Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna saukewa daga cikin motar, wasu Kuma suna rabawa, Ramadan ya tsugunna yadauka yanufi wani gidan yana tunani a ransa gaskiya sahabai sunyi kokari, Kuma suna neman aljannarsu da gaske

Shahaab ma dauka yayi yanufi wani gidan can daban, ya ajiye a kofar gidan, sannan ya dawo yasake dauka yakai qofar gidan Jummai qawar Hajja, sannan yasake dawowa ya dauka yakai gidan Alhaji Audu Wanda hukumar efcc ta qwacewa gidan mansa, dawowa yayi yarungumi taliya guda hudu ya jibge a kofar gidansu Aisha, Sannna yakoma zai Dauko sauran

Cikin baccinta taji wani irin fitsari, cikin sauri ta tashi tad'auki buta da gudu tashige bandaki Dan kwalinta a hannu,ta tsugunna tana fitsari tana daura dankwali, mamaki take wanne irin fitsari ne wannan kodan ta dirki ruwa da yawa Bayan tadawo daga masallaci sallar tarawih dazu.

Jitayi kamar an ajiye wani abu aqofar gida, mamaki ya kamata, saida tayi tsarki Sannan tafuto daga bandakin, cikin sand'a ta nufi hanyar kofar gida tana so ta leqa taga qaran menene wannan, tana zuwa bakin kyauren nasu Sai taji takun mutum, gabanta ne yafadi to kode 6arayi ne?

Matsawa ta sake yi, ta sunkuya taleqa ta cikin wata yar qaramar 6ula inda kyauren yafara cire wa, mutum tagani ya tsaya a kofar gidan, Amma bataga fuskarsa ba, Adede lokacin shikuma Shahaab ya ajiye sauran macaronin daya Dauko, yana ajiyewa kwalin macaronin ya bugi kyauren, jikake garam Sai a fuskar Aisha (=��)
Cikin azaba tace "wayyo goshina"

Mamaki yakama Shahaab, mutum, Kuma muryar mace acikin wannan Daren? Fitilar wayarsa ya kunna, sannan yasaka Hannunsa yatura kyauren cikin mamaki yaganshi yabude alamun basuda Sakata a gidan, yana budewa Idonsa ya sauka akan dogon gashinta Wanda yarufe mata fuska, dankwalin Nata na hannunta, yayinda hannunta guda daya yake kan goshinta tana mulmula wajan data bige, gabansa ne yafadi, wannan kwa mutum ce? Wanne irin gashi ne wannan?

Hannunta tad'auke daga kan goshinta ta d'ago fuskarta ta Kalle shi tace "waye?"

Baisan metake fad'a ba,gaba d'aya hankalin sa, tunanin sa, dakuma Idonsa yanakan kyakykyawar fuskarta yana qare mata kallo, hannunta ya kalla yaganshi fari tas, yasake kallon hannun ko zaiga alamun shafe-shafe, Nan ma yaga babu, ya kalli Dan qaramin bakinta Mai launin pink, mamaki yasake kamashi, tayaya? wannan kyakykyawar yarinyar acikin wannan qauyen?

Ganin tana magana yayi shiru yasa ta meqa hannu dede fuskarsa ta had'a hannayenta suka bata sautin d'as d'as, cikin sauri ya dawo hayyacinsa ya kalleta, cikin masifa tace "waye ya aikoka da wannan kayan?"

Yayi mamaki yar qarama da'ita Amma ta'iya masifa da wani Dan qaramin bakinta kamar gidan tsuntsu, abun mamaki Wai shi ake tambaya waye? Lalle Allah daya gari bambam,dama akwai mutanan da zasuce wai basusan waye MAHMUD WAKILI ba?

Baisan meyasa ba, baisan Yaya akai ba, lokaci daya ya tsinci Kansa dabin shawarar mama da Ramadan, maimakon yafada mata waye shi, saiyace "sunana SHAHAAB"

Cikin 6acin rai tace "to koma de waye, Mahmud Wakili ne kaima yaturo ka Rabon kayan abinci kamar yanda yaraba a wasu jihohin ko?"

Mamaki ya kamashi, Yaya akai tasan sunansa Amma batasan waye Shiba? Bai iya bata amsa ba Sai kansa daya daga mata kawai

Hannu tasa ta gyara dogon gashinta yakoma baya, Cikin jin dadi tace "Alhamdulillah, dama na Dade inaso na ganshi, ka dauki tsiyarsa ka maida masa, Bama so, kafin yabamu abinci Dama can muna rayuwa, shine matsiyaci Mai Kama kudin talakawan Allah yana riqewa,Kuma dayake kama mutane yana qwace musu Kaya Shima ai abun atuhumeshi ne, tunda bamusan daga Ina yasamu kudin dayake facaka dashi ba, qila ma kudin talakawan ne, saboda haka bamaso, Kuma kakoma kafada masa muddin nahadu dashi to haduwar mu bazatai kyaub......"

kafin ta qarasa ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.( '<���)
Bai saba ganiba, Bai taba ganin Wanda ya tunkareshi fuska da fuska yafada masa baqar magana haka ba, asalima kowa girmamashi yake Ana ganin qimarsa, babu Wanda yake masa rashin kunya saide lallashi, inda ace yana candy yayi aure ya tabbatar da tuni ya haifi kamar wannan yarinyar, cikin 6acin rai da daure fuska ya matso da fuskarsa dab da Tata har sunajin hucin numfashin juna, yace"ke!!!, marar kunyar yarinya, yar qanqanuwa dake kin'iya masifa, idan naqaraji kin zagi ogana saina kakkarya qasusuwanki na zubar anan wajan, maza dauke wannan kayan kikai ciki "








Mutara zuwa gobe =�O�<���



SHAHAAB littafin kudi ne, babu tsada nera 300 ne kacal, Yar'uwa kibiya tun kafin free page yaqare.


Zaki tura 300 ta wannan account din

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki tura shedar biyan kudi ta wannan number

08033300034









Mrs Usman ce
'<���
<�8�SHAHAAB<�8�
(Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook=�G�<���
https://www.facebook.com/amnahel



11&12

Tsoro ne yakamata, idonta yayi tsilli-tsilli tana Kallan sa,duk da bata sanshi ba,yanda taga ransa ya6aci tsaf zai iya aikata abinda yafada,wani tsoron ne yasake shigarta, gashi cikin dare ne kartaje haka kawai yakasheta a banza awofi, bare taga yanda yake da kyau, bata Sani Bama ko aljani ne, to sune akace suna shigar mutane su shigo cikin su, gabanta ne yafara faduwa ganin yanda ya matso kusa da'ita kamar zai shige mata jiki


Batare datace masa komai ba ta sunkuya,dogon gashinta ne ya dawo fuskarta sakamakon sunkuyawar da tayi,yasake rufe mata fuska, kwalin taliyar ta d'auka tayi ciki.

Kallan ta yayi yaga yanda uban hips dinta yake juyawa,girgiza Kansa yayi, yafara magana cikin zuciyar sa, inaga fa yarinyar Nan ba mutum bace, yar qaramar yarinya da'ita Amma ta mallaki abubuwan more rayuwa, Kuma inba aljana bace tayaya yanda yakewa mutane kwarjini Amma ita baiyi mataba Sai rashin kunya take zuba masa? Kaiii Gara yayi sauri yabar gidan, idanma aljanar ce to aniyarta tabita,cikin sauri yafuto daga gidan, Aisha kuwa tana ajiye kwalin taliyar tashige cikin Dakin Hajja da sauri gabanta yana faduwa, runtse idonta tayi, Amma shi take Gani a'idon zuciyarta yanda ya matso kusa da'ita ya nuna ta da hannu, yake zare mata ido, dak! dak!! Haka gabanta yake faduwa, Allah yasa ba Gamo tayi ba, Allah yasa ba aljani ne yabude mata idoba.

Sai wajan karfe hudu saura suka gama, har suka koma hotel kuwa jikinsa a sanyaye yake,maganganun yarinyar ne suke masa yawo a zuciya,saida yayi nafila sannan yayi sahur ya kwanta, da asuba kuwa tunda suka tashi basu koma bacci ba sukai shirin komawa Abuja

Da asuba Abbah yana tashin su Aisha sahur, saiyaci Karo da kwalin taliya guda daya, Wanda Aisha tashigo dashi, mamaki ya kamashi, jiyake kwali ne, Amma yana ta6awa yaji nauyi, Hajja tana futowa itama ta tsaya tana Kallan sa, fita yayi daga gidan saboda hayaniya da yaji tana tashi awaje, yana zuwa bakin kofar gida yaci Karo da sauran kayan,fita yayi daga gidan inda yaga mutane Ana tsatstsaye kowa yana fadar Albarkacin bakinsa, wannan yace yaji tsayawar motoci to yayi tunanin Yan fashi ne shiyasa yaqi futowa, wannan yace kaza wannan yace kaza, haka de, Abba yajuyo yashigo da sauran, anan yaga duk mutanan gidan sun tashi, Hajja ta Kalle shi tace "mamuda ashe Wai kaji ita Me sunan qawa taji lokacin da aka ajiye kayan tafuto fitsari lokacin, to Kuma Wai kafin taje bakin qofar har Wanda ya ajiye yatafi, bataga kowa ba, shine tashigo da guda daya taji tsoro kartaje ko aljannu ne" (=�2�)

Murmushi Abba yayi yace "ba aljannu bane Hajja, Ina Yaron Nan Dan kasuwar Nan? Me sunana?"

Hajja tace "waye Dan kasuwa Kuma?"

Yace "shugaban EFCC da'ake maganar sa a gidan redio yana raba kayan abinci gari-gari, ai shi nake nufi, to wai shine ya aiko wasu mutane suka raba mana muma"

Fashewa da Kuka Hajja tayi tana goge hawaye da gefen zaninta, cikin kuka tace "Allahu akbar, Allah yasaka masa da alkhairi, Allah yabiya masa buqatunsa na alkhairi, mamuda kaima bancire rai zakayi kudi ba, kaima Naka kudin yana Nan tafe" (=��)

Aisha ta harareta tajuya tad'auki buta da brush tayi bandaki, har Bayan gama sahur dinsu,zancen aketa maimaitawa, Garin chamo babu sunan Wanda yake yawo saina MAHMUD WAKILI =�L�<���


******

Bayan sun koma Abuja Kai tsaye office suka wuce, saida yarage wasu ayyukan sannan yatafi gida, Bai nufi part dinsu ba, saboda yasan Idonsa idon munirat to yau babu batun daga qafa awajansa, kwana ukun Nan Dayayi jiyake kamar yayi shekara uku ne batareda mace ba.

Sai Bayan Ansha ruwa yaga lafiya lafiya yakai azumin sa, sannan yatafi part din nasu, a wannan Daren munirat tagane kurenta, domin kuwa taji jiki yanda ya kamata
Saide abun mamakin shine kwata kwata baiji wani canji awajanta ba, tana nan kamar de yanda yatafi yabarta,ko kadan bai samu gamsuwa ba, shiyasa Bayan yahuta saiya sake nemanta Bayan wasu awannin, Amma idan yasake maimaita wa dinma duk hakan yakeji, yayi tunanin idan yayi dayawa hakan zaisa yaji shi zam-zam, to Amma sai yaji sa6anin haka.
A 6angaren munirat kuwa tayi tunanin yanda yadage yake abu daya tun farkon dare har tsakiyarsa yaji tayi masa dadi ne, saboda Shahaab irin mazan Nan ne Wanda suke shiru yayinda suka kasance da matansu, tun tana amarya takeso ta rikitashi ta karya wannan dabi'ar tasa taqin yin kukan dadi, Amma duk yanda takai da gyara haka zata jishi shiru, shi Dan sumbatun Nan ma ba yayi, bata saniba dadin tane baikai yayi kukan ba kokuma haka dabi'ar sa take, dataga sun kwashi shekaru masu tsawo Ahaka, kawai saita sallama, tabarshi a hakan dabi'ar sa take, shiyasa yanzu ma bata kawo komai acikin ranta ba, saide Bayan komai ya gama wakana ta isheshi da kukan kissa, shikuma Nan da Nan ya lalace wajan lallashin ta, ko kadan baison abinda zai 6ata ran munirat.


******

Yau satin su daya da dawowa daga jigawa, Amma tunani d'aya yabi yadameshi, yana son ya yakice maganganun da yarinyar tafad'a masa Amma yakasa, 'Dan qaramin tsaki yasaki, yafi awa daya a kwance a gadon mama, so yake tadawo yaji duminta Amma taqi dawowa tana can tana kula da Abincin da ake rabawa sadaka,Lumshe Idonsa yayi yana jin dadin yanda sanyin esi yake ratsa jikinsa, ko kadan bayajin wahalar azumin, sake sakin wani tsakin yayi Bayan tunanin yarinyar yasake fad'o masa, alqur'ani yadauka yafara karanta wa ko zai kawarda tunanin a ransa.

Sai gab da shan ruwa mama tadawo, alqur'anin ya ajiye ya dawo ya kwanta akan cinyarta, Kallan sa kawai tayi takasa magana, wani lokacin idan yayi mata wani abun kamar qaramin yaro, babu yanda zatayi dashi tunda shi kadai gareta, dan haka ta share shi tad'auki remote takamo tashar Sunnah TV tana kalla, saida aka Sha ruwa sannan suka dawo falo, anan ya tarar da munirat tana hada fruit salat, suna zama kuwa ta ajiyewa kowa nasa, wannan Karon mama batayi halin Nata ba, kawai dauka tayi Tasha, kodan saboda azumi ne yasa kwana biyu tayi shiru oho.

Bayan ya dawo daga sallar tarawih ma wajan mama yawuce, har lokacin suna tareda munirat, Sai wajan karfe goma sukayi mata sallama suka tafi part dinsu.
Kai tsaye dakinsa yawuce yayi wanka sannan ya kwanta, so yake yayi bacci da wuri, to Amma saide me? Dan qaramin pink lips din yarinyar yake tunowa, yasake tuna yanda take tafiya da sauri zatakai kwalin taliya cikin gida gaba daya hips dinta wani irin juyawa yake, yatunada dogon gashinta Wanda yafara daukan hankalin sa.
Meyasa ta tsaneshi? Meyasa take hamdala ga Rabbi saboda yace mata shi Yaron Mahmud Wakili ne? Hakan yana nufin akwai abinda ya yi mata, Kuma take neman sa ido rufe Amma bata sameshi ba, laifin meyayi dahar take fada masa cewa Shima ya kamata atuhume shi? Meyasa ta tsaneshi har haka? Wata zuciyar tace dashi yakamata kasan dalili.

Gyara kwanciyar sa yayi ya dawo yana kallon p.o.p din 'Dakin, tabbas inason jin dalilan yarinyar,gashi tanada masifa Amma da alama tanada tsoro, tunda tsawa d'aya kawai yayi mata, yaga idonta yayi tsilli-tsilli kamar ace kyarat ta gudu,idan ita din marar kunyar gaske ce to tsayawa zatayi ta fuskance shi yafada, itama ta fada, ya tuna yanda take zare ido cikin tsoro, baisan lokacin da wani irin murmushi ya qwace masa ba, cikin zuciyar sa yasake cewa yar qarama...
Yasake sakin wani murmushin har dimples dinsa yana futowa, a fili yace "me qaramin baki kawai...."

Munirat data dade da shigowa Dakin tana fesa turaren sa,cikin iyayi tajuyo ta Kalle shi tace"My Dear ni d'in?" (=�3�=�J�)

Firgigit yayi ya dawo cikin hayyacinsa,yasaki wata nannauyar ajiyar zuciya, yaushe tashigo Dakin bai Sani ba?
cikin salon basarwa yace"yes"

Tareda miqa mata hannu yana daga kwancen.

(kaii jama'ah, shegiya yaudara =�D�)

Babu musu ta qarasa tana wani irin taku tana karkad'a jikinta, hakanne yad'auki hankalin sa, har me aukuwa ta auku, tayi tunanin zaiyi mata godia Bayan komai yagama wakana saboda dazu dazun Nan tagama shan wasu magunguna data siya wajan qawayenta, a jikin maganin ma saida akai kashedi idan kinsan kinada kishiya to karkiyi amfani dashi Dan Zaki gigita maigida.

Shikam Shahaab daqyar yasamu yayi released, zuwa yanzu Kam yariga ya saduda,ya daina qorafin komai, danhaka yauma bai nuna mata komai ba.


******

Zaune suke da Hajja, tunani take a ranta hartana cizon yatsa, Sai yanzu ne takejin haushin kanta kan rashin maidawa wannan mutumin martani.

daya ce mata ogonsa ne ya aiko shi, meyasa bata maida masa martani tace yaje ya fadawa ogan nasaba?
Takaici yazo wuyan ta ya tsaya, Sai yanzu haushin kanta duk yabi ya isheta, mutumin datake nema ruwa ajallo Kuma yanzu tasamu Damar da saqonta zaije gareshi Amma tayi watsi da damar ta.

Hajja dake Gefe tace "me sunan qawa yau me Zaki dafa mana a gidan?"

Taji shiru, ita kuwa Aisha tunani ne yayi Nisa batasan ma Hajja tana yimata magana ba.

Saida Hajja tata6ota tace "mesunan qawa!"

Sannan ne ta kalleta, Amma batayi Mata magana ba, cikin sauri Hajja tace "idan de akan naqi yimiki kitso ne kika fara gaba Dani har Ina miki magana kina qyaleni to dauko mataji nayi Miki, saikiyi gabar da mamuda ko Hadiza"(>�-�)

"Hajja menene Kuma ummah da Abba na suka miki Zaki sakosu aciki?"

Hajja tace "kidauko nace, ni banason mita wallahi, dama azumi ne yasa nace bazan miki ba, saboda ranar Bana Gani sosai yunwa tasa duhu duhu kawai nake Gani"

Tashi tayi ta dauko mata matajin tabata, sannan ta zauna suka fara, manyan kitso suka fara guda goma, kasancewar gashin baida cika saide tsawo, Sai yarfe hannu take saboda zafi.

Jummai ce tashigo gidan tasamu waje ta zauna, Bayan sun gaisa tace "Hajja babu Dan sauran abinci awajanku nabawa jikana"(=��)

Hajja tace "Ina zamu samu sauran abinci jummai, muda ba Yara ne damu ba, Hadiza ta daina haihuwa, danma mamudan nawa jarumi ne gashi harda yaransa biyu, Amma ni har nayi zamani na nagama aishi kadai na Haifa, tundaga Kansa ko 6atan wata ban qara ba, Amma shi kinga yayansa biyu "

Jummai tace"um aikuwa mamudan naki ya'iya haihuwa jummai, ga 'Ya'ya nan kyawawa kamar yayan larabawan labanu"

Aisha da takaici ya cikata tataba sauran gashin taji saura guda biyu agama,batason jin takaicin firar Hajja da jummai Wai labanu...

Can Kuma Sai jummai tace "oh nikam Hajja ya mukaji da labarin taliya, har yanzu tana nan muna Jan dafaduka da'ita, wannan yaro Allah de yabiya shi,masu kudi dazasu dinga haka dasun samu Lada awajan Allah"

Hajja tace "masu kudi sunada kudi infada miki, Amma Kuma suna qara son kudin su, kiduba kiga Yan siyasa sunada kudin, wani ma har jikokin sa bazasu taba talauci ba, Amma a hakan nema suke susake Hawa kan mulki, mukuma talakawa muna Nan Sai godiar Allah, ni yanzu ko dubu talatin aka Bani ai jikinane zai fara karkarwa, wallahi zazza6i zai sakani "

Jummai tace"aikuwa in hakane Hajja A'i kakarki ta yanke saqa, Ina Yaron Nan inusa me kanti na qofar gidana?"

Hajja tace "wai inusa wannan me shago?"

Jummai tace "shide, jiya jiyan Nan yazo ya sameni yace tunda ke aminiyata ce inyi masa hanya mana yazo wajan mesunan qawarki, Kuma Hajja A'i inde Aisha ta amince ba abunda bazai muku ba, yanada sakin hannu"

Aisha tanajin haka kunya ta kamata, tatashi da gudu tatafi daki
Jummai tace "laaa Hajja A'i kode harta amince ne, Naga tatafi daki cikin kunya"

Hajja tace "ai mungama amincewa jummai"

"to Alhamdulillah zan sameshi nafada masa, saiki fada mata idan zaizo ta dinga kwalliya, 'Dan janbakin Nan ta dinga shafawa, taci kwalliyarta da mayafi"

Hajja tace "Ina me sunan qawa zata saka miki mayafi? Dan qirgen dangin take 6oyewa, Kuma kinsan Yara inde suna wannan matakin Tofa ko yayan limamai Albarka, Amma inda tana kwalliya ai samari Sai mun kori wasu,tun yanzu ma gashi anfara aike, kinsan Kuma farinjinina ta Dauko da alama, Saboda Nima alokacina saida aka kawomin Goro d'aid'ai har guda sittin"(=�3�)

Jummai tace "to aikuwa zan fada masa dangin farinjini yake so, tun kafin wani yazo yatureshi Gara yadage, 'Dan man Nan ya dinga siyo mata tana shafawa duk Dama Naga jikar Taki fara ce sol ga hanci har baka inni mayya ce incinye kaina" (=��)

Hajja tace "fada masa Kam gaskiya"

Jummai tasake Kallan Hajja tace "Hajja Kuma Yaya kikayi da Goron da aka kawo miki?"(>��)
Hajja tace "ai inafada miki a makaranta ma malamai fada suke akaina, da sukaga Bana kulasu kawai saide kiga sun shirya sun Kai Goro gidanmu, Ahaka Ahaka har guda sittin kinji zancen gaskiya, Amma dayake aure rabo ne duk masu son Nan nawa babu wanda na za6a Sai uban mamuda Allah yaji qan rai "

Jummai tace" ikon Allah, banta6ajin irin wannan labari nakiba ko a hikaya"

Hajja takauda kanta Gefe tace"to yanzu kinji"


******

Yau Shahaab da munirat sun Lula qasar Saudia umara, munirat kamar ta zuba ruwa aqasa Tasha Dan murna, saboda tarabu da jarabar mama, yau itama de take6e itada mijinta.

A hotel suka sauka, kwanansu biyar da zuwa qasar Amma munirat har wata qiba tayi, jikinta yayi wani irin fresh, kasancewar bata tafi da kayan magungunan ta Wanda ta siya awajan qawayenta ba, Sai jikinta yake sauya wa, ita akaran kanta tasan ni'ima ta saukar mata, tunda kullum cikin hutu take babu tunanin mama, saide taita cin fruit masu kyau tana kwanciya, shiyasa a kwanansu na shida tarasa gane kan Shahaab, tunda ya ratsata yaji ta sauya Nan da Nan ya rikice mata, kamar mahaukaci haka ya dinga abu daya.
Yanda take samun hutu a qasar Sai take jin Dama su dauwama Ahaka,ga Kuma uwa uba Mahmud dinta yana tare da'ita, shiyasa gaba daya addu'ar ta taqare 6angare daya, wato Allah yabar mata Mahmud, ya mallaka mata zuciyar sa ya kasance ita kadai yake Gani acikin mata, duk wata mace dazata mata shamaki da mijinta to Allah yasa Shahaab ya dinga kallon ta a namiji

Sa6anin Shahaab daya duqufa wajan yin addu'ah Allah yabashi 'Ya'ya nagari idan yanada rabo,saikuma mama datace masa yadinga yimata adduah Allah yasa kafin ta mutu tahadu da qawarta Aysha Sulaiman Bompai, wuni yake a masallaci yana wannan addu'ar, idan tare suka tafi da munirat gajiya take da jiransa Takoma masauqin su, shikuma daga baya Bayan yagama addu'ar sa saiya dawo shi kadai.

******

Yau gaba d'ayansu atsakar gida sukai sahur, Abba yana Gefe yana karatun alqur'ani, Ummah da jabir da Hajja suna zaune atsakar gida, Aisha kuwa adaki taci Nata abincin, saida tagama tafuto,ta bude fridge din Hajja dayake cike da qanqarar sayarwa, tad'auki ruwan Sanyi ta tsugunna tanasha, Hajja ta bita da kallo tace "kaga shafaffiya damai, inajin bata mayi sahur dinba"

Jabir yace "aikuwa kamar kinsani Hajja batayiba"
Hajja tace "Ahaf! Aini tabiyo, Nima fa wannan sahur din bawani damuna yayi ba, Amma jiya duk da nayi sahur azumin Nan yabani wahala, ko yaya na sunkuya kawai duhu nake Gani, duk jijiyoyin jikina saki sukayi, sallar la'asar ma a zaune nayi ta"
Gaba dayansu dariya suka sa, harda Abba, Hajja kenan me abun mamaki, tace sahur bai dameta ba Amma Kuma mutumin da sahur bai dameshi ba shine yake sallah a zaune tsabar wahalar azumi, Kuma sude asaninsu da Hajja kullum Saitayi sahur, wannan ladan baya wuce ta.

Ta kalli Aisha data gama shan ruwa tace "debomin ruwa a kafara na qulla nasaka a fridge, babu pure water yaqare, harna fara kewar azumi wallahi, tunda muka shiga goman qarshan Nan"

Aisha tatashi zata bata ruwan tace "ai dole kiyi kewar azumi, tunda kina cafkar kudin qanqara"

Sarai taji abunda Aishan tace Amma Saitayi shiru, saboda tasan tabbas tana samun kudin qanqarar, Kuma tsaf me sunan qawa zata fadawa mamuda abinda take samu kullum, danhaka Saitayi shiru taqi ta tanka mata, saima cewa da tayi "Bani ruwan sanyi a fridge Nasha jabir, wadannan masu gaggawar yanzu zakaji sun fara Kiran sallah, idan shan ruwa ne Sai sun gama Jan ajinsu sannan su kiramana sallah, Amma idan lokacin sahur ne abincin ma baya tsirga musu suke tafiya masallaci sukira sallah "

Jabir yayi murmushi yad'auki ruwan yabata


******

Ana azumi na Ashirin da d'aya, sannan su Shahaab sukai shirin tafiya, munirat tasashi agaba tana so tayi wa yan'uwan ta da qawayenta tsaraba, dole yad'auki maqudan kudade yabata, tasashi ya shirya domin suje super market da boutique tayi siyaiyar acan, haka badon yasoba ya shirya suka tafi.

Kai tsaye BIN DAWOOD HYPERMARKET sukaje, shide babu abunda zai siya, kawai Kallan ta yake tana za6ar duk abinda taga yayi mata.

Ajiyar zuciya yasauke, yarasa meyasa yake tunanin ta, tun Bayan tahowar su daga Garin yake nema ya yakice tunanin ta a ransa Amma yakasa, gaba daya taqi barinsa ya huta, yarasa Yaya zaiyi da ransa.(>�&�<���
B&�)

Kayan yaci gaba da kalla, anan yaga wani ribbon dark green Mai masifar kyau, babu Wanda yasake fad'o masa Arai face ita, ya tuna yanda dogon gashinta yake ko ribbon babu, cikin ransa yafara magana "marar kunya 'yar qarama...."

hannu yasa yad'auki ribbon din yaga ansaka shi cikin wani gida, kana Gani kasan yanada tsada, price dinsa yagani,kudin ribbon din kadai yafi kudin daya Bawa munirat tayi siyaiya dashi.(=�F�<���
@&�)

Batare da tunanin komai ba yadauka matashi.







(=�2�>��tabdi sorry Munirat=�%�)





SHAHAAB littafin kudi ne,naira 300 ne kacal =�L�<���yar'uwa siyan nagari maida kudi gida, ki biya naira 300 ki karanta abinki Hankali kwance


Zaki tura 300 ta wannan account din


0164549488
Amina muhammad
GTbank

Zaki tura shedar biya ta wannan number 08033300034









Amnah El Yaqoub
'<���

[10/09, 22:14] +234 803 697 8511: <�8�SHAHAAB<�8�
(Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name
https://www.facebook.com/amnahel



13&14


'Boyeshi yayi a Bayan hannunsa, Karo na farko kenan daya fara 6oyewa matarsa wani abu, Kallan ta yayi yace "munirat idan kin gama kisameni awaje,I'm tired"

Juyowa tayi tace "okay my dear five minutes"

daga Nan taci gaba da tafiya tana za6ar abinda takeso tana sakawa acikin kwando.

Juyawa yayi cikin sauri, yaje ya basu atm dinsa suka dauki kudin ta dollar account d'insa, sannan ya 6oye abun acikin aljihunsa, yakoma cikin mota yana jiranta.

Bayan tagama siyaiyar tafuto,hotel suka koma, saida yaga tashiga wanka sannan yasaka ribbon din cikin jakar kayansa data had'a masa tun Daren jiya.


Cikin dare jirginsu yatashi zuwa qasar Nigeria,Bayan sun sauka munirat Kam bacci ta kwanta, shikuma yatafi wajan mama, saida ya ganta tana bacci sannan ya dawo part dinsa.

Ganin baccin munirat din yayi Nisa yasa ahankali yatashi, yabude cikin jakarsa ya dauke abun kama gashin daya siyo, yasaka shi cikin wata akwati, sannan ya danna wasu numbobi security din jikin akwatin yakoma yarufe, sannan ya ra6a gefen munirat din shima ya kwanta tareda sakin wata irin ajiyar zuciya ya Lumshe Idonsa Sai bacci.

Dasafe baije wajan aiki ba, tun safe da suka tafi wajan mama bai dawo ba, munirat ce tadawo ita kadai saboda tana shirin kar6ar baqin qawayenta Wanda zasu zo mata sannu da zuwa.

Sai yamma yakoma part dinsu, anan yaci Karo da baqin munirat da basu dade da zuwa ba,har hada baki suke suna gaida shi, ya amsa musu fuskarsa adan daure, sannan yawuce daki

'Daya daga cikin su mesuna meji (maijidda) tayi qasa-qasa da muryarta cikin sigar rad'a tace "tabdi, lalle munirat kina qoqari, irin wannan ingarman mijin naki yaushe wasu matan zasu iya dashi, kema fa Dan kina dagewa ne da shan magungunan damuke baki, Amma wallahi da idan ya riqeki, Sai kinyi kuka da idonki"

Murmushi tayi tace"Meji kenan, to waya fada miki baya sakani kukan? Ai ranar dakuka aikomin da magungunan kasa gane Kansa nayi, Nasha wahala ranar harda kuka, har mukaje Saudia a haukace yake "

Dariya suka saki harda shewa, ikee (iklima) data cika bakinta da naman kaza kasancewar tana period bata azumi, tace" ahh waya fada miki mudin na wasa ne? Ai inde kinbi wannan magungunan kina shansu akai akai, wallahi keda kishiya saide kiji anayi a maqota"

Munirat tace "hmm kude kubari kawai, Bari inje insame shi, kunsan shi da shagwa6a yanzu saiya fara min rigima nabarshi shi kad'ai"

Hauwi (Hauwa) tace "A a jeki Kam, adeyi ahankali kar akaryawa megida azumi, Amma fara sallamar mu dadan abun ta6awa saboda shan ruwa, saimu tafi"

Tace "karki damu

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment