Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hauwi, harda tsarabar ku ta Saudia zan kawo muku yanzu yanzu"
tana fadar haka tajuya zuwa dakinta, sukuma suka hada ido tareda ta6e baki, kowaccensu haushi takeji Dama itace a matsayin da munirat din take.


Tunda yashigo yaga munirat bata biyo shi ba, saiya kwanta agadonsa tareda d'ora Kansa akan hannayensa ya zubawa Saman Dakin ido ya fad'a duniyar tunani, tunanin sa yayi zurfi ko shewar da qawayen munirat suke yi ba yajin su.


Mamakin Kansa yake, yana jinsa kamar bashi ba, haka Nan yakeji kamar ansauya shi, Bai ta6a tunanin akwai wata yarinya dazata tsaya masa a ransa Bayan munirat ba,saboda yasan Kansa, yasan bazai ta6a son wata yarinya bayantaba.

To Amma meyasa tunanin yarinyar yakasa barin qwaqwalwar sa? Wata zuciyar tace dashi "may be Dan kanason Yara ne, Kuma ka ganta yar qarama kamar Baby shiyasa kake tunanin ta"

Wata zuciyar Kuma tace dashi "kokuma saboda maganganun data fada Maka ba"
to kuwa in hakane dole ya nemeta domin yaji dalilin dazaisa tace masa matsiyaci, Shima abun atuhume shine, shi me yayi?

But ta wacce hanya zai sake ganin ta?

Cikin jin haushin Kansa yace "Wai meyasa zan damu kainane, saboda wata qanqanuwar yarinya?

Munirat ce tashigo Dakin Bayan ta sallami qawayenta.

Jin shigowar Tata ne yasa Shima ya watsar da tunanin yarinyar, saboda shide yasan cewa ba sonta yake ba, to menene zaisa yadamu Kansa akanta?
Kwanciya tayi agefen sa ta dora kanta akan dantsan hannun sa, cikin kulawa tace "tunanin mekake my Dear?"

Kai tsaye yace "Haihuwa"

Gabanta ne yafadi, tatashi zaune tana Kallan sa tace "My Dear haihuwa ta Allah ce, nide nasan lafiya ta kalau, Kuma kaima haka, sannan sisters dina dasukai aure kowa tana haihuwa a gidanta, Kuma my dear ni banga abunda zai saka tunani ba, kanada komai na rayuwa, meyasa zaka damu saboda haihuwa, ni Bana tunani akan haihuwa, saboda nasan lafiya ta kalau, Kuma haihuwa gadon Miji takebi ba gadon mata ba, inda gadon mata takebi to da tuni na haihu,tunda Bani kadai momy na ta Haifa ba, so nasan matsalar daga kaine, tunda mama ma Kai kadai ta Haifa......"
( '<���)hannu kawai yadaga mata, batare daya kalleta ba yace"please Leave me alone ok?"

Babu musu tatashi tafice daga d'akin Sai mita take cikin ranta, Dame ta rageshi a rayuwa? Kullum cikin neman magunguna take saboda ta gyara kanta yasamu yaji dadi, Amma duk da haka baya Gani, yaje wajan masifaffiyar tsohuwar sa ta hure masa kunne akan haihuwa, Nima zaizo ya dameni.

Shikam tana fita runtse Idonsa yayi, me munirat take nufi? Kenan shine baya haihuwa ba'ita ba? Duk haqurin Dayayi akanta yake zaune da'ita shekara da shekaru bai ta6a yunqurin qarin aure ba shine take fada masa shi kadai mama ta Haifa? Tsaki yasaki yatashi yafita daga gidan gaba daya, ko ruwa baisha tareda su ba, a masallaci yasha, Bayan an idar da sallah ma bai dawo gidan ba Sai wajan shadayan dare,munirat tun tana jiran dawowar sa taji shirun yayi yawa saboda Bahaka yasa baba, saita zargi kanta, kanta tayi wa fada karfa taje yakoyi Zaman waje duk da tasan ayyukan sa bazasu barshi ba, Amma idan ya Koya lokaci daya zasu zigashi yafara neman aure, ita Kuma abinda bazata juraba kenan, shiyasa yana shigowa ta rungume shi tareda fashewa da kukan kissa, tun yana shareta har tayi nasarar shawo Kansa yahuce

******


Yau Aisha gajiya tayi da girkin, gashi Ummah batada lafiya, itama Kuma tagaji, ita Kuma Hajja tana kulada sana'ar qanqarar ta, Dan haka itama yau tayi fuska ta wuce Dakin Hajja tayi kwanciyar ta
Saida Hajja tagama siyar da qanqara lokacin har hud'u na yamma ta gota sannan ta nemi waje ta zauna, taleqa daki tace "me sunan qawa, futo kije ki siyo mana Dan tattasai kidafa macaroni ko jallop ce"

Cikin shagwa6a tace "wallahi Hajja nagaji sosai, jinake kamar na fadi"

Hajja ta Jinjina kanta tace "ai shikkenan Naga alama yau iskanci kikeji tonima nazama yar'iska, kowa ya zauna da yunwar sa" (>�-�)

Aisha tace "A a Hajja, abun bekai nanba,ni Bana fada da Azumi, saide in qarshe aka kaini" daga Nan tafuto daga d'akin tasaka hannu acikin cinikin Hajja tad'auki kudin tattasan,sannan tafita taje tasiyo tadawo ta dora musu abincin


******

Kwana daya Shahaab yayi yana yaqi akan tunanin Aisha, daqyar ya'iya yin wuni daya, da yaji zuciyar sa tana so ta kawo masa tunanin yarinyar, Sai yayi sauri yad'auki wani abun dazai dauke masa Hankali,acikin kwana dayan Nan wuni yayi da jarida a hannunsa,har munirat tana mamakin sa, to Amma Kuma karatun jaridar ma daya fara zata Fado masa, baisan lokacin Dayayi wulli da jaridar ba aikuwa tayi d'aid'ai a falon nasu (=��)

Yau tunda sassafe ya shirya yafita office, yanaso ya tsiri aiyuka dayawa ko hakan zaisa ya yakiceta a ransa, saide yana zuwa ma aikata suka shaida masa cewa yaune ranar dayasa zasuyi meeting akan sabbabin masu bada horo daya gayyato daga qasar Germany domin su sake wayar wa da sabbabin ma'aikatan su dasuka dauka wannan watan Kai.

Hamdala yayi a ransa, yaji dadin hakan sosai saboda shaf Yama manta da wannan batun, shadaya daidai na safe suka fara meeting din.

Qwararrun masu bada horon ne suke bayani cikin salon birgewa dakuma sanin makamar aiki dangane da yaqi dacin hanci da rashawa, Dafarko Kam a nutse yake, yana kallon komai daki-daki yanda yakamata, Amma basufi minti talatin ba da fara meeting din ya Lula duniyar tunanin ta....,wata zuciyar tace dashi "kotayi dinkin sallah?"

Magana masu bada horon suke masa Amma inaaaa... Hankalinsa yariga yatafi, Ramadan dake gefensa yata6ashi, firgigit yayi ya dawo cikin hayyacinsa, Kansa yadafe ya kallesu yace "am.. Idan babu damuwa Dan Allah kuyi hakuri kuci gaba da metting d'in, inada wani Babban uzuri agabana"

Daya daga cikin ma'aikatan efcc din yace "Amma Boss maganar dasuke fa tanada muhimmanci, yakamata ka tsaya..."

Agogon hannunsa ya kalla yace "kuyi hakuri please, Babban uzuri gareni" yajuya ya kalli baqin nasu yace "mr Jone next time ok?"

Kafin wani yasake magana yad'auki jacket dinsa, tareda zira hannunsa guda daya cikin aljihun wandonsa, cikin sauri yafice.

Gaba d'ayansu da Kallan mamaki suka bishi, Bai ta6a yin hakan ba, kowa yasan inde akan aiki ne yana tsayawa ayi komai a gabansa, su kansu baqin basu so yatafi ba, saboda sun so ace yana Nan suka gama bayanin komai, koba komai zasu samu Jinjina daga gareshi.
Ramadan ne yasake basu haquri yace "may be baida lafiya ne, Bari in bishi"

Sun yarda da abunda Ramadan din yafada, tabbas Mahmud Wakili ba qalau yake ba yau.

Tunda yabar Dakin meeting din nasu, Kai tsaye office dinsa yawuce yafara dube-dube cikin loka yana tunani a ransa, ba lalle ne yar qarama tayi dinkin sallah ba, wata loka yabude yafuto da kudi bandir biyu, Yan dubu dubu, aqalla zasu Kai nera dubu Dari biyu,Adede lokacin Ramadan yashigo, yayi mamakin ganin kudi ahannunsa, cikin damuwa yace "meyake faruwa ne Abokina?"

Bai iya qarya ba, haka Kuma bayason yakoya yanzu, danhaka batare dawani 6oye-6oye ba yace "wata yarinya zanje nakaiwa"

Ramadan Kam baisan lokacin daya kwashe da wata irin dariya ba, kujera ya gyara ya zauna yadinga dariya harda Tari.

Baqin ciki ne yakama Shahaab, yazubar da kudin akan table din gabansa, sannan ya zauna a kujera ya jinginar da Kansa a jikin kujerar yana Kallan rufin office din, saida yagama dariyar sa son ransa, sannan yajuya ya kalli Shahaab, baya buqatar yayi wani bincike yasan cewa abokin nasa yagama kamuwa cikin tarkon wata yarinyar, ahankali cikin nutsuwa ta sigar lallashi yace"Shahaab kode kafara son wata yarinya ne?"

Ransa ne ya6aci, cikin fishi yace" wacce irin banzar magana ce wannan Ramadan? Dama tunanin dakake akaina kenan? Yarinya qarama cefa, 'yar cikina, nama haifi wannan yarinyar, sannan Kuma.... Ba data kunya ma.... "

ya qarasa maganar qasa-qasa kamar baison Ramadan din yaji, fuskar Nan yahade ta kamar sabon hadari

Ramadan da yaga Shahaab bai gama yarda son yarinyar yake ba, Sai yayi haquri ya bishi a yanda yake so din, cikin hikima yace" okay,naji, kadena cewa yar cikinka, tunda ba kaine ka haifeta ba, ai Dafarko nayi tunanin budurwa kayi mana, but koma de menene kada ka nuna mata cewa Kaidin kanada Hali "

"menene danna nuna mata inada kudi Ramadan?saboda me zanyi mata qarya Bayan ba sonta nake ba? Idan tagano nayi mata qarya mutunci na zubewa zaiyi a'idonta, yanzun ma abinda yasa kaga na dauki kudin Nan Ina tunanin ba lalle ne tayi dinkin sallah ba, shine zan Kai mata tayi "

Ramadan yace"A'ina yarinyar take ne? Tasan Kai waye?"

Girgiza Kansa yayi yace "no, bata sanni ba, tana jigawa, qauyen damuka raba kayan Azumi, harni take cewa ni abun atuhume ni ne?sainaje nasaka tafadi abinda yake ranta da bakinta"

Mamaki yakama Ramadan, gashi babu damar tambaya kar abokin nasa ya harbo jirginsa,yanzu awannan qauyen Kuma cikin dare har yaga yarinyar datasa yake wannan rawar jikin? Cikin kwantar da Hankali yace "Abokina, inde wannan qauyen ne wallahi kana bata wannan kudin, guduwa zatayi, zatayi tunanin saceta kazo yi, kokuma kaidin Dan yankan kaine, tayaya zaka dauki kudi haka a fili kawai kabawa yarinya Bayan kace bata sanka ba?aikuwa kana bata wannan kudin yanzu nema zatace tabbas kaidin abun atuhumeka ne, Kayi hakuri ka dauki ko dubu biyar ne kabata, ahankali ahankali zata saba dakai harka bata kudaden masu yawa, Amma bade lokacin farko ba, tunda Naga kanaso ka taimaka mata ai nasan ganin ta kake kamar 'yarka, shiyasa kake tausayin ta, Amma Kuma yanada kyau koda abota zakayi da'ita to kasan halaiyarta kafin kufara, yakamata kasamu Mai sonka da abota ta tsakani da Allah bawai don kudinka ba "

Cikin damuwa yace
"Ramadan tayaya zan'iya mata kyautan dubu biyar? Kamar Almajira? Banason qarya, bazan zo daga baya tasan koni waye qarshe tamin rashin kunya ba, Gara infada mata gaskiyar koni waye, sannan inji dalilin dazaisa tacemin matsayaci, idan taqi fada Kuma sainasa ankama ta na zaneta dakyau yanda zata Dena rashin kunya"

Ramadan da jikinsa yayi yayi Sanyi akan maganganun Shahaab saiya tafi duniyar tunani, tabbas Shahaab yanason wannan yarinyar koma wacece,to da alama akwai abinda yahadasu har tayi masa rashin kunya, Wanda 6acin ran hakan yasa yakasa gane sonta yake.
bazai iyu yanaji yana Gani yabarshi yasake aure irinna munirat ba, Gara yafara gwada yarinyar yaga hankalin ta, to Amma shi Shahaab yadage baison qarya, ahankali yasaki ajiyar zuciya yace "zaka iya Abokina, mu gwada hakan"

Badon yasoba haka ya yarda da shawarar Ramadan akan zai 6oye mata koshi waye yaje mata Ahaka, Amma da yayi niyyar yaje ya fuskance ta, yafada mata shine Mahmud Wakili ba Shahaab ba, kamar yanda yafada mata ranar, sannan Kuma yasa tafada masa dalilin ta na zaginsa, Kuma yabata kudin takar6a Dan dolenta (tofa=�2�)


******

Da daddare inusa yazo, yaturo wani yaro Akira masa Aisha, gaba dayansu suna zaune atsakar gida, Yaron yayi sallama yace "Wai Ana Kiran Aisha inji Inusa me Kanti"

Hajja tace "hmm Kaikuwa yaro daga Kai har Inusa me katin Baku iya sakaya suna bane? Aisha haka gatsau ko dadin ji babu? To daga yau karna qaraji,jekace masa gatanan zuwa"

Yaron ya amsa da "to" sannan yafita

Aisha kuwa tanajin Kiran ranta ya6aci, saboda shirin tafiya sallar Ashan take yi, batason yin fashi kullum Sai taje, Kuma hakan baya hanata anjima ma karfe daya da rabi na dare tasake komawa sallar tahajjud,Amma yarasa yaushe zaizo Sai yanzu? To kode shi baya zuwa tarawih din?

Hajja tace "ba kiranki ake bane me sunan qawa?"

Tashi tayi tad'auki hijabin Sai turo dan qaramin bakinta take gaba, tana saka takalmi Hajja tace "zoki dauki dan ruwan Sanyi a fridge kitafi masa dashi, idan kinje Kuma kifada masa karya sake cemiki Aisha, uwarki da ubanki ma me sunan qawar Hajja suke cewa, danhaka karya sake cemiki Aisha, qawata tanada daraja ba sa'ar uwarsa bace" (=��>�-�)

Itade Aisha batace komai ba tad'auki ruwan tafice, da sallama ta qarasa suka gaisa, tace masa "Inusa ga ruwan Sanyi inji Hajja"

Murmushi yayi yace "Haba Aisha, Inusa Kuma? Kuma kowa yana cewa Inusa kema Inusan zakice?"

Tace "Tome zance?"

"a a, Yunus zakice, ai awajanki sunan na daban ne"

Zuciyar ta daya tace "Nima to kadena cemin Aisha, sunan qawar Hajja gareni, Kuma su Abba ma basa fadar sunan saboda irin sunan Hajja ne"

"ikon Allah, to Amma Aisha arasa sunan wadda za'a saka miki Sai sunan qawar kakarki?"

Tace "Um Haka Hajja taso, Kuma Nima duk abinda Hajja takeso to inaso, saboda inason kakata, itama tana sona"

Murmushi yayi yace "Alhamdulillah kice Nima kinasona Kenan, tunda ai Dama kafin nazo saida akamin iso awajan Hajjan, yaushe zata fara kunun Ayar tane?akwai wani sikari (Suger) Dana dade da ajiye matashi, zan kawo miki shi saiki bata, tunda kince kina qaunar Hajja, nikuma kenake so, kinga Nima dole ne naso abinda kike so "

Ahankali tace" A a mungode Amma ka barshi "

"to ai kinji abinda yake had'ani dake, aini ne nayi niyyar baki,idan kikaqi kar6a ba zanji dadi ba, yanzu de Dama zuwa nayi naganki, ko zanji Sanyi araina, nasan zakije sallah, Bari nabarki haka Naga munyi kusan minti talatin, ga wannan naki ne, ki Kai a dinka miki da sallah, kudin dinkin yana ciki "yafadi haka yana bata wata baqar leda

Girgiza Kai tayi tace"a a nagode Amma ka barshi"

Tace "meyasa? Kode kin Rena?"

Kanta ta Girgiza masa, yace "to kar6i"

Hannu biyu tasa ta kar6a sannan tayi masa godia, yace "to yimin murmushi mana"

Kunya ce ta kamata, tasa hannu biyu tarufe fuskarta, cikin sauri ta wuce gida

Tana zuwa tabawa Hajja ledar , ta wuce ta dauki buta tayi alwala, Tai shirin tafiya masallaci

Hajja ta bud'e ledar atamfa ta bayyana, da kudi nera dubu biyu, atamfar irin ledar Nan ce me sauqin kudi (labona)
Hajja tasaki guda tace "Alhamdulillah, jikata tayi goshi, Hadiza, mamuda kunga abin Arziqin daya kawo mata, harda dubu biyu, tashi daya, yabata kudin albashin ta na wata guda"

Abba yace "Allah yasaka masa da alkhairi"

Ummah tace "ya kyauta, Allah yasa ayi damu, ai inusa bashida laifi, yana ganin girman manya duk inda yaganni saiya tsugunna yake gaisheni"


******

Yaso ace yanzu haka yana jigawa, yanaso yasake Sakata acikin Idonsa yaji dalilin dayasa take zaginsa, to Ramadan ya hanashi tafiya yace yabari su shirya sutafi tare.
Shikuma Ramadan dalilin dayasa yayi haka yanaso ne sutafi tare dashi danya dinga cusa masa ra'ayin yarinyar ahankali, harga Allah so yake Shahaab yayi aure ko Shima zai samu magaji

Mama ta kallashi, tunda ya dawo daga wajan aiki take lura dashi acikin tunani yake, kuma yakasa tashi yaje yayi wanka yacire wannan suit din ta jikinsa, hannu bibbiyu yayi tagumi yana kallo, Amma hankalin sa ba akan kallon yake ba,sau uku tana sauya Tasha Amma tana lura dashi ko motsi ba yayi Idonsa yana waje daya

Ahankali tace "Shahaab"

Cikin damuwa yajuyo ya kalleta yace "na'am mama"

Tace "har yanzu baka nemomin mekula Dani ba, koka manta ne?"

Maimakon yabata amsa saiya miqe tsaye, cikin damuwa yace "mama abubuwa sunmin yawa, kisa a duba miki kawai"

Daga yanayin yanda yake magana kad'ai zaisa kagane yana cikin matsananciyar damuwa
Ahankali tasake cewa "Shahaab"

Yajuyo yace "na'am"

"zonan"
Abinda tace dashi kenan, babu musu ya dawo gabanta zai zauna aqasan kafet din, cikin sauri tataroshi, ya dawo kan kujera, ahankali tajashi jikinta ta rungume shi, wata irin ajiyar zuciya yasauke, yasake qanqameta, sumar Kansa ta dinga shafa masa, ahankali har wani bacci me dadi ya dauke shi

Jin yasaki jikinsa yana bacci yasa tata6e baki, cikin zuciyar ta tace "banga amfanin munirat ba, mijinki yana cikin damuwa Amma ko ajikinki, yanzu haka damuwar akan office dinsu ne, tariga tasan inde akan wannan aikin nasu ne to baya kula da cikinsa ma kamar yanda yake kula da wannan office din"

Kusan awarsa d'aya yana bacci, mama da Hankalinta yakoma kan kallo can qasa-qasa taji Shahaab yana cewa " 'yar qarama...., 'yar qarama...."

Mamaki yakama mama, batasan lokacin data Kai dubanta gareshi ba, cikin zuciyar ta take cewa "wacece Kuma 'yar qarama?"






SHAHAAB littafin kudi ne,naira 300 ne kacal =�L�<���yar'uwa siyan nagari maida kudi gida, ki biya naira 300 ki karanta abinki Hankali kwance


Zaki tura 300 ta wannan account din


0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki tura shedar biya ta wannan number 08033300034













Amnah El Yaqoub
'<���
[10/09, 22:14] +234 803 697 8511: <�8�SHAHAAB<�8�
(Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook=�G�<���

https://www.facebook.com/amnahel




15&16



Kallan sa tasake yi, itade tasan cewa Shahaab baya kula mata, yanda yad'auki son duniya ya d'orawa munirat batajin wannan 'yar qaramar dayake fad'a da mace yake, takai shekara da shekaru tana fad'a masa yanemo yarinya ya aura, Amma har Zuwa yanzu saide yace mata shida munirat Sai Allah, tarasa Yaya zatayi dashi, shiyasa ta tattara shi ta watsa.
Ta6e bakinta tayi tad'auki remote tasake sauya Tasha

Sai yanzu ne yayi wani juyi, yaci gaba da baccinsa, yad'ad'e yana baccin sa me dad'i cikeda mafarkin Aisha, sannan ahankali yabud'e Idonsa,mama ta Kalle shi tace "katashi?"

Cikin shagwa6a yace "um"

Tace "to sannu da mafarki, d'agamin cinyata"

Gabansa ne yayi wata irin faduwa "karde mafarkin Dayayi yanzu mama tajishi" shiru yayi yakasa cewa komai, yasan cewa Saitayi masa tatas saboda yanda yaqi jinin a had'ashi da wata yarinyar, Amma yau gashi shine da mafarkin wata qanqanuwar yarinya, haushin Kansa ne ya kamashi, to Shima miye na mafarkin Nata? Daga kwanciya bacci, cikin baccin ma bazata barshi ya sarara ba?

Mama tace "karufawa kanka Asiri Shahaab, kar aikin ku yasaka ka koma qaramin mahaukaci, toma 'yar qaramar me kake kira?"

Cikin qaramar murya kamar baison magana yace "no mama kawai mafarki ne, akwai wata yar qaramar flower ne dana dad'e Ina nema" (>�-�)

"toshi fure har wani muhimmanci ne dashi dakuke neman sa yanzu? Wasa kakeji dashi, kaga tashi kaje kayi wanka,babu abinda munirat take Sai riqe waya, saika sata ta duba ma furen"

Hamdala yayi cikin ransa ganin bata ganoshi ba,daga mata Kai yayi sannan yatashi yatafi

Yana tafiya tad'auki wayarta tasa wata mata akano ta bincika mata yarinya wadda zata dinga kula da ita, Amma anan arewa takeson yarinyar, saboda ta gwada na kudu dayawa Amma babu abun Arziqi

Matar kuwa cikin ladabi ta amsa mata, sannan sukai sallama


******

Yau jummai ce tazo musu gidan tunda sanyin safiya, dukansu kuwa suna gida babu Wanda yafita, Abba ma yana kwance yana jin taskar labarai a redion Aisha.

Bayan sun gaisa ta nemi waje ta zauna sannan tace "Hajja A'i gulma ajali inba'ayi ba amutu, wani zance ne nazo muku dashi keda mamuda Da Hadiza, Amma kafin Nan kunada Dan magi kubani? Saboda yau dafaduka zanyi"

Hajja tace "bamudashi jummai, fad'amin meyafaru?"

Jummai Tace "Ina wannan bawan Allah mejin tausayi da jinqan al'uma? To dazu dazu yayata Datake kano tamin magana tace itama maqociyarta ce wata Mai kudi, tace Dan Allah ayi mata ciki yar aiki, zata turawa wata Hajiya datake zaune a Abuja yarinyar, to Amma hajiyar Abujan ance tanada mugun kudi sosai, Dan da yan kudu take dauka aiki Kuma kasancewar anga tana bada kudi kamar ruwa, Sai mutane suka fara asiri, kowa so yake dansa yaje yayi aiki a gidanta "

Hajja tace" ikon Allah na kwance yafadi..., to ita kwa wannan wanne irin kudi ne da'ita haka kamar yayi?wacece? "

Jummai tace"ai hajiyar Kanon tace wadda take neman yar aikin Mahaifiyar shugaban EFCC ce wannan Yaron de MAHMUD WAKILI, Wanda yamana Rabon kayan Azumi, Amma fa Ana bala'i sosai idan mutum zaiyi aiki a gidan, sannan Kuma akwai kudi sosai,Kuma ance matar tanada izzah sosai, saide Kuma duk masu aikin gidan ma kadai, suna cikin kulawa saboda akwai tsaro a gidan na sojoji da yan sanda, sannan masu aikin ma inde a gidan suke to sun riga sunyi kudi, sainake ganin ko Zaku tura mesunan qawarki, tunda zataci Tasha, ta dinga aiko muku da kudade Kuma"

Hajja tayi ajiyar zuciya tace"ai jummai kin 6ata zance tunda kikace Ana bala'i sosai idan mutum zaiyi aiki a gidan, menene abun bala'i a neman aiki duk dade itama mesunan qawartawa yar bala'i ce?"(>�-�>�#�)

Jummai ta kalli Abba da Ummah tace"mamuda bakace komai ba, Hadiza kiyi magana mana"

Ummah tace "nikam duk abinda Hajja tace ai ya zauna, Hajja ai itace komai na mesunan qawarta, nikam ai kawai haifarta nayi"


Abba yace"gaskiya hakane Kam, saboda haka iya jummai da anyi hakuri da maganar aikin Nan, tunda de yanzu gashi inusa yafuto Kuma naga alama da gaske yake, to kawai babu damuwa zan hadata aure dashi, Nima Hankali na zaifi kwanciya, koba hakaba Hajja?"

ya qarasa maganar yajuya yana Kallan Hajja

Hajja tace"Gaskiya hakane Kam, idan takwarar ta taji Natura ta wata uwa duniya Abuja ma nasan bazata yafeni ba, Nasan halin Aysha Yakubu sagagi, cewa zatayi inrasa wazan tura aiki Sai takwarar ta? Nasan halin abata tsaf zata aikata, danhaka jummai ayi hakuri da wannan batu, me sunan qawa kawai zamu hadata da inusa"

Jummai tace "to shikkenan Hajja, Amma Dan kunqi ne, nikam naso Aisha taje komuma wataran maje Abujan mu dandani Arziqi"

Haka tadinga mita harta fice daga gidan, Sai Alokacin Aisha tasaki wata irin ajiyar zuciya, saboda harga Allah batajin zata Iya yiwa uwar wani bauta, itama Tata uwar tana buqatar kulawar ta, haka kawai saita tsallake mahaifiyar ta da Hajja tatafi tana yiwa wata mata aiki? Matar ma uwar mutumin daba birgeta yake ba, mutumin da taqi jinin taji sunansa, mutumin da saboda shi tadena jin redionta kwata kwata, bazai iyu ba

(tofa>�z�)


******


Yau makara sukai a sahur, saura minti shida Akira sallah Sannan suka tashi, Ahankali Aisha ta bude idonta, taga babu Wanda yatashi sahur, Kuma wani lokacin bacci yana cikin dad'i za'a tasheta ace lokacin sahur yayi, Amma yau Kuma taga ta danyi baccin sosai, hannunta ta miqa tad'auki wayar Hajja, tana ganin lokaci tazaro idonta, durowa tayi daga gadon tace "Hajja....kunyi sahur ne nice Baku tasheni ba?"

Hajja tace "innalillahi wa inna ilaihirraji'un....ankira sallah ko?"

Aisha tace "A a, ankusa de, waidama babu Wanda yatashi kenan?"

Cikin sauri tafita taje tatashi Ummah da jabir, tasake tashin Abba, ai kowa a gurguje yatashi, Aisha yau babu batun brush, kawai bakinta ta kuskure tadauko musu kular dasuka zuba taliya aciki, da Ummah, da Hajja, da Aisha, da Jabir, gaba dayansu kowa hannu yasaka yafara ci, babu batun zubawa kowa, Abba yayi murmushi yaga yanda suka hade Kai kowa tura abincin yake, Ummah ta Kalle shi tace "kaidama ba sahur kake ba, duba mana saura minti nawa Akira sallah?"

Agogonsa ya kalla yace "saura minti biyu"

Cikin sauri suka qarasa cin abincin, ruwa kuwa kowa tashi yayi yake nema yanasha, kowa sauri yake inbakayi ban waje....

Suna gama shan ruwa kuwa aka kira sallah, Sai Alokacin Hajja tayi magana (=��)
"Oni Aishatu... Da yanzu yau munyi shige, wannan azumin na Bana Inkayi sahur ma Yaya aka qare bare Kuma bakayi ba"

Jabir ya kalleta yace "Hajja keda kikace sahur ba damunki yayi ba?"

"Kai da Allah Ina nufin Alokacin danake Aysha Sulaiman Bompai kenan, yanzu kuwa Hajja A'i nake"

Dariya Aisha tasaki tace "Hajja nifa jinake kun tasheni naqi tashi ne, shine kukai abunku kuka rabu Dani, ashe duka gidan yau makara mukayi"

Hajja tace "aini Gara hakan ma,nasan da yanzu kina Nan kina d'ora abincin a harshanki"

Cikin shagwa6a tace "kaii Hajja, aike nabiyo, kece kike cin abinci kamar bakya so"

Hajja tace "wa?.... Lalle yau na yarda bakisan wacece takwararki ba, ai Aysha Yakubu sagagi, idan tanacin abinci ke kyace yar sarki ce, Aysha inda ace me kudi ce ita bansan wanne irin mulki zatayi ba, Ada canma damuna boarding school dinmu ta Goron dutse idan aka zomin visiting mukaje muka kar6i abincin da aka kawomin, wato idan muka koma daki tafara cin abincin Nan saiki dauka yar wani gwamnan ce, saboda Aysha Yakubu sagagi akwai yanga, gashi batada 6oye 6oye, saide kaji haushin ta, Amma tana fadar gaskiya komin dacinta "

Jabir yasako musu baki cikin firar tasu yace"to Hajja ita qawar Taki ba'a zuwa mata visiting dinne ita? "

Tace"Ana zuwa mata mana, Yan gidansu suna zuwa, idan sukazo tare muke zuwa, kawai de Alokacin ne tafi yimin rakiya gaskiya, saboda kaga a wancen lokacin iyayena sunada kudi, ita Kuma nata iyayen basuda qarfi sosai, to saiya kasance Ana zuwamin visiting din sosai, da Azumi kullum Sai ankawo min abinci daga gida, Kuma idan natashi komawa makaranta Bayan motar Sai ancika min shi taf da Kaya, harnaje nadawo Bana iya cin wani abun, direban dayake kaini makaranta idan ya saukeni har dauke min wasu kayan yake yanamin wayo yana cewa ai wannan ma ba lalle kici ba, nikuma babu wayo, Sai ince eh, to haka mukai karatun mu babu abinda yake rabani da'ita, mutane dayawa suna tunanin ma gidanmu daya, saboda Bama fada, koda munyi fada to a ranar zamu shirya, ita babu rufi, idan na 6ata mata rai fadamin take, nikuma da masifa, inhauta da fada, anan

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment