Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mama qafafu, cikin tsantsar ladabi kanta asunkuye, batare data hada ido dashi ba tace "yalla6ai barka da dawowa"

Bece da'ita uffan ba, Sai mama ce data watsa mata wani irin kallo tace "saiki tashi kije, zan gana da Dana"

Cikin sauri yarinyar tatashi tabar wajan har qafafunta na hardewa

Kallan sa tayi tace "Shahaab ya aikin? Kadawo lafiya?"

Kafin yabata amsa agogon hannunsa ya nuna alamun Ana kiransa, ta6a agogon yayi ya amsa Kiran dake shigowa, daga dayan bangaren muryar wani mutum ne yake tashi "ranka yadade kanada baqi daga bayelsa"

Dafe Kansa yayi, kwata kwata ya manta da Zuwansu, ahankali ya kalli mama, shide yasan be'isa yasake fita yanzu ba, cikin muryarsa Mai dadi yace "kafada musu muhadu dasu gobe misalin karfe goma nasafe" daga Nan yakashe wayar, ya maida dubansa zuwaga mama

Hankalin tane taji ya kwanta Bayan taji bazai sake fitaba, taqi jinin ta ganshi nesa da'ita

Tafison kullum ta kasance tareda dannata qwaya daya tal a duniya, batason yawan rashin zamansa agida ko kad'an, cikin kulawa yace "waye yata6aki mama? Keda waye?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace "ai kasan damuwa ta, rashin dawowarka ne gida dawuri, saikuma batun qawata Aysha Sulaiman bompai, dakamin alqwari zaka nemomin ita"

Kansa ya sunkuyar qasa, wannan qawa ta mama! Wannan qawa ta mama!! Da yanada halin dazai mantar da'ita wannan qawar Tata datuni yayi, saboda babu Wanda yasani tana Raye har yanzu kokuma ta mutu, ahankali ya d'ago Kansa ya kalleta, yakama hannayenta yariqe yace "za'a duba agani"

Shiru mama tayi tana Kallan sa, tarasa meyasa Shahab baison maganar qawarta, tun lokacin data fada masa inde taga qawarta Aysha to zata hadashi aure da 'yarta idan mace ta Haifa, tun daga lokacin yaqi jinin tayi masa maganar qawar Tata, saboda bashida ra'ayin yin wani aure yanzu, idan ba bayason Nemo mata qawar Tata ba yaushe zata yi masa maganar amma yace Wai za'a duba, hakan yana nufin Bama shine zai dubaba kenan, ko meyasa yake gudun yin wani auren? Kokuma baida cikakkiyar lafiya irinta maza oho masa, rashin haihuwar sa yana damunta, ga Kuma rashin qawarta wadda take Fata, take Kuma burin tahadu da'ita kafin Takoma ga mahaliccinta, wadannan burikan Nata guda biyu su take Fata su kasance, yau ace taga jinin Shahaab, sannan Kuma taga qawarta Aysha Sulaiman

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Yaya labarin Munirat? Har yanzu haihuwa shiru babu ciki bare ayi tunanin labarin haihuwa ko?"

"Ana Addu'ah de"

Shine abinda yafada mata

Kallan sa tayi dakyau Kai tsaye tace "inaso kafin namutu, Inga qawata Aysha, sannan Kuma Inga yayanka, Qawata Aysha de Ina Nan Ina nemanta, Kuma nasan insha Allah watarana zan ganta, Amma Kai haihuwa bakada tabbas,matarka ba haihuwa zatayi ba, yakamata kayiwa kanka fada, saboda haka yaushe zaka sake aure? "

Gabansa ne yafadi,cikin sauri ya d'ago Kansa ya kalleta, Dan qaramin bakinsa ya bude kamar Mai shirin cewa wani abu, Amma Kuma yakasa magana, ganin yazuba mata ido yana Kallan ta yasa taci gaba da fadin "yakamata kabi shawara ta, ka 6oye kanka kanemi aure, kafuto a matsayin SHAHAAB kanemi aure da soyaiyar tsakani da Allah bata kudi ba, muddin kace zakaje wajan yanmata a matsayin MAHMUD WAKILI,to bazaka ta6a samun soyaiyar gaskiya ba"

Tamkar Wanda zai Fashe da Kuka yace "mama itama Munirat din tana sona, nida ita ai sai Allah mama"

Batace dashi komai ba saboda taqaici kawai wayarta ta d'auka dake Gefe, tawuce dakinta tabarshi anan, hakan yana nufin shiru ma amsa ce game Hankali.

Yana ganin shigewarta daki yaji kamar ya kurma ihu kozaiji dadi, tayaya mama zatace yayi aure Bayan irin dunbin soyaiyar Da Munirat take nuna masa?

Jikinsa a sanyaye yamiqe yanufi part dinsu, duk ruwan dayake sauka akansa ko kad'an baya jinsa, yasan cewa idan yabi Bayan mama ma to bazata saurare Shiba, yana zuwa falon ya hangota gaban TV da remote a hannunta, Riga da siket ne ajikinta dinkin ya zauna Das ajikinta,munirat chocolate beauty ce, Amma hutu, dakuma jin dadin datake samu, da shafa mayuka masu mutuqar tsada yasa gaba daya bazaka ce mata chocolate ba, fatarta tayi wani irin luwai luwai kamar ka latsa jini yafuto, mace ce har mace, Mai aji dakuma wadatar ilmin boko,Daurin ture kaga tsiya tayi, hakan yabawa gashin dokin data saka damar futowa sosai Kai kace halalinta ne, falon bashida wani tarkace, kujerun falon Kala biyu ne, akwai yellow, dakuma ash colour, Sai aka hadasu akayiwa falon qawanya dasu

Tsayawa yayi yana qare mata kallo, haqiqa yana qaunar munirat, Kuma itama ya tabbatar tana mutuqar sonsa, babu abinda ta rageshi dashi, sannan tana mutuqar qoqarinta wajan ganin ta kyautata wa mama, Amma mama bata Gani

Jin alamun kamar Ana kallon ta ne yasa tajuya, tana ganinsa tatafi dawani irin taku me daukar hankali, ta qarasa wajan sa
"barka da zuwa my Dear"

Cikin damuwa ya Lumshe Idonsa ya bude, alamun amsawa, murdaddan dantsan hannunsa ta kama tace "muje kayi wanka, meyake damunka ne Naga kamar kana cikin damuwa, gashi katsaya ruwa ya ta6amin kai"

Ta qarasa maganar tana janshi ciki, ahankali ya janye jikinsa yace "kije kiyi kallonki, yaude na hutar dake, idan nagama zan futo"

Murmushi tasaki, ta rungume shi tasakar masa kiss a kumatu, sannan tasake shi tajuya, saqon Nata yashige shi sosai, har saida hakan yasa shi Lumshe Idonsa, batare daya shirya ba

Washegari da safe bai tashi dawuri ba, sakamakon gajiyar da yayi cikin dare,tun kafin yatashi daga baccin munirat ta silale tatafi part din mama,yau tana so tayi wa mijin ta girki Wanda zaisa yaji dadi sosai kamar yanda yajiyar da'ita dadi adaren yau, ma'aikatan part din ta had'a gaba d'ayansu tasakasu su girka mata irin abunda takeso, cikin qanqanin lokaci suka kammala komai suka jereshi a Babban dinning din na mama, Wanda aqalla zai dauki mutane samada mutum takwas

Har zuwa lokacin Hajiya Mama Ana daki bata futo ba, munirat kuwa zama tayi akan kujera ta sallami masu aikin, wayarta ta d'auka tana chatting da qawayenta, dayawansu tallar magungunan mata suke mata, Wanda ita kanta batasan Dame aka hadasu ba

"menake Gani haka?!!!"

Mama data futo daga daki tafada, Bayan taga abinda aka ajiye a dinning, ta qarasa maganar idonta nakan munirat, fuskarta kuwa shimfide take da 6acin rai

Cikin sauri munirat ta kalleta, gabanta yafadi, da sauri ta sakko daga kan kujerarar ta tsugunna har wayar hannunta na faduwa, cikin ladabi da rawar murya tace "Barka da futowa mama, Ina kwana?"

"daban kwana ba kya ganni? Munirat yaushe Ina cikin gidannan har Zaki shigo min part dina kina bada umarni? Kinyi hauka ne?"

Adede lokacin yashigo part din, yashirya cikin suit kamar kowacce rana

Munirat da idonta yakawo ruwa, qwalla tataru tacika idon, ta girgiza kanta batare da tayi magana ba

Nunata mama tayi da d'an yatsa, tace"maza maza tashi kije tas ki cinye abinda kikasa aka girka, tun kafin ranki Dana iyayenki ya6aci.... "

Cikin sauri ya qaraso falon, cikin ladabi yace"mama kiyi hakuri Dan Allah"

Kallan sa tayi tace "Alhamdulillah... Gara da Allah yakawo ka"

Ta nuna masa munirat da hawaye ya wanke mata fuska tace "tun kafin namutu matarka ce mebada umarni...., to gatanan kasaketa"

Jiyayi kamar mama ta doka masa guduma a qirjinsa, munirat kuwa tanajin wannan furucin, tafice daga falon da gudu tana kuka.


LABARINSU:

Hajiya Mama, sunanta Aysha Yakubu Sagagi, tun Bayan rabuwar su da qawarta Aysha Sulaiman bompai Sai iyayenta suka rasu, daga Nan mijinta ya dauke ta suka tafi Nijar wajan dangin sa, sun dade acan yana kasuwancin sa, daga Nan suka sake dawowa Nigeria, ahankali ahankali har Allah yasa Arziqinsa yasake ha6aka, Bai Barta tayi maraicin iyayenta ba, janta yayi ajiki, ya dinga Koya mata harkokin kasuwancin sa, ahankali harta gane komai, lokaci zuwa lokaci yana tura ta wasu qasashen sarin kayaiyaki, har Allah yasa Shima yabude kamfanoni dadama, anan Nigeria da Kuma Nijar inda danginsa suke

Lokaci daya, sunansa yafuto acikin jerin sunayen masu kudin qasar Dama Africa baki daya, akwai wata Rana daya shirya zaije yataho da danginsa na Nijar, su dawo Abuja da zama gaba daya, yaje yataho dasu a hanyar su ta dawowa jirginsu yayi hatsari suka mutu gaba dayansu.

Mama tayi kuka tayi kuka kamar ranta zai fita, har kwantar da ita akayi a Asbiti, anan ne aka Gano tana d'aukeda ciki na wata uku, haka taci gaba da Kula da cikinta,tasamu mutane amintattu suka tayata kula da dukiyar mijin Nata,kamfanin sa dasuke Nijar tasa akai gwanjon su,Alokacin da cikinta yakusa haihuwa saita shirya tatafi Saudia,acan ta haifi danta namiji kyakykyawa Mai Kama da mahaifinsa sak, ranar suna taso sakawa Yaron sunan mahaifinsa, to Amma data tuna alqawarinsu itada qawarta Aysha Sulaiman bompai, saita sakawa Yaron suna MAHMUD, mutane suke kiransa da MAHMUD WAKILI, ita kadaice bata fadar sunansa, saboda Dan fari ne, Sai take masa alkunya take kiransa da SHAHAAB.

A India yayi degree dinsa na farko, ya karanci bangaren medicine

Haka mama ta hanashi aikin asbiti duk da yanaso, ta dorashi akan harkokin mahaifinsa, kasancewar yanada hazaqa hakan yasa Nan da Nan yasan kan harkar, dukiyar Kuma tasake ha6aka,daga baya Kuma yatafi malesia yayi karatu akan harkar kasuwanci, hakanne yasake bashi damar gogewa akan harkar kasuwancin nasu,sannan ya dawo Nigeria yayi wani karatun afannin economic, daga Nan yafara aiki da hukumar efcc, yafara da matakin karamin ma'aikaci, har Allah yasa sukaga kokarin sa akan aiki dakuma jajir cewarsa,shugaban qasa ya nad'ashi shugaban hukumar, baya had'a kasuwancin su da aikinsa, aikinsa daban, harkar kula da dukiyar da mahaifinsa yabar masa Shima dabam, Kuma yana kula da hakan yana taka tsantsan akan duk wani abu dazai hada aikinsa dakuma kasuwancin sa, yana samun wannan matsayi yahadu da munirat, tanada samarinta sosai, Wanda suka sota tun tana qarama, suka Sha wahala Akanta, suka hidimta mata, Amma tana ganin Shahaab yafuto a matsayin jerin masu neman aurenta saita liqe masa, harma soyaiyar datake masa ta danne tashi soyaiyar, ta Kuma zabeshi a matsayin Wanda zata aura, acewarta yafi sauran samarin Nata nagarta.

Mama bataso yanemi yarinyar ba,taso ace yasamu yarinya da batasan waye Shiba, batasan kudinsa ba, itace zatayi masa soyaiyar gaskiya, Amma tana ganin idon munirat tasan cewa idon yarinyar abude yake akan son kudi, ta fahimtar dashi Amma soyaiyar munirat din data Gani acikin Idonsa yasa tarabu dashi ya aureta, abokan mahaifinsa suka shige masa gaba, Nan da Nan aka bashi ita, kasancewar sa Babban mutum Kuma sananne a qasar.

shekarar su Tara kenan da aure, haka Kuma a tarihin aikin nasu shine matashi na farko daya dade a matsayin shugaban hukumar, ba'a dade da dorashi ba ya auri munirat,a dadin shekarun sa a matsayin shugaba, a dadin shekarun aurensa, gaba daya shekarun sa 39, yayi aure yanada shekara talatin a duniya, Amma babu Wanda zaice yayi wannan shekarun kasancewar yanda yake motsa jiki, yake Kuma kula da jikin nasa, yasan cewa da yana candy yayi aure to tabbas da yanzu yarinyar sa kokuma yaronsa zaikai shekara Ashirin kokuma shatara,to Amma gashi har yanzu shiru babu haihuwa, Kuma yaga munirat abun baya damunta, shikuma yanason yaga yanada yaronda zai gajeshi koda ace baya Raye, kamar yanda Shima yagaji mahaifinsa.
Shahaab bai iya soyaiya ba, idan yanason mutum Tofa yana sonsa, da gaske yake saka mutum acikin zuciyar sa, shiyasa munirat tayi Kane Kane acikin tasa zuciyar, yanason mace Mai gashi, asali ma shine abinda yagani awajan munirat haryaja ra'ayin sa akanta, Bayan sunyi aure yagane gashin dokine take sakawa, maimakon ya hanata saiya qyale ta taci gaba da sakawa saboda Shima yanaso.


Bangaren munirat Kam Bahaka bane, rashin haihuwarsu baya damunta, kullum qawaye take biyewa suna kawo mata magungunan mata Kala Kala, dayawa daga cikin su batasan Dame aka hada akayi suba, kudi Kuma duk lokacin data so samu tana samu awajan mijinta, wani lokacin saita tsokano masa sha'awar sa cikin kissa zata Fashe da Kuka, yana tambaya abinda take wa kuka zata fada masa kudi takeso Kuma gashi account dinta yayi qasa, shikuma jinsa cikin wannan yanayin yasa zai bata kudade, Sannna ne zata bashi hadin Kai su Raya Sunnah yanda ya kamata

Shahaab yana yiwa mama biyaiya, tun tasowarsa yana qarami ita yake Gani, itace take masa komai,baisan mahaifinsa ba, mama itace komai nasa, tana sadaukar da Nata farincikin akan nasa, yana kiyaye duk wani abu dazai sata 6acin rai, yasan cewa Sarai batason munirat, akwai lokacin daya tambayeta meyasa batason munirat Kai tsaye tafuto tafada masa cewa matarsa kudinsa tagani shiyasa ta aure shi, sannan akwai alqawarin dasukai itada qawarta cewa zasu hada yayansu aure, Kuma yasani muddin Aysha ta bayyana Tofa saiya auri yarta inde mace ta Haifa, idan Kuma ba mace ta Haifa ba shikkenan.

Tun daga lokacin idan tasashi yayi wani kokari akai Dan agano qawarta, Sai yayi mursisi da batun, saboda bayason maganar hadin auren Nan datake yi kokadan.

Akwai lokacin data dameshi akan maganar, Amma Shahaab yaqi yayi mata binciken, tayi zuciya tafice tabar gidan a hanya kidnappers suka saceta (=��)

Saida yasha wahala kasancewar sa sannane yasa hukumar tsaro ta qasar tabashi hadin Kai har saida aka kamota daga hannunsu, tundaga lokacin ya zubawa gidansa tsaro, sojoji ne suke gadin mama, banda Yan sanda dasuke Gefe suma suna nasu aikin.

To dayaga de mama da gaske take, shine yabada sanarwa a kafafen sadarwa dakuma yanar gizo, ganin yanzu harkar yanar gizo kowa yanayin ta, shiyasa yayi tunanin za'a iya samun labarin qawar ta mama, abinda bai saniba shine Hajja A'i Kam vivo gareta itama screen din duk ya Fashe, wannan gidan ta abincin dazasuci sukeyi, bata yanar gizo ba(9&�)

To ganin haka yasa hankalin mama ya kwanta, Amma idan ta tuna qawarta, ranar haukace masa take, tun yana bata haquri harya dawo Shima yazama kamar ta, ya dinga zigata, to saita sauko su zauna lafiya.

Tsawon wannan shekarun munirat ko 6atan wata bata taba yiba, data fahimci hankalin mama dakuma shi Kansa Shahaab din yana kan haihuwa, saita shiga damuwa, akan yanda suke nuna son haihuwar, danhaka Sai take jinyar qarya, dasu amai, mama da Shahaab hankalin su yatashi, suce taje Asbiti taga likita ko ciki ne, saita kar6i maqudan kudade awajansa daga baya Sai tace ai ba ciki bane, tayi haka yakai sau uku, mama kuwa tariga tagane kawai kudin yarinyar takeso, bawai Shahaab din ne da haihuwar suka Dame taba

Tarasa Yaya zatayi, aure tsawon shekara Tara babu ciki, but ita hakan bai dameta ba saboda tana cikin daula, ko neman magani batayi, shikuma duk lokacin daya shirya yatafi Saudia Tofa addu'arsa daya ce akan Allah yabashi haihuwa, ita kuwa mama burinta guda biyu ne, nafarko taga qawarta, na biyu Kuma taga Shahaab ya haihu.

Duk juma'ah Ana bada abincin sadaka a gidan, kunu, abinci, dakuma bread tareda nera Dari biyar, wannan Kuma aikin mama ne, tana bada sadakar ne saboda Allah yakaiwa mijinta dakuma ahlinsa ladan.
Ta bangaren Shahaab kuwa lokaci zuwa lokaci yana yin tasa sadakar, Amma yafiyi lokacin zuwan azumi, yana sauke farashin kayan da kamfanonin sa suke sarrafawa domin talakawa su iya siya.

Back to story =�L�<���

******

Jigawa

Aisha ce take sallah, Hajja na gefenta tana Jan carbi, ta kalleta tace "mesunan qawa kiji tsoron Allah, wannan ba sallah kikeba, sallah batafi minti goma ba an idar"

Aisha batace mata komai ba, Sai abincin ta data Dauko tafara ci,batare data cire hijabin jikintaba, qwaine guda daya akan abincin Nata Wanda qawarta Walida tabata, Hajja taleqa kwanon abincin Aishan tace "Menene wannan nake Gani aciki?"

Cikin gatse tace "gishiri"

Hajja tata6e baki, Sannna taja bakinta tayi shiru tana kallon yanda gumi yake jiqa mata fuska, har gashin gaban goshin ta ya kwanta yayi luf-luf dashi, Amma Dan masifa Taki tacire hijabin jikin Nata, bacci ma wani lokacin da hijabi takeyi, tarasa Ina mesunan qawa tad'auki wannan dabi'ah

Wani yaro ne yayi sallama yashigo gidan yace "Hajja A'i abani kunun Aya na nera Dari"

Tace "idan Sadiya ce ta aikoka kakoma kace mata akwai kudin rannan ma"

Yaron yajuya yatafi, baifi minti biyar ba Sai gashi ya dawo, yace "Wai tace babu,bakya Binta bashi"

"au haka tace?, to shikkenan taje na rataya awuyanta, kawo Darin abaka"

Kudin yabata, Aisha tamiqe ta bude Dan qaramin fridge din Hajja tabashi kunun ayar, yatafi

Jabir ne yashigo gidan, Bai nufi wajan Ummah ba Kai tsaye rumfar dasu Hajja suke zaune yaje, ya kalleta yace "Hajja Dan Allah kisiyar min da wayar ki dubu uku"

Tace "kawo dubu biyar de saina baka"

Dariya yayi yace "wayarda batafi dubu uku ba?"

"aikuwa bazan siyar ba saide dubu biyar"

Aisha ta Kalle su tace "kawai kabata dubu ukun in taga Dama ta kar6a kokuma tabarshi"

Hajja ta yatsina fuska tace "yo Ina yaga dubu ukun ma?"

"Arziqi Aina Allah ne, Shima wataran zaiyi"

Hajja najin wannan furucin na Aisha saita Fashe da Kuka, da gudu umma tafuto daga daki tana tambaya "Hajja meyafaru kike kuka? Keda waye?"

Cikin kuka tace "nida mesunan qawa ne, nariga nadade da sanin me sunan qawa d'auka ta take a matsayin sa'arta, tunda taga ta girma tafara nono shikkenan ban'isa inyi magana ba acikin gidannan, saide in fad'a itama tafad'a,inda ace nasan haka halin yarinyar Nan yake tun farko daban Bari ansaka mata sunan qawata ba, saboda Bahaka halin qawata yake ba, saide in uwarta ce take Koya mata rashin kunya"(=��)

Ummah tanajin haka tafara hawaye, duk lokacin da fadan Aisha da Hajja zai tashi, to akanta take hucewa, Kuma ita bata Isa tahana Aisha zuwa wajan Hajja ba, Kota hanata ma Sai taje, Kuma ko tayi zuciya taqi zuwa inda Hajja take to Hajjan da kanta take zuwa sutafi

Ganin Ummah na kuka Sai hankalin Aisha yatashi, menene laifin Ummah anan daza'a ce itace take Koya mata rashin kunya, cikin 6acin rai ta kalli Hajja sannan tace "niba abinda Ummah ta take koyamin, gaba daya halin me sunana nabiyo, haka kawai antashi ansaka min sunan matarda banma santaba, qila ma tamutu" (=�F�<���
@&�)

Abbansu ne yashigo gidan dawowarsa kenan daga rumfarsu inda yake aikin facin tayar mota Kota machine, kukan Hajja ne yaqaru, cikin kuka ta kalli Aisha tace "ta Allah ba Taki ba, insha Allahu qawata tana nan da ranta, Kuma tana bayyana zan tattara kayana intafi inbar miki gidan ubanki"

Abba ne ya kalli Aisha yace "ke rufemin baki anan, marar kunya kawai"
Sannan ya kalli Hajja yace "Hajja Dan Allah kiyi hakuri Kidena kukan Nan, mesunan qawarki batada Hankali yarinya ce Kidena biye mata Kuna sa'insa Dan Allah"

Jan zuciya tayi tace "ai tashen balaga takeji,Kuma wallahi Mamuda bazan haqura ba saika Nemo min qawata kokuma kaje ka siyomin ruwan Roba"

Jabir da dariya ta kamashi saiya silale yabar gidan, Abba kuwa shiru yayi yana tunani, toshi yanzu Ina zaije neman wannan qawar ta Hajja? Shida ba aljani ba tayaya zai dinga yawo gari gari yana neman Aysha Yakubu sagagi, toma Aysha Yakubu nawane a Nigeria?>��
Har gara ruwan ma, danhaka ya kalleta yace "kiyi hakuri to, zan siyo miki ruwan, wanne iri kike so?"

Babu kunya tace "Faro" (>�#�)

Yace "to kiyi hakuri yanzu zanje nasiyo miki" daga Nan yajuya yafita daga gidan, itama ta dakawa Aisha Harara, Sannna tashige cikin dakinta.



SHAHAAB littafin kudi ne, Naira 300 kacal babu yawa,kibiya kafin free page su qare, zaki turo 300 ta wannan account din


0164549488
Amina muhammad
GTbank


Zaki turomin shedar biya ta Number ta 08033300034
<�8�SHAHAAB<�8�
(Romance)


Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha's Name

Like my Page On Facebook =�G�<���
https://www.facebook.com/amnahel


5&6


Baifi minti talatin ba ya dawo hannunsa d'aukeda baqar leda, yana zuwa yawuce Dakin Hajja yakai mata ruwan, budewa tayi taga faro ne guda biyu, tasaka hannu ta bude dayan tafara Sha, Sai da yaga fishin dake kan fuskarta yadan Kauce, sannan yatashi yafuto daga d'akin.

Aisha yasake yiwa fada sannan yashige dakinsa


******
ABUJA

Atamfofi ne a gabanta da shaddodi masu shegen kyau, d'ad'd'agasu takeyi tana magana cikin Isa "kayan sunyi kyau, Kuma sun kawo min su daidai kamar yanda nayi oder"

Ta kalli daya daga cikin ma'aikatanta tace "jeki kiramin munirat"

Cikin ladabi ta amsa sannan tajuya, Bayan wasu mintuna tadawo tace "Hajiya tace gatanan zuwa"

Jijjiga kanta tayi cikin ranta tana fadin lalle munirat ta'isa,intura aikiranta Amma saboda ta nunamin ita yar zamani ce batazata biyo yarinyar sutaho tare ba, saita nunamin itama tanada iko saboda tana auren Shahaab

Saida aka dauki kusan minti talatin sannan taqara so part din na mama,aqasan kafet din ta zauna tareda fadin "Gani mama"

Saida takusa minti goma, ta tabbatar ta6ata mata lokaci kamar yanda Itama tayimata, sannan tatura mata kayan tace "ga kayanki Nan, kidauki kikai wajan dinki"

Cikin ladabi ta d'auka tareda yimata godia, Sannna Takoma part dinta

Tana zuwa dakinta ta zubar da kayan tafada kan gadonta tareda fashewa da Kuka, ita kenan suturar dazata saka ma batada ikon dazata siyo da kanta taza6i irin Wanda take so saide sirika tasiyo takawo mata?

Yaya zatayi da wannan tsohuwar ne? Bata Rasa komai a gidan mijinta ba, wannan matar ita kad'ai ce ta tsaye mata, tarasa Yaya zatayi da'ita, wayarta ta janyo takira qawarta Mery, saide jin wayar Tata akashe yasa takira mamanta, cikin kuka ta zayyane mata komai, daga qarshe mahaifiyar Tata shawara tabata akan hanyoyin dazata dinga samun kudi ta hannun Shahaab, saita dinga siyar kalar kayan Dayayi mata, jin wannan shawarar ne yad'an sanyaya mata ranta.



******



Zaune yake a Babban office din companyn sa na takalma dake lagos, Sai wasu mutane guda biyar dasuke fuskantar sa, cup din tea ne a gabansa Sai turiri yake da alama yanzu aka had'ashi

Wata takarda ce agaban su Mai d'aukeda zanen taswira ta wani qaune dake jihar oyo, daya daga cikin su ne yake tsaye, gaban wata babbar TV dake manne abangon office din, yana Sanye cikin suit kamar yanda gaba dayansu itace Sanye ajikinsu, saide Shahaab yacire jacket dinsa yasakata a jikin kujerar dayake zaune, yad'ora Kansa a jikin kujerar ya kishingida kujerar Sai juyawa dashi take, Hankalinsa gaba daya yana kan matashin dake yin bayanin wajan daki-daki, wani ruwa matashin ya nuna yace "kwata kwata bangaren da zamu Gina company bashida ruwa, Amma a opposite dinsa akwai ruwa sosai Wanda yake wucewa, saide akwai titi a tsakani, sannan kamar yanda muka tattauna da gwamnan jihar, yabamu tabbacin cewa inde zamu ninkawa masu gonakin wajan kudin gonarsu to zasu siyar mana da gonakin, saboda Nan ne yafi da cewa da Gina company shinkafa, dazaran mungama zamu yi gada, wadda motocin zasu dinga bi ta wannan kan gadar, mukuma saimuja ruwan ta qarqashin gadar, wannan shine zanan wajan dakuma yanda yake, ga Kuma yanda tsarin ginin company zai kasance Bayan an kammala ginawa "

Ajiyar zuciya Shahaab yasaki, yace" duk Wanda zamu sayi gonarsu dake wannan dajin, ba ninki biyu na kudin gonarsu zamu basu ba, zamu basu ninki uku insha Allah "

Tafi sauran mutanan sukayi, saikuma daya daga cikin su yace"amma akwai yar qaramar matsala fa oga, nafarko daji muka yanka zamu fara wannan aiki, Amma munyi bincike mungano ginin yayi daji dayawa, yakamata ace wajen ya kasance na jama'ah dayawa ta yanda muma zamu amfanesu, suma Kuma su amfane mu, hakan zaisa kamfanin mu yazama kamar wata kasuwa ce ta daban da kowa zaiyi burin zuwa wajan, duk Wanda yazo wajan, dole zaiso jin farashin shinkafar mu, daga Nan mukuma zamuyi kokarin janyo shi jikin mu harya zama Babban customer awajan mu "

Kallan su Shahaab yayi yace" why not mu qirqiri gari awajan?"

Wani ne daban yace"tayaya?"

Shahaab yace" tunda wajan daji ne, saimu qirqiri gidaje,kamar guda Dari biyu, daidai Zaman mutum daya zuwa biyu, Sai mu rabawa mutane mabuqata, Wanda muka tabbatar basuda gidan kansu saina haya, kaga saisu dawo Nan suci gaba da rayuwar su"

Nan da Nan sukayi na'am da shawarar tasa.

Sign yayi akan takardar dazasu bada kwangilar aikin gidajen, saboda yanaso aikin ya kammala cikin Dan qanqanin lokaci, ba kowa yake son mallaka wa kamfanin ba face munirat, yasan cewa zatayi farinciki sosai, bayason ita kanta tasan da aikin, saide kawai ya gabatar da'ita a matsayin mamallakiyar kamfanin.



******


Da azahar suna zaune atsakar gida cikin yar qaramar rumfarsu, Almajiri ne yayi sallama gidan, yakawo mata jarkokin da aka siya kunun Aya a kofar gida tace"dan malam koma kasake dubamin akwai wasu jarkokin,ba dukane ba"

Almajiri yace "babu jarka Sai guda daya,Kuma Haladu me p.o.s ne yaturata cikin shagonsa yatafi masallaci"

Cikin jin haushi tace "ai shikkenan, qyaleshi, Sai yaje ya kaiwa uwarsa ta dinga d'ura kalanzir aciki, dama sana'ar tace" (=��)
Ummah da Abba sukai murmushi, sude basu Tanka mata ba, suna tsoron tahuce akansu

Tashi tayi tashiga Dan qaramin kitchen dinsu na ginin qasa, tafara zuba abinci, Wanda Aisha tagama girkawa yanzu, Alokacin itama Aishan tazo zata sakawa Abba nasa abincin acikin kula, Hajja ta kalleta tace "yanaga kinata raragefe, zoki dauki abinda

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment