Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai ko?"

Cikin muryarsa Mai aji yace "Bana Nan naje Jigawa"

Mamaki yakama Ramadan, cikin jin dadi yace "masha Allah, kacemin kaje qauye kana kokarin hada kan takardu domin bude sabon account" (>�-�)

Murmushi yayi yace "ba account zan bude ba, cbn zan bude, Wai mekake tunani akai nane Ramadan? Kawai zuwa nayi inji sunanta, last time ban tambayeta menene sunan taba"

Ramadan yayi murmushi yace "ok nagane, to Yaya sunan qanwar tamu?"

"sunan mama gareta"

"Kai kai Kai, kace me Babban suna ce, to Abokina, Allah yabar zumunci tsakanin ka da Ummi"

Cikin sauri Shahaab yace "no, ba ummi ba MAA-MA"

Ramadan da mamaki yagama cikashi yayi murmushi yace "to d'an autan MAMA abokin MAAMA, yanzu de Sai yaushe zaka dawo?"

"gobe babu inda zanje, zan huta, Ina tunanin jibi zan dawo insha Allah"

"ok to shikkenan, Allah ya dawo dakai lafiya, saika dawo din"

Batare daya sake maganaba yakashe wayar yaci gaba da driving, acan bangaren Ramadan kuwa murna yake, ta tabbata de Shahaab yana son yarinyar Nan, oh daga zuwa saudaya harya zare jiki yakoma batare da kowa yasani ba, ko Yaya wannan zance nasu ya kasance Bayan Shiba magana yakeba? Ko yabude baki yayi mata magana? Dariya yasaki yace "Abokina kenan, Allah yakaimu lokacin musha biki"



(SHAHAAB LITTAFIN KUDI NE, IDAN KIKA KARANTA BATARE DA KIN BIYA BA NABARKI KEDA MAHALICCINKI, NIDE BAN YAFEBA)


******


Bayan yagama komai ya kwanta, yakira mama suka sake gaisawa, cikin kulawa tace "kakoma gida ne?"

Cikin sigar shagwa6a yace "um Um mama ban komaba, saina huta de"

Mamaki ne yakamata,tasan cewa Shahaab da munirat Sai Allah, kamar yanda Shima yake fada, Amma yau shine awani gari daban batare da munirat ba, Kuma yake fadar haka, ajiyar zuciya tasauke tace "munirat din tabiyoka ne?"

Yatsina fuska yayi yace "no, bamuyi waya Bama tunda nataso, zande kirata yanzu Bayan mungama wayar nan, kawai inajin dadin inda nake ne mama, babu hayaniya, babu takurawa, babu Wanda yasan Dani, Ina rayuwa ta yanda nakeso, saina huta zan koma"

Cikin tsoro mama tace "akwai Wanda zaice baisan kaba bane Shahaab? Banason damuwa, idan hutun kakeso ka shirya katafi wata qasar mana, canma ai babu Wanda yasanka, kakoma gida ka dauki matarka kutafi hutunku kamar yanda kuka saba"

Cikin shagwa6a yace "mama ki kwantar da hankalin ki, babu abinda zai sameni kinji?"

Tace "to shikkenan, idan kunyi wayar ka gaisheta"

Tace "to mama" sannan yakashe wayar

Kamar wanda aka sakawa cutar mantau, yana kashe wayar Yama manta da batun munirat kwata-kwata, cikin sauri yakira Aisha (=�F�<���
@&�)

Tana zaune agefen gadon Hajja tayi shiru tana tunanin al'amarin Shahaab, tarasa meyasa yake zuwa wajanta? Yakamata ace ta tambayeshi meyasa yake zuwa inda take? Ko wani aikin ogansa yaturo shi Garin?

Wayar Hajja dake caji tad'auki qara, Hajja dake kwance atsakar gida ita dasu Ummah ta daga murya tace "me sunan qawa Bani wayar nan Ana kirana"

Bakinta ta turo gaba tace "ni ake kira"

Hajja tace "au to, ko inusa me shago ne?"

Ahankali tace "um" tareda daga wayar

Zama tayi agefen gado tanajin yanda yake magana kamar mace, ahankali tayi qasa da murya yanda su Hajja bazasu jitaba tace "Wai Kai meyasa kake magana ne kana shagwa6a kamar wani Dan auta"

"mama nah nikadai ta Haifa"

Cikin mamaki tace "shiyasa kake shagwa6a?"

Murmushi yayi cikin shagwa6a yace "ni banyi miki shagwa6a ba"

Tace "ba gashinan ka nayi ba"

Lumshe idonsa yayi, yana jin wani irin dadi cikin zuciyarsa, yace "mama na kawai nakewa shagwa6a saike"

"kaifa ba yaro bane" cewar Aisha

"shine awajanki"

Cikin mamaki tace "kamarya?"

Cikin basarwa yace "babu komai, yau nahanaki bacci, ki kwanta kihuta"

Babu musu tace "to Amma inaso in tambayeka, meyasa kake zuwa garinmu?"

Murmushi yayi yace "ki adana tambayoyin ki, idan nadawo saiki tambayeni,insha Allah zanbaki amsa"

Cikin nutsuwa tace "to nagode sosai"

"Okay" shine abinda yace, tareda kashe wayar gaba dayanta, ko kadan baiyi yunkurin Kiran munirat ba, itama Kuma bata nemeshi ba.


******

Yau kwanan su mama biyu da tafiya, tunda suka tafi munirat bata kira mama awaya ba, shide Shahaab Yakirata yau da safe, Amma bata dauka ba, Shima Kuma bai sake kira ba.
Da rana, masu aikin gidan suka shirya abinci kamar yanda suka sabayi idan mama tana gari, cikin takun qasaita tataho tana tafe tana danna wayarta, Kai tsaye part din maman taje, abincin da aka shirya a dinning ta bubbude, cikin masifa tace "bazan iyacin wannan abincin ba, waye yabada umarni ayi wannan girkin?"

Cikin sauri daya daga cikin masu aikin ta d'ago kanta tace "Anty Idan Hajiya Mama tana nan haka mukeyi, dama kowacce rana akwai irin abincin da muke sauya wa, shiyasa yauma muka yi hakan"

Cikin masifa tace "okay, to yau nice ba mama ba, kuma bazanci wannan ba, saiku dauke kuje kusan yanda zakuyi dashi, saboda tsabar samun waje Ina zaune acikin gidan ban'isa ku tambayeni menake so adafa min ba? Maza maza ku kwashe minsu daga gabana aje azubar adafa Sabo a kawomin"

Cikin sauri suka kwashe abincin basu bar ko drinks ba, suna shiga kitchen suka Rasa Yaya zasuyi da abincin, daya daga cikin su ce tace "Bari nafita dashi ta kofar baya saina bayar awaje"

Dukansu na'am sukai da shawarar Tata, saboda zubar da abincin kamar almubazzaranci ne, Bayan suma dasuke zaune a gidan saboda neman abincin ne yasa suka nemi aikin a gidan.

Bayan sun shirya mata abinda takeso, part dinta ta wuce, akan kujera ta zauna tafara Kiran qawayenta, takira wannan takira waccan, duk da taga Kiran Shahaab, batabi ta Kansa ba, asali ma dadi taji yanda sukayi tafiyar Nan shida mama, yanzu gida ya dawo hannunta, Sai abinda takeso za'ayi, tasan suntafi Niger, inda ace de wani Garin yatafi daban to dole zata damu, saboda tana tsoron karya hadu da wata yarinyar ta dauke masa Hankali, Amma yanzu tunda tare yake da mama, batada damuwa, batada haufi akan mijinta tasan ita kadai ce acikin zuciyar sa, daga ita babu qari.(tofa=�D�)

Da daddare inusa yakira Aisha a wayar Hajja,sunsha hirarsu cikin kulawa, saide rabi zancen duk shine yakeyi, idan yayi mata maganar Hajja nema zaiga Nan da Nan ta ware tanata masa surutu, daga Nan ya fahimci cewa dole zai sake cusa Kansa awajan Hajja duba da yanda Ita kanta Aishan ta dauki Kakar Tata.


******


Washe gari ya shirya yatafi Abuja, tun ranar dayaje wajan Aisha har sukai waya da daddare, baisake kirantaba.

Yana zuwa gida kuwa munirat Sai Gani tayi Ana shigowa da jakarsa cikin falonta, cikin mamaki tafuto daga kitchen hannunta d'aukeda apple, tace "a a, my Dear daga Ina haka babu sanarwa? Harkun dawo?"

Zama yayi akan kujera tareda dora fillo akan cikin sa yace "nide nadawo, Amma mama tana can, Sai nanda 4 day's zata dawo, bata fada miki bane?"

Cikin yaqe tace "Dama...dama....ba Niger kuka tafi tare ba?"

Girgiza Kansa yayi, sannan yad'auki remote yana kokarin sauya Tasha, yace "tatafi ita kadai ne, nikuma naje Jigawa"

Gabanta ne yayi mugun faduwa, tarasa meyasa yake zarya a wannan qauyen, zama tayi akan hannun kujerar daya kwanta tace "Wai kana nufin Kai kadai katafi jigawa? Dan Allah my dear mekake yi a wannan qauyen ne? Wajan wa kake zuwa?"

Cikin mamaki yadago kyawawan idanunsa ya kalleta, sannan ya maida Kallan sa TV yace "to sarkin kishi, naje ganin aikin gidan marayu ne"

Haka kawai taji zuciyarta taqi yarda da maganar tasa, cikin tsananin kishi tace "idan ma wajan wata kaje, to wallahi kafada mata nafi karfin kishi da yar qauye, mijina yafi qarfin ta"

Murmushi yasaki tareda janyo ta tafado Kansa, dankwalin kanta yacire,gashin dokin datake sakawa yasakko kan fuskarta, kwata kwata yanzu jiyake gashin datake sakawar baya birgeshi, yafi son irinna Aisha, ahankali yad'ora kannata akan faffadan qirjinsa ya rungume ta tsamm ajikinsa tareda Lumshe Idonsa, wannan kishin datake yi akansa, saiya tuna masa da Aisha, sake rungume ta yayi yanaji kamar Aishan ya rungume (=�F�<���
@&�>�-�)

munirat kuwa ganin irin rungumar daya mata yasa tayi shiru tareda yin luf a qirjinsa, dama akusa take, saboda kwana biyun Nan abuqace take dashi.
Cikin jin dadi yace"waye ya'isa yaja da uwargida? Um? Fadamin me kike so?"

Dukda itama idonta a Lumshe suke, saida jikinta ya danyi Sanyi kadan, duba da yanda koda yaushe burinsa shine tafada masa metake so? Kuma tasan cewa inda tafadi wata buqatar to babu tantama yimata ita zaiyi, ahankali tasake qanqameshi ajikinta

******

Ummah ce da Hajja suka dawo daga gidan Alhaji Audu, Bayan sunje sunyi wa matarsa murna akan gidan mansa da aka saki, suna zama Hajja ta kalli Abba dazai fita tace "mamuda kaje kayiwa Alhaji Audu murna kuwa akan gidan mansa?"

"eh naje tunda safe, saide Allah yaqara kiyayewa gaba"

Aisha tana jinsu gabanta yafadi, hakan yana nufin kenan da gaske Shahaab, ya fadawa ogan sa maganar gidan man Alhaji Audu? Kenan da gaske shidin Yaron Mahmud Wakili ne? Wani irin farinciki taji ya kamata, wayar Hajja ta d'auka zata kirashi, Sai Bayan takira taji wayar tasa akashe, a fili tace "Allah ya dawo dashi watarana Sai nayi masa godia"

Hajja tace "me sunan qawa zoki siyomin Goro a gidan iya hansai"

Futowa tayi, fuskarta d'aukeda murmushi tace "kawo kudin"

Kudin tabata, Aisha ta kar6i kudin ta duba da kyau, sannan tace "Hajja riqe ashirin dinki, kudin Nan bazai kar6u ba"

Hajja ta bude baki ta kalleta tace "to kawo insauya miki wannan din Sai mamuda ya rufata a qirjinsa yana yawo" (>�-�>�#�)

Babu musu tabata, saida ta sauya mata, sannan taje tasiyo mata Goron takawo mata.

Yau Kwanansa biyar da dawowa Abuja, mama kwanan ta takwas a Niger

Kiran wayarta yayi, yasan duk inda take yanzu de jirginsu yakusa tasowa, Bayan ta d'auka yace "mama kun kusa tasowa ne?"

Ta6e baki tayi tace "to Shahaab matar gida ta tsaneni saboda Allah Ina Naga ta dawowa?"

Shiru yayi, cikin ransa yace "to akwai matsala kenan"

Mama kuwa dataji yayi shiru taci gaba da cewa "matarka bata sona Mahmud, tun cikin azumi Rabon danasa ta a'idona, ranar sallah ma batazo inda nake ba, awayama bansamu matsayin data kirani tamin barka da sallah ba,haka dazanyi tafiyar Nan, batamin Allah yakiyaye ba, yau kwanana takwas awajan dangin mahaifinka nanma batamin waya ba, Nima Kuma anan duk lokacin dasuka tambayeni Ina matarka Sai ince musu bansan inda take ba, saboda Allah idan tana Sona ai zata zo Niger din tayi bikona, Amma zanyi maganin ta, Dani take zancen"

Ran Shahaab idan yayi dubu Toya 6aci yau, yanzu abubuwan na munirat har yakai haka? Mahaifiyarsa? Idan yafara Bawa mama haquri qara tunzurata zaiyi, Gara yabi da'ita yanda takeso, inyaso ita Kuma munirat, su gauraya shi da'ita.

Ajiyar zuciya ya sauke yace "eh gaskiya hakane mama, kinada gaskiya bakya dawo ba, inda ake sonka ai Nan kake zuwa"

Mama tace "ato, Nima abinda nagani kenan, ni yanzu na tattara munirat na zubar, Ina dalili?Gara inyi zamana anan"

Cikin sauri yace "a a mama, ba za'ayi hakaba, kiyi hakuri, ni zanzo indaukoki, idan kowa yaqiki aini bazan qikiba mama"

Tace "yawwa, Gara kazo dinma, kazo ka nuna mata Nina haifeka"

Yace "angama mama"

Sannan sukai sallama, munirat ce tafado masa Arai, kina zaune gida daya da mahaifiyata Amma kikasa zuwa ki gaishe ta? Meyake damunta ne?

Agogo ya kalla karfe shadaya na safe, waya yayi atanadar masa ticket din tafiya jigawa.

Tashi yayi yafara zuba kayansa a wata yar qaramar jaka, yasan idan yaje Niger bazai iyu su barshi ya dawo a ranar ba, dole zai musu kwana biyu, daga Nan saiya taho da mama, Amma kafin Nan zaije ya kaiwa Aisha biro dakuma ribbon din daya siyo mata daga Saudia.

Saida yagama hada komai har ribbon din yana cikin jaka, sannan munirat tashigo Dakin, ganinsa da Kaya yasa ta tambayeshi, "my dear Ina zakaje?"

Fuskar sa babu alamun wasa yace "jigawa"

Ranta ne ya6aci jin inda zaije, gashi bataga fuskar yimasa ihu ba.

Gaba daya ya tamke fuska kamar ma haushinta yakeji, Shikuwa Shahaab abinda tayiwa mama ne yasa yake jin inda yana duka Toda ya rufe munirat da duka yau, da niyya yaqi 6oye mata inda zaije, saboda yasan ta tsani yaje jigawa, yarasa dalilin ta akan hakan.

Ko Kallan inda take baiyi ba yafice yabar mata Dakin, yana fita driver yadaukeshi, Biron Dayayi order Nan suka fara zuwa ya Kar6a, sannan yawuce Airport, basu dade da zamaba jirginsu yatashi, har yanzu jin ransa yake adagule, Bayan jirginsu ya sauka wani driver ne yasake kaishi hotel, Sai Bayan yayi wanka ya huta ne sannan yayi order abinci, spoon biyu yayi, yaji abincin babu teste, tureshi yayi, sannan yafada kan gado yakira Ramadan kozai bashi shawara akan abubuwan da munirat takeyi akan mama,Amma wayarsa akashe.

Dafe Kansa yayi, yarasa meyake masa dadi, Aisha ce tafado masa, ahankali yasake daukan wayar Yakirata.

Bugu daya, Hajja ta dauki wayar,batayi magana ba yaji tana cewa "ke ungo wannan wayar, inajin inusa ne, dankare da shegiyar rowa, har yanzu baikawo miki kudin barka da sallah ba, tayaya ma zan dauke ki nabashi?"(>��)

Bakinta ta turo gaba, cikin shagwa6a tace "Kai Hajja Dan Allah, to Ina ruwanki da kudin dazai Bani? Naga baya Nan yaje dutse"

Hajja tace "oh... Ai jinake rowar samarin zamanin ce tatashi"

Cikin daki tashige, saida ta kwanta akan gado sannan tayi qasa da murya tace "Hello"

"who is Yunusa?"

Aisha tace "na'am?" alamun bata jishi ba

Cikin wani irin 6acin rai da tsananin kishi yace "nace waye Yunusa?"

Bakinta ta turo gaba kamar yana ganin ta, cikin shagwa6a tace "saurayi nanefa"

Cikin masifa yace "maaama, ni kike fadawa saurayinki ne? Waye ma yabaki damar dazaki dinga magana da maza? Waye yace ki saurare shi?"

Har yanzun bakinta yana gaba, tace "Hajja ce"

"okay kina sonsa kenan, yar qarama dake samari zasu fara zuwa wajan ki, kema Kuma har kulashi kike tunda gashinan har wayama kunayi ko?"

Tace "nito ya zanyi?"

Baqin ciki ne yasake kama Shahaab, Yakirata danya danji sauqi Amma gashi yasamu wani baqin labarin, cikin masifa yace "look... Maama You know what? Idan nasake jin kince min saurayinki ne, Sai ranki ya6aci, karatu zakiyi, babu wani aure da zakiyi, ko shekara Dari kikai babu aure bazaki Rasa mijin aure ba"

Cikin sauri tace "eh bazan Rasa ba Amma ai saide Tsoho"

Cikin sigar lallashi yace "kenan kina son saurayinki, bazaki rabu dashi ba ko?"

Murya can ciki tace "to ai Shima yana sona, Kuma yanason Hajja"

Wata irin wawiyar ajiyar zuciya yasauke, domin kuwa amsar data bashi ka kadai ta'isa yasa ya gane cewa ita din ba lalle tanason Yaron ba, duk dade bata futo fili tafada masa tana son inusan ko bata sonsa ba, lalle ya kamata yad'auki mataki akan Yaron koma waye shi, bazai iyu yana abota da yarinya wani Kuma daban yazo yana soyaiya da'ita ba, a ko'ina abota gaba take da soyaiya =�D�=�D�
Ahankali yace "kina gida ne?"

Tace "um..."

"Anjima zanzo, kibar wayarki awajanki,"

Tace "to"

Har zai kashe, saiyace "fishi kike Dani?"

Cikin shagwa6a tace "nifa ba fishi nake ba, bakaine ba kake tamin fada..." tana fadar haka Sai kuka

Dafe Kansa yayi, cikin qasa qasa da murya yace "shikkenan to yi hakuri, nadena, shikkenan?"

Tace "eh, saikazo"

Kashe wayar yayi, yana mamakin yanda kuka baya mata wahala, kamar wanda take zaune cikin tsofaffi, kokuma yarintace take damunta waya Sani.

Allah Allah yake dare yayi yatafi, jiyake kamar yana kan qaya, dazaran yatuno da maganar Yunusa Sai yaji sabon 6acin rai acikin zuciyar sa, wata zuciyar tace tokai menene abun damuwa tunda ba sonta kake ba? A fili yace "Bana sonta, Amma duk da haka ai tayi qanqanta da soyaiya yanzu"

Haka yadinga zirga zirga yakasa zaune, yakasa tsaye, dare nayi, yad'auki hanyar garinsu, tun kafin a shiga sallar ishsha'i yaje Garin, inda yasaba ajiye motar sa anan yayi parking yauma, Kiran wayarta yayi, wayar na hannunta, tana dauka tace "Gani nan"

Wajan Ummah taje, saboda Hajja tafita gidan qawarta jummai, cikin nutsuwa tace "Ummah zanje gidansu Walida na kar6o saqo nadawo"

Ummah tace "karki dade, kinga dare yayi"

Tace "to Ummah, sannan tafuto, a kofar gida taci Karo da Hajja, tace"Hajja natafi gidansu Walida yanzu zan dawo"

Hajja tace "konazo narakaki?"

Cikin sauri tace "A a nayafe"
Hajja ta wuce cikin gidan tana mita, Aisha kuwa Kai tsaye wajansa ta nufa, yauma dakansa yafuto yabude mata motar, sannan tashiga yarufe, Shima yashiga ya zauna tareda rufe motar, kanta aqasa tace "Ina wuni"

Cikin wata irin murya yace "maama"

Tace "um"

"bakya jin magana ta ko?"
Dan qaramin bakinta ta turo gaba, bata bashi amsa ba, Sai yatsun hannunta data fara wasa dasu
Cikin sigar rad'a yace "mekikeji aranki game Dani?"

Ahankali tace "Babban mutum, Mai kima da mutunci a'idona"

Jinjina Kansa yayi, sannan yace "Bayan wannan fa?"

Cikin murna ta d'ago kanta ta kalleshi tace "saikuma godia danake so nayi ma, ansaki gidan man Alhaji Audu, kayiwa oganka godia, a tarihin rayuwa ta, yau Mahmud Wakili yayimin abinda yasakani farinciki"

Murmushi yayi yace "da gaske?"

Cikin farinciki tace "sosai, kafadamin, meyasa kake zuwa Garin Nan?"

Batare da 6oye 6oye ba,yace "saboda ke"

"nikuma?"

Tace "saboda ke nake zuwa, inajin dadi idan Ina Kallan kyakykyawar fuskarki"

Cikin kunya ta rufe idonta

Murmushi yayi yace "Kidena kula samari, kinji ko?"

Daga masa Kai tayi, ya matso kusa da 'ita yace "kinyi alqawari?"

Tasake daga masa Kai,yace "tayaya zan gane kinyi min alqawari babu Wanda Zaki sake kulawa?"

Yatsun hannunta tahada guda biyu sannan ta bashi tace "mu daura alqawari"

Dariya ce ta kamashi, wannan abun datayi saiya tuna masa da lokacin dasuke Yara, haka suke yi shida Ramadan, saida yagama dariya sannan ya kalleta yaga tana kallon sa da mamaki, da alama bata ta6a ganinsa yana irin wannan dariyar ba, hannunsa yad'ora akan Nata, suka qulla hannun su waje daya, sannan yace "shikkenan, kiriqe min alqawari na"

Tace "insha Allah,zan tafi gida, Ummah tace karna dade"

Yace "Okay, gashi" yafadi hakan tareda miqa mata wani sabon biro mai mutuqar kyau, cikin wani Dan qaramin kwali

Kar6a tayi, ta bude kwalin sannan tad'auki Biron tareda ajiye kwalin, cikin murna tace"nagode sosai, gaskiya yayi kyau, banta6a ganin biro Mai kyansa ba,Allah yasaka da alkhairi yaqara budi"

Cikin jin dadin addu'ar data masa yace "Amin,banga kitson sallar ki ba"

Cikin mamaki tace "kitso? Aini Bana kitso sosai, da sallah ma banyi kitso ba"

Cikin jin dadi yace "mugani"

Batare da tunanin komai ba, tad'an zame dankwalin kanta, tace "kagani?"
ribbon din daya siyo mata a Saudia yadauko ya nuna mata yace "indaure miki gashin da wannan?"

Tace "eh"

Matsowa yayi dab da'ita, sannan ya janye hijabinta zuwa kan kafadarta, dankwalin yacire, lokaci daya yayi tozali da dogon gashinta me laushi, saida gabansa yafadi saboda ganin yawan gashin Nata, babu ribbon akan Nata, saide takame shi waje daya ta daure, zamansa ya gyara, yadan janyo kanta yad'ora akan cinyarsa, jitayi kayan nasa yana qamshi me dadi, batare da tsoron komai ba ta Lumshe idonta.
Hannunsa yasaka ya warware gashin Nata, laushin dayaji a gashin ne yasa yafara shafashi ahankali,sannan yadauko ribbon din ya daure mata gashin dashi, maimakon yasaki gashin Nata, saiyaci gaba da wasa da gashin, yana shafa gefen fuskarta,yanayin daya fara tsintar Kansa aciki ne yasa ahankali yasake hade qafafunsa waje daya, but duk da hakan Sanadin dora kanta Dayayi awajan, saida ya haddasa masa shiga cikin wani yanayi.

Ahankali ta d'ago kanta tace "waye yabaka ribbon?"

Cikin Lumshe ido, murya a dashe yace "kena siyowa"

Cikin murna tace "nagode"

Kallan ta yayi, yanda ribbon din yayi mata kyau da yanda yayi mata parking din gashin Saitayi kyau kamar ba yar hausawa ba.

Cikin wata irin murya yace "tashi kije gida, idan zanzo zamuyi waya okay?"

Cikin jin dadi tace "to nagode"
sannan tafara kokarin daura dankwalin ta
Cikin mutuwar jiki yasaka hannunsa ya daura mata Dan kwalin, sannan ita Kuma taja wuyan hijabinta tamayar dashi, tayi masa sallama tatafi gida.
Lumshe Idonsa yayi Bayan fitarta daga motar, saida yaji yanayin sa yadan daidaita sannan yaja motar yabar Garin.
Alhamdulillah mutara zuwa gobe=�O�

(to wannan mu'amula ko Yaya zata Kaya? >��>��)

Anya Shahaab baiyi kuskure ba akan qaryar dayake yiwa Aisha?>��>��



Littafin Shahaab na kudi ne,idan kika karanta min batare da kin biyaba keda mahaliccinki tunda littafi de ba tsada yayi ba,ki biya ki karanta halak dinki Bana Allah ya'isa ba, ga Wanda suke nemana su nemeni ta wannan number 08033300034
El Yaqoub
'<���



Tana shiga gida taga ummanta a tsakar gida tace "Ummah nadawo" batareda tajira amsar da umman zata bata ba, ta wuce Dakin Hajja Kai tsaye, batareda sanin muhimmancin Biron daya bata ba, ta jefashi cikin jakar makarantar ta, fitilar wayar takunna sannan ta matsa gaban madubi ta haska fuskarta da fitilar, juyawa tayi ta Dan kalli parking din gashinta Wanda Shahaab yayi mata, ahankali tasaka hannu ta shafa ribbon din, sannan tace "yanada kyau sosai"

Hajja data futo daga bandaki ta ajiye buta tashigo dakin, ganin Aisha agaban madubi tace "to me akeyi Kuma da wannan Daren ko Kallan abun ake yau ma?"

Cikin sauri ta juyo tace "eh, idan nagani ma ai nawane ko?"

Hajja tace "naki ne Kam, tsaya inkar6o miki fitilar Hadiza saiki sake haskawa yanda zamufi Gani da kyau..." (=��)

Hararar ta tayi, sannan tafice tabar mata d'akin.


******

Kasa bacci yayi kwata kwata, duk yanda yaso ya runtsa cikin dadin rai, kasawa yayi, Kiran wayar mama ne yashigo, cikin wata irin murya kamar ta d'an maye, wadda kanaji zakayi tunanin yana tare ne da mace, kokuma yana cikin wani yanayi,Ahaka yadauka, mama tace "Shahaab lafiya naji ka shiru baka zoba?"

"zanzo gobe" yafadi hakan tareda sakin wani irin numfashi
Cikin zuciyar ta tace "lafiya yake kuwa?"

Afili saitace"kana tareda munirat ne? "

Kai tsaye yace"Eh"

Tace "to Allah yakaimu goben, saikazo" bata jira amsarsa ba takashe wayar

Lumshe Idonsa yayi, tareda sake rungume fillon dake hannunsa, tsawon wani lokaci yana haka, sannan yabude Idonsa yakira number wani mutum, daga dayan bangaren akace "Barka da dare Mr Mahmud"

Ahankali yace "Doctor babu wani magani dazaka Bani ne Wanda zaisa indaina jin feeling ko Yaya ne?"

Doctor yace "subhanallahi, meyayi zafi haka? Tun akwanakin baya kayi min wannan tambayar nace shan magani irin wannan baida amfani, saboda kanada mata, sannan ka godewa Allah ma, kanada lafiya, samun maza irin haka, abune Mai mutuqar wahala, Kaci gaba da saka wannan panties din, suma is okay, banaso in doraka akan wani magani Wanda zai iya zame Maka matsala wata Rana, musanman ma damuke fatan kasamu haihuwa a kowanne lokaci.... "

Dif Shahaab yakashe wayarsa, yarasa meyasa likitansa yake masa haka? Dan yanada mata saiyaqi shan magani saboda sha'awa? Inda yana samun cikakkiyar gamsuwa awajan matar tasane to Shima babu abinda zaisa yanemi wani magani, to Amma baya samu,dole yanemi magani, shikuma Doctor yakasa gane hakan.

Daqyar yasamu bacci ya dauke shi a wannan dare, da sassafe yayi shiri yatafi Niger.


******


Kwanansa biyu a Niger,suka dawo Abuja shida mama,tun Bayan saukarsu a gidan mutane suke sallama falon Nata, daga wannan yafita Sai wannan yashigo, kowa zuwa yake yana yi mata barka da zuwa, ma'aikatan gidan kuwa kamar su zuba ruwa aqasa susha saboda murna, duk yanda mama takai ga yin mulki da izza, sunfi jin dadin zama da'ita akan munirat, mama tana komai ne cikin aji da Kuma tinqaho ita mahaifiyar me gidan ce, munirat kuwa kullum cikin yimusu masifa take, ga tsawa, kwata kwata bata kama girmanta na matar Mahmud Wakili.

Dukansu suka hado kansu sukazo yimata barka da zuwa, Shahaab yana Gefe yana danne danne awaya, yana Sanye cikin suit, jacket din suit din tana riqe a hannunsa, Adede lokacin munirat tashigo, ganin mama da Kuma ma'aikatan gida suna zaune agaban mama, yasa ahankali yatashi yayi wa munirat wani irin kallo Wanda shi kadai ne yasan ma'anar sa, sannan yayi part dinsu.

Mama kuwa nunawa tayi batasan munirat tana wajan ba, haka tabawa banza ajiyarta, ta kalli ma'aikatan sannan ta bude babbar jakar hannunta wadda take cikeda kudade,tadaga jakar ta zazzage kukaden ciki aqasa sannan tace musu "kudebe wannan kuje kuyi shagali na murnar dawowa ta...."

Kafin tarufe baki suka kama wawar kudin, Nan da Nan fuskar kowa tacika da farinciki Sai zuba mata godia suke, hannu kawai ta daga musu alamun su tashi suje, Nan da Nan kuwa kowa ya watse.
Harara ta watsawa munirat datake zaune agefen kujera tana kallon ikon Allah, sannan tatashi zata shige daki, cikin sanyin jiki munirat tace"mama ya hanya?"
Mama ta juyo ta kalleta tace"Dama kinsan nayi tafiya ne?"
Ahankali tace"kiyi haquri mama, nayita kiran wayarki but bata shiga, Amma insha Allah hakan bazai sake faruwa ba, I'm sorry mama"
Tafadi hakan tana dora hannayenta akan kunnan ta.

Mama tasaki ajiyar zuciya tace"tashi kije wajan mijinki, yana'iya dake?"

Daga Nan ta wuce dakinta, cikin sanyin jiki itama munirat tatafi part dinsu.


******

Yau tunda safe, Aisha take aikin tunanin Shahaab, tarasa meyasa inde ta tunoshi Sai taji wani irin farinciki, har so take ta dinga tunanin sa, jiya da daddare Inusa yazo zance Qin fita tayi, acewarta ita batada lafiya (=�F�<���
@&�=�3�)

Cikin zuciyar ta tace "yakamata nafara azumin sitta shawwal kodan addu'ar danace zanyi wa Shahaab, Allah yabashi haihuwa idan yayi aure,"
Tunanin tasake tafiya, tambayar kanta take ko wa zai aura?, itade tasan baya

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment