Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Ina zataje? Tafada musu dutse zataje, suka nuna mata wajan da ake lodin motocin dutse, taje tashiga, mutum biyu ne suka shiga Bayan shigar ta, aka kar6i kudin kowa, sannan driver yaja suka tafi, basu zo dutse ba Sai wajan karfe biyar da rabi, zuwa wannan lokacin duk ta gama galabaita, qafafunta sun dauki ciwo, ga yunwa, tunda tataho babu abinda tasaka acikin bakinta, ko tayi niyyar siyan wani abun idan ta tuna irin sharrin da aka mata saita ji duk duniyar ma tafita akanta, yanzu wannan vedio idan aka turawa wasu awaya shikkenan ita Kuma tagama watsuwa a duniya, lokaci daya, taji wani irin hawaye yasake zubo mata, cikin sauri tasaka hannu ta share, sannan ta nufi inda zata hau motar dazata kaita cikin garinsu, wato Garin CHAMO.


******


Bayan yagama wanka ya shirya, yad'auki computer sa, Adede lokacin munirat tashigo Dakin nasa, fuskarta babu walwala ta Wulla masa wayarta wadda ta kunna vedion da aka turo mata itada mama,wayar ya kalla yaga de irin vedion da mama ta nuna masa ne dazu, yasake kallon vedion ya kalleta, sannan ya Ta6e bakinsa yara6a ta gefenta yawuce, har yanzu idan ya tuna irin ta'asar data masa, wani irin qullutun baqin ciki yakeji a ransa, tabashi mamaki yanda baya zato, ko kadan bayason sake ganin ta, hakanne yasa daya futo zuwa falon su ma bai tsaya anan ba, Kai tsaye yafice zuwa compound din gidan cikin yar qaramar rumfarsu ta hutawa, wadda aka gama qwatata da tsari Mai kyau, ya zauna, sannan ya ajiye computer sa a gabansa yafara binciken location din da Aisha take, fuskar Nan tasa ahad'e, babu alamun farinciki ko walwala atare dashi, fatansa daya, Allah yasa bata cire agogon daga hannun taba, ko minti uku baiyi da zama awajan ba, Mai aiki tazo da sauri ta ajiye masa fruit da Kuma gorar ruwa tareda glass cup a gabansa ta juya cikin sauri.

Munirat kuwa mamaki da taqaicinsa ne suka sake kamata, tunani take a ranta me Mahmud yataka dayake mata wannan abubuwan?tana tunanin ai ayau din ta cancanci yayi mata komai domin ya lallashe ta saboda wannan vedio din, Amma sai gashi yagani, Amma yawuce yarabu da'ita, harda cewa zaizo ya lallashe ta ashe duk qarya ce Da yaudara, dama tariga tasan muddin yafara shiga wajan waccan tsohuwar, to Sai abinda ta kitsa masa, dama can ai itace tabashi lasisin iskanci da yarinyar, tunda itada kanta ta kama yarinyar ta riqe masa, yake ta6a mata nono, to yanzu kuwa dan ya aikata Zina da'ita ai ba zatayi masa fada ba, lokaci daya tasake jin tsanar mama acikin zuciyar ta, Fata take Dama ace ta mutu, kowama ya huta, tunanin da munirat ta dinga yi kenan Bayan fitar Shahaab daga cikin dakinsa.

Acan compound kuwa Shahaab baima kalli abinda aka gabatar masa ba, nutsuwa yayi yakafa Idonsa a computer yana aikin bincike, wata irin ajiyar zuciya yasauke Mai karfi, cikin tsananin farinciki ya furta"Alhamdulillah"sannan ne yad'auki inab guda daya yafara Sha ahankali, saida yasha fruit din sosai, sannan yatashi yanufi part din mama.


******

Lokacin datazo Garin duk mutane sun shiga sallar magrib, kasancewar Adede lokacin ta sauka, Garin take kallo kamar wanda tayi shekara bata cikin sa, wani irin farinciki ne ya kamata, jitake kamar tayi ihu, har gudu-gudu take hadawa dashi domin tayi sauri ta qarasa gida, tana shiga gidan kuwa ta kwasa a guje, Adede lokacin Hajja tana Zaman tahiya a sallarta, Ummah Kuma ta idar da alwala kenan ta miqe zata shige daki, cikin wani irin ihun murna ta daka tsalle ta d'ane umman ta, cikin jin dadi tace"Ummah...."

Cikin sauri Ummah ta juyo tana kallon ta baki bude, mamaki ya hanata yin magana, dariya tayi ta ce"ummah nadawo"

Hajja datayi sallama cikin tsananin mamaki tace"me sunan qawa?"

Cikin sauri tasaki Ummah tafada jikin Hajja tace"Hajja nah"

Sai a lokacin Ummah tayi magana tace"Wai kece Anya kuwa kokwade mafarkin Dana saba ne?"

Cikin sauri tace"Ummah nice mana, Zona mintsine ki kiji" taqarasa maganar cikin sigar tsokana.

Ummah tayi dariya ta Girgiza Kanta,tad'auki hijab tatada kabbarar sallah.
Hajja kuwa hannu ta daga sama ta kalli gabas tace"Alhamdulillah....Allah nagode Maka daka dawomin da jikata gida lafiya,su jummai Yan baqin ciki saide su mutu"(>Ø-Ý=ØÞ)


******


Cikin farinciki mama tace"ikon Allah, ashe tana Jigawan, ninama Rasa Yaya akai kayi dabarar saka mata agogo me d'aukeda na'ura Shahaab,kodan kasaba yin dabara kana kama 6arayin gwamnati shiyasa yanzu ma kayi dabara kakamo 6arauniyar zuciyar ka?"

Cikin sauri ya sunkuyar da Kansa qasa saboda wata irin kunya data kamashi, saida yadan Sosa kansa, sannan ya kalleta yaga ita zuciyarta daya tayi maganar ko ajikinta, ahankali yace"a a mama, ainasan batada waya a hannun ta, nasaka na'urar a jikin agogon ne saboda idan inason ganin ta, zan duba Inga halin datake ciki, banyi hakan da wata manufa ba, Amma Kuma gashi cikin ikon Allah hakan yayi amfani, Bari inkira kakarta inji Yaya ta sauka, dafatan ta'isa lafiya, dazu nakira ta tanata fada, mama bakiji yanda ta rufeni da fada ba, halin ta sak irin na mamanah"(=ØÞ)

Cikin dariya mama takai masa duka tace"d'an mutum wasa ne Shahaab? Ai tanada gaskiya, karabu da'ita karka kirata, kabari gobe mushirya mubi jirgi, Sai muje a basu haquri, daga Nan Kuma Sai ayi maganar aurenku, kaga hakan zaifi, suma zasuji dadi Susan cewa sun turo yarsu gidan karamci"

Cikin jin dadi yace"to mama Allah yakaimu, saimu tafi sassafe ko?"

Mama ta kallashi,Shima kallon ta yayi, Sai a lokacin yaga kallon Fassara take masa, cikin sauri yatashi yabar falon Nata cikeda kunya, Sai aikin shafa lallausar sumar Kansa yake.

Mama data bishi da kallo tana ganin fitarsa tasaki murmushi, ta daga hannunta sama tana yiwa Allah godia daya karkato mata hankalin danta yake son aure yanzu, tana fatan ace anayin wannan aure Aisha tasamu ciki ko Allah zaisa itama taga jikokin ta kafin tarasu.


******

Gaba dayansu su ukun atsakiya suka saka Aisha sunajin yanda take basu labari, Abba ya kalleta yace"amma qawar Hajja banda Shirman ki Dan kun samu Sa6ani da uwar Dakin naki saiki niqo irin wannan hanyar kitaho ke kadai? Bakya tsoron asaceki a hanya?"

Ummah tace"hanya Kam babu kyau, yanda ake diban mutane kamar wasu dabbobi,qasar nan anmaida rai ba'a bakin komai ba"

Murmushi tayi tace"wallahi Ummah Ina mata komai,Bana mata rashin kunya saboda tsohuwa ce, yanda kikaga Hajja itama haka take, Amma idan ta rikice saiki Rasa gane kanta, shiyasa Nima nataho gida, dama nagaji,ga sauran kudina ma kuyi amfani dashi Ummah"
Ta qarasa maganar tana bude handbag dinta, duk sauran kudin dake ciki ta fitar dashi ta basu, Hajja ta kalli kudin tace"me sunan qawa wannan kudin ai yayi yawa,duk na menene haka? Ko kudin aikin naki ne?"

Kanta ta Girgiza Tace"A a Hajja,me gidan ne yabani kudin da Kansa, ban roqeshi ba"
Abba ya Jinjina Kansa, Hajja tace"yawwa nikin tuna min ma, dazu wannan saurayin naki ya kirani, Wai sunansa Shahaab, ke yake nema in baki waya idan kina kusa, na qare masa tatas nace idan yasake kirana sainaci masa mutunci, shida yayi silar barinki gida?"
Murmushi tayi tace" Hajja Aida baki masa haka ba"

Kafin Hajja tayi magana Abba yace"har yanzu de baki rabu dashi ba kenan, bamu Isa mu fada miki magana ki saurari maganar mu ba, ai shikkenan Allah yabada sa'a"

Jikin Ummah yayi Sanyi jin furucin Abba, ta kalli Aisha taga yarinyar tanata Fara'ah, Sai can Aishan ta d'ago kanta ta kalli Abba Tace"Abba Bahaka bane, Amma kayi haquri, duk bayanin dazan Maka ba lalle ka ganeba"
Daga Nan bata sake cewa komai ba tafada duniyar tunani
batason taga yanda Abban ta zaiji kunya, Amma data fada masa cewa Shahaab din de dayake qi shine Mahmud Wakili, Shahaab din dayake qi gidansa yasake tura ta aiki, tasan Hajja zata masa wankin Babban Bargo, ahankali tasake cewa "Abba jabir bai fada muku Mahmud Wakili ne ya turashi qasar waje karatu ba? Bai fada Maka shine yatura ka umara ba?"

Cikin tsananin mamaki Abba yace"mahmud Wakili Kuma?"

Hajja tace"jabir bai fada mana koma ba, Amma menene dalilin yimana wannan abun? Keda kike gidansa bai fada miki saboda me yayi mana haka ba?"

Murmushi tayi ta Girgiza, sannan tace" tunda nafada muku yanzu saiku shirya kuje kuyi masa godia, saiya fada muku da dalilin da Kansa"

Hajja tace"tokode daga zuwa yaganki ya qyasa? Fadamin gaskiya"

Hararar Hajja tayi, tatashi tashige Dakin Hajjan tafara shirin wanka, Hajja tatashi tabiyo bayanta taga harta daura zani da alama wanka zata shiga, kallon ta tayi tace"mesunan qawa Habujan Nan ta kar6eki, jikinki yayi wani mulmul kamar matar kansila, kode kaji kikeci ne kullum?"

Cikin dariya tace"kullum sunake ci, abinci Kala Kala Hajja Sai Wanda naza6a, nama kuwa kamar abun banza"

Hajja tace"ikon Allah, kice naman kaji yana Nan kayan qarfi..."

Aisha tayi dariya tace" karfin ne kawai bakida shi Hajja da kinje kema kinci"

Murmushi Hajja tayi ta qaraso Dakin, ita Kuma ta juya tashige wanka.


******

Yau yariga mama futowa falo,tun sassafe yafuto su kansu ma'aikatan sunyi mamakin ganinsa afalo, yad'ora kafa daya Kan daya yana kallo, yayi mutuqar kyau cikin suit, Sai qamshi yake zubawa, Sai wajan karfe takwas mama tafuto, ta shirya cikin less Mai ruwan golden, hannunta da wuyan ta sunsha sarqa da zoben gold, kana ganin ta kasan daula ta zauna, cikin mamaki ta kalleshi Tace"A a, yana ganka anan Kai kadai?"

Cikin sauri ya sunkuyar da Kansa qasa, yadan shafa sumar Kansa yace"mama ai nagama shirya wane"

Murmushi tasaki, ta nemi waje ta zauna tace"tokoma kacire wannan kayan kasako manyan Kaya, haba Mahmud, wajan surukanka zakaje fa ba wajan Aisha ba"

Kansa yadan shafa, sannan yatashi yakoma part dinsu, itama dinning ta nufa tafara cin abinci,don bazata iya wannan azalzalar ta Shahaab ba, Dan idan tabiye masa taga alama abincin ma bazasuci ba.

Tare suka dawo shida Munirat, shadda yasaka fara tareda babbar riga, kayan sunyi Masa kyau sosai fiyeda qananun kayan, Wanda bai saniba tsaf zaiyi tunanin wani sabon angon ne, agogon hannunsa ya daura sannan yaja kujera ya zauna, munirat ma ta zauna tareda gaida mama, cikin kulawa mama tace "Barka munirat"

Abincin suke ci Hankali kwance, mama data gama tana shirin tashi ta kalleshi tace"jirgin karfe nawa zamubi?"

Cikin sauri ya Kalle ta, saida ya ajiye spoon din dayake shan tea sannan yace mata"jirgi bazai tashi ba yau, saboda yanayin hazo, saide mutafi a mota"

Kanta ta Jinjina tace"to ai saimu wuce ko?"

Tissue yadauka ya goge bakinsa, dama kawai yana tura abincin ne, Amma ya matsu sutafi, cikin sauri yace"toshikkenan muje"

Munirat tayi mamakin sa, tafiya zaiyi Amma ko fada mata baiyi ba, batasan meyasa tsakanin jiya zuwa yau, yake share taba, har zata tambayesu Ina zasuje, Sai taga mama ta kalleta tace"to Munirat zamuje jigawa, kinsan yanayin tafiya bamusan Yaya zata Kaya ba, saboda haka kimana addu'ah,idan daga Nan Kuma kinji anyi masa mata acan saiki shirya kar6ar abokiyar zama"

Cikin sauri Shahaab ya kalli mama, baiso ta fadawa munirat zancen auren ba, yasan tanada kishi dole zata daga hankalin ta, shiyasa yaso saiya dawo saiya sanar da'ita ta cikin ruwan Sanyi.

Dam! dam!! dam!!! Gaban munirat yayi wata irin faduwa, hannunta datake cin wainar qwai yad'auki karkarwa har batasan lokacin da fork din yafadi daga hannun taba,ta zubawa mama ido tana kallon ta, mama dataga yanayin munirat ya sauya tace"ikon Allah, menene abun rawar jiki daga maganar kishiya munirat? Dama yamiki alqawari zai zauna dake kadai ne? Banda abinki munirat yanda Shahaab yakeda kyau irin wannan ai kema kinsan dole yanmata zasu so shi,ballantana ma wannan yarinyar kin Riga kinsanta, Aisha ce, idan ya auro tama itade ba baquwa bace awajanki, dama gida daya kuke zaune shikkenan saiku dora daga inda kuka tsaya, may be Rabon muga qananun Yara agidan ne shiyasa Allah yakawo maganar auren, kema ai zakiso ganin yaran Shahaab suna kuka, suna fada, suna Rikici akan sweet..."

Jikin Shahaab yayi Sanyi, yasaki ajiyar zuciya, yaga alama idan bai katse maganar ta mama ba, Tofa bazata dainaba,Wai ahakan ma Dan batasan da case din filayenta da munirat din ta dauke taje ta siyar ba, dama suna yar tsama to idan tasan da batun filayen Allah ne kadai yasan inda rigimar tasu zata qare, ahankali yace"muje mama"
Yajuya ya kalli munirat, fuskarsa babu yabo babu fallasa yace"saimun dawo"

Munirat dai batasan cewa Shahaab yayi mata magana ba, tadaisan yayi magana Amma kwata kwata bata cikin nutsuwar dazata gane meyake fada, wani irin tashin Hankali ne ya wanzu a Saman fuskarta, baqin ciki ya tokare mata maqoshi, suna fita takifa kanta akan dinning table tasaki wani irin kuka maicin rai, dama ashe Aisha baquwar mama zai aura? Kenan ita ya mallakawa company? Ita Mahmud zaiyi wa haka? Dama tasan hakan zai iya faruwa, tunda har uwarsa ta riqe masa yarinyar ya matsa yaji ba'irin na matarsa bane ai dole ya rikice yabibiyi yarinyar. (=ØHÞ)
Kuka take me mutuqar cin rai, kwata kwata tunanin ta ya tsaya cak, tarasa Ina zata samu mafita, Amma abinda takeji acikin ranta Gani take dazata samu wuqa Toda tsaf zata Iya da6awa wannan tsohuwar(=ØFÞ<Øûß
@&þ)

Mota biyu sukayi, daya suna ciki ita dashi a zaune abaya, Sai driver dayake jansu, dayar Kuma securities ne aciki saboda tsaro.

Suna hanya yake turawa Ramadan text cewa suntafi jigawa shida mama, Sai tsiya Ramadan yake masa shikuma yana murmushi.

(nabarki da Allah keda kika karanta batareda kin biyaba)
******

Aisha ta kalli Hajja tace"Hajja meyake damunki ne Naga kinyi shiru, ko bakya jin dadi?"

Ajiyar zuciya tayi tace"inafa jin dadi mesunan qawa, gaba daya yau Jina nake jikina Sanyi kalau, tun asuba gabana yake faduwa, bansani ba ko mutuwa zanyi"

Cikin tashin hankali Ummah tace"Hajja Dan Allah Kidena wannan maganar, idan bakida lafiya tashi muje nakai ki chemist din Mubarak dogo"

Cikin sauri Aisha ta kalli Hajja tace" Ko wani abu kike so kici saina siyo miki?"

Ganin yanda duk suka daga hankalin su yasa tad'an kwantar da Hankalinta tace"lafiya ta kalau wallahi, kawai gaba nane yake faduwa"

Ummah tace"to kidinga addu'ah Hajja, insha Allah Sai alkhairi"

Kallan Aisha Hajjan tayi tace"mesunan qawa, dauki kudi aqasan fillo na kije bakin kasuwa ki siyo mana kaji, da nasan da zuwanki jiya Aida tun safe zanje insiyo miki, Amma tunda bansani ba kije yanzu ki siyo mana"

Cikin sauri Ummah tace"Hajja aiga kudin datazo dashi jiya, kusan dubu talatin dawani abu, ta d'auka aciki taje tasiyo"

Hajja tace"to jeki dauka ki siyo, kudin bironki da'aka siyar ma mamuda fili yasiya miki dashi,Sai Dan gyare-gyare da'aka yi mana a gidan, yace idan aurenki da inusa yatashi Sai asiyar ayi hidimar biki dashi "

Dan qaramin bakinta ta turo gaba ta juya tana Hararar Hajja, cikin lallashi Hajja tace"to uwar masifa, tashi kije Dan Allah, kibiya gidan qawar ki Walida saita rakaki, tunda batasan kinzo Garin ba, kisiyo harda kayan miya, da kaji guda uku, yau Walima zamuyi, jikata tadawo gida"

Cikin murmushi Ummah ta Kalle su, cikin ranta kuwa dadi takeji yanda Hajjan tasaki ranta tadena maganar mutuwa.


******

Sunci tafiya sosai a hanya, Sai yamma suka shigo jigawa, suna kokarin shiga garinsu Aisha mama ta hangi wani Tsoho yana tafiya akan Keke, itace ya'iyo abayan gari, daqyar yake tuqa keken da alama yajigata dayawa,cikin sauri tace"driver tsaya"

Shahaab ya kalleta da mamaki, glass din ta sauke qasa ta kalli wannan tsohon tace"bawan Allah cikin Garin zaka qarasa ne?"

Cikin sauri ya tsaya ya kalleta yace"hakane Hajiya,ciki zan shiga"

Tace"toshigo mota saimu qarasa dakai"

Tsohon ya kalli motar yaga mota Sai sheqi takeyi tana daukar ido, yaji tsoro karyaje Yan yankan kaine, cikin tsoro yace"a a Hajiya, nagode, Aina qaraso ma, nagode sosai"

Murmushi tayi, ta bude Jakarta tad'auki kudi Yan dubu dubu tabashi tace"to ungo wannan kasai itacen dayawa kadena zuwa da kanka"

Jiki na rawa tsohon ya kar6i kudin hannunsa Sai rawa suke, cikin jin dadi tace"nagode Hajiya, Allah yasaka da alkhairi, Allah yahadamu a aljanna mafificiya, ubangiji yabiya miki buqatunki na alkhairi, Allah Yacika miki burinki"

Cikin jin dadi mama tace"Amin ya Allah, kasan ni wacece?"

Tsohon yace"a a Hajiya saikin fada"

Tace"amma ai kasan Mahmud Wakili ko?"

Cikin sauri yace"ranki ya dade duk qasar nan waye zaice baisan Mahmud Wakili ba? Ko baka sanshi a'ido ba ai zaka sanshi a suna"

Murmushi tasake yi tace"toni mahaifiyarsa ce, sunana Aysha Yakubu Sagagi, qawar Aysha Sulaiman Bompai"

Cikin sauri tsohon ya tsugunna yana zuba mata addu'ah, mama tarufe glass din motar suka cigaba da tafiya, Shahaab ya kalleta yayi murmushi tareda Sosa girarsa guda daya, mama kuwa tunanin qawarta Aysha Sulaiman ne yafado mata, rayuwa kenan, yaude gata acikin jigawa Amma batada Hali ko hanyar dazata hadu da qawarta, lokaci daya jikinta yayi Sanyi, tana wannan tunanin batasan har sun qaraso kofar gidan su Aisha ba, Shahaab ya kalleta sannan yace "mama ga gidan Nan munzo"

Kallonsa tayi tace"mekake nufi? Futowa zakayi muje tare dakai kabawa iyayen ta haquri akan abubuwan dasuka faru abaya, Nima nabawa Aisha haquri akan abinda yafaru"

Cikin kunya Shahaab yafuto daga cikin motar, securities sukazo da sauri suna gyara masa babbar rigar jikinsa, aka budewa mama kofa itama tafuto, manyan motocin dasuka tsaya a qofar gidanne suka dauki hankalin Yan qauyen, Wanda suka sanshi Nan da Nan suka fara qus-qus suna nuna shi da hannu anaso a tabbatar Mahmud wakilin daya ta6a aiko musu kayan abinci ne, kokuma wani ne daban?

Wani yaro ne dayazo wucewa mama ta tare tace"shiga Nan gidan kace Ana sallama Dame gidan"

Yaron yajuya yashiga gidan, Sai gashi sun futo daga gidan shida Abba.

Abba yana ganin Shahaab sai mamaki ya wanzu a fuskarsa, cikin mamakin yace"sannunku da zuwa, kamar yalla6ai Mahmud nake Gani ko?"

Shahaab yayi murmushi tareda sunkuyar da Kansa qasa cikin kunya irinta surukai, cikin ransa yana mamakin mahaifin na Aisha ashe ma yaro ne kamar shi,Mama tayi murmushi ganin yanda Shahaab yake sunkuyar dakai tace"kaine mahaifin Aisha?"

Cikin sauri Abba yace"Eh nine Hajiya, sannunku da hanya, nace Allah yasa de ba wani laifin tayi muku tataho gida ba?, mu munata qoqarin zuwa har gida muyi godia akan abun alkhairin da yalla6ai yayi mana Kuma saina ganku kunzo?"

Mama tayi murmushi Tace"A a Aisha batayi laifin komai ba, mune ma mukai laifi mukazo bada haquri, Yaya sunan Kane?"

Cikin murmushi Abba yace"sunana Mamuda Hajiya"

Cikin farinciki mama tace"Mahmud de ko?"
Tanuna masa Shahaab da Kansa yake qasa tace"shima wannan danane, kamar yanda kasani Mahmud Wakili sunansa, Amma Ina kiransa da SHAHAAB..."

gaban Abba ya yanke yafadi, cikin sauri ya kalli Shahaab, cikin daburcewa Shahaab ya russina tareda Bawa Abba hannu yace"Barka da yammah"

Kan Abba gaba daya saiya kulle, dama Shahaab shine Mahmud Wakili? Wannan shi ake kira an yanka tatashi....,kenan shine yake zuwa wajan Aisha? Kuma shine yasake tura Aisha gidansa aiki? Shine yakaishi Umarah, yakai jabir qasar waje karatu?cikin son sake tabbatar wa Yace"Shahaab-shahaab de Danakeji awajan Aisha?"

Shahaab yayi shiru ganin lokaci daya surukin nasa ya d'agoshi, Dan haka yayi saurin yin qasa da Kansa yana 'Dan Sosa qeyarsa.
Mama tayi murmushi tace"shide,idan babu damuwa ka bamu wajan zama Dan maganganu muke tafe dasu dayawa"

Cikin sauri jikin Abba yad'auki rawa, Wai yau Mahmud Wakili ne da Kansa a kofar gidansa, Mahmud Wakili ne yake zuwa wajan 'yarsa,cikeda mamaki yace"a a, to hajiya ku qaraso ciki mana, ku shigo daga ciki kawai..."

Mama Tace"toshikkenan Takwaran Mahmud mushiga"

Abba yajuya cikin gidan da sauri, mama da Shahaab suka doru abayansa.

Hajja tana sunkuye tana gyara hadaddan kunun ayar data zuba acikin fridge, Aisha tana zaune da abinci agabanta tanaci kamar bataso, Ummah tana Gefe da pure water ahannunta tanasha,saiji sukai Abba yana cewa "kushigo Hajiya, ku qaraso, sannunku da zuwa"

Shahaab yana daga Kansa Idonsa ya sauka akan Aisha, tana hada ido dashi gabanta yayanke yafadi, ta tsaya cak tadena cin abincin, yayinda gaban mama ya yanke yafadi ganin fuskar da bazata ta6a mantawa da'itaba a tarihin rayuwar ta,lokaci daya handbag din data riqe a hannun ta tafadi qasa, qaran faduwar jakar ne yasa Hajja tarufe fridge din ta d'ago kanta, gabanta ne yafadi, hannunta yana karkarwa tafara nuna mama,cikin rawar murya tace"Aysha Yakubu?"

Jin sunan data kirane yasa gaba d'ayansu suka maida kallon su ga Hajiya Mama.


Masha Allah, mutara zuwa gobe=ØOÞ



Littafin kudi ne, nera 300 kibiya ki karanta kada ki karanta abun Allah ya'isa

0164549488
Amina muhammad
GTbank


Kokuma katin MTN

Shedar biya ta wannan number 08033300034







Mutara zuwa gobe=ØOÞ<Øûß








Mrs Usman ce
'<Øûß

Page 24




Wani Irin hawaye ne yazubo daga idon mama,cikin rawar murya tace"Aysha Sulaiman? Aysha kenake Gani haka kokuma idonane?Dan Allah kifadamin kode irin mafarkan danake yi ne?"
ta qarasa maganar hawaye na gudu daga idanuwanta.

Ahankali Hajja tatako tazo gaban mama, tace"nice Aysha"

Cikin sauri mama ta rungume ta,kuka Hajja tasaki mecin rai, mama kuka, Hajja kuka, cikin kukan Hajja tace"Aysha, ashe da Rabon zan sake ganinki a doron duniya?"

Cikin sauri tasaki mama ta daga hannunta sama tace"ya Allah nagode Maka, Allah Ina qara yima Godiya bisa nunamin qawata dakayi wadda na Dade Ina nema tsawon shekaru masu yawa"

Hajiya Mama ma Hawayen ta share, itama ta daga hannunta kamar de yanda Hajja tayi tace"ubangiji na gode Maka, yau Naga Aysha Sulaiman bompai,Babban burinmu guda daya Yacika, saura Kuma d'ayan, Allah nagode maka"

Cikin sauri Ummah ta goge qwallar idonta, itade batasan wannan baqi ba, Amma duk da babu bayani tariga tasan cewa wannan matar itace qawar Hajja, yaude ga qawar Hajja tazo har gida, ikon Allah kenan, kullum labari-labari yau gashi Allah yahadasu.

Aisha kuwa gabanta ne yafadi, duk wannan dramar dasuke idonta yana kan mama, Tun lokacin da Hajja tace
Aysha Yakubu, daga Nan wani irin shock yakamata, yanzu dama Hajiya Mama itace qawar Hajja?.

Shikuwa Shahaab wata irin wawuyar ajiyar zuciya yasauke Mai karfi,domin kuwa abinda ya lura dashi shine Abban Aisha bashida qanwa mace bare Mama tace dole saiya aure ta Yacika mata burinta, dama abinda yake gudu kenan, mama tadage muddin taga Aysha Sulaiman Tofa Sai sun hada yayansu aure, Kuma Alhamdulillah shi bai taba jin Aisha tace abban ta yanada qanwa ba bare abashi, Gara de ita Aishan, ahakan ma tunda gashinan Allah ya hadashi da Aishan cikin hikimar sa ai shikkenan Shima de dan'uwan burin maman ne, tunda jikar qawarta ce.

Abba kuwa ajiyar zuciya yasaki ahankali, cikin sauri ya goge qwallar Idonsa,sannan yayi gyaran murya yace"Alhamdulillah....,Hajja kuyi hakuri kudena kukan Nan haka, ku qaraso ku zauna"
Yajuya ya kalli Aisha da abincinta ke gabanta ta gagara ci, cikin fada yace"ke tashi ki Dauko babbar tabarmar Nan ki shimfida mana, kinfi awa daya kina cin wannan abincin, ga baqi sunzo ko abun zama baki shimfida musu ba"

Cikin sauri Shahaab yayi qasa da Kansa tareda Sosa qeyarsa
Ummah ta kalli Aisha Tace"Ai inta fara dora abinci a harshe saikace basarakiya, na hanata irin wannan cin abincin taqi ji "

Cikin sauri tatashi ta wuce Dakin Ummah tad'auko babbar tabarmar ta shimfida musu.

Ummah ta kalli su Hajja tace"ku qaraso ku zauna"
Tajuya ta kalli Shahaab da batasan waye shi dinba, ita de taga Sai sunkuyar dakai yake yaqi kallon idon kowa, tace"bawan Allah qaraso mana"

Cikin sauri Shima Abba yace"bissmillah yalla6ai"

Yanda yace yalla6ai dinnan Sai abun yayiwa Shahaab nauyi, ahankali yace"to nagode"

Suka qaraso suka zazzauna a tabarma,Aisha tana daga Gefe, duk jinta take a takure, saboda yanda Shahaab yazuba mata mayun Idonsa, ko tsoron su Ummah su kamashi yana kallon ta ba yayi, duk motsin datayi akan Idonsa.

Hajja ta kalli mama, sannan ta nuna Aisha da hannu tace"kinganta Nan,? Babu abinda tabari naki,masifa,rashin kunya, yanga saikace yar wani, wannan cin abinci dakike a makaranta haka itama takeyinsa kamar kin zauna da'ita kin Koya mata yanda kike yi, lokacin da aka haife ta uban yadage sunana zai saka, nikuma nace a a, munyi alkawarin zamu sakawa Yayanmu Aisha, idan Kuma maza muka haifawa to zamu saka musu suna Mahmud, to Alhamdulillah, Dana guda daya ne a duniya gashinan mamuda, ban haifi mace ba bare nasaka mata sunanki, shiyasa Ana haifar ta daya ce sunana zaisaka nadage nace a a, saide yasaka sunanki, to daqyar de mamuda ya yarda, saboda kallon ta6a66iya sukemim Alokacin, tayaya qawar daban masan inda take ba, bansan a'ina zan ganta ba, zan dage ince sunanta zan saka? To dayake de sunan naki duk irin nawa ne, shine yasa mamuda yasaka mata sunanki,idan masifar ta tatashi fada mukeyi akan wannan suna Nata, fada takeyi tana min sababi kawai natashi nasa mata sunan qawata qilama ta mutu, ban'isa ince tanada masifa ba saitacemin ai nice nace asaka mata sunan qawata, danhaka halin qawata ta Dauko..."

Cikin sauri Aisha ta sunkuyar da idonta qasa, wannan tonon silili na Hajja har Ina? Da alama batasan waye wannan yake tareda mama ba, da tasan shine Shahaab dabata mata wannan tonon asirin ba.

Ahankali kuwa ya kalli Hajja yace"nima haka tamin Hajja, ranar Dana kawo muku abinci da Azumi rashin kunya ta dinga zubamin, saura kadan ma ta dungure min kai na...."yaqarasa maganar cikin sigar tsokana.

Aisha ta
DOWNLOAD
DOWNLOAD

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

7 months ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

7 months ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

2 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment