Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tashi Falmata tayi ta zauna tare da goge hawayen dake bin fuskar ta tace

" Maji damuwa ai ta zama dole a gareni babu ta yanda zan iya gogeta a zuciyata muddun ba farin ciki na bane ya dawo, nida banza ɗaya nake a wajen DOCTOR baya son koda gani nane Maji, ban san mena masa ba, shi yana ɗaukar laifin iyayena ne yana ɗaurawa a kaina, Ban taɓa jin inda aka ɗaura laifin wani a kan wani ba sai DOCTOR, wallahi maji bana jin daɗin zaman gidan nan duk yanda naso na fahimtar da DOCTOR mu samu masalaha yaƙi fahimta Maji ba dole damuwa ta dameni ba, shiyasa komai na duniya naji ya fita a Raina, makarantar ma naji bana son zuwa saboda koda naje babu abinda zan gane, sai da nutsuwa ake gane karatu Maji, ni kuma bani da nutsuwa."

Shuru Maji tayi tana jin tausayin ƙawar tata, hanu Maji tasa ta gogewa Falmata hawayen ta .

" Hakane ƙawata tabbas akwai ciwo ace mijinka ya juya maka baya, ni lamarin mijinki yana bani mamaki wai duk Soyayyar da yake miki kamar zai haɗiye ki yanzu babu ita ta juye ta koma tsana, kai gaskiya DOCTOR baya ƙyautawa ko kaɗan, amma ƙawata ki cigaba da hkr insha komai yayi zafi zaiyi sauƙi babu abinda bazai wuce ba sai ikon Allah, ki cigaba da masa biyayya kamar da karki fasa, koda yana hantarar ki, bautar Ubangijin ki kike yi, sannan abinda nake so dake ki rage yawan damuwa karki sawa kanki hawan jini, sannan ki koma makaranta shima zai ɗebe miki kewar wata damuwar domin yafi zaman da kike ke kaɗai a gida, insha Allah farin cikin ki zai dawo kuma nima zan tayaki da addu'a ."

" Hakane Maji na gode insha Allah gobe zanzo school, Ya Mama."

" Mama lafiyar ta ƙalau tace ma na gaishe ki."

" Ina amsawa."

" Kawata da alamu dai bakici komai ba tun safe Ko naga kamar kinyi yanayi da mai jin yunwa.?"

Ajiyar Zuciya Falmata ta sauƙe tace.

" Wallahi kaina ke ciwo ban fita falon bama tun safe ina nan kwance wanka kawai nayi."

" To ai kuwa ya kamata ki tashi muje kici abinci sai kisha magani idan yaso ki dawo ki kwanta nasan baza'a rasa magani ba a gidan likita."

" Akwai a Bedroom ɗin sa."

To tashi muje ki ɗauko kizo kisha koda ruwan tea ne sai ki kwanta nima ba jumawa daman zanyi ba, zan shige shagon saloon ne zan wanke kaina "

Tashi Falmata tayi tana cewa.

" Nayi zaton fa wuni zaki min har ina murna, kice kuma tafiya zakiyi gaskiya ban so haka ba."

" Kinga Hajiya tashi muje kisha magani ina kallonki kafin na tafi."

Murmushi Falmata tayi tana tashi tare da cewa.

" To Mama Maji muje."

Dariya Maji tayi sannan ta tashi suka fito falon tare, Falmata Bedroom ɗin DOCTOR ta shige ɗauko magani ita kuma maji ta shige daining table ta haɗawa Falmata tea, Falmata na zuwa maji ta miƙo mata tea ɗin tana cewa.

" Gashi karɓi kisha."

Karɓa Falmata tayi tana kallon Maji cike da ƙauna, domin kuwa ƙawarta ce tun na yarinta tare suka girma komai tare suke yi, Babu wanda yake son yaga ɗaya daga cikin su yana cikin damuwa, suna ɗaukar damuwar ɗaya daga cikin su damuwar su duka, Falmata tea ɗin tasha haɗe da maganin sannan ne maji tace.

" To Allah ya baki lafiya ni zan tafi sai mun haɗu gobe a school dan Allah ki rage yawan damuwa da tunani saboda kare lafiyar ki."

Murmushi Falmata ta saki tare da cewa.

" Ameen insha Allah zanyi ƙoƙari wajen ganin na kiyaye, ki gaishe da Mama."

" Za taji" Maji tace tare da ficewa, Falmata ma Bedroom ɗinta ta shige ta kwanta, bata juma da kwanciyar ba bacci ya ɗauke ta.



Zaune yake a office ɗin nasa, bayan ya ɗan samu nutsuwa na duba patient ne ya ɗaga wayar sa, My dear sister na gani a rubuce, jikin screen ɗin wayar ringing ɗaya AJIRAM ta ɗaga.

" AJIRAM ya jikin Umman dai, yau ban samu na shigo ba, na fito a ƙurarren lokacine gashi kuma ina da wanda zan duba a wannan lokacin ya jikin nata."

Daga can AJIRAM tace.

" Eh to da sauƙin musulunci amma yau tun safe bige-bige take tun ɗazu hankali na yake tashe, gashi ni ɗaya ce Fanna bata nan."

Cikin tashin hankali DOCTOR yace.

" Subabanallah yau kuma bige-bigen ne ya tashi, yanzu ya kenan ko nazo ne."

" A'a ba sai kazo ba da sauƙi domin da na mata hayaƙin maganin nan bacci ya ɗebeta."

Ajiyar zuciya DOCTOR ya sauƙe tare da furta.

" Alhamdulillah, ina zuwa da yamma naga jikin nata ki kula da ita sosai idan kinga abinda bazaki iya ba kiyi kirana."

" Shikenan to sai kazo."

Kashe kiran DOCTOR yayi, yana jawo wata farar takadda gabansa, Nocking ɗin ƙofa yaji anyi.

" Yes come."

Buɗe ƙofar Maji tayi ta shigo da Sallama, murmushi DOCTOR yayi ya amsa sallamar tare da cewa.

" Yau babbar baƙuwa ce kenan nake da ita."

Dariya Maji tayi tana zama tace.

" Ga dai ƙaramar baƙuwa, Ya aikin."

" Aiki Alhamdulillah amma ba daɗi, kwana biyu kin ɓuya bana ganinki ko a online ne."

Murmushi Maji tayi tace.

" Dama aini ba gwanar hawa online bane, amm DOCTOR wajen ka fa nazo Allah yasa na samu lokacin kasancewar nazo maka lokacin da bai dace ba lokacin aiki."

Murmushi DOCTOR yayi yace mata.

" Aikuwa kin iya zuwa a Sa'a domin kuwa yanzu ina Free ne aikin yayi sauƙi."

" To Alhamdulillah haka nake so, amm DOCTOR nazo ne game da Case ɗinku da Falmata, a gaskiya DOCTOR baka kyautawa Falmata domin kuwa kana zaluntar ta da yawa kaga kuwa yanda Falmata tayi baƙi ta rame ta fita hayyacin ta, sai kace ba Falmata ba, wai dan Allah DOCTOR na tambayeka ashe dama laifin wani yana shafar wani? Taya dan iyayenka sun haifeka sai ace halinku ɗaya ko ka manta da cewa nacacce yana fitowa a cikin rayayye haka kuma rayayye yana fitowa a cikin macacce, idan har mukace zamu dinga hukunta yara da laifin iyayensu, to wallahi mu jira sakamakon Ubangiji, dan Allah ka gyara zamantakewar ka da matarka, domin kuwa Allah ya baka mace ta gari wacce ko wani namiji yake neman irinta domin kuwa irinsu wuya suke yanzu bako wace mace bace take iya juran wulaƙanci daga ɗa namiji, dan koni nan bazan iya jura ba, dan Allah DOCTOR karka bari Falmata ciwo ya shigeta bata cancanci wulaƙanci daga gareka ba."

Shuru doctor yayi yana sauraron Maganar Maji, sanda ta gama kafin ya kalleta yana sakin murmushi yace.

" Gaskiya Maji son kanki yayi yawa wato nine ma na zalunce ta, ba su bane suka zalunce mu, hmmm !! Baki san yara suna gado halin iyayensu ba kenan, to ki sani yau yaro yana gadon halin iyayensa, kinga Maji Nifa bazan iya kyautatawa Falmata domin kuwa idan na kyautata mata dole iyayenta zasuji daɗi ni kuma Bana buƙatar jin daɗin su, nafi buƙatar na gansu cikin ƙasƙanci da tashin hankali tabbas macacce yana fitowa daga cikin rayayye haka kuma rayayye yana fitowa daga cikin macacce, wannan faɗin Ubangiji ne, amma ana gadon hali, bazan miki karya ba Maji bazan iya dawo da farin ciki na da Falmata ba kiyi haƙuri kawai lokaci kawai nake jira da zan bata takaddar sakinta kowa ya kama gabansa."

Maji wani irin haushin DOCTOR taji danne ɓacin ranta tayi tace.

" Saki fa kace DOCTOR, to ina soyayyar da kace kana mata a baya ina wannan soyayyar da kuke yiwa juna tamkar ɗaya zai haɗiye ɗaya, ina take, DOCTOR baka da tabbacin cewa iyayen Falmata sune suka ɓatar da Baba da Aunty Jalila Zargi kawai kake yi, baka da tabbas, DOCTOR na zo nan ne na faɗa maka gaskiya ka dawo hayyacin ka kafin lokaci ya ƙure maka Falmata tana maka biyayya tana kuma shanye wulaƙancin da kake mata kabar ganin tana sonka , wallahi duk sanda ka cikawa Falmata ciki DOCTOR zata bushe maka ta daina jin tsoron ka, kazo kuma kana neman tanƙwarata ta kasa tanƙwaruwa, kashi ma yazo ya fika daraja a gareta, ka dawo hankalin ka kasan me kakeyi kafin lokaci ya ƙure maka bana so kazo kana danasani."

Dariya DOCTOR yayi yana ƙarewa Maji kallon baki da hankali kafin yace.

" Kinsan Hausawa sukace so tsuntsu ne yakan tashi daga wannan reshen ya koma wata, to haka nima babu soyayyar Falmata a cikin zuciyata, bazan taɓa danasani ba danna rabu da Falmata irin tsiya."

" Duka ai irin naku ɗaya ne da ita domin kuwa jini ɗaya ne yake yawo a jikinku, idan irin tsiya ne ita kaga kuwa ai irin kune, idan har haka soyayya take da juyawa masoyinta baya to tabbas soyayya hatsari ne, DOCTOR ka sani cewa idan ka ci amanar Falmata Allah ba.........."

Dakatar da Maji DOCTOR yayi yace.

" Ya isa haka Maji ina ganin mutuncin ki bana son mukawo matakin da zan gaya miki maganar da bata dace ba, mubar maganar haka idan ita kaɗaice ta kawo ki, kina iya tafiya."

" DOCTOR korata kake daga office ɗin ka saboda na faɗa maka gaskiya."

" Saboda kin faɗa min son ranki dai, ba gaskiya ba."


" Okay to na gode sai anjuma Allah ya baka hakuri idan har a cikin maganganu na akwai masu zafi."

Ta ƙarasa maganar tana nufar hanyar fita DOCTOR dakatar da ita yayi yana zaro kudi daga aljihun sa dubu biyar ya ƙirgo yace.

" Ga wannan kiyi kuɗin adaidaita, Ib baya nan ya fita dana basa kay ya mayar dake."

" Na gode bana buƙatar kuɗin ka, ina da na nafef, ka riƙesu zasu maka amfani."

" Haushi na kikaji da bazaki karɓi kyautar dana baki ba."

Murmushi Maji tayi tace.


" Akan me zanji haushin ka?"

" Akan kina zargina da zaluntar ƙawarki."

" Wannan ba zargi bane abinda yake a zahiri ne."

Tana faɗin haka ta fice da sauri, DOCTOR SAIF da zai shigo office ɗinne suka ci karo da Maji, ko kallon sa batayi ba ta shige, shi kuwa kallon mamaki ya bita dashi a ransa ya furta lafiya, yarinyar da duk inda ta ganni sai ta gaishe ni munyi wasa da dariya kafin a rabu, shigewa office ɗin yayi da Sallama ya zauna yana cewa.

" Me yake faruwa.?"

Ɗago kansa DOCTOR yayi a taƙaice yace.

" Meka gani."?

DOCTOR Saif amsa ya basa da cewa.

" Abinda idona ya gani, kai Malam meya sami Maji naga ta fita daga office ɗin nan cikin ɓacin rai."

" Baka tambayeta daka ganta."

Tsuka DOCTOR Saif yaja tare da cewa.

" Bana son rainin hankali malam ya ina tambayar ka kana ƙoƙarin mai dani shashasha................."



08147537180


Kuyi hkr yau ban samu nayi Editing ba, sannan ku sani cikin adduar ku zan shiga axam.


Vote
Share
And comment



*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN*✍🏻


*(UMMU NASMAH CE)*
[8/29, 8:59 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻



❤️ *Love and romantic and funny story* ❤️



*Na*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.


Bari nayi rawa da girgiza son so nake muku my FAN'S gaskiya naji daɗin yanda kuka amshi wannan book ɗin hanu biyu, ko wani group na shiga ruwan sharhi nake gani gaskiya naji daɗi sosai😘😘😘😘



*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Book One*

*Page 11 to 12*

*____________________________________*




_______✍🏻 Murmushi DOCTOR ya saki yana kallon DOCTOR SAIF kafin yace.

" Kaima dai kasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, wai tazo min da wata banzar magana ne akan wannan yarinyar Falmata, wai nine nake zaluntar Falmata kai kaji wata banzar magana da son kai irin na Maji."

Taɓe bakin sa DOCTOR SAIF yayi yana hararar DOCTOR yace.

" Sai ka mata rashin mutunci ko nasan amsar bazata wuce haka ba."

" To akan me zan mata rashin mutunci meta min, amsa kawai na bata daidai da Maganar ta."

" Hmm!!! Haba DOCTOR halinka ne ban sani ba wannan maganar kuma ai wanda bai sanka bane zaka faɗawa, shakka babu ka mata rashin mutunci, Kuma koda bansan abinda tazo maka dashi ba, nasan gaskiya ta faɗa maka tabbas kana zaluntar matar ka DOCTOR, kuma Falmata bai kamata ta samu wannan mungun sakamakon a wajen ka ba ka mata yayi ace kana riritata kamar ƙwai, ka sani Falmata fa ta soka a lokacin da baka da komai, sisin da zaka kashe, baka dashi sai an baka, a wannan lokacin idan baka manta ba samari ne masu kuɗin gaske suke zuwa wajen ta, amma taƙi su tace lallai kai take so, duk da a lokacin kakan nunku basa son Auren zumunci saboda gurɓacewar zumunta, haka Falmata ta dage sai da aka muku Auren, sanda gomnati ta ɗauki nauyin karatun mu haka yarinyar nan tayi haƙuri tana kallo ka tafi India ta jiraka a ɗakin mahaifiyar ta har tsawon shekaru bakwai ka gama karatun DOCTOR ɗin ka, ka dawo kayi sati ɗaya rak ka koma sakamakon aikin da suka ɗauke ka acan, nan ma kayi shekara biyu sannan ne ka dawo ka ɗauke ta kuka koma tare kafin daga baya ku dawo gida Nigeria, yanzu DOCTOR wannan matar data yimaka wannan soyayyar itace abar wulaƙantawa a wajen ka, ya kamata kafin ka yanke mata hukunci ka dinga tunanin baya, wallahi kaji tsoron Allah, ka daina azabtar da baiwar Allah."

DOCTOR ɗago kansa yayi yana duban DOCTOR SAIF yace.

" Gori kake min kenan, to naji tamin halacci sai kuma akace su cuceni ko, to ban riritata kamar ƙwai ɗin ba, kaga DOCTOR SAIF dan Allah tashi ka tafi office ɗin ka, kaima idan wannan maganar zaka min na gode."

" Gaskiya ne ai baka so, shiyasa zaka koreni, Allah ya shirya ka, amm jiya ka iso kuma na fita bamu haɗu ba, Ib ya sanar dani cewa wai a mayar da matar nan opression room."

" Eh nine nace a maida ta saboda ya sanar dani cewa, sun bata ruwa tasha wai har cikin nata ya kumbura."

" Kai Ib ma dai wani lokacin shashasha ne, bafa tasha ruwan ba, sun dai ɗauko zasu bata sai Allah yasa na shigo na hana su bata, kuma matar tana da tunbi ne shiyasa ina ga zaiga kamar cikin ya kumbura."

DOCTOR cewa yayi.

" Ehh ya faɗa min jiyan dana zo, harma naje na duba ta DOCTOR SAIF bari na gudu ina son zanje na dubo jikin Umma."

Tashi DOCTOR SAIF yayi tare da cewa.

" Okay nima bari na shige office ɗina."

Tare suka fito DOCTOR SAIF ya wuce shima DOCTOR ya shige parking space ya ɗauki motar sa ya fice daga Asibitin ya shige family Hause ɗin nasu, kamar ko yaushe ƙofar gidan cike yake da mutane musamman dattawa, shi kuwa SARKIN yana zaune a tsakiyar su, taɓe bakin sa DOCTOR yayi ya ƙaraso wajen tare da sunkuyawa suka gaisa da dattawan ɗaya bayan ɗaya, sai dai Sarki ko YALLAƁOI zance bai samu kallon mutunci a wajen DOCTOR ba bare kuma gaisuwa, haka shima bai kulasa ba gudun ya tsinkasa a cikin talakawan sa, yau dai tsakar gidan babu taron gulma domin kuwa babu kowa sai yara dake famar wasansu, sashin su ya wuce da Sallama ya shiga, Hajjo dake tsaye bakin randa tana ɗibar ruwa ne ta amsa masa da.

" Ameen wa'alaikumussalam , ɗan halak kaƙi ambato, yanzu nake tambayar BULAMA kai yake cemin shima yanzu yake tambayar BELLO kai."

" Kice kamar yadda nima nake neman ki kenan, Ina kuka haɗu da Bello shima nemansa nake."

" Yana cikin ɗakin ka ƙarasa bari na kaiwa AJIRAM ruwa bayi, ina zuwa."

Shigewa DOCTOR yayi cikin ɗakin Umman, bata nan da alamu sun Kaita tollet ne wanka, zama yayi gefen katifa tare da miƙawa Bello hanu yana cewa.

" Bawan Allah jiya na kiraka shine baka ɗaga ba kuma baka biyo kira na ba."

Dariya Bello yayi tare da cewa.

" Bana kusa ka kira nazo kuma zanbi kiran taƙi shiga, ya aikin."

" Aiki Alhamdulillah, jiya AJIRAM take sanar dani cewa kunyi magana akan wani mai magani da yake ƙauyen BINISHED ko."

" Eh tabbas munyi magana, kuma gaskiya ana samun dace sosai a wajen sa, dan akwai wani mutum a bayan layin mu, shima shigen irin ciwon Umma ne, wallahi da aka kaisa can ya warke sosai."

" To amma Bello ina dai ba ɗan tsubbu bane dan gaskiya bana son muje wajen boka."

Dariya Bello yayi yace

" A'a wallahi ba ɗan tsubbu bane malami ne na gargajiya sannan kuma ruƙiyya, babu tsubbu a tattare dashi."

Numfashi DOCTOR ya sauƙe tare da cewa.

" Okay ba damuwa insha Allah zamuje, kamar Ranar asabar tunda ranar ce weekend, to amma waye zai mana jagora kasan dai ni ban taɓa shiga cikin wannan ƙauyen ba."

Bello cewa yayi.

" Zamuje tare nasan ƙauyen Saboda tare mukaje dasu, kuma malamin ya sanni sosai, wannan ba matsala fatan dai Allah yasa mu dace."

" Ameen ma je Asabar ɗin, Ina BULAMA ne kam kwana biyu bana ganin sa."

" Ai kuwa yanzu kikayi saɓani, dan bai juma da fita daga gidan nan ba ka shigo."

" Okay." Doctor ya furta a taƙaice, AJIRAM da Hajjo ne suka shigo riƙe da Umma sun mata wanka kwantar da ita sukayi, DOCTOR duban mahaifiyar tasa yayi da idanunta suke buɗe kamar zaka mata magana ta amsa sai dai ina babu baki, hanunta ya riƙe tare da cewa

" Sannu Umma Allah ya baki lafiya."

Duban Hajjo yayi yace.

" Hajjo alfarma nake nema a wajen ki, ina son zaki dawo ki karɓi AJIRAM jinyar Umma, ita ta koma gidan mijinta ta kula da yaranta, tunda kinga ke kina zaune a gida ba aure.''

Murmushi Hajjo tayi tace.

" Haba Hassan har sai ka nemi alfarma a wajena dan kawai na yiwa Umma jinya nima fa uwata ce Umma babu abinda bata minba a rayuwata, dan haka babu komai AJIRAM ta koma gidan ta, ni zanyiwa Umma jinya."

Ajiyar zuciya DOCTOR ya sauƙe cike da jin daɗi yace.

" Hakane na gode Hajjo, to ke Kuma AJIRAM, gobe zaki koma gidan ki, idan Hajjo ta ɗauko kayan ta, sannan ranar Asabar zamuje wajen mai maganin da Hajjo zamu tafi karki ce zaki zo ki zauna a gidan mijinki idan yaso daga baya sai kije ki dubata."

Nisawa AJIRAM Tayi tace.

" Shikenan yaya Allah ya kaimu goben."

Da ameen ya amsa, Hajja ce ta shigo da Sallama, amsawa sukayi DOCTOR ya ɗaga ido ya kalleta yana sakin murmushi, Hajja kusa da DOCTOR ta zauna tana sakin masa dundu a baya tace.

" Ja'iri jiya da ka gudun yanzu bamu haɗu bane."

Dariya DOCTOR yayi tare da cewa.

" Kinga Malama Hajja, ni bana son yawan Magana karki dameni."

Dariya Hajja tayi tana duban Umma tace.

" Sannu Yamuram kina fama da bautar Ubangiji, Allah ya baki lafiya Allah ya sa zakkar jiki ne" kallon DOCTOR Tayi tace.

" Hassan yanzu babu inda za'a kai Yamuram haka za'a barta a gida, nifa gaskiya bana jin daɗin zaman ta haka ba tare da annemi wani me magani an Kaita ba , duk da kuna karɓowa amma dai ya kamata a ƙara dagewa."

DOCTOR cewa yayi.

" Hajja yanzu ma maganar da muka gama kenan munji labarin wani mai magani a ƙauyen BINISHED zamuje can Ranar asabar zamu kaita."

" Yauwa to Alhamdulillah hakan yafi ai"

Hajjo ce tace.

" Sannu Hajja ina kwana."

Murmushi Hajja tayi tace.

" Hajjo lafiya lau ya uwar taki Merama"

" Lafiyan ta lau tana gaishe kuma."

" Muna ansawa da kyau,"

AJIRAM ma gaida Hajja tayi tana cewa.

" Ina zuwa haka Hajja naga kinsha sari, unguwa ne."?

" Gidan wannan ja'irin wannan wannaki zanje na dubo Falmata, kwana biyu shuru babu labarin ta, tashi ma mu tafi ka sauƙeni."

Hajja ta ƙarasa maganar tana jan kunnen DOCTOR, doctor bai kalli Hajja ba yace.

" Da banzo ba kuma waye zai kaiki.?"

Dariya Hajja tayi tace.

" Kuɗina ne zasu kaini."

DOCTOR cewa yayi.

" Yanzu ma kuwa sai kuɗin naki su kaiki domin kuwa ni ba gida na nufa ba asibiti zan koma."

Hajja cewa tayi.

" Baka isa ba wallahi dole sai ka kaini idan yaso ka juya asibitin."

Juyowa yayi ya fuskanci Hajja yana ƙare mata kallo yace.

" Zaro min idanun da kike ne zaisa naji tsoron ki na kaiki, ke dai malama bini a hankali kawai na kaiki."

Tare suka saka dariya Hajja tace

" To naji angon Hajja, ka dai san bama faɗa ko, tashi mu tafi uban masu gida."

Dariya DOCTOR yasa tare da miƙewa yana cewa AJIRAM.

" Ina FANNA taje ne ban ganta ba.?"

AJIRAM cewa tayi.

" Na aiketa gida na, amma ina ga tama kusa dawowa."

Okay ya amsa yana cewa Bello.

" Sai Asabar ɗin ka shirya zan kiraka, Hajja muje na sauƙe ki na wuce."

Tashi Hajja tayi suka fice mota DOCTOR ya buɗe mata ta shiga sannan shima ya zaga ya shiga yaja motar suka tafi.


DOCTOR hom ya danna a ƙofar gidan mai gadin ya fito da sauri ya buɗe get ɗin, a compaunt ɗin gidan DOCTOR ya tsaya tare da buɗewa Hajja yace.

" To Bismillah fita ni juyawa zanyi."

" Kai!!! Wai dama da gaske asibitin zaka koma."

Dariya DOCTOR yayi yace.

" Au dama kinyi zaton wasa nake miki, asibiti zan koma ban gama aikina ba yaushe zaki koma na turo azo a ɗaukeki."

" To Allah ya tsare a dawo lafiya, eh to ina ga zuwa ƙarfe biyar."

Ta ƙarasa maganar tana fita da Allah ya kaimu DOCTOR ya amsa sannan ya juya ita kuma Hajja ta shige cikin gidan..........





Vote
Share
And Comment




*ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*
[8/30, 7:26 PM] TYPING DOCTOR HASSAN💊💊💊: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻



❤️ *Love and romantic and funny story* ❤️



*Na*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*



Marubuciyar nan taku ta *INDO A BIRNI*


Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.


Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.


Bari nayi rawa da girgiza son so nake muku my FAN'S gaskiya naji daɗin yanda kuka amshi wannan book ɗin hanu biyu, ko wani group na shiga ruwan sharhi nake gani gaskiya naji daɗi sosai😘😘😘😘



*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*

*Book One*

*Page 11 to 12*

*____________________________________*




_______✍🏻 Murmushi DOCTOR ya saki yana kallon DOCTOR SAIF kafin yace.

" Kaima dai kasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, wai tazo min da wata banzar magana ne akan wannan yarinyar Falmata, wai nine nake zaluntar Falmata kai kaji wata banzar magana da son kai irin na Maji."

Taɓe bakin sa DOCTOR SAIF yayi yana hararar DOCTOR yace.

" Sai ka mata rashin mutunci ko nasan amsar bazata wuce haka ba."

" To akan me zan mata rashin mutunci meta min, amsa kawai na bata daidai da Maganar ta."

"

Please Login or Register in order to submit comment