Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanta tace"haba Aisha, meyasa wani lokacin bakida wayo ne? Yanzun Nan ince karki Bawa kowa Amma Zaki ciro kice kinbani?"

Murmushi tayi tace"mama aike kakata ce, nafada miki Ina ganinki kamar kakata Hajja, danna baki ai babu komai, Nima ai bansan zan samu ba saida kika aikeni"

Mama tace"toki riqe, Nima Ina dasu Aisha, Allah yamiki Albarka yahuci gajiya, tashi kije kiyi sallah kici abinci kihuta"

Cikin ladabi ta amsa mata, sannan tad'auki kayanta tayi dakinta, mama tabi Bayan Aisha da kallo, Aisha yarinya ce qarama, Kuma tana zaune dasu tsakani da Allah, sannan da alama yarinyar batada 6oye 6oye, uwa uba abun duniya bai rufe mata ido ba, to Amma abun tambayar menene yasa Mahmud yayi mata wannan siyaiyar? Gashi yarinyar tana cewa yayi mata fada akan saka mayafi, gaban mama yayanke yafadi, hakan na nufin kishin yarinyar yake kenan? Tatuna lokacin daya bude sabon company yayi maganganu dayawa harda zai iya sadaukar da rayuwar sa saboda Aisha, to wacce Aisha yabawa Company kenan?tasake tunawa da lokacin da Aisha take bata labarin saurayinta, taga kishi qarara a'idon Shahaab.

Idan Aishan daya Bawa company daban, to meyasa zai Bawa Wannan Aishan kulawa haka? Abunda baka siyawa matarka ba ka siyawa yarinya?

Zataso ace Shahaab ya auri Aisha,Kodan hankalin yarinyar, gashi tana bata kulawa yanda ya kamata, tun farko irin Aisha taso Shahaab ya aura, to Amma abunda take tsoro shine karfa ace Shahaab yana kula wata yarinyar daban, Nan Kuma yazo yana yaudarar yarinya, yarinya ce qarama bai kamata ace wata alaqa marar kyau tashiga tsakanin ta da Shahaab Bayan alaqa ta gaskiya da Kuma Amana ba, wadannan tunanin Nata babu me amsa mata su Sai Shahaab, Dan haka ta kawar da komai Gefe, tana jiran lokacin dazai dawo gida.=�3�

Wayarta ce tayi ringing, cikin sauri ta duba taga number ce, cikin mamaki ta d'auka tareda sallama, saide qara kawai takeji alamun babu network, tsaki tasaki takashe wayar, daga dayan bangaren kuwa Hajja tasake kira Akaro na biyu, mama ta d'auka tareda sallama, Nan ma qaran taji, Dan dole takashe wayar ta zubawa TV ido, Amma Kuma tarasa dalilin dayasa gabanta yake faduwa tun shigowar Kiran na farko....

Acan gida jigawa Kuwa.
Hajja tasaki tsaki tace"oho, qila wani qaton arnen ne yadameni da kira, dazu nabar wayar naje gidan Jummai Dana dawo Kuma na riski kira har kusan hudu, inajin arne ne ya kirani dan Naga number special ce"

Ummah dake Gefe Tace"A a Hajja kikira de kiji"

Hajja tace"Aina kira, banaji, rabu dashi kawai"

Ummah bata sake magana ba, Hajja ta zauna a kujera tayi tagumi tana kallon Ummah, sannan tayi ajiyar zuciya tace"nikam Hadiza keko 'Dan tunanin 'yar Nan Taki ma bakya yi?"

Ummah tayi murmushin qarfin Hali, Dan zuwa wannan lokacin ita kanta tana so taga yar Tata, Amma Yaya zatayi?

Hajja tace"kyayi murmushi Kam,tunda har dake aka d'aure gindi aka tura yarinyar uwa duniya, nide nagama yanke shawara, nagama hada kudi na jibi zan hau mota inje abujan dakaina a nuna min gidan me sunan mamuda inje in taho da jikata"

Murmushi Ummah tayi, domin kuwa ita kanta tayi na'am da shawarar Hajjan, ajiyar zuciya tasaki tace"to Hajja Allah yakaimu jibin"


Washe gari Aisha tatashi sassafe, ta gyara dakinta tayi wanka, daya daga cikin rigunan da mama ta siya mata tad'auki wata tasaka, tana gyara fuskarta agaban mirror aka turo qofar d'akin aka shigo, wata me kula da ayyukan kitchen ce tashigo jikinta Sai rawa yake tace"Aisha kizo yanzu yanzu inji Hajiya Mama"

Mamaki yakama Aisha, lafiya mama harta tashi yanzu Bayan lokacin futowar ta baima qarasa ba?
Ajiyar powder hannunta tayi, sannan tafuto daga d'akin, saide batasan dalili ba haka Nan take jin gabanta yana faduwa, tun kafin ta qarasa wajan mama, ta hango munirat tsugunne agaban mama tana ruskar kuka, ga wayarta ayashe aqasa, mama kuwa rigar bacci ne ajikinta me kauri da yar qaramar hula tana tsaye wayarta na hannunta idan ranta yayi dubu to duk sun 6aci, qarasa wa tayi wajan ta tsugunna sannan tace"gani mama"

Munirat ta zuba mata wani irin kallon banza sannan tace"munafuka, yar'iska, wadda tagama watsewa take neman lalata min mijina, wallahi tallahi hukuma ce zata rabani dake, Shima Kuma yazo saide ya za6a ni koke, kokuma yasakeni...."

Gaban Aisha yafadi, ta kalli munirat cikin ranta tace tasan Ina soyaiya da mijinta kenan,cikin 6acin rai tace"karki sake cemin zan lalata miki Miji, shi banyi masa wannan furucin ba Sai kece Zaki min?"

Mama da ranta yagama 6aci tace"Aisha acikin furucin ki kinaso kicemin idan ke baki lalata Shahaab ba, shi yana lalata ki kenan, ashe abinda munirat ta fadamin gaskiya ne? Yanzu wannan aikin kuke aikata wa keda Mahmud Amma kikayi shiru baki sanar Dani ba Aisha? Wallahi kin Bani mamaki"

Cikin sauri ta d'ago ta kalli abinda mama take nuna mata,vedio ne nasu itada Shahaab tsirara haihuwar uwarsu suna aikata sa6on Allah, ko kadan Hankalinsu ma baya tare dasu, gabanta ne yayi wata irin faduwa, kanta yasara, duhu duhu yanemi rufe mata ido, numfashinta yafara dauke wa Amma haka tayi qarfin halin janyo shi, lokaci daya ta Fashe da Kuka tace"mama...wallahi.... Tallahi bansan wannan vedion ba, ban aikata ba, bantaba aikata hakan da kowanne namiji ba, mama ki yarda Dani, wallahi Bani bace"

Tafadi hakan tana sake rushewa da Kuka,munirat tace"idan bake bace, waye zaiyi miki qarya? Mijina baya hulda da kowacce yarinya Amma kina zuwa gidan Nan kika maida shi yazama mazinaci"

Kuka ne ya taru yayiwa Aisha yawa, bata iya Bawa munirat amsa ba Sai kuka datake tana Girgiza kanta, mama tace"Aisha kifadamin gaskiya, yaushe irin wannan alaqar tashiga tsakanin ki da Mahmud?"

Cikin kuka ta kalli mama da jajayen idonta, sannan ta Girgiza mata Kai, kwata kwata takasa magana, daqyar ta'iya cewa"bani bace mama"

Mama tasake Kallan idonta tace"to waye ce?"

Wani irin kuka ne yazo mata, tsananin nadamar sakin jikinta ga mama yarufe ta, tayi tunanin idan akwai wacce zata fara shedar ta acikin gidan to Bayan mama ne, hakan ne yasa ta Girgiza kanta, cikin kuka tatashi tayi dakinta da gudu, tana zuwa daki tafada kan gado tana kuka mecin rai, Sai yau tayi takaicin rashin waya a hannunta, data kira shi yazo ya wanke ta a'idon mama, babu Wanda zaibi bayanta awannan lokacin sai shi, wani hawaye ne me zafi yazubo daga idanuwanta, tasaka hannu ta share, Zaman me zatayi Kuma? Wacce take zaune saboda ita bata yarda da'ita ba, asali ma tuhumar ta take tana lalata da danta, wannan tashin hankalin ya'isa, bata ta6a kokarin yin abinda bai kamata ba da Shahaab asali ma shine yake Koya mata wasu abubuwan Wanda bata ta6a aikata hakan akan kowanne namiji ba,da daddare yabiyo ta daki, safe, rana, yadinga Binta da wannan shegen kallon nasa, duk da haka ita ake tuhuma bashi ba, Zaman me zata zauna tayi? Me zaisa taci gaba da zama dasu? Gara tatafi gida Dama tayi kewar Hajja, idan tanada amfani ma, Bayan tatafi zasu Gani.

Tana gama wannan tunanin tatashi tashige toilet, alwala ta dauro, tazo tayi sallah raka'ah biyu, tasake yiwa Allah godia da Shahaab yabata kudi jiya, sannan tayi addu'ah Allah yakare ta akan duk wani sharrin abun qi dazata hadu dashi a hanya, tana kuka tad'auki handbag dinta guda daya, tasaka kudin da Shahaab yabata aciki, sannan ta juya zata bar Dakin hawaye yana fita daga idonta, idonta ne ya sauka akan takardun daya bata na company, har zata fita, saita dawo ta dauke takardun, ko banza bai kamata tabar masa takardun sa ahakan ba, wani zai iya shigowa Dakin ya dauke su, ahankali Tajuya ta dauke takardun, har zata fita, kawai saita sauya shawara ta dawo ta ajiye masa takardun sa akan gado, tafice daga d'akin cikin sauri, tana futowa falo bataga kowa ba, itama bata nemi kowa ba tafice zuwa compound, kasancewar sojojin sun San a gidan take, tana cemusu an aiketa ne, suka bude mata get tafice.


Mama na zaune abakin gadonta hawaye take sharewa,idan ya kasance wannan vedion na Shahaab da Aisha gaskiya ne, Yaya zatayi da wannan yarinyar? Anbata amanar yarinya Amma danta na cikinta yadinga lalata da'ita, Ina tarbiyar data Bawa Mahmud? Ina yayi watsi da aikinsa dahar yafara irin wannan mu'amular Bayan yasan cewa shi din mashahurin mutum ne acikin qasar,?tanajin Aisha a ranta kamar jikar ta, bazata lamunci wani ya lalata mata rayuwa ba tun tana yar qarama,bare Kuma Shahaab,koba komai ita Amana ce awajanta, gashi yarinyar taqi fad'a mata gaskiya bare tasan yanda zata 6ullowa lamarin, abinda tasani shine tunda har yagama lalata yarinya to babu fashi saiya aure ta, idonta cikeda hawaye tafuto falo domin daukar wayarta ta kirashi.

(Shahaab littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba, nabarki da Allah, Allah ya qwato min haqqi na)


******

"Ramadan aure nakeso,zan fadawa mama gaskiya tamin aure"

Ramadan ya kwashe da dariya yace"ikon Allah, Shahaab yau kaine da kanka kake cewa aure kakeso? To munirat dinfa?"

Dan qaramin tsaki yasaki yace"Ramadan banason wulaqanci, nide nafadama aure nakeso, karkaji ansaka rana kaitsaye kace ban fadama ba"

Cikin mamaki Ramadan yace"a a, Wai to har angama magana da iyayen yarinyar ne? Naji kana batun saka rana"

Idonsa ya Lumshe yace"no, nayi mata magana tayi tunani taga yaushe yadace naje nasamu mahaifin ta"

Ramadan yace"Saitayi tunani? Kawai ka shirya kaje ka sameshi, inde tana so kanaso menene abun tunani Kuma?"

Kafin yabashi amsa wayarsa dake ajiye agefen sa tad'auki qara, excuse ya nema awajan Ramadan sannan yad'auki daya wayar yace"Malam Auwali yakake ya kwanan iyali"

Daga d'ayan bangaren Wanda aka kira da Auwali yace"Alhamdulillah yalla6ai, nace wannan filayen Naka danake gadinsu Naga ka turo anfara gini har katanga tayi nisa Amma nikuma baka fadamin za'a ginaba shine nace Bari na kiraka naji Allah yasa de ba laifi mukai ba, kayi hakuri wannan aikin dashi nadogara Kuma dashi nake ciyar da ahlina"

Kan Shahaab ya daure, shide yasan baida wani fili da malam Auwali yake gadinsa Bayan filayen mama guda goma daya siya ya ajiye mata, baida fili ko daya a unguwar saide na wajan mama daya siya mata, shikuma yasan cewa Bayan yagama duba takardun Nan da hannunsa yasaka su acikin ma'adanar sirrin sa ya 6oye mata su, Kuma shide baisa kowa ya Gina suba, cikin mamaki yace"wai wanne filaye kake magana akai malam Auwali?"

Cikin girmama wa da ladabi malam Auwali yace"wannan filayen de daka siyesu kwanaki, to Ana gina manya manya aciki, guda biyu, Kuma gini har yayi Nisa"

Cikin sauri Shahaab yace"bansan da wannan maganar ba malam Auwali, menene amfanin ka awajan za'a fara aikin gini baka kirani kafadamin ba?"

Cikin sauri yace"wallahi tallahi yalla6ai jinake kaine ka turo ayi, shiyasa yanzu ma nakira inji ko laifi nayi"

Shahaab yace"kaje ka samesu kuyi magana, kayi musu bayani saisu fadama Wanda yaturo suyi aikin"

Yana fad'ar haka yakashe wayar, fada yafara yana sababi shi kadai, har wani Kiran yasake shigowa ya d'auka, malam Auwali yace"yalla6ai, sun fadamin wani Alhaji ne ya basu kwangilar aikin, yanzu haka yana cikin Abuja, nace su dakatar da aikin sunqi yarda sunce saka su akayi bazai iyu su daina ba, nace su Bani number Alhajin daya saka su sunce bazasu Bani ba"

Cikin 6acin rai yace"okay haka sukace? Rabu dasu kakoma wajan ka ka zauna, Alhajin zaizo da Kansa ya sameka har wajan gadinka, bazan sake nemansa ba saide shi ya nemeni "

Wayar yakashe, malam Auwali kuwa waje yasamu ya zauna cikin ransa yana fadin to fadan nasu na manya ne, yana kallon yanda masu aiki suke ta kwa6a cement suna aiki, shide ya zauna daga Gefe yana kallon ikon Allah, baifi minti goma Sha biyar da zama ba Sai ganin manyan motoci yayi sun nufo wajan gadan gadan, koda suka qaraso wajan basu saurari mutanan dasuke aiki asaman katanga ba suka nufi ginin suka fara zubar dashi, Nan da Nan masu aiki kowa yake ta ransa, nasama sukayi gaggawar saukowa qasa,anata ihu Ana hayaniya Amma masu motocin Nan kamar wanda suka saka Bluetooth akunne, ko kallon mutane basayi saida suka rushe ginin Nan gaba daya, malam Auwali dayake Gefe yana kallon ikon Allah ya tuntsire da dariya yace"shegiya nera..."

Kamar wanda akai ruwa aka dauke, suna gama baje ginin suka kada kan motocinsu sukayi gaba, masu aiki cikin sauri suka nufi malam Auwali suka bashi waya, yana sallama Wanda yasa ayi masa aikin filin yadinga roqonsa akan yafada masa waye uban gidansa, babu 6oye 6oye yafada masa MAHMUD WAKILI ne.


(littafin kudine,ki karanta abinki yafiya Kuma ban yafeba, nabarki da Allah, zai isar min"

******

Tana daukan wayarta afalo Kai tsaye ta nufi Dakin Aisha tana so ta lalla6a yarinyar ko zata fada mata gaskiyar abinda yake faruwa, saide tana shiga Dakin taga babu ita, babu dalilin ta, Sai wasu takardu data Gani azube akan gado, dauka tayi ta duba takardun, faduwar da gabanta yayi ne yasa cikin sauri ta dafe qirjinta tareda zama akan gadon, takardun tasake kalla cikin sauri tace"wannan ai takardun sabon companyn da Mahmud yabude ne, Yaya akai Aisha tasamu? (tun farko akwai wadda nayi niyyar mallakawa, ita din mace ce mai mutuqar muhimmanci a gareni,zan'iya sadaukar da rayuwa ta domin ta,dalilin hakane yasa na mallaka mata wannan company,ba kowa bace face AISHA).

maganganun Mahmud suka Fado mata acikin rai lokacin daya bude company, ta tuna kallon dayake bin yarinyar dashi washe Garin ranar lokacin da Aishan take hada mata tea, cikin tsananin mamaki tace"kaiii tayaya? Yaushe har suka hadu acikin gidan Nan suka fara soyaiya bansani ba?hakan yana nufin wannan Aishan yake nufi kenan? Idan ba ita yake nufi ba tayaya zata ga takardun acikin Dakin Aishan?.

Cikin sauri tafara qwala mata kira, saide duk inda yakamata ta duba, ta duba babu Aisha kwata kwata, cikin sauri ta doka wa Shahaab kira, Yana d'auka tace"yaushe zaka dawo?"

Cikin mamaki yace"mama meyafaru?"

Cikin tashin hankali tace"komai ma yafaru, narasa Aisha, kazo ka Nemo min ita, duk inda yarinyar Nan take kaine silar 6acewar ta, na nuna mata vedion da kukayi, daga Nan na nemeta narasa"

Cikin mamaki yace"vedio Kuma mama? Wanne irin vedio?"

Cikin sauri tace"kome kake a lagos kabari kazo gida yanzu-yanzu"

Cikin sauri ya amsa mata, domin kuwa Shima Kansa Hankalinsa atashe yake, yanaso yasan waye yasa agina masa filayen mama, sannan yanaso yasan wanne irin vedio ne mama take magana akai, babu 6ata lokaci ya shirya yanufi Airport.

Awa daya da wani abu ce takawo shi gida, a compound ya hango munirat ranta a6ace, tana ganin zuwansa Ana bude masa kofar mota tayi sauri Takoma daki, idan a Kwai Wanda batason Gani bai wuce Shidin ba.

Kai tsaye part din mama yanufa, yana zuwa bata barshi ya zauna ba tamiqa masa takardun company tace"yaya akai wadannan takardun sukaje wajan Aisha?"

Ta qarasa maganar tana tsare shi da idonta.

Gabansa ne yafadi, ya hadiye wani irin yawu sannan yace"mama ki zauna nayi Miki bayani, please zauna"

Babu musu ta zauna, tad'auki wayarta ta bude vedio tace"shikuma wannan vedion mezaka ce akansa? Shahaab Ina Hankalinka yake? Abinda kakeyi da yarinyar Nan kenan shiyasa kake mata 6arin kudi kayi mata siyaiya, ka dauki company kabata, menene ribar irin wannan rayuwar daka jefa Aisha aciki? Yanzu gashi tagudu, na nemeta narasa, shikkenan tashiga duniya kaji dadi" ta qarasa maganar tana fashewa da Kuka...

Kansa yadafe yace"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...."
Yazubawa vedio ido yana kallo,saida yagama Gani sannan yabude breafcase dinsa, yadauko computer sa aciki,sannan yatura vedio yayi Yan danne danne tsawon lokaci, sannan yatura mata computer gabanta yace"mama, idan kikaga irin wannan vedion nutsuwa yakamata kiyi ki kalla dakyau mama, yanzu duba kigani Bani bane, ba Kuma Aisha bane, dora fuskar mu akayi akan vedio,kiduba jikinsu kigani, mama wannan yarinyar tafi Aisha girma, ki kalli surar jikinta dakyau, sannan ki kalli ta namijin Shima kigani, ga zahiri nan computer ta nuna miki, duba kigani mama"

Ajiyar zuciya tayi, ta share Hawayen idonta sannan tafara kallo, lokaci daya tasaki salati tace"yanzu Dama anayin haka Mahmud?"

Yace"gashi kuwa kingani mama?, bani number da'aka turo miki vedion, zansa ayimin tracking dinta"

Babu musu mama tabashi number, murmushi yayi har dimple dinsa suka futo yace"yanzu shikkenan Hankalinki ya kwanta?"

Sake goge idonta tayi tace"AISHA"

Murmushin yayi, sannan ya shafa sumar Kansa yace"mama nida Aisha mun dade muna tare"

Cikin sauri ta Kalleshi, Shima ya Girgiza mata Kai sannan yace"qwarai kuwa mama,nahadu da Aisha tun cikin azumi,Kuma kece silar haduwa ta da Aisha mama, tun lokacin dakika umarceni naje Jigawa State in bude miki gidan marayu saboda qawar ki, tun Alokacin nahadu da'ita, idan Zaki tuna mama Alokacin banda magana saide ince zanje jigawa, ki gafarceni mama, Amma wani lokacin ba wajan wannan aikin nake zuwa ba, wajan Aisha nake zuwa, nadauki shawarar ki data Ramadan cewa in6oyewa budurwar danakeso kaina, hakan nayi akan Aisha, ban nuna mata inada kudi ba naje mata a matsayin Yaron Mahmud Wakili, ahakan ta amince Dani take soyaiya Dani, iyayen Aisha talakawane mama, suna rayuwa cikin kwanciyar Hankali zuwana cikin rayuwar ta saida hakan yata6a wannan farincikin na ahlinsu, duk abinda nasaka ta shi take min,kudin dan'uwan ta datake aiki take Tarawa tana so Yaron yakoma makaranta shita dauka tamin kyauta dashi mama, A'ina zan samu irin wannan soyaiyar mama?akwai Wanda akeso abata agida tace ita Shahaab take so,dalilin hakane yasa babanta yaturo ta aiki Abuja, baisan cewa gidana yasake turo taba, ranar Dana dawo daga Australia a ranar na ganta a gidan Nan idan zaki tuna Alokacin nashiga cikin wani irin yanayi, kiyi hakuri mama, Amma inason Aisha, bantaba son kowacce yarinya kamar son danake mata ba Bayan ke, inaso Dan girman Allah mama kinemomin Aurenta please"

Ya qarasa maganar yana hade hannayensa waje daya, mama data zuba masa ido tana kallon sa tasaki ajiyar zuciya tace"amma kukan anyi munafukai, daga Kai har Aishan ba qananun munafukai bane, ni Ina zaune ashe ku soyaiya kuke shiyasa kake wa yarinyar mutane ihu saboda tace tadena son Wanda ya yaudare ta? Yanzu ashe Dama dakai take? Yanzu fisabilillahi ka kyauta abinda Kamin Shahaab? Kasan Sarai kanason yarinyar Nan Amma shine lokacin da batada lafiya na riqeta kadinga ta6awa yarinya nonuwa kod'an musu babu? Yarinyar Nan bata so Amma haka nasa ta tsaya saida kagama abinda kaga Dama sannan karabu da'ita,meyasa lokacin ko dukanka zanyi bazaka cemin bazaka ta6aba?"

Wata irin matsananciyar kunya ce ta kamashi, yayi sauri ya sunkuyar da Kansa qasa tareda Sosa qeyarsa yace"mama saida nace Miki a a...fa"

Cikin sauri tayi masa daquwa tace"qarya kake Shahaab,cemin kayi dubawa de kake,nasan hakane yaushe zanyi wannan danyan aiki?"

Kansa yana qasa yayi Dan qaramin murmushi, sannan yadan kalleta cikin kunya yace"mama to Zaki nemamin auren Nata?"

Fillon dake gefenta ta d'auka takai masa duka dashi tace"Wato Aisha ta maida Kai marar kunya, aini babu abinda zance, idan kaga zaka iya yiwa munirat kishiya shikkenan, dama kaine kake cewa kaida munirat Sai Allah, yanzu Yaya za'ai Naga Aisha?"

Cikin nutsuwa yace"za'a ganta mama,ki kwantar da Hankalinki,mutuqar agogon Dana daura mata yana hannunta, to dole zansan inda take"

Mama tasaki wata irin ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah, Allah abun Godia, to tashi kaje kabawa matarka haquri Dan itama anturo mata wannan vedion, kabata haquri ka fahimtar da'ita cewa videon hadawa akayi"

Cikin ladabi ya amsa mata, sannan yatashi yad'auki kayansa, yawuce part dinsa, yana zuwa falonsu yayi sallama tareda shigowa, tana zaune afalon saide ko kallon inda yake batayi ba, cikin zuciyar yace"fishi kan fishi kenan, Dama da fishin company yanzu Kuma ga wani ya qaru"

Murmushi yasakar mata, sannan yace"Bari inzo inyi lallashi"

Munirat ko kallon sa batayi ba,Shima Kai tsaye dakinsa yawuce yana tunanin irin lallashin dazai mata kozai samu yau tasakar masa jikinta yayi yanda yakeso da'ita, saboda a matse yake, kwana biyun Nan kawai yana daurewa ne,yana shiga Dakin yacire kayan jikinsa,dagashi Sai Dan qaramin towel a daure a qugunsa, murd'ad'd'an jikinsa yafuto fili, fatar jikinsa tayi wani irin fresh, lallausan gashi kwance akan faffad'an qirjinsa,yana shirin shiga wanka kenan wayarsa tad'auki qara, dawowa yayi ya zauna abakin gado tareda daukar wayar yayi sallama, daga dayan bangaren akace "Ranka yadad'e sunana Alhaji Umar Amare, nine mamallakin filayen Nan guda biyu danasa afara ginamin Kuma yanzu Yara sun kirani sun fadamin katuro a rushe ginin, shine nace ai babu Wanda baisanka ba a qasar, na bincika nasamu number ka awajan yaronka Auwali, nace Bari in kiraka inbaka haquri, Dan manzon Allah kayi hakuri, Nima wannan fili, siyarsa nayi, Kuma nadauki kudi nabawa wadda nasiya awajanta da shedu na dakomai, tasa hannu Nima nasa hannu, tabani takardun filaye Nima nadauki kudi nabata"

Cikin tsananin mamaki yace"wacece ta siyar Maka?"

Cikin tabbatar wa yace"Sunanta Munirat Abdul Salam,domin kuwa Alokacin ma ban sayi filayen ba saida ta tabbatar min cewa mijinta ne yabata su kyauta, saboda kasan harkar ciniki da mata"

Wani irin duhu duhu Shahaab yafara Gani, duk bayanin da mutumin yake masa kwata kwata baya jinsa, tun lokacin daya ce masa munirat Abdul Salam, tundaga lokacin yanemi nutsuwarsa yarasa, cikin tashin hankali yace"Kanaji na? Zanbaka kudin filayenka, da kudin daka kashe na aiki, saika Bani takardun filayen"

Cikin sauri Alhaji Umar yace"to yalla6ai babu damuwa godia nake"

Daga Nan yakashe wayar.

Wasu irin hawayene masu mutuqar zafi suka zubo daga idanun Shahaab, cikin ransa yace"munirat?"








Da alama zancen lallashi ya rushe >�#�<���<���
@&�<���<���
@&�<���<���
@&�



Shahaab littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba nabarki keda mahaliccin ki,inde ubangiji yana sakayya na tabbatar zai Sakamin

300
0164549488
Amina muhammad
GTbank


Ko katin mtn

Shedar biya ta wannan number 08033300034





Amnah El Yaqoub
'<���



Page 37








Gaba daya saiya nemi 'yar sha'awar data addabeshi yarasa(=��)

Kansa yariqe da hannunsa guda biyu yafad'a Kan gadon tareda furta"innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
Wani Hawayen ne suka sake zubo masa,yaji duniyar tayi masa zafi gaba daya, Dame yarage ta? Meta nema tarasa awajansa?meyasa zata masa haka? Har tasan tad'auki takardun filaye ta siyar, me zatayi da kudin? Meyasa mutumin daka daukakeshi fiyeda kowa yake cin amanarka daga baya?menene baiyiwa munirat ba? Haduwarsa da Aisha ne kad'ai yasan cewa yaraba soyaiyar dayake mata gida biyu yabawa Aisha d'aya,jin wayarsa tana ringing ne yasa yayi saurin goge Hawayen Idonsa, a fili ya furta, "dole zan dauki mataki akan munirat".

Wayar dake shirin katsewa yayi saurin dauka, daga dayan bangaren mama tace"Shahaab kaduba kagano inda Aishan take?"

Saida ya daidaita muryarsa yanda bazata gane yana cikin wani Hali ba, sannan yace"ban dubaba mama"

Cikin sauri Tace"A a, Tome kake nufi?shikkenan daga shiga wajan matarka harka manta da batun yarinya?yarinya qarama tafice tabar gidanka kacemin zaka duba Amma kayi biris harka samu munirat ka manta da Aisha,?Anya kuwa Shahaab zan'iya nema Maka auren yarinyar Nan? Tun yanzu ma kana shiga wajan matarka ka manta da batunta, tayaya za'a yi maganar aure tsakani da Allah?"

Duk da yana cikin halin damuwa saida ya danyi qaramar dariya yace"mama wanka zanyi saina duba nagani, karki damu mama, Aisha bazata 6ata acikin qasar nan nakasa dubo taba aduk inda take"

Cikin sauri tace"to hanzarta kayi wankan"

Wayar ya kashe, batareda tunanin komai ba ya lalubo number Hajja, wannan ne kiransa na farko wayar Hajja tun Bayan zuwan Aisha gidansa, kamar jira Hajja take, wayar tana shiga ta d'auka tareda sallama, cikin ladabi yace"Hajja barka da wannan lokaci"

Hajja tace"yawwa barkanmu dai, dawa nake magana?"

Murmushi yayi yace"Sunana Shahaab"

Cikin sauri Hajja tace"kacewa? Shahaab koba Shahaab ba?"

Cikin sauri Shima yace"eh haka nace, nine Shahaab, dama Ina neman Aisha ne"

Hajja tayi ajiyar zuciya tace"wacce Aisha?saida ka salwantar min da jika zaka debo jiki kana tambaya ta Ina Aisha? Nan kazo har gida ka hure mata kunne yarinya tayi tsalle ta dire tace Nan duniya saikai, kasa mamuda yaturata aiki har yau bansan inda jikata take ba, wallahi Shahaab idan Namutu bansake saka jikata a'idona ba hakuma ce zata rabani dakai...." daganan saita Fashe da Kuka

Runtse Idonsa yayi,cikin ransa yace"kuka!,kamar de Aishan"

Cikin nutsuwa yace"kinga, kiyi hakuri, insha Allah zata dawo gida lafiya, kiyi hakuri Dan Allah"

Cikin masifa Hajja tace"zaka rufemin baki ko saina wankeka da Mari? Kashe waya!"

Cikin sauri yakashe wayar yana Girgiza Kansa, da alama rikitacciya ce kamar mama, ajiyar zuciya yasauke, hakan yana nufin bataje gidaba kenan, dole zai bincika yagani, cikin sauri yatashi yashiga wanka


(idan kika karanta baki biyaba nabarki da mahaliccinki)
******

Bayan gwagwar mayar da Tasha, daqyar da d'an turancinta tasamu aka kaita inda zata shiga motar dazata kawo ta kano,suna cikin tafiya tana share hawaye daga idonta kad'an kad'an, waye yayi mata wannan sharrin? Abinda take tambayar kanta kenan, tun tana share hawaye harta Dena,tana addu'ah tana kallon garuruwa da dajujjukan dasuke wucewa har Allah yakawo su kano lafiya,yamma tayi sosai kasancewar hanyar akwai go slow, anan ma bata Sha wahala ba kawai napep ta tare tafada masa tana so yakaita inda zata hau motar dazata kaita dutse, yafada mata kudin, ta d'auka tabashi, sannan tashiga suka tafi, can ma tana zuwa tashar ake tambayar ta

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment