Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka dashi take yini.

Wata irin kewarta yakeji tunma kamin yai tafiyar.

Yayi sallama da iyayen nashi Amma ya kasa tafiya jiran zuwan ayshan yake idan suka gaisa saiya wuce Dan jirgin k'arfe biyar zai hau zuwa Lagos.

Da kwatance ta k'araso gidan duk kwakkwafin mutun banda idanunta baka isa kace kaga wani Abu daga jikinta ba.
Tajima tana kwankwasa kofar gidan sannan ta fahimci antaho budewa.

Sannu da zuwa yaimin bayan ya bude gidan nikuma ta gaidashi tare da wucewa ciki ina kuma kallon tsarin gidan yo wancan lokacin ai hankali ba kwanceba yaushema nasan kan gidan.

Da gudunta ta fito ta rungumeni nima na rungumeta ina murna Dan ganinai kamar an canzata tsabar kyan da tayi saidai 'yar datayi.

Rasa inda zata sakani tayi tsabar murna dole yahada kayanshi yabar gidan Dan gabadaya hankalinta ya koma kaina.
Awaje sukai sallama sainaga tashigo tana share hawaye.
Dariya nasaki inafadin kai yaya Dan Allah kuka kikeyi Dan zai tafi? To kodai in koma ne?

Hararata tayi kamin mucigaba da hira saida naci na koshi sannan nai sallar la'asar dan tun kamin in k'araso aka yita.



Koda zai tashi saida ya kira ta yakuma kwantar mata da hankali Sannan ya wuce nidai iyakaci ido inadaga gefe balle danaga saiwani zubamishi shagwaba da takeyi.

Sakonin yayuna nabata Wanda duk kusan kayan gyaran jikine saikuma kayan k'amshi sannan nakira mama muka kuma gaisawa duk da na gayamusu na sauka lafiya.



***

Dare;
Kwance muke saman gadonta sai labari takemin nima inabata labarin abubuwan da akai batanan anan har muka gangaro akan matsalar Dr.din nan tabani labarin kaf abinda ke faruwa kamin ta numfasa.

Nima wani irin shiru naji kunnena da zuciyata yayi lallai wannan abun akwai d'aure kai ciki,Sannan kuma akwai abubuwa na tsoro toma waye ke wannan iya shegen?

"Amma sainaji kamar ance aurenshi bakwai ko?

" a a aysha biyarne kawai mutunene ke cewa haka nice ta shidda.

"To Allah ya kyauta Ammadai gaskiya yabani tausayi wlh.

" Sosaima saima kinga lokacinda yakeban labari haka iyayenshi Sam basu da kwaciyar hankali kumafa shi k'adaine namiji d'akinsu.




***
Koda mukai sallar isha'i kuma zaman mu mukai mana hira dambun nama mukaci muka koshi inatajin dadi nifa zan iya cewa a aure babu abinda yake birgeni irin inga gida sabo ga kayan d'aki sabbi sannan komai zakai nakane gidankane inason haka.

Dama gida rufe yake shiyasa kawai muka nufi gado"Kinga yaya fati ba barci zamuyiba kitashi muyi karatu kamin yadawo mun sauke kilama hadda matsalar jinni danhaka dagewa zamuyi dakuma addu'o,I Allah ya temaka yasa iyakar damuwar kenan.



** **

Kwana na biyu cikin garin katsina dadi kawai mukeci abinmu ammafa mun tsananta addua dannasan babu abinda yafi k'arfin Allah saidai ya jinkirta lokaci.


Tashi tai dan d'auro alwala kamin tace uhum aini wallahi ko mutuwa nayi yanzu hankalina ya kwanta tunda nasami muradin rayuwata.


Sai wajan 11 muka kwanta bayan mun kunna na yawa,Nidai bansan lokacinda barci ya sureniba dan da hirar su nake saurare.
Da mamaki nai barci gaskiya yanason yaya fati sosai musamman da na lura da yanda yake matukar kulawa da ita.


Lafiya lau muka tashi,Inajin yanda taketa zabga mishi shagwaba akan yabari muje gidansu shikuma yana tirjewa saida Tafara mishi kukan k'arya Sannan ya amince.

Dariya naita mata"Kai yayata gaskiya kin iya shagwaba yanzu ashedai ba ni kadai bace me rigimar da aka raina da danayi Abu sai anyimin sheri Ashe kema kin iya?

Murmushi tasaki,bazaki ganeba aysha Amma fa hakan abun yake maza da yawa na matukar son mace me shagwaba Ammafa itama shagwabar akwai ta hankali data hauka,Na lura Dr.yanaso shiyasa dole na arota na yafama kaina danni duk abinda yakeso tofa sai inda k'arfina ya kare, Tashi maza muyi shirinmu dan Allah mubar gidannan wallahi dama nagaji inaga so biyu nataba fita fa wannan yakaini gidansu da yamma saikuma fitar da mukai da dare.

Saida muka gyara ko ina mukaci abinci Sannan muka shirya,Kamar yadda Al'adar gidanmu take dankuwa mun killace jikinmu ko ina da ina,Sannan ta rufe gidan,A hankali muke tafiya dayake gidan babu irin nisannan sosai shiyasa muna tafe muna hira.


Kai naga inda ake nuna gata dan mamansu Dr. Yitai kamar zata Goya yaya fatin sai nan nan take da ita.

Wani irin farinciki takeji na ganin surukar tata dan tasan wannan karan ya d'auko me tarin ilmi,Saida akai Sallar azahar abbansu ya shigo nan muka gaidashi shima haka yaita murna da ganinmu "Aysha nan zaki zauna mana ko?

Murmushi nai tare da kuma sadda kaina k'asa,A a baba kwana biyar kawai Abba yabani.

" A a ba za ai hakaba aiko nan zaki zauna ko wata daya kiyi Zankira alhajin naku.

Murmushi nakumayi kamin ince ai befi sati biyu mufara jarabawaba.

"OK Allah sarki to Allah ya temaka Ammadai duk da haka zaki iya mana sati daya,Am hajiya kinsata tashiga wajansu yaya bala kuwa?


D'an zakudawa tayi amma yanayinta ya canza" A a alhaji danaga mijinnata be ce taje can dinba,Kumadai kasan halinsu kadda taje wata maganar ta biyo baya.

"A a hajiya aiba biyemusu zamuyiba danhaka ta shirya sai Usman yazo ya kaisu su gaida kowa dan Allah saiya maido dasu bansan wani surutu daban.



***

Babban gidane Wanda yake da bangare bangare kai tsaye bazaka kirasu da masu kudiba haka kuma bazaka kirasa matalautaba.

Bangaren da babban gidan yake usman din ya nufa damu saida yaimata bayanin ga matar Dr.Ahmad nan alhaji yace arakota ta gaisheku sannan yace zaije ya dawo kaminnan mun gama.


Matar tafara manyanta da farinciki ta taremu shiyasa muma muka gaisheta cikin jin dadin kulawar da taimana.

Wata budurwa ta kira da alama diyartace tace duk ta rakamu sauran bangarorin.





Haske writer's association.
12/10/20, 7:49 AM - Naffy Aliyu Umar: JARUMA.
11
Na maman khadija.




"Ah hafsat baki akayine? Cewar wata mata data fito daga bangaren hagu nagidan.

" eh inna matar ya Ahmad ce da k'anwarta tazo gaidaku.

Kamar bazata kuma maganaba sannan tace To ku shigo daga ciki mu gaisa.

Ganin yanda matar keta neman fuskokinmu dake lilleba yasani cire nikaf din dake fuskata itama na cire na fuskarta kamin in shigar da idanuna cikin na matar nace gatanan!!

Adan kunyace tace Allah sarki Allah yabaku zaman lafiya da rayuwa me dorewa Sannu kinji ashema be gari shi amadun?

Mikewa mukai mukabar matar tsaye tana k'aremana kallo.

Dawasu matasa mukaci karo to dayake duk babu nikaf din afuskarmu shiyasa sukabimu da kallo har mun gotasu daya ya kwalama budurwar da muke tare kira ta koma wajansu da Sauri munajin lokacinda yake tambayarta su waye wa incan 'yammatan? Tabasu amsa da cewar matar ya Ahmad ce da k'anwarta.


Zan iya cewa daga d'akin farko bamu kuma samun tarbar arziki ba dan gasudai da yawa Amma Sam basu da hadin kai balle zumunci banda tsabar bakin ciki da hassada babu abinda ke gabansu.
Inda mukaje daga karshe shine alhaji sunusi shima babu laifi dankuwa daga kallon yanda aka gyarawajan zakasan yafi sauran arziki.

Mun tadda me gidan dan saida hafsat din ta kaimu har falonshi muka gaidashi Sannan muka dawo falon matar gidan nan muka tadda wata yarinya bazata wuce sa'ataba.
Ko kallonmu bataiba balle muma mu kalleta hafsat ce tai mata magana,Itakuma yarinyar ta amsa mata a wulakance.

Duk yawon da mukai cikin gidan nan babu Wanda yabamu ko ruwane.balle musaran abinci
Munzo fitane naji saukar muryar wannan yarinyar na fadin uhun kwana nawane kema zaki shude kamar sauran???.

Duk da rikon da ya fati taimin Amma saida ba juyo cikin idonta na kalleta ga uwarta zaune kamin ince idan Ke ko ubanki ke kashewa yau karta kwana duniya kinji ko?

Jana ya fati tai tana hararata hannunta samar kirjinta"Ni matsalata dake rashin hakuri aysha dan Allah kai dinga kauda kai akan rayuwar duniya 'yar uwarshi ce fa?

Harararta nayi kamar idanuna zasu fado kamin ince lallaima sai kawai inzuba ido tagayamana magana bayan hararramu datagamayi ko? To bazan iyaba.

Hafsat ce tace wallahi ya fati gara dataimata haka itafa 'yar rainin wayauce waifa ya Ahmad takeso ahaka shine take wannan hura hancin.


**

Maman hafsat ita tabamu ruwa hadda abinci Sannan mukai sallar la'asar muka fito zamu koma dan usman yana wajan matasan gidan wa inda suke zazzaune daga wajan d'akunansu.

Da alama maganarmu sukeyi dan muna fitowa duk suka Watso idanunsu akanmu,Wani da yake me zubin tsagera ya matso wajanmu yana murmushi"Ashe matar yaya Ahmad ce agidan ai bamu saniba da munkawo gaisuwa.

Murmushi tasaki kamin tace babu komai wallahi ai dayake duk ba saninku nayiba shiyasa.
Anan yagane cewa itace matar Dr. Din.
Kallona yai ina kokarin daura nikaf dina"Sis zamu shigo anjima muga d'akin yayarmu munafatan za ayi maraba damu?

Ban kalleshiba balle yasaran zan kulashi danni gabadaya tarbiyyar gidan bataiminba bama wannan ba har yanzu raina be huceba daga iskancin wannan tsigitsilar yarinyar.




Har muka koma gidansu Dr.ban huceba dannifa haka nake da zuciya wani lokacin musamman idan banyi masifar na zubarda bacin rainaba.


Mamanshi ta taremu kamar d'azu kamin takawomana abinci da lemuna,Komai tsaf bata da k'aramin yaro sai jikarta guda daya dake hannunta me sunanta Amma suna kiran yarinyar da ummi.

Sakin jikina nai mukaita hira da ita yayinda kunya ta hana ya fati ko motsin kirki ni dariyama ta dinga bani.
Anan nake bata labarin duk abinda yafaru damukaje.

Uhunm aifa saidai hakuri Amma wallahi muma haka muke fama dasu saidai idan ba a haduba ko sati biyu ba aima nan yayarsu taso zuwa taima wannan matar me bangaren dama kashedi dakyar muka tausheta tai hakuri ni wallahi banga abin zafiba mufa Ahmad ne kawai namiji cikin gidan na kuma ubanshi ya tsayamishi har yazama wani Sukuma ya basu mazan amma kuma sunkasa tankwarasu balle su zama wasu harma su Mora to hakan bemusuba kuma gani sukeyi kamar ba akyautamusuba bamusan me suke nufi ba.

Haka taita janmu da hira har saida Dr.ya kira wai munkoma gida ko?
Tace mishi a a Nan Yakama fada wai bayace kadda akai dareba.

Mamanshi ce ta k'arbi wayar tana mai fadan ita tace mujira muci abincin dare tukunna.
12/10/20, 7:49 AM - Naffy Aliyu Umar: JARUMA.
12
Na maman khadija.




Wannan usman din shine ya maidamu gida bayan maman tace gobe mu shiryo da wuri ya rakamu gidan yayun Dr.din kamin yadawo dan Sam beson fita shi.

Dagani har ya fatin murna muketayi,Dan gaskiya zaman waje daya babu dadi Sannan zamu ga gari.



***

Tunda nafito wanka nakejin yanda suketa hira abunsu sai shagwaba takemishi shikuma da alama aikin lallashi yakeyi.

Kayan barcina na saka kamin na haye gado ina jero addua kamar yadda nasaba,Bayan alwala wadda gabadaya tagama zama jikina dan ban iya zama batare danayi alwalaba.

Dawowa gefena tai ta kwanta itama tare da sakarmin murmushi har lokacin wayar ba kunnenta.

Bakina na turogaba kamin in yamutse fuska na A hankali naga wayata na haske dan bansan ring ko kadan.

Saida na hariri wayar kamin ince yauwa d'an anace zai hanani barci yanzu.

"Hello"

Kuma hararar wayar nayi kamar yana gabana kamin ince Assalamu alaikum.

Cikin dan jin kunya ya amsamin sallamar kamin ya Dora da fadin"Sorry hajjaju naga bamuyi wayaba tun shekaranjiya shine nace bari yanzu in kira Allah yasa banyi laifina?

Yamutse fuska nayi kamin ince ni wallahi malam yawan maganarka kawai ke hadani dakai kumama fa kacemin Abba yace ka dakata Amma kuma banga kana niyyar dakatawarba.

Inajin ajiyar zuciyar daya sauke kamin yace"Dan Allah ki tausayamin aysha wallahi soyayyarki wahalar dani takeyi Koda abban yace in saurara ainasan yana nufin ku idasa jarabawane shiyasa zandan jira Ammadai duk da haka ai bazan daina kulakiba ko? Ko kinaso soyayyarki ta kasheni ne?

"A a banso gaskiya .

" yauwa autar mata to dan Allah ki dinga kulani ko bazakice komaiba,Kimmasan meya faru?

Gyara kwanciyata nayi kamin ince a a saika gayamin.

"Kinsan malam ashir ai?

Cikin k'osawa da maganar nace eh nasanshi mana.


" Hummm wai Ashe sonki yakeyi kawai saidai naga ya nutsu waje guda saina leka kawai sainaga Ashe hotanki yaketa kallo kina cikin ajin malama binta kinamusu karatu bama kisan an daukeshiba.

Dafe kirjina nayi kamin ince innalillahi malam ashir din? Ammadai be kyautaminba wlh Allah ya kyautamishi to wahalalle.

Cikin jin dadi yai dariya kamin yace bari in barki esha sai gobe zan kiraki Insha Allah,Nasan kula samari ba halinki bane balle ince dan Allah karki kula kowa.

Ajiye wayata nai tare da kallon ya fati data shige cikin bargo har kanta wayar sukeyi har yanzu saidai hirar tasu tai zafine sosai shiyasa ta kudundune ni dariyama ta bani,Juyamata bayana nai nai kwanciyata bayan nakuma jero wasu addu'o,In.



***

Cikin kasala da nauyin jiki tatashi sabida doguwar hirar da sukasha" Kema ai ya fati hadda laifinki wallahi kingaji bazakicemishi zaki kwantaba sai ki biyemishi yanzu gashinan banda makara da kikayi hadda ciwan bacci kikatashi dashi.

Idanunta alumshe ta kalleni kamin tace"Kekam kincika mita wallahi mijinanefa yace yana cikin yanayin buk'ata idan ban tsaya na samamishi nutsuwaba gun wa zashi? Ko so kk haka kawai inkwana Allah na fushi dani?

Shigewa nai kitchen batare Dana tankaba,Dannifa gani nake tacika zurmawa da yawa banjin zan iya lalacewa wajan nunama namiji wannan zazzafan so din bama zan iyaba.


Sai wajan 11 nasafe sannan mukabar gidan lokacin nacika nai taf tsabar zuciya dan da safenma kiranta yai suka shafe wani lokaci me yawa Sannan yabarta ta shirya.


Yauma kamar jiya haka iyayen Dr.din sukaita nan nan damu musamman yaya fati din tunda itace tasun nidai adduata Allah yasa tayi doguwar rayuwa.




**"""***

Gidan hajiya maimuna mukafara zuwa itace babba cikin d'akinsu macece 'yar kasuwa wadda tasan darajar kudi,A harabar katafaren gidanta muka ganta tsaye hadda megidan da yaranta da alama jiranmu sukeyi,Da sassarfa ta iso ta rungume ya fati kamin ta riko hannuna bakinta har kunne tsabar murna.

Wai garin dadi yana nesa, tsayawa fadin haduwar falon bata lokacine dan ankashe mishi kudi na hauka.

Har k'asa muka duka muka gaishe da megidan nata kamin ya wuce Sama sukuma yaranta suka gaishemu bayan ancika gabanmu da kayan ciye ciye na kwalama.

"Amarya ya amarci wallahi rannan naso alhaji ya biya dani gidanki mu gaisa Amma yaki wai kadda mu takura muku,Ashe autan benan?

Kanta a k'asa ta amsa da eh benan.

" wayyo Allah ya dawo dashi lafiya Amma ki saki jikinki mana Fatima mun Riga mun zama daya fa!!


Nikam tuni na saje da 'yammatanta dan manyan zasuyi sa'ata kuma 'yan biyune hasana da usaina.

A hankali takejanta da hira mukuma muna gefe muna tamu dan basu da wuyar sabo musamman da sukemin kallon 'yar uwarsu.


Sam banyi tunanin akwai babban namiji saurayiba gidan,Kawai saidai mukaji sallama duk tashi sukai sunamai sannu da zuwa hadda wani rikemishi hannu gasu manya dasu saidai daga gani zasubaka sha'awa dan akwai shakuwa da tarin kauna tsakaninsu.

Manyan idanunshi ya zube akaina,Cikin daburcewa na jawo hijab dina nasaka Sannan nace mishi ina yini? Lokacin ya k'araso cikin falon har ya zauna.
Ba tare daya amsaba yacigaba da kureni da idanunshi kamin ya dan tabe baki ya kalli hasana tambaya yaimata da idanunshi.

Cikin yanayin zumudi tace mishi YAYA k'anwar matar uncle ce dazu sukazo aunty din tana ciki da mom.

Wani munafukin murmushi yayi kamin ya mikomin hannunshi alamun mu gaisa.

Fararen idanuna na jiuyamishi kamin in boye hannuwana cikin hijab ina turo baki,Yayinda cikin raina nake jinjina iskanci nawasu matasan.

Ruwan da usaina ta mikomishi ya amsa da hannunshi Wanda ya mikomin din yanajin yanda kirjinshi ya tsananta bugawa.

"Yaya in kawo abincin? Cewar saudat tana durkushe gabanshi.

Batare daya kalletaba yace me kuka dafa yau?

" yaya tuwone da miyar ganye.

"Ok kawomin nan.

Kallona yai niko ya yamutse fuska,mamaki nake araina yanda sukemai biyayayya saikace shine ya haifesu Ji yanda yakemusu iko dawani shan k'amshi.
Kuma juyawa nayi Amma har lokacin babu alamun ya fati zata shigo kuma bansan inda suke shigeba,Kuma ta kurewa nayi waje daya danni na tsani ka tasani kaita kallo ko wannan dandai gidansu nazo na tabbata da yanzu nagama wankeshi na k'ara gaba.

" saudat jeki kiramin ya fati dan Allah tazo mu wuce tunda inda zamu da yawa.

Lumshe idanunshi yayi yanajin saukar muryata har cikin jininshi lallai abun babbane.

Ajiyar zuciya na sauke jin tahowarsu ya fatin.


"Ah aunty sannu da zuwa,Ya furta yana mata murmushi.

" yauwa Hafiz ya gida ya aiki?

"Alhamdulillah nadawo na tadda wata bakauya cikin falon nan, Yai maganar yana kallon inda nake.

Harararshi nayi kamin in dauke idanuna daga kashi suko duk dariya sukayi.

Yaso ya kaimu Amma sai mom dinsu tace ai tare muke da usman shine zai kaimu duk inda zamu.

Dafe kanshi yayi Sam bahaka yasoba.

Fakaitar idanun mutane nai naimishi gwalo aiko nan take ya fiddo manyan idanunshi niko na juyamishi nawa na rufe fuskata da nikaf mukabar falon.

Shikadai yasaki dariya tare da dafe kirjinshi lallai wannan yarinyar za a da ita.




Haske writer's association.
12/10/20, 7:50 AM - Naffy Aliyu Umar: 🇯 🇦 🇷 🇺 🇲 🇦 .
13
Na maman khadija



K'asa k'asa nake dariya bayan daidaita zaman mu cikin motar"To muguwa dariyar me kikeyi nifa bansan haka!!!

Wata dariyar nayi kamin in nade nikaf dina,Kai ya fati nifa wannan guy dinne ya ban dariya waifa hannu ya mikomin mu gaisa saikace wasu 'yan tasha.

Itama dariyar tayi kamin tace wallahi kema sa'a kikaci amma ana fadin miskilancinshi kawaidai kila daga kallo daya kin sace zuciyarshi ne shiyasa yaga gara yafara share hanya tun yanzu.

Yamutse fuska nayi,Lallaima yaya Amma wallahi kin cuceni me zanyi da wannan ragowar shawarar? daga ganima ko lafiyar kirki beda ita.

Daga ita har usman din dariya sukai kamin yace Ammdai aysha kin iya sharri wlh.

Ya fatin ce tace Wallahi qalau yake likitane shima kawaidai tsabar hutune tasa saikiga jikinshi kamar malalaci niko birgeni yakeyi wallahi dan akwai tsare gira.


Bakina na tabe kamin ince can da yawarshi wlh ni ko kadan babu abinda yaimin daga gareshi ballema daga ganinshi zai yi riko da d'abi'ar nasara.

Kusan da hirarshi muka k'arasa har gidan hajiya halima itace ke bima hajiya maimunan saidai ita Allah be bata haihuwaba daga ita sai mijin ke rayuwarsu daga bayane ta d'auki diyar hannatu k'anwarta dakebimata to gashi har itama tafara zama budurwa.

Gaskiya duk sunada dukiya koda yake kamar yadda naji mamansu tana fadi cikinsu babu wacce bata aiki shiyasa suke cikin daula dama irinta kenan ko miji beyimakaba kai saimakayi ma kanka.

Rasa inda zata sakamu tai tsabar farinciki da ganin mu.

Me gidanta benan haka yarinyar dake wajanta mesuna iman,Shiyasa daga ita sai meyimata aiki kuma zaune suke suna hira da alama bata da girman kai irin na wasu masu kudin masujin sunfi k'arfin suyi hira da ma'aikatansu.


Kamar wancan gidan nan ma soyayyan dambun nama aka kawonama da lemuna nikam cika cikina nai wlh dan ko ajikina ya fati ce naga saiwani basarwa takeyi.


Sai gab da la'asar mukabar gidan ta dan hira gareta sosai usman dinma nan falonta ya shigo akacigaba da hirar dashi.

Itama kayan k'amshi kala kala tabamu najiki dana kaya dana gida mukai mata godiya har munshiga mota saigata da sauri da Leda ta mikomin.

Amsa nai tare da yimata godiya,Saidai muna fara tafiya naji raina yana Neman baci ashewai dambun naman nan ne ta zubocikin Leda me yawa gaske,Kawai sainai tunanin kodai kallon mayunwaciya tai minne dan taga naci.
Usmanne ya katsemin tunanin danakeyi inda naji yana cewa"Naso ace batai mana robawa ta d'an kullomana wannan dambun naman tsakani da Allah ya hadu.

Ajiyar zuciya nasauke ahankali kamin ince gashi ai shine ta mikomin.

Alhamdulillah ya furta kamin yace wallahi dama har addua nake bari idan munfito gidan aunty Hanna saimu ci kamin mukoma

Please Login or Register in order to submit comment