Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana fadin "to mama, gatanan zuwa"

Cikin zuciyar ta tace "kome take buqata Kuma? Jarababbiyar tsohuwa kawai"

Kallanta yayi yace "kije inji mama"
Daga Nan yawuce toilet.

Bata dauki dogon lokaci ba ta wuce wajan mama, tana zuwa mama tabata kayan data ware tace "ga kayan sallarki Nan, wannan Kuma ki aikawa tsohuwa, inji Dan Albarka Mahmud Wakili"

Maganar tamata ciwo, domin kuwa wani qullutun baqin ciki ne yatokare mata maqoshi, ahankali ta daga mata Kai, cikin ladabi tace "to mama mungode, Allah yaqara Arziqi"

"tun kafin kizo Arziqi Kam Dama can yana qaruwa, ke kanki Arziqin ne ya janyo ki, tashi kibani waje"

Wannan Karon munirat batace komai ba, tatashi tatafi.
Tana zuwa Kai tsaye d'akin sa ta wuce ta zubar da kayaiyakin akan gado, sannan ta zauna aqasan gadon tafashe da Kuka, yana futowa daga wanka yaganta tana kuka, ya kalli kayan dake kan gado, sannan ya dawo da kallon sa gareta yace "menene yake faruwa?"

Cikin kuka tace "yanzu abunda akemin a gidan Nan hakan adalci ne? Ni banida ikon siyo abinda nakeso kullum saide asiyo abani? Mama tayi Kane Kane akan komai nikuma anmaida ni saniyar ware"

Ajiyar zuciya yasaki, baice da'ita komai ba,Dan qaramin towel din hannunsa yad'ora a lallausar fatarsa datake shinning,saida yagama goge jikinsa sannan ya zauna abakin gadon dab da munirat

Ahankali yace "munirat... Mama mahaifiyata ce, nayi tunanin yanda na dauki momynki a matsayin uwa, kema hakane,wani lokacin rikicin mama harda na tsufa, ni abinda nasani arayuwata shine inason mama, Kuma inason duk abinda takeso, karki manta dede da second daya banta6a ganin fuskar mahaifi naba saide a photo, mama itace komai nawa, itace uwata, itace ubana, tamin gatanda ko mahaifina yana Raye abinda zaimin kenan, duk lokacin da mama ta 6ata miki rai kidauka momy ce ta6ata miki, babu yanda zakiyi da'ita, a koda yaushe inaso ne kitayani yimata biyaiya nasamu narabu da'ita lafiya.... Ta hanyar biyaiyar danake mata ne zaisa inshiga aljanna munirat, nikaina nasan wani lokacin Rikici ne kawai irinna mama Amma a hakan nake goyon bayanta Dan in rabu da'ita lafiya, Amma ke kin kasa gane hakan, idan momy ce ta zazzageki wazaki kaiwa qara? Babu Wanda Zaki fadawa saide ma kibata haquri, to inaso kidauki mama kamar momy, idan kikamin hakan kingama min komai munirat.... "

Jikinta ne yayi Sanyi Bayan tagama Sauraron kalamansa, lokaci daya ta sauya kukan Nata ya dawo na kissa, cikin wani irin Salo tace"ainima Bahaka nake nufi ba, Ina kuka ne akan irin wariyar da mama take nunamin, yanzu wannan kayan waye zai dinka min insaka su jibi? Ai Yanzu ni a ganina mama ta wuce ace itace zata dinga siyo mana Kaya, a matsayi na namatarka ainice yakamata ace nasiyo mana, ita Kuma mama ta huta, ni bansan meyasa mama bata sona ba"

Runtse Idonsa yayi, bayason jin kalmar Nan datake fada akan mama, cikin sigar lallashi yace "yanzu me kike so?"

Ahankali tace "ni wannan kayan basumin ba, Kuma momy ma ta dade da dinka irinsu, saide nabawa ma'aikata su, inyaso nida momy muhaqura"

Ahankali yace "a a, ki dauki kudi acikin briefcase dina, saiki siyo muku Wanda kike so, shikkenan?"

Cikin murna da farinciki tace "eh, nagode my Dear"
Tafadi hakan tareda rungume shi ta manna masa kiss akan lallausan lips dinsa.
Cikin wata irin murya yace "Bari mana munirat azumi fa"

Murmushi tayi, tazuba masa wata irin hararar masoya, sannan tafice daga d'akin.



Mutara zuwa anjima, insha Allah zaku samu update =�O�<���

To Aisha de tace ta yanke alaqa tsakanin ta da Hajja=��

Ko Yaya za'a qare akan takardun filayen mama? >��


Bazan tsaya Ina Allah ya'isa akan novel ba, Amma duk wacce ta karanta min littafi batareda ta biya ba nabarta da mahaliccinta, saboda nide ban yafe mataba


Mrs Usman ce
'<���

Page 19&20



Atamfa ce turmi uku da wani yadi irinna maza Mai kyau agaban Ummah da Abba, Bayan Ummah tagama Gani tace "mukam kasan ba zamu samu dinki yanzu ba, saide Bayan sallah mesunan qawar Hajja sai takai mana, Amma Naka Dana Jabir bansani ba ko zaku iya samu"

Aisha datake kwance akan gadon Ummah tana Kallan su batace musu komai ba, har yanzu idan tatuna fad'an da sukai da Hajja jiya ranta sake 6aci yake, kullum sukai fada da'ita saita sako iyayenta aciki.
Kafin Abba yayi magana Hajja ta doko sallama cikin d'akin, kallanta yayi yace "Hajja sannu da zuwa"

Tace "sannu mamuda, a zaune kuke?" bata jira amsar dazai bata ba tad'auki jakar kayan Aisha, Aisha tana ganin haka ta juyar dakanta Gefe ko kallon Hajja batayi ba, Hajja ta kamo hannunta tace "tashi mutafi mana mesunan qawa, duk fadan da mukai dake ai Bama raba makwanci, Amma jiya har kayanki saida kika kwashe, meyayi zafi haka? Tashi mutafi madubinki yana Nan nasake goge miki shi kiji dadin Kallan Kallan da kike" (>�-�=�F�<���
@&�)

Cikin sauri Aisha tatashi, ganin irin kato6arar da Hajja takeson yimata agaban Abba, Wai mutum da abunsa danya kalla shikkenan Hajja ta dinga magana daya, saukowa tayi daga gadon tana tura baki gaba, suka futo daga d'akin Kai tsaye suka koma cikin Dakin Hajja.

Suna zama Hajja tace "yanzu mesunan qawa abinda kikai ya kamata kenan? Ki hadani da walakiri, aiko maqiyi na bazai min irin wannan fatan ba"

Aisha tayi shiru batace mata komai ba, Hajja tasaki ajiyar zuciya tace "shirya muje kasuwa musiyo kaji da d'an kayan miya muzo mu gyara gobe Sai ai miyar sallah dasu"

Tashi tayi tad'auki hijabin ta tasaka sannan cikin qasa-qasa da murya tace "muje"


******

Yana zaune a office dinsa Bayan yagama ganin mutanan office din nasu Wanda suka masa sallama saboda tafiya garuruwan su hutun sallah, Shima tunani yake Ina yakamata ace yaje ya huta?
Itace tafad'o masa, to kode ziyara zaiKai matane? Mamakin Kansa yake, duk lokacin dasuke samun hutu irin wannan babu abinda yake tunawa illa munirat, yanda zai dauketa sutafi wata qasar suje Sud'an huta sannan su dawo, Amma yau kwata kwata yakasa tunawa da'ita, cikin zuciyar sa yace "tunda ba sonta nake ba menene zai dameni dannakai mata ziyara?, to Amma idan naje mezance mata? Wancen Karon akwai dalilin daya kaini, Amma yanzu fa?"

Afili ya furta "babu dalilin zuwan" duk yanda zuciyarsa taso hanashi, haka yaqi yarda, ahankali yad'auki wayarsa yadubo number ta daya d'auka ranar dayaje, batareda tunanin komai ba ya danna mata kira.


******
Suna futowa daga gida sukaga wani me adedeta, cikin sauri Hajja tace "Tsaya! tsaya!! d'an sahu"

Tsayawa yayi, Aisha tace masa "kasuwa zaka qarasa damu"

Yace "ba haya nake yi ba"

Cikin sauri Hajja tace "haba kaikuwa yaro, Nima nasan ba hayar kakeyi ba tunda mukam agarin Nan Ina mukaga wani adedeta sahu, saboda Allah zaka kaimu saina baka 'yar nera hamsin kasayi gasara Kasha ruwa da magariba"

Murmushi yayi yace "tokushigo"

Shiga sukayi, sun fara tafiya kenan wayar Hajja tad'auki qara, cikin mita tace "Kai wannan jaraba da yawa take, da ranar ma baza'a bar mutum ya huta ba?"

Aisha tace "to idan ba'a kiraki da rana ba cikin dare kike so a kiraki?"

Cikin mita tace "aikuwa koma waye bazan dauka ba,da azumin zanji koda Kiran waya?" tafadi haka tareda kashe wayar

Daga nasan bangaren mamaki ne ya kamashi, kamar fa rejecting din Kiran akayi? Metake da wayar zata katse masa kira? Wata zuciyar tace "kasani ko game takeyi?"
Ahankali yace "may be" sannan yasake Dialing number, wannan Karon Kiran yana shigowa Hajja tasa hannu zata kashe Aisha tace "Bani In dauka"

Babu musu Hajja ta bata wayar, ahankali cikin zazzaqar muryarta tace "Hello Salamu Alaikum"

Atsaye yake, Amma yanda yaji muryar Tata tana neman kashe masa jiki, saiya nemi kujera ya zauna tareda Lumshe Idonsa

A 6angaren Aisha kuwa dataji shiru saita sake cewa "Ba'a jinane? Wake magana ne?"

Hajja tace "maganinki kenan, kina ganin number special kece mecewa Zaki dauka, baki Sani Bama ko masu shan jini ne"

Dariyace ta kamashi, Kuma bayason taji shi, Sai yayi sauri yakashe wayar, yana cikin murmushi Ramadan yashigo office dinsa, cikin mamaki yace "Abokina lafiya?"

Saboda Rabon daya ganshi yana irin wannan farincikin harya manta, ahankali ya girgiza masa Kai, sannan yace "nothing"

Aisha kuwa dataji an kashe wayar, saita Bawa Hajja wayarta, me adedeta yace "Hajiya Kidena futowa da waya fa, kinganni Nan, to yau -yau dinnan nafuto daga gidan yari, Kuma satar waya ce takaini, gobe sallah idan kinsan ma zakije wajan idi toki tafi da paper da biro duk Wanda yace kibashi number ki saiki bashi paper ya rubuta miki, kema ki rubuta masa, saboda zamuyi patroll goben"

Cikin sauri Hajja tasake qanqame Jakarta, tace" innalillahi.... Aikuwa Gara daka fada mana Kai 6arawo ne, tsaya ka saukemu anan "

Cikin dariya yace"mama ni bazan muku komai ba, inda zan muku da tuni na zubar daku, kawai de fada muku nake ku kiyaye "

Cikin tsoro tace"to mungode, Kuma zata kiyaye, kasan jikar tawa farinjini ne da'ita kamar kudi, Yanzu haka me Kiran ma inka bibiya mashinshi nintane".


Suna zuwa kasuwa ya saukesu, Bai kar6i kudin su ba, godia suka masa sannan suka shige suka sayi abinda yakawo su, sannan suka juyo gida,ummah ce ta gyara kayan miyan jabir yakai wajan niqa, Aisha Kuma ta gyara kajin ta soya su, Hajja Kuma tadafa musu jallop din macaroni da sauran man da Aisha tayi suyar kajin dashi, sannan sukai wanka suka zauna kowa yana jira Asha ruwa.

Washe gari sallah, karfe bakwai da rabi Aisha da jabir da Hajja A'i suka shirya suka tafi masallaci wajan sallar idi, aqafa suke tafiya ahankali suna tafe kowa bakinsa d'aukeda zikiri, jabir yana Sanye da yadi ajikinsa medan sauqin kudi, Hajja ma taci atamfar ta sabuwa wadda ta dinka da kanta, Aisha kuwa atamfar da inusa ya dinka mata, itace ajikinta, sun sanya sabon hijabi iri daya itada Hajja, Wanda Hajjan ce ta dinka musu.

Suna zuwa masallacin Hajja ta dubesu tace "ikon Allah, dama wannan ne sabon masallacin da'aka Gina?"

Jabir yace "shine Hajja, ga wajan mata can, saiku qarasa, idan an idar kujirani zanzo mutafi"

Hajja tace "to ni yanzu wannan danqareren masallaci da Bismillah zan fara shiga kokuwa?"

Aisha da taqaici ya kamata ta juya fararen idonta tace "Da zagi Zaki shiga, haba Hajja, wani lokacin kidinga abu kamar wata tsohuwa"

Murmushi tayi tace "Allah sarki, mesunan qawa menene Kuma yarage? Tsufa kan ai mun tsufa, saide fatan Inga takwararki, Kuma incika da Imani"

Hannunta Aisha taja batare datace komai ba, suka shige cikin masallacin, sallaya ta shimfida musu suka zauna, basu sake magana ba kowa zikiri yake cikin ransa,basu dade da zama ba wani mutum yazo yana kar6ar sadaka, Hajja ta bude gefen zaninta tabashi nera Dari, Aisha tayi murmushi tareda jijjiga Kai, cikin ranta tace "lalle Hajja yau take sallah"

Bayan sun idar sun koma gida, anan sukaga har Ummah takusa kammala abinci, Aisha ce tacire hijabinta ta kama mata aikin, Nan da Nan suka gama, mutane Sai shigowa suke anata gaisawa, masu shagunan caji Sai kunna waqa suke a mp, Bayan sunci abincin Aisha tayi wa Ummah magana tana so taje gidansu Walida, abinci Hajja tabata tace "kafin ki wuce kishiga ki kaiwa jummai abincin Nan"

Kar6a tayi sannan ta wuce.


******

Acan gidansu mama kuwa hidima tayi yawa, kamar Wanda ake dan qaramin biki, mama tana zaune tana ganawa da mutane masu zuwa yimata barka da sallah, kudi ne masu yawa agefen Dan qaramin fillon kujerar datake Kai, duk Wanda ya tsugunna ya kwashi gaisuwa idan yatashi tafiya haka zata dauki kudin tabashi, Shahaab kuwa bata ganshi ba, tasan yana can waje yana Fama da nasa mutanan, abinci ma bai samu damar zuwa yaci ba, Kuma tasan munirat bata nemeshi akan hakan ba, to itama dasuke zaune gida daya batazo ta gaishe taba bare tayi mata barka da sallah, batasan wacce irin mata Allah yabawa Mahmud ba, kafin tagama tunanin Nata yashigo cikin falon Nata yana Sanye cikin manyan Kaya farare tas,shadda ce dataji dinki Mai kyau da tsari, yasaka babbar Riga, hatta takalmin qafarsa fari ne, yayi mutuqar kyau kamar ka sace shi ka gudu, kasancewar baya saka manyan Kaya kullum Sai suit, Sai hakan yaqara qawata kyan halittarsa, Sai tashin qamshi yake Mai dadi, yana qaraso wa kusa da'ita duk mutanan falon suka tashi suka fice, Kallan sa tayi cikin farinciki tace "masha Allah, Mahmud kayi kyau sosai, yanda kake da kyan Nan Allah yabaka kyakykyawar amarya ku haifomin kyawawan jikoki"

Inda Dane tafada masa hakan bazai ji dadi ba, Amma yanzu wani irin murmushi yayi, tana cewa kyakykyawar amarya, itace ta Fado masa, baisan Ina yarinyar ta kwaso kyau irin haka ba, saikace aljana, cikin murmushi yace "Amin mama, dafatan kinyi sallah lafiya"

"Alhamdulillah Shahaab, ya munirat? Tayi sallah lafiya?"

Cikin mamaki ya kalleta "kamarya? Batazo bane?"

Tace "a a, nida ba nice na haife ta ba, Yaya za'ayi tazo ta gaishe ni, Amma nasan idan mahaifiyar ta tana cikin gidannan bazai iyu a kwana atashi, taqi zuwa ta gaishe ta ba"

"mama kiyi hakuri, zanyi mata magana"

"a a, rabu da'ita, inda Sabo ai yaci ace nasaba da halin munirat, dama kaina ke jira, inaso kasiyomin ticket,gobe zanje marad'i ganin dangin babanka, idan zakaje Kuma saika siyo mana mutafi"

Cikin sauri yace "a a mama, kijeki, ni jigawa zanje"

Cikin mamaki tace "jigawa Kuma?"

Sai yanzu ne ya gane irin Shirman Dayayi, cikin sauri yasake cewa "Eh... Eh.... Ina nufin akan aikin gidan marayun Nan"

Ajiyar zuciya ta sauke tace "to Alhamdulillah, nayi tunanin wani abun ne yataso"

Ahankali yace "a a, Amma mama kwana nawa zakiyi kidawo? Kwana uku yayi?"

"haba Shahaab , har yanzu de kana Nan da halinka bakason inje unguwa in zauna? Kwana biyar nakeso nayi, idan kajini shiru Kuma to sati daya zanyi"

Cikin ladabi yace "to shikkenan mama, Allah ya dawomin dake lafiya,saimu fita goben Nima gobe nakeson wucewa"

Tace "Allah yakaimu, tashi muje nabaka abinci"
Babu musu yatashi suka nufi dinning

Bayan yagama cin abinci fita yayi daga gidan, baije part dinsu ba Sai Bayan ya dawo da daddare, baiyi wa munirat maganar mama ba, yasan Bayan fitarsa zataje su gaisa, abinda bai saniba kuwa shine mama ko idon munirat bata Gani ba, washe gari karfe goma suka shirya shida mama suka tafi, Bai fadawa munirat inda zaije ba, yadai fada mata cewa sunyi tafiya shida mama, mama tayi tunanin Dasafe kafin su tafi munirat zatazo, shiru shiru bata zoba harta fidda rai, haka motoci guda biyu suka rakasu Airport, mama ta wuce Niger, shikuma yawuce Jigawa.


Wannan Karon ma a hotel ya sauka, tunda yamma yake shirin tafiya wajan ta, Amma idan ya tuna maganar Ramadan cewa akwai Wanda suka sanshi agarin, Sai yaji wani irin taqaici,yanason yaganta dawuri kodan yasata agaba yadinga kallonta harya gaji, shi Kansa yarasa meyasa yake murna da zumudin zuwa wajan ta.
Da daddare wata shigar yasake kamar ta jiya, manyan Kaya yasaka harda babbar riga, saide jiya shigar fararen Kaya yayi, yau Kuma light blue ne, shi Kansa daya kalli Kansa a madubi saida ya jinjinawa Hajja data iya auren kyakykyawan babansa Dan Nijar har Allah yasa Shima ya'iyo kamar baban nasa, saikuma yayiwa Allah godia bisa ni'imomin Dayayi masa, turare yafara fesawa kamar wani sabon ango, sannan yasaka face mask,yafuto a gurguje yashiga motarsa, rabonsa da driving harya manta, Sai yake jin wani irin nishadi a ransa, yana tafiya ahankali yana Sauraron yanda gidan Radio suke labarai na gaishe gaishen sallah, Ahaka harya qarasa cikin Garin, yau Garin yaga Yacika da mutane Kuma ga manyan motoci Nan alamun duk wasu wanda basa zama agarin ma sunzo gida bikin sallah, a'inda suka tsaya rannan shida Ramadan yauma anan yayi parking, face mask dinsa ya danja qasa, sannan yad'auki wayarsa yafara Kiran number ta, saida yaji tashiga sannan cikin ransa yace "yanzu da wayar akashe take Yaya zanyi? Ahankali yasake cewa" Sai inje gidan inyi sallama idan mungaisa dasu infada musu wajan yar qarama nazo"(>�-�)

Saida wayar takusa katsewa sannan yaji an dauka, ahankali kamar Wanda yake rad'a yace
"inajiranki a kofar gida"

"waye?"

Shine abinda tace, cikeda tsananin mamaki

Kai tsaye yace "SHAHAAB"

gabantane yafadi harsaida tasa hannu akan qirjinta, idan bata manta ba mutumin dayazo da Azumi yakawo musu kayan abinci har yace mata shi Yaron Mahmud Wakili ne, shine Shahaab, toba rannan yazo ba? Meya dawo yi wajan ta?

Kafin tagama tunani taji yace "I'm waiting for you"
Sannan ya katse wayar, ahankali ta dauki dogon hijab dinta Wanda yazo mata har qasa,haka tafuto daga d'akin kamar kazarda qwai ya fashewa, Ummah na banda ki danhaka ta kalli Hajja tace "Hajja inada baqo a kofar gida, zanje wajan sa daga Nan natafi gidansu Walida, yanzu zan dawo"

Hajja zuciyar ta daya tayi tunanin Inusa ne, Kai tsaye batare da tantama ba tace"ki gaishe ta"

Tana futowa qofar gida ta hango motarsa, Kai tsaye wajan ta nufa, tana zuwa ta Qwanqwasa masa glass din motar, ahankali ya sauke glass din, yana ganinta gabansa yafadi, cikin zuciyar sa yace "yasalam!"

Sannan yabude motar yafuto, ganin wajan babu mutane sosai yasa yakama hannunta yajata ta dayan site din, samun Kansa yayi da bude mata motar, sannan yasaki hannunta ya kalleta tareda nuna mata cikin motar yace "Bismillah"

Kallan sa tayi,tana mamakin yanda Babban mutum dashi Amma yake bude mata mota, yakamata ace tatakawa mutumin Nan birgi akan yanda yake riqe mata hannu kamar wata matarsa, kallansa tayi wata zuciyar tana hanata shiga, Amma ganin shi din Babban mutum ne, a shekaru ma zai iyayin na Abban ta, Saitayi Bismillah tashiga, rufewa yayi, sannan ya zagaya yashiga shima ya zauna tareda rufo motar, juyowa yayi yana fuskantar ta,Kallan ta yafara kamar zai had'iyeta, fuskarta babu kwalliya Amma saiyaga tamasa kyau sosai, cikin ransa yace "yar qarama Kyakykyawa".

Aisha kuwa jitayi motar wani irin sanyi, ga qamshi yana tashi, ahankali ta kama yatsun hannunta tana wasa dasu, kanta yana qasa, ko kadan takasa kallansa,wani irin kwarjini yayi mata musanman yau data ganshi cikin manyan Kaya, tana ganinsa ta Qasan idonta yanda ya zuba mata Ido kamar yanason Gano wani abu a fuskarta, Itakam tana zaune ne, Amma azahiri gabanta faduwa yake, saboda bata taba shiga mota mekyau irin wannan ba tunda take a rayuwar ta, acikin motar ma Kuma da wani namiji, ganin har yanzu yakasa yimata magana yasa tace "Ina wuni"

Saitaji yayi shiru,ahankali tad'an d'ago kanta ta kalleshi tace "Ina wuni"

Cikin sauri ya dawo hayyacinsa, ajiyar zuciya yasaki sannan ya gyara zamansa, ya kalleta cikin qasa-qasa da murya yace "Lafiya"

Daga Nan babu Wanda yasake magana, kusan minti takwas shiru, taga babu abinda yace, Sai aikin kallonta kawai yake,ahankali ta motsa d'an qaramin lips dinta tace "zan'iya tafiya?"
(tab! yaufa Ana zance anan=�
�>�#�=��)
Amnah El Yaqoub
'<���

Page 21&22






Cikin sigar rad'a yace mata "meyasa?"

"gidansu Walida nakeso naje Dama, inaso ta rakani shago"

"what will you buy?"

Kai tsaye tace "biro"

Mamaki ne ya kamashi, gata de yar qarama, Kuma tatashi acikin qauye, Amma tana danjin Dan qaramin turancin dayake mata, samun Kansa yayi da cewa "muje na rakaki?"

Cikin sauri ta kalleshi, tab, Ina zata Iya tafiya dashi acikin Garin Nan, ai kowa kallon dazai mata daban, ahankali ta girgiza masa kanta alamun a a, sannan tasa hannu zata bude motar tafita, cikin sauri yamiqo hannunsa yad'ora akan Nata hannun da nufin hanata fita daga motar, juyowa tayi ta kalleshi har kusancin nasu yayi kusanci tana iya jiyo daddadan qamshin turaren dake tashi ajikinsa, ganin kamar tana tsorace dashi ne yasa ahankali cikin sigar lallashi yace "kina jin tsoro nane?"

Girgiza masa Kai tayi, ahankali yasake cewa "to meyasa kike son ficewa daga motar?"

Ahankali tace "toka matsa mana"

Wani irin murmushi yasaki, sannan yadauke hannunsa dake kan Nata hannun, sosai yayi mamakin furucin ta, ita yanzu tsoro take kartaje yayi mata wani abu, Sai maganar Tata tabashi dariya saboda shi yar qaramar yarinya yake ganin ta, babu yanda za'ayi yayi mata wani abu makamancin Wanda take tunani, yana jin nishadi atare dashine idan yana tareda ita, Sai yake ganin ta kamar wata 'yarsa, inda ace a gidansa take bayajin akwai yarinyar dazata nuna mata gata, to Amma Yaya zaiyi? Allah bai bashi haihuwar ba.

Cikin murmushi yace "Na matsa, shikkenan?"

Kallan sa tayi, taga yanda dimples dinsa suka futo, Sai taga yayi mata kyau, ahankali tace "to intafi?"

"meyasa kike son tafiya ne? Kinsan tundaga Ina nazo wajanki? To tundaga maiduguri"

Zaro idonta tayi,(=�3�)cikin mamaki tajuyo tana fuskantar sa batama San tayi hakan ba,tace "maiduguri? Tome kazoyi Nan Garin?"

Sosai yaji dadin yanda tafara sakewa dashi, cikin farinciki yace "wajanki nazo"

Tace "wajena Kuma?,to meyasa?"

Yace "wancen Karon nazo natafi, ban tambayeki sunanki ba, shine nazo kifada min yanzu"

Cikin tsananin mamaki tace "sunana kawai? Saboda sunana kayi wannan doguwar tafiyar? aikuwa da matarka taji dalilin zuwanka wajena, dasai tayi fishi dakai"

Cikin mamaki yace "waye yace miki inada mata?"

Tace "aikai babba ne, nasan kanada mata, da Yara"

Jikinsa ne yayi Sanyi, haka kawai saiya samu Kansa da fada mata gaskiya "banida Yara"

Cikin tausayawa tace "to Allah yakawo masu Albarka, insha Allah watarana matarka zata haihu"

"Wai waye yace miki inada aure ne? Ni banda aure, very soon de nakeson yin auren"

Sai Bayan yafada mata hakan, Sai yake tambayar Kansa menene ma abun 6oye 6oye? Meyasa zai 6oye mata yanada mata? To Amma yanzu idan ya dawo yasake ce mata yanada aure zata raina shi, zata dinga ganinsa kamar qaramin yaro me magana biyu, danhaka kawai saiya share zancen.

Aisha tad'an kalleshi tace "insha Allah zan fara azumin sitta shawwal, inyi ma addu'ah idan kayi aure Allah yabaka 'Ya'ya masu Albarka"

Cikin tsananin mamaki ya kalleta, zatayi azumi tayi masa addu'ah akan Yara? Abun mamaki, munirat bata ta6a fada masa hakan ba, gashi de itace wadda zata Haifa masa yaran, Amma ko kadan haihuwar bata gabanta, ganin kallon dayake mata ne yasa tace "lafiya?"

Ajiyar zuciya yasauke yace "no, babu komai, kawai... Kawai... de inajin dadin kasancewar ki atare Dani yanzu"
Yafadi hakan yana Lumshe Idonsa.

Yanda yafadi maganar yake Lumshe ido Sai hakan yasa taji wani iri ajikinta, cikin kunya tasa tafukan hannunta tarufe fuskarta cikeda kunya.

Murmushi yayi, cikin dabara yace "Ina Alhajinku megidan Mai?"

Cikin sanyin jiki tace "yana Nan, yazo sallah ma"

Kansa ya Jinjina, tunda yaji batayi masa maganar gidan man ba, yasan har yanzu basu saki gidan man nasaba, Amma yayi mamaki sosai, tunda shine yabada umarni zuwa wannan lokacin ai ya kamata ace anbashi gidan mansa.

Yace "aikuwa nayi wa ogana maganar gidan mansa, insha Allah zaiyi magana, nasan zasu saki gidan man"

Tace "hmm, kaifa bakasan halin wannan ogan Naka bane, nafada maka bashida mutunci, uhmm... Inama zan ganshi, wallahi dasai yagane kurensa" (=�F�<���
@&�)

Runtse Idonsa yayi, cikin zuciyar sa yace "to masifar Tata tazo"

Kafin yabude baki yace wani abu tace "Bari natafi, zanje Walida ta rakani siyan biro, nagode da ziyara"

Ahankali yace "sunanki"

Cikin murmushi tace "A'ISHA"

yace "what!?"

Cikin mamaki tace "meyafaru?"

Cikin farinciki yace "sunan mamana gareki,kiyi hakuri bazan iya fadar sunanki ba, Amma zan dinga kiranki da Maaama"

Murmushi tayi tace "nagode"

Baice mata komai ba, yasaka hannunsa cikin babbar rigarsa yadauko dubu biyar din daya ware tun hotel, yace "gashi,kudinbarka da sallanki ne, duk da ba'a nunamin kwalliyarba"

Rufe fuskarta tayi cikin kunya, tace "a a ka barshi nagode"

Tace "banason musu, ki Kar6a, kisai chocolate, biro Kuma kibari karki siyo, zan kawo miki next time, karki kashe wayarki, zan kira ki idan nakoma masaukina, oya kar6i kitafi"

Hannu biyu tasa ta karba, sannan tace "to nagode" sannan cikin sauri tafice daga cikin motar.

Lumshe Idonsa yayi yana jin wani irin nishadi ta ko'ina.


******

Gidansu Walida taje, saide bata dade da zuwa ba tace gida zata tafi, kasancewar duk firar da walidan take mata bata jinta, sotake tasamu waje ta ke6e ita kadai tayi nazari akan wannan bawan Allah.

Har gida Walida ta rakota, su Hajja basuyi tunanin komai ba, saboda dama gidansu walidan tace zataje, saida suka gaisa dasu Ummah sannan Walida ta musu sallama tatafi gida.

Kai tsaye d'akin umman ta tatafi, kamar jira Yan nefa suke, tana shiga Dakin suka kawo wuta, kwanciya tayi akan gadon Ummah sannan ta duba kudin daya bata yauma dubu biyar ne, Nan take tafada duniyar tunani, shikam wannan wacce irin sana'ah yake dazai dinga yimata kyautar dubu biyar har sau biyu?, lalle in hakane Mahmud Wakili ba qaramin mutum bane, tunda gashi de Yaronsa ne yake yin kyautar dubu biyar, Amma kudin ai yayi yawa, mutumin Nan Dama fad'a ne yafara hadani dashi, idan nasake zagin ogansa Mahmud Wakili muka sake wani fadan daga baya yace nabiyashi kudinsa fa?
Idan ma bamuyi fada ba Yaya za'ayi na tunkari iyayena da wannan uban kudin? Cikin sanyin jiki tasauko daga gadon tasaka kudin acikin asusunta, sannan Takoma Dakin Hajja tasaka mata wayar ta acaji.

Yana tafiya a hanya Ramadan yakira shi, harzaiqi d'auka, saikuma yafasa yad'auki wayar, daga dayan bangaren Ramadan yace "oga jiya naje gida bansamu ganinka ba, yau Kuma nakoma madam tace min kunyi tafiya kaida mama, lafiya

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment