Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nida uwarka aiko?"

Murmushi yayi yace"Hajja hanya fa babu tsaro yanzu, za'a iya saceku acikin daji,kigama lissafin mutanan ki tsaf, saiki fadawa amaryar,duk yanda kukayi da'ita saita fadamin ta waya, inyaso saikubi jirgi, Amma kude bazaku dawo ba idan kunje, saboda haka kuyi sallama da kowa kafin kutafin"

Abba ya Girgiza Kansa yace"haba yalla6ai, a a baza'a yi hakaba, zamu dorama nauyi yalla6ai"

Batare daya hada ido da abban ba yace"Babu damuwa,koba Dan Aisha ba, dole zaku bimu kodan amintar mama da Hajja"

Ummah ce tafashe da Kuka tace"mungode Allah yasaka da alkhairi, Allah yaji qan mahaifin ka"

Gaba dayansu suka amsa da "Amin"

Hajja Tace"A a to tunda jirgi zamubi, bazanyi gayya ba, tun Ana abu na Hankali karkuma a koma na rashin Hankali, saboda haka duk Wanda yake min mutunci dashi za'ayi tafiyar Nan, lalla6a jummai zanyi inyi shiruuuu, tanamin abu komin qanqantar sa zan cireta daga list..."(=��=�2�)

Dariya suka saki gaba dayansu, mama tace"ni bakima kiramin ita mun gaisa ba"

Kafin Hajja tayi magana yan'uwan mijin Hajja suka shigo gidan susu uku, Hajja Tace"A a malam baqori kune a gidan? Sannunku da zuwa"

Ummah ce tasake shinfida musu wata tabarmar suka zauna, Bayan sunyi gaishe gaishe dakuma bayanin juna, anan aka tsaida lokacin biki sati uku masu zuwa, shi Shahaab asan ransa ma a saka sati biyu, saboda shi kadai yasan meyake ji, jiyake kamar ya hadiye Aishan kowama ya huta, Amma Hajja ta daddage tace saide a saka sati uku, kafin Nan sungama kintsawa.

Mama ce tad'auki kudin komai tabayar kamar yanda al'adar Garin take,daga Nan Kuma Shahaab yayiwa securities dinsa waya suzo su tafi, daga Nan shida Abba suka raka tsofaffin gida.

mama da Hajja suna zaune arumfa suna qulla Goro, Wanda za'a rabawa mutane, nasaka ranar Aisha,mama ta kalli Hajja tace"oh bakiga idon Shahaab ba da'aka saka sati ukun Nan, inajin da Kuka zai saki"

Hajja tayi dariya tace"naganshi,Dan qaniyarsa ai gata nake masa, a wannan lokacin nefa zan Dan samu Tasha magungunan Sanyi,muda muke neman haihuwa ai dole mu nemi maganin Sanyi, Shima idan kun koma akwai maganin dazan baki kitafi dashi saiki bashi yadinga Sha,idan akwai sanyin ma to zai rabu dashi insha Allah"

Mama yace"aikuwa zan bashi, zan dinga zaunar dashi Ina bashi yanasha,har komai ma bashi zanyi, ai ba ita kadai yakamata Tasha maganin matan ba, Shima saiya Sha irin Wanda yadace"

Haka suka dinga zancen su har mamakinsu Ummah takeyi, ko gajiya basayi da zance.
karfe biyu daidai sukayi shirin tafiya,Aisha tana daki tanaso ta ganshi Amma Kuma tana kunyar futowa, mama da Hajja sukayi gaba, Abba ya kalli Ummah yace"kira masa ita suyi sallama"

Daga Nan Shima yafice daga gidan, Ummah ta kalli Shahaab dayake tafiya kamar bayaso Dama Kuma Shima abinda yake ransa kenan, jira yake ko Yaya ne yadan kalleta kafin yatafi, Ummah tace"bari Akira ta"

Babu musu kuwa yaja ya tsaya, a gabansa tashiga d'akin Hajja sannan tafuto itama tafice daga gidan, yana tsaye tafuto daga daki tana Sanye cikin hijab, Kallan ta yayi yace"Maa-mah, banda yawo, banaso kina fita kowa yana kallon ki kinji ko?"

Daga masa Kai tayi sannan tace"insha Allah, Allah yakaiku lafiya"

Yace"Amin,saiki fara shirin tar6ata nanda sati uku, ni banso ma akasa lokacin har haka ba, kefa?"

Cikin kunya tace"jinake ma wata uku za'a saka"

Girgiza Kansa yayi, ya matso kusa da'ita yayi kissing goshinta yace"ki kulamin da kanki, banda kula maza, Sai munyi waya"

Tace"to insha Allah"

Daga Nan yafuto daga gidan cikin sauri, saida yagama sallama da mutanan dasuka zazzo Yan Garin yayi musu ihsani , sannan yashiga motar suka tafi, har lokacin Hajja da mama labari suke, saida mota taja, sannan suka juyo cikin gida, tundaga Nan Kuma mutane suke zuwa gidan Ana yiwa Hajja Allah yasanya alkhairi, jikar ta takusa aure.

(littafin kudi ne, idan kika karanta min baki biyaba nabarki da Allah)

******


Wannan Karon kawai Airport suka wuce sukabi jirgi shida mama, suna sauka a Abuja Kai tsaye gida suka wuce shida mama, munirat tana part dinta batasan sun dawo ba, zama yayi akan kujera cikeda gajiya, mama ta wuce wajan ma'aikatan gidan tana sanar dasu auren me gidansu nanda sati uku, yana zaune Idonsa a Lumshe aka masa waya, daukar wayar yayi tareda sallama"ranka yadade mungama tracking din number Nan daka turo mana,angama bincike akan number, yanzu haka yarinyar tana hannun mu, Amma tafada mana ba'ita kadai bace, itada qawarta ne, zamu turo Maka pictures dinsu da sauran information din damuka dauka awajansu ta Email dinka, sauran bayanin Kuma sai abinda kace"

Cikin sauri yace"babu damuwa,Sai munyi waya"

Kai tsaye Email din yaduba

Yana ganin fuskar su yarasa Ina yasan su, mama data dawo falon tayi magana taji shiru, tasake yimasa magana taji shiru, mamaki ya kamata, yazuba wa waya ido yana kallo kome yake kallo? Hannu tasa ta ta6oshi, cikin sauri ya kalleta, tace"tunanin me kakeyi haka?"

Wayar yabata yace"mama wannan sune Wanda suka hada wannan vedion da aka turo muku keda munirat, Amma Kuma narasa Ina nasan fuskokinsu, kamar de qawayen munirat ne"

Mama ta kar6i wayar, tana ganinsu tace"sune mana, qawayen tane, ai wani lokacin idan sunzo Ina ganinsu, tosu menene amfanin hada wannan shirmen? Menene ribarsu nayin hakan?shiyasa banaso munirat ta dinga mu'amula da qawayen banza irin wannan, yanzu banda raini yaza'ai suyiwa mijin qawar su haka?"

Cikin damuwa yace"shine abinda nagani Nima"

Tace"kaje ka sameta kuyi maganar, Amma su din karka yi musu komai, kabar su Suda mahaliccinsu, idan sunyi hakan ne da wata manufar ai gashinan Allah yatoni asirinsu, kodan mutuncin dasuke yi Suda matarka, karabu dasu, Amma kasa a qwace wayoyin su a duba sosai idan akwai irin vedion agogeshi, wannan 6ata suna ne, ita Kuma saika fada mata tasan irin mu'amular dazata dinga yi dasu"

Cikin gamsuwa da bayanin Nata yace"to mama"

Daga Nan yatashi yanufi part dinsu, yana tunanin tayaya zai iya yiwa munirat din maganar aurensa da Aisha?

Yana shiga falon nasu yaga TV a kunne ta nayi, Kai tsaye dakinta yanufa, yanaso ya nuna mata kuskuren ta akan laifin data masa na saida filayen mama, sannan Kuma ya hanata mu'amula da wannan qawayen Nata, saboda karsu dinga Zua suna hure mata kunne har taqi yarda suyi Zaman lafiya itada Aisha, gefe guda Kuma ga wata irin masifaffiyar sha'awa da yakeji, yadade-yadade, abun yamasa yawa, yana buqatar mace,da tunanin maganar auren nasa yashiga Dakin Nata, saide abun mamakin yana tura qofar yaji ta abude, tana zaune akan gado tabawa qofar Dakin baya,dinkin dake jikintane yamasa kyau, shiyasa ya tsaya daga bayanta yajingina da jikin qofar Dakin yana qare mata kallo, wannan ne Karon farko da yaji tsoron yiwa matarsa magana saboda auren dayake shirin yi, munirat kuwa waya take, kwata kwata ba taji shigowar saba, tariga tasan cewa baya gidan shida mahaifiyar tasa, shiyasa Hankalinta kwance taci gaba da fadin"suna dawowa zan sanar daku, zan San yanda zanyi in sakawa securities din maganin bacci alemo susha, Kuna ganin wayata kuzo ku kashe ta"(=�F�<���
@&�)

Cikin tsananin tsoro, mamaki, dakuma firgici, Shahaab yazaro Idonsa waje(=�3�)
waza'a kashe?
Gabansa ne yafara faduwa, magana zaiyi mata, Amma saitaci gaba da cewa"karku damu, nafada muku babu matsalar komai, zan turo muku photon gidan, da inda zaku shiga har cikin dakinta, nafada muku Kuna zuwa kawai ku kashe ta, na tsaneta!, na tsaneta!!, na tsaneta!!!, tashiga cikin rayuwa ta tayi min Kane-Kane, ta hanani Zaman lafiya da mijina, harni zata bude baki tana fadawa zai qara aure, lalle-lalle ku tabbatar kun aiwatar da abinda nasaku,tsohuwa ce bazata muku wahalar kisa ba, Kuna kashe ta kushigo Nan Nima ku yanke ni, yanda baza'a gane dasa hannu na aciki ba, itama yarinyar dazai aura zan dawo kanta, karku kira wayata zan dinga kiranku idan buqatar hakan tataso"

Ruf idon Shahaab suka rufe, kwata kwata saiya daina ganin komai, baisan lokacin da qafafun sa suka fara rawa ba, saiji yayi yafadi qasa jagwab, salati yake acikin zuciyar sa, banda hannunsa guda daya da yakeji yana masa rawa, dayan Kuma ba yayi, saikace Wanda cutar 6arin jiki takeso ta kamashi, cikin ikon Allah yana motsa hannunsa yana salati har yaji hannun nasa yadena rawa, Idonsa yabude ras!.

Tun lokacin daya fadi tajuyo ta kalleshi, idan qirjinta yayi dubu, to yau gaba dayansu saida suka fadi, yanda gabanta yake luguden faduwa harji tayi kamar wani abu yafada cikinta, lokaci daya jikinta yad'auki karkarwa.

Shikuwa Shahaab wani irin kallo yake mata na tsoro, kisa!? Kisan mutum Kuma mutum dinma ba kowa ba Sai mahaifiyar sa?

Lokaci daya Idonsa yayi jajir!
Cikin sauri yatashi yawuce dakinsa, yana zuwa ya zauna akan gado tare riqe Kansa dayake masa barazanar rabewa gida biyu, wani irin kuka ne yazo masa Wanda Rabon Dayayi wannan kukan harya manta, kuka yake sosai harda shashsheka, acikin wannan halin tashigo Dakin nasa ta sameshi, tana zuwa ta zuba gwiwarta aqasa tareda sakin wani irin kukan, tsawon lokaci suka dauka Ahaka, shi yana kuka itama tanayi, saida taga bashida niyyar ce mata komai sannan tasa hannu ta riqe qafafun sa tace"my Dear, Dan Allah kayi hakuri, wallahi nadena, natuba kayafemin, bada nufi nayi hakan ba, kayi hakuri bazan sake ba"

Taqarasa maganar tana dora kanta akan tafin qafafun sa, cikin sauri ya d'ago Kansa tareda goge Hawayen Idonsa, muryarsa adake, kamar bashine yayi kukaba yace"MUNIRAT, kitashi kitafi gidanku daga yau Bana buqatar ki acikin rayuwa ta"

Cikin sauri ta d'ago ta kalleshi, hannunta tahade waje daya tace"mahmud nikake Kora daga gidanka yau?idan nayi niyyar aikata kuskure ashe bazaka Jani a jikinka ka nunamin illar hakan ba?Saboda kasamu wadda tafini?"

Runtse Idonsa yayi, cikin tsawa yace"munirat na tsaneki, nadauki yarda nabaki, na amince dake, nasoki fiyeda kowa abaya, banajin maganar mahaifiyata saboda soyaiyar danake miki, mama na itace komai nawa, itace mahaifina itace mahaifiyata, ban rageki dakomai ba amma kin dauki filayenta kinje kin siyar,banyi miki magana ba, kinsan ko saboda me? Saboda Ina sonki, qawayenki sun hada min vedio na banza da 6atanci nida yarinyar datake ganin darajar mahaifiyata kamar Tata mahaifiyar, sun turo miki, kin dauki gaba Dani, kin hanani haqqi na, now saboda maganar aure Harkina cewa kin tsani mama,aje akashe ta, akashe min mahaifiya ta munirat? Sakamakon dazaki nunamin kenan? Wannan shine tukwicin soyaiyar Dana nuna miki abaya? Yanda kikace kin tsaneta Nima na tsaneki munirat, kiyi hakuri bazan iya cigaba da zama da wadda bata qaunar mahaifiya taba, kifice daga gidannan, kifice daga unguwar Nan,kifice daga cikin rayuwa ta"

Gabanta ne yasake faduwa, dama yasan da maganar takardun data sace? Wata irin tsananin kunya ce tasake rufeta, taji kamar qasa ta tsage ta shige ciki, lokaci daya jikinta yayi Sanyi kalau, bata taba nadamar abinda take aikata masaba Sai yanzu, ta Kuma yi Imani tabbas Mahmud yana sonta, domin kuwa Mai sonta ne kawai zai'iya yin haquri da maganar filayen Nan batare Dayayi mata hukunci ba, ta kalleshi Tace"Mahmud...."

Kafin taci gaba da magana ya dakatar da'ita ta hanyar daga mata hannu(>��<���) yace"munirat, namiki saki daya, kitashi kitafi gidanku"

Cikin tsananin firgici tasake cewa "Mahmud...."

Idonsa ya runtse, ko kadan baison sake ganin fuskarta, cikin 6acin rai yasake cewa"munirat, namiki saki na biyu kitashi kibar min gidana"

Zaro idonta tayi, mamakine yasa tasake cewa "mahmu...." kafin ta qarasa cewa Mahmud din, yasake cewa "munirat.....namiki...."

Cikin sauri tatashi tafice daga d'akin tana kuka mecin rai, ta tabbatar idan bata fitaba, yanda ransa yake a6ace, to idan Ana saki goma, yau zai iya yimata shi.

Ko Kallan dakinta bata Kuma yiba, ta warware Dan qaramin mayafin data daura akanta, ta nufi bakin get tana kuka me tsananin ciwo















(haba Shahaab.... =�-�=�-�=�-�)


(wayyo Anty Munirat >�y�>�y�>�y�)


Allah ka rabamu da sharrin zuciya >�2�<���





Shahaab littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba nabarki keda Allah, nide ban yafe ba


300 kacal
0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN tareda shedar biya ta wannan number 08033300034











Mrs Usman ce
'<���





Page 25





Kasancewar ta matar megidan yasa kokusa basuyi kuskuren hanata fita daga gidan ba, hankalin megadi yaqi kwanciya, ya hanzarta zuwa cikin gidan, yasamu mama tana dudduba kayan da Hajja ta hado mata tataho dashi a leda, cikin rawar jiki Yace"Hajiya...ga Hajiya qarama can tafita tana kuka, da alamun ba lafiya ba, shine nace Bari nazo na sanar dake"

Cikin sauri mama tatashi tace"subhanallahi, Bari inje part din nasu"

Tashi tayi tafice ta nufi part dinsu, zata Iya cewa rabonta data zo part din Shahaab harta manta, saboda bata zuwa gudun kar taga abin 6acin rai, ita Kuma bazata iya yin shiru ba.

Saide tana zuwa tayi sallama taji shiru, Kai tsaye dakinsa ta nufa, yanayin data ganshi aciki ne yasa gabanta faduwa, wani irin numfashi Shahaab yake fitar wa kamar wanda yake gab da shirin mutuwa, salati tasaka tafara tatta6a jikinsa taga abu yaqi qarewa, cikin sauri tad'auki wayarsa ta sanarwa da doctor halin da ake ciki, sannan takira Ramadan shima tafada masa.

Zama tayi tajashi jikinta daqyar, ta dora Kansa akan cinyarta tafara Tofa masa addu'ah, cikin Yan mintuna qalilan doctor yazo, cikin sauri yafara dudduba shi, dayake yazo da kayan aikinsa Kai tsaye ruwa yafara daura masa, yayi masa allurar bacci, sannan yafara harhada wasu alluran, Adede lokacin Ramadan yashigo Dakin da gudu, kan Shahaab din yanufa gabansa banda faduwa babu abinda yake, ko kallon mama baiyi ba yadubi doctor yace"yaya ake ciki? Meyasame shi?dazu dazu fa mukai waya dashi"

Saida yagama hada alluran yayi masa, sannan ya kallesu yace"bawata matsala bace babba, damuwa ce ta masa yawa, saide Kuma kuyi haquri, hawan jini ya kamashi, Dan da ba'a kirani akan lokaci Bama yanayin dayake ciki, zai iya haifar masa da cutar paralyzed, Amma nayi masa allurai,idan yagama baccin zai tashi lafiya insha Allah, Sai abashi wannan magungunan yasha, please Hajiya akula da abunda zai sashi damuwa Dan Allah"

Cikin damuwa mama tace"likita idan akwai damuwa afita dashi qasar waje kawai"

Murmushi yayi yace"Hajiya mama idan abun yayi tsanani nida kaina zance akai shi, nafada miki babu komai, damuwa ce tamasa yawa"

Cikin sauri tace"to wacce irin damuwa ce zata dameshi shida yake shirin zama ango? Nafi tunanin dawowar mu gida ne yanzu, saboda matarsa tafita tana kuka"

Cikin ladabi yace"idan kinyi min izni zan iya tafiya?"

Cikin sauri ta d'aga masa Kai tace"babu damuwa, idan yafarka,zan kiraka"

Daga haka yajuya yafita, mama ta kalli Ramadan daya dafe goshinsa da hannunsa Kansa yana sunkuye, duk wannan batun da ake Kansa yana qasa, yayi Nisa cikin tunani menene yake damun abokin nasa har ya haifar masa da hawan jini?

Mama ta kalleshi Tace"Ramadan ko kunyi magana dashi ne yafada Maka wani abu?"

Ajiyar zuciya yasauke yace"mama munyi magana dashi de ansaka ranar aurensu, Bayan haka yacemin idan yadawo gida zai nemeni,Amma ni Hankali na yaqi kwanciya kode zamu dauke shi daga Nan ne? Gara a fitar dashi mama, banason abinda zai ta6a lafiyarsa, saboda ta ko'ina muna buqatar sa acikin rayuwar mu"

Mama tace"dawowarmu kenan, ni Ina zaune megadi yacemin inzo munirat tafuta tana kuka, Ina zuwa saina ganshi a wannan hali Sai numfashi yake ja baima San inda Kansa yake, Amma mu bari yafarka din mugani, idan da sauqi shikkenan, idan Kuma da damuwa kawai saimu tafi"

Ajiyar zuciya yasaki yace"toshikkenan"

Saida tashafa fuskarsa, tata6a wuyansa taji babu zazza6i sosai, sannan tayi kissing goshinsa, ta gyara zamanta akan gadon itama ta zauna tayi shiru, tsawon awa uku suna haka,Amma Bai farka ba.

(banyafewa duk wacce ta karanta min batare data biyaba)


******

Zaune suke a Dakin Ummah itada Walida, Walida ta kalleta Tace"amarya, har kin fara wani irin haske kina sheqe"

Murmushi tayi, ta daga murya tace"Hajja Dan Allah kibani wayar inkira mama inji ko sunje"

Hajja datake daka mata gumba tace"kede kawai kice abaki waya kikira shahab, Nina Rasa wacce irin amarya cema babu waya"

Walida tayi qasa da muryarta tace"ai yanzu Zaki samu waya, saikin shiga tukunna"taqare maganar cikin wata manufar

Harararta Aisha tayi tace"kyaji dashi"

Hajja ce tad'auki wayar takawo mata, cikin sauri takira mama, saide Alokacin wayar tana daki, ita Kuma tana can tareda Ramadan adakin Shahaab.
Saida tagama dakan gumbar, sannan tahada mata wani magani cikin Dan qaramin bokiti tace"gashinan maganin Sanyi ne, saiki dinga Sha kullum"

Hankalinta yana kan waya tace"to Hajja"

Saida tayi wa mama 3missed call, bata dauka ba, sannan tabawa Hajja wayarta


******


Sai Bayan sallar magrib yafarka, Adede lokacin Kuma Ramadan yadawo daga masallaci, mama kuwa acikin Dakin tayi sallah.

Yatsina fuskarsa yayi tareda dora hannunsa akan goshinsa ya runtse Idonsa, cikin sauri Ramadan yace"Shahaab katashi?"

Mama kuwa jikinsa tafara ta6awa tana fadin" Alhamdulillah, Bari inkira likita"

Kokarin tashi yake zaune, Ramadan yayi saurin riqeshi tareda saka masa fillo a bayansa yanda zaiji dadin zama, kallon mama yayi, cikin shagwa6a yace"mama kaina yana ciwo"

Cikin sigar lallashi tace"nasani, yi hakuri, yi hakuri kaji, nakira doctor yanzu zaizo"

Bata dade da rufe bakintaba kuwa doctor yashigo, sake dubashi yayi ya kalli mama Yace"Hajiya mama jikinsa yayi sauqi sosai," yasake russunawa cikin ladabi yace"Allah yaqara afwa yalla6ai"

Shahaab ya Jinjina Kansa alamun amsawa, mama tace"amma Dr. Yacemin fa Kansa yana ciwo, kana ganin babu matsala ne?"

Cikin sauri yace"babu damuwa Hajiya, inde kun bashi magungunan Dana bayar dazu, zai warware, saide a kiyaye abinda zai sake 6ata masa rai"

Cikin sauri tace"insha Allah"
Dr. Nafita, mama tabi bayansa ta wuce part dinta domin kawo masa abinci.
Ramadan kuwa tashi yayi yabude fridge din dakin yadauko masa fresh milk, yazuba masa acup yabashi, ahankali ya Kar6a yasha yar kadan, sannan yabashi sauran ya ajiye.

Idonsa ya Lumshe, yafara tunanin irin abinda yafaru tsakaninsa da munirat dazu, Ramadan ya kalleshi yace"yakamata katashi kayi sallah"

Babu musu yatashi yashige toilet, saida ya watsa ruwa a gurguje, sannan yafuto jikinsa daure da towel, wardrobe Ramadan yabude yadauko masa kayan sakawa, yabashi tareda fadin "in fadama gaskiya?wallahi bazan iya baka auren qanwata ba, saboda na tabbatar adaren farko saita ga likita"

Harararsa yayi, tareda karban kayan yasaka, sannan yace"idan baka Bani ba, ai gashinan Abokina yabani"

Yana fadin haka yatada sallah, saida ya idar sannan ya Ramadan yace"abokina a koda yaushe kaime sa'ah ne,kanada babbar mace, me Hankali, ilmin boko, wayewa,tareda budar ido wato munirat, sannan gashi yanzu zaka auri yar qaramar yarinya, wadda komai ma saika Koya mata, batada wayewa, batada budar ido,akwai kyan diri, uwa uba meson ka tsakani da Allah wadda ba dukiyar ka tagani ta nuna tana yinka ba"

Shahaab daya zauna agado ya zubawa Ramadan ido yana jin bayanansa, yasaki ajiyar zuciya yace"hakane Kam, Nima na lura Aisha batasan komai ba, saboda kaga yanayin society din data tashi,saide Yaya zanyi? Allah yariga yasakamin soyaiyar ta acikin zuciyata, dole nine zan dinga Koya mata komai harta saba wataran ta dinga yin wasu abubuwan da kanta, Amma nikaina shaida ne, batasan komai ba yarinyar hatta a 6angaren soyaiya ma, nine nakoya mata kiss,Amma last time data min, wallahi jinayi kamar zan mutu....inda ace, tasan ire iren wadannan abubuwan, maganar Allah banajin zan dinga fita wani waje Bayan aurenmu"

Ramadan yazaro Idonsa yace"kiss?yaushe hakan tafaru?"

Kallan mamaki yamasa yace"hakan baya faruwa a tsakanin masoya ne? Kokuma bayan shi nacema namata wani abu ne?"

Cikin tsokana Ramadan yace"wannan abu aduhu, a baqar leda, waya Sani?"

Girgiza Kansa yayi, Adede lokacin mama takawo masa abinci ta zauna sannan tafara bashi, babu laifi yaci daidai gwargwado, Ramadan yabashi magani yasha, sannan mama tace"meyafaru ne akacemin munirat tafuto tana kuka?"

Ransa ne ya6aci, lokaci daya yayi kicin-kicin da fuskarsa yace"mun samu Sa6ani ne mama,Allah yasa baki hanata tafiya ba"

Mama tace"aini batazo ma inda nake ba,yanzu saboda kun samu Sa6ani da'ita saita tafi batareda tasanar Dani ba?nasan bazai wuce akan batun aurenka neba, inbanda munirat ai itace babba, Sai abunda tace zakayi, saboda kamar ita aka yiwa abu marar dadi, Amma idan ta kwantar da Hankalin ta Aisha ai kamar yarta take,Ina Rasa control dina wani lokacin Ina fada mata maganganu saboda nariga nasan cewa Dama can kudinka yasa ta aure ka, to Amma Yaya zanyi? Tunda kana sonta, dole haka zan haqura ai, bansan meyasa bata dauka ta a matsayin mahaifiya ba"

Ahankali yace"hakane Kam, inda ace tana daukar ki kamar momynta, da bazata turo mutane tace suzo su kashe ki ba"

Spoon din hannunta ne yazame yafadi qasa, gaban Ramadan yafadi, dagashi har mama, hada baki suke suna fadin "kisa Kuma?"

Nan take ya basu labarin komai,mama da hawaye yake kwaranya a'idonta tace"amma har saki biyu Shahaab? Meyasa bazaka nemi shawara ta ba?"

Cikin 6acin rai yace" mama duk Wanda yanemi yayi shamaki tsakanin ni dake wannan kadanne daga cikin sakamakon dazai Kar6a ahannunsa, bazan iya hadaki da kowacce mace ba,naji haushin kaina daya kasance Bana Dukan mata,Amma dayau sainayi mata duka kafin tabar gidannan"

Dukan sa mama tayi akan murdaddan dantsan hannunsa, cikin sauri yasaki qara, cikeda shagwa6a yace"mama akwai zafi fa"

Hawayen idonta ta share sannan ta dora kanta akan kafadarsa ta rungume shi sosai, Ramadan ma qwallah ya goge yace"gaskiya hukuncin daka yanke Shine daidai, duk mutumin da bazai so mahaifiyar ka ba, babu amfanin zama dashi, ko a addini mahaifiya aka fara ambata kafin mahaifi,bazai iyu mu hada soyaiyar iyayenmu mata data kowa ba,uwa uwa ce ako'ina"

Mama ta Kalle su tace"Allah yayi muku Albarka "daga Nan ta dauke sauran abincin tafice daga d'akin

Tana fita Ramadan yace"wannan dalilin ne yasa nake sake nunama muhimmancin Aisha awajanka, yarinyar tana sonka sosai, Kuma kun dace yanda baka zato, shiyasa tun farko nake cusa ma ra'ayin ta"

Shahaab yace"gashinan Kuma kacusota dayawa tana nema ta zautar Dani ba"

Kafin Ramadan yabashi amsa mama takawo masa magani acikin wani cup guda biyu, daya maganin Sanyi ne, dayan Kuma na tsumi ne, zama tayi ta ajiye maganin tsumin sannan tabashi na sanyin tace"gashi, Aysha Sulaiman ce tabani shi indinga baka kana Sha, maganin infection ne"

Babu musu ya Kar6a yashanye, yana bata cup din, tabashi dayan maganin tsumin tace"shanye wannan dinma"

Jiyayi kamar yayi ihu, tana ganin yanayin fuskarsa ya sauya tasan zai iya yimata gardama,baikuma Isa yarusa mata aikintaba,danhaka cikin sauri takai cup din bakinsa, bata dauke ba saida taga yashanye, sannan tamiqe tsaye tace"to saida safenku, zanje inkira qawata, tunda muka sauka ban kirasu ba"

Ramadan yace"to mama saida safe"

Shahaab kuwa runtse Idonsa yayi, Ramadan ya kalleshi yace"abokina Yaya ne?"

Cikin damuwa yace" mama batasan halin danake ciki ba take Bani wannan abun ne?"

Ramadan yace"maganin infection nefa,ko bakada shi ai baida matsala maganin"

Cikin sauri yace"Shima dayan data qara Bani duk na sanyin ne?saida nace su saka sati biyu ayi-ayi ayi abunnan, Amma suka daddage itada qawarta, Wai sati uku, Kuma yanzu gashinan tana Bani wannan abun, Yaya takeso nayi ne?"

Dariya Ramadan yasaki yace"to yanzu kuka zakayi?ai itama mama gata takewa Aishan,tsuma mata Kai take yi"

Fillo yadauka yadokawa Ramadan ajikinsa, haka sukaci gaba da zance, har suka gangaro kan batun yanda shirye shiryen auren zai kasance


(keda Allah idan kika karanta batare da kin biyaba)


******


Saida tayi wanka ta shirya, tasa ma'aikata su shirya abinci sukai part din Shahaab saboda Ramadan, sannan tashige daki takira wayar su Hajja, saida ta gaisa da kowa sukayi mata bangajiya, sannan sukaci gaba da magana da Hajja,yawanci zancen nasu duk akan labarin Yan makarantar sune, daga Nan Kuma suka koma kan batun auren Aisha, saida dare yayi sosai sannan sukai sallama, Hajja ta kalli Aisha taga idonta a rufe, a fili tace"mesunan qawa har anyi bacci"

Aisha kuwa tana jinta tayi shiru, ba bacci take ba, kewarsa take, tana so Yakirata, tana so taji muryarsa ko kadanne, bataso Hajja tasan idonta biyu, Dan tsaf zata Dauko mata wata hirar ta hanata tunanin sa.=�H�=�J�

Acan Abuja kuwa kallo Ramadan ya kunna musu, saida suka gama ganin labarai sannan Ramadan yaci abincin da aka kawo,shirin kwanciya sukayi, yakashe musu wutar Dakin sannan yakoma kan gadon ya kwanta, yana kwanciya matarsa takira wayarsa, yad'auki wayar yafita daga d'akin yana sanar da'ita zai kwana tareda Mahmud ne, baijin dadi.

Shiru shiru Shahaab yaji Ramadan bai dawo Dakin ba, dama tunanin ta yayi masa yawa, cikin sauri yad'auki wayarsa yakira layin Hajja, Alokacin Hajja tafara bacci taji waya tana ringing dalilin haka ne yasa tafarka, Aisha kuwa cikin sauri tad'auki wayar, tanaso taga waye yake kira a wannan lokacin kusan karfe daya saura na dare?
Tana ganin number sa, tasaki wata irin ajiyar zuciya, cikin sauri ta dauki wayar

"kinyi bacci?" shine abinda yafara fada mata

Saida tasake yin qasa da muryarta yanda Hajja bazata jita ba, sannan tace"idan wayar tana hannun Hajja fa?"

Yace"ainasan tayi bacci"

Saida tasake yin qasa da murya sannan tace"yanzu suka gama waya da mama fa"

Mamaki ya kamashi, ya dauke wayar daga kunnan sa ya kalli lokaci, sannan yamaida ta yace"su basa gajiya da zance ne?shine tasa mama tazo ta dinga dura min wasu irin magunguna, Kuma idan nace ayi aurenmu da wuri tace Bahaka ba"

Cikin sauri Aisha tace"itama mamanka cede"
Murmushi yayi yace"ni kaka nake yi da'ita, tunda tabani auren jikar ta,Nima nabar dan, nakoma jikanta kamar ke,fadamin meyasa bakiyi bacci ba? Tunani na kike? "

Ahankali tace"Um.."

Ajiyar

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment