Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zaki dauka mana, keda gidan ubanki?"

Ganin Abba yana Nan yasa Aisha bata ce mata komai ba, kawai ajiye kular tayi, Takoma Dakin Ummah tayi Zaman ta

Ko minti uku batayi ba saiga Hajja tabiyo ta Dakin, hannunta dauke da ruwan faro Wanda Abba yasiyo mata jiya, Tasha daya, dayan Kuma tabar wa mesunan qawa=��
Bata tayi tace "ga ruwanki na jiya, na jira kizo kwana da daddare naji shiru bakizo ba, shine na ajiye miki"

Kar6ar ruwan tayi tana cika tana batsewa, Hajja tata6e baki tace "yar Albarka me sunan qawa, ga niqan Aya ta can zoki tacemin ita, sonake na durashi a jarka yanzun Nan"

Murya can ciki tace "to"

Hajja tafuto daga d'akin Takoma Nata Dakin, shiru shiru tana jiran Taga Aisha tazo tayi mata aikin data sakata Amma taji shiru, daga murya tayi tace "mesunan qawa idan bazaki Dena dauremin fuska Ki futo ki tacemin ayar nanba toki dawomin da abata daki, kar akuyarki ta kunce tazo ta shanyemin kijanyomin nayi asarar ayata"

Ummah dake zaune awaje itada Abba, tace "kifuto kiyi abinda aka sakaki mana"

Futowa tayi tana mita qasa qasa, "asara tanawa Kuma, aikuwa itace tasai asara tunda batada qanqara Kuma basu kawo wuta ba, kullum mutum yana abu daya, idan baya gindin murhu to yana wajan Tatar kunun Aya, kwana biyu da mukai fadan ma ni harna huta"

Hajja datake jiyota tana mita tace "to mesunan qawa idan baki tacemin ba waye zai tacemin? Ko mamuda zansa ya tacemin ayar?, saboda wa nake sana'ar? Saboda auren ki ne"

Aisha batace mata komai ba,haka ta tatace mata kunun ayar tsaf, takai mata shi gabanta, Hajja tabata kujera tace "sannu me sunan qawa, zauna anan to"

Zama tayi cikin shagwa6a tace "Allah Hajja nikidena min zancen aure na"

Murmushi Hajja tayi tace "to shikkenan yawuce, yanzu de shawara Zaki Bani, sonake nasiyo tinkiya ko Rago, da Dan kudin Dana Tara na ciniki, idan Allah yasa jabir yasamu gurbin karatu, Sai a siyar da'ita abiya masa kudin makaranta, idan Kuma auren ki yariga karatun nasa tashi, Sai a siyar acika ayimiki kayan daki Mai kyau, Amma ke Yaya kika Gani? "

Ummah dake zaune wajan Abba tayi murmushi duk da bata ji amsar da Aishan ta bayar ba, cikin ranta tana mamakin shaquwar Hajja da Aisha


Da yammah Hajja tasa Abba yasiyo musu kifi, da kanta tashiga kitchen din nasu tana dafawa, saboda tasan cewa me sunan qawa yau taje makaranta Kuma tagaji, Aisha datake duba jarabawar Yara kasancewar sun kusa hutu sakamakon gabatowar watan azumi, tace "Hajja me kike dafa mana ne?"

Cikin tsokana Hajja tace "Kifi ne qwaya biyu nake dafawa bawani abun kasawa a faranti bane"

Itama Aisha tace "Alhamdulillah tosaikici daya kibani daya"



******



Zaune yake akan wasu lafiyayyun kujeru masu laushi a balcony din falon Mama, Wando ne ajikinsa three quarter, da wata Riga yar qarama wadda ta kama jikinsa, kana hango yanda faffadan qirjinsa zuwa jikinsa yayi wani layi layi, dantsan hannunsa yafuto sosai, coffee ne a gabansa Amma yakasa Sha ya zubawa sojojin dake shawagi a harabar gidan ido, azahiri su yake kallo, Amma badini tunanin rashin haihuwar sane yake damunsa, yayi tunani sosai, amma yarasa mafita, maganar Babban abokinsa Ramadan Wanda yaje Italy yake shirin dawowa jibi, itace take masa yawo acikin qwaqwalwar sa, (Yakamata ka qara aure Shahaab, mutum baya cire rai da Rahmar Allah,tsawon shekaru kaji shiru daga bangaren munirat why not kasake auren wata yarinyar ka gwada kagani ko zaka dace? Wani lokacin idan ta cikin gida ta dade bata haihu ba Ana auran ta biyun idan tasamu ciki zakaga itama dayar Allah yabata idan da rabo, sannan karka kuskura ka nunawa yarinyar dazaka aura kanada kudi, tahakanne zaka samawa yayanka uwa tagari....)

Ajiyar zuciya yasaki, Sannna yafara magana cikin zuciyar sa "matarda zan aura, kowa de matarda zan aura, mama kullum maganar ta, matarda zan aura, Ramadan kullum maganar sa Matarda zan aura, tayaya zan'iya yin shigar talakawa saboda neman aure?, inde tana sona menene hadinta da kudi na? Dama a yanzu akwai yarinyar dazata iya auran wani Bayan ya nuna mata bashida kudi? Tayaya mama da Ramadan suke tunanin wata zata Iya sonsa badon abun hannunsa ba? Zata so shi koba kudi? Wacece? A'ina take? Idan yayi hakan Anya yayiwa munirat adalci kuwa?)

Mama tada Jima a tsaye tana kallon sa, duk yanda akai yana cikin damuwa, duk da tasan Dama ba magana ce ta dameshi ba, Kuma tasan cewa Shiba neman aure yake ba bare tace yana tunanin budurwa, to tunanin me zaiyi? Ta tambayi kanta

Kafadarsa ta dafa tace "kode ansamo min sabuwar suruka ne, Ana Nan Ana tunanin ta?"

Murmushi yayi, dimples dinsa suka futo duka biyun, hannunta data maida cikin sumar Kansa ta Yan asalin Nijar yad'ora nasa hannun akan Nata, ya d'ago Kansa yana Kallan ta yace "idan akwai kece mutum ta farko dazan fara sanarwa mama"





SHAHAAB littafin kudi ne, ki biya naira 300 kacal ki karanta abinki Hankali kwance kafin free page yaqare, siyan nagari maida kudi gida=؃�<���

Zaki tura 300 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki tura shedar biya ta wannan number 08033300034

Amnah El Yaqoub
'<���
[13/09, 20:50] +234 803 697 8511: <�8�SHAHAAB<�8�
(Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook=�G�<���
https://www.facebook.com/amnahel




7&8



Munirat datazo part din maman domin yin dinner, ta tsinkayi zancen dasuke shida mama, gabanta ne yafadi, ahankali tajuya zuwa part dinsu, kwata kwata saitaji abincin ma ya isheta, ko inda take saka qafarta bata Gani, daqyar takai kanta d'akinta.

Numfashin tane yake sama sama kamar Wanda zai dauke.
Ahankali taji hawaye sun zubo mata, tarasa meta tsarewaa tsohuwar Nan datake so taga Bayan auren ta, tayi biyaiyar, a banza, tayi kissar a banza, daga ganin mutum a zaune Zaki d'ago masa da maganar aure? Idan bashida ra'ayin auren ma ta tabbatar wannan matar saita saka shi yayi, tana son Shahaab tana kishin sa, bazata taba jurar ganinsa da wata yarinyar ba, hakan bazai taba iyuwa ba, Mahmud natane ita kadai.

Lokaci daya taji tatsani mama, duk mutumin dazaisa dansa yaqara aure, a yimata kishiya tabbas wannan mutumin Babban maqiyinta ne.


Ahankali mama ta sunkuya tayi kissing goshinsa, sannan tace "Allah ya nuna mana, zuwa nayi infada ma na sallami me kula Dani, saboda batada kunya, Kuma bata iya aikinta ba"

Murmushi yayi, idan bai manta ba wannan me kula da maman itace ta kusan Tara, kowa yakawo mata to akwai irin complain din datake masa, Kuma Sai Bayan ta sallamesu ne take fada masa, yanzu idan yayi mata magana to zata fara yimasa mita ne, shiyasa yasaki murmushi ya nuna mata Shima hakan yamasa, ahankali yace "hakan yayi mama, duk wadda bazata miki yanda kike soba, kawai ki sallameta, insha Allah zansa a duba miki wata"


Kansa ta shafa tace "Allah yayi Maka Albarka"

Sannna ta zauna akujerar gefensa tad'auki coffee din tafara bashi da kanta.


Sai wajan shadaya nadare Sannan yabar wajan mama yatafi part dinsu, yana zuwa ya ganta taci wata arniyar rigar bacci, kasa d'auke Idonsa yayi akanta, tana ganinsa ta gefen idonta, cikin ranta tace "tarko na zaiyi aiki da alama"

Perfume tad'auka tafara fesawa, ko Kallan inda yake batayi ba, ahankali yatako yaqara so wajan ta, ta bayanta ya rungume ta tareda dora kansa akan kafadarta, wani irin kiss yasakar mata awuyanta, duk da saqon nasa yashige ta, hakan baisa tayi masa magana ba

Laushin jikinta, dakuma yanda hannunsa yake yawo akan abubuwan dayake so a jikin Nata, shine yasake saka shi tafiya wata irin duniya, cikin shaqaqqiyar murya yace "waye ya ta6amin ke?"

Meza tace masa? Taje wajan mama ne taji suna maganar yimata kishiya? Hakan yana nufin la6e take musu kenan?batare data bashi amsa ba, tajuya ta fuskance shi, zaiyi magana tahade bakinsu waje daya, yana qaunar kiss, shiyasa baiyi mata musu ba yabada Kai, saida sukai Nisa, hankalin sa yagama tashi, tasaki wani irin kukan kissa tajanye jikinta, Takoma Kan gado ta kwanta tana wani irin kuka, cikin tashin Hankali ya kalleta da lumsassun Idonsa,ahankali yataka ya zaune a gefenta tareda janyota jikinsa, can Qasan maqoshinsa yace "meyafaru Kuma? Kiyi hakuri Dan Allah, keda waye Wai? Nine ko?"

Yanda ya rikice yake zuba mata tambayoyi kadai ya'isa kagane cewa acikin tsananin buqata yake, cikin kuka tace "ni inada abubuwan danake son yi da wasu kud'ad'e ne, Kuma account dina yayi qasa sosai saboda nayi wa wasu Yara a family dinmu hidima da kudin"

Hannu yasa ya fuzgota jikinsa har saida qashinta yayi qara, yayi mata rumfa da faffadan qirjinsa, yace "naji, zanbaki duk abinda kike so, Kidena kuka saboda wannan, nawa kike ganin zai isheki?"

Cikin shagwa6a tace "ko ten million ne"

"zan baki"

Shine abinda yafada, daga Nan yaci gaba da abinda yake, tasan cewa ko samada haka tanema awajansa to zai batan, danhaka cikin farinciki tasakar masa jiki yayi yanda yaga Dama da'ita, saide duk yanda yake abu daya, Bai ji yasamu gamsuwa yanda yakamata ba, but duk da hakan yafi ace yana cikin wannan halin na masifar sha'awa, Bayan komai ya lafa tayi tunanin zaiyi mata magana akan kud'ad'en data nema, saitaji yayi shiru, shi kuwa ko ajikinsa, asalima baiga laifin taba ko kadan, menene aciki danta tambayeshi kudi? Haka kuma sigar yanda take neman kudin awajansa yayinda yake cikin tsananin sha'awa Shima bai taba damunsa ba, yaso de ya tambaye ta ko tana amfani da wasu magungunan ne yanzu, yana jinta tana sauya wa a wasu lokutan, shikuma hakan cutar dashi yakeyi, baya samun gamsuwa yanda ya kamata.



******



Gaba dayansu suna zaune acikin rumfar gidan suna shan iska kamar yanda suka saba, Yara ne guda uku suka shigo gidan hannun su d'aukeda doya, manja, dakuma sabulu Dan kamaru.

Bayan sun gaida su Daya acikinsu yace "Wai gashi, daga gidan Alhaji Audu ne"

Godia Ummah da Abba sukayi wa yaran, Hajja ta basu Dari biyu kudin tukwici
Zama tayi tana jujjuya jarkar manjan tana cewa "wannan bawan Allah yanada kirki wallahi, duk zuwa saiya kawo mana abun Arziqi, duk unguwar Nan kowa Alkhairin sa yake fada"

Aisha tafuto daga daki jikinta Sanye da hijabi Dan qarami Amma yarufe mata qirjinta, jarabar son jin radio ne da ita, yanzu ma redio ce a hannunta tana kokarin kunnawa, Hajja tace "mesunan qawa zoki dauke kayan Nan"

Radion ta ajiye ta dauke kayan, Hajja ta qarasa kunna mata, Adede lokacin kuwa kamar ansan Aisha ce take son jin radion adede lokacin ta tsinci muryar me bada labarin yana cewa "ma'aikatan hukumar efcc sun cafke wani sanata, suna tuhumarsa akan cinye kudaden wasu ma'aikata kimanin nera billion ashirin, inda shugaban hukumar MAHMUD WAKILI, ya basu umarni suci gaba da tsare shi harsai sun gama tabbatar da abun da suke zargi"

Ahankali tasaki wani siririn tsaki, Takoma cikin d'aki, tana jiyo Abban ta yana yabonsa "ai yana kokari sosai wannnan bawan Allah , Kuma yaro ne matashi bazai fimu shekaru ba, duk wasu 6arayin Gwamnatin qasar ahankali yake zaqulo su"

Sotake taje ta kashe radion, to Amma Abba yana wajan, Kuma duk suna jin labaran, batasan Yaya zatayi ba, wata dabara ce tafado mata, Ahankali tace "Hajja Dan Allah Zaki Bani kudi insiyo sabon battery? Nacikin radion yayi Sanyi wallahi"

Hajja tace "mekikace mesunan qawa? Ban fada miki ba, da nice na saki jarabar son Jin redion? Zoki dauki abarki"
Takashe radion tana miqo mata abarta, cikin farinciki Aisha ta kar6e radionta, cikin ranta tana fadin "yau son kudin Hajja Nima yamin amfani"(=��)



******



Yau babu inda yafita,mama tace bata so yayi nesa da'ita, tagaji da rashin ganinsa, hakan yasa ya zauna afalo yad'auki system yana chatting,kasancewar babu inda zai fita, saiyayi zamansa da wata Riga marar hannu, gaban rigar an rubuta Adidas, Sai wando three quarter Dayayi masifar yimasa kyau, mama tana daga Gefe tana kallo hannunta d'aukeda Inab tanaci, munirat tana Gefe a zaune tana fadawa qawayenta yau gasu surukar su tasaka su agaba, bataso danta yafita, Kuma taqi yarda yaje part dinsa barema Tasha soyaiyarta da mijinta, wata acikinsu Mai suna zuly ce ta turo mata emogi na dariya, tace mata akwai wasu magungunan da tagani Ana siyarwa na mallaka ne, idan ta siya Sai yanda tayi dashi, mama bata Isa tayi mata katanga tsakaninta da mijinta ba

Nan da Nan tanemi account number, suka turo mata, kudin tatura musu, Nan da Nan sunga ruwan kudi, suka bata tabbacin zasu aiko mata dashi har gida

Dayan group dinsu dasuka bude suka koma, kudin data turo suka raba a junansu, inda daya daga cikin su tad'auki nauyin turo mata ararra6i dakuma tazargade, a matsayin maganin mallakar.(:&�)

Daya daga cikin Yan sandan dake gadin gidanne yashigo ya kalli mama yace "Hajiya yalla6ai yanada baqi awaje"

Kafin mama tayi magana
Batareda daya d'ago Kansa ba yace "akaisu falon baqi"

Mama ta zubawa munirat data qanqame waya a hannu idanu,ta6e baki tayi cikin ranta tace "ko uban me take da wayar?" tayi tunanin zataji tayi magana akaiwa baqin mijinta ruwa, Amma sai taji shiru, ahankali ta watsa mata harara qasa qasa tace "Babu Tarbiyya agida"(=��)

Ita Kuma munirat tsoro take kartasa akai musu lemuka mama tace tana bada umarni tunda ranta, shiyasa ta manna mata(>�7�<���
@&�)
Mama ta daga murya takira me girkinta, da sauri ta qaraso ta tsugunna a gabanta, cikin Isa da Kuma tsantsar iko tace "akaiwa baqi ruwa, suna falon baqi"

Aqalla saida yad'auki kusan minti goma Sha biyar, Sannna yatashi yatafi wajan baqin

Wani Babban falo ne Mai d'aukeda manyan kujeru masu launin ash dakuma dark blue, Kala biyu ne kujerun haka akai adon falon dasu, manyan mutane yagani su uku, kowanne yana Sanye da Babbar Riga, suna shan lemukan da aka kawo musu

Yana shigowa suka zuba masa ido cikin mamaki, jisuke zasuga wani Babban mutum ne qaton tumbi, Sai sukaga yaro matashi, shi Kansa saida yaga baqin nasa sun manyan ta, Sai yaji kunyar yanayin shigar dayazo wajan su da'ita, sumar Kansa yashafa, cikin kunya ya zauna a kujera yana fuskantar su, Bayan sun gaisa daya daga cikin su yace "Nasan baka ganemu ba, baqi nemu daga yobe state muke, akwai Wanda yaturo mu wajan ka ne yace akwai gidaje dakake bayarwa haya anan Abuja, shine mukeso zamu za6i Mai kyau dan qarami guda daya"

Cikin girmamawa yace "eh hakane, akwai gidaje, qananun gidaje muna bada hayarsu a million daya da dubu Dari biyu da hamsin, saikuma manyan, ya danganta de da yanayin irin Wanda mutum yakeso"

Daya daga cikin su yace "ato mezai Hana mugansu, inda yiyuwar mu sauya ai saimu za6i Wanda yamana"

"ok babu damuwa, ga wannan katin, kunemi me number dakuka Gani ajiki, duk zai nuna muku komai, har kudin ma duk shi zaku Bawa"

Katin suka kar6a, tareda yimasa godia, daga Nan suka tafi

Shima tashi yayi, yana amsa wayar Ramadan, dayake sake sanar dashi gobe de yana hanya insha Allah



******


Washe gari dawuri ya shirya yafita wajan aikinsa, Bai dade da zuwa office dinba, aka sanar dashi anyi approved latter sa, yau yanada ganawa da shugaban qasa, muhimman abubuwa yad'auka, sannan yabar office din nasu, security suna take masa baya, Kai tsaye suka nufi fadar shugaban qasa, sun tattauna dashi akan manya manyan cases da'ake Fama dasu a qasar, daga Nan suka dudduba wasu muhimman takardu, akayi musu photuna Sannna yayi shirin tafiya, inda yasamu kyakykyawar Jinjina dakuma yabo daga shugaban qasa, yana futowa Yan jarida sukai masa caaaaa, kowa so yake ya amsa tambayoyin sa, gaba dayansu amsa daya ya basu wadatacciya, yayi gaba, security Sai kare shi suke kamar suna tsoron wani mutum zai iya cutar dashi

Kai tsaye office din nasu yakoma, inda yaci Karo da wani file daya girgiza tunanin sa, Ana zargi mutum biyu daga cikin hukumar tasu, suna kar6ar cin hanci da rashawa awajan qananun ma'aikatan dasuke shirin fitar da list din sunayen su wannan watan Mai kamawa, Jiyayi Kansa yasara, baisan lokacin daya dauki wayarsa yakira Ramadan ba, yana dauka ya tabbatar masa da cewa yanzu yanzu jirginsu ya sauka, zai wuce gida ya huta, zuwa gobe zai futo bakin aiki insha Allah

Sai yanzu ne yaji dadi, ko banza Wanda suke warware matsalolinsu tare ya dawo


******


Tafe suke a hanyarsu ta dawowa daga makaranta, Aisha ta kalli qawar Tata tace "Walida, wallahi naji dadin hutun Nan a wannan lokacin, nafarko ankusa azumi, zamuyi hutunmu cikin azumi, sannan Kuma abun yazo mana a qarshan wata, kinga wannan dubu biyun tawa, wallahi asusu zan siya nasaka aciki"

Walida tasaki ajiyar tace "hmm Aysha kenan, nikam Dama da mamana muke shawarar abinda zanyi da kudina, to itama Hankalinta atashe yake yanzu, tun jiya Abbanah bai dawo ba yana Abuja, Wai EFCC tasaka abokinsa acikin jerin mutanan da ake zargi, Kuma wallahi mutumin kirki ne, bakiga yanda yake yiwa Abbanmu hidima ba"

Aisha tace "Walida kenan, nifa kinga ko sunan mutumin Nan banaso naji, kinga de irin sunan mahaifina gareshi, to wallahi Bana ma son jin sunan, saboda na lura bashida Imani ko kadan, kullum labarinsa ne yake yawo yakama wannan, yakama wancen, jiyama inajin Abbana Sai yabonsa yake, kenifa saboda jin labarinsa ma nadena kunna radio na, ba zanje inyi asarar battery na akan wannan marar mutuncin ba "

Walida tace"A a Aisha, kidena ce masa marar mutunci, Shimafa baban wasu ne, Kuma muma idan wani ya cewa babanmu marar mutunci ba zamuji dadi ba"

Cikin 6acin rai ta kalli Walida tace "to tunda ke yanada mutunci a'idonki, Sai kije mutuncin nasa yasa yasaki abokin Abban ki" daga Nan tayi gaba ta qyale ta, wajan masu saida asusu ta wuce, tasiyo na nera hamsin, ta basu dubu dayan suka dauki hamsin din aciki, sannan tasaka dubu daya da Dari Tara da hamsin din aciki


Tana zuwa gida taga Hajja da jummai a tsaye acan gefen katangar gidan dede tiken dabobi, tanajin Jummai tana cewa "lalle Hajja A'i Jari yanata hauhawa, yanzu kece da tinkiya, Nan gaba kadan wannan tinkiyar Taki tsaf zatayi dubu ashirin"

Hajja tace "kemafa jummai Zaki ki iya siyan tinkiyar Nan, jarabar son kudinki ne bazata barki kisiya ba, Dan Allah Jummai kirage son kudi"

Jummai tace "Hajja A'i ai Ina kokari ma hakan, kullum fa Sai munyi miya da man nera hamsin, kashe kudin yayi yawa"

Baqin ciki ne yasa Hajja takasa magana, ganin shigowa Aisha yasa tace "Wannan akuyar Kuma me kaman kifi ta Mesunan qawa ce" (=��)

Aisha ta kalli Hajja batace mata komai ba, ganin taqi tankawa yasa Hajja tasake cewa "jummai kin ganta ai, wannan me kamar kifin de, itace ta Me sunan qawa"

Girgiza Kai Aisha tayi ta wuce Dakin Ummah, taga alama Hajja neman magana takeji dashi

Ummanta tabawa Asusun Nata ajiya, takuma fada mata kudin albashin ta na wanna watan yana ciki, idan zatayi amfani dashi tafasa Asusun ta d'auka, Sai asiyo Sabo amaida canjin ciki

Godia umman tayi mata, tareda samata Albarka, Sannna tatura Asusun Qasan gadonta.



SHAHAAB littafin kudi ne,naira 300 ne kacal =�L�<���,yar'uwa siyan nagari maida kudi gida, ki biya ki kiranta abinki cikin salama

Zaki tura 300 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki turo shedar biya ta wannan number
08033300034












Mrs Usman ce
'<���
[13/09, 20:51] +234 803 697 8511: <�8�SHAHAAB<�8�
(Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook=�G�<���
https://www.facebook.com/amnahel


9&10


Yauda sassafe yafita aiki, ko break bai tsaya yiba, wajan mama nede bai Isa yafita batare daya shiga yaga halin datake ciki ba, saida tasa masa Albarka sannan yafice a gurguje sakamakon wani zazzafan case dasuke dashi akan kama wani tsohon gwamna da sukayi, Ana tuhumarsa da cinye wasu kudade daya kamata ace anyi aiki dasu acikin jihar tasa beyi ba, banda Dan Karen bashi daya biyo baya Wanda akebin jihar, gaba daya dukkan kadarorinsa sun kama sun riqe, yana zuwa Yan jarida sukayi Kansa da tambayoyi, kasancewar labarin ya watsu acikin qasar, kowa da irin abunda yake fada, wasu na ganin laifin hukumar, wasu Kuma na ganin laifin gwamnan

Sai Bayan yagama tattaunawa da yan jarida sannan yawuce office dinsa, masu take masa baya Kuma suka dakata, ganin Ramadan na jiransa yasa yasaki murmushin dabai shirya ba, suka qarasa cikin office din

"mutanan Italy"

Cewar Shahaab

Ramadan yace "na'am Angon munirat ya ayyuka, jiya baka shigo office ba"

Kafadarsa buyu yadaga yace "wanne ango Kuma Ramadan, jiya mama ce taqi dadi, tace sotake na zauna taita kallo na"

Dariya Ramadan yayi "Hajiya Mama kenan, tana son wannan dannata qwaya daya"

"har mamaki takebani wani lokacin Ramadan, nikaina nasan idan babu ni Tofa babu mama" ya qarasa maganar yana murmushi dinmple dinsa yafuto

Ramadan yace "no, karka ga laifin ta, idan kaine a matsayin datake, nasan saika fita son Yara, saboda ita bata dauki lokaci Mai tsawo ba ta sameka, kaikuma ka dauki wasu shekaru kana jiran haihuwar baka samu ba, kaga kuwa Kai zaka fita son Yara,Kanada lafiya, aure kawai zaka qara, kafara zubo mana Yara, kaima kasan da hakan"

Cikin sanyin jiki yace "Allah yasa mudace"


Cikin rashin mamaki Ramadan ya Kalle shi, wato da gaske de bayason maganar aure, kamar Wanda munirat ta riqe masa zuciya ita kadai, akan suyi maganar auren shine ya kawar da zancen nasu Wai Allah yasa mudace, ajiyar zuciya yasauke yace "Amin, ga wannan file din, nagama aikinsu jiya Dana shigo office, binciken da'aka turani komai yayi daidai, idan kaduba zaka Gani, Bari in barka kayi aiki"

Batare da yace komai ba yaja file din gabansa, shikuma Ramadan yafice daga d'akin office din

******
Aisha data futo sassafe, tafara tattare kayan gidan ta share shi tas,radio ta kunna, Bayan tagama jin labaran safiya tana shirin kashe radio taji hukumar efcc ta damqe wani tsohon gwamna, girgiza kanta tayi ta kashe radion,al'amarin Mahmud Wakili Kuma yanzu yadena bata mamaki, tsoro yake bata,tadebi ruwan wanka a bokiti takai banda ki, Sannna Takoma Dakin Hajja tad'auki Dan qaramin brush dinta da makilin, saida ta kalli Hajja dake kan gado taga bacci takeyi sosai, sannan tasaki labulen Dakin tazare hijabin jikinta ahankali ta ajiye,sannan tacire yar yaluluwar doguwar rigar jikinta ta bacci wacce Taji jiki, Nan da Nan farar fatar jikinta ta bayyana, abinda take 6oyewa cikin hijabi Shima yafuto muraran, gaban tsohon madubin Dakin taje ta tsaya tana qarewa qirjinta kallo,itade tunda tafara wannan abu takejin zafi, bata Isa tabigi wajanba Sai taji kamar Tai ihu,ga tauri bata Isa ko cikin bacci ta kwanta akansu ba, Kuma Sai qaruwa suke kamar tana saka musu wani abu, a tsaye suke qyam a qirjinta Yan madedeta da basufi madedecin lemon zaqi ba, ko yaushe zasu daina ciwon? Ta tambayi kanta

Jin kamar Hajja zata motsa yasa tayi sauri ta daura zanin wanka, sannan ta ajiye kayan data cire

Hajja data dade da bude ido ta kalleta tace "Mesunan qawa, idan kingama kallon kanki amadubin dage min labulen Nan zafi ya isheni, munafuka.... Idan Zaki kalli kanka saiki tasheni daga bacci kice Hajja A'i fice zanyi amfani da Dakin" (=�F�<���
@&�=��=�H�=�J�)


Jitayi kamar ta nutse acikin qasa Dan Kunya, Dan qaramin bakinta ta turo gaba, sannan tafice daga d'akin tana bubbuga qafa cikin shagwa6a, ko labulen bata dauke ba (=��)

******

Da daddare suna zaune a dinning, Mai aikin mama takawo musu abinci tana jerawa, mama tace "Shahaab nifa nafara gajiya da Zaman dinning dinnan, takura nake yi, nafison na zauna aqasa"

Cikin ladabi yace "mama to mukoma Qasan mana, saina baki abincin dakaina"

"a a, yaushe zan saka wahala Shahaab, yakamata de ka nemo min wata yarinyar, wannan din aiki zaiyi mata wahala, ga girki gakuma kula Dani, ita Kuma munirat babu abinda ta'iya Sai danna waya"

Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, yasan idan yaja maganar to ba'a Kansa zata huceba saide akan munirat din.

Mai aikin ce takawo musu lemon data Dauko a kitchen, zata zuba wa mama Nata, Sai munirat ta dakatar da'ita, tace "jeki, Bari in zuba mata"

Mai aiki tafice daga falon, mama ta kalli munirat tace "duk inda kissa take ni banason ta, nida ba namiji ba tayaya za'a min kissa nakasa ganewa? Dacan baki ta6a zuba min abincinba, Sai yanzu? Babu uwar da kike tsinana min a gidan Nan munirat, shiyasa Nima nafi ganin mutunci da qimar wadda take kula Dani akan ki, koba komai ita zata Dauko abinci na takawo min tunda tasan banason Zaman dinning, zata zauna ta dinga matsamin qafafu na saboda kumburi, zata zauna Dani tayi fira Dani ta debemin kewa idan d'ana baya Nan, duk abinda zakumin yanzu daga ke har mijin naki ai duk a banza, tunda Shima gashinan a zaune yakasa nemo min Qawata, Amma da neman 6arayin Gwamnati ne jikinsa yana rawa zaije yakamo su, anan yafi qarfi, saikace Gwamnatin ce ta haifeshi baniba"(>�-�=�F�<���
@&�)

'Dago Kansa yayi zai bata haquri ta dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu, "dakata Shahaab, banason jin komai...idan kuma zayyanomin abinda kata6a yimin zakayi danka wanke kanka saboda rashin nemo min

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment