Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Duk da yanajin nauyin wasu matan domin akwai yayun mama din cikin d''akin Ga kuma baki,Amma haka ya sunkuya ya sunkuci maman yanufi d'akinshi da ita nan dinma be tsaya falowa kuryarshi ya wuce.
Kan gado ya shimfideta kamin ya fara yimata firfita da wata jarida dake gefen gadonshi,Ganin tsawon lokaci shiru kakeji yasashi farajin tsoro ya debo ruwa ya shafamata afuska nan ma shiru kakeji.

Wata irin mummunar faduwar gabace ta sameshi kaddai ace ya kasheta fa?

Makullin mota ya d'auka yakuma sabarta sabida Abba yafi mama girma nesa ba kusaba Sannan ita dama bata da jiki dan ko yaya salame tafita manyanta itace babbar diyarta.

Tsirarun mutanen da basu watseba sukabi Abban da kallo yayinda mahainfin dr. Din ya bazamo yana tambayar lafiya meya faru?

"Kaga kwantar da hankalinka me d'akinace ta suma Amma ku jira yanzu zan dawo.
Komawa yai cikin gida ya kira yaya salame sannan suka nufi asbt.



*''""*
Sabon abune Abba yayi domin lamarine me wuyar sha'ani da d'aure kai shiyasa sai abun yazama na magana cikin yinin ranar Sannan tuni wasu sunsami abin watsawa amedia saidai irin adduan da mutane kemin lamarin dashima abun kallo ne Sannan masu jinjina Abban sunada yawa dan wasu kai tsaye sukecewa su bazasu iya hakanba musamman da saida aka k'arama labarin gishiri da maggi Sabida yafi tafiya.


Wani irin fishi mama ta d'auka da Abban bayan dawowarsu asbt dan har ikirarin barmishi gidanshi tai saidai tuni mahaifinta ya takamata birki kan hakan toma Abu anriga an manyanta.


Shidai Abba be kulataba dan dama yayi tunanin ganin fiye da hakan Dole ya lallaba abarshi tunda ance jininta ya hau lalurar da ba'a taba cewa wani Nada itaba tsakanin shi da ita to ya tabbata shima yanzu da za a aunashi sai ance yanadashi.



Washe gari.

" Ni alhaji sai inga anawa tunanin dakafara tuntubar mamansu kuma kayi shawara tukunna dan kaga hakan yana nema ya zama abin tashin hankali kumama kaga shi kanshi Ahmad din ya nuna rashin aminceearshi akan aurannan dan Allah ai hakuri alhaji aduba maganata kuma ka dubi halin da ita kanta yarinyar zata shiga,cewar mahaifin Ahmad dindanshifa hankalin shi ya Gaza kwanciya akan Wannan aure.


"Hummm Baban Ahmad kenan to yarinya dai diyatace kuma inada ikon auran da ita ga duk Wanda yaimin kuma dole taimin biyayya danhaka aure ya d'auru kuma ko kai bazaka rabashiba danhaka mubisu da addua kawai itakuma zata huce duk irin fishin da zatayi nidai alfarma daya nake nema shine dan Allah kubarmin aysha ta idasa makarantar ta dagabaya saita tare idan ya amince tacigaba gidanshi shikenan idan kuma be aminceba to iyalinshi ce dai,Amma bazan hanashi zuwa ganin matarshi ba duk lokacinda yaso kamin ta idasa.

Rasa bakin da zasuyi godiya sukayi sabida girman al'amarin.Maman kuwa kuka tasaka dan tariga ta sadakar da cewa yaronta bazai kuma samun matar aureba saiga wannan me halin salihan bayin yakuma bashi auren lokacinda ko fita daga radadin rashin dayar babu Wanda yayi.

Kama hannun Abban yayi ya rike yana kuka Amma yakasa ko bude baki balle yayi magana wani abune meshegen nauyi ya dannemishi kirji.
" Karka damu Ahmad nidai fatana ka kwantar da hankalinka ka rike iyalinka da kyau,Kallon mahaifi nake maka sannan ina tausayama halin da kake ciki, Ahmad inda ace ayau aysha zata rasu kamar yadda Fatima ta rasu wallahi inda inada wata saina baka zan dinga jeramaka su har sai komai yazo k'arshe to saigashi saura aysha kawai idan Allah yasa kun rayu tare shikenan dan hakan nake fata Allah yaimuku albarka yasama auren albarka Sannan ka dinga lekowa dan Ku saba da ita din kamin ta tare Ammafa sai kayi hakuri dan ba kalar halinsu dayaba.


Cikin aminci da ganin mutuncin juna suka rabu yayinda motocin katsinan sukabar gidan Sai yakuma komawa kamar babu mutane dan dama yawanci duk na cikin garine kuma sun wuce.



"*"*"

Zaune muke gaba dayanmu Yaya salame Yaya safiyya sai sai yaya maryam sai ni sai mama cikinmu anrasa Wanda zaiyi magana sabida damuwa babu Wanda befice daga hayyacinshiba tsabar damuwa da tashin hankali abinci ko yai kaura daga bakunanmu sai dai ruwan tea da muke banka koda yaushe.

"Mama kiyi hakuri dan Allah kidaina fishi da Abba ki bari Ku fahimci juna tukunna,Nai maganar ina share kwallar idanuna.

" Humm aysha bazan iyaba nagaji da abinda mahaifinku yakemin kullun nunawa yakeyi bani da wani iko akanku saishi duk da shine mahaifinku nikuma ai nice mahaifiyarku nicenan nasha wahala da d'awainiyar kula daku danhaka nagaji saidai mu zauna ahaka tunda baba ya hanani tafiya gida,Amma bazan yaddaba wata uwace za aima haka ta kauda kai? Diyata ta mutu ko bakwai ba aiba sai kawai inji yakuma bayar da wadda tai saura agabana ? Kuma bayan yasan komai dake faruwa? Cemishi akai nagaji da ganinku ne ? Wallahi ko ganinshi banason yi saura kadan ince na tsaneshi da wanne yakeso inji?
Ta idasa maganar tana sakin kuka me cin rai.
Duk tayata mukeyi Sabida tashin hankali sabani babba betaba shiga tsakaninsuba irin wannan kuma kowa yasan laifin Abba ne yakamata ace ko shawara yayi da ita bawai taji abuba haka kwatsam.

Duk hakuri mukaita bata nisam bandamu da halin da zuciyata ke ciki ba nafi buk'atar inga iyayena sun daidaita tukunna.

Jawoni tai jikinta ta rungume tana sauke ajiyar zuciya da alama tafara hucewa tunda tai kukan da yawa.

Ahankali ya lallaba yakoma yana murmushi jin mungama lallashinta shi kanshi yasan tanada hakuri to Amma idan yace zaiyi shawara da ita ya tabbata bazata aminceba tunda na fatiman ma bawai da son ranta akayi ba.


Sai yamma lis ko wacce ta wuce gidanta sai ya kasance dagani sai mama gidan saikuma k'annena guda biyu maza sadiq da umar.

Dole kowa yajawo dauriya Amma kewarta na nan like cikin ran kowa.

Sam banjin dadin ganin yanda har yanzu babu jituwa tsakaninsu mama dan kula da komai nashi ma ta barmin komai na ayyukan gida idan banyiba to saidai yayi da kanshi so biyu ina yunkurin yimata magana Amma saita tsawatar min,Akan babu ruwana in zubamusu ido.



**""**
"Aysha tunda abubuwan da suka faru bamu samu zamaba inaso in baki hakuri akan hukuncin Dana yanke batare da na tuntubekiba.

Matsawa nai kusa dashi tare da Dora kaina Akan cinyoyinshi tare da matse hannuwanshi,Dan Allah karkai haka Abba kadda kace zakaimin haka kai mahaifinane bani da kamarka duk duniya kuma Allah ne yabaka damar zabamin mijin daya dace dani danhaka basaikace komaiba babu abinda ke faruwa batare da amincewar ubangijiba komai rubutacceni danhaka tuni na amince da zabinka abbana Amma ina Neman alfarma daya Abba!!

Shafa kaina yake yana kallon cikin idanuna wa inda ke fitar da hawaye" Karki damu komai kikeso ki tambayenikanki tsaye kinji ko?


Abba kayi hakuri Ku daidaita da mama gidan babu dadi yanzu kuma har yanzu batajin dadin jikinta.

Sharemin kwallar idanuna yai kamin yace karki damu aysha naima mamanku laifi kuma zanbata hakuri saidai kinsan nafiku sanin halinta shiyasa nabata dama tadan huce tukunna kingane ko ki kwantar da hankalinki insha Allah zakiyi farinciki Allah yaimiki albarka ya jikan 'yar uwarki bari inkira miki Ahmad din ki gaisheshi dan tunda suka koma yake kwance ba lafiya saikimai sannu banda tsiwa esha.



Bata jima da fara ring ba aka d'auka da kyar nasamu na daidaita muryata nai Sallama.
Jin muryar mace yasani sauke ajiyar zuciya.
"Ina yini?

" lafiya lau,Aysha ce?

Miyau na hadiye kamin ince eh nice Yame jiki?

"Jiki Alhamdulillah da sauki barci yakeyi Amma idan yatashi zai kira mungode Allah ya saka da alkhairi yayarshi ce Halima.

Ajiye wayar nai ina sauke numfashi godiya naima Allah da ban fara buga tsakin da nai niyyaba idan an daga wayar.



***

KATSINA.Ashe tun ranar da suka koma yake kwance dan jininshi yai mugun hawa saida yai kwana uku asbt Sannan yadawo gida da jinyar kwana biyu tsakani yaronshi ya rasu shima sabida kyanda da yayi yanzu khairat ce kawai diyarshi.Abubuwa sunyimishi yawa Ammafa yanzu wannan auren shine tashin hankalin shi ina zaikai aysha amatsayin mata Sannan yasan Hafiz na sonta har yanzu wannan tunanin ne ke kuma cunkushe zuciyarshi yaji kirjinshi na suya.

Tuni ya koma gida gaban iyayenshi yakuma tabbatar da cewa bazai kuma zama wani gidanshiba koda ayshan zata tare to tabbas saidai su gyara nan gaban iyayenshi su zauna bazai kumayin nesa dasuba duk abinda zai sameshi to ya sameshi gaban mahaifanshi.

Tashin ya kenan daga barshi ya buk'aci yin wanka tokuma usman dake temakamai benan dole saidai yayarshi hannatu ta kamashi zuwa bayin dan gabadaya jikinshi yagama saki sabida ciwo"Sannu dan Allah ka cire komai aranka k'anina insha Allah zakayi dariya wataran kaga jikinki yakiyin sauki yanzu kanaso mu rasaka ne?


Kanshi ya girgiza mata yana zama inda takeson zaunar dashi kamin ta hadamai ruwan wankan ynason yayinshi da yawa domin maidashi suke kamar baby babu ruwansu da girmanshi.
"Ko in cud'aka ne?

Harararta yayi yana turo baki.

Ficewa tai tana dariya dama tsokanarshi tai niyyar yi.

Saida taji motsin ruwa alamun yafara wankan sannan ta canza mishi zanin gado tacigaba da gyaran d'akin saida taga komai ya kammalu Sannan tadamai turaren k'amshi ta zauna jiranshi.
Dr. Ka gama ne?

Idasa bude k'ofar yai kamin yace boxer zaki mikomin insawa tukunna.

Baki da bakar bes ta mikamishi,Saida ya saka sannan ya kirata tazo ta kamashi.
Cikin jin dadi yake kallon dakin ta gyara ko ina" Sannu auntyna dama d'akin ya daman wallahi.

Saida ta zaunar dashi kamin ta mikomishi cream ya shafa shima sama sama dan beda kuzari ko kadan jikinshi.

Kwanciya yayi itakuma tafita dan kawomishi ko tea ne tunda besan abinci.

Karo sukaci da maman da kuma abokinshi salim Wanda yaudinnan yadawo daga k'asar waje besan komaiba dake faruwa.

"Lafiya? Cewar maman tana kallon Hanna din.

" Kushiga mama wanka yayi ne shine zan kawomai tea ko Allah zaisa yasha ,Salim saukar yaushe?

Sosa kanshi yayi kamin yace aunty ko gida banjeba wallahi saukar kenan nayo nan dan duk nasami labarin abinda yafaru to bamma gama abinda ya kainiba na taho hankalina yaki kwanciya.



Rungume juna sukai kamin ya koma ya kwanta yanajin wata irin nutsuwa ko babu komai amininshi yadawo gareshi.

"Sannu dr.naji duk abinda yafaru dan Allah ka k'ara hakuri insha Allah komai yazo k'arshe dannima akwai binciken da zanfara yanzu kaidai ka kwantar da hankalinka ka fahimci duk wa inda kake tarayya dasu ta hakane zakasan wa inda ke kullamaka wannan sharrin insha Allah.

" Ansanan tashi ka amsa kasha saikasha maganin kuma wallahi bansan gaddama,Dazuma matarka ta kiraka!!

Har Neman kwarewa yayi da tea din daya kurba sabida yanda yaji maganar Asama.

Kallonta yake alamun tambaya,Danhaka ta watsa hannuwanta"Wallahi da gaske nake amma da lambar abbansu danhaka idan ka huta saika kira kasami lambarta.

Salim ne yai murmushi kamin yace ai aunty insha Allah cikin satinnan ma zamuje garin idan yakuma warwarewa saimu ganota da kyau oh Ashe itama rabon dr. Ce wallahi yarinyar mace ce.

Harararshi Dr. Din yayi kamin yace ka gama yabonta sai munje taimana wanka da ruwa wlh danni wannan yarinyar tsoronta nakeji.

Dariya suka saki gabadayansu hadda maman data kuma shigowa cikin d'akin.

Nanfa suka zauna hira dan jikin nashi yau da sauki.





Wai wane kalar zama za ai tsakanin Dr. Da JARUMA?


Shin zai auri diyar yayan mahaifinshi kuwa?


Wake kashe matan Dr.?


Duk wa innan amsoshi zaku samesu cikin cigaban labarin JARUMA akan naira Dari uku kacal 300 inafatan masoya zaku bani hadin kai kamar yadda kuka saba.

Nasan dai zakuso kuji wani irin zama za ai cikin wannan gida.


Taku har kullun Aysha maman khadija.



Labarin JARUMA yakoma na kudine sabida wasu Dalilai.

Nagode


Tsarin biya.

Acct no.
0005074141,Aisha sabiu, Ja'iz bank.

Kokuma MTN Cart ta wannan layi.
08142643253.


Saina jiku.




Haske writer's association.
12/10/20, 7:52 AM - Naffy Aliyu Umar: 22




Abba zanje indubo zainab har yanzu kwance take jiya mukai waya nace zanzo in dubata.


"Aysha kefa rigimammace wani lokacin,Nagayamiki banine keda hakkinshige da ficenkiba kumafa kinsani tunda kinada ilmin nan hasalima ninan ina cikin d'alibanki, Kawai kiranshi zakiyi idan kika gaisheshi da jiki saikimishi bayanin wacece zainab Sannan ki tambayi izinin zuwa dubota ko?

Turo baki na nai gaba kamin intashi gabanshi bansan meyasa yanzu kullun sai ya kawo abinda zai hadani dashi shekaranjiya har lambarshi saida yasamin awayata,Inaso in fita har gidan yaya maryam nakeson zuwa amma Abban yaki Dana tambaya saiyacemin in tambayi mijina.



Bayan sallar isha'i.

Kwance nake saman sallaya inata tufka da warwara sonake in tambayi fitar Amma kuma narasa yanda zanyi bammasan mezaice shima tunda naga shima d'an wulakanci kaddama in kira ya yankwa na ni.
Kiran Abba ya shigo wayar da sauri na d'auka ina saurarenshi.
" kinji ko aysha kisan yanda zakiyi ki turomin mamanki kuma ki kawomin tea yanzu.

Ajiye wayar nai ina zare ido ni ya zanyi da mama ko maganar Abba bataso yanzu.

Saida na had'a tea din na kai mishi sannan nadawo nashiga d'akinta.

Kallo daya taimin ta kauda kai"Yau baki kwanta da wuriba kenan ko akwai damuwa ne?

A a mamana babu komai Amma dai abbane ke kiranki .


"Tashi ki fita bansan hauka,Kamin in gauramiki mari.

Saida na koma bakin kofa Sannan nace,To mama Abba dai mijinki ne kuma Tara na ganku qaddarata data ya fati iri dayace saidai insha Allah akwai banbanci ba fushi yakamata kiyiba tunda an Riga an daura auren Addua zakiyi da fatan alkhairi saikiga Allah ya duba tawakkalinki ya canza tunanin dake tashin hankalinki Wanda hakan kesawa kina kokarin take dokokin Allah,To yaudai Abba na kiranki amatsayin mijinki kin amsa gayyatarshi kinsan hukunci Wanda duk bazamu soshiba,Mama idan laifine ni Abba yaimawa dan wallahi tun farko na tsani dr.haka koda akai auren ko ganinshi banso yanzu haka ban iya barcin kirki tunda igiyoyin aurenshi suka hau kaina,Amma nasan koke bakisan hakanba tunda ban nunaba dan nasan nunawar tawa babu abinda zatayi aikin gama ya gama.
Allah ya huci zuciyarki mamana ya sanyayata.

Ficewa nai daga d'akin ina share hawaye dan sosai nake cikin damuwa saidai wani bazai taba ganewaba sabida dama haka nake ni.

Gyara kwanciyarta tayi saidai tuni duk maganganunanata nanata kansu cikin kwanyarta tsaki ta buga"Matsalar yara Susan addini babu halin kai kuskure sai akama jawomaka aya da hadisi😃.

Tashi tai ta wuce.

Saida naga tashige falonshi sannan na lallaba nasaki lalbulen, Sam babu dadi kaga iyayenka sun sami sabani saikaga zaman gidan ma yana nema ya gundureka.



Harna kwanta saikuma naga tunda dare beyiba bari kawai in kirashi.

Tajima tana ringing dan sai akaro na biyuma Sannan naji and'aga.
Hararar wayar nayi jin yayi shiru wato bazai iya yin maganaba.
Assalamu laikum ina yini ya jiki?

Da sauri yatashi zaune har yana bige Salim Wanda ke chart gefenshi.

"Lafiya Alhamdulillah ya kk?

Lafiya lau.Shiru nai ina zare idanu saikace yana gabana.

" Uhumm inajinki ayshana"

Turo bakina gaba nai ina yamutse fuska,Dama zan tambayeka ne!!

Jawo Salim kusa dashi yai yana murmushi yanda zasuji duk abinda zance.

Adake yace "Inajinki meya faru?

Uhum dama dama Sunanta zainab k'awatace mun zama kamar 'yan uwa bani da kamarta To bata da lafiya shine nakeso inje in dubota.

Kife wayar yai suka kama dariya jin wani kalar sharhi kamin su kintsa ya d'aga wayar.

Cikin nuna isa dan ya gwadata yafara magana" Ammadai kinsan ni bansan yawo ko? Makaranta kawai na yadda kije bazan yadda da yawon banzaba.


Kutt ni kakecema me yawan banza ko? To wallahi saima naje danma kasamu na tambayeka shine zakabini da sharri kai bamma yafemakaba wallahi kuma sainaga yaka da abbanku ai dama jiya yacemin ko maganar banza kaimin ingayamishi kitt na yanke wayar ina huci.


Dariya suke hadda kwanciya "Kai mutumina kace wannan babyn zazzafa ce kai kaji masifa ko hadiye miyau batayi wai maganar banza to itama ta rama,Ya idasa maganar yana dariya sosai.

" Haba ai shiyasa nai haka danka fahimta ba irinsu d'aya da fatimaba koda yake dama Fatima tasha bani labarinta tace min tanada dadin zama Ammafa sai mutun ya daure Sannan bata da tsoro,Kuma inaga sai nan da October zata shiga 18 years.

"OK Amma gaskiya yarinyar kyakkyawace mutumina Allah yasa abokiyar zamanka ce tayi ta ko ina balle tarin ilminta kota nan kasami saukin wasu abubuwan Amma yakamata kadaina abinda zaka tunzurata inba hakaba bazaku fahimci junaba,Yanzu ka Adana lambarta saika turamata izinin zuwa dubiyar.




***
Akace tsakanin mata da miji sai Allah tabbas wannan magana haka take dankuwa tun wayewar gari na fahimci su mama sun shirya duk da har lokacin afuskarta babu walwala Amma kuma babu wannan fishin sosai afuskar.
Balle danaga takaimishi abin kari da kanta,Ni dariyama sukaban dan tabbas sunji jiki su dukan.

K'arfe 11 nasafe nagama shirina dan zuwa dubo zainab kamar yadda nace dan dama koda be turomin sakon injeba wallahi nayi niyyar zuwa duk da nasan hukuncin hakan Amma takaicinshi bazai bari insami nutsuwaba idan ba gumamishi abin haushi nayi ba.

" Kadda ki jima tunda yayarku tace tanason ganinki kadda tazo bakinan ki gaishemin da ita kila zuwa yamma inshigo dubata.


Sallama naimata nabar gidan dan babu wani nisa sosai tsakanin mu.



***

"Dady ka tausayamin kasa in auri yaya Ahmad dan Allah wallahi zan aureshi koda zan mutu nima Allah ina sonshi.

Makemata baki yayi kamin yace anya kinada hankali kuwa mamana? To kima daina wannan maganar dan tunda yasaba kashe matanshi wannan ma bawani kai labari zataiba haka kawai sai in d'aukeki inbashi wata biyar yai yawa kinzama gawa ko? To karma ki fara indai ba so kikeyi in cire soyayyar danakemikiba in sassabamiki kammanniba wallahi.

Bakinta ta toshe tana kuka dan tsabar shagwaba wadda aka horata akanta,Tashi tai fuuu tabar wajan tana ihun kuka Amma saiyawani basar da ita dan ya gwammace taita kukan akan ya bawa Ahmad auranta dan shifa har yanzu mamakin mahaifin Fatima yake akashemaka yarinya Amma ko gamajin zafin mutuwarta bakai ba Saika kuma bada wata lallai ma yanaga yanacikin salihan bayi😃.

" Indai kikane yanzu kika farashi ummi dankuwa alhaji bazai taba yadda ki auri Ahmad ba danhaka garama ki hakura.

Cikin kuka tafara magana haba mana momee domme bazaku ganeba sabida Allah Dan Ku bakuyi auran sosayyayba shine nima kuke nema kuyimin bakin ciki inba hakaba mene abun damuwa danna temaki d'an uwana? Amma shikenan duk kunbi kun tsamgwami Bawan Allah Sabida kawai wannan qaddarar to nidai wallahi shi nakeso.




***

"Gaskiya alhaji najima banga mutumin kirki irin mahaifin marigayiyaba wallahi abun har mamaki yakeban fa!!!

" Humm ke dai bari kawai nifa daskarewa nayi ranar sabida tsabar yanda maganar ta bugeni kuma kinga hatta sadakin shine ya biyashi Ni bansan da abinda zan sakama da wannan mutumi ba.

"Ai babu abinda zamuyi mishi daya wuce addua alhaji sannan d'azu naima wannan yarinyar magana nace tazo sufara hada lefe tunda duka duka yarinyar bewuce kwanaki ta gamaba Kuma kaga bamusan yanda zasu sa lokacin tarewar ba ko?

" Eh kin kyauta hakan shine daidai,Sannan shima Ahmad din yakamata yazo suje su gana da ita yarinyar tunda ga Salim yadawo saiya rakashi.

"To Allah ya shigemana gaba Ammafa yacemin babu wani gidan da zai zauna nan yakeso shine nace to saidai wannan d'akin ko? Tunda kaga ukune hade saisu dinga amfani dashi kayanda za akawomata kuma saiya zubasu wani gidan yanda insun canza shawara saisu koma ko? Ammadai kai ya kagani?


" a a hakan yayi Allah ya k'ara rufa asiri zuwa dasafe zai shiga wajan induba idan akwai abinda yadace sai ayima d'akunan Amma kadda ki manta tunda jikinshi ya warware to ko zuwa gobe lallai suje su gana da wannan yarinyar.

"To Alhaji insha Allah ni bammasan gidan wa suka shige ba.



** ** **


" oh aysha wallahi sai inga kamar wasa wai kinyi aure abin yazomana abazata jiya malam yazo dubani duk sainaji yabani tausayi wallahi yace dama ba rabonshi bace ke kuma wai dama yasan kinadai kulashine kawai amma bakicika sonshi ba.

Ke dallah share nifa wallahi bazan tsaya in bata lokacina wajan soyayyaba,Inama mukaga lokacin batawa,Kuma yanzu yanda Abba yaimin irin wannan auren inda ina son wani Aida tuni hankalu sun tashi.

"Eh kuma hakane d'azuma kiranshi biyu yanajin yaya jikina.

Shewa nasaki kamin ince hegiya kodai har ya juyo nan ne dannaga shima matse yake da auren ai.

Dariya kawai tayi.

Shigowar message cikin wayata yasani kallon wayar.

Kimin shiri na musamman ina nan tafe gobe insha Allah.

Hararar wayar nayi kamin in maidata cikin jakata.

Dariya tasaki kamin tace kodai oganne naga anyima wayar kallon love.

Duka nakaimata kamin in cire hijab dina danyin sallah.




***



Tafe suke suna hira kallo daya zakaimusu kasan hankalinsu akwance yake duk da cewa Ahmad din ya rame sosai Dan da ka kalleshi zakasan yasha jinya.
Salim kejan motar.

" Zullumin haduwa da yarinyar nan nake wallahi damacan bata sona nifa bansan tashin hankali salim.

"Kaima kajika da


Please Login or Register in order to submit comment