Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

de Sai mutane sun shiga tsakani sun raba mu, Amma kabamu awa uku, saide kaga mun shirya, ko ban kulata ba, to ita Kam saita kulani, tundaga Nan da mutane suka gane halin mu, ko sunga suna fadan saisu qyalemu saboda sunsan zamu shirya"


Aisha tace"to Hajja bakida photon tane kinuna mana? "

Tace"inada shi mana, yana cikin adaka ta aqasan gado na, zan nuna miki takwararki, har saurayinta na makaranta ma duk inada photon sa, Shima zan nuna miki "

Cikin sauri Aisha tace"au Hajja har soyaiya kuke a makaranta? "

Hajja tace" emana, kafin muyi candy kowacce tanada saurayi, mudinga rubuta wasiqa muna aika musu, suma suna aiko mana, Bayan munyi candy ne Kuma muka rabu da samarin kowa tafara tunanin aure, ni muka dawo jigawa, ita Kuma suna kano "

Jin ankira sallar asuba yasa firar tasu ta tsaya, Abba yatafi masallaci, sukuma kowa yafara kokarin daura Alwala.


******


Yau saura kwana uku sallah, tunda sassafe yatashi yayi wanka, yadauko suit takai Kala biyar, duk wadda yad'aga saiya ga batayi ba, daga qarshe yasaka wata ruwan toka wadda ta qarfi fatar jikinsa

Yayi mutuqar kyau shi Kansa daya kalli Kansa a mirror yasan yayi kyau, murmushi yayi yad'auki turarensa yafara feshi dashi ajikinsa
Munirat data shigo Dakin saita zubawa sarautar Allah ido tana kallo

Cikin mamaki tace "my Dear yanaga ka zubar da kayaiyaki akan gado, lafiya?"

Batare daya kalleta ba yace "naza6i Wanda zan saka ne"

"to yanzu duk wannan daka zubar akan gadon basu Maka ba? Dubafa kagani harda suit din Dana siyoma a Cairo"

Yatsina fuska yayi sannan ya kalleta yace "wannan naza6a"

Hannu tasa a qirjinta ta hardesu, sannan ta fuskance shi sosai tace "zakaje wajan Mr President ne?"

Gabansa ne yafadi, Sai alokacin yadago Kansa ya kalleta "no, zamuje jigawa nida Ramadan,ganin aikin gidan marayun Nan"

Wata wawuyar ajiyar zuciya tasaki sannan tace "Alhamdulillah....na yi tunanin wajan wata zakaje wallahi, yanda kake zuba kwalliyar Nan ai sai kasa jinina yahau, nasan inde kafita saiwata ta kallemin Kai, Amma tunda qauye zakaje, nasan banda damuwa,nasan Babu wadda tayi daidai da kalar mijina a wannan baqauyen Garin, babu ita, ba Kuma za'a yitaba"

Kansa ya girgiza yace"hakane"

Bakinsa yad'ora akan goshinta yasakar mata kiss, sannan yafice daga d'akin cikin sauri

Kai tsaye wajan mama yatafi, ganin ta yayi tana matsa qafafunta da kanta, cikin sauri ya qaraso ya tsugunna yaci gaba da matsa mata qafa fun, Kallan sa tayi tace "masha Allah,Dan mama yau Kuma Sai Ina? Ko qasar zaka Bari Amma baka sanar Dani ba?"

Murmushi yayi, dimples dinsa suka futo, yace "Wai nayi kyau ne mama?"

Tace "sosai ma kuwa, kamar Ango"

Murmushi yayi tare dayin qasa da Kansa, yad'ora hannunsa akan sumar Kansa ya Dan Sosa qeyarsa, sannan yace "haka munirat ma tace Wai nayi kyau, babu inda zanje mama, jigawa kawai nakeson zuwa saboda ganin aikin gidan marayun dakika sakani"

Cikin farinciki mama tace "Allahu akbar, Allah yayi Maka Albarka Mahmud, yanda kakemin biyaiya kaima Allah yabaka Wanda zasuma fiyeda haka, Allah yasa kafin nabar doron duniyar Nan Inga jikokina Kuma Inga Qawata Aysha Sulaiman Bompai"

Cikin sanyin jiki yace "Amin mama, Bari intafi, Ramadan yana jirana a Airport"

Tace "to Allah ya dawo daku lafiya, ABINDA KAJE YI ALLAH YABAKA NASARA AKANSA"

Ahankali yace "Amin mama" sannan yakama hannunta yayi kissing Bayan hannun, yafice daga falon cikin sauri, binsa tayi da kallo tana jin dadi a ranta, cikin zuciyar ta tace "Allah ka qara aramin lokacin dazanga yayan Mahmud dina...."



Motoci biyu ne suka rakashi Airport, daya yana ciki, dayar Kuma sojoji ne, suna zuwa Ramadan yazo da sauri yatareshi, sannan suka qarasa cikin Airport din.

Bayan sun sauka a dutse, wani direban ne yasake daukar su, Kai tsaye wajan aikin gidan marayu suka wuce, komai yayi, suna aikinsu yanda ya kamata, saida sukai sallar la'asar awajan, Shahaab ya dubi Ramadan yace "muje ko?"

Ramadan yace "Ina?"

Kai tsaye yace "Abinda yakawo mu"

Wayarsa ce tafara ringing Kiran munirat, Bayan sun gaisa tana masa qorafi bai ta6a tafiya yaqi kiranta ba, Sai wannan tafiyar, goshinsa yadan shafa yayi shiru, shi Kansa yasan gaskiya ta fad'a masa, baisan menene yake damunsa ba yau din, haquri kawai yabata, sannan yafada mata aiki ne yamasa yawa, zasuyi waya anjima, daga Nan yakashe wayar

Kallan sa Ramadan yake lokacin dayake waya da Munirat, gaskiya Shahaab ya sauya sosai, Kuma yasan cewa duk a dalilin wannan yarinyar ne, kowacce irin yarinya ce haka data sauya masa tunani lokaci daya? Shikam zai so yaga wannan yar baiwa, to matsalar Kuma shine shi yaqi yarda son yarinyar yake, Amma babu damuwa ai lokaci zai nuna komai.

Shahaab yace "Ramadan bakajini bane?"

Ramadan yace "najika Sarai, kaine de kunnanka yadena aiki, idonka yarufe, kwata kwata ka manta waye Kai, ka manta cewa kaine MAHMUD WAKILI...."

cikin rashin fahimta yace "mekake nufi?"

"Abokina kaine kace min yarinyar Nan batasan waye kaiba, asalima ce mata kayi kaidin Yaron Mahmud Wakili ne, Kuma Sarai ta ganka, Kuma yanzu Sai muje garinsu da yamma, mu parker mota aqofar gidansu, muyi magana da'ita, karka manta ita kadai ce batasan waye kaiba, bawai mutanan Garin ba, itama nayi mamaki dakacemin bata sanka ba, to yanzu kuwa muna zuwa, idan wani yaganka ya ganeka, zai fadawa na kusa dashi, Shima ya fadawa wani, dahaka mutanan qauye su taru azo wajan Mahmud Wakili ayi masa godia saboda kwanaki ya aiko musu kayan abinci, Shahaab kana buqatar privacy, karka manta a Abuja ba Kai kadai kake yawo ba, Nan dinma kwanciyar hankalin jihar ne yasa kake yawo ko'ina haka "


Ajiyar zuciya ya sauke yace "to aini banga abun damuwa ba, saboda bawai zama zanyi da yarinyar har mutane suzo su taru akaina ba, kawai de Naga suna cikin yanayi na rashi, shiyasa zan taimaka mata, sannan Kuma ta fada min abinda yasa take min rashin kunya, idan batada hujja saina mata hukunci daidai da rashin kunyarta inkama gabana, shikkenan fa "

Ramadan yace"idan kuwa ka temaka mata ai zataso kudinga zumunci, ko yar wayar nan idan tana cikin halin buqata zata Iya kiranka ai, kayi hakuri muje da daddare yafi sirri gaskiya, babu wanda yasan munje, babu Wanda yasan mundawo"

Badon ransa yasoba haka yayi shiru, Bai qara magana ba saboda 6acin rai Wanda shi Kansa baisan dalilin hakan ba, Ramadan yadan juyo ya Kalle shi qasa-qasa dariya ta kamashi ganin yanda abokin nasa yahad'e girar sama data qasa


Karfe biyar na yamma suka koma masauqin su, saida aka Sha ruwa, suka huta, wajan qarfe bakwai da rabi suka futo, Ramadan ne yake driving, shikam Shahaab a sonsa, driver yakawo su, Amma Ramadan Sai yaqi yarda yace babu damuwa shi zai kawo su Garin.

Haka suka taho su biyu, da tambaya da komai Allah yakawo su Garin CHAMO, mutane dayawa Sai kallon motar suke saboda yanda take daukan ido tana wani irin qyalli na sabunta, Ramadan ya juyo ya Kalle shi yace "inane gidan?"

Kalle-Kalle yafara, can yace "danyi gaba kadan"

Ramadan yayi gaba, yasamu wani waje can Gefe ya Parker mota, Shahaab ya kalli Ramadan yace "Anya ba zamu koma ba kuwa Ramadan? Gabana faduwa yake, karnaje aljana ce"

Ramadan ya riqe hannunsa yace "mutum ce, duk da banganta ba nasan mutum ce, Ana daure duk wani shedanin aljani lokacin azumi, saboda haka kayi addu'ah kawai ka qarasa gidan"

"tokai bazakaje ba?"

Ramadan yace "Ina jiranka amota, ka dauki Bluetooth dinka saimu dinga magana ta waya"

Girgiza masa Kai yayi, sannan yasaka hannu yabude gidan Bluetooth din yad'auki guda daya,yacire jacket din suit din jikinsa, yacire Agogonsa Mai tsada, niktie din wuyansa ma yacire shi, Jiyayi botir din gaban rigar tasa ya kamashi, yasaka hannu ya6alle guda uku, Nan da Nan kuwa lallausar sumar qirjinsa tafara bayyana kadan, saida yagama gyarawa tsaf sannan yafita daga motar yana tunani a ransa yaushe zai iya bata kyautar dubu biyar saboda ya gwadata kamar yanda Ramadan yabashi shawara? Yanzu Yaya za'ayi ya ganta?.


Tafiya yake ahankali hannunsa daya zube cikin aljihun wandonsa, Sai Kalle Kalle yake kamar yana tsoron wani Wanda yasan shi ya ganshi
Har yaqara so qofar gidansu Aisha, yaja ya tsaya agefen wata bishiya dake kofar gidan, yadade a tsaye awajan yana tunanin wazai tura gidan Akira masa ita?to wazaice Akira masa shida baisan sunan taba?
Ramadan yakirashi yace "kakirata?"

"no, Ina jiran yaro de"

Yace "okay"
sannan yakashe wayar

Shiru shiru babu wani yaro dayazo wucewa ta qofar gidan, bishiyar yasake kalla yanemi waje ya zauna ko Allah zaisa wani Yaron yazo wuce wa, har qarfe takwas da rabi babu alamun mutum Kuma unguwar tafara yin shiru saboda sallar tarawih da aka fara mutane duk suna can suna Sallah

Wani sauro ne yarafka masa cizo abayansa cikin sauri yamiqe tsaye yakai hannun sa wajan yana sosawa, tunani yafara a ransa yaushe Rabonsa ma da cizon sauro?
Kafin yagama tunanin yaga wata tafuto daga gidan, hannunta d'aukeda sallaya,da alama wajan sallah zataje.


Hankalinsa ne yakoma kanta, Hasken wayar Hajja dake hannun ta tana dannawa shine yasake bayyana kyakykyawar fuskarta, hijabin Nata dogo ne har qasa, yanada hula hijabin Sai hular tayiwa doguwar fuskarta kyau sosai, gabansa ne yafadi, kafin zuciyar sa tayi masa tunanin wani abu yayi sauri ya qarasa wajan tareda fuzgota can Gefe, sakamakon fuzgotan Dayayi har jikinsu yana haduwa Dana juna, wayar Hajja tayi Gefe tafadi aqasa, gabanta ne yafadi, abinda takawo ranta kawai masu satar mutane ne zasu saceta, ganin kafafun mutane sun dauke babu wani Wanda zai ceceta yasa tafara kokarin qwace hannunta daya riqe Wanda tuni yafara yimata zafi, Bayan ta qwace hannunta ta kwasa da sauri zata koma gida, cikin sauri shima yakai mata wani irin ruqo bai samu nasarar kama hannunta ba, hakan yasa hannunsa ya sauka akan Bajajjan Qugunta, baisan lokacin daya sake yimasa wani irin ruqoba,tsoro ne yasake kamata, har zuwa lokacin batasan waye ba, cikin sauri ta bud'e dan qaramin bakinta zata masa ihu,tun kafin tasaki ihun cikin sauri Shima yasaka tattausan tafin hannunsa na Dama yatoshe mata baki,hannunsa na hagu Kuma yana riqe da Qugunta, kallanta takai gareshi, lokaci d'aya tagane shi,zuba mata ido yayi yana qare mata kallo acikin duhun, haka itama shid'in take kallo.
Alhamdulillah free fage yaqare=؃�<���=؃�<���=؃�<���=؃�<���=؃�<���

Yaya makomar soyaiyar Inusa Mai Kanti awajan Aisha?

Yaya alaqar ta da Mahmud Wakili zata kasance?

Yaya haduwar Aysha Sulaiman Bompai wato Hajja A'i, dakuma qawarta Aysha Yakubu Sagagi wato Hajiya Mama?

Yaya alwashin munirat zai kasance?>��

Ba'iya wannan ce gwagwar mayar da littafin ya qunsaba,akwai drama iri iri, Kashi daban daban, domin kuwa littafin Shahaab yazo da wani Salo na daban, kede kawai karki Bari abaki labari, bahaushe yace da abaka labari, Gara kabayar =�


Duk me buqatar cigaban littafin SHAHAAB, zai tura nera 300 kacal=�L�<���ki karanta abinki Hankali kwance >�p�

Zaki tura 300 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma kitura katin MTN na nera 300 kacal, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034 =��
Amnah El Yaqoub
'<���

17&18


Cikin damuwa takira wayar mahaifiyar ta, Bayan sun gaisa da juna tace "Momy Mahmud ya sauya min gaba daya"

Cikin kulawa tace "sauya wa kamar Yaya munirat? Banason shashanci, yanda Mahmud yake sonki banajin zai iya aikata miki wani abu"

Cikin shagwa6a tace "momy yanzu yarage nemana, koda yayi tafiya baicika nemana kamar da ba, idan yana gida saide yayi shiru yadinga tunani, ni bansan meyake damunsa ba"

"kinjiki da shirme munirat, yaushe Zaki barshi da damuwa to? Kema kinsan abinda muke samu awajansa idan kikayi watsi dashi to zamu daina samu, kici gaba da bashi kulawa, 'yar kissar Nan, kina sake janye hankalin sa, Sai kiga komai yayi daidai"

"to shikkenan Momy, zanyi"

"yauwa, kina Dan adana wasu abubuwan de ko?"

Tace "momy wanne irin abu?"

"munirat banason shirme, kina matar Mahmud Wakili Amma ace ke d'an gidajen Nan ma bakida shi, bakida wata kadara daza'a siyar miliyoyin kudade, kina zaune ba Cas, ba as, yana mutuwa bakida komai kenan saide tumunin takaba, danhaka kishiga hankalin ki"

Jijjiga Kai munirat tayi, alamun ta gane inda momy tasa gaba, cikin murna tace "nagane momy, zakiji kyakykyawan bayani awajena momy, ki kulamin da kanki bye"

Tafadi hakan tareda kashe wayar.




(duk wacce ta karanta min novel batareda tabiya ba, nabar ta da ALLAH, domin nide ban yafe ba)


******

Hannu tasa tacire masa nasa hannun daya rufe mata baki dashi, cikin 6acin rai tace "ka qyaleni"

Lokaci d'aya yasake ta,tsugunna wa tayi tad'auki wayar Hajja da screen din yasake fashewa, cikin tashin Hankali ta dora hannunta duka biyun aka tace "innalillahi..." cikin sauri ta juya zata koma gida da alama ma ta manta da mutum akusa da'ita

Da sauri ya ruqo hannunta, juyowa tayi cikin fishi ta Kalli yanda yariqe mata hannu, gaba daya ma Sai mamaki ya kamata ganin yanda yake riqeta babu wata shakka ko tsoro atare dashi, ranta ne yayi baqiqqirin, ahankali tasaki ajiyar zuciya, sannan tadawo kusa dashi tace "sakarmin hannu malam, ko Bayan kama abubuwan bayin Allah Wanda basujiba basu Gani ba da ogan Naka yakeyi yanzu Kuma harda kama mutane yafara?"

Wata irin iska ya furzar daga bakinsa, Bayan tunawa Dayayi ashefa yafada mata shi din Yaron Mahmud Wakili ne, to Amma shi menene laifin sa danya sa an kama kayan 6arayin Gwamnati? Meyasa take masa haka ne? Hannunsa yatura cikin aljihun wandonsa, dayan hannun Kuma yana riqe da tsintsiyar hannunta, batare daya saketa ba yace "kifadamin menene oga na yamiki?"

Aisha ta Kalle shi tace "toka sakarmin hannu saina fada Maka"

Hannun yasaki, sannan ya nuna mata Qasan bishiya inda ya zauna kafin tafuto, babu musu ta zauna, Shima zama yayi, yana mamakin yanda yake zaune da wannan qanqanuwar yarinyar Kuma awani gari qauye irin wannan, Aisha ta juya ta Kalle shi, cikin zazzaqar muryarta tace "Kanaji ko Yaron oga, Mahmud Wakili bashida mutunci" (=�F�<���
@&�)

Cikin sauri yajuyo ya kalleta, ransa ne ya 6aci, Amma saiya danne yace "meyasa?"

Gyara zamanta tayi kamar Dama jira take ya tambayeta, cikin sauri tace "Alhamdulillah, Gara da Allah yasa ka tambayeni,kullum shi bashida aiki saide kaji yakama abubuwan mutane yarufe, kullum maganar da akeyi kenan a gidan redio, sannan Kuma ga mutane Nan mabuqata bazai taimaka musu ba, saide yabawa Yan ball, Dan Allah Kai a ganinka wannan mutunci ne? "

Baqin ciki ne ya kamashi, yanzu Dama saboda wannnan dalilin yarinyar Nan take zaginsa? Jiyayi kamar ya kwada mata Mari, Kallan ta yayi akaron farko tunda suka zauna, ahankali yace"shine kawai?"

Cikin sauri tajuyo tana Kallan sa sosai tace "Ina kuwa, haka yakama gidan man Alhaji Audu maqocinmu, bawan Allah gashi da taimako, kullum idan ya dawo daga kudu saiya kawo mana tsarabar kayan abinci da manja, Amma shine yasa aka kama masa gidan mansa"

Tana fadar haka ta dora kanta akan qafafunta tafashe da Kuka

Shahaab Sai yayi shiru yana Kallan ikon Allah, yanzu yanzu yarinya ki gama bayani Amma kifashe da Kuka? Kamar wata tsohuwa? to kode da tsofaffi take zaune? Ahankali ya motsa lips dinsa kamar bayason magana yace "Menene abun kuka? Sannan waye yafada miki Mahmud Wakili ne yakama gidan mansa? A Abuja gidan man yake?"

Cikin kuka ta d'ago kanta tace "akano gidan mansa yake,kuma efcc ne suka kama masa, tunda aka kama masa har yanzu ko shinkafa kwano daya bai qara aiko mana ba, muda muke samun abinci ta qarqashin sa aimu Mahmud Wakili yacuta, Kuma insha Allah idona Idonsa saina fada masa baqar magana har ya mutu bazai manta Dani ba "

Cikin ransa yace"baqar magana na nawa Kuma "(=��)Gara yatafi, yaga alama gaba daya zallar yarintace a tareda'ita

Hannunsa yazura cikin aljihun sa yadauko dubu biyar, kamar yana tsoron bata yace"gashi"

Kallan kudin tayi ta girgiza Masa Kai tace "um Um, ankusa idar da sallah natafi saida safe" tamiqe zata saka gudu

Cikin sauri ya ruqo hannunta, sannan yamiqe tsaye, yazare wayar Hajja dake hannunta, yasaka mata kudin cikin tafin hannun, sannan yayi danne danne a wayar kamar yana neman wani abu, yabata wayar tareda cewa "kisai ice-cream"

Daga haka bai qara cewa komai ba yajuya yatafi cikin sauri,saboda shi harga Allah kunyar bata kudin yake, kudin yayi qanqanta dayawa.

Aisha ta riqe kudin ta bishi da kallo, harya shiga mota, suka tashi, akan idonta, cikin zuciyar ta tace "nikam inani Ina wani ice-cream, banta6a Sha Bama"

Ahankali ta juya ta nufi masallaci jiki a sanyaye kamar kazarda qwai yafashe wa, tunani take aranta Yaya za'ayi ta nuna wannan kudin agida? Tace musu wa yabata? Duk da bata dubaba tasan kudi ne masu yawa,tana wannan tunanin harta ta'isa masallaci, bata samu mafita ba


******
Suna cikin tafiya Ramadan ya Kalle shi yace "kaganta ne?"

Kai tsaye yace "Eh"

"tafada ma abinda yasa tazageka?"

Dan qaramin tsaki yasaki yace "Shirman tane kawai"

"Yaya sunan tane yarinyar?" cewar Ramadan

"I don't know"
Yafada a gajarce

Murmushi Ramadan yayi, cikin ransa yana fatan ace su sake dawowa Garin


Bayan sun idar da sallar Kai tsaye gida ta wuce, Hajja tana cikin dakinta, Ummah Kuma tana Dakin Abba, danhaka saita wuce Dakin Ummah, da wayar Hajja ta haska ta duba kudin, gabanta ne yafadi, lokaci daya ta zaro idonta waje tace "dubu biyar?"

Tunda take, bata ta6a riqe kudin daya Haura dubu biyu ba, Amma yau gashi Wai ita aka Bawa dubu biyar, Tome zatayi da wannan kudin? Tasan cewa idan Ummah ko Abba suka Gani kashinta ya bushe, hatta Hajja ma saita tambayeta waye yabata wannan uban kudin?

Wani tunani ne yazo kanta, tasan babu me bude mata asusunta, koda tace umma ta d'auka toba ta6a mata kudi take ba, Dan haka cikin sauri tatura kudin cikin asusunta sannan tafuto ta wuce Dakin Hajja


******
Bayan sun koma hotel sunyi shirin kwanciya, yad'auki wayarsa yakira wata number, Bayan mutumin yadaga wayar Shahaab yace "Alhaji Inuwa akwai wani case din gidan Mai na wani Alhaji Audu, I don't know who his father... Please kadubamin file dinsa menene abunda yake faruwa"

Alhaji unuwa yace "Angama yalla6ai, yanzu hakama Ina office akwai aikin danake, Bari aje yanzu yanzu aduba"

Kashe wayar yayi batare daya ce masa komai ba


Baifi minti talatin ba dayin wayar su Sai gashi Alhaji unuwa yasake kira, cikin ladabi yace "yalla6ai file dinsa baya wajan mu, anturashi Abuja, abinda bincike ya tabbatar kenan"

Ahankali yace "ok" tareda kashe wayar

Addu'ah yayi ya kwanta tareda Lumshe Idonsa, Sai yanzu ne yake jin wata irin nutsuwa tana shigarsa, wadda shi Kansa baisan dalili ba.


Washe gari suka koma Abuja, Kai tsaye office suka wuce dagashi har Ramadan,magana yayi a duba masa file din Alhaji Audu, aka duba aka Gano, sannan suka kawo masa, saida yaduba yaga shine file din da aka kawo masa kwanaki yace akai shi wani office din suduba

Kar6a yayi sannan yabawa Ramadan yace suje suyi binciken dazasu akan file din, idan sun gama saisu sanar dashi.


Kasance war kwana daya baizo office ba Sai ayyuka suka taru suka masa yawa, Bai koma gida ba Sai Bayan sallar la'asar.

Da daddare Bayan yagama komai, yad'auko wasu takardun mama na wasu filaye daya siya mata da kudin ta daya saka hannun Jari awani company, takardun sunkai guda goma, yasan cewa idan yabata kudin ma cewa zatayi ya ajiye, shiyasa yayi dabara yasai mata manyan filaye dasu, daya Bayan daya yagama dubasu, zai dauke kenan Sai aka kira wayarsa, yayi mamaki ganin Kiran daga office dinsu ne, Bayan ya dauka suka tabbatar masa cewa wannan file din daya basu sungama bincike akansa, tabbas kudin Alhaji Audu ne, ba kudin sata bane, ya saida wasu kadarorin sane, sannan ya Gina gidan man, umarni ya basu cewa atura file din zuwa kano, Sai asakar masa gidan mansa.

Wani irin farinciki ne ya kamashi Bayan yagama wayar, shi Kansa baisan dalilin yin farincikin ba, maganar tace tafado masa Arai, "kanaji ko Yaron oga... Mahmud Wakili bashida mutunci"

Murmushi yayi, yamiqe tsam yashige toilet domin watsa ruwa, kwata kwata ya manta bai dauke takardun filayen mama ba.
Munirat data shigo Dakin domin kawo masa coffee,taci Karo da takardun azube atsakar d'aki, juyawa tayi ta kalli cikin Dakin kamar tana tsoron wani zai ganta, tsugunna wa tayi tadudduba takardun taga na filaye ne, mamaki ya kamata, ta ajiye coffee din hannun ta, ta sake duba takardun dakyau, take hudubar mahaifiyar ta tafado cikin ranta, cikin sauri ta dauke takardun manyan filaye guda biyu, sannan tayi gaggawar ficewa daga d'akin batare data ajiye masa coffee dinba.

Shahaab kuwa ya dade yana wanka sannan yafuto jikinsa daureda towel, hannu yasa yadauke takardun batareda yasake dubasu ba, Kai tsaye yabude wata yar qaramar akwatin sa ta adana sirri, yasaka takardun agefen inda ya ajiye ribbon din daya siyowa Aisha,kallon ribbon din yayi na Yan seconds sannan yasaka wasu numbers yarufe akwatin, ya shirya tsaf, sannan yafada kan gado tareda daukar wayarsa, number daya dauka a wayarta yakamo ya zubawa ido yana kallo, cikin zuciyar sa yace "ko tayi bacci yanzu?"

Har zai kirata saiya fasa, Tome zaice mata?
(nikam nace idan ka kira ma dandalewa zakayi da Hajja >�#�)

Ahankali yace "idan taji labarin Mahmud Wakili yasa ansaki gidan man Alhaji Audun nasu, nasan zatayi farinciki" fillo yaja yarungume a qirjinsa, da wannan tunanin bacci me dadi ya dauke shi, saida yatashi sahur mamaki ya kamashi yau meya hanashi neman munirat har yayi bacci shi kadai? (>��)


******

Zaune suke atsakar gida, Aisha da Jummai suna tsince shinkafa, jummai ta kalli Hajja tace "Amma Hajja A'i wannan 6arawo naku da rashin kunya yake, Dan tsabar rashin mutunci ga mamuda yana kwance atsakar gida Amma har ya'iya dirowa cikin gida irin wannan me tsaro?"(>�#�)

Aisha takwashe da dariya tace "infada miki iya jummai nice nafara jinsa lokacin daya shigo, Ina tsugunne aqofar bandaki naji kamar andiro ta cikin bandakin, aikuwa nayi tsilak natashi nadawo kusa da Abba"

Jummai tace "ahaf, to inaga Dama yasaba shigowa yana muku dauke dauke, Amma naso kun kamashi, da Sai mun Tara masa jama'ah"

Kafin su bata amsa daya daga cikin jikokin ta yazo Yakirata, daga Nan tayi wa su Hajja sallama tatafi gida.
Hajja tacewa Aisha"nikam da 6arawon Nan yashigo ya kwashe min kudin qanqara Aida bazanyi azumi ba gobe, wuni za'ayi Ana yaiyafa min ruwa"

Ummah data futo daga daki tace "Gobe jajiberan mutane Sai shiri suke yi, azumi yatafi kamar yau muka d'auka"

Aisha tace "au Wai Ummah da gaske gobe jajiberan kasuwa zataci kenan?"

Hajja tace "insha Allah jibi zamuyi sallah, mun kusa muhuta, gobe Kuma kasuwa zataci, inada cinikin qanqara gobe"

Aisha tace "dole ki riqe lokacin kasuwa ai, saboda kina samun kudi, larabawa suna kuka azumi zai tafi, kekuma murna kike jibi zakiyi sallah"

Hajja tace "ke suma kukan munafurci suke, wannan wahalar azumin idan dan'adam yakaishi lafiya ai abun azo har gida ayi masa barka ne, insha Allah jibi sallah"

Aisha tace "Wai Hajja waye yacemiki jibi sallah? Idan kuma ba'aga wata bafa?"

Hajja tace "ke Bari kiji, duk masifarki daga gobe de mungama azumin Nan, ke koba'a gamaba nikam na sauke, Kuma babu uban daya Isa yasa nayi, ai kowa kabarinsa daban"

Aisha tace "yanzu ma babu Wanda yahanaki saukewa, walakiri ne zai kamaki yadinga jibgarki kekadai babu me cetonki Sai Allah...."

Lokaci daya Hajja A'i tafashe da Kuka, ihun datasa ne yaja hankalin wasu samari daga waje suka shigo gidan sunyi tunanin mutuwa akayi, Ummah kuwa cikin ranta cewa take innalillahi wa inna ilaihirraji'un, yau Kuma abun na Hajja yatashi, tambayarta samarin suka farayi waye yamutu? cikin kuka Hajja tace "yanzu munzali, nime sunan qawa zatayi wa fatan walakiri yakamani da jibga kamar wata kafura"

Kafin su munzali subata amsa ta juya ta kalli Aisha tace "insha Allah babu abinda walakiri zaimin, fatan ki yaqare akan Hadiza da Mamuda..."

hawaye ne ya taru a'idon Ummah, ahankali ta juya ta shige cikin dakinta, sumasu munzali suka Bawa Hajja haquri sannan suka juya

Aisha kuwa harara ta zubawa Hajja, sannan ta wuce Dakin Hajjan kaitsaye, duk wani kayanta dayake Dakin Hajja yau saida tafitar dashi tas..., ko dankwali bata Bari ba, ta wuce ta maida shi Dakin Ummah, Ummah tana kallanta batace mata komai ba, ahankali ta zauna abakin gadon ta kalli mahaifiyar Tata tace "Ummah Dan Allah Kidena kuka saboda wannan tsohuwar, kiyi hakuri insha Allah ni nariga na yanke alaqata da Hajja, hakan bazata sake faruwa ba"

Ummah batace da Aisha komai ba, abinda tasani shine idan tabiye mata suks taru suka zagi Hajja, to Ana jimawa zasu shirya da Hajjan, menene amfanin ka daurewa yaro gindi? Ita kanta tasan cewa haifar Aisha kawai tayi, Amma duk wata wahalar ta da rainon ta Hajja ce tayi, shiyasa suka shaqu, koka shiga tsakanin suma kaine zakaji kunya.


******

Kayane masu mutuqar kyau da tsada azube agaban mama, dubasu tayi sosai sannan ta ware wasu, wayarta dake gefenta ta d'auka takira Shahaab Wanda ya dawo daga wajan aiki yake shirin shiga wanka, yanaso yatafi masallaci wajan tafsir, cikin ladabi ya dauka kamar yana gabanta, munirat data gama debe kayan daya cire Sai jinsa tayi

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment