Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sonta, inda yana sonta dole zai fadawa Abbanta ai, kamar yanda inusa yanemi izni agida, to Amma meyasa yake zarya awajanta? Wata zuciyar tace" zumunci "

Da wannan tunanin na zuciyarta, yarinta tasa tadinga yaudaran kanta cewa zumunci ne yake kawo Shahaab wajan ta.

Ko kadan acikin Yan kwanakin Nan bata ma son ayi mata maganar inusa, gaba daya Shahaab yashiga cikin qwaqwalwar ta yayi mata format din komai,kasancewar ta yarinya qarama, babu cikakken Hankali, saita dauki yarda Dari bisa Dari tabashi, ta yarda dashi yanda baya zato.

Washe gari kuwa tad'auki azumin sitta shawwal, Hajja data gama yin dumamen tuwo, tazubo musu tace "me sunan qawa tun dazu kin shiga daki kinata hada kan takardu kokema littafi Zaki fara rubutawa kamar takwarar ki?"

Dago kanta tayi ta kalli Hajja sannan tace "littafi take rubutawa takwarar tawa?"

"littafi kuwa, tun kafin muyi candy haka zakiga tatara Yan ajinmu tana karanta musu Bayan tagama rubutawa, idan akwai inda tayi kuskure saisu gyara mata, inajin su Alokacin nikam daukar komai nake shirme"

Aisha tace "Bayan kinqi nunamin photon ta"

"me kike ci nabaka na zuba? Zan nuna miki ita ai, yanzu de taho muci tuwon Nan tukunna"

Yatsina fuska tayi tace "saide kici, nikam azumi nake"

Cikin sauri Hajja tace"azumin me?"

"sitta shawwal"cewar Aisha

" wanne irin sitta shawwal? Kinga... Ba sitta ba, ko kamsa ne bazanyi ba, kema inajin bakya jin ranar da ake zubawa ne shiyasa, ingama Ramadan cif, sannan inzo inyi wannan?"

Aisha ta kalleta kawai ta girgiza Kai batare da tayi magana ba

Bayan ankira sallar magrib Aisha Tasha ruwa sosai tayi wa Shahaab addu'ah, Amma addu'ar Tata tafi karkata ne akan Allah yabashi haihuwa idan yayi aure, kasancewar ya6oye mata cewa yana da aure, shiyasa koda wasa batace Allah yabawa matarsa ciki ba, fatan ta idan yayi auren Allah yabashi haihuwa Mai Albarka.
Washegari Hajja ta dauki azumin sitta shawwal, babu Wanda ta fadawa tana azumi, da azahar Ummah takawo mata abinci saitace Sai anjima zata ci, kunun Ayane a gabanta tana hadawa, saida ta zubasu acikin jarkoki sannan tasaka su a fridge da rufe.
Wani yaro ne yayi sallama yace "Wai abani kunun Aya na Dari bakwai"

Cikin murna Hajja tatashi, tadauko leda babba, ta zuba masa Yan Dari-Dari guda bakwai tabawa Yaron, shikuma yabata dubu daya, tad'auki canji tabashi tana cewa "idan sun shanye kadawo min da jarkokin kaji"

Yaron ya amsa, sannan yafice daga gidan.

Baifi minti ashirin da tafiya ba ya dawo yace "Wai abani pure water na nera ashirin"

Hajja tace "babu pure water yaqare, Ina jarkokin da'aka Sai kunun Ayar?"

Yaron yace "sun tafi dasu"

Cikin sauri jabir dayake zaune agefe yace "Alhamdulillah... inda nine ma Yan hamsin-hamsin zan siya yanda zaki Rasa jarkokin dayawa, haba Adinga maganar jarka de, kasai abu ai shikkenan jarka tazama taka"

Kafin Hajja tayi magana wani Almajiri yashigo da wasu jarkoki a hannunsa yace "Hajja ga jarka inzaki siya"

Jarkokin ta karba tafara dubasu, saida tagama dubasu tas sannan tace "wannan ai duk irin jarkokina ne dasuke 6ata, waye yabaka?" (=�F�<���
@&�=��)

Yaron yafara rantsuwa yace "wallahi abakin kasuwa na tsinto su, banaki bane"

Cikin masifa tace "Kai jeka da abunka, sunyi qazanta dayawa, bazan siya ba, a tsinto jarkoki abakin kasuwa a kawowa Hajja mahaukaciya tasiya, debe su daga gabana bazan siya ba"

Aisha ta futo daga d'aki kanta babu dankwali, Sai qyalli gashin Nata yake kasancewar tashiga rana, ta kalli Hajja tace "keda kikace duk irin jarkokin kine?"

Hajja tace "mesunan qawa Ina kika samu wannan abun daure gashin? Sai daukan ido yake daga Gani yanada tsada"

Cikin ko'in kula tace "Walida ce tabani"

Hajja tace "tunda babanta yanada Hali zata Iya baki wannan Kam, jeki kar6omin wayata a gidan Jummai, dazu nabayar takaimin maqotansu naji sun kunna inji, 95 ne Dani shine nakeso subatse min ita"

Jabir yace "Hajja waya a 95 kika Kai wajan caji?"

Cikin masifa tace "to Ina ruwanka? Wayar nan fa saboda mesunan qawa nake kaiwa caji, idan tafara waya da inusa Kai kace akansu aka fara soyaiya"

Jabir bai sake magana ba, yaga yau Hajja masifa takeji, komai akayi mata Sai masifa, baisan azumi take ba (>�#�)

Aisha kuwa hijabi tasaka, sannan taje ta kar6o wayar tabawa Hajja, Hajja tana Gani tace "ya haka? Menake Gani kamar 50 percent?"

Aisha tace "Wai data cikane shine jikan iya jummai yake kallo kafin kizo ki Kar6a"

Hajja ta Jinjina kanta tace "Amma kuwa jummai anyi marar zuciya da bazata iya futo na futo da jikokin ta akaina ba"
Ta juya ta kalli jabir tace "ga wayar inzaka siya kawo dubu biyun kawai"

Jabir yace "banaso akai kasuwa"

Cikin jin haushi tace "ai shikkenan"

Tajuya ta kalli Aisha tace "me sunan qawa ki shirya kije kano gobe, kisiyomin kayan hadin kunun Aya a singa, idan kikai wa su Malam kwana biyu saiki dawo" (malam mahaifin Hajja)

Tace "to Hajja Allah yakaimu"


******

Washe gari da yamma Aisha tatafi kano, dayake sun dan kwana biyu ba suje Garin ba Sai take murna da tafiyar Tata, gab da magrib ta qarasa kano, kasancewar a yankaba baban Hajja yake, kawai napep tashiga aka kaita har gida, malam da matarsa guda daya kishiyar mahaifiyar Hajja, dayake mahaifiyar Hajja ta rasu, Sai kishiyar ta, sunyi murna da zuwan Aisha, Fati jikar qanin Hajja datake zama a gidan tana tayasu Dan aikace aikace Nan da Nan ta janye Aisha da surutu, dayake Dama akwai Sabo a tsakanin su, Bayan sunci abinci Nan suka shige daki suka fara zancen samari, Fati tace "Aisha Ina samarin ki, nasan yanzu ankusa aurenki, tunda ku ba'a barin yarinya ta girma sosai kamar Nan"

Aisha tace "samari suna Nan, ni besan ma nataho ba, saide Hajja tafada masa idan yaje gida"

Faty takama ha6arta tace "tafiya babu yiwa saurayi sallama? Anya kwa dashi za'ayi?"

Dariya Aisha tayi tace "ke Ina naki saurayin?"

"Auwal yana Nan Shima, ai Yanzu tunda kinzo, zan kirashi yazo ku gaisa,"

Aisha tace "to Allah yakawo shi lafiya, yawwa Fati nikam in tambayeki mana, wata qawata ce tanada saurayi, to agida ansan shi, Kuma tana sonsa da farko, to Kuma Sai wani mutum yazo, batasan ko waye ba, Amma shi Dan maiduguri ne, duk Bayan kwanaki saiya kawo mata ziyara, Kuma har kudi yake bata, to seta fara tunanin sa, Kuma fa bece yana sonta ba, Wai yafi so kawai su zauna tare yadinga kallon ta, to dan Allah me hakan yake nufi"

Fati tayi fari da idonta cikeda yarinta kasancewar batafi Aishan shekaru ba tace"toshi meyasa ba zaije gidansu yace yana sonta ba?ai babu zumunci tsakanin mace da namiji, inde namiji yanason yarinya da gaske to zakiga wajan mahaifin yarinyar yake fara zuwa, saboda haka Ita qawar Taki, tace masa tanason wancen Wanda Yan gidansu suka sanshi, Shima tace masa inde yana sonta yafuto"

Cikin sauri Aisha tace"to ai bece yana sonta ba, itace take sonsa "

Fati tace" rainin wayo ma, Kuma baya sonta yake zuwa wajan ta? kawai idan ita tana sonsa zata Iya auren sa, tayi wuff dashi kawai "

Dariya sukasa, Aisha tace"ke babba nefa"

Fati kuwa cikin rashin kulawa tace"Babban,ai anfi yimusu shagwa6a, kiga sunata siyo Maka abinda kakeso"

Aisha tace"to shikkenan zan fada mata"

Fati tace"kifada mata wallahi"
haka suka kwanta bacci gaba dayansu daga ita har Aishan babu me hankalin da zaiyi tunanin meyasa to namiji zai dinga zuwa wajan ka kawai yana 6ata Maka lokaci shibece yana sonka ba, shibe futo fili yabari iyayen yarinyar sunsan dashi ba, itama fatin dayake yarinya ce kwata kwata bata gane cewa Labarin da Aishan tabata ba'akan qawatar Aishan ne ba.

******

Tsaye yake ahabar gidan nasa, tunda ya dawo daga sallar la'asar baifi ta ko'ina ba kasancewar yau juma'ah, Sanye yake da wando three quarter Sai Riga yar qarama wadda tasa farar fatarsa futowa sosai,sojoji Sai zagaya gidan suke suna zare ido, Bluetooth ne amaqale a kunnan sa yana magana da Ramadan, ahankali cikin qasa qasa da murya yace "ok saika qaraso"

Ajiyar zuciya yasauke yazira hannayensa cikin aljihun wandon nasa, sannan ya qarasa wajan wata yar qaramar tumfa da aka qawata ta da kujeru masu kyau, lemuka ne a ajiye awajan da ruwa dakuma fruit, Sai wata wayar tasa datake ajiye awajan, zama yayi tareda Dialing number Aisha, yadade baiji shirmanta ba, yanaso ya ganta yajita akusa dashi, fiyeda yanda yake son jin muryarta, yaga alama idan bashine Yakirata ba, ita bazata kirashi ba, yana kira Alokacin wayar tana hannun me ita, Hajja ta d'auka tareda sallama, jin ba muryar Aisha bace yasa yayi sauri yakashe wayar, yana d'ago wa yaga Ramadan ya qaraso, hannu yabashi suka gaisa, sannan yace "nasamu saqo ta Email dina Gwamnatin kano tana gayyata taron daza'a yi na Yan kasuwa, sannan akwai Daurin auren wata yarinya da mahaifin ta yake aiki a qarqashin hukumar mu dake jihar kano, mahaifin yarinyar ya turomin saqo cewa yanaso inyi masa waliyin yarinyar, so Naga duk rana daya za'a yi, shine nakeso ka rakani"

Ramadan yace "ok babu damuwa ai, yaushe ne tafiyar?"

"gobe insha Allah"

Ramadan yace "Allah yakaimu"

Fork ya dauka yad'auki yankakkiyar pineapple din dake gabansa, cikin aji yake taunawa kamar bayaso, sannan ya kalli Ramadan dake tsiyaya ruwa a cup yace "Naje Jigawa"

Ramadan batareda daya kalli Shahaab ba yace "eh aika fadamin kaje saboda kaji sunan yarinyar Nan ko?"

Shahaab yace "nakoma" (=�
�)

Cikin mamaki Ramadan yace "Tofa, yaushe?"

Kafadarsa yadaga alamun rashin damuwa yace "kaide tunda nacema naje, ai shikkenan, dole Sai kaji ranar?"

Murmushi Ramadan yayi yace "a a babu dole, amma wannan Karon zuwa kayi domin kaji shekarun ta nawa ko?" (>�#�)

"no, tacemin tanason biro, shine naje nakai mata"

Cikin sauri Ramadan yace "yanzu saboda biro ka6ata kudin jirgi kawai kaje kakai mata kadawo?"

"to ai tana sone, Dame zatayi rubutu idan bankai mata ba?"

Ramadan ya jinjina Kansa, tsananin mamaki ya hanashi magana, shikam zai so ganin wannan yarinya, gaba daya tatafi da hankalin Shahaab, ya tabbatar inda ace bai bashi shawara ya6oye mata Kansa ba, da tuni iyayen yarinyar da'ita kanta yarinyar sun dade a Abuja, idan kayi masa magana ko sonta yake saiyace shi temakon ta yake, koma wacece ba qaramin so yake mataba, idan kuwa ya aure ta,Toya tabbatar Sai abinda tace, saboda ko lokacin dayake neman munirat, baiyi wannan haukan ba, fisabilillahi saboda biro?(>��)

Ajiyar zuciya yasauke sannan yace "gaskiya Abokina kanason yarinyar Nan"

Cikin sauri yace "no, kawai de birgeni takeyi, tana birgeni sosai gata yar qarama, Amma tanada abubuwan more rayuwa najin dadin aure"

Ramadan ya katse shi da cewa "to tunda hakane mezai Hana ka aureta? Abubuwan dakake fada tana dasu saika more abunka Kai kadai?"

Kai tsaye yace "munirat fa?"

Haushi ne yakama Ramadan, baisake ce masa komai ba, saiya Dauko masa wata hirar, wadda ta danganci aikinsu(=��)


******

Washe gari asabat fati tatafi islamiya, Kuma basa tashi da wuri Sai karfe hudu da rabi, Aisha datake San tafiya jibi ta kalli malam shida matarsa tace "Baba malam nikam zanje insiyowa Hajja saqonta, jibi nakeso natafi"

Malam yace "to ai Zaki de gane ko?"

Murmushi tayi tace "zan gane mana, ai wajan bashida wahala"

Kudi yadauka yabata yace "to ga kudin adedeta, saikin dawo"

Sallama tayi musu, sannan ta shirya cikin wata doguwar Riga ta atamfa, tasaka hijabi sannan tatafi, tun kafin tafiyar su tayi nisa taga Garin Yacika da goslow, gashi de tafiyar bawata me Nisa bace Amma sun kusa awa daya a hanya, Dan adedetan ne yasaki tsaki yace "wannan hanyar akwai go slow sosai Bari mu sauya hanya"

Cikin damuwa Aisha tace"ni banaso ma karfe shida tamin a waje wallahi, da nasan haka Garin yake da go slow da tun safe nafuto nayi abinda yakawo ni"

Dan sahun bece mata komai ba,ya sauya hanya, Shima dakyar suka qarasa, bata dade awajan ba ta siyowa Hajja duk abinda take buqata, sannan tafara neman abun Hawa, tun tana tarewa harta Dena, saboda duk Wanda tatare saide yayi gaba yabarta, haquri tayi kawai tafara tafiya da qafar ta batare da tasan hanyar dazata kaita gida ba, tana cikin tafiya harta gaji ta nemi waje ta zauna, gashi yamma tayi, kowa nema yake yatafi gida, wani me adedeta ne ya tsaya yace "yanmata Ina zakije?"

Fada masa tayi, saiyace "gaskiya hanyar akwai go slow saide musauya hanya idan zakije shigo"

Cikin sauri tace "inde zaka kaini gida ai shikkenan"

Cikin gajiya ta shige cikin adedetan, sun fara tafiya kenan ya tsaya ya dauki wani fasinja, irin cikar da hanyar yayi ne yasa kowa Sai tsaki yake saki, Aisha taga duk hanyar dasuka bi motoci ne da adedeta suke layi babu wadatacciyar hanya, cikin 6acin rai tace "Wai meyasa yau Garin Yacika da yawa ne?"

Dan sahun ne yace "manyan qasar ne suka shigo Garin, gaba daya sunzo sun haddasa mana cunkoso agari, tun safe jiragen sama suke yawo agarin Nan, idan wannan yatashi Sai wannan ya sauka"

Daya fasinjan ne dayake gefen Aisha yace"Eh wallahi, Wai manyan Yan kasuwa ne suke taro, Kuma Dama yau din akwai aurarraki da'ake yi"

Aisha batace komai ba, saida suka zo wucewa ta wani layi taga gaba daya anhade motocin a hannu daya, ankashe daya hanyar, Dan sahu yace "to munyi gudun Gara.... Muda muka guji go slow kaga ashe gidansa mukazo, ita wannan hanyar ma ai kwata kwata ba'a bin dayan hannun"

Dayan fasinjan yace"Eh wallahi ance shugaban EFCC Mahmud Wakili aka sauka a daya daga cikin gidajen, Wai saboda bayason hayaniya shine aka Hana wuce wa ta dayan hannun gaba daya"

Gaban Aisha ne yafadi,cikin faduwar gaba tace"to meyasa ba zaije hotel ba tsakani da Allah Sai Nan hanyar"

Fasinjan ne yace "ance babu manyan hotel sun qare Sai qanana, inda kinsan waye Mahmud Wakili ma toda bakiyi maganar hotel ba, saboda ance baya sauka a qaramin hotel"

Haushi ne ya hanata magana, ahankali ta juya ta kalli hannun Daman ta, taga titin gaba daya babu motar datake bi,asalima sojoji ne suke shawagi atitin kowa hannunsa d'aukeda bindiga, ta kalli manyan gidajen da'akace ansauki Mahmud Wakili aciki,mutum daya jal saboda shi ankashe titi babba kamar wannan, bayason hayaniya to me zaisa yazo Garin? Sukuma manyan qasar suka biye masa akayi masa abinda yakeso aka shiga haqqin talakawa, yanzu irin wannan layin adedetan dayake gabansu yaushe zasu qare har tasamu taje gida?
Lokaci daya Shahaab yafado mata, ko yana Ina? Tunda yace shi Yaron Mahmud Wakili ne ko tare sukazo? Ko yana maidugurin?

Juya fararen idanuwanta tayi tace "tsaya Dan sahu"

Babu musu ya dakata, dama bawani sauri tafiyar tasu take ba, futowa tayi daga ciki hannunta d'aukeda ledar kayan data siyo, kudinsa tabashi tace "ga kudinka, zan qarasa da qafa ta, shikuma Wanda ya haddasa mana go slow din yaje mun rataya a wuyansa"(=��)

Murmushi yayi yakar6i kudin, Aisha kuwa haushi ne fal ranta, tafiya take Amma ta nayi tana waigowa tana Kallan gidan da akace ansauki Mahmud Wakili aciki, Sai yau tasake tabbatar wa shi din ba qaramin mutum bane, ganinsa zaiyi wahala,haka taci gaba da tafiya har taje gida, qafafunta kuwa sunyi bud'u-bud'u da qura, bata dade da zuwaba aka kira sallar magrib.

Washe gari saurayin fati yazo, kasancewar Aishan tace gobe zata tafi gida, shiyasa yazo da yamma,shirya wa sukayi Fati tayi kyau sosai cikin abaya baqa, Aishan ma Abaya tasaka wadda fati tabata jiya,saide Tata launin dark green ce, hijabi tayi niyyar dorawa akan abayar, Sai faty ta hanata, da magiya da komai tasa Aisha ta yafa mayafin rigar, ba rolling tayi ba, kawai parking din gashinta tayi, tayafa mayafin abayar sannan ta mayar dashi Bayan kafadunta, abayar tayi mata kyau sosai, Kuma tsawonta yayi mata daidai, irin abayar Nan ce wadda akewa shaf daga qirji, Qasan Kuma yabude sosai, batada wani ado sosai Amma Kuma tayi kyau rigar sosai, yanda Allah ya wadatata da Babban Hips, Sai ya sake bajewa acikin abayar, madedetan Breast dinta suka Dan taso daga gaban rigar, jakar Walida ta riqe tasaka can jin kudinta Dari biyar aciki, sannan suka fita wajan Auwal saurayin fati.

Suna zuwa suka sameshi zaune akan motar sa,Dafarko da yaga Aisha tsorata yayi, musanman da yaga gashin gaban goshinta yafuto yaga gashin yalala kamar Bana bahaushiya ba, saida fati ta yi masa bayanin Aishan sannan yasaki jiki da'ita suka gaisa sosai, daga Nan Kuma Sai hira ta 6arke a tsakanin su, ganinsu duka Yara daga ita har fatin saiya biye musu suka dinga zance wani yayi dariya, wani Kuma ya girgiza Kai cikin ransa yace quruci....

Bayan sungama shan labarinsu fati tace "Yaya Auwal kakaimu wajan yawo Dan Allah, kaga gobe Aisha zata tafi"

Cikin farinciki yace "tokuje ku tambaya agida saiku futo muje"

Babu musu suka koma gida suka fada, kasancewar ansan Auwal din, ba 6oyaiye bane Sai aka barsu, Kai tsaye suka shige motarsa yaja suka tafi, park yafara kaisu, daga Nan Kuma suka tafi wani Babban Mall, domin siyo ice-cream, Aisha cikin ranta Sai murna take yau de zatasha ice-cream itama.

Basu dade da shigaba sukaga mutane sunata futowa, basu kawo komai aransu ba suka dinga shiga waje waje suna ganin mall din,Auwal dayake biye dasu abaya yace "fatima kudauki abinda kuke sofa kunji ko"

Cikin murna tace "to ya Auwal"

Hannun Aisha taja suka je wajan perfume, Aisha de guda daya ta d'auka, Fatima Kuma tazabi irin Wanda takeso, ta kalli Aisha tace "ki qara mana, bashi ne yace mu dauka ba?"

Aisha tace "A a, nifa nafison ice-cream,kede ki za6a Sai muje in dauki ice-cream din"

Fatima batace komai ba Sai za6ar turaruka take, sannan ta kama hannun Aisha sukabi ta wata hanya suna neman inda ake ajiye ice-cream din, cikin rashin Sani Aisha tabige wasu setin glass cups, qaran da abun yayi ne yaja hankalin ma'aikatan mall din.

Gaban Aisha yafadi, ta dora hannayenta aka tace "nashiga uku" (=�F�<���
@&�)

Kafin Auwal ya qaraso wajan wasu Yan sanda su biyu, da wasu security mata sun qaraso wajan Aisha, suna zuwa basuyi wata wataba suka kamata, cikin 6acin rai Auwal yace "miye haka, ya zaku kama yarinya ku riqe kamar wanda tayi muku sata? Kufadi nawane kudin kayan ku saina baku"

Cikin 6acin rai daya daga cikin security yace "ba damuwar mu bane abinda tafasa, abun damuwar shine wanene ma yabaku iznin shigowa cikin wannan mall din Adede wannan lokacin da muka sallami kowa?"

Auwal yace "oho, ta sama muka Fado tunda abude muka ga qofar"

Jin furucin Auwal yasa ransu yaqara 6aci, memakon ya basu haquri baiyi ba saima raina musu Hankali yake, wata security ce mace tace "ai kawai a wuce dasu folice station, bazai iyu munada Babban customer, haka kawai saboda masu shigowa yin photo susa hankalin customer mu yatashi ba, a tafi dasu kawai"

Jin wannan furucin ne yasa Fatima ta Fashe da Kuka tana basu haquri


Tunda suka shigo Mall din shida Ramadan da sauran guard dinsa, baiji motsin kowa ba, dama Kuma hakan yakeso, shiyasa ma tun kafin yazo yaturo musu saqo ta Email cewa zaizo shopping mall din, yanaso abashi awa biyu yagama abinda zaiyi, idan yafita, Sai subar sauran mutane su shigo,yarinyar da yayiwa waliyi jiya, ita yazo ya siyawa gift yanaso yabata.

Kukan Fatima dakuma hayaniyar datake tashi tsakanin Auwal da sauran security shine yad'auki hankalin sa, ransa ne ya6aci, kwata kwata baison hayaniya arayuwarsa, cikin 6acin rai ya kalli Ramadan tareda nufar inda yake jin hayaniyar tana tashi, sannan yace "muje"

Jijjiga Kai Ramadan yayi sannan suka nufi wajan, guard din dake bayansa cikin sauri suka rufa masa baya.
Shan kwanar da zaiyi, Idonsa ya sauka akan Aisha(=�F�<���
@&�)
Wata irin faduwar gaba ce ta ziyarceshi, Jiyayi Kansa yayi wata irin sarawa cikin sauri ya damqe hannun Ramadan yaja shi sukayi wata irin kwana suka dawo baya,duk da sunbar layin dasu Aisha suke gabansa bai daina faduwa ba, menene zai faru data ganshi? Mezai ce mata? Hakan yana nufin da yanzu asirinsa ya tonu kenan tasan cewa da Mahmud Wakili take mu'amula batare data saniba....., meya yakawota kano?

6oye fuskar sa yafara yi a Bayan Ramadan kamar wani 6arawo(=��)

Daga Ramadan har sauran body guard Kallan Shahaab suke da mutuqar mamaki, zare ido suka fara suna dube dube atunaninsu wani abun cutar wa Shahaab din yagani.

Cikin tsananin mamaki Ramadan yace "Shahaab lafiya? Meyasame ka?"

Yana 6oye a Bayan Ramadan din cikin fada yace "dalla malam Kamin shiru, duk ba kaine kajamin ba?"
Mutara zuwa gobe =�O�<���
Ramadan yace "kamarya?, mekake nufi ninaja?"


"Tura musu mutum daya kace su sallami yaran can injini, sannan subata haquri"

Ramadan da mamaki yagama kasheshi, yace "okay" sannan yajuya ya kalli daya daga cikin guard dinsu yace "kace a sallami yaran can, sannan abasu haquri inji Mahmud Wakili"

Cikin sauri yanufi wajan da su Aisha suke, yana zuwa yayiwa daya cikin security din dasuke fada da Auwal magana.

Ramadan yadan leqo yaga abinda Shahaab yake gudu, anan yayi tozali da wata kyakykyawar yarinya, shagala yayi da Kallan yarinyar, fada dakuma tashin Hankali yasa Dan qaramin da kwalin abayar data yafa akanta yasa yayi qasa, dogon gashinta yafuto fili muraran, Shahaab daya d'an leqo da Kansa ta Qasan Ramadan Shima ya leqo yana ganin ta, ransa ne yayi baqiqqirin ganin dogon gashinta awaje, ribbon din daya daura mata shine akanta, haushin mazan wajan yafara ji dasuke tsaya tareda ita, yanzu haka kowama kallon gashinta yake, yasake Kallan Auwal da'ake fada dashi, cikin tsananin kishi yace "ko wanne yaro ne Kuma wancen?"

Ramadan ya juyo ya kalleshi, yaga fuskar Nan tasa tayi kicin kicin hankalinsa kacokam yana kan wancen yarinyar.

Su Aisha basu San menene yafaru ba Sai Gani tayi wannan securities din duk sun sunkuyar da kansu qasa suna fuskantar ta, har rige-rigen bata haquri suke, haushi da Kuma mamakin su ya kamata, yanzu yanzu suka gama cewa zasu kaisu folice station Amma Kuma suna bata haquri yanzu, kamar wasu masu Fama da aljannu, taqaici da 6acin ran da aka bata ne yasa tayi jifa da turaren data dauka, tajuya tafice cikin fishi, ice-cream dinma tafasa Sha,har suka fice daga mall din Ramadan bai daina kallonta ba, yarinyar tahadu ta ko'ina, babu wani namiji me lafiya dazai ganta yakasa yabawa.

Shahaab kuwa yana ganin yanda tafice cikin fishi yace"to 'Yan masifar sunzo"

Ramadan yajuyo yasake Kallan Shahaab daya 6uya abayansa Sai magana yake shi kadai, Kallan rashin fahimta yayi masa sannan yace "meyake faruwa ne?"


Wata irin ajiyar zuciya yasauke tareda Lumshe ido yabude, sannan yace "MAAMA"

Ramadan daya dauki haske cikin sauri ya zaro Idonsa yace "what...?"

Shahaab bai iya bashi amsa ba Sai Kansa daya daga masa kawai

Suna shiga mota Auwal yafara lallashin fati saboda kukan datake yi, saida tayi shiru sannan yaqara Bawa Aishan ma haquri, Bai qyalesu ba saida ya tabbatar sun Dan saki ransu, sannan sukai sallama suka shiga gida, Bayan sunyi shirin kwanciya Aisha banda tsinewa masu mall dinnan babu abinda take yi,ta nayi itama fati tana tayata, daqyar suka samu bacci ya dauke su


(Shahaab littafin kudine, idan kika karanta batareda kin biya ba, nabarki keda mahaliccinki, nide ban yafe a)

******

Tunda suka dawo masaukinsu Shahaab yayi shiru yana tunani shi kadai, Babban abinda yafi 6ata masa rai shine yanda ya ganta dawani yaro.
Ramadan ya kalleshi yace "Wai Dama haka yarinyar Nan take?, Shahaab Anya kuwa bahaushiya ce?"

Kansa ya jijjiga masa alamun hakane, ajiyar zuciya ya sauke yace "gaskiya tanada kyau sosai, amma Kuma yarinya ce sosai ya'akai Takeda kyan diri haka?"

Cikin masifa Shahaab yace "bansaniba, meya Hana kabita ka tambayeta?"

Murmushi Ramadan yayi, Bayan yagano kishi ne yake cin abokin nasa, ajiyar zuciya yasauke sannan yace "menene abun 6acin rai Kuma a magana ta?"

Cikin fishi yace "to kazo gabana Sai wani yabon ta kake, kaiba matarka ba, ba komai ba, ni abinda yafi 6atamin rai ma shine Yaron Dana gansu tare, bansan Yaya zanyi in tambayeta Shiba, zatace min Yaya akai nasan taje mall, idan nace Ina tareda ogana tace Amma nakasa yimata magana Ina Gani security suka ka masu, Ramadan duk kaine kajamin wannan abun, inda kabarni naje mata a Mahmud Wakili na, daduk haka bata faru ba, daga Kai har mama kira kuke idan zanyi mu'amula da mace tona 6oye mata kaina, na6oye mata koni waye, ta hakane zansan mesona tsakani da Allah, Ramadan ni banga amfani 6oyewa MAAMA kaina ba, saboda yarinya ce qarama, batada wani ilmi akan Zaman takewar rayuwa, yanda yarinyar ta yarda Dani idan saceta zanyi da tuni na saceta, na lura batasan komai ba akan soyaiya Sai abinda aka Koya mata,nafada mata banda aure, ta yarda, nafada mata nidan maiduguri ne, tayarda, nafada mata ni Yaron Mahmud Wakili ne, tayarda, duk wani abu Dana fada mata yarda take saboda

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment