Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yagama shiryawa.

Yana zaune da wayarshi ahannunshi da alama wani amfani yakeyi da ita,Ganin yanda hayaki ya rufe d'akin yasashi zubamin ido da alamun kallon tambaya yakebina dashi.

Kauda kaina nayi nai kamar banga kallon da yakeminba na matso har gabanshi dan shima ya shak'i hayakin,Saida naga yafara tari Sannan na matsa ina kunshe dariyata.


Bedaice komaiba nima kuma banyimishi bayanin komai ba.


Ledar daya shigo da ita d'azu na d'auko tare da d'an budewa ina leko dadin dake ciki dannifa tun d'azu miyan bakina yake katse.

Marairaicewa nai ina kallonshi,Ganin yaki cewa inci tun d'azu.


"Meye kika tsareni da ido ne ? Kazar amarci ce idan kin shirya,Zaki iya cin abarki ki k'oshi.

Miyau na hadiye dan na fahimci inda maganar tashi ta dosa,,Basarwa nai tare da fara yagarta ko mazubi ban nemaba.
Saida nai taf da cikina sannan na d'ora da lemo ina lumshe ido.

" To Alhamdulillah naci na koshi Saura barci kuma.

Bedai kalleniba Saima gyara kwanciyarshi da yai,Wucewa nai na wanko bakina nadwo na tsallakeshi nakoma can k'arshen gadon Sannan na kwanta.

Anutse na karanto adduar Neman tsari Sannan na lumshe idanuna.



**

Duk irin yanda yaso ya daure kasawa yai dan kwanciyar da yai kusa Dani batawani wadaceshiba.
Ahankali ya matso tare da mannewa cikin jikina dan akwai tsoron abinda yafaru jiya cikin zuciyarshi.
Numfashi ya sauke tare da shigewa sosai Dan har saida naji rikon cikin barcina.

Shigar iska cikin munnena yasani far kawa daga barcin da nakeyi.

"Nakasa barci baby tashi ki temakamin dan Allah.

Yamutse fuska nai kamin ince" Dr.me zanyimaka cikin darennan dan Allah?

"Tashi zakiyi muyi hira,Sannan kiban labarin hayakin da kikai min d'azu ko so kikeyi ki mallakeni ne?


" Kajika da tsirfa dan Allah!! Sabida Allah cikin tsakiyar darennan zanbaka labari? Kuma mezan mallake anan kana fama da wahala,Daga gani aljanace ta aureka,Ni matsa barci zanyi.

Mannamin Sumba yai gefen kunnena saida naji wuta ta d'aukemin nawani lokaci Sannan nadawo daidai.
"I LOVE You my lovely baby"

Tsitt nai ina jin yanda bugun zuciya ta ya tsananta,Bazance banji dadin jin Kalmar ba saidai tazomin abazata dan banyi tunanin samunta nan Kusa ba.

"Nifa kabar cemin baby.

" Naki din ke din babynace kuma masoyiya idan kikabani dama zan maidaki kamar jaririya dan kulawa dan Allah ki amince mu zama Abu d'aya Aysha.,Amma bazanyimiki doleba duk lokacinda kika amince INA maraba dake,Ammadai gayamin turaren me kikai min ?

Dariya nayi kamin ince"Duk kabi ka damu hayakin korar shaidanune dan kadda yauma su dawo sukuma jimaka ciwo.

Murmushi yai Yana kuma nanik'ata"Wallahi nasha wuya jinai an shakeni fa inaga aljanunki ne sukazo zasu kasheni.


Murmushi nai kamin ince "Humm kaidai fadi gaskiya aljanunka dai wa inda basuso ka rabi kowa.

" Da gaske nake baby banda wasu aljanu kawaidai bansan abinda ke damunaba Allah,Kinga yanzu buk'atarki nakeyi amatsayinki na halalina Amma gefen zuciya ta inajitsoron kasancewa dake,Banso in jawomiki matsala.


"Bawata matsala dr.hakkinka na kaina nasani so bazanyi wasa dashiba,In kana buk'ata babu matsala indai ka cutar danine zance ban yafe ba.


Dariya yasaki Yana haskeni da wayar dake hannunshi" Aysha yanzu na tabbatar da cewa kedin k'aramar yarinyace, Yo inba hakaba kinsan abinda kike fadi kuwa? Nauyina zan doramiki fa?


Turo baki na gaba Nai kamin ince"Ni wallahi ba yarinya bace tunda gashi harka aureni,Kumama ko mene aidai nasan bazan mutu ba ko?


"Eh hakane bazaki mutuba Amma zakiji ajikinki danni ba saukine daniba,Amma baby meyasa bakijin kunyata ko nauyin gayamin magana ne ko duk cikin tsanar da kikai minne? Dannasan tun lokacina da marigayiya bawani sona kike ba ko?

Matsawa nai can k'arshen gadon na lullube,Dannaga so yakeyi saimunyi fada dole kamin muyi barci ni bammaga amfanin zuwana d'akinshin barci ba saikace wata 'yar iska.


Lamo yai shima Yana tufka da warwara lallai aysha da wayonta saidai har yanzu Yana hango tsiwarta,Sannan har yanzu bama ta d'aukeshi matsayin miji ba,Idan ya fahimta daidai to zaigane cewa k'okari takeyi naganin ta sauko hakkokinshi dake kanta.
Idonshi ne yakai kan labulen window Wanda iska keta kadawa,ahankali yake ganin yadda wata doguwar inuwa ke kai da komowa kamar irin zaka shiga gida amma kuma ka tadda an kulleshi dinnan.

Rufe idanunshi yai yakuma budewa aikuwa inuwarce daga gani ta dogon mutun ce Amma be isa yagane inuwar mace ce kota namiji ba,Sabida yanda akai kamar ansa rigar sanyi me hula.

Lumshe idanunshi yai Yana kuma addua cikin ranshi domin yasa koma menene addua da wannan hayakin ya hanashi shigowa balle ya cutar dasu,Sai yanzu ya tuna da maganar da Fatima ta taba gayamishi cewar akwai wata inuwa dake yawo cikin gidan idan benan tun batajin tsoro harta fara tsorata.
Matsawa yai jikin ayshan tare da makalkaleta Yana shak'ar k'amshin gashinta.



***

Wannan karon komai nema yake ya lalace mana bansan ya akai hakan ta kasanceba,Idan mukai wasa wannan yarinyar saitayi sanadiyyar tonon asirinmu Wanda mukai shekara da shekaru muna boyewa.


"Wannan magana dakai gaskiyace to yanzu menene mafita? Dan gaskiya yarinyar shaidaniyace kallon kowa take kar.


"Shawara akan kawai asami wacce zataje ta kai wannan kullin cikin d'akinta idan shirirta tasameta ahaka zamu aiwatar da nufinmu kundai San bamu k'adai bane ke buk'ata idan har muka nawata to rabon wasuce ba tamuba.

" oga ka kawo shawara Abar wannan aikin ahannuna nikuma zansan yadda zanyi.
*Sirrin* *boye*



Bayan sati daya.

Tuni nazama 'yar gida dankuwa dama ni bani da irin bakunta dinnan, Nikeyi mana girki kuma har d'akin maman ina gyarawa to gidan babu mutane da yawa shiyasa aikin gidan ma beda wani yawa, iyayenshi na matukar kulawa dani,Shiyasa nakejin dadin zama dasu.

Tsakanina da oga kuwa sai sabani kusan kullun saimunyi fada dashi,Wanda har mama saida taimana fada musamman shi tunda shine babba Amma bebar takalataba Wanda ni kaina nafara tunanin kila dadi yakeji idan yaga munyi sama dashi.



Tsaye yake gaban mirro Yana d'aura agogonshi,Amma idanunshi na kaina nikuma danake fuska hade dan kuka ma nagama,Sabida murdemin hannu da yayi.

"Zoki fesamin turaren zan wuce.

Saura kirin in fashe haka na nufi gabanshi na fesamishi turaren batare danako kalli inda yakeba,Yayinda shikuma yake jin duk babu dadi ganina cikin damuwar,Gashi kuma nakasa musa mishi akan umarnin daya bani,Abinda kekuma tsananta soyyayarta cikin zuciyarshi shine rashin gardama da biyayya dan ko wane kalar fada zai shiga tsakani indai zai ce zokiyi kaza to zatayin koda ranta abace yake.

Hannuwana ya riko yana k'okarin ganin mun hade ido Amma nikuma saina kuma sadda kaina k'asa inajin wani qullutun bakin ciki da ke tasomin daga zuciyata,Dama nasan zamana da Dr. Ba wani dadi zaiyiba kawaidai dan kadda in sabama iyayenane.

" Bazaki kalleniba Baby menai miki?

Jinake kamar in shakeshi innaji yana cewa babyn nan saikace wata sabuwar haihuwa.
"Shikenan ni zan wuce jirana akeyi idan sun iso ki kirani zan dawo kinji ko?

Adawo laifiya nai mishi kamin in zauna bakin gado nasaka kuka,Trolydina na jawo na shirya kayana tsaf wa inda zantafi dasu dan yau dinnan kano zan kwana saidai duk abinda zaifaru ya faru.



Muna cikin aiki nida mama na abincin da zamu tari yayuna dashi saiga wata budurwa ta shigo mesuna asiya,itama diyar k'anin mahaifin Dr. Ce.

Gaida mama tayi amma ni ko kallona bataiba,To nima dama raina abace yake shiyasa bammabi ta kantaba.

" Bakiga matar yayanki bane asiya?

Saida tawani yatsuna fuska kamin tace"Naganta mama ai ita yakamata ta gaidani tunda na girmeta.

Kallo d'aya naimata na d'auke kaina inacigaba da juye lemon danagama hadawa na abarba dan nasan 'yan gidanmu ciki dabai komai munfison na gargajiya mu hada abunmu da kanmu.

"Ni matsalata daku rashin kunya asiya idan kin girmeta aikuma matar yayanku ce kuma dole taci wannan darajan danhaka bansan shirme ki gaidata nace"

Saida ta wani bata fuska kamin tace wallahi mama saikisa ta rainamu idan kinamana haka Ammadai ba komai taci darajar yayan, Morning.

Wani uban tsaki nasaki amemakon amsawar kamin in fice daga kitchen din nakoma falo na zauna tare da d'aukar wayata dan kiransu inji sunzo INA yanzu dan insamu inyi wanka in shirya.


"Kingani ko mama?

" Dan Allah ni kyaleni duk bakune kukeja ba? So kukeyi dole saita biyemuku anta masifa,Komai ya k'ara lalacewa ko? Inba hakaba ina ruwanku da ita? To wallahi duk bazakuji dadiba idan Babana yaga wannan abun da kukeyi kundaisan hali idan kukashiga gonarshi.


Ina waya tadawo falon itama,Inagamawa na tashi na wuce bangarenmu batare da ko kallonta nayiba.

Cikin 'yan kwanakin danayi na lura da cewa kusan duk 'yammatan family's dinsu Dr. Din sonshi sukeyi kawai dai akwai dalilin dake hanasu nubawane kokuma dan basu ganin fuska wajanshi dan naga ko gaisuwarsu bacika amswa yakeba.
Mitsw toma ni ina ruwana dasu daduk zasu wani samin ido imma cinyeshi zasuyi karewar so meya dameni.


Anatse nai wankana tare da yin kwalliya abinda bantabayiba tunda aka kawoni gidan ,Iyakata hoda.
Nai kyau sosai dan dama Allah yaimin baiwarshi,Idona yasha kwalli ga k'aramin bakina dayaji jambaki Wanda yadace da shigar less din danayi.

Jin shigowar mota yasani zabura na fesa turare na nufi falo.

Da Dr. Nafara cin karo hannunshi d'auke da abulkhairi yaron ya maryam.

Ina ganin yanda yai wani iri daya ganni kamin ya idasa shigowa idanunshi kamar zasu fado tsabar yanda kwalliyata ta bugeshi,To gaskiya banga laifin shiba dan koni nasan nayi kyau ba d'an k'aramiba.

Da guduna na k'arasa ina tsallen murna tuni gyalen dana yafe kaina ya sauka dan dama jiya nai tsifa sonake ya safiyya taimin kitso yau kamin su tafi.
Da sauri mama tafito bakinta awashe tanamusu sannu da zuwa kamin ta amshi yaron hannun Dr. Din tanafafin"Kai aysha memakon kice su shigo su zauna kuma saiki makalesu abakin kofa? Sannunku da zuwa Ku shigo mana sannunku da hanya.


Jinai kamar insaka kuka ganin yanda Dr din keta hira dasu bansan lokacinda wannan sabon yashiga tsakaninsu ba,Ko da zan shiryamusu abinci shima tayani ya rink'ayi kawowa falon.
Shigarmu ta k'arshe kitchen dinne ya matseni jikin bango yana kallon cikin idanuna "Wato ni kika raina kikema fushi ko? Gashinan yanzu kinga su Yaya saiwani Washe baki kikeyi ga kwalliya kinsha nikuma baki taba tunanin kiminba ko inaso ko?

Idanuna tuni sunciko da hawaye dan sosai ya matsane"Kafi kowa sanin cewa auren dole akaimin bawai sonka nakeba,Amma hakanan na jure sabida inyi biyayya ga iyayena insami lada ko? To Amma kai kanaganin kamar dolene zama da kai,To zanbi 'Yan uwana yau inkoma gida dan bazan iya cigaba da zama dakaiba dama daurewa nakeyi Amma abubuwan da kakemin sunyi yawa bansan ma'aunin da zan ajiyesuba tsabar kiyayyar da kakeminne kokuma kai kalar salon soyayyarka ne haka to bandai saniba kuma ban fatan sanin,Danhaka ka kwantar da hankalinka zan barmuku gidanku dan Wallahi yanzu abinda kakemin banda tsanarka babu abinda yake k'aramin.
Da k'arfi na kwace daga rikon da yaimin na wuce falon ina k'okarin maida hawayen dake niyyar zubomin.

Cikin tsananin tashin hankali da damuwa ya wuce bangarenmu yana nanata duk kalaman da nagayamishi,Lallai Ashe yanada aiki kenan.


Tuni nasake cikin 'yan uwana inata murna,Yayinda suma ta bangarensu duk hankalinsu ya kwanta ganin yanda nakuma canzawa daga gani bani da wata damuwa.

"Wai Yaya sadiya memakon Ku taho da yara saikuka taho Ku kad'ai!!

" Hahhha kirki damu Aysha Abba yace idan ansami hutun makaranta da kanshi zai hadomiki kansu ya kawo tun safe har yamma.


Saida akai Sallar azahar Sannan mama tace mu koma bangarenmu muyi hirar can,Dan dama tuni an kaimin kayana wa inda sukazomin dasu Sauran tsaraba kuma mama tace akai kitchen dayake anyi sa'a usman yana gida yau.

Duk saida suka watsa ruwa Sannan muka dasa hira jinake kamar naita kwarara ihu sabida farinciki.

Tsarabar kayan k'arshi dakuma magunguna na mata suka kawomin masu kyau da inganci domin kamin auren komai mama bata yarda anyiminba wai sainaje nakwana biyu tukunna.

Duk adanasu nai Sannan mukacigaba da hira,Jinake kamar mu dawwama haka bansan nayi kewarsuba sai Yanzu Dana gansu.



Sunayin Sallar la'asar sukafara shiri dan Abba ma cewa yai k'arfe uku su juyo.

Mama ta had'amusu sha Tara ta arziki,Lokacin Abba ya dawo sunata fira da kanshi yasa usman yace ya maidasu katsina dan dama shatar ta haya sukayi wajan zuwa gadai motocin Amma babu wacce ta iya tukin.

Ganin nafito jaye da akwati yasa duk suka zubamin ido yayinda dr.ya mike tsaye tare da yowa wajena kirjinshi na tsananta bugawa.

Abba ne ya matso Kusa dani yana kallona"aysha ina zuwa da jaka kuma?

"Abba gida zani binsu zanyi,Ni bazan zauna dashi ba.

Kallon tuhuma sukabi Dr. Dashi,Yayinda shikuma ya sadda kanshi k'asa " Abba wallahi banyimata komaiba.

Lallashina sukafara yayinda na tubure saima kuka danasaka dan sosai nake jin bansan zama nan din.





Wannan labari na kudine ,Biyan Dari uku shizaisa kasami kisami naki.

Acct no
0005074141,Aisha sabiu,Ja'iz bank.

Mtn Cart.
08142643253.



Haske writers association.
12/10/20, 2:30 PM - Naffy Aliyu Umar: 32



"Zonan diyata gayamin meya faru ko kunyi fada ne? Cewar Abba cikin sigar lallashi.

Fuskata cabe cabe da hawaye nace Abba ni bazan zauna dashiba kullun saiyaci zalina hankalinshi ke kwanciya dama ai bawani sona yakeba.

Bansan maganar da nai me wata manuface da ban ba saida naga duk kunya ta kamasu sannan na fahimci tunanin da sukai shi kanshi Dr din ya sadda kanshi k'asa yana shafar kanshi.

Da alamun kunya yafara magana" Kinga to kiyi hakuri kibari sutafi idan be dainaba da kaina zan kaiki gida kinji ko?

Ihu nasa tare da zamewa na zauna.

Kallo daya zakaima Dr kasan hankalinshi amatukar tashe yake balle yanda ya lura da kallon tuhumar da iyayenshi ke mishi,Ga wannan kunya ta tonon sililin da taimishi Wanda yasan duk tunanin da zasuyi shine matsamata yake da buk'atarshi shiyasa har take Neman guduwa.

Ya halimace ta matso wajena tare da zaremin ido"Tashi ki wuce dan gidanku kuma tunda haka zaki dingayi babu Wanda zaikuma zuwa wajan ki tashi kona cimiki yanzu yanzu nan wurin.

"Cikin ihun kuka nake fadin nifa bansan nan gida zani.

Yaya safiyyace tazo ta kamoni tare da komawa dani cikin falon tana lallashi sosai nake kuka" Kinga gayamin meyake miki? Bakiso yana rabar kine?

" Ya safiyya befa sona shima nima ban sonshi shiyasa kawai yakemin abinda yaga dama kumamafa aljanu ne dashi!!!

Rikemin hannuwa tayi"To shikenan yanxu ki kwantar da hankalin ki da mun koma gida zanje wajan malam tsoho inyimishi bayani kinga zuwa gobe sai indawo in kawomiki maganin da zaibada idan ma akwai yiwuwar in wuce dake kawai sai ki Bini Amma yanzu idan mukatai tare Abbanmu bazaiji dadiba zaiga kamar bakimishi biyayya ko?

Kaina na d'aga alamar eh Amma har lokacin kuka nake dan zuciyata tariga tazo wuya.

Nan ta barni sukuma suka wuce,Kuka nakeyi irin me shegen cin rai dinnan.

Abba ne ya zauna Kusa dani tare da riko hannuna "Aysha Ashe kema haka kike da rigima ko? To kiyi hakuri da kaina zan d'auki mataki bazai kuma cin zalinki ba,Kaikuma zonan!! Ashe dama baka sonta Amma mu bamu saniba?


" Abba wallahi k'arya takeyi inasonta sosaima kullun sainagayamata Amma bata yarda.

"To meyasa kakecin zalinta? Cewar mama dan itama kukan da nakeyi yafara tsorata ta.

Yamutse fuska yayi" Kai mama nifa wallahi sharrine kawai kalar nata idan ba hakaba nifa tunda aka kawotama iyakata hannunta Amma zatawani yimin sharri.

Shigowar wata mesuna halisa yasani hadiye kukana suma duk sai sukai shiru,Diyar yayan mahaifin Dr dince.

Ko kallonta banyiba yayinda idanun Dr din ke akaina yana kallona.
Atsaye ta gaida har Abban saikace anyi mata dole Sannan ta k'araso ta zauna tana kallona.

Hirar karamci irin na iyayena suke yi yayinda nikuma bake gefe Sai hadiyar zuciya nake sabida kukan da nasha.

Kamar ance in d'ago kaina sainaga sai kallona takeyi,Muna hade ido sainaga tasaki irin dariyar shakiyanci dinnan,To dama zuciyata Asama take bansan na idasa wajantaba balle Marin Dana kifamata saida naji salatin su mama.

Dan dama tuni Dr. Ya wuce ciki maida jakar kayana.

"Aysha kyaleta mana yi hakuri k'anwarkice meyasa zaki mareta? Cewar mama tana shiga tsakanin mu.

Hararar maman tayi kamin tace eh dole kimata magana cikin lallashi tunda 'yar gwal ce to wallahi saina rama marina koba jikinta ba.

Baki maman takama kamin tace" Koba jikintaba jikina kenan? Waiku dan Allah meyasa duk Baku da nutsuwa ne matar yayan naki zaki yi fada da ita da girmanki da komai?

"Eh koma inane saina rama,

" Ke hajiya kyalesu dan Allah taimata abinda takeji zata iya ni bansan fitina,Yanzu nan inda iyayenta zasu ji saikinji wata masifar zata taso.


Kunkunai tafara Wanda dagaji wata rashin kunyar takeyimusu,Aiko nakuma cakumota ina k'aramata wani marin.
Fitowar Dr. Yasa mama kaucewa shikuma ya iso da sauri ya banbareni jikinta,Cikin bacin rai ya kalleta kamin yace"Bar nan kamin inci uwarki,Idan kikakuma shigowa gidannan saina karya wa inan sillayen k'afafun naki wawuya kawai masu bakin halin tsiya.

D'agani yai sama ya nufi bangarenmu dani kan kafadarshi duk irin zillewar danake besa ya saukeniba haka kukana.

Saida ya direni Saman gado kamin ya shige jikina tare da toshemin bakina da nashi,inaji ina gani amma ya hanani ko motsin kirki,Kukan ma tuni Yakama gabanshi.



"Kai yarinyar akwai fada alhaji aigara dataimata haka yanzu taba 'yan uwanta labari wannan itace daidai dasu wlh.

" Sosai kuwa nibakiga ko tashi banyiba ina kallon lokacinda takemata dariya,Dama alhaji lawal ya tabbatar min da cewa ita aysha fadane da ita ba kamar Fatima ba,Amma kuma tanada dadin zama,Rikicine kawai nata balle ga haushin rashin tafiya gida,Gara da taimata hakan ai.




Ahankali ya zare jikinshi yana sauke ajiyar zuciya,Murmushi yasaki ganin yanda fuskarta duk tai hawaye,Idonshi ya sauke akan bakina,d'an karami dashi da ragowar janbaki jikinshi,Ya kalli kyawawan idanu ga gira me kyau,Murmushi yakuma saki afili yana fadin komai naki me kyau ne Aysha Inafatan Allah ya daidaita tsakanina dake ya kore dukkan shaidanun dake niyyar shiga tsakaninmu.

Anatse ya gama shirinshi tare da sumbatar fuskata yabar d'akin duk da yasan maraicene Amma ya gwammace yabarni inyi barci da ya tono wata fitinar.



"Ina zaka kuma? Cewar mama tana kallonshi.

" Barci tayi mama zanje wani waje indawo insha Allah lafiya zata tashi.

"Kai zonan" Matsawa yai kusa da Abban tare da zama.

"Ka gayamin gaskiya akwai wani Abu na damuwa ne tsakaninku? Dan Nasan haka kawai bazatayi wannan borin ba na d'azu tace saitabi 'yan uwantaba.

" Kanshi yashafa Abba banyimata komaiba wallahi kumafa rashin kunya takemin Amma kyaleta nakeyi kawaidai rigimace kalar tata.

"To dan Allah ka kula kodan mahaifinta banso inji wani Abu Mara dadi tsakaninku dannasan ko d'azu 'yan uwanta bazasuji dadiba dan Allah ka kula.




**

Madara na kwaba da Zuma inasha Idona alumshe tsabar dadi.
Cak ya tsaya da aikin da yake yana k'aremin kallo nikuwa ai bammasan yanayiba.

Dariya yayi ahankali kamin inji sautinshi" Baby me kikesha haka?

Gira d'aya na d'agamishi kamin ince madarace da Zuma bawani abin kwadayi ba.


Murmushi yai kamin yace"To shikenan kisha ki koshi nikuma anjima insha cikin jikinki ko?

Cikin gatse nace eh kasha idan ka ganta.


Cigaba da aikin shi kawai yayi nikuma nacigaba da kwadayina.


Saiwajan goma da kwata yace tashi muje mu kwanta duk da dai gobe zan iya hutawa ammadai barci nakeji tashi muje.

Mikewa nai ina jera hamma danni bayan ma ya hanani kwanciya da kila tuni na jima da barcina.


Turare kawai na fesa na wanke baki garin akwai sanyi babu wankan da zankumayi.


"D'akina zamu kwana yau,

Jan dogon hijab dina nai zuwa d'akinshi haushin wannan ikon mallakar da yakemin nakeji Amma Nasan babu yanda zanyi tunda k'arkashinya nake.

Dagashi sai boxer amemakon yasaka kayan barcinshi.

" Kana kallo naima wancan d'akin hayaki Amma kace mudawo nan kuma bayan rushin ya sike,Idan sukazo sukaita dakaka babu ruwana wallahi.

Dariya kawai yayi tare da jawoni jikinshi ya zare hijab din dake jikina Sannan ya kashe wutar.

Lamo nai jikinshi ina jin yanda zuciyarshi ke bugawa kamar yadda tawa nima ta tsananta bugawar musamman danaji hannunshi saman kirjina abinda betaba minba.

"Yaya"

Dariya yasaki kamin yace"Yaukuma suna kika canzamin?

Turo bakina nai cikin shagwaba nace Abu kake tabamin fa!!.


"Nasani aysha Amma ina buk'atar nutsuwa ne koda bazanyi miki komaiba,Inkuma anyi me gaba d'aya shikenan.



Please Login or Register in order to submit comment