Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nufi ciki dani lokacin harabar gidan tacika da mutane dan duk na cikin falon sun fito jin amarya ta iso.






Wannan labari na kudine ki biya d'ari uku domin samun naki.

Acct no.
0005074141,Aisha sabiu,Ja'iz bank.

Kokuma mtn Cart.
08142643253.
12/10/20, 2:29 PM - Naffy Aliyu Umar: *Labarin* JARUMA na *kudine* ki *biya* *d'ari* uku *domin* *kisami* naki.



28



Kai tsaye d'akinta ta wuce dani mama da zainab na biye dani,Asace na kalli ko ina gaskiya gidan yasha gyara dan gashinan sai k'amshin sabon fenti yakeyi.

Gefen gadonta ta zaunar dani kamin tace"Ki kwantar da hankalinki ki daina wannan kukan nan ma gidankune gani mamanki bazan bari kowa ya tabamin ke ba.

Ficewa tai domin kulawa dasu maman dan tabarsu falo da sauran mutane.

Mama babu ruwanta da kiran ayi wani Abu da kanta tacigaba dayin nan nan dasu maman yayinda shikuma Abba yake tare da Abban Dr. Din acan falonshi da sauran abokai.



Sallar la'asar.
Zuwa lokacin duk mungama hutawa hatta Dr. Yashigo gidan dan naji maganarshi d'ayan d'akin yana gaida mama.

,Zaune nake wajan k'afafun Abbana hannuna na cikin nashi tuni gidan ya koma sai yayin Dr din,Tunda dama bawani taro akeyiba dama masu tarar amaryane kawai.

"To Alhaji mufa munyi abinda ya kawomu kuma Alhamdulillah zamu wuce,Cewar Abbana yana murmushi dan sosai hankalinshi ya kwanta da irin tar bar da akaimana.

" To madalla mungode Allah yasaka da alkhairi Ubangiji Allah ya kaiku gida lafiya insha Allah munanan zuwa domin yimuku ban gajiya dan Allah atayamu da addua.


"To kai likita zamu wuce ga k'anwarka nan tazo saimuce Allah ya kade fitina tsakaninku ya daidaita yabaku zaman lafiya,Dan Allah kayi hakuri dan gaskiya aysha da Fatima akwai banbanci Sam ba halinsu d'ayaba Allah ya baku zaman lafiya da hakuri da juna.

Ahankali ya matsa wajan Abban tare da riko hannunshi ya Dora saman kanshi yanajin yanda zuciyarshi ta tsananta bugawa sosai yakeso yaima Abban godiya saidai besan ta ina zaifara ba haka kuma wace kalar yadace yayiba,Saidai yasan cewa yanajin mutumin kamar yadda yakejin mahaifinshi cikin zuciyarshi.

Yasan idan ya bude baki kukane zai kwacemishi shiyasa ya gwammace yai shiru Amma har lokacin hannun Abban yana akanshi.

Murmushi Abbana yai sannan ya shafa kanshi karka damu yarona Allah yabaku zaman lafiya akula da addua kaji ko.


Kukana yasasu yin shiru gaba daya dan harwani shakewa nakeyi tsabar yanda kukan yatasomin gaba daya,Ashe dama haka kowace mace takeji lokacinda aka kaita wani gida domin zaman aure,Gaskiyan hausawa dakan fadi cewa aure yakin mata.

Cikin rad'a Abbana yace" Tashi ka kamata kushiga ciki kaita aikin lallashi kamin ta tashi hankalin kowa wajan nan.

Cikin hanzari ya mike kamar Wanda yake jiran umarni dama.
Jinai kawai yana jamin hannu alamar intashi,Duk da nasan cewa inada taushin jiki Amma sainaji na Dr. Kamar yafi nawa,Ina kuka sosai ya d'agoni yai waje dani duk irin tirjewar da nakeyi,Dayake bangaren da zamu zauna din rufe yake amma an nunama mama da zainab cikinshi,Basuso kowa yashiga shiyasa suka maidashi suka rufe.
Kai tsaye d'akin mamanshi ya wuce dani,Yanajin wani mugun tashin hankali sabida sautin kukana dake bugun zuciyarshi.
Kan cinyarshi ya zaunar dani bayan ya zauna gefen gadon, Duk irin zillewar da nakeyi besa ya sakeniba saima k'uguna daya rike kam tare da cusa fuskarshi cikin wuyana.

"Shshhhi yi hakuri Abba ne? Ko mama? Nine? Yi hakuri zan kaiki ki gansu duk lokacinda kikaji kinaso kinji ? Yi hakuri kinsha kuka da yawa fuskarki duk ta tashi yi shiru kinji bazan cutar dake ba nan ma gaki ga mama gakuma Abba kinbaro wasu kinsami wasu yi hakuri.
Ganin naki daina kukan yasashi kawo bakinshi daidai kunnena,Ashema ayshan Dana sani raguwace me shegen kukan tsiya kamar baby.

Tsak kukana ya tsaya tare da tureshi daga jikina idanuna kamar zasu fado k'asa tsabar harararshi dnakeyi dama gashi idanun duk sunkuma yin ja.

Dariya taso ta kwacemishi Amma ya gintse dan dama yasan tsokanata kawai zaisa wannan shegen kukan ya tsaya" Eh ko k'arya nayi? Daga ganin wannan idanun naki nasan tun shekaranjiya kikeyin kuka idan ba raguwaba wacece zatai hakan ko mayanka za a kawoki ai yakamata ki nuna jarumta ko?

Saida na share hawayena kamin ince"eh naji kuma babu ruwanka dani dayake bakai aka raba da iyayenkaba ai dole kace kuma wallahi komawa gida zanyi ai nasan hanya.
Dole nai shiru batare da nayi niyyar yi ba Dan tuni ya rufemin baki da nashi.
Wani irin Abu nakeji Wanda ban isa ince ga abunba Saidai tuni wuta ta d'aukemin.

Da sauri ta juya ta koma ganin yanda k'anin nata yai nisan kiwo,Murmushi tasaki aranta tana fatan Allah ya daidaita komai kuma ya karesu daga sharrin dukkan abinda Ya halitta.,Dama hijab dinta zata d'auka dan yima su Abban rakiya dole saidai ta fita ahaka.


***

Godiya sukeyimusu kamar zasu aro baki tsabar farinciki,Zainab ce tai kwal kwal da ido tana kallon Maman"Dan Allah idan ayshan ta huce zan kira wayarta.

" Karki damu zuwa anjima kadan zata warware Allah ya tsareku yasa asauka lafiya.

Ahaka sukai Sallama da juna cike da farinciki lallai yau sunga inda ake girmama mutane,Anrabu kowa yana ganin mutuncin juna.

Tunkamin suyi nisa mama tasaka kuka zainab na tayata Allah yasani daurewa kawai takeyi Amma gaskiya Allah ne kawai yasan halin da zuciyarta take ciki,Dama shine me bata kwarin guiwa to tana kallo shima dauriya kawai yakeyi.

Yana jinsu suna koke kokensu Amma haka ya daure ya d'auki hanya fatanshi su sauka lafiya saiya lallashi barshi hankali kwance.



**

Dan kanshi ya sakarmin baki dan tuni jikina ya saki namadaina kokarin kwatar kaina daga gareshi.

Shafamin baya yake Ahankali,Muryarshi ashake yace "Kiyi hakuri insha Allah bazakiyi danasanin amincewa da aurena ba Allah yaimiki albarka ya sassautawa zuciyarki.

Kwantar dani yai gefenshi har lokacin yanad'an jijjigani saikace me kwantar da baby, Ahaka mama tashigo d'akin.
Tuni nai barci Sai sauke ajiyar zuciya nakeyi.

Yafitoshi tai da hannunta sai sukai waje saida yawani lallaba.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya zauna kan kujerar" Mama najima banga mutane masu karamci irin Abba ba wallahi koni bazan iya abinda yaiba,Ki tsananta addua agareni mama Allah yasa in rayu da aysha hakika zaku iya rasani idan na rasata inajinta duk bugawar numfashina mama ina sonta irin Wanda bantabajin irinshiba gashi itakuma bata sona mama kullun saitamin tsiwa,Bansan ko zata iya zama daniba.

Kamo hannuwanshi tai tana kallon cikin idanunshi wa inda suke alumshe kamar mejin barci"Karka damu babana zaka rayu da aysha insha Allah zakuyi rayuwa me tsayi da ita zata soka zata kasance dakai harma ta Haifa maka kyawawan yara,Zamu tsananta addua Allah baya barci zai amsa mana.


Kwantar da kanshi yai jikinta yanakuma naniketa"Mama aysha ta cika rigima wallahi.


"Karka damu kanka zata bari kumama ai kataba gayamin cewa kanason mace me rigima ko ka fasa ne?

Dariya ya saki yana boye fuskarshi cikin jikinta.


" Innalillahi nabani kaidai anyi qaton banza wallahi,Mama kina kallo sai kuma nanikeki yakeyi saikace meshan nono? Cewar aunty hannutu yayarshi.

Dariya kawai sukayi kamin su hade nan ana hira ko wanne fuska cike da farinciki da walwala.



*Sabuwar* _rayuwa_ .



Zan iya cewa daga yanzu ne rayuwar tafara dankuwa yanzune zamuji labarin ni JARUMA.

Bayan sallar isha'i gidan dagani sai mama wacce keta bakin kokarinta naganin nasaki jikina nafara walwala Amma ina,Bunu bunu na share hawaye tsabar yanda kewar gida ke damuna,Ina sane da mayen kallon da Dr. Kemin shiyasa duk na kuma takura.

"Tashi kije ki rakata d'akinta dan Allah saita huta gaba daya Cewar Abba yana kallon mama.

Kuma shigewa nai jikinta ina niyyar bare baki,Haka kawai nakeji nakoma wata sakarya sabida tsabar kuka.

" ah subhanillahi menene abun kuka kuma,Bazaki je can din bane?

Kaina na d'agamishi ina share hawaye.

Kallon Dr. Sukai Wanda yakasa ya tsare tun d'azu jira kawai yake ace ku shiga ciki.
Bata fuska yai tare da kauda kai.

Tashi tsaye Abban yai yana fadin"Nikam nayi nan Duk yau jikina be hutaba Allah ya tashemu lafiya.

.
"Kinga aysha tashi muje in rakaki babu abinda babana zaiyi miki idan ma Wani Abu kike tunani,Kai kuma babu ruwanka da ita ka kwana d'akinka itama ta kwana nata kanaji ai?

"To Mama"

Saida taita aikin lallashi Sannan namike bayan nagama harare Dr. Din sabida mayen kallonshi ko gajiya beyi.

Doguwar Addua nayi kamin in shiga da k'afar dama,Kamar yadda maman keta jaddadamin
Yayinda shikuma yake ta binmu abaya.

Da kanta ta hadamin ruwan wanka saida taga nashiga sannan tafito ta d'aukomin kayan da zansa,Sannan
Tafita bayan ta kora dr.din tanata nanatamishi kadda ka takurata dan Allah kaga har yanzu bata sake damuba.


Sosai nai wanka tare da gyara jikina nan da nan naji gajiyar da naketa fama da ita tana warwarewa.

Shafa nai anatse bayan na rufe d'akin.
Saida nasaka doguwar rigar barci Mara nauyi,Sannan najawo farantin da aka shiryomin kayan abinci.
Ganin hadda kayan hadin tea sai kawai na had'a dan jin cikina nakeyi acike.



Acct no.
0005074141,Aisha sabiu.Ja'iz bank.

MTN Cart.
08142643253.




***

Saida ya gama shirinshi harya kwanta Amma kuma yaji Sam bazai iya barciba yau,Lopton dinshi ya d'auko yacigaba da aiki har tsawon wani loakaci Kamin yashiga ya d'auro alwala dan ganin dare yashiga sosai.

Sosai ya duk'ufa wajan gayama Allah kukanshi duk da cewa yasan shine ya jarabceshi da wannan musifar.

K'arfe uku da kwata ya gama abinda yake kai tsaye ya nufi d'akinta dan yasan bazai iya wani barciba indai ba jinta cikin jikinshi yai ba.

Ahankali ya bude kofar tare da haska wayarshi kai tsaye ya wuce k'urya yai amfani da wayarshi har zuwa gado.

Jiyai zuciyarshi na wani irin tsalle tsabar shauki.






Haske writers association.
12/10/20, 2:29 PM - Naffy Aliyu Umar: 29




Ahankali ya zare jallabiyarshi tare da rabawa gefenta ya kwanta,Tare da zagawyo hannunshi akan ruwan cikinta,Wata irin karfaffar ajiyar zuciya ya sauke tare da kuma danna kanshi cikin jelolin kitson dake watse akan filo.


Cikin barci naji duk na takura,Amma dayake barcinne ke kaina sai ban motsaba.


Sama sama ya dingajin kiran sallah,Saida yai tsam da tunaninshi saiyaji ashema tada sallar akeyi.

Ahankali ya warware nakewar da taimishi ya lallaba yabar d'akin, Agurguje yai wanka gami da alwala,Saida yagabatar da Salla Sanna ya nufi d'akinta.

Sallame sallata kenan naji shigowarshi,Batare Dana kalleshiba nace"Ina kwana?

"Lafiya lau,Yanzu nake niyyar zuwa tashinki Ashema kin tashi ya kwanan bakunta?

"Alhamdulillah,Lafiya lau.

"Masha Allah zanje in inkwanta.

Kallonshi nai kamin ince kwanciya kuma?

" Shima kallona yake kamin yace"Eh mana ko akwai wata damuwa ne ?

D'an harararshi nai kamin ince sosaima kuwa,Nufinka yanzu saikaje ka kwanta babu wasu adduan Neman kariyar Allah daga sharrin yinin yau shine zakace zuwa zakai ka kwanta ko har ka gama.

Wata irin nutswa yaji tana sakkomishi Amma afuska be nunaba"To nidai gaskiya nayi abunda na iya sauran kuma ai saikiyi mana ko?

Tashinai tsaye ina kallonshi"Tab lallai kanada matsala indai hakane muje ka kwanta din.
Tashi yai ya nufi d'akin shi yayinda nabishi abaya,Yana zuwa ya haye gado nikuma na zauna gefenshi da k'aramin al'qur,ani ahannuna.

Abayyane na karanto suratul bakara daga farko har k'arshenta Sannan na rufe al'qur,anin lokacin idanunshi arufe duk tunanina barci yakeyi.

Ashe lamo kawai yayi.
Tafin k'afarshi ta dama na tofamishi suratul nass ata hagun kuma na tofamishi suratul falaq.
Tashi nai nafara gyaran d'akin duk da cewa babu wani datti cikinshi.

Anatse na kammala komai,Sannan nabar d'akin.

Ajiyar zuciya me k'arfi ya sauke kamin ya gyara kwanciyarshi wani irin matsanancin farinciki ke baibaye dashi.

Shigowar kira wayarshi yasashi saurin danneta kamin ya d'auka yana Allah ya wadarai da arna Sam basu da tsari me kyau.

"Hello Daniel ya kake?

Da shegiyar hausarshi yafara magana" Lallai kana hutawa oga shikenan saidai naji labari har amarya tatare kuma bayan nace ka gayamin zan shigo gari kamin time din ya haka?

"Karka wani damu nasan dai wani nauyin zaka Dora ma kanka to babu komai abinda kaimin ma asauran nabaya har yanzu ina godiya kuma kasan wannan karon gida na zauna tare dasu mama shiyasa babu Wanda yasan tarewar.


Mikewa tsaye yai daga inda yake cike da takaici Sam beso jin hakanba dole ya canza hanya kamin komai ya kwabemishi balle idan har yarinyar da aka kwatanta mishi ita din ce" OK saina shigo naga amarya Amma bakakyautaminba ka gaishe dasu mama.


Ajiye wayar yayi yana sauke numfashi, Shi ya rasa wane kalar so Dr. Daniel kemishi ba,Shidai yasan bawani kulawa yake bashiba Amma Shidai yana like dashi duk da cewa yanzu shi aikinshi ya dawo katsina shikuma yanacan abuja.
Tsaki yaja tare da gyara kwanciyarshi yacigaba da tunanin amaryar tashi kamin wani daddadan barci yaigaba dashi.




*
*
Banwani koma barciba dan ba sabona bane barcin safe,Shiyasa na kammala gyaran ko ina nasa k'amshi kamin nashiga wanka lokacin takwas nasafe ya gota.


Shiri na nai cikin Riga da zani na atanfa tare da saka k'aramin hijab fuskata babu kwalliya Amma hakan behana bayyanar da kyau na,Sai tashin k'amshi nakeyi sabida turarukan danai amfani dasu na kaya Dana jiki.

Cikin siririyar muryata wadda takuma sanyaya sabida kukan danasha kwana biyu,Nai sallama kaina ak'asa ganin mama da Abban zaune sunata hirarsu da alama basu da sauran damuwa.

Murmushi tasaki ganin tafiyata lafiya lau,Tai tunanin bazai iya barinaba ayanda ta ganshi jiya.


Duk'awa nai har k'asa na gaidasu sannan nasami gefe na zauna gidan shiru babu motsin yara,Yarinyar da maman ke riko tuni ta gudu wajan 'yan uwanta dama diyar aunty halima ce,To daga jarabawa saitaki dawowa.

"Ina megidan naki yake aysha ko be tashiba? Cewar Abba yana murmushi.

Akunyace nakuma kauda kaina ina murmushi.
Banjima da zama ba saiga Dr. Cikin shigar k'ananun kaya yai kyau sosai fuskarshi fes harwani sheki takeyi bantaba mishi kallo irin na yauba,Shi dimma idanunshi na kaina tuni ya manta da wanzuwar iyayenshi wajan.

Zama yai tare da gaishesu,Nikuma na gaisheshi batare Dana kalleshiba.

" Ai shanake bazaka fitoba yau sabida angwanci,Cewar Abba yana dariya.
Adan zaman danai daga jiya zuwa yau na lura abbansu nada matukar son wasa.

Yamutse fuska yai kamin yace"Kai Abba agabanta? Zakasa ta rainani ai.

Duk dariya sukai kamin maman tace kamata kuje ga abinci can Ku k'arya.

Ido na zaro ganin ya matso wajena,Da sauri na mike dan karma ya kamanin gabansu saikace wata Mara lafiya.

Cin abincinma bawani saki jiki ba sabida yanda yakebin ko ina najikina da kallo,Ikon Allah shi ko wane kalar mutunne oho.

Shigowar wasu 'yammata cikin falon yasani yanke tunanin Dana fad'a,Saida suka gaida su maman kamin su wuto wajan da aka tanaza danyin break din.

Da kallon mamaki nabisu dan babu wacce nasani cikinsu gasu har su hudu ko wacce da tulin takardu hannunta da alama daganan makaranta zasu wuce.

"Yaya ina kwana?

Tare suka had'a baki wajan gaidashi saidai ga mamakina sainaga babu wacce ya kalla cikinsu balle ya amsa,Hasalima yai wani irin hade fuska wadda ni kaina Saida naji kamar intashi inbar wajan.
Cigaba yai da cin abinshi kamar besan suna wajanba.

Nidai dama cikinsu babu wacce taimin magana amma idanunsu na kaina.

" Kin k'oshine kona baki?

Duk kallonshi mukai,Kamin in ture ragowar nagabana na mike,Shima mikewa yai tare da zagayowa ya kama hannuna mukabar wajan.
Tsabar d'aure fuskar da yayi yasani binshi saikace wata bindi.


Bansan ya suka k'areba Amma nai mamakin wulakancin da yaimusu gasu masu kyau dasu,Nasan 'yan uwanshine tunda gashi sunacemai Yaya.


Saida ya maida kofar ya rufe sannan ya hadeni da jikinshi"Ke bakauyar inace haka ake gaida miji dama?


D'an turo baki nai kamin ince"Mijin ya fati dai ni babu wani miji anan.

Cironi yai daga jikinshi yana kallon fuskata"Aysha da nayi niyyar barinki zuwa wani lokaci Amma gaskiya wannan maganar da kikeyi ita zatasa in gwamiki ni mijinki ne kinji ko?

K'okarin kwace jikina nai Amma ya rikeni kam yanabin fuskata da kallo,Niko saina runtse idanuna kam.



***

"Dady bazan iya hakuri ba wallahi son Yaya zai kasheni yau dasafe danabiya gidan bakaga yanda yakuma kyau ba,Duk wannan tashin hankalin babu Dan Allah ka auraminshi dady!!!

Saida yagama kallonta kamin yace Ameera baki da hankali wallahi,Waike kina tunanin zan yarda ki auri Ahmad ne? To idanma kina wannan tunanin gara ki bari dan indai ina cikin hayyacina to bazan auramiki Ahmad ba,Bandama ke wawuyace meye abunso jikinshi? Idan kyaune ai kema kinadashi,Inkuma kudine kina zaune Allah zaibaki Wanda yafishi tunda ke kyakkwaywa kumama jiya basiru ke gayamin cewa ummi diyarshi itama son Ahmad din take shiyasama ya maidata kano wajan k'anwar mamarta to wallahi ni idan kika dameni kauye zan kaiki wajan gwaggonku ladidi can ki k'arata wajanta.


Kuka tasaka wiwi amma ya kauda kanshi haka kawai nima inje abun yadawo kaina ai tunda har wannan abun yakawo yanzu to bazan yadda kema kishiga jerin masu mutuwaba,Wannan ma da yake murna da iyayenshi kina nan zaune zakiji jini ya balle mata ta rasu.






*Wannan* *labari* _na_ *kudine* ki *biya* d'ari uku *kisami* *naki* .



***

Tashina kenan daga barcin dolen dayasani wai dole sainayi barci kuma saigashi nayi din Ashe dama ina buk'ata.

"Anshinan gulmamma Ashe dama kinason barcin Amma kika k'i kwanciya saida kikaji lafiyayyen jiki,Rike mama ke kiranki tun d'azu kinji dadin aure ko nemansu bakiyiba.

Kallo nabishi dashi bayan yabar d'akin ni mamaki yakeban yanda yake sakemin Amma gaban mutane saikace besan wani Abu waishi walwalaba,Dan yau gidan yini akai yin bak'i shikuma beje ko inaba.


" Hello mamana ina yini?

"Lafiya lau Aysha na inafatan komai lafiya ko?


Cikin shagwaba nace komai qalau mama Amma kewarku ta dameni d'azu har kuka nayi Allah.


" Ki kwantar da hankalinki yau saura kwana shidda su maryam suzo wajanki ki fadi duk abinda kikeso zanyi k'okarin sama miki kamin lokacin kinji ko?

"To Mama ina Abbana?

Gashinan yanacin abinci yace zai kiraki anjima amma saikin daina wannan koke-koken tukunna,Kina Amfani da ruwan dumi ko?

Akunyace nace kai mama nifa bemin komai ba.


Dariya tasaki har inajin sautin
Abba shima yana tayata,Ajiye wayar nai Nima ina sakin murmushi.




Acct no.
0005074141,Aisha sabiu,Ja'iz bank.

Ko MTN Cart.
08142643253.



***

Cikin nutsuwa na gama shirin barci Saidai zuciya ta ta tsananta bugawa aduk lokacinda na tuna kashedin da Dr.yaimin na lallai yau d'akinshi zan kwana.

Zumbulelen hijab nasaka bayan nagama shafe jikina da turare,Jan kofar d'akina kawai nayi sabida barcin da nakeji yo dare yayi sha daya saura sabida kallon Dana tsaya yi.

Ahankali na turo k'ofar,Ajiyar zuciya na sauke ganin d'akin duhu nasan dai Kila yai barci.


Boyayyar ajiyar zuciya yasaki,Beyi tunanin zanki zuwaba,Cikin ranshi yake nanata kad'an daga auran mace wadda tasan addini kuma take aiki dashi,Kuma lafewa yai har saida yaji hawowarta gadon.






Haske writer's association.
12/10/20, 2:29 PM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦 .
30



Cikin nutsuwa nai addua na shafama jikina shikuma na tofamishi daga nesan da nake dannifa ganin abun nake wani banbara kwai har yanzu wai nice kwance gado d'aya da wani,wanin ma mijin ya fati,Mutumin da kullun nake mitar ta zabeshi tabar sauran masoyanta Alhalin babu abinda zai gwada musu saidai ko miskilancin.

Zabura nai zan ruga jin hannunshi jikina,Saiko ya jawoni gaba daya na kifu kanshi.

"Kedai bakauyace wallahi haka ake zuwa gun miji?

" Nifa kai...shiru nai tare da yanke maganar da nai niyyar fadi,Kadda injama kaina ya tabbatar da maganar da yayi d'azu da safe.
Miyau na hadiye kamin ince kayi hakuri.


Dariya me sauti ya saki kamin yace"Baby kaddai ace har kin tsorata bakineki ya mutu?


Duk da cikin duhune Amma saida na yatsina fuska"Allah ya kyauta kacemin wani baby saikace haihuwata tayi.

Fuskata ya laluba kamin inyi wani tunani ya hade bakunanmu.

Wani irin shegen rugugi me tsananin k'arfi ya cika kunnuwanmu abun saikace cikin film gawani irin matsanancin duhu daya mamaye d'akin.

Cikin rawar jiki Dr.yaso fidda bakinshi cikin nawa,Amma bansan meya faruba saidai naji nakuma damkeshi cikin jikina,Wata irin kuwwa mukaji cikin kunnuwanmu dan har saida muka danne kunnwanmu.

Cikin zuciya ta nafara addua dan nafarajin tsoro duk da cewa wata zuciyar tawa nakuma bani kwarin guiwa.

Matseni yai cikin jikinshi,Kamar Wanda keson boyeni dan kar wani Abu yasami damar cutar dani.
Wata irin fincika akai mana wadda ta tilastamana watsewa gefe gefe.
Dr.fadawa yai can fuskarshi ta bugu da gefen gado inajin lokacinda yai wata k'aramar k'ara kamin inji shiru niko iyakata saman gado.

Ahankali haske dake d'akin ya dawo sabida dama akwai Wanda ya d'an shigo
12/10/20, 2:29 PM - Naffy Aliyu Umar: 31



Cikin nutsuwa nagama shiri na Sannan na kunna rushi na nema garin habbatussauda, na barbada saida nagama turare ko ina Sannan na nufi bedroom dinshi,Nasandai zuwa lokacin

Please Login or Register in order to submit comment