Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zamu koma gida,saiga kiranshi yashigo,Saida naji gabana ya fadi,Haka na daure na d'aga.

"Babyna'

" uhum kayini lafiya ya aiki?

"Alhamdulillah yanajiki kamar kina tafiya badai baki gidaba ko?


Ahankali nace eh ban gida Ammadai ganinan zan koma inahanya.

Wayyo Allah ai sai masifa tatashi" Aysha kina wasa dani ko? Yaushe kika rainani har haka wato ni ga sakarai ina nan abanza kekuma kina can kina yawon ki wato ga d'an iska ko?

Kayi hakuri dan Allah yanzufa nake kan hanya da niyyar komawa kuma ba.....

"Ke dakata da Allah kamin ranki ya baci yanzu nan wlh.

Kashe wayar nai ina Jan tsaki.

Ya dalha yafaramin fad'a" Ke aysha me yasa zaki kashemai waya kinsan takaicin da mutun yake shak'a kuwa idan aka kashemai waya? Balle kuma ga mutumin da kake tunanin kanada iko akanshi danhaka ki daina kuma anjima kibashi hakuri sam babu dadi.

To kawai nace Amma araina inajin bazan bashi hakurin ba,Banson mutun me shegen kishin tsiya.




****
"Kambu uban can ni wannan yarinyar ta kashema waya? Lallai ta d'aukoma kanta masifa wallahi na rantse da Allah gobe zaki dawo garinnan ko bakiso zanga wanda ke sama tsakanin ni dake,Masifa yaketayi cikin d'akin ko zama yakasa,Saima wasu tuna nika dake biromishi na cewa kilama yanzuma ba gidan zata komaba gaba daci dan dama tun farko ya fahimci tafi marigayiya son yawon tsiya,Shiko bazai yadda ya d'auki wannan gangancinba haka kawai.

Zama yai tare da tallabe kumatu yana Sauke numfashi,Wai yau shine aka kashema waya? Lallai idan ya kama baby sai yaga kuzarinta ya bar jikinta,Babu duka balle zagi Amma zai gyaramata zama.


Ficewa yai zuwa falo yana fitar da huci ta bakinshi.

Kallo daya maman taimishi ta furta " Kaikuma lafiya?


Ragwaf ya zauna kamin yace"Wai mama Kamar ni baby zata kashema waya?


Harararshi tai kamin tace "Akan me zata kashe maka waya kuma?

" wai mama dan kawai inayimata fad'a kan yawon tsiya shine taimin wannan iskancin Allah saina gyaramata zama tukunna zatasan kala ta.

"Kai dallah rufemin baki Sauna,Kaje dai ka barar da auranka wallahi Dan wannan yarinyar kar take kallonka kuma tsaye take bawani tsoron takife zatai ba,Danhaka kabi sannu ka koyamata sonka tukunna.

Sassauta zafin daya d'auka ya fara kamin yace" Mama narasa yanda zanyi da ita wallahi ita indai zata yawo to bata da matsala nikuma Wani irin masifaffen kishinta nakeji mama dan Allah kidinga nunamata abinda nakeso da wanda banso dan Allah shiyasafa nace kusa dake zamu zauna.

Diremishi abincin tayi tana kallonshi"Naji kaima yakamata ka kiyaye wa danku zauna lafiya,Kuma meyasa d'azu bakazo ka kai inna gambo gida ba?

Yamutsa fuska yai "Mama nifa wallahi wannan tsohuwar taku bataiminba Allah zubin marasa gaskiya gareta,Ina ruwanta da aysha da zata damu kanta da saita ganta kinji yanda tai ta mita kuwa? Saida nace mata insha Allah zan kawota Sannan ta hakura,Kuma wallahi babu inda zan kaita.

Shiru tai batace komaiba sabida tagaji da nunama mutane cewa lafiyar innan qalau,Ita mamaki ma takeyi idan taji ana fadin hakan tarasa me suke gani har sukeyin irin wannan maganar akanta.




***


Da bacin rai nashiga gida,To dama nai Sallar isha'i shiyasa ruwa kawai na watsa nai kwanciyata duk da barci nakejiba Amma na gwammace in inkwanta din ko zuciyata zata rage wannan zafin da takeyi.


Mamace ta lek'o" Aysha qalau kike kuwa?

"Mama ya cika masifa wallahi bakiji fad'an da yakeminba kilama da kusa yake saiya makeni shi ya cika zuciya nikuma bansan haka.

Zama tai gefena" To tunda kin fahimci halinshi ai Saiki dinga kiyayewa ko? Kefa mace ce aysha wallahi yanda kika taso cikin hikima basira da kuma hangen nesa ga tunani da tsantsar ilmi nai tunanin zaman aure bazai miki wahalaba,Saigashi tun kamin aje ko ina kinfara korafi da sauransu.

D'ora kaina nai saman kafad'arta"Mama shine yacika kishin tsiya,Be yarda ko waje in lek'a Alhalin shi kullun saiya fita.


Dariya tai kamin tace uhum abar shirita ayi me? Muje kisha kunun ayar saiki kwanta ki huta dan nasan yaudai kun yawatu.



"*"*"

Jikina na shafe da humra me matukar dadin k'amshi,Sannan na kwanta tare da Addua Wani irin ciwon Mara nakeji me zafi sosai.



Gajiya yai da liliyar wayarshi danhaka ya danna kira zuciyarshi cike da adduar Allah yasa ta huce.

Cikin siririyar muryata wadda ta had'u da ciwon dake damuna,Nai sallama tare da gaisheshi.

Tashi yai ya jingina da gadon,tare da lumshe idanunshi "Babyna meya faru?


Cikin shagwaba nace marata ke ciwo kaikuma kaitamin fad'a.


" Sorry Sannu kinji bazan kumaba Amma kema yakamata ki dinga jin tausayina ko? Yanzu ya kikejin ciwon maran?

Bayani naimishi nan ya fahimci babu shigar ciki jikina dan alamun al'ada zanyi kusantar da yaiminne yakeson kawo sauyi"Gobe zanzo saimu dawo gida kinji ko?


"A a Dan girman Allah karkamin haka kabari Sai nai kwanaki dan Allah kar kazo kaji?


" Nagama magana baby yauma bansan yanda zan iya barci babu keba,Danhaka bazan iya jurewaba kedai kawai ki shirya Saima anyi azahar Sannan zan taho danhaka kiyi komai natse.




Labarin JARUMA na kudi ne.

Idan kina buk'atar shi zaki iya tuntubar wannan layin.

08142643253.





Haske writer's association.
12/10/20, 2:48 PM - Naffy Aliyu Umar: 48



Wani irin bak'in cikine ya tasomin jin abinda yace,Amma nasan ba yanda zanyi tabbas idan yazo sai ance inbishi.

Aiko idan hakan tafaru zan bashi mamaki wallahi,Nifa nai tunanin idan mace tai sa'ar auran mijin dake tsananin kaunarta to shikenan bata da sauran damuwa,Ashe abun ba haka bane Ashe son da yakemaki bazai hanashi kartamiki rashin m Ciba tunda wannan ai damuwace.



Kwanciya na gyara tare da rufe idanuna ina hango fuskarshi cikin bacin rai da damuwa dan nasan dai kila yanacan yana cika yana batsewa banda tijarar da yaimin d'azu.




***
"Inna lafiya meya kawoki wajena?


Bakinta ta bude tanamai murmushi,Saidai dogayan hakoran daya hanga bakinta yasashi ja baya jikinshi yana tsuma.

Wani jini ya digo daga bakinta,Kamin tace" Kai amadu zuwa nai in gargadeka,Matarka,Matarka,Matarka itama ina sonta zatabi 'yar uwarta batare da wata damuwaba danhaka anshinan ka bata da hannunka.

Maida hannuwanshi baya yai jikinshi na rawa innalillahi me menene wannan?

Dariya tasaki yayinda manyan hakoran nan suka kuma wani zazzagowa,Tunkaroshi tafarayi bakinta na zubar da jini yayinda shikuma yai wani irin tsalle saigashi k'asan gado dim yafado.
Tuni ya dawo hayyacinshi,Ga wani matsiyacin tsoro daya duromishi,Da sauri ya kunna kwan d'akin haske ya gauraye ko ina Amma hakan besa ya dainajin tsoro ba,Jikinshi yagama dubawa yaga babu abinda ya sameshi Sannan ya sauke wata ajiyar zuciya da besan yana rike da itaba.

Alwala ya d'auro yazo ya kabbara salla dan bega ta kuma kwanciyaba anaso a lalatamishi rayuwa,Dan tabbas idan wani abu yasami aysha a yanzu to rayuwar ta shima saita lalace.

Barcin da be komaba kenan.




****

Washe gari; Tun safe nagama shirina nabar gidan dan bangama ziyaraba gara inje inda zani kamin yazo kuma ace in shirya inbishi.

Abba yaso ya hana Amma sai nace mishi ai gidan baba malam zani kuma ba jimawa zanyiba.

Gidansu zainab na tsaya dan dole Saida tai wanka Sannan muka wuce.


Kallon wayata nai karo na wajan bakwai,Tsoron wani fad'an nashi nake Shiyasa nakasa d'aukar wayar.

Ahankali na d'aga kiran tare da rufe kunnena dan karma yaji hayaniya yai tunanin yauma fita nai ga wani shegen ciwon Mara daketa sakad'ata ,Amma haka nake yawon.

Cikin sanyin murya ya furta"Baby inata kiranki baki kusa da wayar ne ko,Ya jikinki?

Saita muryata nai kamin ince"In a kwana katashi lafiya? Jiki Alhamdulillah naji Sauki.

Horn din wani me mota bayanmu yasa Dr. Yai wani irin shiru kamin yace"Aysha nufinki baki gida?

Batare da wata damubawa nace"Eh ban gida naje wajan baba malam Amma ina hanya zankoma gida.


Ajiyar zuciya ya sauke kamin yace "OK shikenan idan kin k'arasa zan kiraki kinji ko?

Kashewa mukai nida zainab" Ke kinji ajiyar zuciya daya sauke kuwa? Saikace ina wata uwa duniya shima yana wata,Hakadai mama tacemin jiya wai alamun kauna ne nuna kishi,To nikuma ina tunanin nashi yai yawa,Tunda aka kaini garinnan fa bantaba fitaba Sai so d'aya shima da mama kuma bakiga yanda yaita bak'in rai ba,Saiko rasuwar da akayi shima cikin mutane haka yace intaho mutai gida,Tunda nazo nan kuwa ai saidai yayi hakuri tunda dama bance ga iyakar inda zanjeba.


Dariya tasaki kamin tace"Wallahi shiyasa nakejin tsoron aurennan aysha saikiga abubuwa duk sai ahankali ga wasu nauye -nauye dake hawa kan mutun duk ka takura,Nifa soyayyar kawai ke birgeni shiyasa kikaga na hakura da malam ashir matarshi 'yar tijarace na tabbata bazata bari muji dadin rayuwarmuba,Nafison in auri wa yayye d'an boko kuma Mara mata duk da cewa naba Allah zabi kuma nashin nake jira Ammadai ni asona kinji zabina.


"Riko hannunta nai,Karki damu insha Allah zaki samu wanda zai zamemiki alkhairi kilama ki aure katsina Kinga har makaranta Saimu koma tare kedai kawai ki dage da Addua insha Allah zaki sami miji dan gaske.




""""

Akai-akai ya dinga saukar da numfashi dan sosai ya rike kanshi wajan ganin be balbalamin masifa ba kenan yauma da bata da lafiyar bata hakuraba kenan? anya ba k'afar kare ta gaigaya ba? Yarinya sai shegen son yawon tsiya? Bari yaimaza ya gama Sallamar mutane dayatafi Sallar azahar ba office din zai komaba.

Da zafi-zafi yaci gaba da duba mutane,Sabida yasamu yagama akan kari.



***

Da takaici da bak'in ciki tatashi sabida sam bataso tajema Ahmad din da suffarta ba taso ace tayi kalar wata macen yanda bazai taba tunanin wani abuba,,Amma yanzu taje da kamanninta ai Sai yai tunanin wani abu cikin ranshi,Damma namijine ba mace ba,Namiji na da kyaliya akan irin wannan amma ta tabbata da macece zuwa yau wayewar gari tafara Neman maganin miyagu.

Kwanciya ta gyara tana tunanin ta hanyar daya kamata ta tunkari gidan akaro na biyu.




***

"Ka fahimci yanda Ake banbanta niyyar ko?
Sadda kanshi k'asa yai kamin yace" eh na fahimta Guraben yin shine ban rikeba.

"To babu matsala ai haka nakeso duk abinda kaga baka fahimta daidaiba to ka tambaya hakan shine zaisa kayi addininka cikin kwanciyar hankali,Idan ka kwanta da mace zakai wankan tsarki shine naimaka bayaninshi yanzu,Haka kuma idan kai mafarkin ka kwanta da mace,Matukar ka fitar da wani abu to lallai,Saikayi wannan wankan sannan zakayi sauran ibadunka danhaka ka nutsu ka rikeshi idan kaga Abinda baka fahimta kai magana,Biyamin abinda ake fadi yayin yin ruku'u kamin mu d'ora.


Shigowar Ahmad din falon yasa suka maida kansu gareshi.

Saida ya gaida Abban Sannan ya mik'ama Abubakar din hannu,Yayinda dadi ya cikashi har yanzu dadi yakeji idan yaga an mik'a mishi hannu kokuma an rungumeshi.


" Sai ina kaikuma kasha manyan kaya haka? Cewar Abban yana kare mishi kallo.


Sunkuyar dakai yayi yana shafar kanshi"Abba kano zanje"

Idanu ya fidda kamin yace"Ikon Allah da wannan uwar ranar haka? To kabari Sai gobe mana saurin me kakeyi haka?

Kuma sadda kanshi k'asa yai yana shafar k',eyarshi"Abba kadai bari inje in d'aukota wallahi tacika yawo kuma nidai hankalina be kwanta ba.

"To shikenan Allah ya tsare,Kai sadiqu tashi ka rakashi,Kuma dama inaso incemaka ya kamata kafara Neman mata ko kuma ni in nema maka dan dole asami me ilmin addini wadda zata fahimtar dakai wasu abubuwan,kaima hankalinka ya kwanta da kyau.


Duk ajiyar zuciya suke sauke bayan barinsu gaban Abban.
" Kai man yanzu ni ina zansami matar aure? Bayan nasan hausawa sunada gori sosai musamman idan suka sami irinmu.

Saida ya daidaita zamanshi cikin motar Sannan yace"Karka damu insha Allah za a samu wacce zatai daidai dakai kuma bazaka sami matsala ba yanzu dai bari muje idan na d'auko baby muka dawo Sai asan abin yi,Amma ai mata basu wahala ta garin ce dai ke wahala yanzu.


Suna tafe suna hira wanda yawanci na karatunan da sukayine kamin su gangaro Akan addini dan Sosai yakeso yaga ya fahimci abubuwa da yawa ,Sai kuma Allah yasa yanada fahimta sosai.




**

Agaggauce ta d'auraye hannuwanta tare da d'aga wayar jin takusa katsewa.

"Wai kuwa aysha ta dawo gidannan kuwa?

" wallahi yaya bata dawoba tun d'azu nake kiranta saitacemin gatanan Amma bata shigoba,Ni bammaso mijinta yazo ya tadda batanan bazaiji dadi ba.

Tsaki yaja kamin yace babu yanda banyi dakeba yarinyar karta fita Amma kikace wai ba jimawa zatai basaikace kin manta aysha da shegen son yawon tsiya to maza ki nemeta takoma gida danni tak'i d'aukar wayata.


Afusace itama ta danna wani kiran.

Zainab na mik'ama wayar yayinda itama ta maidomin ita tana fiddo ido,Kuma maidamata nai itama ta maidomin tana fad'in ke nifa wallahi bazan d'auka ba mama ta zageni.

Cikin marairaicewa nai Sallama.

"Wato aysha kin rainani yanzu ko? Dan gidanku ba cewa kikai kuna hanyar dawowaba? Kenan sai anyi la'asar zaki shigo,Yanzu abbanku ya kira yagama balbaleni da fad'a kumadai kinsan hali ko? Kina nan kina wannan sha shancin shima zai daina kowaki matukar ya fahimci wannan shegen yawon kikeyi,Kinajina ko? Maza maza ki dawo wallahi.


Numfashi na sauke kamin ince wai kai Abba ya koyama mama fad'a wallahi da mama babu ruwanta,Ke me k'unshi zoki wankemin hakanan kitson ma ai sauri a idasa dan Allah.




***

Gudu yai da motar bana arziki ba Shiyasa kamin wani lokaci Saigasu cikin garin kanon Kuma kai tsaye gida suka zarce dan babu lokaci sosai .

Tunda suka shigo Layin ya hangesu su biyu ko wanne da dogon hijab har k'asa ga safar k'afa ga Kuma nikaf anatse suke tafiya duk maitar mutun be isa yafadi wani abu na banzaba garesu,Kai yanayin tafiyarma kawai zai nunamaka akwai nutsuwa wajan.

Aranshi yaji cewa aysha na ciki dan Yasan da wuya idan ba ita bace d'ayar.

Kofar gida suka faka motar tare da zama suna jira.

Tunda ga nesa Dana hango su naji kamar inyi kwana in koma sabida Bansan fad'a gashi Kuma gaban wannan tubabben gakuma zainab.


Rike hannun zainab nai gam kamin ince mata gashinan yazo shida wannan abokin nashi daya tuba.


Sallama mukai musu tare da gaishesu,Da kyar dr.ya Amsa ran nan nashi hade sai wani harare harare yakeyi da alama jiyake kamar ya kaimin bugu lokacin dan dai bashi da yanda zaiyi ne.

"Wuce ki d'auko kayanki mu wuce"

Cisge nikaf din kaina nai kamin na turo baki"Kaji ka.

Wani mugun kishi ne ya Kuma tasomai ganin yanda kyakkyawan fuskata ta bayyana gakuma wani k'unshi daya hanga hannuna,Fatanshi Allah yasa shi kad'ai ya gani.

Hannuna ya d'amk'a yai cikin gidan dani yayinda abubakar da zainab suka bimu da kallo suna dariya.





Labarin JARUMA na kudine.

300.

Acct no.
0005074141,Aisha sabiu ja'iz bank.


Ko ki tuntubi wannan layin.

08142643253.




Haske writer's association.
12/10/20, 2:48 PM - Naffy Aliyu Umar: 49




Hadeni yai da bangon falon Baki ya zaremin manyan idanunshi wa inda suka surka daga farare zuwa ja ja ja.

Sadda kaina k'asa nai ina turo bakina gaba.

"Babyna jikinki ke fitar da wannan k'ashin haka? Cikin sanyin murya yai maganar kamar wanda akasa dole,Shiyasa nakasa banbancewa da wani yanayi yai maganar haka.

Hannunshi d'aya yasa ya matsemin kirji,Har Bansan nasaki ihu ba Sabida zafi dama ciwo sukemin haka kawai.

Da Sauri ya sakeni yana ciremin hijab din" Sorry yi hakuri dan Allah menene meya faru akwai ciwo ne?

Da sauri ya maidamin hijab din jin Sallamar abubakar daga waje,Batare da yajira nabashi amsar duk tambayar da yaimin ba.

"Wuce kicema mama zamu shigo Kuma ki tabbata kin shirya yanzu dan wallahi bazan barkiba kimma rainani aysha.


Da zainab naci karo danhaka muka wuce ciki tare,tanamin dariyar wai mijina yacika kishi gaskiya.



" Yakamata ka rage nunamata wannan zafin kasan dai yarinyace Sannan dole saikabita sannu.

Yamutsa fuska yai yana kallon Abubakar din"Bazaka ganeba yarinyar nan wallahi bataji gabadaya idanunta tsaye suke ni bamma taba ganin wanda ya rainaniba irinta.

Dariya yai kamin yace"Kuka raina juna dai Dan kaima Ai zafinka kake nunamata,Nidai ba wannan ba,Wacece wannan da suke tare?


Tuni fuskarshi ta Washe da farinciki"K'awartace Sunanta zainab Kuma bata da aure ko zaka shiga cikin manema ne?

Dogon hancinshi yaja,Kamin yace gaskiya tai min Ammafa na rantse da Allah tsoro nakeji kaga ni ba bahausheba kadda su hanani ita tsoro nakeji.


"Kai da Allah jibeka da wata magana ta banza haka banda shirme irin naka Ai Abba na nan shine kamar mahaifi agareta dan babanta ya rasu kawai barima mu tsaya mu jirashi ya dawo kawai mu gabatar da kanmu daga baya saiku daidaita da ita,Yo ai babu macen da zata gujeka haka kyakkyawa dakai.

Tokarewa nai daga bakin kofa,Nace tace ku shigo.




**
**
**
" kai Bansan hauka ba cewa nai ku wuceba? Tafiyar dare zakuyi kenan alhalin kunsan hanyar duk bawani kyau ne da itaba?

"Ayi hakuri Abba munason ganinka ne shiyasa,Cewar Dr. Din yana sadda kanshi k'asa.



" To to inajinka lafiya ko?

"Lafiya lau Abba dama abubukar ne yaga zainab shine yace inyimaka magana idan ba ai mata miji ba yanaso ya shiga cikin mane ma.


Tuni ya bude baki yana sakin murmushi" Ah to Alhamdulillah Allah ya sanya alkhairi to zanyi magana da ita mahaifiyarta dakuma can iyayen nata maza Sannan zan tuntubi yarinyar insha Allah babu matsala kome kenan zan shaida muku,Yanzu kui k'okarin wucewa tukunna Bansan tafiyar dare.


Ihu nasaki tare da cacume mama wata irin muguwar kewarta naji Tunda naga tafiyar ta tashi.

Wayyo mama dan Allah ni bazan jeba,Aidama nace bazan komaba wayyo mama dan Allah banzuwa,Abba bazan jeba.

Rikoni yai jikinshi yana Murmushi "Haba JARUMA ta meyai zafi haka? Dan Allah ki kwantar da hankalinki ni da kaina zan zo in ganki idan ankwana biyu,amma yanzu idan kina wannan kukan ai shima Saiyace bazai Kuma kawokiba yi hakuri yarinyar Abbanta.

Ina tirjewa ina komai haka Abba yasani cikin motar Ko sallama da zainab banyiba mama ma bamuyi wata sallama ba.


Tun ina kuka har barci yai awon gaba dani batare da nasaniba.

Juyawa yai yana kallon bayan jin shiru,Dayake yanzu abubakar ne ke Jan motar.

Murmushi yasaki kamin yace rigimammar kawai aiko zaki jima bakizo gidaba yarinya.


" Kajika da wata magana ai tayi k'okari ma,Kasan barin gida babu dadi wallahi sunayin k'okari ma,Kaidai kai k'okarin ganin ka lallabata.


Da hirar yanda zasuyi wajan ganin sun jawo ra'ayin zainab din suka mik'e hanya.




"""*

" Amma alhaji memakon Kaimin magana in hanashi tafiya dan Allah? Ina laifin ya barta ko kwana hudu tayi ko biyar?

"Kudai mata wani lokacin tunaninku beda yawa wallahi,Yo inba hakaba kawai daga kaita taga iyayenta sai ya barta taita zama can aurensufa har yanzu beyi wata d'aya ba aima yayi k'okari daya barta kwana biyun.

" uhum tunda kace hakadai shikenan ni Wallahi Bansan takurawar da yakema yarinyar nan ina lurafa har ta fara ramewa gaskiya yakamata kaimishi magana dan Allah.


Dariya yasaki kamin yace"Kemadai inaga kin zama 'yar saka ido,Inba hakaba wayace ki lura din?Kumama ai ahankali zata saba dashi,Niko babu ruwana wallahi,To ma Sai ince mishi kabar kusantar matarka?
A a bazan iyaba Allah yabasu zaman lafiya ahankali komai zai daidaita tsakaninsu kinga shi yana sonta itako har yanzu babushi cikin zuciyarta,Zaman auren kawai takeyi irin na mutanen da wanda sai tsantsar biyayya Amma babu soyayya,Shikuma yaron nawa memakon ya tsaya ya koyamata sonshi ya tsaya shirme sai shegen bakin rai da zafin zuciya.




**

Wannan tafiyar bansan lokacinda aka cinyetaba,Dan barcina nai sosai Kuma cikin nutsuwa to ni kad'aice baya Kuma kwanciyata nai kamar ina gado balle inji wani abu.

Tattausan hannunshi naji Saman fuskata, Da farko na d'auka kwarone saida na dafe wajan Sannan na fahimci hannune.



Gabadaya duhu kota ina Amma yai amfani da wayarshi Wajan Samar da haske wajan"Taso baby inkuma baki iyawa to saina shigar dake ko?


Kwace jikina nai ina murzar ido kamin in fice ta d'aya bangaren,Dan ya Riga yai wani bake-bake ta nan wajan.

Jikina duk yai tsami haka ya biyoni da jakar hannunshi,Banga wannan tubabben ba Kuma ban tsaya nemanshi ba.


D'akin mama na nufa bayan na watsar da miyan bakina.

Tana zaune saman gadonta tana shafa man zafi a k'afarta na shiga d'akin.

"Oyoyo diyata Sannu da hanya Saukar yaushe haka?

Toilet dinta na shiga na wanko bakina da fuskata,Sannan nafito" Mama yanzu muka dawo ina yini nasameku lafiya?


Riko hannuwana tai"Sann aysha wallahi ko kad'an be gayamin

Please Login or Register in order to submit comment