƙar mota ne ta tsaya a gabansu tasha tintak glass, Falmata cike da masifa tace.

" Mtsss kai kiji wani shiga haƙƙin ɗan adam, haka kawai kayi parking a gaban mutane suna tsaye."

Ta ƙarisa Maganar tana ƙoƙarin matsawa daga wajen bata yi taku biyu ba HABEEB ya zuge Glass ɗin motar yace.

" Assalamu alaikum Amincin Allah ya tabbata a gareki Falmata sa'ar mata."

Jin muryar sa yasa Falmata ko juyowa bata yiba ta matsa gefe a binta, Maji ne tace.

" Malam HABEEB dama kaine ka tsaya bamu ganeka ba, ya aiki."

Murmushi HABEEB ya saki yana kallon Falmata ya cewa Maji.

" Nine WALLAHI tare kuke kenan, ƙawarki kamar wacce take jin haushi na, bansan laifin dana mata ba, Ni kuwa gashi Allah ya ɗaura min jarabawar sonta."

Murmushi Maji tayi tace.

" Babu wani laifi daka mata kasan halin mutumiyar juju gareta, kuma tana ganin bata gama iddaba, bazata saurari kowa ba, karka damu."

Numfashi HABEEB ya saki tare da furta.

" Well, ina zaku ne da sassafe haka."

" School zamu je."

Falmata ta basa amsa.

" Okay ku shigo na rage muku hanya ko tunda ta hanyar school ɗin naku zan shige."

" Okay to bari nayiwa mutumiyar Magana."

Ta ƙarisa Maganar tana nufar Falmata, tsayawa tayi gabanta tace.

" Kizo muje HABEEB ya sauƙe mu."

Harara Falmata ta jefawa Maji tace.

" Saboda bamu da kuɗin mota ko? To bazan shiga motar sa ba, sai ki dakata mu tari a daidaita ko, mu wuce tunda dama bashi ke kaimu ba?"

" Haba Falmata haba dan Allah, wannan ai bai kyautu ba, ya za'ayi mutum da mutuncin sa, ya tsaya ya miki magana kiƙi kulasa, sannan yanzu yace ya rage mana hanya kinƙi, anya kuwa kin masa adalci, dan Allah kizo muje ya sauƙe mu."

Kunkuminta Falmata ta riƙe tana taɓe fuska.

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!!! To meye haɗina dashi da har dole sai na masa adalci, baƙar Magana na faɗa masa, ko zaginsa nayi, ko ance dole sai na sauraresa? Nifa ba yarinya bace, ki daina tilasta ni dan Allah, motar sa ne nace bazan hauba, ko ana dole ne, dan Allah ki ƙyale ni."

" Bazan ƙyaleki ba Falmata dole na faɗa miki gaskiya, Please kizo muje mu shiga dan Allah ya KAIMU."

" Wallahi Maji bazan shiga motar sa ba, yau kam, kinji na ratse, idan zaki hau kije ki hau ban hanaki ba, zamu haɗu a makaranta, amma ni dai bazan hau ba, ki daina ƙoƙarin haɗani da wani NAMIJI domin kuwa akwai idda a kaina kinsan kuma hakan haramun ne."

Shuru Maji tayi cikin damuwa ta dawo wajen HABEEB tace masa.

" Dan Allah HABEEB kayi hkr wallahi taƙi yadda muzo mu hau, tace akwai idda a kanta I am sorry kaje kawai."

Ɗan murmushi mai ciwo HABEEB yayi tare da kaɗa kansa yace.

" Ba damuwa na gode Maji, hanu yasa cikin aljihun sa ya zaro dubu goma ya bata yace, ga wannan kuyi adaidaita."

Maji jikinta a sanyaye ta karɓi kuɗin sannan HABEEB yaja motar sa ya bar wajen su kuma suka tare adaidaita Maji tsabar haushi bata kula Falmata ba, har suka isa cikin makaranta, sunci Sa'a kuwa Malam Ahmad bai shiga ba, Kusan takwas da rabi Malam Umar ya shigo, ya sanar dasu cewa yau Malam Ahmad bazai samu zuwa ba, su jira lectures na gaba sannan ya fita.

" Maji ranta a ɓace ta ciro wayar ta, ta hau game ba tare da ko kalli inda Falmata take ba, domin kuwa yau haushin ta take ji, Falmata ganin yanda Maji ta haɗa fuska ya sata cewa.

" Maji wai me yake faruwa ne kam naga ranki a ɓace tun muna cikin nafef na fahimci hakan.?"

Maji bata ɗaga kai ba tace.

" Idonki ne kawai yake ganin haka, kuma ai kinsan ba ko yaushe mutum yake cikin nishaɗi ba."

" A'a Maji ba haka muka fito ba, fa daga gida kina cikin sakin fuska muka fito tun haɗuwar mu, da HABEEB naga yanayin ki ya sauya, ko dai kina jin haushi nane akan HABEEB."

Murmushi Maji ta saki tare da ɗago kai ta kalli Falmata tace.

" Saboda me zanji haushin ki, akan HABEEB?"

" Saboda na nuna bana sonsa, ina tunanin hakan ne ya sa fuskarki ta sauya."

Murmushi Maji tayi tare da Girgiza kanta tace.

" Hmmm!!! To meyasa zanji haushi bayan bani da ikon tursasa makauniyar zuciyarki taso wanda bata so, ke dai kawai tsarguwa kikayi, ni yanzu na sanya miki ido ne, kije kibi Umarnin zuciyarki tunda har yanzu kin kasa yin hankali bana tunanin zakiyi hankali koda nan gaba dan haka kije kiyi abinda kikaga yafi miki sauƙi a rayuwarki tsakanina dake ido koda shawarace na daina baki, kije ki cigaba da son wanda baya ganin mutuncin ki, tunda zurki marar lissafi ne da tunani."

Falmata cike da raunin murya tace.

" Har kullum baki fuskanta ta, kin kasa gane cewa laifin zuciyata ne, ba laifi na ba, ita DOCTOR kawai shine wanda take sannan bata tunanin zata iya haɗa Soyayyar sa dana wani, ki fahimce ni bazan iya Soyayya da wani NAMIJI ba, ba'a iya tilastawa zuciya taso abinda bata so."

Murmushi Maji tayi ta bata amsa da cewa.

" Hmmm!!! Ki daina ɗaurawa zuciyarki abinda ba laifinta ba, domin kuwa ana tilastawa zuciya taso abinda yake alkairi a gare ta, abinda ba alkairi ba kuma dole ta haƙura dashi tabi abinda yafi alkairi a wajen ka, Allah da kansa acikin littafin sa mai tsarki cikin suratul Baqara yake cewa : kutiba alaikumul ƙitalu wa huwa kurhun lakum, wa asa antakrahu shai'an wa huwa kairun lakum, wa asa an tuhibbu shai'an wahuwa sharrun lakum, wallahu ya'alamu wa antum la ta'alamun : an wajabta yaƙi a kanku, gashi kuwa kuna ƙinsa, sau da yawa kukan ƙi wani abu, alhaki kuwa shi alkairi ne a gareku, sau da yawa kuma kukan so abu, alhali kuwa shi sharri ne a gareku, Allah yasan abinda ku baku sani ba.
Misalin Soyayyar da kike yiwa Hassan, wanda babu alkairi a cikin sa, Falmata, duk Soyayyar da akace an ginata bisa ga turbar da iyaye basa so, to wannan Soyayyar dole sai ta samu nakasu a tare da ita, dalili kuwa shine kin saɓawa iyayenki, saɓawa iyaye kuwa babban laifi ne mai girma a wajen Ubangiji, na Tabbata da tun farko da iyayenki suka baki umarnin ki rabu da Hassan, da kin musu biyayya da yanzu bakya cikin wannan mawuyacin halin da kike ciki, abinda Babba ya hango yaro ko ya hau tsauni bazai taɓa hangowa ba, gashi yanzu kin fara ganin raahin bin umarnin iyaye, meyasa bazaki haƙura da. Hassan ba, ki jira alkairin ki, domin kuwa na lura sam babu alkairi tsakanin ki da wannan ɗan tashan wanda baisan darajar manya ba, ki farka daga nannauyan baccin da kike Falmata, ki rabu da wannan ɗan tashan, ki daina tunani da zuciyarki kiyi tunani da ƙwaƙwalwar ki, domin itace kawai zata faɗa miki gaskiya, ita Zuciyarki bazata taɓa gaya miki gaskiya ba, ko yaushe nuni zata miki da abinda tafi ƙawatuwa dashi, musamman irin taki zuciyar da take makahuwa wacce babu abinda take gani, sai Soyayyar mutumin da bai dace da rayuwarki ba ki lissafa da hankalin ki, ki gani, nasan lissafin ki zai sanar dake zuciyarki kaiki take ta baroki inda fitowa take miki wahala.?"

" Ban san ya zan fahimtar dake irin son da nake yiwa DOCTOR ba, rabani dashi wallahi rabani da rayuwata ne, bazan iya ciresa a raina ba, Saboda ba nine na halittawa zuciyata Soyayyar sa ba, kiyiwa Soyayya adalci Maji ki daina alaƙanta ta da tilastawa, domin kuwa ita ba'a iya tilasta mata Soyayya ciro ce daga Ubangiji wanda babu wani mahaluƙin da zai iya tuge wannan tsiron sai ubangin daya dasa shi, ki sani muddun zuciyata tana bugawa da soyayyar DOCTOR, ƙwaƙwalwa ta, bazata taɓa tunani ba, domin kuwa zuciyata ta toshe duk wani hanyar tunanin ta, babu abinda take nuna mata sai Soyayyar DOCTOR, haka zalika, bani da wani lissafi idan ba nasa ba, ina lissafa rayuwata dashi, dan haka zuciyata tayi nisan da bazaki taɓa sauya mata ra'ayin ta ba, Maji ina cikin tsoro da fargaba domin kuwa na yiwa iyayena alƙawarin da bazan iya cika musu ba, tausayin Mama yasa na ɗauki wannan alƙawarin, yanzu ya zanyi bazan iya cika musu alƙawarin dana ɗauka ba."

Ta ƙarisa Maganar muryar ta, tamkar za

Please Login or Register in order to submit comment