Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafuto,Shahaab yana ganin ta yatashi tsaye, ahankali yace"Dr. Yaya jikin Nata?"

Mama da Hajja cikin sauri suka fasa fita suma suka dawo wajan Dr, mama tace"likita cikin yagama zubewa ko?"

Dr. Ta kalli Shahaab tace"jikinta da sauqi Alhamdulillah, saide tasamu rauni akanta, sannan Kuma ta zubar da jini da yawa, muna buqatar me irin jinin ta yazo mu dauka Sai aqara mata"

Sai Alokacin yasaki ajiyar zuciya, Ummah kuwa har lokacin tayi shiru kawai addu'ah take acikin zuciyar ta,Dr. Ta dubi mama tace"cikinta yana Nan bai fitaba, saboda ankawo ta Asbiti akan lokaci, da andauki tsawon lokaci ba'a kawo taba, to da tuni yazube, yanzu de muna buqatar jinin"

Ummah ta daga hannunta sama tana godewa Allah, Hawayen farinciki dakuma tausayin yartata yana tsiya ya daga idonta, Shahaab ya juya ya kalleta cikin sauri ya kauda kansa Gefe, matar tanada alkunya sosai, tunda suka shigo asbitin yaga bata cewa um bare um um, ya tabbatar duk yanda suke jin ciwo aransu basu kaita ba, tafi kowa jin ciwon abinda yasamu Aishan, Amma gata a zaune ta nutsu tana mata addu'ah, saiya sake jin Hankalinsa ya kwanta akan auren Aisha, koba komai tasamu tarbiya ta 6angare guda biyu, Hajja da Kuma mahaifiyar ta, kafin yagama wannan tunanin yaji Abba yana cewa"muje a dauki nawa agani ko zaiyi mata"

Cikin sauri Shima Shahaab yace"muje Dr."

Duka su ukun ne suka bita lab, aka dauki na Abba da Shahaab, dakuma Ramadan, Ana dubawa a kaga na Abba da Ramadan ne yayi daidai da Nata, na Shahaab baiyi ba,nasu aka dauka aka saka mata, sannan Shima Shahaab sukaje aka duba nashi hannun, inda yaji ciwo.

Bai kwanta ba, Ana gama masa sukaje suka duba jikin driver Wanda yaji ciwo harda karaya a hannunsa, sun dade a d'akin sannan suka futo, kan kace me Asbiti Yacika kowa yana zuwa dubashi, banda masu kiransa awaya suna masa jaje kasancewar labari ya watsu ko'ina, ba'a basu damar ganin Aisha ba Sai dare,gaba dayansu d'akin suka shiga, Alokacin itama ta farka Shahaab yana gefenta yana bata tea marar madara kamar yanda ta buqata, ansaka mata bandeji a goshinta, mama tace"Takwara ga abinci kici saiki Sha magani ki kwanta ko?"

Yatsina fuska tayi, sannan tace"mama banason cin abincin Nan"

Shahaab yayi qasa da murya bakinsa gab da Nata yace"mekike so?"

Kai tsaye tace"fruit zansha"

Cikin sauri yatashi yadauko mata fruit din dake ajiye agefe, ya zauna yafara bata,Ummah da Abba suka hada ido sukai murmushi, Ummah tace"to Allah yasawaqe, Bari mutafi gida"

Hajja tace"to saida safenku Hadiza, Allah yakiyaye hanya"

Aisha ta kalleta tace"Ummah idan zakizo gobe kimin kwad'on zogale, Amma karki sa suger aciki, kawai kimin haka"

Cikin sauri Shahaab yace"zogale Kuma?"

Kallonsa tayi, tayi kalar shagwa6a da fuskarta batace masa komai ba, Girgiza Kansa kawai yayi, baice komai ba

Ummah tayi murmushi tace" to zan kawo miki"
, sannan suka fita, Ramadan Kuma yabisu abaya domin rakiya.


Mama da Hajja ne suka zauna da Aisha, Shahaab da Ramadan kuwa basu tafi gida ba Sai wajan karfe goma Sha biyu saura, a hanya Ramadan ya kalleshi yace"yanzu menene abun yi? Yaya za'ai da mutanan Nan?"

Shahaab yasaki ajiyar zuciya yace"zanyi musu waya su lallasa musu jiki sannan su kaisu gidan kurkuku su rufesu, ciki harda ita ogar tasu, inda ace cikin Nan yazube, wallahi saina makata a court"

Ramadan yace"yanzun ma ai dole Sai an tura case din court,Amma yakamata kasanar ayi Maka tsakani kaida munirat, saboda yanzu da abun yazo da qaran kwana da tuni cikin da muke murna dashi yazube, sannan driver yamutu, kaga rayuka guda biyu ace a dauki haqqin su abun babu dadi, kawai ayi muku tsakani kaida ita"

Shahaab yayi murmushi baice komai ba,shi kadai yasan me yagama shirya wa a ransa, haka suka qarasa gida Ramadan ya ajiyeshi, sannan yatafi gida, shi kadai ya kwana a gidan Bayan yayi wanka, Dasafe Ramadan yakai matarsa asbitin ta duba jikin Aisha, sannan yawuce gida yadauko Shahaab Wanda yake shirin futowa domin tafiya asbitin , Kai tsaye yace"muje wajan wadancen masu laifin"

Babu musu Ramadan yajuya kan motar sa zuwa police station, suna zuwa mutanan wajan suka fara bashi girma Ana gaishe shi,Sarai yaga momy a zaune agefe itada yayun munirat su biyu, Sai share hawaye suke, Amma yayi mursisi yarabu dasu yayi kamar bai gansu ba,Kai tsaye d.p.o yawuce dasu zuwa office dinsa,Bayan sun gaisa dakuma jajanta abinda yafaru Shahaab yafuto dawasu takardu guda biyu daga cikin aljihunsa yabawa d.p.o sannan yace"kabawa munirat wannan takardun, sannan atura case din court, ayi musu hukunci daidai da abinda suka aikata, Badon Allah yakiyaye ba, da yanzu driver na, da matata dakuma abinda yake cikinta sun mutu"

Cikin sauri d.p.o tace"Angama ranka yadade"

Ramadan yasaka hannu a aljihunsa ya ajiyewa d.p.o damin kud'ad'e sannan suka futo daga office din.

Ahanya Ramadan ya dubi Shahaab ysce"nayi tunanin zakace ayi muku tsakani kaida ita, sannan ayi musu duka gaba dayansu, Amma sainaga kace abata wasu takardu menene amfanin hakan?"

Shahaab yayi murmushi yace" wannan takardun danace abata, tafi Dukan da zance ayi mata, wannan takardun danace abata Sai ta gwammaci ayi mata duka akan ta gansu, babu wani abu dazaka yiwa mace,macen ma wadda take sonka, irin ka saketa, munirat tayi min abubuwa qarshe nasaketa saboda idan nabarta agidana ma to na budewa fitina da tashin Hankali qofa,takardun danace abata Kuma results din maamah ne na samun cikinta, wannan ma kadai ya isheta"

Ramadan yayi ajiyar zuciya yace"abun de babu dadi, Allah yasa mudace ya kiyaye gaba"


Shahaab ya Lumshe Idonsa yace"Amin"


Bayan tafiyarsu Shahaab , d.p.o yabawa wani kofur takardar da Shahaab yabashi yace"abawa waccen matar"

Kofur yakar6a yawuce yabawa munirat da idonta ya qeqashe ko d'igon hawaye babu,taso ace taji labarin mutuwar Aisha, saboda ta kowanne ganni Gani take itace tayi mata katanga tsakanin ta da Shahaab, haqiqa taso ace ta mutu saita ga Ina zai Kai rawar jikin dayake akan ta, shikkenan yayi biyu babu,itan dayake qi yasake ta, Aishan dayake so tamutu, tana budewa taci Karo da result din cikin Aisha na farko Wanda akayi mata test a Nigeria, sannan ta duba dayar taga Wanda akayi mata test ne a India, ihu tasaka tana kururuwar kuka, tayi watsi da takardun, lokaci daya numfashinta yafara yin sama, tasa hannu ta dafe qirjinta, cikin sauri su momy suka qarasa suka dauki takardun domin ganin abinda yasa ta cikin wannan hali, suna Gani jikin momy yad'auki rawa,hakan yana nufin Shahaab de lafiyarsa kalau abun daga 'yarta ne, hawaye ne yazubo mata, cikin tashin hankali tafara roqon Yan sandan su taimaka su futo da munirat daga magarqama domin taga halin da yarta take ciki.


(littafin kudi ne, idan kika karanta baki biyaba nabarki da ALLAH)

******


Zaune suke a d'akin da aka kwantar da Aisha, Shahaab yazuba mata ido yana kallon yanda take cin kwad'on zogale kamar marar gata, daya gaji da kallon ta saiya dauki wayarsa ya turawa Dr da sukaje wajan sa India saqo ta email dinsa dangane da matsalar cikin Aisha shin yanzun zai iya kusantar ta? Dr Kuma ya tabbatar masa zuwa yanzu Kam babu matsalar komai, Kuma yin hakan zai sake taimaka wa abinda yake cikinta yazama Mai lafiya da Kuma kuzari, idan bayayi dinma akwai matsala, jin wannan bayanin ne yasa Shahaab farinciki, yayi masa godia sannan sukai sallama ya maida wayarsa cikin aljihunsa.

Satinta d'aya a Asbiti aka sallameta, duk wata kulawa data dace anbata, sosai jikinta yayi kyau saide fari data sake yi, tunda suka dawo gida Nan ma mama da Hajja basu Barta Takoma part dinta ba, saida tasake murmurewa sosai sannan Hankalinsu ya kwanta sukai maida ta part dinta, zuwa wannan lokacin an yanke wa su munirat hukunci inda aka tura su gidan kurkuku tsawon wasu watanni.

Ranar da Aisha Takoma part dinta a ranar Shahaab yasake zama ango, domin kuwa tsawon lokacin Nan daya dauka baiyi ba saida ya fanshe shi, Kuma abinda yasake bashi qwarin gwiwa shine yanda yaga Aishan itama tanaso, a ranar basu zo part din mama ba, suna can manne da juna suna soyaiya kamar zasu cinye kansu.


Washe gari suna zaune a dinning suna fara breakfast,Aisha ta miqe tana cewa"bari in sake shan tea dinnan naji yamin dadi sosai"

Mama tace"bari inhada miki takwara, yi zamanki"

Babu musu ta zauna, mama Kuma ta had'a mata tea din Wanda yake turiri sosai saboda zafi, Aisha tasa hannu zata kar6a Shahaab yayi wuf ya kar6e cup din yace"mama wannan ai yayi zafi dayawa"

Hajja tace"to d'aga mata shi zakayi?Dan Allah kudena sangarta yarinyar Nan,kubarta ta dinga aiki da kanta saboda haihuwa ce a gabanta"

Cikin damuwa Shahaab yace"ni ban hanata shaba, Amma wannan de yayi zafi dayawa idan kuma yaqona min Baby fa?"(>�-�)

Hajja ta tuntsire da dariya tace"idan batasha ruwan zafi ba, ai zatasha a wankan jego, zamu gauraya ne"

Shahaab baice komai ba saida yaga tea din yadena turiri sannan yabawa Aisha, mama kuwa murmushi tayi tana jin dadin yanda Shahaab yake Bawa Aisha kulawa.


Haka rayuwar tasu take tafiya cikin kwanciyar Hankali,idan Aisha tayi fada da Shahaab to akan cikin tane,bata Isa tadanyi gudu ba kokuma wani aikin saiya fara yimata fad'a yana masifa zata kashe masa Baby,hakan dayake mata saiya sake harzuqa ta tabiye masa su dinga fada, daga qarshe Hajja tayi mata fada da nasiha akan ta dinga yimasa uzuri akan cikin, abinda yadade shekara da shekaru ne yana nema yanzu Kuma yasamu, fadan Hajjan ne yasa take haquri dashi Ahaka har Cikin Yacika wata takwas, a Asbiti aka bata umarnin ta dinga yin tattaki saboda jikinta, cikin yafuto sosai ya girma duk Wanda ya ganta zaiyi tunanin haihuwar tazo yau ko gobe ne, Nan kuwa akwai sauran kusan wata daya, yau ma tagama Dan zazzagaya compound din Adede lokacin Shahaab yadawo daga wajan aiki, daga nesa ya hangota tana tafiya daqyar ga uban hips dinta yasake bajewa babu hijabi ajikinta wani mayafi tad'an yafa hannunta d'aukeda d'ata tanaci, Sai wata me aiki a gefenta tana riqe da wani plate Wanda yake d'aukeda d'ata dakuma kayan marmari, bata lura da zuwansa ba, Alokacin da aka bud'e masa mota yafuto harsun shige part din mama, Shima Kai tsaye part din maman yawuce yana zama a kujera ta kalleshi tace"Uncle sannu da zuwa"

Yace"yawwa Maamah,Ina Baby na?"

Idon mama ta Faka taga hankalinta baya kansu, sannan taja hannunsa tad'ora masa akan cikin tace"tun dazu yaketa motsi"

Qasa yayi da muryarsa cikin rad'a yace"ko yanason jin d'umin Babansa?"

Babu musu ta daga masa Kai, murmushi yayi sannan yajuya ya kalli Mama yace"mama, adena barin Maa-mah tana fita compound Dan Allah, baki saiya kamata, mutane Sai kallon ta suke itama Sai ciye ciye take agaban su"

Aisha tanajin haka cikin shagwa6a ta turo Dan qaramin bakinta gaba,mama ta galla masa harara sannan ta maida Hankalinta kan kallon datake.

Shima da yaga bata tanka masa ba, saiya futo da takardu daga cikin briefcase yabawa Aisha yace"kisa hannu a wannan takardun,Ana qoqarin daukar ma'aikatan dasuka dace a kamfanin ki, idan akwai Wanda kike so kisake d'auka saikiyi musu magana su kawo takardunsu Sai a tantance su agani".

Kallonsa tayi tace"Uncle Dama inaso In fadama Dan Allah inason in koma makaranta kodan saboda aikin Nan, inaso Nima indinga zuwa office, Ina aiki kamar mata ma'aikata"

Lokaci daya yanayin fuskarsa ya sauya, ya kalleta yace"tunanin da kike kenan?"

Cikin sauri tace"emana, to tayaya zan riqe company Bayan ba karatu nayi ba? Ai dole in koma makaranta Uncle"

Cikin daure fuska yace"wannan tunanin ki kenan,idan Zaki cire karatu aranki, toki cire, domin kuwa,ba-za-ki-yi ba"
Yaqare maganar a rarrabe

Wani irin kallo tayi masa, bata Tanka masa ba tatashi ta wuce dinning domin kuwa wata irin baqar yunwa takeji, mama ta kalli yanda Aisha take tafiya daqyar, ta juya ta kalli Shahaab tace"kaje Kaci abinci mana, kosai kagama fad'an karatun tukun?"

Murmushi yayi yace"mama Dan Allah tayaya zan Barta tatafi wata makaranta?Kuma Babyn nawa waye zai dinga bashi kulawar data dace?tunda cikinta ya tsufa Hankali na atashe yake, fatana kawai tasauka lafiya,Amma ita maganar karatu ma take, Ni wallahi tausayi ma take Bani kwana biyun Nan daqyar takeyin komai, har yanzu bata cika shekara Ashirin ba, ko zata Iya haihuwar ma da kanta?"

Mama ta ajiye wayar hannunta wadda take ta gwada Kiran layin Hajja Amma taqi shiga, ta kalli Shahaab tace"tayaya Kuwa zata Iya haihuwa tunda nauyin mijinta ma bata iya daukewa?"(=�2�=�H�)

Shahaab ya kalli Mama da sauri, cikin kunya yasosa qeyarsa, batare da yace komai ba sum sum yawuce dinning din Shima.(=��)




Please kuyi hakuri da wannan bayawa, nagaji ne =�O�<���





Shahaab littafin kudi ne, ki biya naira 300 ki karanta, idan kika karanta baki biyaba nabarki keda ALLAH


0164549488
Amina muhammad
GTbank


Kokuma katin MTN tareda shedar biya ta wannan number 08033300034




Mrs Usman ce
'<���

Page 25





Zama yayi a dinning d'in yana kallonta qasa qasa,abinci takeci da hannunta dayan hannun Kuma wayarta take danna wa, ahankali yatashi tsaye yazare wayar hannunta, sannan ya zauna tareda ajiye wayar agabansa, Kallonsa tayi, tace"Uncle fati zan kirafa"

Abincin yasake qara mata yana fadin"kici abincin tukunna"

Batare datace komai ba tamaida Hankali wajan cin abincin, saida taci taqoshi, sannan tafara hamma, kallonta yayi, Adede lokacin itama ta kalleshi, cikin kulawa yace"bacci?"

Tace"wallahi, bacci nakeji uncle, tunda natashi Dasafe ban sake yin bacci ba"

Abincin sa yakeci cikin kulawa ya nuna mata dinning din yace"kwanta, Bari ingama Sai muje ki kwanta"

Babu musu ta dora akan dinning din, har saida yagama cin abincin sannan ya kalleta yace"muje, ko bazaki iyaba na daukeki?"

Murmushi tayi tace"zan'iya uncle"

Hannunsa takama suka nufi wajan mama, yad'auki kayansa suka tafi, mama tabi bayansu da kallo tana murmushi, cikin ranta tana tunanin wayaga Shahaab da d'a?inajin da zai iya da jikinsa zai dawo da ciwon Aisha, ansan cewa dole a tausaya mata kasancewar ta yarinya qarama ga Kuma halin datake ciki, Amma itama lokacin data haife shi shekararta goma Sha takwas, ita haihuwa aita Allah ce, idan Allah ya sauketa lafiya abunda ake Fata kenan, Amma saka damuwa acikin rai duk ba nasa bane, addu'ah kawai itace mafita.

Suna shiga part dinsu ya maida kofar ya rufe, yasaka hannu ya dauketa cimak, basu tsaya ko'inaba Sai dakinsa, akan gadon ya kwantar da'ita, sannan yafara rage kayan jikinsa, saida yacire komai yarage dagashi Sai boxer sannan ya kwanta tareda janyota yashigar da'ita cikin jikinsa, hannunsa ya dora akan cikinta, sannan yayi kissing din wuyanta yace"Cikin Nan tunda ya girma ya hanani rungume mata ta yanda ya kamata"

Murmushi tayi tace"nan gaba kadan ma tsakanin mu zai dinga kwanciya"

Murmushi yayi Shima yace"idan mace ce to wallahi bata isaba, idan namiji ne Shima wallahi bai isaba,babu Mai shiga tsakanina da matata Sai Allah"

Murmushi tayi tana Lumshe idonta tace"me kakeso mu Haifa uncle?"

Sake Sakata cikin jikinsa yayi sannan yace"ke mekikeso ki Haifa?"

Idonta a Lumshe tace"mace...,inason in haifi 'ya mace insaka mata sunana, sannan Kuma ace tana Kama dakai, Mai dimple irin Naka, indinga yimata kwalliya, indinga yimata vedio, mudinga fita yawo, tazama babbar qawata"

Cikin jin dadi yace"nide nafison ki haifamin namiji, saboda shine jigon gida, Kuma shine idan Allah ya rayashi zan'iya dorashi akan komai nawa, zai taimaka min akan komai Sa6anin mace, Amma Kuma a mahanga ta Hankali saide muce Allah yabamu mafi alkhairi ko?"

Murmushi tayi tace"hakane, Allah yabamu mafi alkhairi" daga Nan ta Lumshe idonta, tanajin yanda yake kissing wuyanta, hannunsa Kuma yana cikin rigarta yana shafa cikinta.

Sun dade suna bacci, bacci Mai cikeda nishadi dakuma jin dadi, shi bai farka ba itama haka, saida suka dauki lokaci sunayi sannan suka tashi, kayanta yacire mata, ya dauketa suka shige toilet, a toilet dinma sun dade acikin ruwa suna murzar jikin junansu kamar karsu rabu, sannan suka futo suka gabatar da sallah,basu je part din mama ba Sai dare, suna zuwa kuwa Aisha taga Hajja tazo, tsaya wa yayi yana waya daga Gefe, ita Kuma ta qarasa wajan su, Hajja ta kalleta tace"meciki"

Murmushi tayi tace"Hajja Ina Ummah, meyasa Baku taho tare ba?"

Hajja Tace"ina Hadiza Ina zuwa gidanki me sunan qawa?Nima yanzun zuwa nayi muna magana akan yajin da za'a miki"

Shahaab daya qaraso falon ya zauna agefen Aisha yace"Hajja wanne irin yaji Kuma?"

Kallan sa tayi tace" d'an yajin daddawa mana da akeyi, haihuwa tana tafe ai muma Gara mufara shiri,wannan yarinya Allah de ya saukeki lafiya"
Ta qarasa maganar cikin alhini,Aisha ta harareta tace"ji Hajja,Dan Allah ni karkisa naji tsoro, mama kinga Hajja ko" ta qarasa maganar tana kallon mama

Mama tayi dariya tace"rabu da'ita takwara, kalau Zaki haihu kinji,keda kike da likita atare dake, babu ruwanki da shan wahala"

Shahaab yayi murmushi, zai iya yiwa wani komai Amma baya jin zai iya ta6ukawa Aisha wani abu, kwata kwata bashida qwarin gwiwa inde Aisha tana cikin tashin hankali, gaba daya rud'ewa yake yarasa meyake masa dad'i.


Har qarfe Tara Hajja tana gidan, tana zaune suna Dan ta6a hira itada mama, tana Kuma Kiran mutanan Chamo suna ta magana akan shirye shiryen haihuwar Aishan, Sai wajan karfe goma sannan tatashi zata tafi mama tasa hannu tajata ta zauna tace"ai kinzo kenan,narasa me kike yi acan gidan idan kinje wallahi, ki zauna anan mana mudinga Dan zantukanmu"

Hajja tace"ko? To ai can dinma Hadiza tana zaune ita kadai babu dadi, Kuma idan muka zauna din muna Dan ta6a hirar mutanan mu nacan"

Shahaab yayi murmushi yace"kiyi zamanki kawai Hajja, itama ba mijinta yana Nan ba"

Cikin sauri Aisha ta kalleshi tareda mintsi ninsa, murmushi yayi yana shafa wajan yace"yi haquri, ni bada wata manufar nafada ba"

Mama tace"ai Gara dakika mintsine shin kozai tuna akan surukansa ake magana"

Hajja tace"to Bari in zauna, idan na kwana biyu anan Sai inje can itama namata kwana biyu"


Haka sukaci gaba da Zaman su afalon suna kallo suna hira, har shadaya na dare sannan suka koma nasu part din, acan dinma Bayan ta kwanta shi computer ya dauka yadan rage wasu ayyukan sannan shima ya kwanta.

Haka mama ta dinga yaudarar Hajja ta hanata tafiya sukaci gaba da zamansu a gidan cikin kwanciyar hankali har cikin Aisha Yacika wata Tara cif, tun daga Nan Kuma hankalin kowa yadawo kanta, ma'aikatan gidan ma kowa ido yazuba mata yana jira yaga mezata Haifa, sunsan cewa uban gidan nasu Sai yafi kowa murna akan haka.

Tun Ana tunanin haihuwar akan lokaci har suka daina, saida ta qara sati biyu, Alokacin ma basuyi tunanin haihuwar zata zo ba, itama Kuma kasancewar haihuwar ba sanin ta tayi ba, Sai hankalin ta bai kawo mata haihuwar ba, yau tunda safe yafita wajan aiki, Alokacin tana bacci bata tashi ba, tun shekaran jiya take danjin ciwon baya, saitayi tunanin ko yawan kwanciyar datake ne, ga mararta tana mata nauyi, babu Wanda ta fadawa wannan sauyin yanayin nata
Baccin Nata yayi dadi sosai, kad'an kad'an mararta tana mata ciwo, tasa hannunta akan marar taci gaba da bacci, can bacci yayi Nisa taji wani irin ciwon Mara yataso mata, cikin azaba tafarka, yatsina fuskarta tayi, sannan ta sakko da qyar ta wuce toilet tafara fitsari, anan taci karo dawani irin ruwa yana zuba ajikinta,hakan yasa tacire kayanta tafara wanka, kafin tagama wankan taji marar Tata tasaki, ahankali tagama komai tafuto tayi sallah, sannan tasaka wata doguwar Riga me fadi ta nufi part din mama, ahankali take takawa ma'aikata Sai sannu suke mata, mamaki yasake kamata jin wannan ruwan yana sake bin jikinta, tana saka qafarta a part din mama, taji gaba daya qafafunta sun riqe, mararta ta d'aure dawani irin ciwo na fitar Hankali, cikin azaba ta tsugunna awajan tana runtse idonta, mama da Hajja suna zaune kwata kwata hankalin su baikai bakin qofar ba, Aisha kuwa idonta a runtse yake wani irin gumi ya tsatstsafo mata, jitayi wani irin abu yana neman rabata gida biyu, tsananin azabar dataji ne yasa tasaki wani irin qara tareda fadin"mama!!!"

Azabure suka juya itada Hajja, suna ganin Aisha a tsugunne suka fita a guje sukayi kanta, Hajja tana duddubata ta kalli Mama tace"Aysha inajin haihuwar ce tazo"

Mama da jikinta yakama rawa tace"eh gashinan Kam Naga kamar akan gwiwa take"

Cikin sauri suka d'ago ta Hajja ta riqeta tana mata sannu, hawaye ne yafara bin fuskarta tana yarfe hannu, mama kuwa a guje tashige d'akin da suka adana kayan haihuwar ta Dauko wasu kayan, sannan tafara Kiran wayar Shahaab, yana d'auka tace"kana inane"

Yace"ina office mama,meeting muke"

Tace"to yarinyar Nan ce babu lafiya, Ina tunanin haihuwar ce tazo, gashinan Nan de zamu tafi asbi..."
Kafin tagama magana taji ya kashe wayar, wayar ta kalla kawai ta jefata cikin Jakarta, Alokacin har Hajja sun qarasa gaban mota, gaba daya ma'aikatan gidan kowa mamaki ne ya kamashi ganin yanzu yanzu ta wuce ta gabansu Amma har naquda tatashi, suna shiga cikin mota driver yaja a guje suka fice daga gidan.

Ko Nisa basu yiba suka hadu da Shahaab, yana ganin motar su ya tsaida su, yafuto daga motar dayake, yakoma cikin motar su mama, yashiga gaban motar sannan driver yaja, juyawa yayi ya kalleta kwata kwata ma bata cikin hayyacinta, mama da Hajja sun sata atsakiya Sai sannu suke mata, yayinda Hajja take goge mata Hawayen idon Nata, shikam Idonsa ne yayi zuru zuru kamar marar lafiya, baya cikakken minti daya, batareda ya juya ya sake kallon ta ba, suna zuwa asbitin aka kar6eta, Hajja tafara Kiran wayar Ummah da Abba zata sanar dasu, Shahaab ya zauna yad'ora Kansa akan hannayensa, abun duniya yataru yayi masa yawa, yayinda mama take zarya takasa tsayuwa haka Kuma takasa zama waje d'aya,suna jiyo yanda Aisha take kuka tana salati, har kusan awa daya bata haihu ba, ahankali yatashi yacire suit din jikinsa, yacire agogon hannunsa ya ajiye su anan, Kai tsaye yashige cikin d'akin, mama da Hajja suka bishi da kallo, yanayin da yaga Aisha yasa gabansa faduwa, ba kowa ne yafado masa Arai ba Sai mama, itama haka Tasha wahala kafin ta sameshi, kasancewar sunsan cewa Shima yasan aikin shiyasa babu Wanda ya hanashi, sun dauki tsawon lokaci Ana abu daya, sannan haihuwar tazo gadan gadan, shida Kansa ya qarata, sannan ya kar6i haihuwar ta da Kansa, shi Kansa yayi mamakin yanda yasamu wannan qwarin gwiwa, lokaci daya su Hajja sukaji kukan Baby Yacika falon, hawaye mama tafara, tana zubawa Allah kirari dakuma godia agareshi, acikin d'akin ma Shahaab yana ganin Babyn a hannunsa wani irin hawaye me dumi ya zubo daga Idonsa, nurse din dake gefensa tasa hannu ta kar6i Babyn sannan tace masa"yalla6ai congratulation, Baby boy ne"

Hannu yasa ya goge Hawayen, sannan yafara cire safar hannunsa, yakoma ga Aisha yana kallon ta, wadda tuni baccin azaba yayi gaba da'ita, sauran nurse din Kuma suka fara gyara mata jikinta, saida aka gyara baby tsaf, aka saka masa kayan Sanyi farare masu mutuqar laushi, sannan suka Bawa Shahaab shi, nurse din tace"yalla6ai gashi,Bari mu qarasa gyara madam"

Babu musu ya kar6i Yaron Wanda yakasa dauke Idonsa akansa, Yaron yana bala'in kama dashi sosai, babu abinda yabari nasa, fari ne tas 6ul6ul dashi kamar ba Aisha ce ta haifeshi ba.


Yana futowa mama da Hajja da Kuma Ummah da Abba Wanda Zuwansu kenan sukayi Kansa, gaba dayansu kowa kokari yake ya kar6i Babyn, Hajja ce tayi nasarar kar6arsa, ahankali yasaka hannu yasake goge Hawayen Idonsa,yace"nagode mama"
Mama tace"godia tame Kuma Mahmud?"
Saida yasake goge Hawayen sannan yace"dakikasa nazama likita, duk da baki barni nayi aiki ba yau gashi dalilin karatuna na temaki matata"
Murmushi tayi ta kalleshi Tace"to naji, yanzu de kayi shiru kuka Kuma ya qare Mahmud, saide ka godewa Allah bisa kyautar Dayayi ma"

Cikin sauri Hajja tace"um um Aysha barshi ya koka, irin wannan Baturen d'a haka ai dole ubansa ya koka harda shashsheka..."(=��)


Gaba dayansu dariya suka saka, Shahaab yayi mata wani irin kallo me cikeda harara, sannan ya goge Hawayen idon nasa, mama Tace"Ashe zaka iya kar6ar haihuwar? Yaya jikin nata to?"

Ahankali yace"tana bacci, bansaniba Kota farka, nafuto zasuyi mata dinki"

Hajja tace"oh wannan yarinya tana ganin dinkuna, gana Daren farko gana haihuwa"

Shahaab yaji wata irin kunya ta kamashi kamar ya nutse awajan, kasancewar Ummah da Abba suna wajan, Sai akai sa'ah Adede lokacin aka kira wayarsa, cikin sauri ya matsa Gefe yafara wayar, daga office dinsu ne, sunyi tunanin zai dawo aci gaba da meeting din, Sai yafada musu labarin haihuwar, yakuma nemi excuse awajansu,Bayan Nan Kuma yakira Ramadan, yana dauka yace"Albishirinka"

Ramadan yace"goro"

Shahaab yace"Maamah tasauka,Nima nasamu Baby boy dina"

Ramadan yace"Alhamdulillah, Allah abun Godia, kuna Ina yanzu?"

Cikin farinciki yace"muna Asbiti"

Ramadan ya kashe wayar, shikuma Shahaab yakoma wajan su Hajja, yana zuwa yaga Yaron yana hannun Ummah, Adede lokacin nurse ta futo tafada musu cewa sun maida ta Dakin hutu idan anjima zasu iya shiga su ganta.

Zuwa yamma mutane sun cika asbitin, mutanan dayake meeting dasu, dakuma Wanda Ramadan ya faffadawa kowa kokari yake yazo yaga Yaron Mahmud Wakili, gaba dayansu suna cikin ke6antaccan Dakin da aka Kai Aisha, tana zaune kalau da'ita

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment