Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kudin dayake bashida d'a nashi na Kansa, tausayin sane ya kamata,itakam Dame zata sakawa wannan mutumin a rayuwa? batasan lokacin da hawaye ya wanke mata fuska ba, dama ita Aishan yake nufi? Ashe sunanta yasaka Bana matarsa ba, Bana mahaifiyar saba, wacce irin soyaiya ce wannan?

Cikin kuka tafara Girgiza masa Kai Tace"A a, ban cancanci haka daga gareka ba, matsayi na baikai Nan ba, abun yayi yawa, ka barshi Dan Allah"

Matsowa yayi jikinta, kamar wanda zai rungume ta, Cikin sigar rad'a yace "haba kekuwa,menene abun kuka Kuma? Kinaso kimin asarar Hawayen ki kooo?" yaqare maganar cikin wata irin murya me cikeda fitina,
Matsowa yasake, ahankali yad'ora hannayensa a fuskarta, yariqe fuskar, sannan ya matso da bakinsa dab da fuskarta yad'ora harshansa akan kumatunta, yafara lashe Hawayen datake zubar wa, jin abinda yake ne yasa tarufe idonta ruf..., ta nemi kukan datake tarasa, saida yaji tadena kuka, sannan yahade bakinsu waje daya,al'amarin daya saka duka zukatan masoyan cikin wani Hali na shauqi da begen juna, hakan yasa wannan Karon batasan lokacin data bashi hadin kaiba,Dan qaramin lips dinsa take Sha ahankali, hakan datayi ne yasake gigita Shahaab, cikin fitar wani irin numfashi da tsantsar soyaiya, yake yimata wani irin kiss,gaba daya ya manta acikin dakinta yake, zuciyar sace take zigashi akan yata6a abubuwan Nan guda biyu masu dadin shafawa, wata zuciyar Kuma tana hanashi, daqyar ya'iya zare bakinsa, gudun kada ya aikata abun kunya acikin gidansa yasa cikin mutuwar jiki, yasakar mata kiss a goshinta, tareda miqewa ya fice daga d'akin cikin sauri.



Haka yakoma part dinsu Idonsa cikeda jaraba, yayi mamakin ganin munirat zaune afalo ta dora qafa daya Kan daya, yana sallama ko d'ago kanta batayi ba bare ta amsa, cikin mamaki ya qaraso wajan ta ya tsaya yace"munirat bakiji Ina sallama bane?"

Kamar da dutsi yake magana haka munirat tayi masa banza, ajiyar zuciya yayi, yarasa dalilin yin fishin ta, yace"meyafaru kike fishi?"

Nanma batace masa komai ba tayi shiru, Kansa ya Girgiza kawai yawuce dakinsa, idan ma akan rade radin dayake ji ne matarsa tana fishi saboda yabawa mama company ai yana ganin hakan ba zaisa tayi fishi ba, tunda shide bai futo fili yace budurwarsa yabawa ba, Yan kalamai yayi sannan Kuma yabayar da company, yanzu inda maman yabawa ma kenan haka zata yi fishi? Hakan na nufin idan mama yabawa munirat tana daga cikin Wanda zasuyi fishi akan yayiwa mahaifiyar sa kyauta, maimakon itama tayi kokari tasamu abinda yafi company awajansa, Girgiza Kansa yayi yashige toilet ya watsa ruwa,domin yanayin da yakeji ajikinsa Sai ahankali, Bayan yayi wanka yafuto ya shirya sannan ya kwanta tareda rungume fillo tsam a qirjinsa ya Lumshe Idonsa.

Bayan ya idar da sallar asuba yana dawowa part dinsu yakoma ya kwanta, Bai dade da kwanciya ba akayi masa Kiran gaggawa daga kamfanin su dake lagos, cikin sauri ya shirya ko sallama baiyi da munirat ba yafita yayi part din mama, itama yaga bata tashi ba Sai ma'aikata dasuke aiki a falon, Bai kula gaisuwar dasuke masa ba yajuya cikin sauri yafita, Kai tsaye Airport yawuce daga Nan yawuce lagos.

Meeting suke akan wani tallafi dayake son yiwa mata Wadanda basuda sana'ah.

Saida meeting yayi Nisa aka tambayeshi takardun dasuka fara tsara komai aciki a last Zaman da sukai yadafe Kansa sannan yace"wallahi na manta, Bari nakira Sai abayar akawo"

Munirat yakira, Amma yayi mata missed call kusan hudu bata dauka ba, tunawa yayi tana fishi dashi, saiya Girgiza Kansa kawai yakira wayar mama, mama tana dauka yace"mama barka da safiya"

"barka Mahmud, nafuto yin break Yara suke fadamin kazo"

"eh mama nazo, Ina sauri ne anyi min Kiran gaggawa daga office dinmu na lagos, gashi Ina sauri ma namanta da wasu takardu agida"

"to yanzu Yaya za'ayi? Katuro Ramadan ya dauka"

Tashi yayi yakoma can Gefe, cikin shagwa6a yace"mama kibawa wannan yarinyar takawo min mana"

"wacce yarinya Kuma Shahaab? Inada wata yar ne Bayan Kai?"

Saida yasake yin qasa da murya sannan yace"wannan yarinyar fa....me kula dake "

Mama tasaki Dan qaramin tsaki tace"wai Aisha kake nufi? Shahaab tayaya zan turo ta lagos Bayan bata ta6a zuwa ba? Koba haka Bama agabana jiya kasa yarinyar Nan kuka, idan tazo inda kake Kuma ai sai duka"

Murmushi yayi yace"shikkenan mama, Bari nakira Ramadan din"

Wayar yakashe, yadokawa Ramadan kira, yana dauka Yace"Ramadan wasu takardu nakeso kaje gida kadauko ka kawo min su lagos kokuma kabawa wani daga cikin ma'aikatanmu yakawo min"

Ramadan yace"abokina wallahi Bana gida, madam ta matsa, muntafi yankari, tana so tayi kallo"

Runtse Idonsa yayi, ahankali yace"jarababbe kullum kana gida, ai hutu yaqare saika dawo bakin aiki"

Murmushi Ramadan yayi yace"abar kaza de acikin gashin ta"

Wayar yakashe yasake Kiran mama ta d'auka tace"zaizo?"

Yace"mama baya Nan, yaje Bauchi state"

"tunda kadage Sai yarinyar Nan ta taho de nasan ko yana Abuja abinda zakace kenan,ka fadawa matarka takawo takardun, Sai akawo"

Cikin murna yace"to mama"sannna yakashe wayar

Daya daga cikin sojojin gidan yakira, ya turashi part dinsu sannan ya turawa munirat text, Bayan taga text din saida tagama shan qamshin ta, sannan ta Dauko tabashi, shikuma yaje ya kaiwa mama.

Mama tasa aka kira mata Aisha adaki, Bayan tazo tace"Ki shirya zan aikeki yanzu, zaki kaiwa Mahmud wadannan takardun"

Cikin ladabi ta amsa mata, Sannan ta juya daki, tana tafiya mama ta dauki wayarta tadubo mata wasu dogayen Riguna Masu kyau, tayi oder, Bayan Tashirya tafuto mama tace"zauna akwai kayan daza'a kawo miki yanzu"

Zama tayi tareda fadawa cikin tunani inane mama zata aiketa itada ba ko'ina tasani ba, wani form mama tabata tace"Aisha ga form din banki nasa an kar6o miki, kicikeshi, idan ansamu lokaci saikuje kiyi bvn abude miki bankin"

Cikin ladabi tace"to mama nagode, Allah yasaka da alkhairi "

Cikin jin dadi mama tace" Amin ya Allah "

Sun Dan dade suna jira sannan aka kawo kayan, mama tad'auki ledar tabata tace" to gashi kije kisake shirya wa saiki futo kutafi "

Har qasa ta sunkuya ta karba cikin murna tana yiwa maman godia.

Kai tsaye d'akin Takoma tafara bude kayan, cikin farinciki tasaki wani irin ihun murna tareda fadawa kan gadon, dogayen riguna ne Yan Dubai masu kama da abaya har guda biyar,Sai jaka da takalmi guda bibbiyu, wadda tafi daukan Hankalinta ta d'auka wata baqar abaya wadda akayiwa adon stone a hannu dakuma Qasan a bayar da qirjinta,gaban madubi Takoma tasake taje dogon gashinta, ta daure shi, sannan tasaka rigar, fuskarta babu kwalliya ko kadan kawai lipstick tad'an shafa alips dinta, tayafa mayafin a bayar, tad'auki jakar ta riqe ta kalli kanta a madubi, lokaci daya gabanta yafadi saboda gaba daya ta sauya kamar ba'itaba, ita kanta tasan zuwan ta Abuja ta sauya nesa ba kusa ba.

Futowa tayi zuwa wajan mama, tundaga nesa mama ta qare mata kallo cikin ranta tace"masha Allah "
Aisha tanada kyau, babu Wanda zaiqi Aisha, gata yarinya qarama ga Hankali, Kuma batada girman Kai kasancewar ta yarinya Sai yanda akai da'ita akan komai, saboda idonta bai bude da sanin rayuwa ba, tana wannan tunanin Aishan ta qaraso ta tsugunna awajanta tace"mama nafuto "

Mama tace" masha Allah takwarata kinyi kyau, toga wannan takardun zakije lagos ki kaiwa Mahmud "

Cikin sauri ta d'ago ta Kalle ta"mama lagos Kuma? Ai bansan hanya ba"

Murmushi mama tayi"nasan bakisan hanya ba Aisha, ajirgi Zaki tafi, direba zai kaiki Airport, sannan Kuna sauka a lagos ga wayata Zaki tafi da'ita saiki kirashi kifada masa kinzo"

Hankalin tane yadan kwanta sannan tace"to mama"
Tareda karbar takardun da wayar, direba ne yashigo mama tayi masa bayanin komai daga Nan suka tafi.

Suna zuwa Airport yahadata da wani, cikin kulawa da girmamawa mutumin ya kalleta yace"muje ko"

Aisha tayi mamakin yanda ake bata kulawa awajan kamar yar wani, itade tasan bakowan kowa bace face yar gidan mamuda da Hadiza, Amma sauran mutanan dake wajan kowa Kallan yar gidan Mahmud Wakili yake mata, duba da yanayin shigar ta, dakuma kalar fatar ta, uwa uba yanda ta riqe babbar wayar mama qirar iPhone tana Kallan pictures, kai kace wani abu muhinmi takeyi, tunda ta zauna babu Wanda yayi kasadar qaraso wa inda take, saboda kallo daya zaka mata kasan cewa irin yayan masu kudin Nan ne Wanda ake 6atasu Ana basu manyan wayoyi suna abinda suke so, bata Jima da zama ba jirginsu yatashi zuwa lagos, acikin jirgin de duk Wanda yayi mata kallon qwaqwaf, zaisan atsorace take, kamar ace kyat tazura da gudu, Amma Kuma yanda take kallon window tad'an basar, Sai hakan yasa babu hankalin Wanda yadawo kanta, tunanin rayuwar ta take Wai yau itace a jirgi a dalilin wa dalili ta, basu dauki tsawon lokaci ba suka sauqa a lagos,miqewa tayi tsaye tana daukan takardun, saide dayawa daga cikin mutane kowa yana dauke da jakar Kaya ne, Sa6anin ita da kawai takardu ne a hannun ta Sai yar qaramar handbag dinta, shiyasa kowa kallo daya zaiyi mata yasan cewa lalle yar wani ce, tafiya daga ke Sai takardu? (>��)

Ita kuwa ko ajikinta saboda batasan yanayin ma yanda ake tafiyar ba, wajan sakkowa daga jirgin ma ahankali ta sakko harta futo cikin mutane kamar yanda taga kowa yanayi, wayar mama ta dauko ajaka Takoma Gefe.

Dakanta ta rubuta number,Nan da Nan kuwa sunansa yafuto,MY SON, wayar na shiga yadauka cikin sauri saboda Dama jira suke tun dazu, cikin sauri yace"mama anbata ne?"

Cikin sanyin murya tace"nazo,Ina filin jirgin"

Murmushi amsar ta tabashi, cikin jin dadi yace"Welcome Baby, bani 5 minutes kinji"

Tace"to"

Tana nan a tsaye tsawon wani lokaci saiga kira yashigo wayar, tana dauka direba yayi mata magana akan yazo daukan ta ne, fada masa inda take tsaye tayi, shikuma ya qaraso suka tafi, basu dade suna tafiya ba suka qaraso cikin Babban company, suna tsayawa driver yace"ga hanyar dazakibi Nan"

Ta'amsa masa,sannan ta nufi hanyar tana tafiya, daga can nesa ta hango shi a tsaye agaban wata qofa, yayi kyau sosai cikin suit Amma babu jacket, hannunsa duka biyu zube cikin aljihun wandonsa, ita yake qarewa kallo yayinda bugun zuciyarsa yake sauya wa, Sai yanzu ne yayi danasanin zuwan ta, haka ta taho da wannan shigar tundaga Abuja kowa yana qare mata kallo? Lokaci daya yaji wani irin kishi ya kamashi, ahankali yajuya yashige cikin office din, Aisha kuwa tana ganin shigar sa cikin ranta tace"yayi kyau kamar saurayi"

Ta qarasa wajan kenan zata shiga, wani Dan sanda yataho da sauri yace"ke Ina Zaki shiga?"

Cikin rashin Sabo da shiga waje irin wannan tace"ciki zan shiga"

"kamarya ciki zakishiga, Ina I'd card dinki?"

Bude kofar da akai ne yasa ta kalli kofar, Mahmud dinne yafuto ya kalli Dan sandan, sannan yayi mata alama data shigo cikin office din, cikin sauri Dan sandan ya russuna yace"kiyi haquri Dan Allah, kinji"

Aisha batace masa komai ba, tabi Bayan Shahaab suka shige, suna shiga wani irin Sanyi ya bugeta, Babban office ne Mai d'aukeda manyan dinning table guda biyu, daya kalar baqi ne, dayan Kuma milk ne, a shimfide yake da carpet tareda wani dogon esi a tsaye daga Gefe, ga wata uwar plasma a jikin bango, Sai manya manyan pictures dinsa guda biyu a manne abango, mutane hudu ne a zaune a dogon table din, dukansu suna Sanye da suit, kallon ta suka tsaya yi, cikin ladabi yace"ina kwananku"

Cikin sauri suka amsa mata, Shahaab kuwa ya daure fuska yasa hannu ya kar6i takardun tare nuna mata dayan table din da hannu alamun ga wajan zama, zama tayi tareda zubawa TV ido, inda ake haska yanda yanmajalissa suke meeting akan yanda za'a qara inganta tsaro aqasa, Shima zama yayi, Amma shi fuskantar mutum hudun yake, takardun yaduba sannan ya basu suka fara dubawa suma.

Saida yaga hankalin su yakoma kan takardun sannan yatashi yadauko mata wani Babban tire me d'aukeda flask din ruwan zafi, da Green tea, da madara da bournvita da Nescafe dakuma suger Dan kwali, ya ajiye a gabanta, sannan yad'auki qaramin glass cup da spoon yajefa mata green tea din guda daya acikin cup din,ya sunkuya kamar zai bata, yayi qasa da murya cikin sigar rad'a yace"meyasa kika futo da wannan kayan?"

Itama cikin qasa da murya tace"mama cefa tabani"

Girgiza Kansa yayi, sannan yace"kihada tea Kisha"

Daga masa Kai tayi, shikuma yajuya yakoma dayan table din dasuke zaune, ganyen shayin tacire, tamaidata cikin kwali, ta zuba madara kusan cikin cup din, ta bude bournvita Shima tazuba dayawa, sannan tazuba ruwan zafi tadamasu da kauri kamar chocolate sannan tafara Sha,(=��)

Shahaab dayake kallon ta ta gefen Idonsa cikin ransa yace"quruci dangin hauka... Ko tsoron ciwon ciki batayi

Tanajinsu daya daga cikin su ya kalli Shahaab yace"mutum Dari ne a jikin takardar mu,za'a basu horo acikin camp Bayan an sallami masu bautar qasa"

Yajuya ya kalli na gefensa yace "kayi waya da masu kula da camp, nawa zamu basu tsawon sati daya?"

Cikin sauri yace"aini already munyi waya dasu, sunce abada ko nawane, shine nake Gani why not mubashi kudin Dan kadan, inyaso kowacce Sai a sallameta da dubu ashirin ashirin?"

Shahaab dayake sauraron su yace"amma idan akai haka lissafinmu zai rushe, lissafin da mukai last time kusan million biyar zamu kashe,abashi kudinsa kawai yanda ya kamata, sukuma matan tsawon sati dayan da zasuje suyi a camp din Nan za'a Koya musu cake,popcorn,dakuma donut, ranar dasuka gama abawa kowacce injin aiki dakuma jarin dubu goma,dole za'a rage yawan masu Zaman banza babu sana'ah agari"

Daya daga cikin su dayake rubuce rubuce ya d'ago yace"duk da haka de kudin yafi million biyar, saboda a Kwai kudin abincin su,abinsha, sutura dakuma fetir din daza'a siya saboda kunna inji daddare, sannan matar Nan daga wata qasa zata zo domin training dinnan, itama dole za'a saka kudin sallamarta aciki"

Dariya suka saka gaba daya, daya na gefen yace"wallahi wannan Yacika qaqalo abubuwa"

Aisha data gama shanye hadin madararta, tazuba ruwan zafi a cup din Dan kadan tahada tea dashi marar madara tafara Sha ahankali, cikin zuciyar ta tace"kowa kata6a yacema babu tayi yawa Amma su gasu suna qirga millions"

Kallo ta maida Hankalinta Kai, har suka gama meeting dinsu,baqin suka fita, Shima ya tattara kayansa yace mata"muje ko "

Cikin sauri ta dauki Jakarta tayi gaba, takusa zuwa kofar yasa hannu ya fuzgota, batayi wata wataba tafada cikin faffan qirjinsa, Bai tsaya jiran komai ba yasaka hannunsa ta baya ya rungume ta tsam a qirjinsa, wata irin ajiyar zuciya yake saki kamar Yaron daya dade baisha nonon uwarsa ba, tsawon minti biyu suna haka, ahankali yasakar mata kiss agoshi, sannan yace"good morning"

Murmushi tasaki, bata amsa masaba ta qwace jikinta daga nasa ta nufi kofar, babu musu Shima yabita, Dan Sandan dake waje a tsaye, shi yabawa key din sannan suka tafi shida ita, suna shirin shiga mota driver ya qaraso, cikin kulawa Shahaab yace"malam Hassan babu damuwa ka zauna, zankaita Airport ne"

Cikin girmamawa yace"to yalla6ai a dawo lafiya"


Tunda suka fara tafiya babu Wanda yayi magana, hannu yasa ya kunna karatun alqur'ani suna saurara har suka qaraso wani super Market, kallon ta yayi, yace"muga jakar taki"
Cikin alamun tambaya tabashi jakar, budewa yayi babu komai cikin jakar kamar yanda ya tsammata,hannu yasa a aljihunsa sannan yasaka rafar kudi Yan nera hamsin hamsin kimanin dubu hamsin, sannan yace"kiyi amfani dashi idan kin koma gida"

Mamaki yakama Aisha, kafin tayi magana yafice daga motar tareda shigewa cikin super market din, kayan kwalliya yad'auko mata,da ice-cream dakuma turaruka, sannan yadawo cikin motar yad'ora mata akan cinyarta yace "kiyi hakuri bazan iya kaiki wajan cin abinci ba, saboda yanayin shigar ki, zan iya fada daduk Wanda ya kalleki, haka Kuma ban'isa in Hana a kalleki ba, sannan ko agida ne kidinga saka hijab banaso ko a falon mama nadinga ganinki babu hijab saboda kowanne lokaci mama cikin baqi take maza da mata"

Cikin ladabi tace"insha Allah, Amma wannan kudin yamin yawa, ka ajiyemin awajanka to, idan zan kashe saina dinga karba"

Murmushi yayi baice mata komai ba Kuma bai Kar6a ba, yaja motar suka tafi Airport din, Allah ya temaketa akwai jirgin dazai sake tashi nanda minti arba'in, danhaka yayi parking a cikin airport din suka zauna amota, kasancewar glass din motar tinted ne babu Wanda ma yake lura da motar, ajiyar zuciya yasauke yace"akwai ice-cream aciki ki dauka Kisha kafin kuwuce"

Wani irin farinciki ne ya kamata har yana mamaki, cikin sauri ta bude ledar tadauko babbar robar ice-cream din tadebo a spoon takai masa bakinsa tace"haa"

Murmushi yayi yabude bakin babu musu, cikin ransa yana farinciki kasancewar karatun dayake dora mata yana shiga cikin kanta tun kafin tashigo cikin hannunsa, saida tabashi yasha sannan itama Tasha, saida Tasha ta qoshi ta d'ago ta kalle shi tace "nagode sosai, Allah yasaka da alkhairi"

Cikin sauri yace"wait.... Meyasa ne bakya son Kiran sunana?"

Kallan sa tayi tace"sunan Abbana gareka, bazan iya fadar sunan ba"

Murmushi yayi yace"kamar yanda kike da sunan mama nah,kinga shikkenan nahuta saiki za6amin suna Mai dadi Wanda ya dace Dani"

Murmushi tayi cikin kunya tarufe fuskarta, kallon ta yasake yi cikeda nishadi yace"meyasa baki saka zobe ko agogo a hannunkiba Amma Kuma gashi kin siya kinyi kyauta dashi?"

Ta6e baki tayi tace"babu komai"

Batare da damuwa ba yabude wani waje cikin motar yadauko wani agogo Dan qarami na mata Mai kyau, daga Bayan agogon yaduba yasake gyara na'urar datake jikin agogon, sannan yakama hannunta ya daura mata agogon, cikin jin dadi tace"nagode"

Cikin rashin damuwa yace"ban yarda ba, banason godiar ki, idan kinji dadin kyautar Dana miki yakamata ki nuna min nagani"

Tace"tayaya?"

Kafada yadaga yace"lokacin dakika Bani kyautar naki agogon menayi?"

Idonsa ta sunkuyar qasa sannan tace"kiss"

Murmushi yayi sannan yace "uhm bissimillah"

Babu musu ta dora Dan qaramin bakinta akan agogon tayi kissing dinsa, cikin wani irin kallon soyaiya yace"bahaka zakiyi ba"

yamiqa hannu yakamo hannunta me agogon yad'ora bakinsa yasakar wa agogon wani irin kiss Mai tsayawa Arai, sannan ya maida bakinsa kan Bayan tafin hannunta yafara tsotsar sa ahankali, gabanta ne yafadi, tarasa wanne irin d'a mama ta Haifa, ko kadan baya gajiya da kiss, tanajin sa yanda yake tsotsar Bayan hannun Nata ahankali, salon yanda yake Sha ne yasa taji yanayin ta yana sauya wa, cikin sauri ta qwace hannunta, cikin qanqan da ido yace"why?"
Dan qaramin bakinta ta turo gaba tace"ni.... Nifa wani iri nakeji"

Murmushi yayi yace"Nima haka nakeji, gashi Nima kimin"
Yafadi hakan tareda miqo mata hannunsa

Cikin shagwa6a tace"nide a a, haka kawai daga kawo takardu Kuma mama ta gane abinda nayi, nide tsoro nakeji"

Kansa ya maida kan kujerar dayake zaune yace"Aisha"
Yakirata da wata irin murya cikin rad'a.

Kallonsa tayi tace"na'am"

"inason ki sosai, please karki rabu Dani Dan Allah, kiyi tunani kisa min lokaci inaso inje Inga Abbanki"
Jikinta ne yayi Sanyi, ahankali ta daga masa Kai, tace"insha Allah zanyi tunanin, Kuma zanci gaba da sonka har qarshen rayuwata"

cikin jin dadi yace"kinyi alqawari?"

Cikin sauri tace"eh"

Agogon hannunsa ya kalla yace"nagode, muje na rakaki, lokacin tashin ku yayi"



Mutara zuwa gobe insha Allah =�O�<���



SHAHAAB, littafin kudi ne, idan kika karanta batareda Kin biyani haqqi naba, to ban yafe ba, nabarki keda mahaliccinki

Nera 300 kacal, zaki turo ta account dina kokuma katin MTN ta wannan number

0164549488
Amina muhammad
GTbank

Number 08033300034







Mrs Usman ce
'<���

Bata sake tabbatar da cewa Mahmud Wakili Babban mutum bane saida yariqo hannunta suka qarasa cikin Airport din,mutanan dasuke bashi girma awajan kadai ya'isa ya tabbatar Maka da cewa shi din Mai fada aji ne acikin qasar, yanda yake riqeda hannun Nata hakanne zaisa kagane cewa kode budurwarsa ce, kokuma masoyiyar 'yarsa da yakeji da'ita, mayafin kanta ne yadan zame kadan, gashin gaban goshin ta yadan futo, Dakatawa yayi da tafiya ya fuskanceta ya tsaya ya danja mata mayafin abayar har kan goshinta, yanda gashin zai rufu, sannan sukaci gaba da tafiya, Hauwi dake Gefe itada ikee suka saki wani irin murmushin kissa, cikin sauri batareda Shahaab yasani ba, suka dauki photonsa shida Aisha,ko minti biyar baiyi ba ma'aikatan wajan suka qwace Aisha daga hannunsa acewarsu tunda suna Nan ai babu amfanin zuwan sa wajan da Kansa,=��
hannu ya basu sukai musabaha daga Nan yajuya cikin sauri da wannan takun nasa na jarumai Kuma jajurtattun mazaje.

Wani ke6an tattacen waje aka kaita, tana zaune tana tunani kode takira Hajja da wayar mama su gaisa dasu Ummah kafin tabawa mama wayarta?
Wata zuciyar tace meyakaiki? Kina yar aiki meyasa bazaki karbi wayar masu aiki yan'uwanki ba? Saita sake tunanin cewa tana gama wayar Kuma ai zata goge number, cikin sauri tad'auki shawarar zuciyar ta, ta danna number Hajja aikuwa waya tashiga, saide harta katse, Hajja bata dauka ba, tsaki tasaki, tana kewar Yan gidansu sosai, tunda tazo saudaya sukai waya, jitake kamar tayi tsuntsu taganta acikin gidansu.

Sake Kiran tayi, Shima harta gama ba'a dauka ba, wasa wasa har saida takira Hajja sau hudu, bata dauka ba, daga qarshe Sai hakura tayi tadena Kiran, tayi saurin goge number Hajja din, d'ago kanta tayi tana kallon ma'aikatan wajan yanda kowa yake abun gabansa, wani irin haske tagani kamar na camera anyi mata photo, tajujjuya taga bataga komai ba, saita daga kafadunta alamun shikkenan, Adede lokacin Kuma wani ma'aikacin yazo yace tatashi suje, jirginsu zai tashi.


Hauwi ta kalli ikee tace"kinga abinda muke fada ko? Wannan yarinyar ba itace munirat tace mana baquwar mama ceba?"

Ikee tace"ai gashinan tana zaune yarinya qarama zata qwace mata mijin, Dan Allah kiga yanda yawani riqo ta harda gyara mata mayafi saikace wata matarsa, waya San ma daga Ina suke? Idan kika bincika ma may be yarinyar tasaba zuwa suna sheqe ayarsu anan, inba hakaba Ina baquwa ina Hawa jirgi?"

Hauwi tace"nima tunanin danayi kenan, yariqe hannunta qam yaki saki ko kunyar mutane bayaji, ai daga Gani ma Dama can kinsan tasaba dashi, aini tundaga lokacin da munirat tacemin mahaifiyar sa tariqe yarinyar shikuma yana ta6a mata nono, nasan da walakin Goro amiya, ai uwarsa ce ta daure masa gindi"

Ikee tace"bakiga suma ma'aikatan wajan yanda jikinsu yake rawa ba? Suna wani bata girma saikace yar gwamna, basusan baquwa ce tazo cin Arziqi ba, kiduba kigafa ko kayan hannunta basu dubaba suka Barta tashige dashi"

Hauwi tasaki ajiyar zuciya tace"yanzu Yaya zamuyi da wannan pictures din? Muturawa munirat kawai, taga abinda mijinta yakeyi da baquwar datake cewa tasan mijinta baya kula mata Dan haka bazai kula wannan yarinyar ba"

Ikee tasaki dariya tace"bakida Hankali, tunda kikaga yana rawar jiki yana Bawa yarinyar Nan kulawa daga qarshe aure ta zaiyi mu muna zaune, uwarsa bazata hanashi ba tunda Dama so take yayi auren, ga shawara, mezai Hana muyi amfani da fuskokin su, mudora fuskar akan wani vedio din kawai sai mu turawa uwarsa da Kuma munirat din, suna Gani kinga mun tada fitina, daga qarshe mu ziga munirat yanda zata daga Hankalinta hartasa yasake ta, shikuma uwarsa ta hanashi mu'amula da wannan yarinyar, kinga daga qarshe mu saimuyi wuf dashi"

Dariya suka saka harda tafi, suna wannan dariyar sukaji sanarwar jirgin rivers zai tashi, cikin zumudi suka tashi, dama kowacce ta gaqu ta ganta awajan Nata Alhajin.

Suna sauka taga driver daya kawo ta yana jiranta, da alama Shahaab yafada musu sun taso ne,wajan sa ta nufa tashiga motar suka tafi gida, suna zuwa gida ta wuce part din mama, cikin murna mama ta kalleta tace"um um kaga yanmata, yau anhau jirgi Sai Fara'ah kike kamar gonar auduga"

Cikin murna ta zauna aqasan kujerar da mama take zaune tace"wallahi mama naji tsoro sosai,amma daga baya sainaga abun ma babu wahala Kuma Nan da Nan Naga har munje"

Mama tace"to Alhamdulillah, ya hanya?, nasan halinsa,inji de baiyi miki fada ba?"

"A a mama, baimin komai ba, yayimin magana de akan mayafin dana yafa, Wai meyasa bansaka hijab ba,? sainace masa aikece kika Bani kayan, shikkenan Sai yayi shiru, kinga ma abunda yasiyamin"
Tafadi hakan tana miqawa mama ledar hannun ta, mama ta kar6i ledar ta bude, turarukan data ganine yasa gabanta yafadi, idan bata manta ba akwai lokacin dasuka fita yawo ita dashi zuwa Cairo, tata6a ganin irin wannan turaren tace masa ya siyawa munirat shi, Amma firr yaqi siya yace turaren yayi kudi dayawa, Amma abun mamaki gashi ya siyawa Aisha, tasake duban kayan kwalliyar taga kayan kwalliya ne masu mutuqar tsada Wanda ita kanta Aishan ma tana da tabbacin batasan Yaya ake amfani dasu ba, kafin tagama tunani taji Aisha tace"harda wannan agogon na hannu na ma mama, shine duk yasiyamin, kiyi masa godia mama"

Mama ta kalli Aisha da sauri, tasake Kallan agogon hannunta Wanda kallo daya ta masa ta tabbatar da na gold ne, lokaci daya Kan mama ya d'aure(=��)

Cikin mamaki Tace"A a, Wai duk Shahaab dinne yabaki wannan kayan?"

Aisha da bata gane yanayin fuskar mama ba tace"shine mama"

Mama ta kalleta tace"toki adana agogon ki dakyau kinji? Karki Bari wata tayi miki wayo ta qwace miki, yanada tsada sosai"

Cikin sauri ta d'ago ta Kalle mama tace"mama toki Kar6a kisaka a hannun ki, nabaki duka"

Ta qarasa maganar tana murmushi tana qoqorin ciro agogon, mama tayi murmushi ta Girgiza

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment