Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

D'akin maman ya wuce kai tsaye cike da zullumin me zaiji.

"Amin wa alaikassalam likita ka dawo?

" Eh nadawo mama Sannu da gida.


"Yauwa ya aikin?

" Alhamdulillah.

Shiru yad'an biyo baya kamin tace"Ga aysha can yau babu lafiya ashe dama tana ciwon Mara gayacan yau tun safe take kuka.


Abayyane ya Sauke ajiyar zuciya kamin yace"Har hankalina yatashi Amma Allah yabata lafiya bari naci abinci sainaje na samomata abinda zatasha,Amma yanzu ai yayi sauki tunda naga barci ya kwasheta.

"Ameen to shikenan ga shi can na had'amaka idan akwai abinda kake buk'ata Saikamin magana nima kwanciya nakeson yi kaina yaimin nauyi wallahi.



***


" Naje wajan malam yaimin gamsasshen bayani game da Ahmad ,Tabbas Allah ya kawo k'arshen mace macen matanshi Ammafa har yanzu akwai Sauran Rina akaba,Kuma bega ko meneba balle musan matakin d'auka danhaka ni bazan yarda ki auri Ahmad ba alhalin har yanzu bezama mutunba idan kina ganin zaki kuma jiran ko shekara d'ayane to inkuma zaki kawo wanine ki aurenki to yanda dai kika gani.


"Wai sabida Allah hakan da kakeyi kyautawane ? Ace yarinya takoma tana juyaka Saikace itace ta haifeka ba kaine ka haifetaba? Kumama yanzu kai kanada tabbas din zai aureta nan da shekara d'ayan? Saikace bakasan waye Ahmad ba,To nidai wallahi babu ruwana kekuma idan zaki fiddo miji kiyi aurenki to bismillah inkuma zaki tsaya jiran gawon sanu to matsalarki.fuuu tatashi tabar d'akin ranta bace tuni ta dawo daga rakiyar mijinta da 'yan uwanshi akan abinda sukeyima Ahmad da iyayenshi dan ta gano ba komai bane musabbabi Sai hassada.

" Ke dallah kyaleta wani lokacin haka take birkitatta hakuri kawai nake d ita,Ki kwantar da hankalinki dan ko badan Allah ba Sai Ahmad ya aureki indai ina raye,zanga k'aryar iskanci.





Haske writer's association.
12/10/20, 9:13 PM - Naffy Aliyu Umar: Kan madubi na ajiye mishi karikitanshi Sannan na wuce had'amishi ruwan wanka dan nasan lokuta da dama wankan shine abu na farko da yake farayi.

Karo naci da kirjinshi wajan fitowa damk'oni yai ya kuma kankance manyan idanunshi"banganeba inazaki haka baki cud'amin bayana ba?


Miyau na hadiye ina zare ido"Dan Allah kai hakuri Allah ban iya yima babba wanka ba.


"Kwantar da hankalinki dama ni bance kin iyaba,Amma baby nifa mijinki ne bawani abu bane dankin tayani,Sannan hakan zai k'aramana shakuwa da kaunar junanmu pls baby!!


K'ankame jikina nai ina turobakina dan nasan wayau kawai yakemin bawani abuba.


Saida yagama gigitani sannan ya maidoni saman gadon,Daganan bekuma Saurarenaba dan da alama yau din kurma yazama.




***

"Naji kinyi shiru ko sainazo ne?

hijab din dake jikinta ta cire"Haba kaikuma kazo kayi mene din? Ba saika zoba,Kumama banji kace komaiba akan maganar makarantar da naimaka jiya ko baka amince bane?


"Ah aminci mana zee karki damu banda matsala da wannan ai na amince tuni.


K'asa k'asa takemishi dariya jin yanda yakemata magana da hausarshi mara dadi.

"Kinyi shiru?

Turo baki gaba tai itama tana jin haushin nacinshi na tsiya"Nifa fita zanyi yanzu da inda zanje.

"Ok ok to shikenan idan kindawo zan kiraki dan Allah kinji ko,.

ajiye wayar tai tana gyara kwanciyarta,Ba laifi.yanzu tad'an fara jinshi aranta ba kamar farkoba da take ganin kamar ba'a kyauta mataba,To yanzu ga tausayinshi da takeji gara tai hakuri ta rungumeshi dan tabbas tasan zata kwashi lada.


Lumshe idanunshi yai yana murmushi shikenan Allah ya temakeshi zai sami mace ta gari kuma me kunya,Allah ya rufamai asiri leke leken da yayi besa ya auri wataba tabbas da yanzu ana nan anakai ruwa rana akan yanda za ai sabida sabon addinin daya Samu.
Sai maganar mahaifiyarshi data fadomishi,Dayake ya ziyarceta kwana biyu da suka wuce Sam be gayamata zaiyi aureba,Dan bata huce daga fishin da takeyi dashiba na addinin daya canza.




""**""

ina nannade cikin kirjinshi ahankali nake sauke numfashi wani irin daddadan barcine ke niyyar surata.
Ina yanda yaketa boyeni cikin jikinshi saikace kaza me boyen kwai,Ahankali yaketa shafar bayana da kitsona.

"Nagode Allah yasakamiki da alkhairi aysha,Allah yaimiki albarka nagode.

Lamo nakumayi ina rufe idanuna dan wani irin barci nakeji.

kirana yakumayi cikin wata irin malalaciyar murya"Baby"

Turo bakina nai ina niiyar saka kuka"Waikai ka kyaleni barci nakeji fa.


D'ago fuskata yai ya sumbaci libs dina kamin yace"ai tashi zakiyi muyi wanka tukunna kumama inajin yunwa.

Kuma gyara kwanciyata nai ina turo baki.Tunanin irin murzar da yaimin yanzu ya fadomin tare da uban sambatun da yaita zubawa,Saikace yaune na karkon yi.

tureshi nafarayi ganin yanda yake kuma lalubata,Yanzu kam da tsiya komai ya wakana nai kuka har idanuna saida suka canza,Jikina yaiwani ligi ligi dani ga zufa ga hawaye jinake kamar in bude bakina inta ihu kokuma in runtse idona idan na bude inganni kan gadon mama,Waima abinda akeyi cikin auren kenan? Daga girki sai aikin gida dakuma wannan wahalar? Shin kowane namiji ne haka kokuwa Dr ne yake haka?

Hannuna ya dumtse cikin nashi kamin yace"Kowane namiji da kalar halittar da Allah yaimishi baby nikan haka Allah yayoni da yawan sha'awa Tausayinki da nakeji shike sani d'agamiki k'afa amma da kinsaba dani sosai sosai shikenan kiyi hakuri kinji?

Hannuna nasa na rufe bakina dan Sam banyi tunanin maganar da nakeyi da zuciyata ta fitoba,Ashe yajini.


Yanzu kam Saida ya temakamin sabida jigatar da nayi,zuciyata zillo kawai takemin akan inyimishi Allah ya iSa Amma wata zuciyar na hanawa.

Da kanshi.yaimin wankan Sannan shima yayi,Duk motsin da zanyi idanunshi na kaina damun hada ido ya sakarmin murmushi.


Saida yai alwalar la'asar Sannan yafita nikuma nakoma falo gobobina sai ciwo sukemin kuma har lokacin ban dainajin yanda nakejin wata guntuwar sha'awar ba.

Wani tsaki nakumaja ina yamitse fuska,Daidai shigowarshi cikin falon.

Zama yai gefena yana kamo hannuna"Sorry baby nineko? Bari inci abincin.

"A a yi zamanki ai zansawo dakaina tunda kin had'a sannu.

Kunya tasani daina kallonshi musamman danaji ya dage yimin Sannu.



Cin abincinma haka yayishi a lalace saidai naman danaga yanata tsinta zuwa gidan na fahimci yanason nama sosai musamman farfesu.



Dare.

"Aysha tashi kije ki kwanta karma mijinki ya shigo ya tadda bakinan kinji ko?

Marairaicewa nai kamin nace"wayyo mama kibarni nan dan Allah.

Zargintane ya tabbata dan dama tun shigowarta gidan ta lura da yanda jikina yaiwani sanyi gakuma idanuna da suka nuna alamun nai kuka,Gashi kuma yanzu ina fadin bazan koma bangarenmuba.

Zama tai gefena tare da dafani"Kinga aysha hakuri zakiyi kowace mace da kikasani saida ta wuce wannan qalibalen danhaka kiyi hakuri balle kuma ke irin mijinki mara hakuri,Yanzu ki kwanta nan ki huta idan ya shigo gidan saiyazo nan ku wuce, Ni bammasan inda suka shigeba shida Salim kokuma suna kan hidimar abubakar ne oho.



Agajiye yashigo gidan. Bewani yi mamakin rashin ganinaba dan lokuta da dama yasan dama wajan mama nakan jima musamman idan be gidan.


Anatse yai wanka yafito,yafara tsane jikinshi kenan yaga an gitta ta gabanshi,Saidai bega komaiba sai kawai ya share yacigaba da abinda yakeyi.

Da mamaki ya waiga ya kuma kallon gadon"Ah baby yanzu kika shigo ne?

Shiru babu magana.

Matsowa yai gaban gadon abinda yagani ne yai mummunan tashin hankali.




maman khadija.


Haske writer's association.
12/10/20, 9:17 PM - Naffy Aliyu Umar: Wani irin tsalle yai saigashi can wajan k'ofa tabbas shidin namijine amma be yadda da irin wa innan abubuwan danshi hidima indai akwai jinnu ciki to tsoronta yakeji,.

Uwar jikin gaba d'aya na ayshan ne kamar yadda yagani Saidai daga wuyanta zuwa kai bai isa yace na wace kalar dabba neba shiba na jaki ba kuma bana tinkiyaba .Jikinshi babu inda be tsuma haka ya fice kanshi na wani irin sarawa tun farkon ganin abun.

Kai tsaye d'akin maman yashige dan tasota taje taga yanda babynshi ta koma,Amma me yana shiga ya hangeni kwance saman gadon maman hadda rufar bargo.

Kirjinshi yai wata irin bugawa,Dan yakasa banbance wacece ta gasken.

Ahakali ya dinga matsowa har saida yaga fuskata fes Sannan ya sauke numfashi gadon ya haye tare da shigewa cikin bargon ya manne da jikina har kirjinshi be bar bugawaba .


Sanyi da lema lemar danaji yasani bude idanuna,Dayake d'akin yai duhu yanzu shiyasa banga fuskarshiba Amma k'amshinya kawai ya sanarmun da waye.

Cikin muryar barci nacemishi"Tashi muje kaci abinci.


Mak'alkaleni yai kamin yace a a bazaniba banjin yunwa bazanciba.

Lamo nai cikin jikinshi ina adduar Allah yasa karyace zaimin wani abu dan wallahi nagaji.

Shiru shiru banji yaimin komaiba Saima kirjinshi danakeji yana wani irin bugu kamar dai wani abu ya firgitashi haka.


Barcina nai na gasken gaske Amma shiko kusan kwana yai mutsu mutsu harda mafarkin suffar matarshi ta canza daga ta mutane.




""""
"Banga ahmad masallaciba lafiya ko?

D'an jim tayi kamin tace gaskiya ban saniba danni jiya har na dawo nan be shigo gidanba ammadai bari na dubo dan jiya d'akina nabar matarshi ko yaje sun wuce to bandai saniba.


Awahalce ya wayi gari dan tun cikin dare wani irin zazzabi ya sakko mishi ga ciwon kai shiyasa ko danatashi sallar asuba. Nikadai nai abuta dannasan ba iyata zaiyiba,ga ciwon kai,Idanunshi sunyi ja kuma jiyoyin kan duk sun tashi.


Ya hanani ko kwakkwaran motsi dan yana makalkale cikin jikina yabari inkira mama ma yaki jikin nan saikace dahuwarshi akeyi.

Hawaye ketabimin fuska bansan nadamu da Dr.ba sai yanzu dan sosai naji hankalina yatashi bayanshi naketa shafawa ahankali inayinishi addua dannasan ita kawai yake buk'ata balle daya hana aje a kirawo wanda zai temakamishi.


Muna cikin wannan yanayin naji Sallamar mama ajiyar zuciya nasauke ina zare idona dayake d'akin akwai ragowar duhu musamman da labulayen ke rufe ruf.


"Aysha"

Muryata shake nace nace mama ganinan yaya ahmad ne beda lafiya kuma ya hana intashi in kiraku.

Subhalillahi garin ya haka yaye bargon tayi aiko wani hucin zafi yai sama danni dama zufa nakeyi sabida yanda zafin jikinshi yaima nawa yawa gakuma rufa.

Da kanta ta je ta d'aukomishi jallabiya da gajeran wando. Sannan ta dawo d'akin har lokacin yana manne da jikina ko yaya na motsa saiyakuma likemin.


Lambar abubakar abba yakira dayake dama yana gidan nan yake kwana wajan Dr.Na samartaka ne yaxama nashi yanzu.

Drip yafara sakamishi da allura,Sannan na lallaba nabar gadon Saikuma mukai cirko cirko tsakiyar d'akin dan daga gani yanajin jiki balle kuma damuka yanda lokaci zuwa lokaci yake jujjuya kanshi alamun akwai abinda ke damunshi duk da cewa barci ya d'aukeshi.


Har tara nasafe babu wanda ya motsa cikinmu,Balle ai maganar neman abinda za a karya dashi,Garama abubakar daya kira salim ya gayamishi,Kuma ciwon saiya bashi mamaki dan jiya duk gantalin da Dr yayi tare suka yishi kuma beji yace wani waje namishi ciwo ba.



***"""***


Zaune take gefen gadon manyan idanunta masu tsananin haske ta haske fuskarshi dasu tanamai wani irin kallo wanda zai nuna ysantsar soyayyarta gareshi,Magana tafara cikin sassanyar miryarta" Ba cutane ya kawoni garekaba Ahmad ni masoyiyarka bansan zaka tsorataba da ban fitomaka ta wannan suffar ba,Nima macece kuma babu abinda matarka zata nunamin zan yimaka dukkan abinda kakeso zanyimaka biyayya iyakar iyawata zan haifamaka yara Amma inaso ka saki matarka ka zauna dani ni kadai na isheka rayuwa kaji ko?

Fes ya bude idanunshi akanta macece kyakkyawa da ita saidai tacika tsawo sannan tafi kama da kakirata da inuwa.

"Nasan keba mutun bace nikuma mutunne dabhaka kifita hanyata kibarni in zauna da matata ina sonta soyayyarta daban take cikin zuciyata, Dan Allah kifita rayuwata!!!


"Hahhhaha bazan iyaba Ahmad da zan iya kuwa da tunda aka haifeka nayi.danhaka ina sonka kuma kaima dole ka soni, Bazan cutar da matarkaba tunda kqnasonta taci albarkacin son da kakemata saidai bazan kyalekuba zancigaba da shiga tsakaninku har saika saketa Ahmad,Dogon hannunta ta kawo da zummar shafar gabanshi,Aiko dawani irin ihu da zabura ya farka.


Nida mama har rige rigen danneshi mukeyi dan karya cire allurar.

Salim ne ya matso kusa dashi yana kiran sunanshi,Sai ahankali ya fahimci su waye cikin d'akin,Idanunshi ya sauke akaina saiyaga idanuna duk sun jeme alamun nasha kuka,hannuna ya riko tare da zaunar dani gefenshi,sorry baby kukan me kikeyi haka uhum?

Wasu hawayenne suka cikomin idanu Amma na hanasu zubowa.


cire allurar yai ya maidata jikin ruwan sannan ya kalli salim"Temakamin salim banyi Salla ba.

Duk tsoro yakuma kamamu ganin be iya mikewa saima wata irin rawa da jikinshi ya d'auka.



Rike salim yai kam cikin toilet din tare da saka kuka zuciyarshi tariga ta karaya yagaji da wa innan abubuwan dake faruwa yajima beji wanda k'addara take wahalwaba kamarshi,Godiya yakamata YAIMA Allah kokuwa sauki yakamata yafara nema?

Rungumeshi Salim din yayi yana tayashi kukan batare da ya tambayi meke faruwaba.
Kusan salim din yatayashi wankan duk da yaso ya kira matar tashi amma Dr ya nuna bazata iyaba sabida shikadai yasan abinda yakeji jikinshi,Shiyasa sukai amfani da tawul ya gyara jikinshi Sannan yayo alwala.


Abba da abubakar sundawo dayake dama rubutu sukaje amsowa,Dacan Abba irin mutanen ne wa inda suke ganin komai camfi ne kokuma rashin yarda da wani abu daya danganci jinnu Amma sanadiyar Dr duk ya sadida yanzune ya tabbar da cewa mutun ko aljan na iya cutar da wani mutun Ammafa da IZININ ALLAH,shiyasa addua tazama dole akan dukkan musulmi.


Ina gefen mama ina sharar kwalla har lokacin yayinda itama takejan ajiyar zuciya dan duk munji kukan da sukayi cikin bayi.

Sabanin abba da abubakar da basu jima da shigowaba.


Azaune yai Sallar sannan mama takawomishi tea me kauri,Saidai hadiya daya yai yafara kakarin amai.


Abbane yabashi rubutun,yqnabata fuska yana komai saida yashashi shifa sam besan irin wa innan abubuwan,Gara abashi adduar yayi abinshi da kanshi.


Ganin ya kwanta yasa duk muka fice falo akabar salim kadai kusa dashi.

Ahankali yake labartamishi abinda yagani jiya da dare dakuma mafarkin da yayi yau da safennan kamin,yafara wata irin jijjiga yana murde mirde.





Labarin jaruma na kudine.



Haske writer's association.
12/10/20, 9:19 PM - Naffy Aliyu Umar: Rikeshi yai jikinshi yana hawaye tare da tofamishi duk adduar da tazo bakinshi,Wannan wace irin jarabawace haka me matukar nauyi lallai bawa ba'abakin komai yakeba.

Ahankali rawar da jikinshi keyi tafara lafawa har ya fara sauke numfashi alamar barci zaiyi.

Hawayenshi ya share kamin ya fita falo inda mukai dako dako muna jiran fitowar salim din.

Ragwaf ya zauna yana dafe kanshi"mama wannan karon fa ahmad na bukatar tsananta addua dan gaskiya akwai matsala bakuga abun da ya dingayi ba yanzu danhaka yakamata duk mutashi daga barcin da mukeyi.


Shiru falon ya d'auka kamin Abba yace yanzu me ya kamata ayi to?

Ganin da nayi d'akin yai shirune yasani fadin"Abba mezai hana a yawaitamishi sadaka? Sannan ayimishi saukar alkur'ani sannan akwai addu'o,in da ake tofawa cikin ruwan sama kona zam zam dan korar shaidanu wannan abun da yakeyi yanzu hadda sharrinsu.


Anan kowa yai na'am da wannan shawarar kuma mazan suka fice neman abubuwan bukata.



""**""

Gidan cike yake da danginsu na uwa dana uba Sai yanzu ne na tabbatar da cewa dr.d'an dangine kawai dai basu da son zumunci ne,Inkaga dan uwanka gidanka to wata hidima ake amma haka kawai basu cika ziyarar kowaba.


D'akin maman babu kowa sai salim da keta rafka gyangyadi zaune saman kanshi,gabadaya ya zabge ciwon kwana daya kawai,Damma namijine Amma sam ko hayaniya beso yanzu shiyasa duk aka koma falo.


Da sallama nashiga cikin d'akin hannuna da kwando wanda aka shirya duk abin buk'ata na abincin.

Ahankali ya bude idanunshi ya zubeso kaina,Nan da nan na nemi rudewa danwani daburcewa nayi nafara kame-kame.

Murmushi yasaki kamin ya mikomin hannunshi.


Ahankali na matsa wajanshi tare da mikamishi nawa hannun"Baby fitsari nakeji kuma inaso na watsa ruwa.

Cikin jin dadin yafara samun sauki nace nace"To bari in hadamaka ruwan sai salim ya tayaka yanda kukai d'azu.

Mirmushi kawai yasaki yasan magana ce na gayamishi.

Rikeni yai kam bayan nafito yana kallon cikin idanuna"Baby rigimarki yawane da ita temakamiki yaifa yaga kinata kuka kin fice hayyacinki,kina ganin Mijin ki zai wuce ya barki ko?

Kauda kaina gefe nai ina turo baki.

Hannu yakai ya faski kuncin salim dake barci yana fadin "dallah tashi baho kawai haka ake jinya dama ? Kawani saki lebe kana jan munshari ko?

Murmushi kawai yai yana kallonshi,yayinda cikin ranshi yaji dadin ganin sauyin da jikin yayi.

"Wanka nakeso inyi gashi kuma yanzu baby tace ita zataimin ya kenan?


Da sauri salim din ya mike yana fadin"Ah Allah yabaku hakuri yo meyai zafi barima in koma falo.

Bakina har rawa yake wajan fadin dan Allah ka tsaya wallahi karya yakemin.


Wata dariyar suka d'auka kamin.salim yace"Aysha mijinki ne kemiki karyar ko? Ya idasa maganar yana ficewa daga d'akin kuma be bar dariyar ba.


"Shikenan na korar miki shi muje ki wankeni 'yammata.


Duk da wannan tsokanar da yakeyi Amma jikinshi ruf yake da zazzabi k'arfin haline kawai irin na namiji.


Duk sunne sunnen kan da nakeyi ahaka saida naimishi wankan inayi yana yarfeni da ruwan saida ya jikeni sannan hankalinshi ya kwanta.


Da kanshi ya rubuta wasu magunguna yace salim ya siyomishi.
Sai lokacin 'yan dubiyar sukafara gaisheshi dan falo yakoma.

Duk inda nai idanunshi na kaina kuma damun hada ido sai ya kashe ido daya saikace wani d'an duniya,Shiyasa duk saina kasa sakewa saima lafewa jikin mama danayi.


Haushi da takaici ke cimin zuciya dan ina lure da duk yawancin 'yammatan nan idanunsu na kanshi dan dama kwanaki saida ya hannatu tacemin duk yawanci sonshi sukeyi haddama wa inda suka hakura sukayi aure , mutuwar da matanshi keyi ne kawai ya hanasu fiddo maitarsu fili dan iyayensu ke hanasu nunawa ma.

hada ido nakumayi dashi aiko na wurgamishi harara saikace idanuna zaso fado.


Bakinshi ya bude yana kade halshenya kamin ya girgiza kanshi fuskarshi cike da murmushi.



""**""

"Wallahi yau danaga ya ahmad sainaji nakuma mutuwa kanshi gaskiya matarshi ta more wallahi insha Allah dana shiga zan fitar da ita dan da alama ba k'aramin so yake mataba.

"Aikuwa wallahi danni duk wannan zazzafan kallon da yakema ina kallonsu sainaji ma sumbani sha'awa dama ance miskilin namiji yafi iya soyayya dan Akwai mutuwa akan duk wacce sukeso.


Da wannan hirar ko wanne ya nufi bangarensu,Ummi ce dakuma wata diyar k'anin baban ahmad din mesuna shukura.

Ita kanta shukurar ahmad din takeso dan dai ita da sauki bata zafafa ba kamar ummin sannan ita tana sauraran wasu samarin.



. . ."Kai Allah yasani naji tsoron ciwon yaron nan Amma kaga yanzu luf kamar ba shiba ko?


"Kedai bari kawai ai malam sunusi ya gayamin cewa yanzu beda wata matsala saita jinnu kuma dole dai an dage da addua kamin su fara wahal dashi ko iyalinshi,Kinga yakamata ki kora yarannan hakanan naga su basu niyyar tafiya kaddafa suce zasukai.dare su masu d'an uwa kowacce tazo da guntun hawayenta kamin ajima kuma anfara shewa kai mata ko???


Dariya tasakI kamin tace kajika da wata magana auta sukutun babu lafiya ai dole su rude,Ni kaina aruden nake ai.

Hirarsu suke cikin raha sabida 'yar nutsuwar da suka samu ba kamar yinin yau ba.



""""

"Wai kuwa kina gyara jikinki kuwa aysha?

Turo bakina gaba nai ina zare ido"Ya halima Allah ina gyarawa kumamafa wahala kawai yakebani,Nidai zan dinga gyarawa zuwa nan gaba Amma wallahi yanzudai akwai matsala.


Dariya suka Sakamin kamin ya hannatu ta saba yaronta da take goyo"Shikenan bari abari har ki kuma sabawa kinsan mazanne dole saida gyaran balle irinsu auta 'yan zalama dole saikin jure kamin kisaba dashi.

Godiya naimusu sukaimin sallama dan lokacin har an fara sallame Sallar isha'i.




""***"

Anatse nai shirin barcina na fesa turare tare da hayewa gado ina addua,Hutun kawai nakeso dan gaskiya yau nagaji sosai.



Haka kawai ajikinshi yakejin kamar ana binshi.domin sawunshi har wani nauyi sukemishi,Sam beyarda ya juyaba balle yaga abinda zai.tsoratashi ko tashin hankalinshi.


Saida yai addua,sannan ya shigo d'akin.

Ahankali naji yana shafar fuakata dole na bude idanuna wa inda ke cike da barci.

"Tashi muje ki rakani wanka wallahi tsoro nakeji.






Haske writer's association.
12/10/20, 9:22 PM - Naffy Aliyu Umar: Da wani irin mamaki nake kallonshi kamin nace tsoro kuma?

Kuma marairaicewa yai kamin yace"Eh mana jinake ana bina nasan kuma ina shiga bayin zata kallar miki abubuwa gara muje ki tsare abinki ko?

Harararshi nai Amma cikin zuciyata dariya nake,Sam mutun bazaiyi tunanin zai iya maganganu irin wannan ba tsabar yanda yake gwada miskilacinshi.
Koda yake ai dama taken mune mu mata namiji duk masifarshi saiya rusuna gaban macen da ta amsa sunanta na mace.

Yes akwai maza marasa mutunci ko masifaffu,Amma wallahi matukar mace tasan kanta zata iya gyarashi kuma su zauna lafiya.

Misali mijinki wutane tsabar jaraba da masifa, To kekuma in kikatashi saiki koma mishi ruwa ruwanma me shegen sanyi,Wallahi duk fad'anshi wataran saiya daina matukar kinyi hakuri.


idan mijinki me shegen son kudine da mako,To babu boka balle malam tsananin biyayyarki gareshi zaisa kunya ta dinka kamashi yaimiki abu koda beyi niyyaba.

Idan kuma dangin miji ne Hummm inkin tashi dan Allah kibawa banza ajiyarsu ki dinga rayuwarki kamar duk basu sun mutu wanda yai dake kiyi dashi wanda beyi dakeba share banza kiyi rayuwarki domin bazaki taba yimusu daidaiba duk abinda zakimusu saisun zageki matukar ba nacikin novels bane😂.

"Kinyimin shiru fa?

turo bakina nai kamin nace to wai kai dolene wankan? Yau dinnan kai wanka yakai biyar ka hakura mana sai gobe.

Bata fuska yai kamin ya d'agoni gaba daya"Bazan iya kwanciya banyi wankaba kuma babu ruwanki da iyakar wankan da nayi dan anjima ma saina kuma wani idan nagama sunna tashi muje.


Nasan ba kyaleni zaiba shiyasa sai kawai na mike nariga nagaji ne sosai sabida zirga zirgar danasha cikin gidan ga aikin girki tunda mutane da yawa damma Allah yasa sai akai miyar farko da yawa,saiya kasance da abincin ya k'are sai kawai a maida fara ayanka kayan lambu.


Cikin nutsuwa na had'amishi,Amma daya taba sai

Please Login or Register in order to submit comment