Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fararen idanuna,Abun saiya bada wani style na daban shiyasa be fahimci harararshi naima amma ogan ya fahimci hakan shiyasa yasaki dariya"To babu komai muna godiya Daniel hadda wata dawainiya haka kuma?

Tare suka fita nikuma na zauna ko kallon kayan daya ajiye banyiba.


"Hey man wanna yarinyar rigimammace sosai kaga yanda take hararata tana turomin k'aramin bakinta?

Sosai aranshi yaji haushin maganar da yayi Amma ya share dan babu yanda zaiyi dashi.


Sumbatar hannuna yai tare da zama" Babyna yafa gane kina harararshi wallahi,Kinga da kika juya idanunki dinnan d'azu bakiji yanda wani abu ya tsargamin nan da nan ba.

K'okarin ture bakinshi nakeyi Amma yana kuma lafewa,Saida yagama tsotseni Sannan ya sakeni tuni jikinshi ya saki saiwani maida numfashi yakeyi akai akai sabida yanda yataso fitinarshi.

"Ki dinga hakuri baby idan kikace zaki biyema wa innan 'yammatan Allah zasu zautar dake ne bakiga duk kusan halinsu daya ba?

" Toni ina ruwana Ai wallahi babu wacce zataimin in kyaleta nifa duk jiransu nakeyi sonake akai matakin da ssai sunfara shakkar shigowa nan wallahi.

"Yanzu ke in banda abinki inda anbarki da kausar da ya zakiyi da ita dan Allah?

Jinake kamar in fallamishi mari kenan ya raina k'arfina kenan!! To ai tunda kana tunanin babu abinda zan iya da barina kai da itan kaga yanda zamuyi kuma kasan Allah? Ko yanzu bawai kyaleta naiba jira nake mukuma haduwa saina had'amata jini da majina ita da shegen daya aikota.

" Allah yabaki hakuri gimbiya ainasan zaki iya,Yanzu d'agani inje masallaci Amma bazan dawo da wuriba me zan wutomiki dashi?

Idanuna na d'aga sama kamin ince"Kaga da sweet da wannan naman irinnan rannan dinnan?

Murmushi yasaki tare da lakacemin hanci da baki"Wato wannan bakin ya iya kwadayi ko?



"*"*

Misalin Tara da rabi na dare.


Kwance take tai lamo amma ba barci takeyiba wani irin masifaffen ciwon ciki ke damunta wanda tafaraji tun da yamma amma be tsanantaba kamar Yanzu.

Huzaifa autansu ne yashigo kofin tea hannunshi yana turari" Gashi inji mama tace idan kingamasha ki fito falo saikisha magani.

Nunamishi inda zai aje kawai tayi amma ko magana bata iyaba tsabar yanda takeshan wahala.



*"*"

Sai wajan goma nadare yashigo gidan lokacin har naima mama sallama na wuto d'aki dan shirin barci.

So d'aya na kalle na kauda kaina sabida haushi Sam Bansan wannan fitar Daren da yakeyi Amma na lura kusan kullun sai yayita yakejin dadi shiyasa na d'auki d'amarar rabashi da ita.

"Baby bakimin sannu da zuwa fa"

"Ashe dama har yawo idan mutun yaje sai anyimishi Sannu da zuwa? To nidai gaskiya bazan iyaba kuma wallahi idan baka daina wannan yawon darenba ka rubuta ka ajiye wallahi duk randa naje gida Allah ban dawowa.

Baki sake yake kallona kamin yace" Shikenan naji yi hakuri bazan kuma fitaba idan babu wani dalili hakan yaimiki ko?


Saida yai wanka Sannan mukaci naman daya shigo dashi,Wani kalar nama ne na k'aramar dabba sannan anyimai wani irin gashi me ruwa ruwa Saikace tsanannen farfesu,nikuma hakanan nakeji dahuwar taimin dan gaskiya akwai dadi sosai.

Da kanshi yaimin shirin barci tare mukai addua Sannan yajani jikinshi"Kwanta in kuma shafamiki maganin"

"Waikai kabari inshafa da kaina saiwani kallemin kakeyi kumadai kasan cewa babu kyau kallon jikin mutun ko?

" Haba Babyna nifa mijinki ne kin sani Allah ya yarjemin in kalli ko ina na jikinki har ma in taba Danhaka bawani abu bane dan na kalla kumama ai lalurace tunda magani zan shafamiki.


Da lallashinya yasamu ya kwantar dani tare da budeni da niyyar shafa maganin.



****

Cikin daren ciwon ya matsa mata nan da nan hankula suka tashi,Akafara Neman yanda za ai akaita asbt domin dare yashiga lokacin sosai.

Mamarta da d'agata da niyyar sakamata doguwar Riga kawai Saidai sukaga jini nabimata k'afafu kamin aiwani yunkuri yafara biyomata ta hanci har yana kwareta.
Ihu maman tasaki tanakiran sunan uban dayaje canzo kaya dan tafiya asbtn.
Tsananin tsoratan da sukayi yasa duk tunaninsu Neman kaucewa tana rungume hannunsu tafara jijjiga kamin wani lokaci jikinta yasaki alamar rai yayi halinshi, bakinta da hancinta jage jage da jini banda wanda ya zuba ta k'asanta.

Shikenan kausar angina ramin mugunta kuma kin afka.

Saura muga mekuma Daniel ya kawo.





Dan Allah kuyi hakuri abubuwne sukaimin yawa wlh.


Nagode.




JARUMA.



Haske writer's association.
12/10/20, 2:33 PM - Naffy Aliyu Umar: 40





Kusan kashe din maman yai tasiri akanshi dan sosai yaso Yauma yakuma taramin wata gajiyar,Amma sai Allah ya temakeni ya kyaleni amma duk da haka saida nasha matsa sosai kamin yabari muyi barci.



"Zaune nake cikin falona na bude ledar da nagani me d'auke da kayan kwalam kala kala wani kalar namane ya birgeni ahankali nafara cinshi inajin yanda dadinshi ke tafiya dani.
Saida nagama cinyeshi tas Sannan kawai saina lura da jini ne cikin robar amemakon romo,Wanda da farko tabbas romo ne nagani.
Ina ajiye robar atsorace kawai sainaji wannan naman yana hadewa cikin cikina gashinan inajin tsawonshi yanda ya hade yakoma kamar k'adangare.
Kuka nafara da k'okarin fiddashi kawai sainagayafara cin hanjin cikina yana tsitstsinkasu,nan da nan nafara aman jini tabaka ta hanci tabaka ta hanci.

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un wayyo Allah zan mutun wayyo Abbana hanjina.

Afirgice na tashi kamar yadda shima ya mike tare da rarumoni jikinshi,Matseni yai yana tofamin addua kamar yadda nima nakeyinta abayyane ga jikina daketa uban rawa.

Hade bakina da nashi yai duk da naso in kwace tunda gabadayanmu daga barci muka farka to bedamuba shiyasa nima na jure hakan dayakema an gyara bakin kamin akwanta.

Kuma shigewa nai jikinshi,Inajin yanda yake juyani har saida yaji jikina ya daina tsumar da yakeyi Sannan ya sakeni yana kuma sumbatar goshina"Baby kincika tsoro meyasa kike firgita ne?

"Dama dole kace haka ai tunda an had'ani aure da kai danni dacan Bansan irin wa innan abubuwanba,Barcima me dadi Neman hanani yinshi akeyi yanzu gaskiya yakamata ka gayamin gaskiya Dr. Indai ba aljanu garekaba to gaskiya kai mayene haba abun yai yawa"

Idanunshi ya fiddo gabadaya baki bude kamin yace"Haba Babyna nine mayen kuma?

"To bakaiba nice mayyar haba mana, Nidai gaskiya acanza inba hakaba duk randa kabari nakamata cikin mafarkina narantse da Allah kasheka zanyi har lahira,Kasandai ance idan kai mafarkin maye kuma kaimai wani abu to azahiri zaiji ajikinshi ko? To wallahi ni kasheka zanyi haba Nina gaji tunda na aureka hankali na be kwanta gaka da bak'ar mugunta.

Shigardani yai cikin jikinshi yana murmushi dan gani yake kamar har lokacin atsorace nake shiyasama yakejin nishadi jin yanda nake magana.


Mutsu mutsun kwacewa nakeyi amma ya matseni dole na hakura na kwanta jikinshi kamin insakamishi kuka dan haka kawai naji hankalina yaki kwanciya da mafarkin danayi.

Inajin yanda yake matsarmin jiki Amma nai banza dashi har Bansan lokacinda barci yai gaba daniba karona biyu.



****

K'arfe biyar na asuba duk wanda yakamata yaji mutuwar yajita,Abun yai matuk'ar firgita mutane balle idan akaji yanda tai mutuwar,Temako d'aya da Allah yai shine bata fadi cewa tazo gidansu Dr. Ba hakika da wani zargin ya hau kanshi,Shiyasa sai mutane sukafara tunanin kodai ciki tayi tazo zubardashi yai ajalinta.

Kuka mama tasaki lokacinda taji labarin mutuwar,Kenan da Yanzu ayshace ta mutu kenan? Nan da nan ta d'ora zargin dasa hannunta 'yan uwanta da abinda yake damun yaronta kenan? To inba hakaba taya za ai hakan ta faru?

Shigowarshi sallar asuba kenan ya d'aga wayarshi daketa haske.
"Mama ganinan nadawo masallacin"

"Yauwa to maza kazo ka kaini gidan suwaiba kausar ce Allah yaima rasuwa.


"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un mama mutuwa fa kenan? Innalillahi ganinan mama.

Tuni na mike tsaye ina kallonshi.

" Kinji kausar ta mutu cikin dare Aysha, Tashi muje in kaiku keda mama gidan saka dogon hijab.



"Kai wannan abun daban mamaki yake Ahmad kenan suwaiba tanada masaniyar duk abinda ke samun matanka kenan? Wai dan Allah me naima suwaiba haka? Wace kalar masifa ce wannan?

" Mama mutuwarnan bata kyautaminba wallahi naso kwarai ace nahadu da ita inji labarin komai, naso inji ubanda yabata maganinan koda yake taima kanta ai Itama taji idan akwai dadi,Kinga yanzu wani zargin zaikuma hawa kaina kilama ace nine na kasheta.


"Ashirye nake Ahmad zanbawa kowa mamaki wallahi nagaji nagaji bazan kuma yadda a lakamaka sharriba nagaji Wallahi zan saba da kowa wannan lokacin.

Nidai ina gefe ina jinsu Ammafa ni kaina banso mutuwar kausar ba naso inkuma haduwa da ita naso inji wani abu daga gareta.


Cike muka tadda gidan,Mama tana rike da hannuna ahaka muka ratsa mutane zuwa k'uryar d'akin inda 'yan uwan mamanta suke zazzaune ko wanne ya ci kuka ya k'oshi,Saina turo ranar da ya fati ta rasu muma haka muka kasance cikin damuwa da tashin hankali.



K'arfe Tara nasafe mutane duk sunyi sauki dan tun takwas aka kaita makwancinta,.

Cikin yanayin shagwaba na matsa jikin mama" Mama yunwa nakeji rana tayi.

"Af na manta wallahi yi hakuri" Ke hafsat samoma aysha tea tasha.,Mama tai maganar tana kallon wata wadda na fahimci kamar itama nan gidan take.

Banso hakanba dannifa gajiya da zama ne nayi shiyasa nace haka bawai yunwar tafi damunaba.

Mikama mama wayarta nayi ganin Dr.na kiranta.

"Hello mama nace ku fito mu wuce hakanan ko?

" Gaskiya ni ba yanzu ba Babana.

"To mama turomin baby mu wuce Da yamma na maidota.

Kallona tai dama nai bakam inajiran yanda za ai,Sainaji tace" tashi ki je yana jiranki yace da yamma ya maidoki,Ayo abinci zan aiko in amsa kinji ko?


Tuni na saba hijab dina na fice to dama nagaji balle danaga duk wanda akacema ga matar Ahmad sai inga anamin kallon tausayi kenan nima nakusa mutuwa kenan.



***

"Oh da Yanzu fa shikenan har an kaini kabari an rufe ko?

Murmushi yayi tare da matse hannuna dake cikin nashi" Hummm da Yanzu na haukace dai baby .

Tea nafara had'amana danshima yunwar yakeji Sannan na soya kwai dan yace shi babu abinda zai ji dan yasha tea kawai.

"Zo muyi wanka Babyna"

K'okarin rugawa nayi ya cafkoni yana dariya"Babu inda zaki Allah zo nan kinji,Bawani abu zanyi miki ba.

Tabe fuska nai zan saka kuka Amma ya rufemin baki da nashi fuskarshi cike da walwala.

Saida yagama tandeni saikace tsohon maye Sannan ya kyaleni muka shiga wankan.

Da kanshi ya cudeni duk da cewa wasanni sunfi yawa ahaka muka fito,Yana tsokanata wai da antabani sai inkama tsiyaya Amma tsabar mugunta ban bari ya tabani yanda yakamata.

Nidai bakina kawai na turo kamin ince"Waikai k'anwarka ta rasu Amma sai iskanci kakeyi nidai babu ruwana wallahi.


Riga da zani na atamfa nasaka sannan nai kwalliya,Na fesa turare.

Shiko jallabiya kawai yasa sai turare yafita falo"Baby zomu bude tsarabarki ta jiya"

Samun kaina nai dajin wata faduwar gaba,Amma haka na mike tsaye na nufi falon.

Tuni ya fiddo kayan dake cikin ledar yana jiran k'arasowata.

"Kinga wannan ledar namane ciki Amma banciba nadai bude yanzu saimu cinyeshi kamin anemi abinda zamuci da rana da wanda za akaiwa gidan rasuwarcan,Kai kalli alawar nan daga gani zatai dadi.

K'okarin bude 'yar robar nake ina fadin nifa zanyi girkin kai kuma zaka tayani dama haka mama tace.

Uban ihun Dana saki shiyasashi sakin alawar dake hannunshi ya taroni tuni na mik'e tsaye ina sakin wani ihun idanuna rufe sai rawar da jikina keyi kota ina.

Makalkaleshi nai ina kuwwa abinda yakuma firgitashi kenan balle daya kalli abinda nakema ihun.

Subhanillahi, Innalillahi menene wannan lahaula wala kuwwata illabillah.
D'agani yai gaba daya yamaidani saman kujera tare da cewa karki bude idanunki aysha.

Shi kanshi jikinshi rawa yakeyi Sannan tsigar jikinshi duk tagama tashi,Tunanin abinda zaiyi yafara sabida besan ta yanda zaikashe abin ba.

Mofer ya jawo ya danne murfin robar tare da d'aukewa ya fita harabar gidan dagacan baya.

Kananzir ya d'auko da ashana ya tuttula abin da robar gabadaya Sannan yasa ashanar.

Wata irin zabura yai lokacinda yaji wayarshi na ring da sauri ya dafota tare da d'aga kiran jikinshi na rawa"Hello salim kana inane?

"Ah lafiya najika haka kuwa, Kai kana ina haka? Ganinan zanzo gidanku naje gaisuwane mama tacemin kayo gida kaida aysha.

" Eh mundawo dan Allah yi sauri ka k'araro ganinan gida yi sauri.


Yana saka wayar aljihu salim din na shigowa dan be shigo da motarshi cikin gidan ba.

Agabansu abin yacigaba da cin wuta,Salim kasa magana yai saidai ganin abun na Neman yo tsalle waje yasa suka nemi mabugi,Shikuma Dr. Yakuma zuba kananzir din.

Sosan filon kujera ya shafeni nan take na tsala ihu bakuma tare Dana kuma bude idanunaba.

Da gudu yayo cikin falon shikuma salim ya tsaya wajan wutar.

Da wuri na d'ane jikinshi ina kyarma shikuma ya rungumeni sosai jikin jikinshi yana shafar bayana, Kuka nakeyi ahankali ina kuma likewa jinake kamar in tsaga jikinshi inshige ko Allah zaisa tsigar jikina ta daina tashi.



Saida salim ya tabbata wutar tagamacin abin ya kone kurmus Sannan ya nufo cikin gidan yana mamakin abinda yafaru.


"Ahmad meya faru haka ya akai?

" k'okarin ganin ya yakiceni daga jikinshi yake amma ina kuma likewa nake ina kukana"Kaga kyaleta tasami nutsuwa wa innan kayan na menene? Cewar Salim din yana zama akan kujera.


Saida dibara yasamu ya zauna Sannan ya maidani jikinshi yanad'an rufamin kallabina akaina da kafadata datake abude"Wallahi mutun mugune Salim Ashe Daniel bada zuciya daya yake zaune daniba? Shima ayshan yakeson kashewa salim jiya yazo kamar yadda kasani,To saiya kawo mata wannan tsarabar amatsayin gift na aure kamar yadda yace.
To jiyan saida na duba abinda ke cikin ledar sainaga duk kayan kwalamane dai haka,Saidai cikin wannan robar wani namane me kyau da romanshi,Ko tabashi banyiba saina bari Sai zamu kwanta in nunamata saimuci.
Tokuma tunda na shiga sai bankuma fitowaba muka manta da kayan gaba daya,To kuma kaga yau tun asuba muna gidan rasuwannan sai ba dadewar nan muka shigo yanzu muna bude ledar kasan menene cikin robar?

Kai salim din ya girgiza yanajin yanda k'irjinshi ya tsananta bugawa.

"Wallahi Salim wani abune kamar kadangare Amma kuma bayanshi kamar na kada sabida kurzini kurzinin da yake dashi bakinshi cike da wasu kalar hakora sai yawo yakeyi cikin jinin da nagani romo jiya.

Salim da kaina naga naman jiya wallahi kaga kenan inda taci zuwa yau tafara ciwon ciki dannasan dole hademata cikin ciki zaiyi yafara cin hanjin cikinta,Salim meyasa mutanen duk dake kusa dani sune macuta gareni?
Meyasa saini?
Meyasa ni bazan zauna da mataba?
Meyasa akeso dole Sai an batamin suna?


" Kayi hakuri Ahmad ka kwantar da hankalinka dan Allah ai godiya yakamata kayima Allah tunda har gashi yanzu abinda ke boye yana fitowa fili damani wallahi najima ina zargin Daniel sabida yanda yake mugun shigemaka,Ashe mugun yasan abinda yakeyi.

"Bari inzo muje yau ba sai gobeba zan nunamishi kalata wadda be saniba wlh.


" Kai babu inda zamuje yau ka tsaya tasami nutsuwa tukunna,Yanzu bari in kone wa innan ma,Ina zuwa.





JARUMA na kudine idan kina buk'atar shi to ki tuntubi wannan lambar.
08142643253.




Haske writer's association.
12/10/20, 2:33 PM - Naffy Aliyu Umar: 41




"Babyna"

Kuma lafewa nai har lokacin tsigar jikina batabar tashiba,Bankoso in motsa.

D'agani yai gaadaya ya nufi d'akinshi dani,Ya direni Saman gadonshi,Saida ya kwanta sannan ya kwantar dani jikinshi yana shafar bayana lokaci zuwa lokaci yana sumbatar goshina da kuncina,Soyake kawai inyi barcin ya fice daga gidan yau dinnan saiya dangana da inda zaiga Daniel saiya gayamishi abinda yake nufi dashi wallahi.

Tun yanajin sukur sukur dina har saida yaji shiru,tunanin inda za a sami abincin da za akai gidan rasuwan yakeyi, Ahankali ya lallaba ya sauka daga gadon tare da canza kaya komai cikin sand'a yakeyi.


Zaune ya tadda salim cikin falon.

Zama yai cikin yanayin sanyin jiki kamin ya fitar da wani zazzafan huci ta bakinshi"Kalla nan salim har yanzu tsigar jikina batabar tashi ba Dan Allah kalli nan,Yai maganar yana nunama salim din tsintsiyar hannunshi,Inda k'ofofin gashinya duk suke mike.

"Ka kwantar da hankalinka Ahmad insha Allah za asami mafita kaga yanzu be kamata tun yanzu ka nemeshiba ka bari Sai zuwa gobe lokacin ita aysha tasami nutsuwa sosai sai muje koda abujan ne kaga sai ayi wadda za ai amma yanzu ita mama batanan sannan ita aysha bata da wata nutsuwar kirki balle mubarta mu wuce ko?


" Hummm bazaka ganeba Salim Yanzu haka jinake kamar inyi tsuntsuwa in ganni gabanshi haka nakeji,Wallahi bazan taba kyale Daniel ba saiya gayamin uban mene hadina dashi,Sannan me yake bina dashi.


"Kaidai na gayamaka ka kwantar da hankalinka, Mubi komai Sannu,Ammafa gaskiya kaina ya kulle Ahmad to menene tsakanin kausar da Daniel? Tare sukeyin aiki kokuwa kowanne zaman kanshi yake? Waima mutane nawa suka hadu wajan ganin sun tarwatsa rayuwarka? Kai man,Akwai matsala fa!!!


" Nasani Salim nikaina nasan cewa akwai matsala wallahi shikenan duk ni suka sama ido kenan? Shiyasafa ni kaina nakejin tsoron kaina abun yai yawa wallahi tun tuni nafara tunanin kodai da gaske ni mayen ne Ashe mugayene kewaye dani,To da wannan abun ma ai da kasheni kawai sukayi suka huta,Dan Allah katashi muje mu nemi munafukin Allah mugu.


"Kai matsalata dakai kenan rashin hakuri wallahi dallah kabari mubi komai ahankali mana,Yanzu dai bari inkira hafsat tazo sai suyi girkin da za akai can gidan,Daga baya saimuyi maganar data dace Amma dan Allah ka jure dan kasamu itama tasami kwarin guiwa.




***

Akai akai nake nake share hawaye tunda na farka daga d'an barcin da bawani jimawa nayi ina yinshiba.

Tunani nakeyi gaskiya masu harin rayuwar matan Dr. Nada yawa gaskiya bazan iyaba nagaji da zama dashi,Tunda kullun da sabon abinda zangani,Kenan gabadaya rayuwata tana cikin had'ari kenan?.

Da sauri na share hawayena,Lokacinda naji Sallamarshi.

Shima cikin sanyin jiki ya k'araso kusa dani tare da rungumeni cikin jikinshi yana d'an bubbuga bayana" Kuka kikeyi ko baby?


"Bakaso inyi kukane Dr.? To idan bakaso ka maidani gida kamin ku had'u ku cinyeni wannan wace kalar masifa ce daga wannan sai wannan?


Tallabo fuskata yai yana kallon cikin idanuna wa inda ke zubar da kwalla sharemin yai kamin yace" Wai baby waye yacemiki ni maye ne? Kema zargina kikeyi da cewa nine ke kashe matana?


"To Dr. Idan ba hakanba menene? Gabanka k'anwarka taso zubamin magani da Yanzu nasan na mutu,Sannan jiya abokinka yakawo wani ji abinda yakawo inci dan Allah? Tunda kasan halinshi da mugun abunshi me zaisa har ka amince kuyi abota dashi? Shikenan kai kullun da kalar damuwar da zan gani gidanka kenan!!!.


" Aysha kiji tausayina mana,Wallahi banda laifi kema kinsani Amma tunda kina ganin haka ki k'ara hakuri insha Allah zan tsananta bincike kwanan nan tunda yanzu anfara samo bakin zaren ai kinga dacan babu wata alama data nuna ga inda matsalar take,To kinga yanzu koda kausar ta rasu ai ga wata hanyar da zanyi bincike ko?
Dan Allah ki kwantar da hankalinki kedai kawai ki tayani da addua insha Allah komai zaizama labari baby da Sannu zaki fahimci cewa babu abinda nasani daga wannan abun dake faruwa, Yanzu tashi kije ga hafsat can tazo matar salim saita kamamiki kuyi girkin da za akai can gidan rasuwar.

Cikin shagwaba nace Dr. Nifa nagaji jikina namin ciwo!!

"Sorry babyna idan kungama zanyimiki wanka saina tausa miki jikinki Sannu kinji.



Kasancewar hafsat nada son hira shiyasa kawai nasamu tunanin dake cikin zuciya ta ya ragu.

Bansan inda Dr. Da salim din sukajeba,Baby aysha na bayana na Goya sabida sosai nakeson yarinyar balle da akace wai takwara akai min.



*"*"*

Mamakin irin kallon da yayarta keyimata takeyi wanda hakan yasa harta fara tsarguwa duk da cewa har lokacin tana cikin tsananin tashin hankali na mutuwar d'iyar tata Amma kuma sam takasa fahimtar irin kallon tuhumar da yayartata takeyimata.


Saida aka fara sallar azahar Sannan suka samu kebewa.

Mamance tace" Suwaiba me naji mutane na fadi?


Habar zaninta tasa ta share hawayenta kamin tace "Yaya wallahi sharri akemata Amma kausar batabin maza hasalima mazan basu gabanta,Sharrine kawai ake mata wai ta zubar da ciki dan Allah karki yadda da hakan wallahi k'aryane.

Tabe baki tai kamin tace Allah ya kiyaye to,Ammadai yakamata ki daina mata kuka hakanan kuma jiya ina da ina tacemiki zataje?

Cikin shessheka tace Yaya daga gidan hasina sai gidanki tace zata kuma data dawo tacemin bataje gidankiba sai yau

Please Login or Register in order to submit comment