Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dakewa zakayi kawai kajemata amatsayin miji kawai kadda ka kuskura taga gazawarka tun yanzu wallahi kaja girmanka ka nunamata kai namiji ne kuma Kaine sama da ita dole zata sauke duk abinda ke kanta.

" To shikenan zan ko karta insha Allah.


Innalillahi wa inna ilaihirraji'un kallacan salim ga aysha dincan ta haukace.




Last free page.


Acct.no
0005074141,Aisha sabiu ja'iz bank.

Kokuma mtn cart.
08142643253.

Littafin JARUMA na kudine ki biya d'ari uku kacal danki mallaki naki.
300.




Haske writer's association.
12/10/20, 7:52 AM - Naffy Aliyu Umar: 23.



Tsananin firgici yasa motar Neman kwacemishi dakyar yasamu suka daidaita gefen titi suna maida numfashi gudu gudu sauri sauri suka isa wajan mahaukaciyar wadda take da shirgin kaya akanta sai tsince tsince takeyi babu abinda ya dameta.

K'okarin rikota Dr. Din keyi Amma salim ya hanashi sabida shi kanshi ba k'aramar tsorata yai ba.
"Ciro wayarka maza ka kira Abban muji meya faru yaushe tasamu lalurar da har tai wannan dattin kalli k'afatunta fa Amma tabbas itace towai meya faru?

Neman lambar da suka tsaya yi yasa suka nemeta suka rasa abin kamar almara dole suka ajiye wayar suka fara nrmanta da inda ta shiga Amma ina kamar allura cikin ruwan kogi kome kalar ta basu kuma ganiba.

Wajan awa d'aya suna gantali ad'an rukunin hadda tambaya suka dinga hadawa amma ina ko giccinta babu.

Dole suka koma mota,Da sauri ya balle murfin robar ruwan daya d'auka ya kwankwada har lokacin maida numfashi yake ga jikinshi dake rawa.
" Ka kwantar da hankalinka bari mu k'arasa insha Allah babu matsala Allah zai warwaremana komai kaji ko? Cewar salim shima yanakai ruwa bakinshi.


Cikin rashin kizari suka idasa unguwar Wanda akofar gida suka tadda Abban Wanda ke tare da wani da alama magana sukeyi.

Mamaki yakuma kamasu ganin Abban cikin walwala bakamar yadda suka zataba.

"Yanzu kuke tafe sannunku da zuwa,Malam barau kaje kawai zanshigo kasuwar anjima insha Allah sai in duba.

Da kanshi yaimusu jagora cikin gidan" Ku shigo nan Ku gaida mamanku saiku huta kasha jiki amadu duk ka lalace.

Akunyace sukebin bayanshi har zuwa falon maman.

Akunyace suka gaisheta kamin Abban ya kaisu falonshi,Anan suka kuma duk'awa har k'asa suka gaidashi tukunna,Ya amsa musu cike da walwala"Ainaso in zo da kaina in dubaka to saikuma wasu dalilai suka hana dan Allah ka kwantar da hankalinka duk abinda kaga yasamu bawa to da sanin Allah idan lokacin wucewar qaddarar ka yayi saikaji shiru komai ya wuce saidai labari,Bari in taso maka ita yau kwance take tun safe sabida ciwon Mara.

Agaggauce suka kalli juna saikuma suka sadda kawunansu k'asa.


"Ayi kokari Asama musu abinda zasuci ina ita ayshan take har yanzu jikin be fada bane?

"A a taji sauki barci tayi tana cikin d'aki.

Cikin barcina naji muryan Abba na kwalamin kira .
Ahankali na bude idanuna wa inda sukaimin nauyi tsabar kukan danasha yau dan nasha wuya sosai.
Hannuwana ya kama natashi zaune ina tabe baki zan saki kuka.

" Sannu Allah yabaki lafiya kinji tashi kije ki gyara jikinki ga mijinki nan yazo daganan ma saiya rubutamiki magani yanzu zanje kasuwa in dubomiki seti masu kyau da tsada saiki hada Dana 'yar uwarki ko?
Kaina kawai na d'agamishi tare da mikewa nashige toilet.



"Nafarajin tsoro salim anya bawani abun zai faruba kaji fa? Kuma wallahi wannan yarinyar aysha ce .

" Nikaina nai mamaki wallahi Amma tunda naga mun nemeta mun rasa naji araina wani abunne Amma mataki daya dazamu d'auka shine Addua dole mudaina barci Ahmad dole ka dage da ibada azumi da sauransu Sannan sadaka mu tsanantata Allah ya bayyana dukkan abinda yake boye kasan ita sadaka tana tunkude dukkan bala'i da masifa sannan maganin dukkan wata lalurarce wadda tafi k'arfin magani.

"Na yarda salim na amince wallahi ni kaina nafarajin tsoron kaina bansan wace kalar masifa ce ke bibiyar rayuwataba Amma insha Allah zan dage.

Shiru sukai lokacinda sukaji sallamata.

Dawata sallamar nashiga cikin falon hannuna da ruwa da lemona,Kamar yadda nasaba saida na duk'a na gaishesu Sannan na fice na d'auko dambun nama Wanda maman tace indawo in d'auka.

Ajewa nai gabansu kamin in koma gefe na takure dan ganin abun nake wani banbarakwai gakuma ciwon Mara da har lokacin ke sadakata.

Har hada baki suke wajan fadin " Ya jikin?

Banza nai dasu gaba daya sai hannuna Dana cusa k'asan marata.

"Kai ka matsa kaimata sannu kuma ka lallasheta kalli fuskartafa daga gani yau tasha kuka, Bari infita waje kaikuma kayi abinda yadace,Duk cikin rad'a yai maganar sabida kadda inji besan wani shegen kunne ne daniba.


Ilai ko yana fita shikuma yataso ya matso kusa dani,Kai lallai namiji Sam beda kunya wlh.
Hannun dake k'asan marata yafara laluba zai jawoshi.

Arazane na d'ago kaina tare da kallonshi,Aiko muka hada ido,Kuma sadda nawa nai ina kallon hannunshi dole na fiddoshi waje kadda inje ya tabomin inda ban zataba.

" Kinaji ina cewa ya jikinki amma kika shareni kin manta matsayina a gareki ne?

Tuni idanuna sun ciko da kwalla to dama me Neman kukane aka jefeshi da kashin awaki.
Be fargaba saidai yaji shesshekar kukana natashi.

K'okarin rungumeni yafara nikuma ina turjewa dannaga bawai ta ido gareshiba.
"Ki tsayamana duba marar zanyi bawani Abu zanyimiki ba.

Turo bakina gaba nai ina ja baya daga jikinshi"To ka tsaya daga haka mana basaika matso inda nakeba.

Kanshi ya shafa kamin yace " Baki sanni bane ko cutar dake zanyi?

"Nasanka mana Amma mene na tabani to?

" Waye ni?

Dan harararshi nayi kamin ince wayefa daya wuce mijin yaya fati.


Murmushi kawai yasaki kamin yace to yayi kyau,Wane kalar magani kikasha?

"Ni babu maganin da nasha.

" OK yafara zubane abin?

Kauda kaina nai tare dayin shiru.


Inajin sautin murmushin da yayi kamin ya kuma matsowa wajena.

Da sauri nace nifa be fara zubowaba.

"Ok.
Rubutu yai a wayarshi kamin ya maida ya ajiye yana kallona" Sorry bari akawo allura inyimiki saikisha magani.

"Ni wallahi bansan allura jiyama ba saida akaimin wataba.

Be tankaminba saima sauka da yayi ya jawo danbun naman yafara ci hadda wani lumshe idanu.

Muna nan zaman shiru shidai wayarshi yaketa latsa,Yayinda nikuma nake takure sabida juyawar da marata kemin har lokacin.

Sallamar salim tasa duk muka kalli kofar.
Daga bakin k'oafa ya tsaya tare da mikomishi ledar.

Kuka nasaka ganin yana hada allura ni ma zafin alluran ke gabanaba wurin da zaimin nake tunani.

Wani murmushin gefen baki yai kamin ya jawoni jikinshi,Dagabada da hijab din jikina ya cukuikuyeni saigashi ko motsin kirki nakasa zama yai sannan ya dorani saman cinyarshi yad'an kifani akirjinshi,Saidai kawai naji shigar alluran dan ko bude wajan banji yayiba.

Wata shegiyar tsuwwa nasaki kamin kuka ya biyo baya.

" To gashinan mijin Fatima yaimiki allura kuma nasan anjima kadan zaki kira mijin fatiman kimai godiya tunda ya temakeki ni tasar ni dallah raguwa kawai me bakin kuka.

Jinai kamar inta jeramishi Allah ya isa lokacin Amma ba hali dan cikin k'ankanin naji wata hajijiya na yawo dani kamin in ankare saidai naji nakoma jikinshi.

Kwantar dani yai sannan ya kira Salim ya dawo sukaci gaba da hirarsu kamin Abba ya dawo Sabida sunaso su gayamishi abinda suka gani ko Allah zaisa shima akwai wani temako ta bangarenshi.



**

"Kuyi hakuri Dan nashiga runtsumine bayan barina nan inafatan babu matsala kunci abinci ko?

Kowa kai a k'asa suke amsawa sosai sukejin nauyi da kunyar Abban.

" eh Abba babu matsala munci abinci tun d'azu dama muna jiranka ne zamu wuce to kuma akwai wata matsalane shine muka tsaya jiran da wowarka,Cewar salim.


"OK to to inaji Allah yasa lafiya Ammadai bari ince nadawo tukunna dan yunwa nakeji.

Duk murmushi sukai suna kuma sunkuyar dakai,mamakin halinshi suke babu ruwanshi.


Shigowa nai cikin falon da sallama hannuna d'auke da kayan abincin Abban.

Sannu na zuwa nai mishi, Yayinda shikuma yake tambayata ya jikin?

" Abba naji sauki mijin ya fati yaimin allura kuma nasha magani.

Duk da kallo suka bini bayan na juya mamaki ne ya kama Abba jin sunan Dana kirashi dashi yayinda sukuma kunya takuma lullubesu.


"Karka damu hadda kuruciya ahankali zata fahimci komai.


" Abba dama d'azu wajan zuwanmu nan ne farkon shigowa gari kawai mukaga aysha cikin hali na hauka mun tsaya harma Dr. Saida ya tabbata Saidai kamin wani lokaci muka nemeta muka rasa tokuma saimukaga ta nan lafiya lau,To gaskiya abin ya d'auremana kai gaskiya
12/10/20, 7:53 AM - Naffy Aliyu Umar: 24




Subhanillahi!! Ikon Allah to to kuma kun tabbata itan ce?

"Eh Abba wallahi ba kamaace itance muka gani,Kuma shi Ahmad ma har saida ya kama hannunta Amma kuma garin Neman wayarka duk sai mukaga batanan.

" Ikon Allah to Allah kyauta yakuma kiyaye gaba ,Allah ya karemana ita yanzu inaga be wuce sati biyu ba ta gama saikaje kafara shirin tarewarta karka damu zansan abin yi kaidai kaje ka dage da Addua Salim adinga tayashi da addua insha Allah komai zai warware,Kutashi Ku wuce bansan tafiyar dare bari inyimata magana saikuyi sallama.


Tsaye nai gaban inda yake zaune ina kallon can wani waje daban Amma kuma inajin yanda idanunshi ke yawo akaina.

"Kanwata haka zamuyi sallamar bazaki bani wata zazzafar kulawaba kindai sai ni lafiyayyen namiji ne ko? Kuma inada buk'atar kulawa ko?


Turo bakina nai gaba ina harararshi yau kawai nafara fahimta Dr. Beda kunya Amma idan bakasanshiba bazaka taba yin wannantunanin akan shiba, Sabida kallon farko da zakaimishi zakace miskiline Wanda ko magana zataima wahala,Amma ni gashi daga aure yashiga tsakanin mu harya mance da cewa ni k'anwar matarshice yana gayamin abinda yaga dama.

Harararshi nayi tare da kauda kaina.

" Humm zan kiraki anjima inji ya jikin idan kina buk'atar wani Abu ki dinga gayamin dan Allah tunda yanzu hakki nane kinji ko?

"To,Kawai nace tare da wucewa zanshige gida.

Duk kallo sukabini dashi kamin salim ya kira sadiq Wanda dawowarshi daga islamiyya kenan yabashi wasu ledoji yace yakai cikin gida tare da bashi kudi wai su raba.



***

" Abbansu lafiya kuwa tunda yarannan suka tafi nakejinka shiru lafiya ko? Ko akwai wata matsala ne?

Yasan idan ya gayamata sai hankalinta yafi nashi tashi don dama har yanzu yana lura da ita cewa atsorace take da auren dan ranar da ayshan tafara ciwon Mara hadda kuka wai ko mutuwa zatayi,Dagabaya da yaimata dariya cewa tayi kasan ance idan maciji ya sareka to ko bakar Leda ka gani zaka ruga.

Murmushi ya kakalo kamin yace tunanin yanda zamu tsara tarewar aysha nakeyi kinsan takusa gamawa d'azuma kan setinta nashiga kasuwa.

"Wannan ai ba abin damuwa abbansu tunda komai munadashi alhamdulillah ni indama zakaji ta tawa danace kawai ba sai anyi taroba,Kawai nan da sati uku yazo ya d'auki matarshi kokuma kai ka rakata ko yayunta tunda abun duk anzama d'aya.

" Eh nima nai tunanin hakan danhaka ki dai tayamu da addua dannasan ita aysha bata da matsala so insha Allah banjinta zanyi waya da iyayen Ahmad din kome kenan sai in gayamiki.

"To babu damuwa Allah ya kaimu lokacin lafiya.

Tsam yatashi yabar gidan dankuwa bega ta zama ba.




***

" Gaskiya kayi sa'ar surukai wallahi Sam basu da matsala tabbas yanzu samun irinsu zaiyi wahala yanada fahimta sosai mutumin.

"Hakane salim gaskiya alhamdulillah mamar ce dai da fari ta nuna bataso tun auran marigayiya to kuma dayake yafi k'arfin gidanshi saita hakura,Amma wannan ma anacemata an d'aura auren ta yanke jiki ta fadi saida ta yini asbt sannan tadawo hayyacinta to dai inaga ta hakura tunda gaka yanda ta karbemu yau babu wata matsala.

" Kai ai tai kokari Dr. Wallahi amata ba kasafai za a samu wa inda zasu iya wannan abun ba tab gaskiya ka k'ara rikesu amana Ahmad banda wauta.

Insha Allah zan kiyaye salim Ammafa wannan karon nace gaban mama zan zauna nagaji da yin nesa dasu.

"Eh hakanma yayi kaga zasu debema juna kewa,Ammafa abinda yafaru yaban mamaki wlh anya ba abinda ke kashe matanta jikinka yakeba kuwa?


Kallonshi yai kamin yace kafara tunanin da nakeyi kenan? To wallahi nimanan tunanin da nakeyi kenan wallahi naji rasuwar Fatima fiye da yanda zan kwatantamaka tanasona sosai nima har saida nafara sonta,Bata fushi salim wani irin hakuri gareta wallahi.


" Karka damu komai lokacine Ahmad idan Allah yakawomaka iyaka babu Wanda ya isa ya hana danhaka mucigaba da gayama Allahn wataran sai labari.



Bayan sati daya.


Ajigace nashigo gidan tsabar yunwa dakuma gajiya yaudai Allah ya nufa nagama lafiya nida scondry school kuma saidai a lahira idan anayi insha Allah.

Neman kwale rigata nakeyi atsakar gidan,Mama ta hararoni tana fad'in"Kul kika tube anan wallahi idan wani ya shigo fa? Da auranki tashi in kaimiki ruwa saiki watso,Wai duk jarabawarce? Yaudai an gama sai hankali kuma ya kwanta ko?

Mama wallahi bama jarabawar bace kawai tsabar casun da mukayi ne yo daga yaufa shikenan!!


Baki ta bude kamin tace"Allah ya shirya aysha ta sani ga shagala kin zama hawainiya me rikid'a Allah ya shiryamana ke to.

Shigewa nai cikin bayin dan wani irin zafi nakeji tsabar ranar Dana shawo.

Saida naci na koshi sannan na kishin gida danni gaskiya ban yarda Salla ta kufcemin duk wuya.
Niyyar barci nake naji wayata tana ringing dole na d'auka,Yaya safiyya ce kemin Allah sanya alkhairi Sannan tace inzo gobe zataban wani Abu me dadi.
Dariya kawai nayi dannasan yanzu haka bawani Abu bane dan inje ne,Kawai.

Ina ajewa wani kiran na shigowa, Kamar bazan d'aukaba saikuma na d'aga.


"Amincin Allah ya tabbata gareki sarauniyar mata amaryar Dr. Ahmad d'an lelen mama.

Turo bakina nai gaba dare da hararar wayar saikace shine gurin, A yamutse nace amin tare dakai Amma waye d'an lelen k'aton gardi dakai.


Dariya yasaki kamin yace lallai yarinya kinci abinci ya kk yasu mama koda yake
Bama saina tambayekiba dan duk munyi waya dasu koda yamman nan ya jarabawarar ?Angama lafiya ko?


" Alhamdulillah komai qalau nagode.

"Masha Allah,Har kinyi wanka kin huta kenan?

" A a wankan kawai nayi ban hutaba ruwan wankanne mama tasamin yacika zafi shine nake zufa har yanzu nikuma iska nakeso yanzu me yawa.


Gyara kwanciyarshi yayi yana mamakin surutun ayshan saidai tuni damuwar da yake ciki ta kau wannan karon wata irin zazzafar soyayyarta yakeji wadda be tabajin kwatankwacinta akan sauran matan da ya rasaba.

"Aysha tsabar shagwaba tasa kikasa mama had'amiki ruwan wanka?

" Kajika mamarka ko tawa? To ni nan har Abba hadamin ruwan wanka yakeyi idan banda lafiya,Mama ma batajima da daina cudani wankan ba danhaka babu ruwanka.


Dariya yake sosai jin wautar ayshan to wai ahakan ne zataci sunan JARUMA Alhalin bega komaiba cikin sai tsiwa da shirme,Lallai Ashe akwai aiki gabanshi kenan"Amma aysha idan aka kawoki nan wa zai dinga hadamiki ruwan wankan?

"Gaka" Ai dole kai zakana hadamin tunda Kaine ka aureni kuma kace kaji ka gani dole ka jure,Yauwa dan Allah zaka barni inyi karatu sosai? Wallahi nima likita nakeso inzama.


"Humm Aysha ba karatunki bane matsalar tunanina shine ko zakiyi tsawon zama dani kingadai yanda abubuwa ke kasancewa ko?


" uhunm kana tunanin wai nima zan mutu? Kamabar wannan tunanin danni babu tsinannen da zai hanani rawar gaban hantsi sai kwanana ya kare bazan mutu yanzu ba insha Allah suma wa incan duk kwanansu ne ya kare shiyasa,Ka kwantar da hankalinka nikam na debo kwanaki da yawa.

Tashi yai zaune tunda tafara maganar sabida yanda yaji maganar nafita babu wannan shagwabar sai tsantsar kwarin guiwa da karsashin eh dafa gaske take,"To Allah yasa aysha nadafi kowa farinciki kuma karatu saikin kai duk matsayin da kikeso insha Allah.

"To sai anjima nifa nagaji yau ka gaidamin da mama.


Zubama wayar ido yayi bayan ta kashe" Ah ikon Allah ta kashe saikace ita ta kirani kai wannan yarinyar sanin daidai dinta sai Allah, Ya ubangiji kai ka jarabceni da son wannan baiwa taka Allah ka daidaita tsakanina da ita ka k'arfafi zaman mu Allah kasa abokiyar zamanace Allah ka amincemin tazama uwar dukkan yaran da zan haifa.





Haske writers association.
12/10/20, 7:53 AM - Naffy Aliyu Umar: 25




Shiri na musamman yayu ne ke yimin domin kundaisan Al'adar hausawa ta gyaran amarya.

Cikin kwanakinnan kullun sai Dr. Ya kirani haka mamanshi da abbansu kullun sai munyi waya da alama suma sosai suke sona danna lura da irin kulawar da nake samu daga garesu.

Har zuwa yanzu babu wata jituwar kirki tsakanina dashi dan da wuya ya kira waya agamata batare da munyi fada ba ,Shi kanshi har mamakin kanshi yakeyi da yake biyemin muyi fadan tunda lokuta da dama salim yakanyi mishi fadanhaka.



**
Zaune yake cikin office dinshi fayil din wata yake dubawa da infection yaima mugun kamu bekaiga ganin wurinba Amma tsabar yanda awon ya nuna tana cikin mawuyacin hali haka kawai yaji tsigar jikinshi tatashi dan damafashi shegiyar kyamace dashi,Shiyasa tanamishi bayani ya fara turata awo.

Ring din wayarshi ya dakatar dashi daga magungunan dayafara rubuta mata.

Ajiye wayar yayi bayan ya d'auka amma kuma zaji dukkan abinda za ace.

"Mijin ya fati ina yini ya aiki?


" Alhamdulillah k'anwar fati me kikeso ne? Nasan dai haka kawai ba za a kiraniba adaidai wannan lokacin Allah yasa ba yawo zakice zakije ba?


Cikin shagwaba nafara magana"Waikai dan Allah shikenan babu halin in kiraka saikace wani yawo zani inkuma ban kiraba kace banyi maka biyayya Nisan kalar kaba.


Murmushi yasaki kamin yace "To yi hakuri yanzu dai ina office gayamin meya faru?

" Dama wajan malam zanje yau shine zan gayamaka.

Dariya kawai yayi kamin yace to shikenan Allah ya tsare Amma banda kaiwa dare dan Allah kila gobe in biyo masu kawo lefe muzo tare.


"Ah ah kajika kazo kayi me gaskiya karkazo kai zamanka kawai kai ko kunyama bakaji har fad'in za akawomaka lefe kake to nidai babu ruwana dan ko kazo ba ganina zakaiba atashi aiki lafiya.


Wani shegen tsaki yasaki lokacinda yaga ta kashe wayar,Wannan yarinyar na wulakantashi wallahi shifa ba a yankemai waya Amma ita kullun ahaka suke rabuwa koda shine yai kiran kuwa.

Da sauri ya lalubo lambar ya dannamata kira.


Saida naga zata yanke Sannan na d'aga .

" So nawa zanyimiki kashedin kashemin waya?

Yamutsa fuskata nai,Nidai ina mamakin kalar hakurin ya fati wallahi duk yanda kaimishi saiyace bakai daidai ba bansan ya akai ta iya zama dashiba,"Kajika dawata magana to kudinka ko nawa nicefa nakira kuma nagama magana na yanke sai kuma yazama laifi kainifa wallahi nima nan da ka ganni kwalluwar kai nace bar ganina da k'aton hijab ko yaushe,Kuma yanke wayar nayi ina harararta Kamar itace taimin laifin.


Amemakon yaji haushi ko ranshi yabaci saima wani nishadi dayaji ya dabaibayeshi shiyasa yafara sakin murmushi batare da yai niyyaba.

Ganin yarinyar na kallonshi yasashi hade girar sama data k'asa yacigaba da rubuta mata magani dan beyi niyyar duba yanayin kurajen dake gabantaba.

Ballema wannan wayar da yayi gabadaya saiyaji kasala ta sakko mishi,Sati biyu ki dawo ki kula sosai.




**

"Anya aysha kina kyautawa kuwa? Ke bazaki zauna da mijinki lafiya ba,Ina sanefa kullun sai kunyi fada kamin Ku rabu shima bansan kalarshiba da yake biyemiki kuna wannan shirmen ba.

" Toni mama kullun fa saiya cokaneni yakejin dadi,Rannan fa cemin yai wai k'aramar fuskace dani Kamar ta budurwar mage.

Dariya tasaki tanakuma kallon fuskata din yayinda nikuma nasaka kuka dan jinai kamar yaune yake fad'in maganar dama ranar har kuka saida nayi balle danarasa abinda zance mishi tunda rashin kunya bawai tarbiyar gidanmu bane.

Ganin ina kuka yasata kwantar da murya kuma ta daina dariyar"kinga yi hakuri bake nakeyiwa dariya ,Kai shimadai ya iya rikici Wallahi kyaleshi shima ai fuskar tashi shigen irin takice balle yaimiki Sheri yanzu kije ki shirya sai ki wuce banso kiyi yammaci.




***

"Kai Ammadai komai yayi wallahi gaskiya alhaji yayi kokari komai yayi ai yakamata ma su daina yin barnar kudinsu akanka hakanan duk auren sai sun wahala maka,Cewar salim yana dariya.


", hahhha naka wasa alhaji ai autan kenan dagani babu saura fa ai dole kaga sun rude saima kaga yanda mama ke riritani mutumina ina alfahari da hakan saidai bansan yanda zamu k'arke da wannan rigimammar yarinyar ba Dan wallahi tafini rikici.


Shima dariya ya saki kamin yace humm Ammadai ai Kaine ke kuma dorata tunda kana biyemata kana tayata Wallahi inkai wasa zakasha wahala kwarai da gaske.


" Bansan ya zanyiba Salim wallahi ina sonta son da bantabajin irinshiba,Inajin kamar aysha itace rayuwata bansan lokacinda soyayyarta taimin wannan mugun kamunba,Ka tayani da addua salim wannan karon idan na rasa aysha nasan cikin biyu dole d'aya zai faru kodai in mutu in bita kokuma in haukace dan wallahi inajin abinda bantabajin irinshiba akan kowace mace sai akanta,Yanzu haka wani lokacin jin kewarta nake kamar zata kasheni salim dan Allah ka tayani da addua!!!!


Ajiyar zuciya ya sauke yayinda tausayin Ahmad din ya dabaibayeshi"karka damu insha Allah

Please Login or Register in order to submit comment