Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai khairat da muhusin Amma duk suna wajan kakanninsu kuma ni kaina ganinsu wahala yakemin wallahi garama muhusin anakawoshi weekend wani lokacin Amma khairat nema sukema su haramtamin ganinta,Tunda suna tunanin nine na kashe mamarta kadda itama na kasheta,Ahankali ya idasa maganar yanajin wani dacin zuciya.

Itama marairaicewa tayi kamin tace kayi hakuri dan Allah komai lokacine wataran sai labari da sannu zasu gane ba laifinka bane kaji Dr.kayi hakuri.


Rungumeta yai ya sumbaci kincinta kamin yace jeki d'aukomana filet muci abinci inbaki labarin waye Ahmad dakuma yanda mata shidda suka mutu masu aurena.





Haske writers association.
12/10/20, 7:46 AM - Naffy Aliyu Umar: JARUMA.
7


Na maman khadija.




"Kamar yadda na gayamiki ko kika sani Alhaji Ibrahim shine mahaifina 'yan asalin wannan garinne haka mamana suna cikin gidan yawane duk da cewa alhajinmu yanada kudi sosai Amma 'yan uwanshi suka hanashi yatashi gaba daya su takwas ne maza biyar mata uku amma matan biyu sun rasu saura daya, Mahaifina kusan shine k'arami cikin mazan Amma matan kebimishi to gaskiya duk ya fisu arziki nesa ba kusaba danshi yana aikin gwamnati sannan ga kasuwanci,To ahaka yazama wani cikinsu Amma suka hanashi ya koma gidan shi daya gina sabida suna tunanin idan yaimusu nisa bazai iya temakamusu ba.
Ahaka dai zaman ya kasance da dadi babu dadi anadai tare kinsan zaman gidan yawa yanda yake.
Matasalar data tilastamana barin gidan shine haihuwar mata da mama taitayi saida ta haifi yara biyar duk mata Sannan haihuwar ta tsayamata gorin yau daban na gobe daban baga matan gidanba baga mazan gidanba dan wallahi basu da wani hadin kai kawaidai kowa akwai abinda yake boyewane cikin zuciyarshi.

Wannan halin yasa Abba yabar gidan batare da ya kuma sauraran 'yan uwan nashiba,Saigashi ko shekara mama bataiba cikin sabon gidan ta haifeni nine auta Fatima dagani mama bata kuka haihuwaba,Abba mutunne me hakuri sosai shiyasa duk abinda danginshi kemishi be taba damunshiba, yayuna duk sunyi aure kuma ko wacce saida tai karatu me zurfi Sannan yaimusu aure shiyasa yanzu haka duk suna aiki d'ayace kawai batayi itama mijinne be yardaba wacce nake bi mawa tana can garinku tana aure, Ahankali duk zaki sansu.

Ina matakin k'arshe na karatuna a London wani iftila'i ya fadoma Abba Domin kawai wayar gari akayi dukiyarshi nata lalacewa cikin sati guda saida yakoma gidan da yake cikine kawai yaimishi saura Amma har kudin acct dinshi saida suka Lula shi kanshi bazaice ga abinda ya faruba balle wani yabada labari abun kamar almara, Ke kinsan irin kadarorin da Abba yakedasu kuwa gonaki filaye da gidaje.
Nanfa surutun mutune ya yawaita kowa da abinda yake fadi na zargi akan abban,Nidai bansan meke faruwaba dan saida yai ma yayuna kashedin kadda Wanda ya gayamin matsalar da ake ciki.

Abu kamar wasa saiyazama gaske dan da ya ajiye aiki amma yaga zaman bazai yiwuba dan ko jali saiya koma bedashi,Kinsan haihuwar mata tanada matukar muhimmanci Fatima wallahi lokacin su aunty suka d'auki nauyin gidan.domin Abba besami halin komawa aiki ba.
Inacan bansan abinda ke faruwaba matsalar kudi tatasomin sabida jarabawar k'arshe da zanyi danhaka babu wani damuwa na kira Abba akan ya turomin kudi kuma masu yawan gaske,Babu wata damuwa ya sayar da gidan da suke ciki yakuma komawa gidan gandun daya baro duk da cewa ranshi besoba sannan mutane natamishi jaje da Allah ya kyauta saidai sabanin 'yan uwanshi wa inda murnarsu ta kasa boyuwa sabida ya dawo cikinsu saima maganganu da sukaita yadama mama magana akan arxikin da sukayi gashi angulu ta koma gidan ta na tsamiya.

Zaman da su mama sukayi a gidan zamane Mara dadi dankuwa kullun da kalar gorin da matan gidan kemata Amma Sam bata taba kallonsuba dan itama mama kusan halin Abban gareta Saidai ita idan ka cikata akwai bak'ar zuciya.

Saida na kammala karatuna tsaf tsabar kyan da takarduna sukayi yasa suka rikeni awani babban asbt inda sukafara biyana wasu makudan kudi amatsayin albashi.

Abba yayi fada sosai Amma nai shiru dashi Nafara aikina dan bansan halin da suke ciki ba.

Wata biyu kawai dafara aikina na turomusu kudi wajan miliyan daya da rabi nace sufara sama albashina albarka duk da cewa akwai wasu 'yan harkoki da nakeyi,A can din.


Abba shiru yai da wa innan kudi bema fara tabasuba saida akai wajan wata biyu Sannan yasa yaron wani abokinshi ya bude wannan shago inda aka zuba kaya kuma akasami yaro nutsattse yafara tsare wajan.

Ingajerce miki labari Fatima saida nai shekara biyu sannan na aje musu aikinsu musamman da Abba yafara min fada sosai akan rashin dawowata.
Saidai me na dawo Nigeria da soyayyar wata yarinya me suna Firdausi itama 'yar nan ce amma ankaita ganin likita can londan din kuma ni tagani kasancewarmu 'yan kasa daya kuma gari daya kawai sai mukafara soyayya da ita kuma mahaifiyarta ta amince da hakan dan itama da alama naimata.

Hankalina yai matukar tashi lokacinda mama keban labarin duk abinda yafaru dan akalla shekarata biyar kenan rabona da Nigeria toma duk me yai zafi hakan saikace abin sa hannu.
Babban asbitin abuja nafara aiki bayan iyaye sunshiga maganata da fiddausi ban iya jure ganin iyayena cikin wannan gidan ba danhaka watana daya da dawowa nasaimusu wani kerarren gida nesa da unguwarmu ta da.
Saida suka tare Sannan nakoma wajan aiki.

Watanni takwas da dawowata akai bikina da fiddausi Alhamdulillah dayake dama mun fahimci juna da ita sosai saidai tanada wani ciwo a bayan mahaifarta dan sabida shi ma aka kaita London taga likita to gaskiya Saida akaimata maganin shi kamin su dawo Ashe bayan watanni biyar da yin aikin tacigaba dajin ciwon Amma tai shiru. Satinta uku gidana ciwon yatashi sabida kusantar da nakemata ina tabo ciwon,Sai nakaita asbt aranar kuma nakaita gidansu ta yini to suma sun san ciwon yatashi, Nan fa aka kuma dagewa magani. Gaskiya tana sona domin naso lokacin ta zauna gaban iyayenta na dinga binta can kullun danta sami kulawa saita nuna a a bataso ta barni tonikuma ga aiki lokacin.
Watanta biyu gidana Fatima farkin barci jini ya ballemata wallahi kamin duk iyayena da nata su iso asbt ta rasu.

Shiru yai yana sauke numfashi yayinda fatiman ke kuka sosai tana kuma shigewa jikinshi.

"Kowa lokacin niyake tausayi dayake dama duk kusan ansan da ciwon kawaidai babu Wanda yakawomata mutuwa kusa ne sabida yanda ake gani tana harkokinta.

Watanta bakwai da rasuwa na hadu da wata yarinya can abuja itakuma sunzo practical ne nan asbtnmu kawai sainaji ta kwantamin arai musamman dana lura duk ta fisu nutsuwa wa inda sukazo tare.
Akwai wani abokina mesuna Daniel shi nasa ya shigemin gaba aiko kamin su gama soyayya tai nisa tsakaninmu,.bayan na sanar gida akazo aka tambayamin to ashema mahaifinta d'an nan ne danhaka kamin tafara aiki akai bikinmu.

Fatima yanda kikasan almara haka saudat tafara ciwo tun ina tunanin laulayine hardai na kaita asbt naimata awo na musamman eh akwai ciki lokacin saidai bashine dalilin ciwon cikin da dakeyiba.

Watanta shidda agidana lokacin cikinta na wata hudu saita kama zubar jini shi wannan abokin nawa Daniel na bashi ragamar dubata,Indai yaimin bayanin cikin jikinta ne zai zube.
To dole mukai hakuri dan dole saiya zube din,To kuma sai yaki faduwa gaba daya da kaina naimata wankin ciki sannan aka dibi jinina aka k'aramata lokacin ga mamarta ga tawa duk tare suke da ita asbt.

Nikuma gida nake kwana.

Cikin barcina nai mafarkin wani mutun k'ato dashi ya danneta kamar rago ya yanka wuyanta, Wallahi ban iya komawa barciba har asuba gari be idasa wayewaba na kwasa zuwa asbtn,Saidai ina zuwa na tadda su mama nata kuka wai saidai aka farka akaga ta rasu Amma akwai d'an digon jini abakinta.

Basaina gayamiki na Shiga tashin hankaliba.

Ko shekara ba ayiba Abba ya nemamin diyar wani abokinshi me suna sajida wallahi kyaykkyawa da ita Fatima Amma ko shekara bataiba gidana itama ta rasu kuma abinda ke tsoratani shine duk kusan ciwon ciki ya kashesu kuma ko wacce saita zubar da jini kamin ta rasu.

To alokacinne 'yan uwan Abba suka fara maganar wai gaskiya yakamata a tuhumeni ina nake kai yaran mutane,Ranshi ya baci jin maganganun da danginshi ke fadi Amma dayake hakuri ne dashi sai be kulasuba.

Ni kaina naji tsoro Fatima bankuma cewa inason auren ba saida nai wajan shekaru biyu tokuma gaskiya inada bukatar mace sosai ajikina sainace Abbana ya tambayamin cikin yayunshi ko akwai Wanda zaibani auren diayarshi, Amma ga mamakinmu wallahi yanda kikasan hadin baki kowa cewa yai a a hazai iya bada diyarshi inda za a kashetaba.

Dole saidai na hakura alokacin inata adduar Allah ya kawomin wacce zata amince ta aureni.




Haske writers association.
12/10/20, 7:47 AM - Naffy Aliyu Umar: JARUMA.
8

Na maman khadija.




Bayan wani lokaci saina tafi wani cost can k'asar faransa watana takwas na dawo cikin wata sabuwar nasarar kowa yaso inyi aure lokacin Saidai bani da wacce zata aurene ke ni kainama tsoron tunkarar wata mace nakeyi da sunan so.
Wannan abokin nawa ya matsamin sainayi aure nikuma ina gayamishi ban ra ayi yanzu bansan meye matsalarshi da aurenaba balle shi ko daya har lokacin be yiba.

Akwai wata yarinya me suna zainab k'anwar matar wani abokinmune usman to matar ta haihu munje barka kamar yadda mukeyi imu-imu cikin abokai,Nidai bansan meya faruba Amma tunda Daniel yaimata kyauta shikenan yarinya ta haukace Sai ni kowa yai mamaki ke daga karshe har gidanmu take biyoni kan dole iyayenta suka amince da auren danda suma sun like akan bazasu kai yarsu inda zaka mutu .

To da zainab ne muka haihu saidai tunda cikinta ya tsufa lokaci zuwa lokaci takancemin itafa wani mugun mafarki takeyi,Saidai in yimata addua ince sharrin shaidanne kawai da aljanu.
Lafiya lau ta haihu nasami me sunan mama muke kiranta da khairat,Mutane anata tayani murna domin ana tunanin qaddarata tazo k'arshe.
Ashe abin bahakaba bane, Ranar da khairat tai watanni uku ranar zainab ta matsa wai sai anyima yarinyar bikin cikar watanni uku lafiya.
Naso in ki lokacin Amma zainab tasa fitina saida na amince yayuna sukazo aka shirya komai sabida agida za a yi komai.
Ina wajan aiki suka gama kammala komai kuma alhamdulillah sun tsara komai kuma komai ya tsaru yanda yakamata ban gayyaci kowaba daga abokaina ko matansu sai mutun daya dana gayamawa wato Daniel kuma shima na gayamishine bawai Dan ina tunanin zai zo ba tunda su suna katsina nikuma har lokacin ina abuja.
Kamar yadda ta kirani tana gayamin kowa yazo daga dangina zuwa nata sabida gidan cika yai saidai nai matukar mamaki da takecemin wai hadda abokina Daniel shima yazo kuma yaima yarinyar kyauta ta gasken gaske.

Naso indawo aranar koda da yammane tokuma gaskiya aiki yaimin yawa Amma tunda larabace sainai hakurin gara inbari juma'a kawai indawogaba daya har ma da k'arin sati daya Nima inaso in huta.

Saidai me ranar alhamis ina barci naji kiran waya cikin magagi na d'auketa Dan sosai barci ke kaina yo dare ya tsala lokacin.

Bansan lokacinda natashi zauneba sabida tsabar dimuwa data sameni wato sautin mahaifina naji yana fadin ko me nake ciki inyo asubancin dawowa gida Dan ga zainab nan sunkawo asbt jini ta baka ta hanc.


Zakiyi mamaki Fatima Dan kuwa awannan lokacin nabaro abuja kuma dagani sai kayan jikina.

Saidai koda na iso tuni aikin gama ya gama Dan har angama shirya zainab za akaita kwancinta,Nasha wuya Fatima nasha zagi wajan mutane tundaga lokacin suka dauke khairat ganintama saisunga dama suke bari inyi duk irin zuwan da zanyi kuwa.
Kinji mata hudu ko?

Kanta kawai ta iya dagamishi Dan sosai take kuka sabida tsabar tausayinshi,"Amma anya babu hannun abokinka cikin wannan ta'adin kuwa Dr ?

"Allah masani Fatima saidai bantaba kamashi da wani Abu makamancin hakanba Saima tausayina danake hange koda yaushe cikin idanunshi duk da yake shidin ya kasance kafiri.



Tundaga wannan lokacin na d'auki alkawarin bazan kuma aureba har duniya ta nade saidai na manta da alkalamin qaddarata Wanda be kareba Amma wallahi Fatima ina cikin yanayi na damuwa da tashin hankali sabida ni kaina nafara tunanin lallai kila nine ke cinye matan nawa duk da cewa ko naman mutun bantaba jin sha'awar ciba.


Tsananin sha awa dake damuna yasa na fara kula wata yarinya duk da na lura da batajin magana irin masu saida abincinnan tunkamin tafiya tai nisa na fahimci bawai aure take soba kawaidai 'yar a holece.
Dole na kyaleta,Amma duk cikin katsina saida narasa matar aure Fatima domin kona fara Neman kamin wani lokaci saikiga maganar ta lalace sabida yanda 'yan uwan alhaji ke kai sukata.
12/10/20, 7:48 AM - Naffy Aliyu Umar: JARUMA.
9

Na maman khadija.




"Numfashi ya sauke kamin yace tashi muje ki kuma gasa jikinki idan munyi Sallar la'asar saina idasa miki ko?.
Dan turo baki gaba tai kamin tace kai Dr Dan Allah ka idasamin ai labarin yazo k'arshe.

Dariya yayi tare da kuma rungumeta jikinshi.

" najima sosai ina walagigin Neman wadda zan aura amma babu bakuma wai matanne babu ba a a kawai wadda zatai kasadar aurena ce na rasa.
Haka hankalin iyayena ya tashi da yayuna To Amma babu yanda zasuyi.

Akwai wata dattijuwa dakema mama ayyukan gida itace tace ga wata marainiya nan datake riko idan zan aura.
Fatima yarinyar bata wuce inyi 'yar aiki da itaba Amma haka na amince da aurenta sabida dama bata da kowa sai wannan tsohuwa itakuma da alama ba rikon kirki takemataba.
Kuma yarinyar bata wani damuba sunanta fadila haka na aureta kuma ninai komai nidai fatana kawai in sauke abinda ya dankaremin Mara,karfa kice wai zaune nake ban Neman magani wallahi Fatima duk bokonnan da kikeganina cikinta haka nake shan hayaki ko garin magani ko rubutu idan ma ban ansoba to mama ko alhaji wani zai amso haka yayuna duk wadda taji me magani haka zaki ganta dashi.

Lafiya lau na zauna da fadila Saidai itama wajan haihuwar yaron ta rasu dan ko ganinshi ma bataiba yaron yana hannun yaya hauwa dan lokacin itace me k'aramin goyo ita ta shayar dashi,Ana yaye yaron yaran wannan tsohuwa suka d'aukeshi to shinefa har yanzu saidai muje mu ganoshi Amma nayi alkawarin indai kinyi shekara babu abinda ya sameki to zandawo da rikonsu hannuna,Nagaji Fatima wannan kaddarar tanada wuyar d'auka cikin mutune nayi kuka harna gaji bansan abinda ke bibiyar rayuwataba dan Allah ki tayani da addua nidai abunnan ya isheni.


Kuma shigewa tai jikinshi tanajin wani irin d'aci cikin ranta inama tanada damar dakatar da damuwarshi lallai data aikata hakan kodan ya huta da damuwa da zullumi.
"Kayi hakuri dan Allah komai zai wuce sukuma yaran Allah ya rayasu Amma baka tunanin 'yan uwan abbanku zasu iya yimaka wannan d'aurin musamman yanda kaxo ka watsa abinda ka shirya? Sannan shima wannan abokin naka yakamata kai taka tsan tsan dashi wallahi yanzu Allah ya kawomu wani lokaci da cuta tai yawa musulmi ma Neman yanda zai cutar da dan uwanshi yake balle kuma Arne Wanda bema yarda da Allahn ba yakamata ka kula gaskiya Amma gashi ni bamma ganshi ba.


" Zanyi insha Allah amma ni bana zargin kowa sai Wanda Allah ya tona asirinshi lokacin ne koma waye zai gane waye Ahmad wlh.
Daniel benan yana Uganda Amma yakusa dawowa nasan zaizo har gida Ku gaisa.
Shiru taimishi danfa ita hakanan taji arnen be yimataba.

Saida ya tabbata takuma Shiga ruwan Sannan yabar gidan yabarta da rigimar saita bishi.

Gidansu yakuma zuwa saidai ya tadda mahaifin nashi be dawoba shiyasa ya wuce wajan wasu sabgogin nashi duk da yaso ya zauna gidan ya huta bama wannan ba yakosa yaji abinda malam din zaice ne.


Sai bayan magriba yakuma komawa gidansu lokacin har abincin darensu an anshirya be shiga da motarshiba dan beso ya jima,Hankalinshi yayi gida.


"Naso kwarai da gaske inji wani Abu daga shi baba malam din saidai wallahi becemin komaiba Saima hakuri daya bani haka nataso batare da wata takamaimai din magana ba danhaka ka dage da addua muma zamu tayaka kuma ina kuma gargadinka babu ruwanka da 'yan uwana kome zasuce maka ban amince ka tanka musuba dan Allah,Tashi kaje kabaro diyar mutane Allah ya tsareku yai muku albarka,Cewar alhajin Ahmad din.

Da kasala ya koma gida dan gani yake kamar itama fatiman bazasu jimaba zatatai ta barshi lallai idan beyi da gaske ba to zai rasa imaninshi akan wannan qaddarar.

Da gudunta ta rungumeshi tana sakarmishi kukan shagwaba dan sosai tsoro yakamata lokacinda duhu yafara mamaye gari.

Rungumeta yai tsam jikinshi yana shakar kamshinta lallai Fatima tacika mace,Ahankali yakeji tana bin hanyoyin jininshi duk da cewa har yanzu be tabbatar da sonta yakeba.

" sorry madam na barki gida ke d'aya ko? Kiyi hakuri gida na biya saikuma na tsaya na siyomiki abin dadi.
Kayan hannunshi ta amsa suka k'arasa cikin falon inda wani sassanyan k'amshi ke tashi ga kuma sautin karatun alqur'ani dake tashi k'asa kasa.
Dadi yaji cikin ranshi ko babu komai shaidnun dake bibiyar rayuwarsu zasu barsu su huta kwana biyu.

Be jimaba yafita sallar isha'i .
Danhaka saida yadawo Sannan suka cika cikinsu sunayi suna zolayar juna dan kauda tunanin dake Neman addabar zuciyarsu tunda dare yayi.


Yanzu ma duk noke nokenta tare sukai wanka sannan suka fito da kanshi yaimata shafa ya bata kayan da zata saka,Yanacan yana niyyar saka kayane kira yashigo wayarta.

Dariya tasaki lokacinda taji k'aradina duk korafin tace zata kirani amma naji shiru.

Hakuri tabani tana dariya kamin tace"Nafa kira wayar ki mama tacemin kina islamiyya shiyasa saiban kuma kiraba shanake zakiyi hutun ko kwana biyu ne sabida hidimar bikinanna da akasha?

"A a wallahi zaman ne banso shiyasa naje komai lafiya ko?

Lafiya lau 'yar kanwata nasan kinyi kewata Amma banji kince ya Dr. Ba.

Tsaki naja tare da kashe wayata,dannifa da gaske bansonshi wlh.

Dariya tasaki hadda kwanciya yayinda ya tsaya kallonta dan mamaki ma tabashi be taba gani tana dariya irin hakaba.

Shima dariyar yasaki kamin yace"Aysha ce ko?

Gyara kwanciyarta tayi kamin tace eh itace Wallahi yarinyar nan tacika rigimar tsiya.

Zama yai gefenta kamin yace" Babu wani rigima tsabar masiface kawai dake cinta.

Shigewa tai jikinshi ganin yana miko mata hannuwanshi Sannan tafara magana har lokacin akwai musmushi saman fuskarta"Gaskiyarka Dr.aysha nada fada sosai Amma dole sai an kureta Amma inba hakaba bazaka zata tanada matsalaba,Yanzu haka kwanann nan Abba yakashe wani kes wallahi wata yarinya ta kama taimata dukan tsiya bayan Abba Nada hanya da saidai muji an rufeshi kuma dayake tasan ita keda gaskiya police din ma kartamusu rashin mutunci tayi dakyar aka kashe maganar mu kanmu wani lokacin shayinta mukeyi shiyasa Abba yake kiranta da JARUMA, Sabida wani lokacin idan tai Abu saikaga kamar namiji wlh,Amma kuma kalli jikinta saikace wacce bazatai kwari ba.

Dariya yasaki yana kuma sunsunar gashin kanta, Dan wani irin shaukin son kasancewa da ita yakeji yana tasomishi"Aini kaina na lura da masifarta Dan zuwan da mukayi kawai kuma kin manta randa muka hadu dake za ai mata allura? Kin manta yanda akaita dambe da ita?
Dariya tayi itama,Ban mantaba wlh aysha Nada hakuri kuma akwai abubuwan birgewa tare da ita Ammafa bazaka gane hakanba sai idan matsala bata hadakuba.

"To Allah yabata miji nagari.

" Amen Amma Abba yace ba yanzu zaimata aureba bama wannan ba har yanzu bata idasa makarantaba sai yanzu sukeyin neco amma kaga bangaren addini tuni tai sauka tai hadda littattafan addini kawai take bita wata irin kwalwa Allah yaimata Dr. Indai karatune da anyi yashiga kenan yanzufa Abba ya daina mata karatu Dan duk kusan wasu littattafai daya sani tagama saninsu saidai yanzu idan ta koyo tazo ta doramishi karkaso kaji yanda suke artabu kaci dariya har koyar da matan aure takeyi Ammafa duk ranar da sukabata mata rai to sunyima kansu Dan sai sun biyo hanya biko.


"Kai amma gaskiya ta birgeni wlh Allah ya temaka zanyi tafiya sati na sama insha Allah saitazo ta tayaki zama kwana hudu kawai zanyi.

Lalubarta yafara abinda ya katsemusu hirar saidai daga yanayin yanda yaga tana nokewa yasan cewa batasone Amma batason batamishi rai.

Shikuma yanajin kamar bazai iya hakuriba.





Haske writers association.
12/10/20, 7:49 AM - Naffy Aliyu Umar: JARUMA.
10

Na maman khadija.



Rikemishi hannu tayi tana kuma marairaicewa duk da cewa cikin duhu suke.

"Sorry akwai ciwone har yanzu?

Kanta ta girgiza mishi alamun a a.

" To kibarni inyi yau bazakiji wahala irin na jiyaba insha Allah wallahi marata har kullewa takeyi kinji yi hakuri.

Tsoro yasa ta cimimiye jikinta lokacinda yake rudamata jiki da zafafan kisses ahankali yake mata rada cikin kunne akan tasaki jikinta zaibi komai ahankali.

Yau dinma tasha wahala amma dai ba kamar jiyaba.



Bayan sati daya.
Alhamdulillah cikin satinnan sun mori ranakun cikin tsantsar soyayya da kulawa sosai yake riritata balle itakuma da take kaunar kamar ranta,Duk da cewa ta lura yanada yawan bukata Amma hakan besa ta taba nuna gazawartaba kamar yadda yayunta keta bata labari.

Da kanshi ya kira abban ya nemi alfarmar Dan Allah abar aysha tazo zaiyi tafiyane amma daya dawo zai maidota da kanshi.
Abban besoba amma ganin yanda yaketa marairaicemishi yasa ya amince.


Maganar iyayyakun gidan kuwa luf sukaji Dan kullun da karatun alqur'ani suke kwana

Please Login or Register in order to submit comment