Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tasan bazanyi mata qarya ba,nafada mata inason haihuwa idan nayi aure da bakinta tace zata fara azumin sitta shawwal tayi min addu'ah ko Allah zai ban haihuwa, yanzu Mena aikata haka? Inda nafada mata gaskiya tunda farko dazan iya futowa a ko'ina ne in kare ta amatsayina na Mahmud Wakili"

Jikin Ramadan ne yayi Sanyi,kafadarsa yadan bubbuga yace "kayi hakuri Shahaab...,Amma shawarar damuka baka nida mama itace mafita,inda bakayi hakan ba, zaka San halaiyar yarinyar ne kamar haka? Ni banga laifin taba dakake cewa baka sonta, wannan yarinyar babu inda bazaka shiga da'ita ba, asalima yarinya ce qarama Sai abinda ka dorata akai zatayi, Amma tunda baka sonta, kadena zuwa inda take, kanisanceta, idan Kai kasan zuciyar ka, ita bakasan Tata ba, zata Iya sonka, qarshe karabu da'ita, hakan bai kamata ba, karabu da yarinyar mutane kawai "

Cikin tsananin kishi Shahaab yace"Nina Rasa gane inda kanufa Ramadan, saika dinga nunamin kamar so kake narabu da yarinyar kaikuma kaje ka aure ta"

Dariya ce ta kama Ramadan, Amma saiya danne, yace "Aure kuwa da gudu"

Shahaab yayi masa wani irin kallo, cikin zuciyar sa yace zan dauki mataki, dole zan kawo qarshan komai, haka suka kwana babu wanda yasake magana, kowa da abunda yake saqawa acikin ransa, shikam Ramadan ransa fes yayi bacci, ko banza yasan ya tunzura Shahaab, dama da niyya yafadi hakan danya ga gudun ruwan abokin nasa.

******

Washe gari tunda safe, Aisha tatafi gida, tana zuwa Hajja ta tareta cikin murna, tsarabar Lemo da bread din data kawo musu suka rarraba har jummai saida aka kaiwa, cikin sauri ta shige dakin Hajja ta dauki wayarta tafara duddubawa ko Shahaab Yakirata, saide bataga komai ba, tunani tafara me zata siyo masa idan yazo tabashi Shima a matsayin tsarabar kano? Wani tunani tayi, cikin sauri Takoma Dakin Umman ta, asusunta dayake Qasan gado tafasa,dubu biyar biyar din daya bata sau biyu, dakuma dubu biyunta na albashin ta, tahada dubu goma Sha biyu, tasaka hijab dinta ta cewa Ummah da Hajja "natafi gidansu Walida yanzu zan dawo"

Hajja tace "dole kije Kam kwana biyu Baku hadu ba, itama rannan tazo nace mata ai kin tafi kano"

Aisha batace komai ba tafice, tana fita kofar gida bata nufi gidansu Walida ba Kai tsaye wata hanya ta d'auka, saida taci tafiya sosai, sannan taje wani Babban shago, tabawa me shagon kudin tace "gashi abani agogo da links"

Cikin sauri ya d'ago ya kalleta yace "to wanne Kala kikeso?"

Tace "Nima bansaniba ba, kawai kabani me kyau"

Murmushi yayi yace "to Wanda zai saka fari ne ko baqi?"

Tace "fari ne"

Cikin farinciki yabata agogon da links din tuwan toka yace "to wannan zaifi kyau"

Kar6a tayi sannan tafice, acikin hijabinta ta 6oye su, sannan Takoma gida tasaka su acikin kayanta


******

Da yamma yaga Shahaab sai shiri yake, manyan Kaya ne ajikinsa na wani yadi Mai mutuqar kyau, cikin mamaki ya sake Kallan sa yace "fita zamuyi ne? Naga Kanata shiri"

Cikin sauri yajuyo ya kalli Ramadan din sannan yace "fita zanyi de"

Daria ce ta kama Ramadan, yayi murmushi yace "to naji, Ina zakaje?"

Kai tsaye yace "jigawa"

"Amma Shahaab kasan fa jirgin safiya zamubi mutafi Abuja, yanzu karfe hudu, idan katafi yaushe zakaje harka dawo?"

Kallan sa yayi yace "akwai tafiyar dazanyi zuwa Australia goben da yamma idan mun koma Abuja Dasafe, tafiyar zata daukeni wasu Yan kwanaki masu yawa, dole zanje inyi sallama da Maama, ko zan tafi ne batare data Sani ba?"

Ramadan yayi murmushi yace "a a, Amma Dan Allah katafi Dani danna sake ganin ta" (=��)

Cikin daure fuska yace "zanyi sallama da yarinya kana cewa zakaje, idan kaje a'ina zaka zauna? Ka zauna anan kawai, zan saka face mask inje dakaina indawo"

Yana gama fadar haka yafice daga d'akin, Ramadan yasaki murmushi cikin ransa yace "Allah yakai damo ga harawa...."

Idar da sallar magrib dinta kenan, tafada duniyar tunaninsa, sotake ta kirashi, Amma Kuma tasan idan ta ta6awa Hajja katin waya to zata gane, Kuma ta dinga yimata mita kenan,kamar almara taji wayar tana qara,tana dubawa taga number shice, cikin sauri ta d'auka sannan tashige Dakin Hajja, cikin wata irin murya wadda zaka tabbatar yayi kewarta yace "Maaaamah"

Wani irin yarrrr taji ajikinta, ahankali tace "na'am"

Kai tsaye yace "Ina kofar gida"

Cikin murna tace "da gaske?"

Yace "sosai, kifuto yanzu"

Tace "to" sannan takashe wayar

Daki ta wuce tadauko abunda ta siyo masa dazu, sannan tafuto tana Sanye da hijabi dogo, Ummah ta kalla tace "Ummah zanje wajan Walida"

Kafin Ummah tayi magana Hajja tace "keni narasa gane wannan zarya da kike a gidansu Walida, kusan kullum Sai kinje inji de lafiya?"

Dan qaramin bakinta ta turo gaba tace "littafi zan kar6o fa"

Ummah tace "kuma kullum bakida aiki Sai zuwa da daddare? Kishiga hankalin kifa"

Hajja tace "Allah ya kyauta, toki tabbatar kina kar6owa Zaki dawo"

Cikin murna tace "to Hajja"
Sannan tafice daga gidan cikin murna, wannan motar bada ita yake zuwaba, Amma kasancewar tasan anan yake ajiye motarsa, saita nufi wajan, tana zuwa bata jira yafuto yabude mata ba, tazagaya ta bude tashiga, sannan tarufe, Kallan sa tayi cikin farinciki tace "Dama wallahi sonake naganka, na Dade inason muyi waya inbaka labari"

Cikin mamakin farincikinta yace "meyasa baki kirani ba to?"

Cikin shagwa6a tace "to ai idan na kiraka Hajja zata gane, Kuma zata San nata6a mata katin waya"

Cikin ransa yace Kati Kuma? A fili saiyace "Dama ba wayarki bace?"

Girgiza kanta tayi tace "wayar Hajja ce"

"wace Hajja?" ya tambayeta

Tace "kaka tace, Amma Kuma wayar a hannu na take wuni, inayin game da'ita, yanzu Kuma Dana dawo Naga duk ta gogesu daga wayarta" ta qarasa maganar idonta na cikowa da qwalla

Cikin sigar rad'a yace mata "menene na kukan Kuma? Kincika shagwa6a Maama, Kidena yin game, kici gaba da karatu yafi"

Murmushi tayi tace "kasan me? Inaso inyi karatu inzama likita, indinga aiki a Asbiti, inkai babana Saudia, nikuma saina tafi tareda Ummah na da Hajja"

Wani irin daci yaji acikin ransa, saboda idan akwai abinda yatsana to shine matarsa tayi aiki, baya fatan ma ace yarage ta tawani Fannin bare har tayi tunanin yin aiki domin samun kudi, matsayin matarsa yawuce tayi aiki abata kudi, saide ta dauki kudin tabawa ma'aikata, wata zuciyar tace dashi to ita matarka ce? Acan Qasan maqoshinsa yace "yes"

saboda kada ta gane yanayin dayake ciki na rashin son karatu,Sai yayi Murmushi yace "nikuma fa? Bazaki kaini ba?"

Dariya tayi, tace"kaima saimu tafi dakai to,kabani wayarka nayi game kaji"

Cikin ransa yace"kodan yarinya ce? Yanzu inashi Ina wani game a wayarsa? Kallan ta yayi a fili yace "banda game"

Cikin sauri tace "to cartoon"
Murmushi yayi yace "Shima babu"

Bakinta ta turo gaba tace "to photuna"

Daukan wayar yayi batareda tunanin komai ba yabata, saboda yasan shide babu pictures dinsa aciki, haka babu wata shaida dazata Gani ta tabbatar mata cewa shine Mahmud Wakili.

Kallan pictures takeyi dayawa na takardu ne Wanda batasan kona menene ba, wajan videos tashiga, anan taci Karo da video na wata mata da'akayi mata operation, cikin sauri tabashi wayar tareda fashewa da Kuka, cikin kuka tace "Dama haka ake ciro yaro? Bazan iya aikin asbitin Nan ba, nafasa, saide indinga saida Kati"

Dariya ce ta kamashi, cikin dariyar yace "da kudin katin Zaki kaimu Saudia kenan?"

Batace Masa komai ba Sai kuka datake, wayar yakashe gaba daya, sannan ya gyara zamansa yajuyo yana fuskan tarta, yarasa Yaya zaiyi mata, tacika shagwa6a dayawa, yanzu tayaya zai fara lallashin ta?
Ahankali yad'ora tafukan hannunsa a fuskarta yariqe fuskar Tata dakyau sannan yace "kiyi shiru, bafa haka akeba, kawai hadawa akayi, yi hakuri kinji?"

Kanta ta daga masa, hawaye ya silalo daga idonta, ahankali yasaka hannunsa guda daya ya share mata Hawayen, duk yanda yaso daqin ta6a dogon hancin ta, kasawa yayi, hannunsa yad'ora akan Karan hancinta yafara shafawa ahankali, rufe idonta tayi, hakan saiya qara yiwa fuskar Tata kyau, gashin idonta daya hadu da dan'uwansa yajiqe saiya kwanta yayi luf,cikin wata irin murya Mai Kama da rad'a yace "ogana zai turani qasar waje maama, Dan Allah karki kula kowa kafin nadawo kinji..."

Cikin sauri ta bude idonta, sannan ta janye hannunsa daga fuskarta tace "yaushe zaka dawo?"

Yace "zan'iya yin wata daya, mezaki Bani Wanda zan dinga tunawa dake?"

Cikin sauri tad'auko agogo da links din data siyo masa, ta ajiye akan cinyarsa tace
"gashi"

Mamaki yakama Shahaab, ya kalli abinda ta ajiye masa akan cinya yace"na menene wannan?"

Ahankali tace "siyo Maka nayi, kaima kasaka a hannun ka, tsarabar kano ce, kasan naje kano, tona siyowa su Hajja bread da Lemo, shine kaima nasiyo ma"

Mamaki ne yahana Shahaab magana, ya zuba mata ido yana kallon ta, yanaso ya tambayeta wanne yaro ne ya gansu akano Amma yarasa ta wacce hanya zai tambayeta? Sake Kallan agogon yayi, sannan yasaka hannu yacire agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya ajiye shi agefe, links dinma ya ciresu, sannan ya maida kallon sa gareta yace "to dauki kisaka min"

Kallan sa tayi tace "ai ban'iya sakawa ba"

Ahankali cikin qasa da murya yace "dauki saina gwada miki"

Babu musu ta dora hannunta acinyarsa tad'auki agogon, sannan ta dora tafin hannun ta akan nasa, wanne irin laushi taji hannun nasa nayi, agogon ta dora akan hannunsa Wanda gashi Yacika shi sosai, shagala yayi da kallon ta, dogon hancinta yake Gani dakuma yanda take qoqarin daura masa agogon, cikin shaqaqqiyar murya yace "wannan dayan zaki saka acikin wannan qofar, shikkenan"

Kallan sa tayi jin yanayin muryarsa tad'an sauya, sannan ta Girgiza masa Kai, tayi abinda yace, tana dauke hannunta yad'ora bakinsa akan agogon yayin kissing dinsa, sannan ya kalleta yace "nagode, saura link's din"

Babu musu Shima ta d'auka tasaka masa da temakon sa, suma saida yayi kissing dinsu, Aisha de tana ganin ikon Allah, sannan taga ya juyo yace mata "Ina kika samu kudi kika siyomin wadannan abubuwan?"

Cikin rashin damuwa tace "kudin daka Bani ne, nahada da Wanda nake Tarawa saboda qanina yatafi makaranta, shine nasiyo ma dasu"

Jiyayi wani irin shock ya kamashi, kudin da take Tarawa saboda qaninta yatafi makaranta? Hakan yana nufin shita sadaukarwa da kudin kenan saboda tayi masa kyauta yaji dadi,wacce irin yarda yarinyar Nan tabashi? Dama ashe akwai yarinyar dazai samu yanzu ta dinga bashi irin wannan kulawar? Ashe akwai yarinyar datake sonsa da gaskiya? Hakan yana nufin mama da Ramadan sunyi gaskiya kenan, yakamata zuwa yanzu ace yafada mata abinda yake ransa, ga Ramadan ma dayake kusa yana cewa tsaf zai iya aurenta, cikin sanyin jiki yamatso dab da ita, ahankali yad'ora Kansa akan cinyoyinta

Zaro ido tayi cikeda faduwar gaba, menene haka Shahaab yake mata? Hannu tasa tafara janye masa Kansa, Amma sai yaqi bata damar hakan,saina hips dinta daya riqe yajin kamar su dauwama Ahaka, dagewa tayi ta janye Kansa, cikin sauri yakama hannayenta yariqe da hannunsa biyu, Kallan qwayar idonta yayi sannan yace "maama kinason aure yanzu?"

Mamakin tambayar tasa tayi, saida tad'an juya idonta sannan tace "inaso Amma banason kishiya"

Gabansa ne yafadi, cikin sauri yace "meyasa?"

"saboda Hajja ita kadai ce, Ummah nama ita kadai ce, Nima nikadai zan zauna da mijina, banason hada komai nawa da wata, yaje can Dakin, yazo Nan dakin, nifa ko tunawa nayi anayin kishiya raina 6aci yake, Ina Gani a cewa wata mijina shine mijinta, idan yayi wani abu a Dakin amarya, yaje Dakin uwar gida yafada mata"

Cikin sauri Shahaab yace "koda mijin baida surutu?"

Itama cikin sauri tace "koda kurma ne, idan zan kirashi to inde yana gaban matarsa bazai dauka ba, nifa banason damuwa ko kadan musanman akan kishiya,namiji yaje wajan kishiya ta, Nima yazo wajena"(=�H�)

"yazo wajan ki yamiki mei?"(=�3�)
Yafadi maganar yana zaro Idonsa

Sai a lokacin tatuna dawa take magana, cikin wata irin masifaffiyar kunya tayi sauri ta 6oye fuskarta da tafukan hannunta

Murmushi yayi, sosai maganar Tata tabashi dariya, yar qanqanuwa da'ita har tasan kishi, idanu yazuba mata yana sake qare mata kallo, ahankali yamiqa hannayensa yakama fuskarta, Kallan sa tayi taga yanayin Idonsa yana sauya wa, ahankali tadora hannunta akan nasa hannayen daya riqe fuskar ta tana so ta janye masa hannayensa,Kansa ya Girgiza mata, yayinda yake sake matso da fuskar sa dab da Tata, gabansa ne yake faduwa, zuciyarsa na sake zigashi akan yafada mata abinda yake ransa,dogon hancinsa yad'ora akan Nata hancin, yahade goshinsu waje daya, lips dinsa yana gogor Nata, ahankali cikin muryar rad'a yace "maamaaaah....,maama Ina sonki"

Yanda yafadi maganar cikin wata irin murya, dakuma yanda take jin lips dinsa yana ta6a Nata, hakan ne yasa tashiga wani irin yanayi Wanda bata ta6a tsintar kanta aciki ba, cikin salon shagwa6a da narkewa yace "kema kina sona?"

Gabanta ne yafadi, numfashinta yana fita da sauri da sauri, idan tace bata sonsa tabbas tayi qarya, ahankali ta bude Dan qaramin bakinta tace "Nima Ina sonk...."kasa jurewa yayi, Bai Bari ta qarasa ba yahade bakinsu waje daya.

Wani irin qarfi taji yazo mata, Nan take tafara kokarin hanashi abinda yake, Amma ruqon Dayayi mata yasa takasa qwacewa, tanajin yanda yake tsotsar bakinta ahankali kamar yasamu sweet.

Jikinta ne yafara rawa, bata sababa, bata ta6a aikata hakan ba, wannan ne dalilin dayasa take jin komai Sabo agareta, bata iya yimasa komai ba, tana jinsa yana shan bakinta son ransa, saida yagama kissing din Dan Kansa, sannan ya zare bakinsa ahankali, har yanzu hannunsa yana riqeda fuskarta, cikin qasa qasa da murya yace "ki kula min da kanki maama,karki kula kowanne saurayi Dan Allah, Ina dawowa daga qasar waje zanzo inyi magana da Abban ki"

Daga masa Kai tayi cikin mutuwar jiki, batareda tace komai ba ta bude motar tafuto sannan tarufe, akan idon malam Manu maqocinsu, Wanda tun shigar ta cikin motar ya ganta, haka Kuma yaga futowar ta (=�F�<���
@&�=�3�)

Kai tsaye gida ta shige tana tafiya hannunta yana kan lips dinta Wanda yaji tsotsa, tunani take Dama wannan ne kiss din?.
Kai tsaye d'akin Hajja ta wuce, tanajin Hajja tana cewa "mesunan qawa fira tayi dadi yau kin dade awajan Walida"

Bata amsa mataba ta qarasa shigewa daki tareda fadawa kan gado, wani irin yanayi takeji ajikinta Wanda tarasa gane Kansa

A 6angaren Shahaab kuwa daqyar ya'iya komawa kano, Alokacin shadaya da kwata na dare, hannunsa akan mararsa yashiga gidan da akayi musu masauqi,yadade acikin motar yana kar6ar caji kafin yabude motar yafuto, duk yanda yake jin azaba daga ciki, Bai Bari Ramadan yagane halin dayake ciki ba (=��)

Kai tsaye toilet yashige domin tsaftace jikinsa.


******

Yau kwana biyu kenan da tafiyar Shahaab Australia, tana lura da Abban ta tun washe Garin ranar da Shahaab yazo wajan ta take ganin yanayin sa ya sauya, komai yana yinsa ne a sanyaye, yau ma zaune suke a tsakar gida gaba dayansu, Hajja tana dura kunun Aya, jabir yana zaune kusa da Ummah, Abba kuwa yana Gefe ya zubawa Aisha ido itada qawarta Walida yana kallon su, tun shekaran jiya da malam Manu ya shaida masa cewa yaga Aisha tashiga motar wani, sun dauki lokaci acikin motar, sannan tafuto, shikkenan yashiga damuwa, yarasa waye yake son rushe wa yarsa tarbiyar daya bata tsawon shekaru, a yanda yakeji yanzu, zai iya yi mata dukan lahani idan ya tambayeta motar ubanwa tashiga taqi fada masa gaskiya

Walida ta kalli Aisha tace "tabdi, wallahi na manta ban taho da biro naba, Kuma sonake yau kisake koyamin lesson plan dinnan Dan inyi sauri in qarasa, jibi muke son komawa makaranta hutu yaqare Kuma"

Hajja tace "ai kun samu ma kundan huta, Amma da ace lokacin azumi Kuna zuwa Aida jikinku Yagaya muku"

Aisha tasaka hannunta cikin jakar makarantar ta tana cewa "Bari inbaki nawa Biron, saikiyi dashi Amma Sabo ne, Baiyi laushi sosai ba"

Walida tace "Bani"

Zuciya daya Aisha tadauko Biron da Shahaab yabata, ta miqawa Walida Biro, Walida tana ganin wannan biro tazaro idonta waje, cikin tsananin razana tace "la'ila....waye yabaki wannan Biron? Wallahi irinna babanmu ne sak, Shima gwamna ne yaraba musu shi Kuma yace mana biro ne Mai mutuqar kyau da tsada, dubu Dari biyar ake saida shi" (=�F�<���
@&�)


Hajja ce tazaro idonta waje (=�3�)
Abba kuwa Aisha ya zubawa ido yana jira yaji daga gidan ubanwa tasamu Biron, Ummah da jabir ma idonsu yana kan Aisha, yayinda kan Aisha yasara, tarasa asama take ko'a qasa, gabanta yahau luguden faduwa.






(tofa Al'amari ya lalace yau =��>�y�)





Littafin Shahaab na kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta abinki Hankali kwance, idan kika karanta batareda kin biyaba, keda mahaliccinki,.

08033300034
Amnah El Yaqoub
'<���


Page 21

Kafin Aisha tayi magana Hajja tace"kekuwa Walida da masifar qarya kike, yanzu inbanda qarya, wanne irin biro ne za'a ce dubu Dari biyar saikace kudin qaramin gida?"

Aisha da idonta ya furfuto ta juya ta kalli Hajja, jitake kamar babu nauyi ajikinta, Sai takeji kamar tana tashi sama ne saboda tsabar rashin nauyi, har zuwa yanzu idon Abba yana kanta, duk wani motsi datayi, idonsa yana kanta

Walida kuwa kallon Hajja tayi tace" Hajja.... Wallahi Allah da gaske nake, nasan Abbana bazai mana qarya ba, lokacin ma agaban mu yabawa Alhaji Ali yace aje a saida Biron zai sayi fili da kudin"

Hajja ta kalli Aisha datayi tsumu-tsumi tana zare ido tace"mesunan qawa a'ina kika siyo Biron?"

Cikin faduwar gaba tace "Hajja ni Bani akayi, Kuma Wanda yabani bashida kudin da Walida take fada bare harya'iya siyoshi"

Abba daya zubawa Walida ido yana kallon ta yace"tashi kije gida Walida, qawar Taki zatazo ta sameki"

Babu musu Walida tatashi tana cewa Aisha "to wallahi ki binciki Wanda yabaki karkije na sata ne, idan kinzo saimu qarasa rubutun"
Daga Nan tasakai tafice daga gidan

Abba ya kalli Aisha fuska babu Fara'ah yace "bani Biron"

Babu musu ta dauki biro tabashi, Kai tsaye yatafi gidan Alhaji Ali domin jin gaskiyar magana,ko kadan bai yarda da maganar da Aisha tafada akan Biron ba, Ummah datake tsoron yiwa Aisha fada Hajja Tahau kanta da masifa tace "Allah yarufa asiri"

Aikuwa cikin sauri Hajja tace "Amin, aiya dade da rufawa"

Cikin sauri Aisha tatashi ta shige dakin Hajja, gaba daya fuskarta ta sauya tunani take da kokonto akan maganar da Walida tafada mata, Ina Shahaab zai samu kudi har nera dubu Dari biyar?
Lokaci daya ranar da sukaje mall itada fati yafado mata Arai, da fad'an da masu mall din suke mata, Kuma lokaci daya suka dawo suna bata hakuri saboda wani body guard datagani da baqin glass yazo yayi magana dasu, ta tuna lokacin dasuke cewa Babban customer dinsu ne yazo Kuma bayason hayaniya.

Fadawa tayi kan gado tana Girgiza kanta, tasake tuna lokacin datake cikin adedeta ance mata Mahmud Wakili yazo shi aka sauka acikin gidajen data Gani,gabanta ne yake faduwa, meyake shirin faruwa ne?To Amma Kuma ai yace mata shi Yaron Mahmud Wakili ne bare tayi tunanin ko qarya yake mata, tasan cewa Shahaab bazai ta6a yimata qarya ba, Shahaab bazai fada mata abinda bashine ba, yanada Hankali, Kuma yanada nutsuwa, sannan babba ne yanada shekaru, bazai yi mata qarya ba, lokaci daya kanta ya d'aure, tarasa waye zai bata amsa, wayar Hajja ta d'auka cikin sauri har hannayenta na karkarwa tafara Kiran layinsa, saide Kuma wayar tasa akashe(>�&�<���
@&�)

Tana daga d'akin tajiyo Abba ya dawo, kujera yar tsugunno yaja ya zauna agaban Hajja dasu Ummah, sannan yace "naje na kaiwa Alhaji Ali Biron, yace zai Kai a siyar dashi,zan jira shi inji Yaya ake ciki"

Hajja tace "nifa mamuda itama Walidan data fadi maganar kallon mahaukaciya nake mata, tsakani da Allah tayaya me sunan qawa zata samo wani biro har dubu Dari biyar?to kaima tun kafin infara yima kallon mahaukaci kawai kayi shiru"

Abba yace "Hajja kenan,bakisan abinda yarinyar Nan take qullawa bane"

Jin abinda Abba yace yasa gaban Aisha faduwa, kode Abba yasan tana kula Shahaab?

Kafin Hajja tayi magana suka jiyo sallama daga kofar gida, jabir ne yatashi yafita, Sai gashi ya dawo yace "Abba Ana sallama dakai"

Kallan jabir yayi yace "nikuma? Suwaye?"

Jabir yace "wasu baqi ne, Amma Naga tare suke da Bulama"

Abba yace "baqi tareda Bulaman Gari? to Bari naje,"

Yafadi hakan tareda nufar kofar gida.
Yana zuwa yaga baqi su hudu, tareda bulaman Garin,hannu ya basu suka gaisa, daya daga cikin baqin ya kalleshi yace "kaine mamuda?"

Abba yace "eh nine,meyake faruwa?"

Yace "karka damu babu komai, munzo ne daga National Hajj commission,ma'aikatar aikin Hajji, muna farincikin sanar dakai sunanka yafuto acikin jerin Wanda zasuje Umara cikin wannan satin, sannan danka yasamu gurbin karatu a qasar Australia, zamu wuce daku dutse domin yimuku international passport"

Abba yayi shiruu kamar baiji abinda suka fada daidai ba, cikin tsananin mamaki yace"ranka yadade Saudia de Dana Sani?Kai inaga de kuskuren adreshi kuka samu"

Daya daga cikinsu yace"Muma Umarni ne muka Kar6a daga sama,kashiga kasanar agida muje mucika umarnin da'aka bamu"

Cikin mutuwar jiki Abba yajuya cikin gida tunani fal ransa, dama mutum yana samun karatu ne batareda yanema ba?jabir din dasuke fafutuka yasamu ko legal Ringim ne yatafi yayi diploma shine yanzu yasamu gurbin karatu a qasar waje? Tayaya? Yanzu a wannan zamanin har akwai mutumin dazai biyama Saudia ne batare da yasankaba? Kuma sunce umarni aka basu daga sama, hakan na nufin koma wanene yasaka su to wani Babban ne a qasar, Kuma yayi bincike sosai akansa tunda gashi har yasan yanada d'a namiji

Yana qarasawa cikin gidan yafadawa Ummah da Hajja abinda yake faruwa, Hajja tace "to mamuda, dayake Saudia de Kiran Allah ne bazan hanaka zuwa ba, Amma abun da mamaki ace an dauki nauyin karatun jabir, kaikuma anbi Yama Umara, to waye ne wannan?"

Ummah tace "Hajja koma wanene ba qaramin masoyinmu bane, wataqila lokacin da zamuji dadi ne yazo, Allah yasaka masa da alkhairi, yasa ladan abunda yayi yadinga binsa har qabarinsa"

Abba ya jijjiga Kai yace "hakane, Amin ya Allah"

Cikin sauri Aisha tafuto daga daki tace "Abba Allah yasanya alkhairi"

Baice da'ita uffan ba, Sai kallon jabir da yayi yace "Kai taso muje"

Cikin sauri jabir yatashi suka fita, Kai tsaye dutse sukaje kamar yanda mutanan suka fada, anyi musu passport duka su biyun,Wanda sukaje gida suka Dauko su sune suka kar6i passport din, sannan suka dubi Abba, daya daga cikinsu yace "Zaku iya komawa gida, yanzu zamu Kai passport din Abuja, za'a yi muku visa"

Abba de da yaga abun nasu da gaske ne, saiya tsugunna yafara yimusu godia, cikin sauri suka tarbeshi yatashi tsaye, sannan sukace babu komai, Abba har hawaye yake yana qara yimusu godia, daqyar suka samu yayi shiru, sannan sukai sallama dasu

Basu koma gida ba Sai dare, agida ma magana daya aketa maimaita wa, mata Sai sallama suke yi a gidan anayiwa Hajja Allah yasanya alkhairi mamuda zai tafi Umara, Abba yarasa Ina Yan gari suka samu labari, Amma daya tuna da Bulama saiya Dena tunani akan hakan.


(Shahaab littafin kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta abinki, duk wadda ta karanta batare data biyani haqqina ba nabarta itada mahaliccinta,
0164549488
Amina muhammad
GTbank)

******

Cikin dare hadari yahadu sosai, Nan da Nan aka tsinke da ruwan sama, acikin wannan ruwa Aisha tatashi tafuto tayi alwala, kafin Takoma daki duk ta jiqe, Dakin Takoma ta kunna wayar Hajja ta shimfida sallaya, sannan ta kashe hasken wayar tacire kayan jikinta, ta dauki wani kayan tafara sakawa, cikin rashin Sani tad'an bigi breast dinta,cikin sauri ta runtse idonta saboda zafin dataji, tarasa meyasa wani lokacin suke mata ciwo, sannan Kuma kullum cikin qaruwa suke, hijabi tasaka sannan tatada sallah, Bayan ta idar haka ta dinga addu'ah Allah ya dawo da Shahaab lafiya domin ya wanketa akan wannan biro, yazo yafada musu Bahaka bane, sannan tayi wa Allah godia akan abun farincikin daya samu Abban ta da jabir, tayi musu addu'oi sosai, sannan ta kwanta awajan tana istigfari, batasan lokacin da bacci ya dauketa ba, saiji tayi Hajja tana tashin ta sallar asuba.

Tunda suka tashi da safe ta gaida Abban ta taga ya amsa mata daqyar, jikinta yayi sanyi, haka Takoma Dakin Hajja ta kwanta batareda kowa ya lura da yanayin datake ciki ba, da yamma Alhaji Ali yazo gidan yayi sallama da Abba, Abba na fita suka gaisa da Alhaji Ali, anan Alhaji Alin yaqara tayashi murna saboda samun labarin Dayayi Abba yasamu kujerar umara, sannan yaqara da cewa "Mamuda ga wannan kudin, jiya nakira wayar ka akashe, dama inaso in fadama ne Wanda yake siyan Biron baya Nan, Sai yaransa nasamu, sukuma sunce bazasu siyeshi haka ba saboda babu kwalin Biron, danhaka zasu iya siya dubu Dari hudu da hamsin, ga kudin Naka"

Jikin Abba ne yafara rawa ganin wannan uban kudi, ,qafafunsa suka fara karkarwa yana neman faduwa, ahankali yasaka hannu ya kar6i kudin sannan yace "nagode Alhaji Ali, zanzo gidanka anjima"

Alhaji Ali yayi godia yajuya yatafi, Abba kuwa duhu duhu yake Gani daqyar yakai Kansa gida,yana zuwa ya zauna akan tabarmar da Hajja da Ummah dakuma jabir suke zaune, ya ajiye kudi agaban Hajja, tsorata sukai da yawan kudin, cikin 6arin jiki Hajja tace" mamuda Ina kasamu

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment