Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata zuciyar na tilastamin yin farinciki musamman idan nai tunanin yanda kowa ke tambayata har yanzu babu wani motsi dan ko kwanaki saida yaya halima tace ya maidani asbt ko barin da nayi yabarmin wata matsala.

haka yayuna kullin adduar su"Kema Allah yabaki aysha da munzo na zainab mudawo naki.


Da Sallama muka shiga falon yana rike da ledar daya siyomin fruit.
Rungumar mama yai yana dariya,Yayinda Abba yabishi da harara yana fadin"Yau ga katon kawai meye haka kuma?

Duk dariya mukayi kamin yakoma wajan Abban ya rungumeshi tare da sumbatar hannun Abban"Kai dai kawai kace kishi kakeyi Abba,To kaima gashinan inafatan hakan yaimaka,Cikin kunnenshi yaimishi rad'a,Kufa nake tayawa murnar samun jika daga autanku Abba.


Da Sauri ya dago yana dariya"Alhamdulillah masha Allah, Allah ya inganta yasa arabu lafiya.


Kaina na sunkuyar k'asa musamman danaga dr.nawani kashe ido ko kunya babu.

mama ma farinciki sosai ta nuna kamin ta koma kusa dani"Aysha ko kinason wani abu?

Haka kawai naji kunyarta takamani"A a mama sallah zanyi.


"Allah ya raba lafiya madam"Cewar abubakar yana dariya.

Harararshi nai tare da wucewa ciki,dan banyi Sallar magriba ba.


Ina zaune cikin bayi hannuba saman cikina ina shafawa mamaki nake wai wani cikin nasamu!ikon Allah koda yake irin yanda Dr. ke hanani sukunima AI INDA hakane da tuni najima da samun wani koda yake dama hausawa sunce zafin nema baya kawo samu.

Sam banji motsinshiba Saidai naji hannunshi Saman nawa dake kan cikina.

Watsamin ruwan yai Sannan ya d'agoni gaba daya.

Saida ya direni gado kamin yace"Kimmayi Sallar kuwa?

girata d'aya na d'agamishi.

murmushi yai kawai tare da girgiza kanshi sabida kusan d'abi,arshice magana da gira wanda zama dashi yasani fara koya yanzu.

"Je kiyo alwala to dan yanzu zakiji isha'i itama lokaci yayi.

Anatse nai sallata tare da tsananta addua akan abinda ke cikina,Saikuma fatan Allah yasa kadda karatuna yazama shiririta.



**

"Wai fishin me kikeyi zainab? Dole dai saikin tashi hankalina dan kinga banson damuwarki ko?

Wani bata fuska takumayi tana niyyar tashi tabashi wuri.

Rikota yai"Yi hakuri gayamin ya kikeso ayi yanzu?

"Cewa kawai zakayi in shirya gobe muje gidanku inga kowa da kowa Sannan kuma bazaka kuma kin d'aga wayar momee ba,Ka kasa ganewa sadiq wallahi banjin dadi kullun saika kira mahaifiyata kaji yata tashi sannan da dare saikamata saida safe,Saikuma inga mahaifiyarka ta kira ka kasa d'agawa ya kake tunanin zanji? Mahaifiyarka baka da kamarta duk da addininku yake ba d'ayaba Amma.kasani jawota cikin jikinka.shine zaisa har itama tai n'am da addininka har tayi sha'awarshi,Amma ahaka da kakemata babu abinda zai karamata a zuciya Sai tsana da jin haushi sabida zata dinga tunanin shine ya nesan tata da yaronta dan Allah kai hakuri ka shirya muje biyayyarka gareta fa dole ne kaj?


gyaramata zama yai.jikinshi "Ok to shikenan zamuje Amma ba gobeba saidai juma'a saimuyi mata weekend can.


Sumbatar kuncinshi tai tana mishi godiya.


Zubamata ido yai kawai yana mamakin halinta,Yayinda wani barin na zuciyarshi ke adduar Allah yasa idan sunje kadda momeen ta wulakantasu dan ko kwanaki dayaje wuk'ama ta d'auka zata kasheshi.



BAYAN KWANA UKU.

Wata irin kulawa nake samu daga garesu meban mamaki Sai yanzu nakuma tqbbatar da irin son da sukeyima cikin.
Rana guda yayunshi suka ware sukazo wai tayamu murna,Kuma kowacce da kalar kayan kwalam din data shiryomin.



***

Tun tana dari dari da matar har tafara sakewa sabida bataga wata fuskar cutarwa tare da surukar tata ba.
Saima tafarajin.haushin Abubakar din dan duk shigowa saiyace tafa dinga kula.



Ahankali take k'arasowa falon gidan babu kowa sai momeen kadai sauran duk suna makaranta dayake k'annenshi biyu ne kawai daga sunday me bima Abubakar din Sai merry Auta.


Nuna mata kusa da ita tai ta zauna kamin tace"Sannu fa,"

Akunyace zainab din ta Amsa mata tana sadda kanta k'asa.

Yayinda itakuma momee din abun ya birgeta shiyasa saita zumaba Zainab din idanu tana kuma nazarinta"Kinga danial ya gujeni ko?


"A a momee d'anki ne kuma be isa ya canza hakan ba danhaka babu yanda za ai ya gujeki duk inda zashi beda kamar ki,Yace dai bakison ganinshi ne shiyasa yake kauce miki dan kadda ranki ya dinga baci.

"Ni inason ganinshi shinedai yanzu be sonmu tunda ya canza sabon addini narasa yanda zanyi dashi gashi mutane nata min dariya wai yarona yafi k'arfina,Cikin damuwa ta idasa maganar daga gani tana cikin bacin rai akan hakan.


Kuma matsawa tai jikinta tare da riko hannuwanta duk da cewa cikin zuciyarta tsorace take da ita.


"Momee sadiq d'anki ne kuma babu wanda ya isa yaja da wannan.Sannan shigar shi wani addini bazai ragemishi komaiba Saidai k'ara samun d'aukaka,Sannan addinin musulunci shiyafi kowane addini daraja iyaye Domin mu addninmu ya tabbatar mana da cewa biyayyar namiji ga iyayenshi.hanyace ta shigarshi.Aljanna kamar yadda biyayyar mace ga mijinta shine hanyar shigarta aljanna,Bazai kuma barinkiba momee kije wajanshi duk lokacinda kikeso idan kuma nan wajanki kikeso mu zauna To zamu zauna tare dake duk dan kiyi farinciki.

Rungumeta tai tanajin dadi da nutsuwar duk maganar da zainab din taimata,Saidai rungumar da taimata yasa zainab din fara yunkurin amai Sabida k'arnin dataji momeen nayi.

Daidai shigowar Abubakar din.


Asakwane ya idaso yana jeromata sannu yayinda tsakanin surukar da mijin zaka rasa wanne yafi rudewa,Yai mamaki amma duk da haka yaji dadi kuma yai farincikin fara Sakkowar momeen daga fishin da takeyi,Dan dama be ta k'annenshi tunda shine komai nasu dolene subi abinda yakeso,Sannan basuyi girman da zasu botsare mishi ba.


Yana rungume da ita harta gama aman,Ga mamakinshi saiyaga momeen na gyara wajan tanayi tana ma zainab din Sannu, Danial me takeso taci kuma tunda tayi amai?

"Barta momee babu abinda zataci bari ta huta.



Sunje da niyyar kwana biyu,Amma sai zainab din ta nuna zata zauna da surukar nawani lokaci.

Babu kalar masifar da abubakar din beyimataba Amma ta nuna itadai can zata zauna dole ya barota ya koma katsinan da niyyar sai karshen.sati yakoma ya d'aukota.


Ba k'aramin farinciki momeen tai ba dan sosai zainab din tashiga ranta.

Saigashi cikin Amincin Allah Cikin kwanakin da zainab din tai tare dasu Sun yaba da kyawawan d'abi,unta harma sunajin sha'awar tsarin addinin.


Aban garenshi kuwa Saida yai kwana biyu sannan ya kirata shima dan yaji lafiyar jikinta ne.

Cikin farinciki ta gaisheshi yayinda shikuma ya amsa a cinkoshi,dan sosai yai missing dinta tunda sukai aure basu taba raba makwanciba balle har a yini ba aga junaba Amma yaji muryarta qalau kenan ma shi kadai keshan wahalarshi.


"Albishirinka Dr,

Saida ya harari wayar kamin yace"Babu wani goro da zanbaki danni fishi nake dake ma.


"Yamutse fuska tai kamin tace To shikenan yabasheka ai.
"Tsaya tsaya gayamin zanbaki.

"d'azu merry ke cemin zata musulunta idan ta shirya kuma gaban momee mukai maganar Amma bataimata fada ba,kuma bata bata fuskaba.

"Alhamdulillah ya furta abayyane yana kuma tuno maganar Ahmad dake lallashinya Akan yai hakuri kila zamanta can yasa su fahimci gaskiya.




BAYAN WATA BAKWAI.


***

Zaune nake afalo na mike k'afafuna sabida kumburin da sukayi.Mama na kichen Amma ahaka muke hira kusan hirar akan yaron zainab ne wanda yaci sunan Abba Amma ana kiranshi da abulkhairi dan tuni ta haihu tana katsina yanxuma maganar dawowarta akeyi.
Abubuwa da yawa sunfaru ciki hadda musulintar maman abubabar watanni hudu da suka wuce shiyasa Abba ya yanke shawarar idan zainab tatashi dawowa to sukoma gidan Ahmda gaba daya tunda babbane kamin yai gininshi,Dan sukuma fahimtar addini sosai tunda su sukansu suka musulunta.


Sannan girman jikina dan.yanzu banda matsalar komai Inuwar Dr. tagaji ta hakura dashi Sabida yawan amfani da jan miski da mukeyi sannan kowa be barci idan dare yayi,Hakika Allah ya amsa,Tunda gashi komai yazama tarihi.

Sannan Dangin abba sunzo sun nemi gafarar abban da iyalinshi akan dukkan abinda yafaru.

Shiyasa hankali ya kwanta ta ko ina,Adacan babu wanda yai tunanin wa innan abubuwan zasu wuce,Saigashi yanzu saidai labari.

Tunda nasami ciki so daya naje gida sabida makaranta gakuma laulayi shiyasa nak'osa in haihu Nima nakoma gidan.


Saukar lallausan hannunshi saman k'afafuna yasani saurin maida idanuna kanshi.

"Sannu da zuwa Dr.

"Yauwa babyna,Sannu da kokari Ai kin kusa insha Allah.

Murmushi nasaki kawai tare da rike hannunshi da tuni ya sakashi cikin rigata"Dan Allah kabari mama fa tana kichen.

"To naji Amma kitashi muje ciki tukunna dan Allah karkice a a pls.

Saida yatemakamin Sannan na mike.

Dama nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki Dan Yau kwana biyu ba aiba shinefa ya gaza hakuri,.


Sosai nabashi hadin kai tunda nima inaso,Saidai me tunda yafita daga jikina naji wani irin dunkulewa da cikin yai yana kwance gefena nikuma ina gefe ina murkusu.

Saida ya bude idanunshi Sannan yaga halin danake ciki.

Da saurinshi ya daura tawul tare da direni k'asa dan gabadaya haihuwar tataho.


Dagani saishi cikin d'akin har nagama artabuna,Dayake dama ya aje komai na bukata sabida tsaron lalura.

Allah yabani haihuwar namiji yaron babbane sosai shiyasa saida ya k'arani dan yasami hanya sosai.

Kuka nasaka lokacinda yakemin dinkin dan Allurar da yaimin banwani ji amdanintaba.


Sannu yaketa jeramin kamar zaiyi kuka sabida tsabar tausayi.


Mamaki naketayi wai na haihu dama kullun addua ta itace Allah yasa kadda inyi doguwar nakuda.

Saida yagama goge yaron wanda keta kuka Sannan ya temakamin na kwanta gado.

Da mama sukaci karo zata shigo cikin bangarenmu.

"Kuka naketa ji kamar nan Ko kunnena ne?

Hannunta yakama zuwa cikin d'akin.

Mamaki ya kasheta ganin k'aton jaririn gabana nikuma lokacin nafara barci.

lokaci guda ta duk'a tare da yin sujada tsabar farinciki.

D'aukar yaron tai tare da rungumeshi tana kwararomishi addua.




***

Shagali akai banida shagaliba,Dan kowa ya.shaida na nesa dana kusa.

Kwananmu tara mukai kano wanka wanda mamanshi da kanta ta tsara hakan.

Dr. beso hakanba Amma ganin anfi karfinshi.dole ya hakura.



Duk sati yake zuwa dubomu yayinda duk zuwa da fada muke rabuwa,Nacinshi yasa inayin kwana hamsin mama ta tarkatoni wani zuwa da yayi,Babu kunya yaita mata godiya.

Dady shine sunan da muke kiran yarona dashi dan sunan mahaifina yaci.



komawarmu katsina muka bude sabon shafin soyayya da tsantsar kulawa da juna dan ni kaina yanzu nasan inason Amadina.

Bamu da wata sauran matsala sai dan abinda ba a rasaba na rayuwa.

Tunda nakoma makaranta sai rainon dadyn yakoma wajan mama.


Tuni su zainab sun tare gidansu ita da surukarta dakuma kannen mijin wa inda ke tsananin sonta.


Todai dama haka rayuwar take mahakurci mawadaci.




kwance muke muna hira nidashi gwanin nishadi kusan duk labarun abubuwan da suka wuce yakeban.

"Kinga dama kince komai zai wuce gashi Allah ya amsa nima nazama daga cikin mutane.


dariya nasaki kamin nace kenan da ba cikin mutane kake va?

"Eh mana kemafa maye kike cemin ko?


murmushi nai kamin nace eh mana tunda gashi ko yanzu ka lashemin kurwa nace inba kaiba sai rijiya?




maman khadija ke muku fatan Alkhairi.



duka anan nakawo karshen.wannan labari,

Nagode sosai.


Dan Allah duk wanda nabatawa inafatan ya yafemin.

Allah yasaakwai wani abu na amfani da dayanmu.zai iya amfana dashi.

kura kuran dake ciki Allah ka yafe mana.





Haske writers association.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment