Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka ganni ka kuma nuna Ka sanni,Kasan abinda yasa na yafe maka? Yai maganar yana tsareshi da jajayen idanunshi.

Da sauri ya girgizamishi kai dan mamaki yagama kamashi na cewar da yai wai ya yafemishi.

" Nafarko sabida konace zan d'auki mataki babu amfani sabida bazata dawoba,Na biyu kuma baka kaiga cutar da baby ba Allah ya tsare ta ya kareta,Dan haka shiyasa na yafe maka.


Wasu irin zafafan hawaye ya share kamin yace"Nagod Ahmed, Inaso kaimin alfarmar shiga addininka idan ka amince,Inaso in rabu da duk abinda na mallaka sai abinda gumina yabani kawai,Kaimin wannan alfarmar!!!


Har rige rigen rungumarshi sukeyi sabida yanda abun yazomusu amatukar bazata.

A tsorace yaso ya ruga ganin yanda suka kakumeshi Amma ya kasa Sabida bugun da yasha

Duk irin damuwa da tashin hankalin da suke ciki saigashi sunkoma hira tuni sun sakashi tsakiya sabida farinciki.

Salim da kanshi ya dafamishi ruwan zafi ya gasa fuskarshi sabida kunburin fuskar tafara.


Duk wani abu da yasan zai buk'ata me muhimmanci ya d'auka suka juyo zuwa katsina.



To ba anan gizo yake sak'ar ba.

Shin wai mutun nawa ne sular kukan Ahmad din???





Wannan labari na kudine.

Acct no.
0005074141,Aisha sabiu.Ja'iz bank.


Kokuma a tuntubi wannan layi.

08142643253




Haske writer's association.
12/10/20, 2:34 PM - Naffy Aliyu Umar: 44




Da misalin shabiyu na dare suka shigo saikace korarru saida Dr. Yakai Dr. Daniel daya daga cikin gidajenshi,Sannan salim ya wuto da Dr. Din gidan.

Da kyar Abban ya budemishi k'ofar falon Sannan yashigo haushi yasa be tanka mishiba musamman daya ganshi dagashi sai treekwata saikace wanda ya dawo yawon duniya.

Lallabawa yai ya nufi bangaren ba tare da ya kuma kallon hararar da Abban kemishiba.

D'akunan duk bude,Nashi ya wuce ya watsa ruwa gami da alwala,Sannan ya nifo nawa.

Ina kwance nai d'ai-d'ai Saman gado hankalina kwance dan nai tunanin bazai dawoba shiyasa koda mama tace in kwana d'akinta nace A a nan ma zan iya kwanciya.

Saida yagama k'aremin kallo,Sannan ya lallaba ya kwanta tare da shigewa cikin jikina.


Cikin barci naji ina shak'ar numfashi me dumi sabanin na d'azu dole na bude idanuna wa Inda ke cike da barci.


Sumbatar goshina yai tare da furta Hi!! Baby"

Harararshi nai Dan sosai ya haskemin fuska da wayarshi.

Lalubata yafara aiko na fara tureshi ina kuma shagwabe fuska,Shikenan yanzu zai nemi kasheni.

"Wayyo ni ka bari dan Allah ban warkeba.


" Ah kai baby iyayen sharri Saikace wata jinya kikai? Kodai dinki akaima wajan ya isa ya warke zuwa yanzu Amma shine zakice wai baki warkeba,Kumafa daga abuja nake ko ruwa baki ban ba!!!

Turo bakina gaba Nai kamin ince"Toni babu ruwana ai tunda ba aikenka wani yayiba Sannan babu wanda kaima Sallama cikinmu sabida duk baka d'aukemu da muhimmanci ba.



"Shhhhh!! Haba baby ya zakice haka?

Kinsan su mama zasu hana ne shiyasa ban gayamusuba Sannan kema idan na gayamiki zaki iya sanar musu shiyasa kawai nai shiru Amma kiyi hakuri suma da safe zan basu hakuri OK?


Saka hannunshi yai cikin rigata yana taba abinda yafi d'aukar mai hankali,Bansan na lumshe idonaba sabida yanda sakon daya tura ya isa nan take.

Muryarshi can k'asa naji maganarshi yana fad'in" Babyna inafa jin yunwa zan kwana da yunwa fa.

Bakina na tsuke kamin nace kayi hakuri to kasakeni saina samo maka abinda zakaci.

Kuma makale ni yai cikin jikinshi yana sumbatar bakina"No baby barni inji duminki dan Allah nai missing dinki irin sosai dinnan.


Irin matsar da yaimin yasani kasa ko motsin kirki wani irin tsorone ya tasomin ganin ya kashe hasken wayar.

K'arfin da Allah yabashi yasamin dan tunaninshi zuwa yanzu nasaba dashi.

Nai kuka Nai kuka hadda Allah ya isa Amma bai kyaleniba Saida yaji yakai matakin da dole zai kyalenin Sannan ya rungumeni yana samin albarka gami da jijjigata.


Duk yanda yaso intashi muyi wanka k'i nai Dan yana fara damuna nasaka kuka dole ya rungumeni, Saida yaga nai barci.Sannan ya tofeni da addua yatashi ya gyara jikinshi,Abincin da be nemaba kenan.




***

Tunda ya kwanta yaketa nanata kalmar shahada wani irin dadi da nutsuwa yakeji wanda keta hauhawa cikin zuciyarshi,Beyi Dana sanin kasancewar Ahmad abokiba tunda gashi ta sanadiyyarshi Allah ya kubutar dashi,Saikuma yake kuma tabbatar da halarci na musulmi lallai bayajin zai iya abinda Ahmad din yayi wato yafiya akan duk wanda Yakama da binshi da irin wannan mugun sharrin.

Fatanshi ya wayi gari lafiya domin ya zama cikakken musulmi Yasan koda danginshi sun juyamishi baya to yanada tabbacin Ahmad bazai juyamishi baya ba.

Kuma muskutawa yayi yana tuno budurwarshi Jessy wadda sukai Alkawarin aure,Yasan yanzu maganar dole zata watse.
Watsa hannunshi yai akan kirjinshi duk tunani yagama addabarshi,Musamman daya kwanta dinnan domin ya huta.





"""***"""

Nai Tunanin zan tashi da wani ciwon Amma sainaga natashi k'alau dani.

Duk Inda nai mayun idanunshi na kaina yana bina da wani kallo na k'asa k'asa,Yayinda nikuma duk nagama tsarguwa kunya na Neman kayar dani.

Cafkoni yai yana dariya ganin na nufi kofa zan fice"Haba baby zo mana ina zaki?

Baki na turo kamin nace"Ni babu Inda zani zanje wajan mama ne in tayata aiki.

"Rikomin hannuwa yai ya sumbata kamin yace" Muje Saina kamamiki Amma da naso ki kwanta ki huta aysha ta.


Tare muka nufi falon,Maman ma bata fitoba danhaka tare dashi muka fara had'a abinda za a karya dashi duk da dai bawani abu yakeminba Ammadai yana tsaye yanaban labarin abinda yafaru jiya da sukaje abujan.

"Amma Dr. Kana ganin babu matsala? Kaddafa kaje ku amince mishi ya yaudareku?


" Karki damu insha Allah babu wata matsala damacan ya jima yana sha'awar addinin lokacin shigarshi ne dai sai yanzu yayi,Anjima idan Abba ya fito zan yimishi bayani sai asan yanda za ai dashi,Gakuma uwar dukiyarshi dayace beso aikin kanshima yace transfer zai nema zuwa nan.


"To Allah ya sanya Alkhairi ya tabbatar dashi akan hanyar gaskiya.


" Yauwa babyna Ameen nagode miki Allah yaimiki albarka, Yanzu kina had'a abincin dashi ko? Dan yanzu zanje in d'aukoshi anan zai karya.

Turo bakina gaba nai ina yamutse fuska.

Sumbatar bakina yai yana dariya"Haba mana autar mata ,Bak'onmu nefa?

Rike bakina yai cikin nashi duk mutsu mutsuna besa yasakeniba.
Asama mukaji muryar mama na fad'in "Subhanillahi kai Ahmad gaban wuta?

Da sauri ya sakeni ya koma jikin frij yana maida numfashi, Yayinda nima nai gefe ina Jan numfashi.

Saida ya daidaita kanshi sannan yafita yana gaisheta,Daganan ya wuce bangarenmu da alama shiryawa zaiyi,Nan ya barni da jin kunyar mama musamman datafaramin fad'an " Ke aysha mezaisa ki biuemishi gaban wuta kinaso ya jefaki cikin wuta ne?

Nidai samu nai Na kammala,Sannan na lallaba na nufi bangarenmu.

Yana zaune gefen gado dagashi sai k'aramin tawul da alama da wani yake waya wadda ta danganci aiki.

Wani mayen kallo yabini dashi yana lasar Lib's dinshi,Jinai kamar in koma balle danaga yana wani mikomin hannu alamar in zo gareshi.

Kan cinyoyinshi ya zaunar dani yanacigaba da wayar tare da shafar gashin kaina wanda na fara tsefe shi.

Ajiye wayar yai yana kamo jekar gashina "Baby kitsonki ya tsufa gashi maman katsina tace bakison kitso ya za ai kenan?


Zubamin ido yai ganin ina hawaye" Baby meya faru?

Sakin kukan nai gaba d'aya "Kace zaka kaini gida Amma har yanzu baka kainiba dan Allah ka kaini zan dawo kaji?

Cikin kirjinshi ya sakani yana shafar bayana" Shikenan naji jibi juma'a zan kaiki shikenan ko? Amma banso inga kina damuwa bazanso ganin kukankiba gimbiyata kadda ki dinga azabtar dani da kukanki kinji ko?

Turo bakina gaba Nai ina harararshi"Ba wani nan ko jiya ba saida kasani kukan ba?

Dariya yasaki yana sumbatar cikin kunnena"Baby ai wannan kukan irinshi akeso shidin abin sone danhaka ba irin wannan ake guduba ko yanzuma wani zan saki dangaskiya inaso ,Kuma kema Inda kinsan abinda nakeji da kin dingajin tausayina kina jawoni ki bani koda yaushe.


Rikon da yaimin yasa dole na biyemishi,Saida ya gama Sannan nasamai kukan sangarta,Kamar yadda yace.


"Ban boyemikiba aysha tun farko saida na gayamiki inada yawan buk'atar mace,Danhaka k'okarin sabawa dani zaki fara kinji ko?


Lamo Nai jikinshi ina share kwallah,Yayinda cikin zuciyata nake tsara yanda zan ki dawowa gareshi idan har ya kaini gida.


Barci ya kwasheni batare sani ba,shiko wanda yai be wuce na 'yan mintinaba,Yatashi ya gara jikinshi ya fice.



""""


A kintse ya tadda Dr. Daniel yana jiranshi,Shiyasa kawai yana zuwa ya d'aukeshi suka yo gida sabida yanaso ya had'ashi da Abban asan yanda za ai dashi.
Kiran salim yaketayi Amma saidai ta gama ring ta yanke batare da ya d'agaba.
Wani uban tsaki Dr. Din yasaki kamin yace"Shege idan an bibiya yanacan bayanta kwance ko wayar ya kasa d'auka.

Dariya Daniel keyi hadda hawaye,Tsagaitawa yayi ganin wayar Ahmad din na ring.

"Dallah kai wane irin mugun bak'auyene ina ta kiranka Amma ka kasa d'auka,To indai mutun ya girma to wallahi Yasan ya girman haba!!! Cike da fusata ya idasa maganar yanajin yanda salim din keta sakin dariya.

" Kaga dallah Sauraramin kai wane irin mugu ne ? Jiya ka hanani kwana da iyalina nufinka yauma bazaka barni in hutaba? Dan Allah ka kyaleni haba mutun sai bak'ar masifa saikace makaho.

Ashar ya dannama salim din kamin ya ajiye wayar,Yana huci.

Shidai Daniel na gefe yana murmushi abotar salim din da Ahmad na matukar birgeshi.




****

Sosai Abban ya fahimci bada wata manufa yakeson shiga addinba Allah ne ya shiryeshi kawai ta wannan hanyar,.


Shigowar salim cikin falon yasa suka kai dubansu gareshi,Saida ya gaida Abban sannan ya mik'ama Ahmad da Daniel hannu wanda murnarshi ta kasa boyewu an bashi hannu duk saida suka fahimci hakan.


"To Alhamdulillah Allah shine abin godiya,Kai salim da Ahmad kutashi ku wuce wajan aikinku dannaga kwanakinnan iya shege kawai kukeji,musamman kai Ahmad wallahi ka kula aikinka amanarka ne kaji ko?
Ku wuce ni zan kaishi wajan malam hasan yanzu afara d'orashi bisa hanyar abinda yadace,Maganar dukiyarshima data kasance ta haram to itama za asan yadda za ai da ita,Kudai bar komai hannuna tunda ni ba uzurine gabanaba kamar ku kunji ko?
Kutashi ku sannayi.


Marairaicewa dr.yai kamin yace Abba nifa ko karyawa banyiba wallahi!

" Harararshi yai tare da nunamishi wajan abincin da hannu.

Anatse sukaci abincin hadda salim wanda saida ya ciko cikinshi gidanshi Amma ganin na nan saida ya k'ara.

"Kai nifa har yanzu banga madam ba ko bata tashi barcin gajiyaba?

Saida ya saki murmushi kamin yace" Wallahi kazama d'an iska salim to bata tashiba.

Daniel yai dariya"Gaskiya koni ban gantaba .

"Kai kyaleshi wulakacine kalar nashi tunda be gantaba aiyasan bata tashiba,Kuma wannan abincin daka loda ita tayi shi balle kacemata Raguwa.


Da wannan barkwancin suka rabu,Inda sukabar Daniel nan tare da Abban suna hira.



""
Saida naj barcina na tsire Sannan natashi,Baki kawai na wanke na nufi falon mama dan yunwa nakeji.

Ban tadda mama ba Sabida ta nufi wajan adduar kausar yau.


Gaida Abba nai Sannan na gaida Daniel wanda yakasa ko d'aga kanshi ya kalleni kamar dai mai jin kunya haka.

Juya musu baya nai nayi Karina anatse Sannan nakoma bangarenmu nadaiji tashin motar Abban daga baya.



Wannan labari na kudine ki tuntubi wannan lambar domin siyen naki akan farashi me sauki Naira 300 kacal.
08142643253.



Cikin kwanaki biyunnnan da suka biyo baya nasha wahala hannun Dr. D'an hakurin da yakeyi gaba daya ya daina kuma sakin jikinshi yakeyi sosai ya murjeni,Gabadaya nai 'yar fuska,Ammafa jikina ya sauya na kuma haske fatata har wani sheki takeyi,Ramar ma jikina beyiba sai fuskata.

Yana tsananin kulawa dani,Abinda nakeso shi yakemin haka idan na nuna banso to ko yanaso hakan hakura,Matsalar dai kawai buk'atar shi da yake matsamin da ita,Nakuma lura hakan ajininshi yake,Da farkonedai ya dinga d'an tausayamin,Amma yanzu duk yanda zan nuna banso bema saurarena saiya gama ya lallasheni.



Kayana na kintsa cikin k'aramar jaka,Shidai yanata bina da kallo Amma beyi maganaba hasalima chart yakeyi da wayarshi.


"Nagama shiryawa Yaya"


Dariya yasaki jin yanda na canza mishi suna sabida wahala,wajan kwana uku kenan nafara kiranshi da Yaya wanda Yasan matsamin din da yayi ne yasani canza mishi sunan.
Rikoni yai yana murmushi.

"Wai yaushe na zama yayanki ban saniba?

Cikin shagwaba nace to nidai wallahi kai yayana ne,Dan Allah katashi muje kai wanka ranafa zatayi.

Lumshe idanunshi yai yana lalubar bakina,Saida yagaji dan kanshi Sannan ya sakenj ya wuce yin wankan.

Wata ajiyar zuciya wadda Bansan ina rikontaba nasaki tare da zamewa na kwanta ina shafar lebunana.




Cikin kwana biyunne dr.Daniel ya Amsa sunan abubakar saddiq wanda yanzu ya amsa sunan cikakken musulmi Inda Abba ya zama kusan mahaifi agareshi,dan shine komai nashi,Dukiyarshi tas aka rabar da ita yanaso idan Allah ya dafamishi yasake sabon zubi,Babu wanda Yasan ya musulunta daga danginshi saidai 'yan tsirarun abokai,Shiyasa har yanzu hankalinshi yake kwance,Wajan malam hasan yake yini yana kuma fahimtar dashi addini kamar yadda aka tsara.




Saida yagama yimin wulakanci,Sabida yaga na matsu da yin tafiyar Sannan ya fito muka isa falo dan yima su mama Sallama.


Tsarabar da zankai gida tabashi yakai mota Sannan mukai Sallama cike da farinciki.





Haske writer's association.
12/10/20, 2:34 PM - Naffy Aliyu Umar: 45




Saida tafiya tai nisa Sannan ya riko hannuna fuskarshi sam babu walwala,Shiyasa na kame kaina tunda Bansan abinda ya bata mishi rai ba.

Inajin yanda yake murzar hannuna kamar wanda akaima umarnin yin hakan.
"Babyna dan Allah basai kin kwana ba zuwa yamma kawai mu juyo mu dawo gida abinmu ko?

Wani irin mugun murmushi na saki kamin in d'agamishi kaina banso ma inyi magana balle in fadi wadda zata batamishi rai yafasa maidani na gwammace inyi shirun tunda na lura Neman fitina kawai yakeyi.

Cigaba da magana yai" Kinga inajin kunyar su maman kano bazan iya kwana wajansuba,Sannan bazan iya barci ba idan banjiki cikin jikinaba kinga Ai zan iya samun matsala ko? Amma idan muka koma gida shikenan hankalinmu kwance ko?

Kaina nakuma d'agamishi yayinda cikin raina nake nanata rainin hankali irin na shi watoma mu dawo yau? Lallai zaiga tsiya.

Duk da cewa yai mamakin amincewar da nayi da wuri Amma hakan besashi k'in jin dadi ba sabida amincewar da nayi.

Barci ne ya kwasheni batare da nasan zai zo dinba.

Kwanciya ya gyaramin a jikinshi Sannan yacigaba da tukinshi wanda lokaci zuwa lokaci yakan sumbaci kaina dake kan cinyarshi.




***

"Naje gidan Ahmad so uku kenan Amma bansami nasara akan matarshi,Dan haka ki canzamin da wata amemakonta dan ina buk'atar sabon jini jikina babu dadi.

Waigawa tai ko ina cikin d'akin kamin tace " Da dai za ai hakuri to tabbas da matar tashi Zaifi dadi domin itama yarinya sharaf da ita,Amma tunda abuk'ace kake to yanzu zan fita insamo wanda zanbaka daga baya Saika koma can din domin shan natan.


Zaninta ta d'aura aka ta fice tare da jawo d'akin ta d'auki wata roba da ragowar Abincin dabbobi ke ciki,Saida ta juyeshi Sannan tai gaba da robar ahannu tana gayawa almajirin dake mata ayyuka wai tatafi Neman dussa.

Can nesa da unguwarsu ta bulla,Yayinda taketa watsa idnunta ko ina domin ganin tasamu abinda tafito nema.


Wani gida da taga yanada yalwar yara ta nufa,,Ta kwad'a sallamarta kai kace mutuniyar kirki ce.
Duk matan gidan na tsakar gida suna hira yayinda yaran gidan keta wasanninsu gefen iyayensu.
A mutunce suka gaisa kamin tace Dan Allah dussa nake nema har sari ma inayi idan kuna saidawa.

Daya daga cikin su ce tace"Aiko bamu ajiyar dussa nan gidan sabida muma munada dabbobin saidai ki tambaya gaba.

Idanunta nakan yaran ta juya ta fice tana fadin to shikenan na gode Sai anjimanku.


Sauke numfashi wata siririya tayi"Uhum inada dussar wallahi niyyar saidawace banyiba danni wannan matar bataiminba yawancin irin tsoffinnan wallahi duk mayune saisu fake da Neman dussa ko saida daddawa daganan ai ram dakai.

Suna nan suna wannan hirar,Dayake sanadin gidansu yake ,Wata matashiya tazo shigowa tai karo da tsohuwar itakuma zata fita.
Sosai suka bigi juna duk da cewa yarinyar taso kaucema tsohuwar,Bata tankamataba ta fice gidan yayinda yarinyar ta bita da kallo tana bata hakuri.


Idasa shigewa gidan tai tana fadin"Mama me kukaima tsohuwar can tafita batako kallon gabanta kunga yanda ta bangajeni kuwa? Wallahi kaina har ya Sara.

Wannan magana itace ta k'arshe ga wannan yarinya dan tuni tsohuwar tai ram da ita.


Kwanciyar da yarinyar tayi daganan Allah ya saukar mata da matsanancin ciwo wanda tsohuwar tazama itace sila.

Wannan tsohuwar?????



***

Ba k'aramin mamaki naiba danaji yana shafar fuska ta Wai intashi munzo.
Mik'a nai jikinshi Sannan natashi zaune ina yamutse fuska,Ganina kofar gidanmu yasani idasa wartsakewa,Ina k'okarin ficewa daga motar.



Rik'eni yai da k'arfi Yana hararata"Ke Bansan shirme ki tsaya mufita tare mana.

Cikin shagwaba na turo bakina gaba ina harararshi,Jikina har Wata tsuma yakeyi tsabar yanda nasa rai da ganin mutanen gidan.

Basar dani yai cikin motar Yakama waya,Yayinda nacika nai FAM ina harare-harare,Fitowar Abba daga gidan yasashi saurin yanke wayar ya bude ya fito nima na fito,Da gudu na k'arasa wajan Abba ina makaleshi.

Cike da farinciki ya rikeni Yana dariya oyoyo JARUMA,Sannunku da zuwa Ahmad tafiya babu sanarwa haka?

Sosa kai yai yana duk'e gabanshi sabida kunya.

Sakin Abban nai Na nufi ciki bakina har k'eya bama kunneba.

Ita kanta mama murnar takeyi bakinta yaki rufuwa balle dataga yanda nakoma dama Kuma burin kowane iyaye kenan,suga kwanciyar hankali ga 'ya'yansu.

D'akina na shige na haye gado dan sosai nakejin yanda nai mugun kewarshi,Yayinda su mama suka bini da dariya,


Shima Dr. Nan falon mama yai zamanshi duk da Abba yaso yaje falonshi Amma yace nan ma ya isa babu matsala.

Mama ficewa tai dan kammala girkinta yayinda hira ta barke tsakanin abba da dr.din.

Lambar zainab na lalubo na dannamata kira dannasan babu Inda zataje daidai wannan lokacin.

"Ke dallah ki sauri kizo ganinan gida yanzu mukazo.

Ihu ta saki itama,Kamin tace" Wayyo 'yar uwa ganinan tafe dama har mafarki nai wallahi ganinan zuwa.


Ina nan nai lamo inajin hirar su Abba sama sama,Saiga zainab din ta fado tana ihun murna.

Dak'uwa Abba yai mata kamin ya d'ora da fadin kufa har yanzu baku da hankali banda hauka mene amfanin wannan ihun kundai girma yanzu ai.

Gaishe da Dr tai ta wuce bakinta har kunne ko damuwa da fadan Abban batai ba.

Rungume juna mukai muna murnar ganin juna.
Tundaga lokacin babu wanda yakumajin d'uriyarmu tsabar hira.

Tare da Abba suka wuce masallaci,Kamin su dawo mama ta gama shirya Inda zasuci abinci.

Sai lokacin zainab ta wuce akan zataje tai wanka ta dawo muje gidan wata k'awarmu data haihu kamin infara ziyarar da zanyi.

Dadin jikina naji da Nai wankan Sannan nai sallah.

Wani lafiyayyen kunun aya mama ta ajemin babban Kofi wai na shanye duka,Yamutsa fuska nai ina tunanin ta yanda zan iya shanyeshi,Saidai ina fara d'andanashi naji wani masifaffen dadi Bansan na lumshe idanuna ba saida naji dariyarta,Saman kaina "Kai mama Wallahi ban iya kalar wannan ba.


" Eh nasani Amma zan koyamiki kamin ki wuce wannan na musamman ne.

Har k'ure cikina saida nayi kamin intashi inbar wajan.


Kusa cin karo nai dashi yafito daga falon Abba Yana waya.

Manyan idanunshi ya fiddo tare da cafkoni yana waigen bayana"Ke baki da hankali ina zaki kikai wannan gayun?

"Nifa gidansu zainab zanje sai ta rakani injema sajida barka jiya akai suna saina taho da naman suna na.

Dariya yasaki kamin yace" K'arfin hali wato ke kika haihu ko? To babu Inda zaki danni bawai yawo nakawoki kiyiba.

Rungumeshi nai bayan

Please Login or Register in order to submit comment