Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan uban kudin?"

Baice da'ita komai ba, ya kalli jabir yace"kiramin yayarka"

Jabir yaje Dakin Hajja yace "qawar Hajja kizo inji Abba"

Haka kawai taji faduwar gaba ta ziyarceta, cikin sanyin jiki tafuto ta zauna akusa da Hajja, ahankali tace "Abba Gani"

Abba yajuya ya kalli Hajja yace "to Hajja gatanan, wannan kudi da kike Gani kudin biro ne, saboda haka ta bude baki tafada mana waye yabata Biron? Saboda ni kwata kwata ban yarda da yarinyar Nan ba"

Yajuya yasake kallon Aisha da kanta yake qasa, idonta Yacika taf da hawaye, sannan yace "AISHA...., fadamin waye yabaki wannan Biron? Sannan Ina kike zuwa da daddare?"

Cikin sauri Hajja tace "bangane Aisha haka Kai tsaye ba mamuda, sunan qawar tawa kake kira haka? Ashe zaka iya kirana Kai tsaye Nima? To Bari kaji idan baka yarda da wannan yarinyar ba mamuda Nina yarda da'ita,tayaya za'ace biro qwaya daya jal nera dubu Dari hudu da hamsin? To shi Biron baya qarewa ne?"(>��)

Abba yace"Hajja wannan biro haka kudinsa yake, kuma qarya take tasan inda taje ta Nemo shi, saboda ban yarda da ita ba, ta bude baki ta fadamin gaskiya kokuma yanzun Nan inyi mata dan'iskan duka wallahi"

Hawaye ne ya zubo daga idonta, ahankali tafara shashshekar kuka, cikin wata irin murya tace "Abba Dan Allah kayi hakuri"

Cikin 6acin rai Abba yace "ta tabbata kenan abinda malam Manu ya fadamin gaskiya ne ko? Irin tarbiyar Dana baki kenan ko?"

Hajja ta kalli Aisha tafara tafa hannu tana salati, tace "Nina Rasa abun damuwa anan mamuda, waime kake nufi da wannan maganar taka ne? Memakon kayi murna yarinya tafara samo mana kudi Amma Naga Kai tuhumar ta ma kake, ni idan hakane ai jummai rufata tayi, inusa ba mijin aure bane, duk Wanda yabawa mesunan qawa wannan biro ai shine mijin aure "(=�D�=��=�F�<���
@&�)

Ummah ta zubawa Aisha ido tana kallonta, Sarai tasan akwai abinda take 6oye musu, yanayin ta kawai zaka kalla kasan batada gaskiya,tsoronta daya kartaje wani marar tsoron Allah yayi amfani da rashin wayon 'yartata yana amfani da'ita awani waje, saboda babu Wanda zaiga qirar Aisha yaji bai kwadaitu akanta ba,share Hawayen idonta tayi,cikin muryar kuka Ummah tace"waye yabaki Biron? Sannan Ina kike fita da daddare?"

Cikin kuka tace" Ummah ni gidansu Walida nake zuwa"

Abba yasa hannu yad'auki wayar hajja dake ajiye agefe, number Walida yadubo yakira Walida yasa ta a amsa kuwwa yanda kowa zaiji abinda take fada, Walida tana daukan waya Abba yace "Walida mamuda ne"

Cikin ladabi ta gaishe shi, Shima ya amsa mata, sannan yayi mata ta manya yace "meyasa bazaki yiwa qawar ki fada bane ta dinga zuwa gidanku da rana, Amma kullum saide tazo da daddare, mu kinga munyi mata fada, taqi jin maganar mu"

Walida bata gane shan cikinta Abba yake ba, tayi murmushi tace "Abba da daddare Kuma? Ai Aisha bata zuwa da daddare, sau daya tata6a zuwa wajena da daddare Kuma Shima narakota har gida, ka tambayi su Hajja zasu fadama ma nazo gidan"

Abba yace "eh anyi haka fa, na manta wallahi, toki gaida mutanan gidan" daga Nan yakashe waya.

Kukan Aisha ne yake tashi awajan, sosai take kuka harda Jan zuciya. Abba ya kalleta yace "muna jinki, wajan wa kike zuwa?"

Cikin kuka tace "SHAHAAB"

Hajja tanajin haka tafara tafa hannu,Nan da Nan hawaye yafara sauka akan kumatunta, cikin mamaki tace "mesunan qawa?,to kode shine yabaki ribbon din Dana Gani a kanki kikace Walida ce tabaki?"
Babu musu ta daga kanta alamun hakane,
Cikin 6acin rai Abba yatashi ya wanketa da Mari yace "waye SHAHAAB?"

Zafin Marin ne yasa tasaka hannu ta dafe kuncinta, muryarta na rawa cikin kuka tace "shi.... Shin.. Shine yake zuwa yake kirana awaya Sai naje, Abba Allah Ina sonsa nide"

Wani Marin Abba yasake mata, cikin 6acin rai da takaici yace "shine kike binsa har cikin mota yana hure miki kunne ko? Ai kinsan da maganar inusa, wato irin mayaudaran samarin Nan ne yake zuwa wajan ki yana hure miki kunne harni Zaki kalla kina cewa ke kina sonsa ko? Idan na qara ji kince kina sonsa saina kakkarya ki a gidannan, Kuma daga yau babu ke babu shi,inusan damuka Sani shi zamu baki"

Cikin kuka tace "Allah banason inusa, nide Shahaab nakeso"

Jin abinda tace yasa Abba yayo kanta zai rufe ta da duka, cikin sauri Hajja tajanyota jikinta,
Hawaye ne suka sulalo daga idanun Ummah,koma waye wannan Shahaab haqiqa yariga yagama hurewa yarsu kunne, tunda gashi har mahaifin ta yana fada itama tana fada.

Hajja tasaka salati tana sake rushewa da Kuka, cikin kukan tace "wannan masifa Dame tayi kama? Mesunan qawa Ina kika samo wani Shahaab Kuma? Yaushe Zaki bi saurayi har cikin mota? Kifadamin su waye iyayensa inje inji Dame suke taqama da dansu zaizo wajanki batareda ubanki yasani ba?"

Cikin kuka tace "Hajja ni bansan iyayensa ba, Kuma nide Allah Shahaab nakeso"

Hajja tace "to inajin de aljani ne, Danni banta6a jin irin wannan sunan ba, saide a jinsin aljannu, ninasan ba zakiyi haka da niyya ba mesunan qawa, Gamo kikai da aljan"

Abba yace "babu wani aljani Hajja, Sai iskanci dayake damunta, Kuma ni bazata 6atamin suna ba, bazata janyomin abun kunya agida ba...."

Jin furucin Abba yasa Hajja tasake rushewa da Kuka tace"mummunan bakinka ba'a kan mesunan qawa ba, inda zatayi ciki da tuni tayi, jinake can unguwar gabar Yara suna Nan sunkai su talatin kowacce cikin shege ne da'ita, ita kanta Malamar asbitin dasuke zuwa wajanta take zubar musu cikin itama cikin shegen ne da'ita, Bayan Wanda ta haife, Amma ninasan Mesunan qawa inde tabiyo halin takwararta to ba zatayi cikin shege ba"

Ummah ta kalli Hajja da sauri, yaushe akayi ciki agarin har mutum talatin? (=��>��)
Tagama lura cewa soyaiyar Aisha tasa kwata kwata Hajja bata ganin laifin yarinyar,ko kadan bazata iya tsawatar mata ba,Abba yace "tunda kince kina sonsa, tona tabbatar kona miki katangar qarfe tsakanin keda shi watarana bazan San lokacin dazaki tsallake kije wajan sa ba, danhaka ki shirya, zanje in samu jummai infada mata ta shirya takaiki can kano, daga Nan kuwuce Abuja akai ki gidan Mahmud Wakili aiki, tunda da naji tausayin ki nace ba zakije ba Gara ki zauna agaban mu abaki inusa, to yanzu Gara kije, dade ki zauna agari kina satar fita kina shiga motar saurayi bansan meyake miki ba, Gara kije can kikama aiki"

Yana fadin haka yafice daga gidan, Bai Zame ko'inaba Sai gidan Jummai qawar Hajja.

Aisha kuwa kuka tasa harda burburwa a jikin Hajja, "Hajja ki masa magana, Allah ni bazanje ko'inaba,Ina ruwana da wani Mahmud Wakili da zanje gidansa aiki, Kuma arasa gidan Wanda zanje aiki Sai wani Mahmud Wakili?, aini ba baiwar sa bace...."

Hajja ta share Hawayen idonta ta kama hannunta zasu shige daki, Aisha ta qwace hannunta taci gaba da kuka, Ummah tatashi ta wuce daki, domin kuwa ita hukuncin da mamuda ya yanke yayi mata daidai,babu Wanda zai nuna mata son Aisha kaf duniyar, Amma hakan ba zaisa taqi Bawa mijinta goyon baya akan tarbiyar yarinyar ba.

Jabir ne ya matso wajan ta yad'ora hannunsa akan dogon gashinta daya barbaje saboda kukan datasha, kannata yake shafawa tareda bubbuga bayanta alamun tayi hakuri, Shima kukan yake bashida bakin dazai iya lallashin yayar tasa, tana jinsa tafada jikinsa sukaci gaba da kukan gaba daya.

Awannna rana wuni sukai gidan babu dadi, Aisha banda Jan zuciya babu abinda take, abinci ma taqi Ci, Sai sharar hawaye take, Hajja tabata haquri harta gaji, ta qanqame wayar Hajja tana ta gwada Kiran Shahaab Amma abun baqin ciki waya taqi shiga, har dare Aisha tana daki taqi futowa waje, tana jiyo Abba yana shaida musu gobe jummai zatazo ta dauketa su tafi, jin babu Wanda yayi masa magana akan hukuncin nasa yasa wani sabon hawaye ya silalo daga idonta, baqin ciki yataru yazame mata goma da Ashirin, har gara ace wani gidan zataje aiki akan de taje gidan Mahmud Wakili,mutumin da kullum burinsa shine kamawa talakawa kayansu da kudaden su shine abinda ya'iya? Banda gidan man malam Audu daya saki bata ta6ajin inda akace yasaki gidan man wani ba, wayar Hajja tasake d'auka tafara Kiran layin Shahaab, saida ta kirashi yakai Sau goma,saide amsar guda daya ce, shine wayarsa akashe take.


Haka kowa yayi bacci Amma idon Aisha biyu, mutumin da taqi jininsa, Wai itace zataje gidansa aiki, Shahaab ne kawai zai fiddata daga wannan qulli, shikuma baya Nan, shin yasan Biron Dama haka kudinsa yake? Shine yasiyo mata da Kansa? Ko wanine yabashi? Shida yake Yaron Mahmud Wakili yaushe har zai samu wannan uban kudin? Anya ma kuwa yasan wanne irin Biro yabata? Haka ta dinga tunani tana yiwa kanta tambaya Wanda babu me amsa mata su Sai Shahaab, shikuma yamata Nisa.

Tana cikin wannan hali batasan yaushe bacci ya dauketa ba, washe gari haka ta zauna adaki taqi futowa, abinci ma qinci tayi, tun hajja tana lallashinta harta gaji taqyaleta, wajan qarfe goma Sha daya Abba yashigo tareda jummai, yana zuwa yacewa Ummah "kira mata Wannan yarinyar zasu tafi yanzu"

Cikin sauri Hajja tace"innalillahi wa inna ilaihirraji'un.... Yanzu mamuda da gaske kake ashe,? Yanzu rabani zakayi da me sunan qawa,?to babu inda yarinyar Nan zataje "

Cikin nutsuwa yace" Hajja, tafiyar ta shine yafi alkhairi, zamanta anan bansan wacce irin magana zata Dauko min ba"
yana fadar haka yashige Dakin Hajja yakamo hannun Aisha suka futo, kuka take tana Kiran Hajja, Hajja ta kama hannunta ta riqe itama tana kuka, daqyar Abba ya fizgeta suka fita waje, wata yar qaramar mota ce a kofar gidan, cikin motar yasaka ta, sannan jummai tashiga, shikuma yarufe musu motar, yasunkuyo da Kansa ta window yace "idan kunje kano, Akira hajiyar a tambayeta aji koda tasamu yar aikin to asake tura mata Aishan ko bude get ne ta dinga yi musu, zamanta acan din Hankali na zaifi kwanciya, nasan babu ita babu haduwa da wannan Yaron dayake hure mata kunne"

Aisha tana jinsa saide ko d'ago kanta batayi ta kalleshi ba, kanta na cikin qafafunta tana kuka.

Jummai tace "karka damu mamuda, nasan ma za'a dace insha Allah, bazan dawo gida Bama Sai an tabbatar min sunje Abujan lafiya, kayi mata addu'ah"

Cikin sanyin jiki yayi murmushin qarfin Hali, tareda barin jikin motar yana juyawa gida, shi Kansa bazai so yarsa mace qwaya daya jal tayi nesa dashi ba, Sai dole, yana tare da'ita gida daya bai ta6a sanin akwai Wanda yake zuwa yana Kiran yarsa ba, zancen ma yawuce kofar gida agaban jama'ah saide a mota, Allah ne kadai yasan abinda zai faru inba Allah ne yakiyaye ba, juyawa yayi ya kalli motar yayinda suka fara tafiya, cikin ransa yana Binta da kyakkyawar addu'ah, Idonsa nakan motar har suka yi Nisa yadena hangosu.








Da alama Jummai ta shirya yin futo na futo tsakanin ta da Hajja=��=��

to, takwara tatafi wajan takwararta=�D�, rashin kunya tatafi wajan masifa da iko>�y�>�y�

Wannan shi ake kira, angudu ba'a tsiraba =؁�<���
@&�mahaifi yatura 'yarsa inda yake gudu =��

Menene zai kasance Idan Shahaab ya dawo yaga Aisha acikin gidansa?>��

Yaya makomar qaryaiyakin daya dinga shuka mata?>��





(SHAHAAB littafin kudi ne, idan kika karanta min batareda kin biya ba, nabarki keda mahaliccinki,nera 300 Ne kacal bansaka kudi me yawa ba


0164549488
Amina muhammad
GTbank

My number
08033300034

Mutara zuwa gobe =�O�<���

Amnah El Yaqoub
'<���
Salam Alaikum,masu fitar min da littafi nagode, masu karanta wa batareda sisinsu ba nabarku kuda ALLAH,nide ban yafe muku ba, bazan yafe ba Kuma har abada, nabarku da futowar rana da faduwarta.

Masu cewa indinga yin posting biyu a rana kuyi haquri gaskiya bazan iyaba, Alokacin danace zan dinga yin posting biyu a rana, nayi tunanin yin VIP group 500, shine nace zan dinga yin posting biyu, to yanzu 300 dinma wasu suna cewa ta musu tsada,shiyasa nafasa yin VIP din, maganar posting biyu ta rushe, duk page guda daya, Ina bata awa hudu ne akansa, awa uku typing, awa daya editing, tayaya zan dinga bata awa takwas a rana inyi page guda biyu? Ayyukan gidan Ina zan kaisu? Masu min magana ta private inyi Yaya dasu? Masu kirana inyi Yaya dasu? Gaskiya kuyi haquri, kullum zamu dinga posting daya, idan Allah yasa nasamu lokaci zakuga posting biyu, idan bansamu ba zakuga daya, duk lokacin dakuka ga guda daya please =�O�<���kuce Allah yayi masa Albarka Faqad=�L�<���.


Page 22


Ganin tafiya de tazama dole yasa tabawa kanta haquri tayi shiru har Allah yakaisu kano lafiya, Bayan sun huta sun d'anci abinci Hajiya Amina tace "baba jummai ai nayi zaton kunfasa kawo yarinyar ma, itama Kuma Hajiyan bata sake kirana akan maganar ba, Amma gaskiya Ina tunanin tariga tasamu ma, Bari de inkirata inji Yaya ake ciki"

Addu'ah Aisha take a ranta Allah yasa tariga tasamu din, ba komai ne yasa take kukan barin gida ba Sai rabuwa da Hajja dakuma tunanin yanda Shahaab zai dawo yaji labarin bata Garin.

Jin Hajiya Amina tana magana awaya yasa tamaida Hankalinta kanta, Bayan sun gaisa cikin ladabi Hajiya Amina tace "Hajiya Mama Dama akan maganar me kula dakene, nace gashi ansamu wata yarinya idan har yanzu baki samu ba"

Daga can 6angaren mama tayi magana, Sai Hajiya Amina tace "a a wallahi yarinya ce qarama baki ganta ba, Kuma babu qazanta a tareda ita, ke kanki Sai hankalin yarinyar ya birgeki, babu wani datti tsaf take, babu Wanda zaice yar aiki ce"

Mama ce tasake magana, Sai Hajiya Amina tasake cewa "to.... To shikkenan, saisun zo d'in, babu komai wallahi Nima nagode"

Aisha tanajin haka ta Lumshe idon ta, shikkenan tafaru ta qare.

Kallan su tayi tace "to Alhamdulillah tace ba'a samu ba, Aisha saiki huta yau, gobe zansa driver daga Nan yatafi dake, zai Kaiki har can insha Allah"

Jummai tace"to yanzu Amina Yaya batun kudin aikin ta?saboda idan nakoma inshaida wa mahaifinta yanda mukai dake "

Murmushi tayi tace"idan taje gidan Hajiya Mama zata fad'a mata yanda zata dinga biyanta, Nima tace zata turomin wani abu ta account dina, Baba jummai Aida kinsan gidan da Aisha zata tafi da bakiyi min maganar kudin aikinta ba, saboda duk Wanda suke aiki a gidan suna samun alkhairi sosai, bare Kuma Nata aikin special ne, bawani aikin wahala zata dinga yiba,"
Tajuya ta kalli Aisha sannan tace"Aisha idan kikaje babu ruwanki da harkar kowa kinji ko? Mahmud yanason mamansa, zai iya yin komai saboda wannan tsohuwar matar, bayason abinda zai 6ata ranta, Kuma zai iya 6atawa da kowa saboda ita"

Iya jummai tace "yawwa to ai Gara kifada mata tun yanzu kinga idan taje gidan shikkenan tahuta da bincike akan halaiyar 'Yan gidan, menene ma zai had'ata da wannan matar bare har ta 6ata mata rai?"

Hajiya Amina tace "inde ta kiyaye tsakaninta da mama to ai batada wata matsalar komai, saboda a yanda naji shine, Mahmud din yana son matarsa sosai, amma duk soyaiyar dayake mata inde ta 6atawa mama rai to sa6ani take samu dashi"

Tunda suka fara magana Aisha bata saka musu baki ba Sai yanzu, ahankali tace "yanada mata?"

Murmushi Hajiya Amina tayi tace "haba Aisha, Babban mutum kamar Mahmud Wakili ai dole ya ajiye iyali, Amma ke ai ba 6angaren matarsa zakije ba, kefa kina wajan Hajiya mama, duk ayyukan da zakiyi to abinda ya shafi mama ne"

"wanne irin aiki ne?" tasake tambaya

Hajiya Amina tace "Zaki dinga kula da'ita, zaki dinga riqe hannunta kudinga Dan tattaki a gidan saboda ciwon qafafunta, zaki dinga matsa mata qafafunta, idan angama abinci Zaki zubo mata ki kawo mata, zaki dinga yimata hira saboda karki Barta cikin tunani"

Aisha ta Jinjina kanta tayi shiru, irin wannan hidima haka saikace basarakiya?(>��)
Iya jummai tace"saboda Allah yanzu wannan har aiki ne?ai wannan bazaka kirashi aiki ba tunda kince matar ta manyanta wannan aikin ai idan ka taimaka mata kaima zaka samu Lada,tobakada aikin fari bare na baqi kawai zama fa zakayi tareda ita,"
Tajuya ta kalli Aisha tace"me sunan Hajja,kisa aranki saboda Allah Zaki mata komai, sannan ki kalleta kamar Hajjanki, insha Allah sakamakon ki yana wajan ubangiji"
Haka suka dinga zancen gidan har dare, kasancewar akwai kayan kallo a gidan Sai Aisha tad'an saki ranta tana kallo,lokaci zuwa lokaci Hajja da Ummah suna Fado mata Arai.

******

Hajja ta kalli Ummah da Abba tace"yanzu mamuda abinda ka aikata kayi daidai kenan? Yarka guda daya jal 'ya mace ka dauketa ka rabamu da'ita? Mamuda kodan yanda na shaqu da mesunan qawa ashe bazaka Gani ba?bansan cewa bakada mutunci ba Sai yau, Ina kuka yarinyar Nan tana kuka haka ka rabani da'ita, ai shikkenan babu komai, yau ka nunamin kafini iko akan AISHA"
Tana qarasa fadar haka ta Fashe da Kuka, cikin sauri Ummah ta kalleta jin sunan AISHA data fada Kai tsaye, abinda bazaka ta6aji Hajja tafada ba, ahankali tace"Hajja kiyi hakuri, abinda yasa bansaka baki ba akan maganar yarinyar Nan, Hajja ke kanki sheda ce munbawa Aisha tarbiya, kema kin bata, Aisha tana da Hankali, Barta de da rashin kunya wani lokacin, Amma abun mamaki da tsoro shine yanda ta'iya kallon idon mahaifin ta tace ita Shahaab take so, yana Dukan ta Amma yarinyar Nan haka take sake fada ita Shahaab take so, Sai abun Nata yabani tsoro, lokacin da akazo da maganar inusa ko musu batayi da mu ba, Amma zuwan wannan yaro Shahaab cikin rayuwar ta gaba daya ya sauya mana tunanin Aisha, yanzu dasuke shiga mota suna zance bamu San yaushe take zuwa wajan sa ba, inda ciki nema haka zaiyi amfani da qananun shekarun ta yayi mata, Amma Kuma saida tatafi nake jin kamar mun aikata kuskare, Ina tsoron kar Yaron Nan Shahaab yabita can Abujan suci gaba da abinda suke" tana fadar haka tafara share hawaye

Hajja datake kuka tace"kul Hadiza, banaso na qara ji kince mesunan qawa zata aikata wannan mummunan aikin, inde halin takwararta ta'iyo babu abinda zata aikata, kuskure de ubanta gashinan yariga yayi, duk abinda yabiyo baya, saiya kuka da Kansa"
Tana fadar haka, ta share Hawayen idonta tatashi tashige dakinta tanajin kamar zataga Aisha tana game a wayarta.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke yana sake gaskata wa zuciyar sa cewa dade ace yabar Aisha anan, Gara tatafi Abujan yafi masa kwanciyar Hankali, ko banza idan Yaron yazo yagaji da zuwa zai haqura yabar masa yarsa

******

Washe gari karfe Goma nasafe suka tafi, jummai bata tafi ba saida taga tashin su Aisha sannan itama tafara haramar tafiya gida.

Sai Bayan la'asar suka Isa Abuja, Aisha tun tana bacci tana farkawa harta daina,bata ta6a tafiya me Nisa irin wannan ba, Sai abun yazame mata Sabo, tunda suka shigo cikin Garin kuwa tabaza ido tana kallo, sunyi tafiya me Nisa sosai acikin Garin sannan suka qaraso wani tanfatsetsen gida, baki bude take ganin tsaruwar gidan, yanayin unguwar babu hayaniya, Babban titin daya kawoka har bakin get din gidan ta kalla babu wasu mutane dasuke zama awaje kamar yanda akeyi a garinsu, Lema ce a kwance akoi'na alamun ruwa aka gama yimusu, Sai yanayin Garin yasake yin kyau, bata gama mamaki ba taga sojoji sun bude musu get din gidan, saida direban ya basu wani I'd card suka Gani sannan suka barsu suka shiga, batasan dalili ba haka Nan ta tsinci kanta da faduwar gaba har Sai tafara karanta "hasbunallahu wani'imal wakeel" acikin ranta.


Motar su tana tsayawa aharabar gidan taga sojoji ta ko'ina suna shawagi, Sai yanzu tasake ganin kyan gidan, tashin Hankali ne ya wanzu akan fuskar ta, yanzu wannan gidan mutane ne suke rayuwa aciki gida kamar aljannar duniya?
Sai yanzu ne tasake tabbatar wa Mahmud Wakili ba qaramin mutum bane, duk yanda ake bata labarinsa ashe yawuce haka, wannan shi ake kira jinka yafi ganinka.

Direban ne yafuto yabude mata motar yace "futo muje" yanda yabata girma harda su bude mata mota yasa Shahaab yafado mata Arai, duk yanda yake da kyau dakuma shekaru bude mata mota yake kamar itace shugabar sa, kawar da tunanin tayi daga cikin ranta suka qarasa cikin part din Hajiya Mama.


Tsaruwar falon Nata ne yasa Aisha tasake daga kanta ta kalli falon sosai, batace komai ba face Jinjina kanta datayi, wata mata ce zaune acikin daya daga cikin kujerun falon ta dora kafarta daya Kan daya,banana ce a hannunta tana karya kamar bata son ci, hankalin ta nakan abinda ake yi a TV.

duk da daga nesa ta hangeta saita ga batafi Hajja shekaru da tsufa ba, daya daga cikin masu aikinta dake tsaye abakin kofar itace tace dasu "sannunku da zuwa, ku qaraso"

Direban ne ya amsa da "yawwa" sannan tayi musu jagora zuwa wajan mama, qasa ta tsugunna tayi wa mama magana sannan ta juya zuwa kitchen

Cikin farinciki mama ta juyo ta Kalle su tace "sannunku da zuwa,mutanan kano ne?"

Aisha batayi magana ba Sai kallon matar take, haka kawai taji matar ta kwanta a ranta,kwata kwata a shekaru batafi Hajja ba, saide kana ganin ta kaga hutu da jin dadi daram ajikinta, tayi tunanin zata yi musu kallon wulaqanci a yanda ake bada labarin izzarta.

Zama sukai har suna hada baki wajan gaida ta, cikin murmushi tace"sannunku da zuwa," ta maida kallonta ga Aisha tace"yar kyakykyawa kece Mai aikin?"

Cikin sauri Aisha ta kalleta sannan tayi qasa da kanta, cikin ladabi tace "eh nice MAMA"

Jin yanda ta kirata da mama Sai hakan yayi mata dad'i, duk yanda akai yarinyar tanada nutsuwa, cikin jin dadi tace "masha Allah, kema daga kano kike?"

Kanta aqasa tace "A a Jigawa"

Gaban mama ne yafadi,jin sunan Garin yasa ta tuna da qawarta Aysha Sulaiman Bompai, Sai taji a ranta koda batada ra'ayin yarinyar to dole zata sake riqeta saboda tafuto daga jihar da qawarta tayi aure, dalilin Garin dole zata dauketa, cikin murmushi tace "menene sunanki?"

"AISHA" tafadi hakan kanta tsaye.
Mama tace "masha Allah,kice tsohuwa ce"

Murmushi su Aisha sukayi, Adede lokacin Mai aikin takawo musu abun motsa baki, mama tace "kikai masa Dakin baki saiki dawo kitafi da Aisha"

Cikin ladabi tace "to mama"

Tashi Direban yayi yabi Bayan me aikin, Bayan sun tafi mama tasake kallon Aisha tace "Aisha kisaki jikinki kinji? Maganar gaskiya Ada maiyi min hidima nace akawo min, to Amma kasancewar kinfuto daga jihar datake da dumbun tarihi awajena, saina ji bazan iya sakaki aiki ba, idan babu damuwa zan dauke ki kamar jikata, Nan gidanku ne, kidaukeni kamar mahaifiyar ki, ni banida matsala inde anyi min abinda nakeso, abu daya nakeso kikula dashi shine banaso idan Dana yazo inda nake Inga wani mahaluqi awajena, inde Mahmud yana tare Dani inaso inganni nida shi mu biyu"

Cikin ladabi Aisha tace"insha Allah zan kiyaye mama"

Mama tace"kinada account ne Wanda za'a dinga tura miki kudin aikinki aciki?"

Cikin mamaki tace "kibarshi mama, ba saboda kudi Abbana yaturo ni aiki ba saidon laifi Dana aikata masa Kuma yake hukuntani ta wannan Fannin, koba Dan haka Bama Ina ganinkine kamar Hajja ta, saboda haka zan yi miki komai tsakani na da Allah Kuma saboda Allah"

Cikin mamaki mama ta kalleta, awannna zamanin har za'a samu yarinya wadda abun duniya bai rufe mata ido ba kamar wannan yarinyar? Jitayi yarinyar tasake birgeta, tun farko irinta taso Allah yabawa Mahmud dinta,Amma Allah baiyi ba.

murmushi tayi tace"Aisha ai ba'awa iyaye laifi, biyaiya ake musu sosai, yanda Mahmud yake kyautata min yakemin biyaiya inda yaji cewa kinyi wa iyayenki laifi har suke hukuntaki toda saiya zaneki"(=��)

Murmushi Aisha tayi tafara wasa da yatsun hannunta, (nikam nace me zanewa ai shine maqasudin me laifi mama =��)

Adede lokacin yar aikin tadawo, mama ta kalli Aisha tace"za'a bude miki account Sai Adinga saka miki kudinki aciki, wannan haqqin ki ne, bazan tauye miki haqqi ba, tashi kuje zata nuna miki d'akin ki, kiyi wanka kici abinci kihuta, zuwa gobe"
Tajuya ta kalli Mai aikinta tace"Mansura baquwa ta ce wannan, takawo min ziyara ne daga jigawa, a kaita daki na musamman"
Cikin ladabi mansura ta amsawa mama, itama Aisha tayi wa mama godia tana tunani fal ranta, wacce irin mata ce wannan? Ita datazo aiki meyasa ta 6oyewa yar aikinta tace ita din ziyara ta kawo mata? To menene na jihar Jigawan tayi mata dahar take ganin qimarta saboda kawai tace daga jigawa take? Haka ta dinga yiwa kanta tambaya har suka bar wajan maman.

Acikin falon maman Dakin yake daga can Gefe, tsaruwar Dakin ne yasa Aisha ta shagala da kallon komai, daki saikace baza'a mutu ba, akwai komai na more rayuwa aciki, nuna mata komai tayi, sannan ta juya ta fita domin kawo mata abinci, tana fita Aisha ta zauna jagwab akan gadon Dakin, cikin zuciyar ta tace"duk wannan daular gidan saboda wannan tsohuwar? Aikuwa yanda na'iya zama da Hajja Toda kowama zan zauna"


Har dare tana daki bata sake gigin futowa falon ba, tunda taji mama tayi mata kashedi akan idan danta yana Nan tana buqatar kebewa,

3 Comments On SHAHAAB
avatar
fateema

1 year ago

Reply

Allah yakara basira

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to fateema

Ameen

avatar
ummu-swabir

10 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment