Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu matsala komai yazo k'arshe Allah yaimana maganin dukkan abinda bamu iyawa ya iyamana kar ya barmu da iyawarmu,Yaya maganar kai lefen yau?

Suntafi tun safe ai yanzu saidai maganar dawowa.

To Allah ya shigemana gaba,Mu yanzu wane shiri yakamata muyi ko mu fara?

"Ai inaga babu wani shiri wurin zama ne to kuma anriga an gyarashi, komai akwai saidai sabbin d'inkuna da zakaimin,Ya idasa maganar yana dariya.

Bugu ya kaimishi shima yana dariya" Lallaima bakaji da kyauba dan babu dinkin da zanyimaka tunda bawai d'aurin aure zamuba camma naji mama tace sunfasa taron kaga ko ai iyakarmu d'auko amarya kaikuma kana nan gida zaune.

"Hakane kam Amma yakamata kaimin ko kala biyar ne yanda zanyi angwancin da hujja,Wai ya maganar madam ne akwai sauran lokaci ko?


" wallahi kuwa dama ciwon bayane ke damunta to kuma sunce wai ba haihuwa bace duka satin cikin 34 kaga da saura.

"Eh amma hadda laifinka gaskiya Salim yakamata kadan dinga d'agamata k'afa kafa kusan kila damunta da kakeyi shine kesata ciwon bayan kadan bata lokaci kaga,Idan zaka wuce zan rubutamaka magani saika wucemata dashi Allah ya rabasu lafiya.


""**""

"Miskin ki ya k'are ko Akwai saura?

Abulkhairi nakema wasa kamin ince kai ya maryam nacemiki inada saura tun jiya da mukai waya ko?


" Keni dallah ajiyeshi ki kalloni nan yanda zaki fahimceni bansan shirme.

Ajiye shi nai ina turo baki.

"Wannan abin naki yanaban mamaki wallahi wani lokacin sai kidinga Abu kamar me junnu anshinan cikin ruwan wankanki zaki dinga digawa kamar ranar tafiyar taku insha Allah ankawo wa inda zaki wuce dasu dan Allah karki dinga wasa da k'amshi aysha dan Allah.

" To ya maryam insha Allah zan kiyaye ki kuma bani lemon saina wuce gida dashi naga yamma tayi yanzu zakiga yafara kiran waya wai in koma gida.

"Babu komai ai yamayi kokari tunda jiya ma yabarki kinfita ko? Kince kinje gidan malam tsoho,Kinyima Dr. Din maganar karatunki kuwa?

Nayimishi yaya kuma alhamdulillah ya amince dama nasan da wuya idan zansha wahalar shi tunda yasan dadin aikin shima,Balle su manya manya.


" Tashi ki wuce kadda maraice ta rufa gaba daya dan Allah ki dage da addua insha Allah zaki rayu cikin gidan mijinki har ma ki hayayyafa da izinin Allah,So nawa kikai wankan lallen?

So uku kawai nayi yaya Amma anjima idan zan kwanta zankuma shawafa Ammafa daga yau nagama danni wannan santsin da jikina keyi wallahi bansan shi.



Sai bayan magrib na isa gida me napep na ajiye ni kiran wayarshi na shigowa Saida na sallami mutumin ya wuce Sannan na d'aga kiran.


Sam bejira na gaidashiba yafara balbala fada.

"Saida nagayamiki kadda kikai magriba wai meyasa kika rainanine iye? Kodan kinga ina sakemiki ne? To wallahi kadda ki yadda kisan true colour dina dan rankine zai baci kinajina ai?

" Cikin kololuwar bacin rai nafara magana nima dan yaga kaini bango saikace irin haihuwata yai dinnan"Kaga dakata mijin ya fati ban shigo ba balle ikon ka yafara aiki kaina nasan abinda nakeyi dan kaga an auramin kai na hakura shine zaka fara fiddo da kalar halinku Ku maza wa inda suka sami wuri? To wallahi a a bazan d'aukaba inace wannan alfarmar Abba yanema wajanka kwanaki? To domme zaka nemi takurani yanzu nasan fa abinda nakeyi,Kai auranma nafasa banyi ko dole ne?

Yanke wayar nai tare da saka kuka dan tuni nashigo cikin gida.
Ni kaina nasan inada zuciya sosai idan ka taboni.

Ruwan da mama ke mikomin na amsa inasha ina kuka kuma me sauti dan tariga tazomin wuya,Wallahi mama ban sonshi ni Allah Abba ya dawo nafasa aurenshi yacika masifa da bala'i bazan iya zama dashiba.





Haske writers association.
12/10/20, 2:28 PM - Naffy Aliyu Umar: 26




Ganin yanda na birkice lokaci guda yasa hankalinta tashi,Innalillahi take nanatawa fili da boye kamin ta riko hannuwana"Nacefa kiyi hakuri zansa abbanku yaimai fada rufe bakin dallah saikace k'aramar yarinya wallahi inda zaki dinga mishi kuka to kuwa zaigama rainaki...Kiran wayata ya katse maganar da takeyi duk muka zubama wayar ido har ta katse wani kiran yakuma shigowa.

Wurgi nai da wayar tare da shigewa d'aki kuma har lokacin hawaye nakeyi.


Shigowar Abba gidan yasa mama tsayawa daga niyyar shigewa d'aki da takeyi tafaramai sannu da zuwa.

"Ah waye ke kuka kuma ina yaran gidan?

" Hummm yaya har yanzu ina cikin zullumin aurannan wallahi sunki daidaita kansu kullun sai fada tsakaninsu anya bamuyi wautaba kuwa?

"Meya faru kuma?

" Nima ban saniba Ammadai inaga sabani suka samu dan gashican tana ihun tafasa auranshi kozai mutu bazata zauna dashiba tamaki yimin bayani saidai ko zaka shiga kasanta da bak'ar zuciya.


Ina niyyar kabbara sallar magriba Abba yashigo d'akin,Aysha meya faru ne haka keda mijin naki?

"Wasu hawayene suka subomin,Abba dan Allah kai hakuri ka rabani da mutuminnan wallahi ya cika kalar laifi da fada nagaji bazan iya zama dashiba.

" Subhanillahi yi hakuri gama sallar ki sameni falo ina jiranki.



"""


Dafe kanshi yai tare da wargar da wayar bayan yagama kiran yaji anki d'auka wani irin haushin kanshi yaji yakamashi,Waima yaushe yafara wannan bak'kin kishin Wanda betaba sanin yanada shiba, Toma meyajamishi bata ran wannan d'angwalolon yarinyar,Kai Innalillahi kaddafa tace tafasa aurena Dana mutu wallahi oh God!!

Shigowar salim cikin office din yasashi sauke ajiyar zuciya,.Yana kallon fuskar salim din.

"Dr.ya garin nayi tunanin ka wuce gida ai nace baridai in k'araso injaka muje ka dubamin madam gaskiya wannan karon cikin na wahalar da ita ni kaina na k'agara inga ta haihu.

Wani zazzafan huci ya fitar kamin yace Zauna salim na ballo ruwa wallahi,Yanzu nagama waya da aysha tace tafasa aurena dole in rabu da ita.

A tsorace ya fiddo idanunshi kamin yace " Ah ban ganeba garin yaya?

"Fada naimata salim bansan me zafi naimataba tagayamin duk maganar dataga dama yanzu kuma na kirata tak'I d'aukar wayar.

" Kai Innalillahi wai yaushe ka canza Ahmad? Yaushe duk wani kwarin guiwarka ya gudu? Meyasa zaka takurata wannan fa auren dolene akai mata kaima kasani Amma tai hakuri tai biyayya kuma shine zaka tasata da fadace fadacenka? Kana tunanin idan mahaifinta yace ka saketa zaka kuma samun watane nan kusa? Wama zaiyi shahadar kuma baka aure? Meyasa zaka dameta ka takurata kaida zaka dage wajan lallashinta har Ku fahimci juna why saika takurata?


"Bansaniba salim bansan meyasa nake takurataba ,Saidai nasan akwai zazzafan kishinta dake barazanar halakani wallahi, Nagayamaka inasonta ko wani motsi nai tana makale cikin zuciya ta duk lokacinda ta tambayeni fita wani waje bankuma samun nautsuwa saita koma gashi ta cika yawo kuma,Dan Allah ka temakamin wallahi ta daina d'aukar wayata.


Salati yakeyi cikin zuciyarshi yayinda ya zubama Dr. Din ido yana hango tsantsar damuwa da tashin hankali ciki gakuma soyayya Wanda taimishi mugun kamu,Lallai akwai gagarumar matsala wannan karon indai ya rasa matarshi,Kila cikin biyun dole daya yafaru ko mutuwar dayace kokuma haukan Wanda duk ba a fatanshi.

" To ni yanzu bansan yanda zamuyiba inaga saidai idan Abban zamu kira ko?

"Kunya nakeji Salim banso yafara ganin laifina tunkamin tatare gidana kadda yafara tunanin bazan iya rikemai yarinya ba.

" Dallah kiranshi zakai tunda ka Riga ka aikata ai dole mu nemi mafita ni Wallahi damanasani da ban biyoba banza kawai ka koma saikace wani yaro An gayamaka so haukane da duk zakabi ka rude kuma ka ruda yarinyar mutane?


Harararshi yayi tare da jawo wayar daga inda ya wurgata.


Adai dai lokacin Abba ketamin fad'a akan maganar da nai ta cewa bazan zauna dashiba ina zaune gabanshi inata share hawaye shikuma yana fada gami da nasiha har nai shiru,Saiga kiran wayar dr.din yashigo.

Akunyace da girmamawa kamar yana gabanshi ya gaidashi kamin yai shiru har saida salim ya d'an zungureshi kadan.
"Uhum Abba dama d'azu mund'an sami sabani da aysha ne tokuma yanzu inata kira amma bata d'agawa shine nace ko zaka d'an yimata magana.

" Ash sha Allah ya kyauta to Amma kaima yakamata ka dinga kulawa Ahmad kaga gatanan zaune tana kukan tafasa aurenka Kaine babba yakamata ka daina biyemata bazance me ya had'akuba Amma dai zance idan kun shirya to cikin satinnan zan kawota nida mamanta dannaga inba hakaba kamin ma atare zaku iya lalata auran.

"Alhamdulillah Abba nagode sosai Allah ya jikan mahaifa Allah ya sakamaka da mafifin Alkhairi nagode Allah ya gafartamaka dukkan zububanka nagode Abba wallahi a shirye muke tun tuni.

Kuka nasaka jin abinda Abban yace,Yayinda ya ajiye wayar yana dariyar Dr.din dan sosai yaji yanda ya rude,Batun yanzuba yasan cewa soyayyar ayshan ta kamashi sosai batare da shi kanshi yasan da hakanba.


" Tashi ki wuce d'aki bansan shirmen banza.




*
Kyakkyawan rungumar dayaba salim din yasashi kallonshi dan da sauraranshi kawai yake.

"Gatacan tana kuka mutumina Abba yace cikin satinnan zai kawota da kanshi wayyo dadi Allah nagode maka.

Ganin irin kallon da salim din kemishi yasashi gintse fuska yana tabe baki,Shi kanshi yanajinshi wani irin cikin kwanakinnan duk yagama gigicewa gakuma zullumi ta bangare guda shin aysha zata rayu dashi tsawon lokaci kukuwadai itama tafiya zatayi ta barshi.

" Wallahi inka bari yarinyar nan tasan kanamata wannan mugun son Allah sunanka sorry zata yankwanaka ne zata dinga yin wuju wuju da kai mutumina,Lallai wannan amarya ta musammance dan ban taba ganin ka nuna haka akan wata diya mace ba.


"Karka damu da wahalar da zata bani danni ma wallahi wuyar zan bata idan mungaji saimu hakura,Ni kaina ina mamakin wannan abun da ita nake kwana cikin raina da tashi salim ko yaya na motsa saita fadomin wani irin shaukin soyayyarta ke d'awainiya dani ,Anjima kadan zan kirata in lallashi abuta kadda tazo bamu daidaitaba tabarni da kallonta,Inko mun shirya nasan ko zafi zan rage kovan kaiga aikata ogan ba.

Dariya sukai tare da tafawa kamin su wuce gidan salim din inda zai duba matarshi khadija.



***

Bayan Sallar isha'i.
Kwance nake nai lamo inata tufka da warwara tsabar tunanin dayasha kaina ga wani shegen ciwan kai dake damuna.
Ganin komai nakeyi kamar almara wai anyimin auren kuma da mijin yayata wannan mutumin me shegen girman kan tsiya da miskilanci,Nasan be sona kamar yadda nima bemin ba Amma kuma ina tsoron kalar zaman da zamuyi saukinta d'aya naji mama tace gidansu zamu zauna,Nasan mamanshi bazata bari ya cutar daniba, To Amma kuma idan mamanshi ta kareni daga cutarwarshi tokuma abinda yake cutar da matanshi fa? Koda yake inada Allah na tabbata babu abinda zai dameni Sannan nai alkawarin yin doguwar d'amara domin cin uwar danginshi musamman wa inda suka kasa boye kiyayyarsu akanshi ko iyayenshi dan so kusan uku ya fati nagayamin sunje har gida sun zageta tas Amma koshi Dr. Din besan anyiba kuma har Allah ya karbi rayuwarta besan zancenba.

Sabida sunada 'yammata da yawa gakuma samari kowanne angama cusamai kiyayyar su Dr.din dan kawai Allah yayisu da arziki sama da nasu.

Wani dogon tsaki naja lokacinda wayata ta isheni da k'ara kamin in jawota ban bude idanuna ba balle inga waye danhaka akunne kawai nasata batare da nayi maganaba.

"Aysha kina jina?

" Uhum"Kawai nace tare da gyara kwanciyata dannasan duk kashe muryarnan da yakeyi bazai hanashi masifeniba idan tsiyar ta motsa.

"Uhum" Shine gaisuwar ko? Babu komai ya kk ya hakuri dani?

"Nifa wallahi barci nakeji kaina ke ciwo.


" Kefa matsalarki kenan aysha kincika wulakanci kindaisan dole inkira inji ya kike ko?

"Kadai kira kaimin fadan daka saba Amma bawai kaji ya nakeba,Dazu wane irin wulakancine bakaiminba ai baka tsaya Ka surareba,Sai yanzu zakace ya nake?


" To naji sarkin korafi kiyi hakuri,Kece kincika laifi aysha,Sam Fatima ba haka takeba,Alhalin kinfita tarin ilmi nasan kinsan abinda ya dace Amma bansamin nutsuwa idan kin fita kumafa bawai dan ina sonkiba a a kawai albarkacin igiyoyin aurena kikeci.


"To naji kuma nagode zan iya kwanciya?


" Meyasa kikeyin haka aysha ammadai kinsan ni mijinki ne ko?


"A a gyara batunka dr.mijin ya fati dai.


" Au haka kikace? To shikenan zaki shigo hannuna zan tabbatar miki da cewa ni mijinki ne bana marigayiyaba,Zakiyi bayani dalla dalla.


"Eh kace haka din idan Ka kamani Ka kasheni baki daya.


Ajiye wayar nai ina hararar umar daya kawomin kwadon zogale da romo Wanda mama takemin kullun Yanzu.
Ajewa yai tare da ficewa dan kadan daga aikina in huce kanshi yasani.



Murmushi yaita saki ganin na ajiye wayar kamin ya shafi jikinshi yana hango yanda zaici zali da wannan abun.Dan yai alkawari duk wannan bakin saiya mutu saiya dasamata tsoro da shakku kai hadda kunyama cikin zuciyarta.

Gyara kwanciyarshi kawai yayi sabida yanaso zuwa shabiyu nadare yakoma gidan salim yasan zuwa lokacin insha Allah ko bata haihuba to ta kusa.





"*"*"*


" Alhaji naga sai murmushi kakeyi lafiya kuwa?

"Alhamdulillahi komai lafiya dama akan maganar Ahmad ne d'azu surukinshi ke gayamin ran juma'a zasu kawo ayshan shida mamanta amma kuma sati nasama yayunta zasuzo suma suga d'aki,Wato nidai najima banga mutumin arziki irinshiba wlh ina ganinshi da daraja fiye da wa inda muka fito ciki d'aya dasu tunda gashi yaimin abinda babu Wanda zai iya ko kwatanta hakan.

" Hakane gaskiya ni kaina yanzu duk sallata akwaisu cikin adduata domin babu abinda zamu iya biyansu dashi bayan adduar.


"To madallah yanzu saiku fara shirin karbarsu kisa usman yaje can cikin gida ya fadi ran juma'a za akawo amarya kadda kuma aki gayamusu abin yazama na tsegumi.





Ranar juma'a.




Haske writer's association.
12/10/20, 2:28 PM - Naffy Aliyu Umar: ___ _wannan_ _labari_ na _kudine_ idan kina _buk'atar_ shi _zaki_ biya d'ari uku _domin_ _kisamu_ .



27

Tunda naga angama kammalamin duk wani Abu na buk'ata nake aikin kuka tun mama na lallashina har itama takoma share hawayen,Ran alhamis yayuna duk nan suka yini ko wanne da kalar shawarar da yakeban zuwa dare gidan yai shiru dan duk kowa ya watse hadda makota da sauran dangi da ukazo.

"Haba aysha indai ba so kikeyi kigama tashin hankali naba yakamata kiyi hakuri hakanan kalli yau daya yanda kika koma haddani fa zamu raka ki,Kuma juma'a ta sama yayyenki zasuje can suyimiki yini menene abun damuwa ?


" Mama nifa bansonshi dan Allah kice afasa kokuma yadawo nan garin da zama shima.

"Naji tashi kije Abbanki na kira zansan abin yi Ammafa idan kin daina wannan kukan.



Idanunshi ya zubamin lokacinda nashiga cikin falon kasancewar akwai hasken nepa,Hannunshi ya nikomin nikuma na nufi jikinshi tare da sakin wani kukan gani nakeyi kamar nima daga natafi zan mutu in daina ganinsu shiyasa hankali yai mugun tashi,Ga shegen tsoron da zainab tabani akan auran kusanma wannan zulluminne ya hanani sukuni Saida tabani labari sannan na fahimci maganar da yaimin kwanaki na cewar lallai zangane kurena ahannunshi duk tunanina shegen bugu zaimin Ashe shi tunanin shi daban.

Ahankali yake shafar bayana yana bubbugani har saida yaji kukana ya tsaya Sannan ya gyaramin zama yanakuma sharemin fuskata da hijab dina Wanda duk nagama jikeshi tsabar kuka.

" Haba aysha kadda kisa infara danasanin aurar dake mana,Ina hangomiki nagartar Ahmad shiyasa naimiki wannan gatan sannan ina tunanin cewa zaki iya temakonshi kema dan Allah kibar kukannan insha Allah wataran saikinyi dariya sabida kowa ya shaida irin son da yakemiki yanzu kinga kenan bazaki sha wahalarshiba ko? Ki daina kuka Allah yaimiki albarka kinga shima can kin tashi hankalinshi yace kwana biyu baki d'aga wayarshiba hankalinshi yadaga sosai ko dazu wajan kira biyar yaimin duk yanaso yaji ya kike,Dan Allahki kwantar da hankalinki idan kina buk'atar ganina wayata kawai zaki kira haka mamanku da kaina zan dinga kaita Sannan yayunki suma zasu dinga waiwayarki bansan ganin wannan damuwar kinji?

Ahankali na d'agamishi kaina ina sauke ajiyar zuciya tsabar yanda naci kuka.

"Kinga anshi wannan takardar addua ce kala kala gatanan ingantattu idan kinje saiki duba nasan duk kin iyasu saidai tsarin yanda za ayisune kadda ki yadda kiyi wasa,Ki rike mijinki ki kyautatamishi idan kikai laifi mu kika ja mawa dan za ace tarbiyarmune danhaka ki rufamana asiri aysha wannan masifar da rikicin duk ki ajesu yanzu kin girma,Duk abinda ya faru Wanda be mikiba ki tsaya Ku fahimci juna bansan yawan korafi da kai k'ara ,Gaki ga iyayenshi ki kyautata musu kamar yadda kikemana suma iyayenkine acan baki da kamarsu dan Allah ki zauna da kowa lafiya kinji?


Kaina nakuma d'agamishi ina Jan majina.

" Tashi kije ki kwanta Allah yaimiki albarka.




**""**

"Wannan yarinyar matsalane da ita salim yanzu dan Allah ni yanzu laifin me naimata da zata daina d'aukar wayata banfa kuma yimata wani Abu ba,cikin damuwa ya idasa maganar.


" Dan Allah ka dinga ragema kanka damuwa Ahmad kasan kanada lalurafa,Kumama ai kasan dole taji babu dadi ko? Rabata da gida zakayi fa? Ka kyaleta babu wani Abu gobe iwar haka tana cikin gidannan insha Allah kaga shikenan duk ta wani Abu ya k'are ko? Tashi muje kaima yarinyar huduba dan Allah har yau kwana uku lokaci na kurewa baka rad'amata sunaba.

Bewani so ba Amma tsabar babu yanda zaiyi haka ya mike saiwani yamutsa fuska yakeyi saikace budurwa.


Koda suka tafin, Kuma lallashinya yakeyi har suka k'arasa,Matarshi zuhra ta tarbesu da farinciki kamin ta kawomishi babyn.

Saida ta zauna Sannan ta mik'a yarinyar taimishi godiya akan hidimar da yakesha dan ko jiya akwati uku haka ya dire na kayan baby sai nata Saikuma na yaranta biyu takwaranshi Ahmad sai kuma babban mesunan mahaifin salim din suna kiranshi da khalifa.

Harararta yayi kamin yace"Bar ganin kina jego sai insa oga ya zaneki Allah idan baki daina wannan godiyarba,Mik'amata yarinyar yayi yana murmushi "Gata munsamu baby aysha Allah ya rayamana ita.

Duk murmushi sukai kamin ta amshi yarinyar tafice shikuma Salim ya zunguri Ahmad din yana sakin dariya" Gaskiya ka zurma da yawa mutumina Allah yasa damuwarka tazo k'arshe.

Maida kanshi jikin kujerar yai tare da lumshe idanunshi,Fatanshi Allah ya daidaita tsakaninsu dan yana hango rikici,Musamman dayasan har yanzu kallon mijin yayarta takemishi,"Muje ka rakani gida in kwanta nagaji wallahi.



Washe gari.


"Tun safe nadasa sabon kuka ko karyawa kin yi nai duk irin lallashin da mama takemin besa nai shiru ba har ta gaji ta kyaleni tacigaba da harkokin gabanta dan tun dare tagama shiryamin komai nawa dakuma abinda tasan zan iya buk'ata kamin randa su Yaya maryam zasuje.

Tun safe gidan ya cika da danginmu wa inda suka zomin Sallama zainab na gefena tana tayani kuka duk da cewa tun jiya Abba yace ta shiryo da ita za aje.


Da misalin k'arfe biyu daidai narana mukabar gida cikin motar Abba kuma da kanshi yakejan motar mama na gefenshi yayinda nida zainab muke baya ko k'annena Abban be yarda sun biyomuba.

Sosai Abban yai tafiya kuma har lokacin hirarsu sukeyi hankali kwance saikace ba niyyar kaini wani gida sukeyiba.



. **
Cikin wani farin boyel yafito sai bula uban k'amshi yakeyi yafito a angonshi hannunshi rike da wayoyinshi guda biyu,Da sauri Yaya haliman tafito kallabi ahannu" Banfa ganeba habibi munyi magana dakai d'azu yanzu kuma kana niyyar ficewa ina zaka?

Cikin shagwaba yace"Kai aunty iyakata plaza fa kuma ba jimawa zanyiba dasun shigo kawai ki danno ni nikuma zandawo akan lokaci insha Allah.

"To shikenan adawo lafiya zan rigaka ganin amarya Kenan?

Saida yakai bakin kofar fita falon kamin yace" Babu komai ni anjima da ita zan kwanama.


Akunyace ta wuce kitchen batai tunanin zaice hakanba sabida falon cike yake da matan babanninsu dakuma 'ya'yansu yawanci duk 'yammatane,Dama ta lura da kallonshi da suketayi.

Wani uban tsaki inna uwale tasaki kamin tace ayidai mugani idan tusa zata hura wuta,K'aryar banza kawai.

Baba gaje dake matsar hannun diyarta danfa gaskiya ita dama son Ahmad din takeyi kawaidai tsoron mutuwa yasata kin nunawa,Amma yau ganin da taimishi saitaji bama zata iya hakuraba,"Uhum a Allah dai yasa wannan rayayyace.
Duk kusan zukatan 'yammatan yau dai saida suka motsa to Ahmad dai mutun be isa ya kushe shiba yayi tako ina.

Dama tsabar bakin ciki da ganin kwaf ya kawosu bawai zuwan Allah bane.

Sunkuma kasa sun tsare sai sunga amarya da wa inda suka kawota.

Duk da suna ganin yanda aminan alhajinsu Ahmad din keta kaida komansu kamar bikin na mazane ba mataba,Sabida basusan mahaifin ayshan ne tafe da abarshi ba.



***

Bansan cewa barci naiba saida naji muryar mama sama-Sama tana fadin tasarta zainab Allah ya nufa mun iso lafiya.

Tashi nai zaune ina addua kamin na bude idanuna wa inda sukaimin wani irin nauyi.

Tuni Abban Dr. Din da abokanshi sun fito dan tararmu lokacin mama Nata fama dani infito amma na makale gani nake kamar makasata za ashiga dani.

Kamo hannuna Abban Dr. Yayi kamin ya fiddoni bakinshi har kunne yana gyaramin lullubin kaina"Sorry 'yar gatan diyata daina kuka babu Wanda zai takuraki indai ina gidannan,Sannunku da zuwa hajiya.

Dariya mama tayi kamin tace nikuwa ai nayi fishi sai yanzu ka ganni kanata diyarka.

"Hahha aimin afuwa natuba Sannunku da zuwa.

Maman Dr. Ce tafito da saurinta cikin ado ta rungume mama cikin farinciki suke amsama juna kamin ta karbi hannuna daga na Abban ta

Please Login or Register in order to submit comment