Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saita rufawa kanta asiri tayi zamanta adaki, bata fatan ace ma ta ganshi, menene ma hadinta dawani danta bare har zaizo tazo tasasu agaba?

Haka ta dinga tunani, daga qarshe Takoma tunanin gida, gashi de tana cikin gida har gida, Amma Kuma tana tunanin su Hajja, Sai yau taji taqaicin rashin waya, da yanzu kiransu zatayi taji muryar su, ko Hajja tayi kunun Aya yau? Haka ta dinga tunani har bacci ya dauketa Bayan tayi sallolin dake kanta

Washe gari tunda tayi sallar asuba bata koma bacci ba, kitchen tashiga tana taya masu aikin yin wasu ayyukan, anan suka Dan saba da'ita ganin tanada budadden baki har suka sake wayar mata da kai akan yanayin gidan,yanda tasake dasu sosai ta basu mamaki, saboda Hajiya Mama bata ta6a yin baquwa wadda tashiga ransu kamar Aisha ba, gashi ita ba yar aiki ba Amma tashiga cikin su kamar wasu yan'uwanta, basu gama aikin ba Sai karfe bakwai da rabi, sukam kowa daki Takoma, tunda sungama aikinsu, saide idan mutanan gidan sungama bacci sun futo shine zasuzo su zuba musu, Aisha Kam bata koma ba, afalo ta zauna tana kallo har mama tafuto, less ne ajikinta wuyanta da hannunta d'aukeda sarqa da zoben gold,kana ganin ta kasan kudi, hutu, Dajin dadi ya zauna mata, cikin sauri Aisha ta gaishe ta, sannan tace "akawo miki abincin yanzu?"

Mama tayi murmushi tace"nace kisaki jikinki tsohuwa, kidinga yin abunda yadace kawai basai kin tambayeni ba, saide idan kinyi idan Bana buqata zan sanar miki"

Aisha tayi murmushi jin sunan da mama ta kirata tace "to insha Allah" sannan tanufi dinning tafara zuba mata abincin.

Abincin takawo mata, maimakon ta zauna aqasan kujera, saita zauna akan kujera kusa da mama(=�3�>�-�)

Mama ta kalleta cikin mamaki, saboda ba'a ta6a yimata hakan ba, koda yaushe masu mutanan gidan girmamata suke, kafin tagama tunanin Aisha ta debo abincin a spoon tace "mama bude bakinki dakaina zan baki abincin"

Wani irin shock ne yakama mama,lokaci daya Mahmud yafado mata Arai, inda ace tayi masa aure da wuri, da yanzu tanada Jika kamar wannan yarinyar, inama yanda halayen yarinyar yake, haka halin munirat yake? Da menene zaisa ta dinga Yiwa Shahaab maganar qarin aure? Murmushi tayi tace "Aisha Anya kuwa baki ta6a aiki awani gida ba kafin Nan?"

Cikin sauri tace"a a mama,banta6a yiba,inajin ki araina ne kamar kakata Hajja, kiyi hakuri Bana daukar ki a matsayin uwar gidana, Ina daukar ki ne a matsayin kakata Hajja, inda Hajja ce take matsayin ki, Tozan iya goyata ma, saboda Hajja tana sona"

Murmushi mama tayi, tarasa meyasa yarinyar ta kwanta mata fiyeda sauran Wanda take dauka aiki, ganin ta take kamar jikar ta, wani lokacin Kuma Sai halaiyarta ta dinga birgeta taji Dama ace Mahmud da'ita yafara haduwa, babu musu ta bude mata bakin, ahankali cikin kulawa Aisha tafara bata abincin, harta kammala munirat bata shigo part din na mama ba, dama Kuma Aisha batasan cewa akwai Wanda suke zuwa cin abinci part din maman ba


******

Tun karfe takwas munirat ta shirya cikin dinkin shadda Wanda aka kashewa kudi wajan dinki, mayafi ta yafa, tad'auki hand bag dinta tareda takardun filayen mama Wanda ta dauke batareda Shahaab din yasani ba, fita tayi tasa driver yakaita wajan wasu mutane, yana daga cikin mota ita kadai ce tafita, sun dade a tsaye da mutanan sannan ta basu takardun filayen, aka dauki kudi acikin wata jaka aka bata, kudin ta karba Takoma cikin mota, daga Nan banki suka wuce tabayar a saka mata kudin acikin asusun ta, bata dawo gidaba Sai wajan karfe goma Sha daya, Kai tsaye Part din mama ta wuce.

Adede lokacin Aisha tana qasan kujera, mama tana zaune a kujera tana kallo, Aisha Kuma tana matsa mata qafafunta, hira suke kad'an kad'an mama tana sake yabawa da yarinyar acikin ranta, kodan irin sunanta Dana qawarta Aysha Sulaiman Bompai gareta?
Ahankali tace"Takwara ta akwai kayan danayi miki order na sakawa, Naga bakizo da Kaya ba, idan aka kawo miki saiki dinga amfani dashi, Amma ai bazai iyu ace yanmata babu kwalliya ba"

Aisha tayi murmushi kafin tayi magana munirat tayi sallama falon, daga Aisha har mama, kallon su suka Kai gareta, Aisha tana ganin ta haka kawai taji matar bata mataba, saide Kuma kallo daya zaka mata kasan cewa yar Gayu ce, tanaji da ado da wayewa ta Yan birni, qasa tayi da kanta, munirat ta qaraso kusa da mama ta zauna, tace "barka da safiya mama, nafita unguwa ne bansamu Dama nazo munyi break ba"

Babu yabo babu fallasa Aisha tace mata "Ina kwana"

"lafiya," munirat ta amsa a daqile

Mama tace "Munirat munyi baquwa Baku haduba jiya, daga Jigawa State take, sunanta AISHA,nafada miki ne saboda ki kiyaye fadar irin sunan surukar ki,ga abinci can a dinning Zaki iya tashi"

Munirat tayi shiru kanta aqasa, idan ta fahimci mama tana nufin karta kira sunan wannan bafulatanar yarinyar kenan, saboda irin sunanta gareta, to yanzu sotake ta kirata da ANTY AISHA kokuma MOMY AISHA? cikin danne fishin ta tamiqe tana cewa "wallahi na qoshi mama, saide ko anjima inyi lunch, a hanya Naga Goro har zan siyo miki Kuma wani abu ya dauki Hankali na bansiyo miki ba"

Mama batace da'ita uffan ba, Aisha tayi tunanin zata tanka, Sai taji maman tayi shiru, anan tasake tabbatar wa mama akwai cikakken iko, Bayan munirat tafita Aisha tayi ajiyar zuciya tace "idan anyi niyar siyo miki ai saide kawai kigani mama"(=�2�)

Mama tace "Aisha kenan,Allah yayi miki Albarka, Sai hakuri al'amarin, wannan itace surukata matar Dana MAHMUD WAKILI"

Haka Nan Aisha taji gabanta yafadi, Amma bata kawo komai a ranta ba, saita kama addu'ah cikin zuciyar ta


******


Washagari jirgin Abba da jabir yatashi, Abba yatafi Saudia, jabir Kuma yawuce Australia, tunda aka fara musu hidimar tafiyar babu wata hanya da'aka Bari har su kasan ga sahihin mutumin daya dauki nauyin tafiyar tasu,tundaga ranar da sukaje dutse Abba Kam Yama manta da batun su, saboda kawai ganin abun yake kamar wasa, Amma haka mutanan suka sake dawowa tareda Mai Garin Garin, aka gama musu komai har suka tafi.

gidansu Hajja shiru babu wani dadi saboda Abba baya Nan, jabir baya Nan, Aisha bata Nan, daga Ummah Sai Hajja, kullum jummai tana zuwa wajan Hajja domin Sudan zanta, Amma Hajja bata kulata, haushinta takeji saboda da'ita mamuda yahada Kai suka tura mesunan qawarta Abuja.

Tunda Abba yatafi kullum saiya kira su ta wayar Hajja sun gaisa, har yau daya cika kwana takwas, yana shirin cika sati biyu sannan ya dawo gida.

A bangaren Aisha kuwa yau tacika kwana goma a gidan, batada damuwar komai, tana zaune lafiya a gidan, Kuma har zuwa yanzun bata ta6a saka Mahmud Wakili a idonta ba, damuwar ta de guda daya ce rashin jin muryar Hajja dasu Ummah, saikuma tunanin Shahaab, tana tunanin ranar dazaije gidansu bai sameta ba.

Yauma munirat da mama suna zaune afalo, munirat da wayarta a hannunta tana tura kudade tana order kayaiyaki da kudin filin mama data siyar (=�F�<���
@&�)

Mama tana mata kallon gefen ido tana mamakin shegen danne dannen waya irinna munirat, Aisha ce tafuto falon tayi kyau sosai cikin doguwar Riga irin kayan da mama ta siya mata, cikin ladabi tace "mama nagama gyara miki Dakin, yanzu saukowa qasa zakiyi, kokuma ki kwanta in tsefe miki kanki, kitsonki ya tsufa mama"

Mama tayi murmushi tace "Bani abinci de infara ci tukunna, nagode da qoqari, Allah yasaka miki da alkhairi"

Murmushi tayi ta nufi dinning tazubo mata abincin, sannan tadawo ta zauna tafara bata abincin abaki, munirat ta Kalle su, wani irin baqin ciki ya to kare mata maqoshi, ta maida Hankalinta kan wayar ta.

saida tagama bata abincin sannan tafara tsefe mata kanta, cikin kulawa tace "mama idan kinajin zafi fa kifadamin saina dinga yi miki ahankali"

Mama tayi murmushi tace "babu zafi Aisha, inda nake zuwa kitso ma suma kamar hakan suke min, Allah yayi miki Albarka"

Cikin jin dadi tace "Amin mama"

Munirat ta kalli Aisha, taga Sai wani qara yin fresh take, cikin kwanakin datayi a gidan yarinyar gaba daya sauya wa take kamar wanda ake mata wankan inji, haushinta takeji musanman wannan dogon gashin Nata dayake tsokale mata ido, kwata kwata yarinyar bata kwanta mata ba, tacika rawar Kai da fi'ili dakuma cusa Kai, jide yanda ta shige wa mama daga baqunta kamar wanda suka shekara tare.
Tashi munirat tayi tatafi Part dinta, mama ta kalleta tace"munirat bazata sauya ba, yanzu kiduba kigani ko sallama batamin ba tatafi, tun lokacin da Mahmud zai aure ta naqi yarda, to kinsan sha'anin Dan yau, bazan iya hanashi ba saboda shi kadai Allah yabani, dole in so abinda yake so, dayake sonta yake kamar ransa, saina bashi Dama ya aure ta, tunda akai auren nide banji wani dadi ba, Amma shi Ahaka yake son abarsa"

Aisha cikin ranta tace"Allah yaqara, ai Shima dannaki bawani mutunci ne dashi ba, Gara daya auri daidai dashi, nida zan ganshi ba Dana tambayeshi Ina Yaronsa SHAHAAB? (tofa=��)
Amma a fili saitace "kiyi hakuri mama, watarana Sai labari"

Mama tayi shiru batace komai ba, domin kuwa inda Sabo yaci ace tasaba da halin munirat.

(idan kinsan baki biya kudin littafin nanba kika karanta to nabarki da futowar rana da faduwarta, harga Allah banyafe ba)


Yau satinta biyu a gidan, Kuma yau Abbanta ya dawo daga Saudia, saide ita Kam batasani ba, har Zuwa wannan lokacin batayi waya da kowa ba, Amma takai maqura wajan kewar Yan gidansu, yau jitake kamar ta qwaci waya takira Hajja, batason kar6ar wayar mama saboda kartace mata tana mata shishshigi, haka ta daure tafita wajan mama domin yimata aikin data saba.

Yau mama tashi tayi da son ganin qawarta Aysha Sulaiman Bompai, tayi nisa a tunani, tana tunanin irin rayuwar da sukai itada Aysha Sulaiman, yanzu sun kusa shekara saba'in, Amma da alama basuda Rabon haduwa da juna, shi Shahaab yayi mata alqawarin yin aikin gidan marayun ta akan lokaci, to yatafi Australia har yanzu shiru bai dawo ba, waya Sani ma ko tunda yatafi baya yiwa masu aikin waya?yakamata ya dawo haka, domin ayi sauri a qarasa a saka marayun aciki.

Tana wannan tunanin batasan har Aisha tazo wajan ta ba, tasan yanzu lokacin matsa mata qafafu yayi, danhaka ta zauna tafara matsa mata qafafun

Cikin damuwa mama tafara Girgiza qafafunta, ga damuwar rashin qawarta, ga Kuma shi Shahaab yatafi yayi zamansa, ta dade Rabon Dayayi tafiya yad'auki tsawon lokaci haka batareda sun kasance tare ba, taqi jinin ganinsa nesa da'ita, Aisha ta jijjiga kanta, ganin tana matsa mata qafafun Amma ita Sai jijjiga qafa take, ahankali tace "mama ki tsaya inyi miki tausar, kada qafafunki su kumbura,"

Ciki-ciki ta amsa mata dacewa"Yaya kike so inyi ne? Haka zan tsaida qafata niba itace ba, ba katako ba?tashi kije idan kingaji"

Cikin fishi Aisha ta kalleta tace"babu inda zanje... Rikitacciyar tsohuwa kawai, Ana kokarin nema miki lafiya Amma bakya Gani,"(=�F�<���
@&�=�F�<���
@&�=�3�=�2�)

Mama tayi shiruuu tana kallon Aisha da mamaki, da alama da gaske de yarinyar Nan daukar ta take a matsayin kakarta kamar yanda tafada.

Aisha tasake kallon mama cikin fishi tace"sai kallo na kike kamar baki sanni ba, bazan Dena matsa miki qafafun ba tunda lafiyarki ake nema"

Tana fadar haka tad'auki qafar Tata ta dora akan cinyarta, sannan taci gaba da matsa mata qafafun









(tofa..... >��=��, Hali zanen dutse, me Hali...... )


Mutara zuwa yamma insha Allah =�O�<���


Littafin Shahaab na kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta,idan baki biyaba kika karanta wallahi banyafe ba.


0164549488
Amina muhammad
GTbank

Kokuma katin MTN ta wannan number 08033300034







Mrs Usman ce
'<���


Page 22





Banda kallo babu abinda mama take wa Aisha, Wai yau itace wata yar yarinya take fada mata wadannan maganganun, Kuma abun mamakin da d'aure Kai ko kadan bataga laifin yarinyar ba, ta lura tsakani da Allah yarinyar take zaune da'ita, tunda duk abinda tafada mata made akan lafiyar ta take fadan, Dan qaramin tsaki tasaki, Aisha ta kalleta, ahankali ta ajiye mata qafar ta, sannan ta wuce Dakin maman tad'auko wani Mai datake mata amfani dashi, tadawo falon ta zauna tasake daukan qafar Tata ta dora akan cinyarta ta dinga shafa mata man, saida tagama sannan ta ajiye mata qafar ta ko sallama bata mata ba ta wuce dakinta

Mama ta bita da kallo harta shige daki, wayarta ta d'auka takira Shahaab, yana dauka cikin damuwa tace "yaushe zaka dawo?"

Murmushi yasaki dimple dinsa suka futo, shi Kansa yanaso yadawo kodan Aishan sa, yace "mama nakusa dawowa kiyi hakuri, Ina fatan de babu wata matsala ko?"

"yakamata kadawo saboda aikin gidan marayun Nan"

"mama komai yana tafiya daidai, duk wasu ayyukan Dana Bari Ramadan yana kula da komai, Kuma yana sanar Dani halin da ake ciki, kiyi hakuri nakusa dawowa kinji?"

Tace "yaushe?"

"nanda ten day's insha Allah"

"kwana goma ai yayi yawa Shahaab, please kadawo dawuri"

Yace "to mama insha Allah, ki kula da kanki" dif yakashe wayarsa.

******

Ruwan zam-zam ne a gabanta cikin wata babbar gora tana qulla shi a leda, Jikan iya jummai ne a tsugunne a gabanta, saida tagama qullawa sannan ta kalli Ummah datake kakkarya bagaruwa tace "kawo idan kingama"

Ummah tabata, Kar6a tayi ta kalli Yaron tace "kanajina ko ididi, kakai duk gidajen Dana lissafa Maka, kace inji Hajja A'i tsarabar mamuda ce ta Saudia , kaji nafada Maka karka Bawa jummai ruwan zam-zam dina, har yanzu a hanci na take, kadan nake jira in fato ta" (=��)

Ummah tace "Hajja da kinyi hakuri anbata Shima baisan zaije Saudian Nan bafa, Kuma mu aiki jikanta Amma muhanata ko ladan ganin ido?"

Cikin masifa hajja ta kalli Ummah tace "to Hadiza fadamin abinda yakamata inyi, waini tare kika ganni da jummai ne kokuma kece kika hadani da'ita? Nan tazo har gida ta samfe min jikata tayi gaba da'ita, har yanzu ko d'uriyar yarinyar banqara jiba, ai wallahi tsakanina da jummai saide kallo, da Hankali na ba zanje har gida in dauki jikar ta in kaita uwa duniya aikatau ba, ci muka Rasa ko Sha?"

Ummah tace"kiyi hakuri"

Hajja tace "haka de"


Yaron ne yad'auki robar yafita, Hajja tatashi tafara tace niqan kunun ayarta da'aka kawo mata yanzu


******

Kamar kullum Yauma da safe tatashi tafada kitchen kamar yanda tasaba, suna cikin aiki ta kalli daya daga cikin masu aikin tace "mansura Dan Allah Aron wayarki Zaki Bani inaso nakira mamanah"

Mansura tace "wayata tana d'akin mu, jeki dauka"

Cikin murna tatafi Dakin,wayar tana caji, ta cireta takira Hajja, a lokacin tashin su kenan daga bacci Ummah tana kokarin dora musu abincin Kari, Abba yana Gefe yana jin redio yayi fresh dashi har wata yar qiba yaqara, Hajja tanajin qaran wayar ta, ta d'auka tareda cewa "wannan kira da sanyin safiya kode mutuwa akayi?"

Wani irin farinciki ne yakama Aisha jin muryar Hajja, muryarta ta bude tayi magana cikin sigar tsoratar wa tace "Aljana manuba ceeee"

Hajja tasaki dariya tace "tazo takamamu nida ke, yar bantan uba"

Dariya Aisha tasaki tace "waisaida kika ganeni? Ke Hajja"

Cikin farinciki Hajja tace "haba mesunan qawa, ko a mafarki kika sauya murya kika min magana ai dole nagane,mesunan qawa shikkenan jummai ta rabani dake, mamuda yashiga tsakanin mu, kina samun abinci de kinaci Kina qoshi ko?"

Cikin sauri tace "Hajja inacin duk abinda nakeso, bakiga gidan ba, qaaaaato, ga abun dadi sunaci kullum wani abun ma bansan sunan saba, Kuma ko Hajja har bread ake rabawa duk juma'ah baki gansu ba manya manya fulawa zirrr"

Hajja ta zaro ido tace "kice daqyar kike iya daukan guda daya?"

Zaro ido tayi tace "Biredin?"

Hajja tace "emana, naji kince fulawa zirrr..." haushi ne yakama Aisha tace "Kai Hajja Dan Allah, kinfara ko?"

Cikin sauri tace "Allah yabaki hakuri me sunan qawa, kullum inata kewarki, inji de matar gidan tabaki madubi babba?"=��=��

Fari tayi da idonta, sarai tasan Inda maganar Hajja ta dosa, murmushi tasaki tace "akwai,kuma kullum saina kalla abuna, tunda banaki bane nawane"

Hajja tasa dariya tace "toga Hadiza, Amma bazan baki mamuda ba, har yanzu a wuyana suke shida jummai"

Murmushi tayi tace "tobata"

Ummah ta kar6i wayar suka gaisa, tayi qasa da murya yanda su Hajja bazasu jitaba tace "ki kama kanki de aduk inda kika tsinci kanki, banda shiririta, banda kula maza, ki tsare mutuncin ki, Kuma bance kiyi musu rashin kunyar Nan Taki ba"

Cikin sanyin jiki tace "insha Allah Ummah"

Hajja ce ta qwace wayar tace "zan ajiye number, idan inaso inyi magana dake saina dinga kiranki tanan ko?"

Cikin farinciki tace "to Hajja, Sai anjima"

Bayanta ta jinginar a jikin gadon Dakin tatafi tunani, rayuwa kenan, yau itace take rayuwa awani waje daban, su Hajja suna wani waje daban, Allah yaso tama tariqe number su.

Kitchen din Takoma suka qarasa aikin, bata koma dakinta ba afalo ta zauna ta jira mama tafuto, daga Nan tafara yimata aikin data saba, saide fuskarta adan daure take, ta lura gigin tsufa ne yake damun mama kamar de Hajja idan ta rikice musu wata Rana.

Haka taci gaba da Kula da mama, bata fasa kyautata mata ba, koda tayi niyyar yimata tsiya idan ta tuna nasihar da Ummah ta yi mata saita fasa, mama tanajin dadin yanda Aisha take bata kulawa, yarinya qarama da'ita Amma tasan yanda take kula daduk wasu al'amuranta, da alama Dama can tana aiki a gidansu, ta lura kwata kwata yarinyar tadena sakin jiki da'ita kodan saboda Dan Sa6anin dasuka samu kwanaki ne? Toyaya zatayi? Tunanin qawarta ne ya janyo hakan, duk lokacin data tuna Aysha Sulaiman Bompai tanajin ranta yana 6aci, Gani take kawai mutuwa zatayi batare data ganta ba, burinsu na hada 'ya'yansu Aure, bazai tabbata ba, duk lokacin datake cikin wannan yanayin shi Kansa Shahaab dinnata uzuri yake mata, saboda ta dinga 6acin rai kenan.

Yau satin Aisha hudu daidai a gidan,Kuma yau ne Shahaab yayi wata daya da kwana biyar da tafiyar sa,yau Aisha tana matsa wa mama qafafu mama tace "Aisha yau yakamatakuje ki bude account kema,Amma Naga Sai fishi kike Dani har yanzu"

Cikin ladabi tace "kiyi hakuri mama, Bana fishi dake, Amma maganar kudin Nan kibar ta"

Mama tayi shiru tana kallon ta, tayaya zata bar yarinya tana mata aiki babu ko sisi Aida shiga haqqi, dole zasuje su bude Adinga saka mata kudinta, taga har yanzu yarinyar tana fishi da'ita, duk da bata futo fili tafada mata gaskiya ba, bazai iyu tafada mata dalilin dayasa ta 6ata mata rai rannan ba, abinda ya shafi tsakaninta da Aysha Sulaiman Bompai wannan tsakanin sune, Bai shafi masu aikinta ba, tana wannan tunanin taji Aisha tace "mama kihuta lafiya"

Daga Nan tatafi daki, saboda wani irin zazza6i datake ji tunda safe,ga qirjinta ciwo yake har cikin boobs dinta Wanda takejin wani irin abu aciki me zafi, haka bayanta ma yana mata ciwo kadan kadan



(Allah karabu da rashin sanin ciwon kudin mu =��=��=��in samu kudi na daqyar insai abu, Kuma in zauna Ina fitar dashi saboda shirme, duk wadda tasan bata biyani haqqi naba nabar ta da Allah, bazan taba yafe mata ba)

******

Yau cinema akwai wasa, Ball za'a buga me zafi, tun rana Hajja tagama harhada komai na kunun Aya, da yamma ta zauna zata Fata d'urawa acikin jarkoki, Kallan uban kunun ayar dake gabanta tayi, ta juya ta kalli Abba dayake shirin fita qofar gida tace "mamuda ai bakaga ta fita ba, zuwa zakayi ka zauna ka duramin wannan kunun ayar, tunda ka sallami Wadda take min"

Abba baiyi musu ba yadawo ya tsugunna yafara d'ura mata kunun ayar, koda wasa ba zaiyi kuskuren yin maganar Aisha da'ita ba yanzu, saboda yanzu saita fara yimasa bori tace lalle lalle Sai yaje yadawo mata da'ita

Hajja tasaki tsaki tace "tunda Wanda nake Tarawa kudin registration din yatafi makarantar ai sai infara tattara kudina inje dakaina in dawo da Mai sunan qawa, bazai iyu duk lokacin dazanyi durin kunun Aya sainaje majalissa-majalissa Ina nemanka ba"=��=��

Ummah ta ajiye tsintsiyar hannunta tawanke hannayenta, sannan tazo ta zauna itama sukaci gaba da dura mata, saida suka gama tsaf... Suka saka mata shi cikin babbar kula sannan Abba yamiqe zai fita, Hajja tace"Ai baka gama ba, jeka nemomin me mashin"=��

Bai iya cewa komai ba Sai "to Hajja"

Sannan yafice daga gidan cikin sauri.


******

Kallon Yaron dake gabansa yayi, yau Yacika sati na uku kenan a qasar Amma yaro harya fara sauya wa, fatarsa tasake fresh Sai wani irin haske yake yi, jaridar dake hannunsa ya ajiye yace "jabir ka tsaya ka nutsu kayi karatu kaji? Kaga wannan karatun shine gatanka, idan kayi karatu iyayenka ma zasuji dadi su sakama Albarka, karka sa tunanin gida a ranka, kasa karatu agaba kayi abinda yakawo ka kakoma gida lafiya"

Cikin ladabi jabir yace "to Alhaji nagode sosai, Allah yasaka da alkhairi, abunda kayi mana Allah yabiyama da gidan aljanna"

Murmushi yayi yace "jabir aiba nine nadauki nauyin zuwanka qasar nan dakuma karatun kaba, oga nane, Shima yana tare damu acikin qasar saide ayyuka dasuka yi masa yawa yasa baisamu lokaci ya ganka ba, yanzu haka Nigeria zamu wuce, wannan wayar ma shine yace akawo ma, idan yasamu lokaci zai kira layinka "

Cikin mamaki jabir ya kalli mutumin da tsananin alhini, tunda suka fara hidimar tafiyar su shida Abba wannan mutumin yake Gani, yayi tunanin shine yad'auki nauyin karatun nasa, ashe bashi bane, to waye wannan?

Murmushi mutumin yayi kamar yasan abinda yake cikin zuciyar jabir yace "nasan kanaso kasan waye yakai Abban ka Saudia,sannan kaima yakawo ka qasar nan karatu, to zaka sanshi very soon, ya tabbatar min idan yasamu lokaci zai kiraka, idan ya kiraka saika yi masa kowanne irin tambayoyi"

Jabir yace "to shikkenan Alhaji nagode, Allah yakaiku lafiya, Allah yasadamu da alkhairi"

Mutumin ya amsa masa da "Amin" sannan sukai sallama yatafi gidan da'aka kama masa, shikuma mutumin yanufi Airport.

******

Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja.

Tsaye yake yana jiran motoci su qaraso daga gida,kasancewar babu wanda yasan da zuwansa, saida ya sauka sannan ya kirasu, Sanye yake cikin Riga da wando, baqin wando, da Riga Ruwan toka me ratsin baqi, Sai glass din Idonsa baqi, dakuma agogo baqi,Wanda yasake haska farar fatarsa, Sai takalmin qafarsa kambos fari, gashin kannan nasa yasha gyara Sai sheqi yake,Bai 6alle botir din gaban rigar tasa duka ba, yabar guda uku a bude, hakan ne yasa ake iya hango lallausan gashin daya kwanta akan faffad'an qirjinsa, hannuwansa zube cikin aljihun wandon sa, Dan qaramin tsaki yasaki Bayan yasake kallon agogon hannunsa, yadubi Alhaji Ibrahim Wanda suka dawo tare yace"Alhaji zaka iya tafiya, gasunan sun qaraso"

Alhaji Ibrahim yabashi wani Kati tareda cewa"to oga, ga wannan katin, number wannan Yaron ne jabir"

Katin ya Kar6a, tareda turashi cikin aljihunsa yayi gaba batareda yasake cewa komai ba, wajan da aka Parker motocinsa ya qarasa, cikin sauri aka bude masa motar yashiga, sannan suka dauki hanyar gida, Kansa ya jinginar a jikin kujera yana jin yanda bugun zuciyarsa yake sauya wa Zuwa faduwar gaba matsananciya.

Bai dauki hakan a matsayin komai ba, tunda yasan mama tana lafiya, munirat ma haka, saide Aisha ce bai saniba, itama Kuma so yake ya qarasa gida yabude wayarsa datake kiransa da'ita Yakirata yaji muryarta ko zai samu ya'iya runtsa wa a Daren yau din.(=��)

Suna qarasa wa gidan Kai tsaye yawuce part din mama, tana zaune afalon ita kadai, abinci ne a gabanta tana kokarin hadawa, cikin jin dadi dakuma shagwa6ar daya saba ya rungume ta tabaya yace"mamaaaa.....I miss you"

Mama da batasan da zuwansa ba cikin farinciki da jin dadi tajuyo tace"mahmud?''

Murmushi yake saki kamar bashi ba dayake daure fuska kowanne lokaci, kwanciya yayi akan kujerar tareda dora Kansa akan cinyarta yace"mama nayi kewarki dayawa, nayi kewar cinyarki "

Dogon hancinsa taja, cikin farinciki tace"ai gashinan kadawo, Bari inzuba Maka abinci Dama yanzu nake shirin cin abincin Nima"

Cikin sauri yatashi zaune yana fuskantarta, cikin 6acin rai yace "mama bangane ba? Kece Zaki zuba abincin da kanki? Ina masu aikin suke?"

"masu aiki suna Nan Shahaab, sukam ai sungama aikinsu sabuwar yarinyar datake kula Dani wadda na dauka itace de batazo tabani ba,Kai ni rabona da'ita ma tun Daren jiya, kwata kwata yau bansata a'idona ba, fishi take Dani na babu gaira babu dalili, datage ala dole saita dinga kula Dani ta qarfi da yaji kamar likita ta, yanda kasan kudi ake biyanta idan tanamin fada akan matsa qafafun Nan nawa"

Cikin 6acin rai yace "what...?, fada Kuma? To idan qafar tana miki ciwo sosai fa?"

Ganin yanda ya rikice yasa mama Tace"A a tanada gaskiya ai,yanda take kulawar Dani yasa ma yanzu banajin ciwon qafar sosai "
Badan ya gamsu da maganar tataba yace"to waye yayi miki ayyukanki na yau kenan?"

"waye zaimin tunda d'an Dana Haifa baya Nan bare yamin?" cewar mama

Ransa ne yasake 6aci,yanzu idan me kula da mama batayi mata komai ba hakan yana nufin munirat bazata zo tadinga temaka mataba? Kenan ko Bayan ransa munirat bazata ci gaba da

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment