Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewar yaje d'aukokiba Sai abbansu ke gayamin ina laifin ya barki ko kwana hudu kiyi ko biyar!!!Amma ki kwantar da hankalinshi insha Allah wataran sai kije kiyi sati abinki kyaleshi kinji?

Kaina na d'aga tare da maidashi Saman kafadarta ,Lokuta da dama sainaji kamar da mamata nake tare,Yanda takeji dani bataji da yaron nata duk da cewa naga shima yanayima iyayenshi shagwaba da yayinshi Amma sam beyi gaban idona da nazo wajan zai fuske yafara zare ido.



Dambun nama da lemo ta kawomin,Sabida ita na taddata da wata d'abi'a ta indai akai Sallar isha'i to zata bayar da abincin da yai saura sabida bataso ya kwana Saidai a zubar.
Bama wata yunwa nakeji ba Amma haka ta matsamin dan tasan anjima kadan Zai idasa rarake wanda ke cikin nawa,tunda dai tasan zalamarshi bazata bari yabarni in hutaba.

K'amshin turareshi yai mana sallama kamin ya idasa shigowa,Janye kwanon dake gabana yai yana gaida maman"Wai mama dan Allah tare fa muka dawo Amma ita kin jawota nan kina cikamata ciki nikuma ko oho kenan?

Sanye yake da farar jallabiya ta Mara nauyi bak'ace wadda tai matukar yima fatar jikinki kyau,Sai tashin wani Sassanyan k'amshi yakeyi fuskarshima fes kamar wanda yashafa hoda.


Harararshi nai tare da kauda kaina gefe.

Yayinda mamar Itama ta harareshi"Kaini bansan shirme kai yarone da zan tsaya wani lallashinka dan kaci abinci? Ya hanya ya Kuka barosu.

Saida yacika bakinshi da naman kamin yace kowa qalau mama suna gaisheki ga Sako can mama tace akawomiki.

"Allah sarki aiko angode Allah yabar zumunci,Zandai sami usman ya kaini inyi yini insha Allah, Idan ankwana biyu.

" Aysha muje ki wanka ga ruwa can na had'amiki.

Turo bakina nai kamin nace nidai gaskiya a a babu wankan da zanyi Sanyi ma nakeji.


"Ah k'arya kike wallahi dole ki yishi dan bazaki kwanta kusa dani kina tsamin daud'a ba.

To shikenan ma saina kwana wajan mama kaikuma ka kwana can ai hakan yayi ko?

Kauda kanshi yai gefe yayinda cikin zuciyarshi yake nanata,Inba wahala tajiba Sam bakinta be mutuwa,Yayinda maman keta dariya cikin ranta jin diramar da mukeyi.



"*"*"

Wai mene kake bina dan Allah?

"Ke bansan shirme cud'a zanyi dallah.

Toni wallahi banso ,Kai nifa idan ka dameni ma zan iya yin tafiyata wajan mama,Dama kanaji tace idan ka dameni in koma can ko?


Kwanciya yai tare da juyamin baya" Shikenan Allah yabaki hakuri ni namayi barcina tunda bakison temakona Allah ya tashemu lafiya,Ki kashe kwan nan idan kin gama.


Dadi naji ganin yai kwanciyarshi,Sannan nashiga wankan,Saida na k'ara na zafi sannan nai wanka na bayan na diga turaren da yaya maryam tabani ciki.

Jinai kamar kar in fito sabida yanda naji jikina na wani irin k'amshi ga kitsona da kunshiba sunyi matukar kyau,Bakina na tabe inajin haushin wanda nai dominshi ko nuna yagani beyiba,Balle in sa ran zai yaba ma.




***
Saida nagama addu'a na tas Sannan na gyara kwanciyata,Duk tunaniba tuni ya jima da barci,Ashe lamo yai.

Tunda naji hannunshi jikina sai na kama tsuma da rawar jiki,Sam bansan wannan abun har yanzu ban hango dadin da ake fadi anashaba,Sai tsabar wahala kodan ni har yanzu nakasa sakin jiki da shine?
Mamaki yake sosai cikin zuciyarshi jin yanda jikina ke kyarma,Saikace yaune karo na farko da zai fara shiga jikina.





Labarin JARUMA na kudine idan kinaso zaki tuntubi wannan lambar.

08142643253.




Haske writer's association.


Maman khadija.
12/10/20, 2:49 PM - Naffy Aliyu Umar: 50



"Ke aysha menene?

Kuka nasaki ina matse cinyoyina wani shegen tsoro naji ya Sakkomin ta ko ina ya lullubeni.

Maidani Yai cikin jikinshi yana shafar bayana" Sorry to menene abun kuka Kuma? Tunda bakiso na bari,Ko wani waje namiki ciwo ne?

Kaina na girgiza mishi ina Sauke ajiyar zuciya,Ni yinne kawai banso yayi balle nasan yana gamawa zai sani wankan dole.

Saidai me? Barin nashi beje ko inaba,Can cikin barcina naji yacigaba da lalubata.
K'okarin kwacewa nafara Amma ya rikeni kam cikin jikinshi.

"Dan Allah kai hakuri Dr.

Bazan iyaba baby kiyi hakuri ahankali zanyimiki Amma bazan iya hakuriba,Bakiga na kasa barci ba?


Tuni yafara nisa yayinda nikuma nake motsin kwatar kaina dan da gaske nake yaudai banso,Balle idan na tuna abubuwan danaci da sha wajan yayuna da mama wanda suka tabbatar min da cewa zai gigice yayinda nikuma zanji ajikina,Hadda wannan tsoron ke Kuma dabaibaye zuciya ta.

K'afafuna ya harde cikin nashi yana magana cikin,Lallashi da canzawar yanayi" Haba babyna sosai kike saina baki wahala yau ko? Kuma kice ban tausayamikiba,Nace zanmiki ahankali fa.

Be kuma saurarataba haka ya saki jikinshi yafara nunamin wata zazzafar soyayya,Acewarshi.

Tun ina gane abinda yakeyi har Saida jikina yasaki banda surutan da yakeyi babu abinda nakeji Suma sai sama sama nake jiyoshi.
Duk idan nai k'okarin tureshi jikina to idan yatashi komawa saiya shigeni da kyau da kyau tuni nai wani mugun laushi jikina ya saki,K'afafuna kamar ba nawa ba sabida wahala.




**

Girgiza tai so uku Saigashi tazama wata shirgegiyar mage bak'a sud'ul da ita da wasu manyan idanunta kuma jajaye.

Tsalle tai ta fad'a cikin wani kwando nan da nan ta bace cikinshi.

Ta fitane cikin fishi da niyyar yau kota halin k'aka saita sami abinda takeso dan bata taba Samun matsala irin wannan ba sai yanzu.


**


Da kanshi ya temakamin na gyara jikina,Shi kanshi sai yanzu yakuma tabbatar da yarintar da ake fadin naimishi, Sannan gashi dai yana iya bakin k'okarin shi wajan biyan buk'atar shi Amma wajan yaki saki,Balle sabo ya shiga.

Gyara d'aurin tawul din k'ugunshi Yai tare da bude goran ruwan"Anshinan sha saiki kwanta menene na hawayen kuma?

Turo bakina gaba nai "Toni bansan wankan.

"To baby ba anyi wankan ba shikenan? Nifa banso ki kwana da datti ne jikinki balle mu da muke cikin tsaka me wuya,Dan nasan duk kusan wani mugun abu cikin dare ake k'ullashi,Shiyasa kwanciya cikin tsarki da alwala ma kariya ne kinji ko?

Ajiye ruwan Yai yana gogemin bakina, Tare da mannamin kiss Saman idona" Allah yaimiki albarka babyna,Nagode da kika kasance k'ofar da zan shiga dan samun nutsuwata.

Kwanciya nake niyyar yi ya rikeni"Tsaya in canza miki Riga saiki kwanta.

Da kanshi ya sakamin rigar,Sannan shikuma ya saka gajeran wando ya hayo gadon.
Rungume ni Yai jikinshi yana shafar bayana "Baby.

D'an motsawa nai Amma ban Amsaba.

" Allah yaimiki albarka.

Cikin shagwaba na fara tureshi jikina,Amma saiya kama hannun nawa ya sumbata yana sakin murmushi.

Addu'a yaimin Sannan ya shigar dani jikinshi"Yi barcinki kinji? Bazan kuma yimiki wani abu ba Sai asuba idan Allah ya kaimu.




""*""
Wajan bemata Nisan zuwaba musamman data taho da mugun nufi cikin ranta,So take kamin garin Allah ya waye komai ya kammala.


Shigowar ta cikin gidan batasami wata matsalaba haka ta ratso ko ina Har saman kaina inda nake kwance ina barcina.

Mafarki.

Jin nauyin da kaina yaimin yasani bude idanuna batare da na tsaya jinkiraba,Bakina d'auke da addua Neman tsari daga dukkan sharri.
Ido biyu nai da wannan shirgegiyar magen da manyan idanunta jajir dasu.
Tunanin ta inda ta shigo nafara ba tare da jin tsoron ganin da naimataba,Wani ikon Allah kuma Dana juya kusa dani Sai banga Dr.ba,Kenan d',akinshi ya koma kokuwadai shine ya rikid'a dan dama ni har yanzu bawani yarda dashi naiba.
Yanda wannan kyanwa tai min kuri da jajayen idanunta haka nima nake kallonta da fararen nawa taiwani goho Saman mirona kenan tanayo tsalle kaina zata dira.

Wani gurnani tafara tana zubar da miyau Sai kawai naji wani kwarin guiwa yazomin kai tsaye musamman da na lura kamar Itama tsoron fad'omin takeyi.

Wani uban tsalle da ta dirko Saida tsigar jikina ta tashi gaba daya kamin wani lokaci mun kacame wani matsiyacin fada,Domin fadane na ganin kowa yasami sa'ar kowa.

Kayan jikina basu da nauyi dan rigace me shara-shara yasamin kuma ko pant ban yarda yasaminba Sabida alokacin jin wajan nai yanamin ciwo.

Wata karta da ta kawomin da faratunta Saida fatar cikina ta fara jini.

Wani uban ihu na zabga wanda ya karade kaf gidan.

Ta wutsiyar idonshi yake kallon yanda nake haure haure Amma be iya yanke nafilar da yake ba, Saida yaji Wannan fitar ihu Sannan ya haura gadon batare da ko sallamewar Yai ba.

Lokacinda take niyyar guduwa ne Allah yabani ikon damk'ar wuyanta nan naimata wani mummunan riko,Saigashi jini na biyo mata ta hanci da baki.

Kirjina da hannuwana duk sawun faratuntane ga wata azaba da nakeji Amma hakan besa na saketaba tun tana yakushina har Saida naji taimin nauyi ahannu alamun na kasheta,Sannan na saketa.

Saidai sakin da naimata shine yai dai dai da farkowar da nai daga wannan mummunan mafarki mara dadi.
Ganinshi nai saman kaina yana niyyar zubamin ruwa afuska,Ashe wai jijjigani yaketayi Amma naki farkawa shine yakoma ya debo ruwa.

Aje kofin Yai tare da tallaboni jikinshi.
Wani irin duhu nagani bankuma sanin me duniyar take ciki ba balle in k'arar.


Ihu da salati yasaki lokaci d'ayaDai dai lokacinda maman da Abba suka turo k'ofar Sabida dama suna tsaye ne da niyyar kwankwasa kofar.

"Wayyo Allah nabani mama kalla kiga ta daina numfashi ,Innalillahi wayyo Allah meya faru haka.

Ganin yanda duk ya rude yasa Abba juyawa yana fad'in rufemata jikinta sai asan abin yi.

Da kanta ta nemo doguwar Riga ta sakamin yayinda yake kaina har lokacin yana kira yana Sambatun yabani meyake faruwa haka.

" Kai d'aukota muje asbt gaskiya tunda taki farfadowa,Cewar Abban shima cikin tashin hankali.



***

Yaraf ta fad'o tsakiyar d'akinta ko numfashin kirki batayi gashi dama gidan babu kowa balle tasami wanda zai temaka mata.

Haure haure tafara da shure shure yayinda wata irin farar kumfa ke biyomata baki da hanci.




***

Kusan tsaye duk suka kwana banda msallaci ko nan da can babu wanda ya matsa,A kai akai yake hawaye bayan yagama kallon agogon dake cikin d'akin.

Abba ne ya dafashi"Haba mana Ahmad ka kwantar da hankalinka insha Allah zata farka kaimafa likita ne kuma kasan zata warware ko?

"Cikin alamun tashin hankali yace Abba kalli hannuwanta.

Gabadaya suka matso gaban gadon aiko sai hankalinsu yakuma tashi sabida tun daga wuyana har zuwa hannuwana Yai wani irin tashi musamman wajan wuyana.

Naso nason jinin dayagani Saman jikin rigar daidai cikina yasashi saurin yaye rufar da akaimin, tuni ya manta da Abban na wajen yai Sama da rigar aiko saiga wata babbar yanka wadda har lokacin take tsatso da jini.

Wani irin taga taga yai zai fadi Abban ya taroshi yana salati dole ya zaunar dashi sabida tsumar da jikinshi ke yi.

Sautin kukan mama ya cika d'akin tanayi tana salati.

Dole tafita ta kira likitan dake aiki lokacin suka dawo tare,Allah yasa mace ce.

Cikin girmamawa ta duba duk abinda yadace domin Dr. Din oganta ne sosai,Kuma suna ganin mutuncin juna.


" Amma mama da karnuna sukai fad'a ne?
Cewar likitar lokacinda take zuba wata allura cikin drip din.

Duk shiru sukai sabida babu wanda keda amsar tambayar da tayi,To shima wanda suka kwana taren cewa yai kawai haka yatashi ya ganta,Amma yanzu koma menene to ya bayyana kila wani mugun abunne yazo ya farmata sukai wannan mummunan fad'an daya hanata farkowa har yanzu.


Ahankali nakejin yanda yake shafar hannuna wan inda Duk suka tashi kamar an kakkarce.

Tuni na farka Amma ko motsi nakasa sabida tsabar nauyin jiki,Tuni rana tagama haske ko ina Sabida goma nasafe tayi lokacin.
"Aysha. Yauwa mama ta farka,Da sauri ta matso dan dama yanzu gyangyadi yafara janta.

Abbane kawai ya wuce gida shima dan ya samo abinda za acine domin har lokacin babu wanda suka gayamawa Sabida Tunanin ta inda za a fahimci abun.


Kasancewar wajan wajene na wane da wane shiyasa komai akwai na buk'ata,Tuni maman tashige domin had'a ruwan zafi,Shiko tallaboni yai jikinshi yana kiran sunana.

Runtse idanuna nai ina tuno mafarkin da nayi,Duk tunanina Dr. Ne aiko hakan na fadomin na wani ingijeshi daga jikina Duk da cewa babu kwari jikina,To ma idan bashi bane to waye? Kuma ya akai be temakaminba lokacinda nake buk'atar temakon ?kai shinema tunda Ai banganshi akan gadonba tunda tare muka kwanta,To kuma ai magen Dana shake kamin insaketa saida naga kanta da fuskarta sunkoma na wata tsohuwa to ita kuma wacece?


Da kallon mamaki yabini yana zare ido kamin wani irin tsoro ya dira ranshi.

Mugun kallon da nabishi dashi yasa guiwarshi tai matukar sanyi har besan lokacinda ya fad'a Saman kujera ba .

Fitowar mama daga toilet din yasashi runtse idanunshi yana danne kirjinshi da yakejin yana wani irin matsanancin bugu.

"Sannu aysha sannu Allah yabaki lafiya,insha Allah kintashi kenan Allah ya kiyaye gaba muje ki wanka Ki gyara jikinki Saikiyi Sallah duk da lokaci ya Riga yafita Allah yabaki lafiya.

Ko motsa jikina nakasa,Sabida nauyin jikin balle in tashi,To dama ga wata irin wahala dayabani da garen gakuma k'arin wata azabar ga rad'adin da nakeji daga hannuwana kirjina dakuma gefen cikina.

Kallon tuhuma tabishi dashi,Da Sauri ya mike tare da d'aukata gaba daya ya nufi toilet din dani.

Sosai yaimin wankan,Amma na hade girar sama da k'asa kamin ince" Fita ka bani wuri" Duk da cewa cikin siririyar muryar nai magana kuma ta marasa lafiya Amma saida yaji yanda ta bugeshi.


Ficewa yai cikin tashin hankali mamaki da tsoro nakuma baibayeshi.

"Ya ka fito kuma?Kaida zaka tsaya Ka temaka mata?


D'an marairaicewa yai kamin yace" To mama ta nuna bataso shiyasa na kyaleta kadda taita kuka.





Labarin JARUMA na kudine idan kina buk'atar karantashi zaki biya naira Dari uku300 ta wa innan tsarikan.

Acct no
0005074141,Aisha sabiu ja'iz bank.

Kokuma a tuntubi wannan lambar.

08142643253.



Daga yanzu duhu uku ya yaye Sauran abinda yai Saura kuma zamuji daga INA yake.



Haske writer's association.
12/10/20, 2:49 PM - Naffy Aliyu Umar: 51



Da kallon tausayi tabishi ganin ya koma gefe ya zauna yana dafe kanshi idanun nan duk sunyi ja sun k'ankance sabida rashin barci damuwa da tashin hankali.

"Kasamu kasha ko tea din mana tunda gashinan Allah yasa tatashi lafiya,Kilama zuwa anjima mu koma gida dannaga jikin alhamdulillah.

Numfashi ya sauke kamin yace" Mama bazan iyaba naga kamar ma fishi takeyi dani wallahi ba laifina bane bansan hakan zata faruba,Da na hana bansan abinda ke bibiyar rayuwataba,Ina cikin damuwa mama.

Komawa tai kusa dashi ta zauna"Haba babana kar kasama kanka wata damuwa mana,Ai godiya zamuyima Allah daya fara bayyana komai kaduba kaga Abinda yafaru baya mana antaba Samun cigaba kamar yanzu? Ai godiya yakamata miyima Allah Dan komai daf yake da zuwa k'arshe dan Allah ka maida komai ba komaiba kumama ban tunanin aysha fishi takeyi dakai,Inkuma fishinne to na tabbata Saidai idan wani abun ka mata ammafa ba wannan ba tunda tasan dai babu yanda za ai kazo zaka kasheta balle har kai mata raunika haka.

Kanshi yaita d'agawa cikin jin dadin maganar maman kamin ya lallaba ya koma toilet din.

Nagama bayan gida kenan ya shigo,Da mamaki nake kallonshi kamar yadda shima ya zubemin idanunshi yana kallona.

Cikin tsokana ya to she hancinshi tare da cewa "Kai baby kashinki shegen wari wallahi,Da kanshi yai flushing hannunanshi ahanci wai wari.
Nidai banza nai dashi dannasan Neman magana kawai yakeyi.

" To juya inyi miki tsarki.

Wata uwar harara na wurgamishi kamar idanuna zasu zazzago tsabar masifar da nakeji na cin zuciyata.

Da wankan da komai haka yaimin duk da irin buge bugen da nakeyi,Saida ya tabbata ya gyaramin ko ina Sannan ya d'oramin babban tawul yana kallon idanuna"Ko kina da magane ne? Ke nifa wallahi zan iya turmesheki wajannan inyi abinda naga dama saikiyi fishin da hujja ah to.

Kallon gefen ido nai mishi kamin ince"Duk abinda zakai zaka iyayi amma nafi k'arfin ka cutar dani wallahi,Mugu kawai.

Shaf ya manta da cewa har yanzu zarginshi nakeyi Saida nai wannan maganar.
Ranshi bewani baciba Sai ma murmushin daya saki"Karki damu ke bazan kashe kiba haka zamu dawwama da juna inajin dadina cikin jikinki.

Hannuna yaja muka fita Sam babu damuwa fuskarshi.


Kuka nasaki sabida takaici ga zafin da hannuwana keyi da wuyana inda sawun kartar yake.
Da sauri mama ta matso kusa dani tanamin Sannu sabida ahankali nake tafiya,Inajin wani ciwo daban daga k'asana sabida wahalar daya bani da Daren.

"Menene?
Cikin kukan nace mama zafi jikina keyi.

Fita Dr. Yai Saigashi ba jimawa ya shigo da allura dakuma wani magani me kama da man zafi,Lokacin Sallah nakeyi shiysa saiya nemi waje ya Zauna suna magana da wadda banjin maganar da sukeyi.

Saida nasha tea Sannan ya danneni yaimin allurar saida nai kuka,Duk da mama tanata mishi fad'an meyasa be bina ahankali ne.

Da kanshi ya shafamin maganin aduk inda yatashi Sannan ya koma ya zauna gefena yana murmushi dan wani irin harararshi da nakeyi.


Cikin mintinan da basu wuce biyar ba barci yai gaba dani,Amma kuma be jimaba nafara mafarkin abinda yai sanadiyyar tashina ina sakin ihu.
Wai wannan magen da mukai fad'a da ita ta dawo wajena tana kuka Amma idanunta na zubar da kwallar jini" Ke aysha meyasa zaki kasheni kinsan iyakar shekarun da nayi ina cin mutane kuwa? Meyasa zaki kasheni? Ni nan nakashe matan amadu har hud'u kuma Kece ta biyar shine zaki kasheni? To bazan mutuba ni kadai.

Cikin mafarkin.
Matsawa nai daga gabanta"Ke macuciyace kuma azzaluma an yarda dake Amma kinacin amana to tunda Kece dama ke kashemai mata Allah ya to na asirinki kuma saina gayama kowa dan ayi Allah wadai dake,Sannan ki Sani ni nafi k'arfinki haka zaki mutu ki barni.

"Hahhhhhaha k'arya kike aysha dole zamu mutu tare,Idan ma ban kashekiba nan gaba k'adan inuwar mijinki zata kasheki garama ki tsaya in kasheki ki huta.
Gadan gadan ta danneni da wani irin matsiyacin k'arfi,Da kyar nima nasamu na riko wuyanta wanda saida naga ta daina motsi hannuna Sannan nasaki.

Ihun da nai yasa duk suka dawo gabana,afirgice natashi ina fadin na kasheta na kasheta wallahi ta mutu.

Addua suka fara tofamin cikin tashin hankali kamin infara samun nutsuwa, Miyau na hadiye da k'arfi ina kallon hannuwana wa inda suke cikin na Dr. Sai rawa sukeyi.
Wani abu naji me dumi yana biyomin hanci, Kamin in kai hannu mama ta saki salati.
Shima rudewa yai" Mama jini fa.

Maidani yai ya kwantar yana gogemin hankalinshi gabadaya tashe yake.

Lumshe idanuna nai ina tuno fuskar matar tabbas nataba ganinta idan ban mantaba rasuwar ya fati hadda ita cikin wa inda sukaje gaisuwa daga danginshi na nan.

Cikin siririyar murya nace "Dr. Na kashe wata mata.

Matse hannuwa na yai kamin ya kuma sharemin hancina da jini ke fitowa" Wacece Aysha?

"Wata matace ban santaba Amma kamar 'yar uwarku ce nataba ganinta so daya rasuwar yaya fati tace itace ke kashe maka matanka kuma nima kasheni zatai,Itace taimin wa innan raunikan wai zamu mutu tare.

Tuni zuciyarshi ta karye wannan wace irin masiface wai? Rungumeni yai cikin jikinshi yana shafar bayana yayinda mama tai tsaye tana hawaye,Kaddai zargin mutane ya kasance gaskiya? Domin tasan tabbas anje gaisuwa mutane da yawa to wacece ciki?
Wacece take cutar da yaronta haka?
" Kaga Ahmad kodai gida zamu komane anemi na gargajiya? Gaskiya abun yafara bani tsoro wannan bala'in har ina?

Shigowar salim da Abba yasa sukai shiru.

Anatse mama taimusu bayani wanda yasa duk hankula suka kuma tashi,Danhaka sai Abba yace Salim yaje ya kaishi wajan wani malam muntari yaimishi bayani,Tunda yanada almajirai ko sadaka abasu Allah ya kawo iyaka.
Shikuma Ahmad din to ya maidamu gida kawai.



***

Sosai yake lallabani har yamin wanka Sannan yaimin shafa,Mama kuma na falo tana K'okarin d'aura abinci.
Zuga guda likitocin sukayo wai dubani domin babu wanda yaima magana saidai sukaga d'akin wayam bamu.


"Me kikeso yanzu?

Da kallon tausayi nabishi dan gaba daya yawani susuce har idanunshi sun fad'a lallai yana cikin jarabawa" Babu abinda nakeso Dr. amma inajin barci kuma inajin tsoron inyi inkuma ganin matar.

Zama saman gadon yai kamin yace"Karki damu zo kiyi barcinki jikina babu abinda zai sameki kumama tunda kin kasheta ai bazaki kuma ganintaba zo kiga,Saman cinyoyinshi ya kwantar dani yana shafar bayana,Kamin wani lokaci barcin yai awon gaba dani,Dan Allurar kashe radadin da yaimin tanasa barci gakuma magungunan danasha.



"Ina yarannan suke?

Har lokacin idanunta jajir suke sabida kukan da tasha gakuma damuwa.
"Suna cikin d'akin su inaga kwanciya sukayi.


Ragwaf ya zauna saman kujera yana aje ledar hannunshi" Rike nan kiga samu gora ki juyemata ciki saiki sakamata frij Allah ya kyauta,Malam yace duk sharrin miyagune bawasu aljanuba kamar yadda muke tunani, Allah ya k'ara tsarewa Ammafa yace tabbas ta kashe koma wacece,Domin idan sunso cutar da kai rikid'a sukeyi,Sai suzo maka siffofi kala daban daban,Kuma idan har kasami nasara akansu to kuwa azahirima kasamu,Idan kikai mafarkin kin kashe mage to da wuya ba itan kika kasheba Saidai idan ba kusa kukeba bazakiji mutuwarba,Haka idan kukai kokawa cikin mafarkin idan kinsha wuya haka zaki tashi da ciwon jiki to Itama abangarenta

Please Login or Register in order to submit comment