Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yauwa jikin da sauki amma akwai zazzabi har yanzu asamo mata magani dan d'azu tasha fanadol amma be saukaba.

Matsowa yai jikina tare da kamo hannuna"Baby meya faru?


Wani kallon baka isaba naimishi,Yayinda cikin zuciyata nake tuno yanda yaimin tas d'azu da safe har yana fadin dukan tsiya zaimin bayan ya gwadamin k'arfinshi wajan biyan bukatarshi,Himm namijin kenan.

Fisge hannuna nai tare da lallabawa na canza kujera,Haba malam ai wlh kayi da 'ya indai nice.





haske writer's association.
12/10/20, 9:46 PM - Naffy Aliyu Umar: 61



Kirjinshi yaji ya buda dan sam be zataba kuma ayanzuma saiyaga kamar akwai rama sosai jikina,wani tsoron yakamashi kaddafa mutane sufara zargin wata cutarwar ke ramar mishi da mata.

Miyau ya hadiye kamin ya nade hannun rigarshi,Kamin in ankare saidai naji yai sama dani yana fadin bari muje in dubaki.

Duk irin haure hauren da nakeyi besa ya sakeniba saida muka dangana da d'an k'aramin falon mu,Zama yai tare da d'orani Saman cinyarshi yana shafar gadon bayana"Sorry bansan baki da lafiyaba wallahi sannu.

Kuma tsuke fuskata nai dan karma yai tunanin Sauki,Nifa dama bawani sonshi nakeba kawai biyayya nakema iyayena Amma tunda iskanci yakeso ai kowace mace nada kalar nata wallahi saidai ta boye.

Riko hannuwana yai cikin nashi yana murzawa ahankali yayinda yawani kankance idanu hadda langabar da kanshi Gefe saikace wani na Allah"Baby nai miki wani abu ne?


Manyan idanuna na watsamishi kamin ince"Babu abinda kaimin dr.Sabida kasan babu zuciya cikin kirjin aysha balle tasan bacin rai da farinciki,Sannan babu ruwanka da ciwona dama ko lafiyata lau ai nasan inakan hanyar mutuwa tun da har iyayena suka baka aurena,Danhaka lafiyata da rashinta duk bata damekaba please.


Wani irin sanyi jikinshi yai ganin yau dai bacin raina ya bayyana.

Kunsan dama abinda yakamata shine mace tabar saurin fushi da nunama miji damuwa shine zaisa duk randa ta bata ranta zai gane harma ya gyara kurenshi,Amma idan koda yaushe kina cikin bacin rai to bazai taba gane cewa yaimiki ba daidaiba wataran.


Yajima zaune yana murzar hannunshi kamin ya kwale kayanshi ya shige cikin bargon da na kudundune ciki.

Shigar dani cikin jikinshi yai kamin yafara magana ahankali bayan ya tube rigar dake jikina"Dan Allah karkiyi fishi dani aysha wallahi bansan abinda ke damunaba haka kawai nake samun kaina cikin damuwa da bacin rai musamman idan ina tare dake,Amma kiyi hakuri zan gyara kuma zan kiyaye dukkan abinda nakemiki wanda bakiso insha Allah komai zai zama tarihi kamar yadda kike fadi kullin.

Ni kaina saida nai tunanin anya ba wani shaidanin keson shiga tsakanina da mijinaba? Dan ana iya gane irin soyayyar da dr.kemin koda zaman dan lokaci akayi kuwa.


juyamishi baya naso yi Amma ya matseni jikinshi yanajin yanda zafin jikina ke kuma shiga jikinshi"Kiyi hakuri dan Allah bazan kumaba aysha bazan kuma saki kuka ba bazan kuma yimiki abinda bakiso ba.

Lamo nai jikinshi ina lumshe idanuna dan sosai nakejin dadin k'amshin turarenshi.

Bansan lokacinda barci yai awon gaba daniba.



Lamo yai yana tufka da warwarar abinda ke shiga kanshi har yake bata ran babynshi,Tabbas bata cancanci damuwa daga gareshiba musamman idan yai la'akari da irin yanda auren ya kasance kuma ya tabbata har yanzu bawani son azo agani takemishiba kawaidai tana kokarin ganin ta kiyaye dokokin Allah ne.


Akace tsakanin mata da miji da Allah.

Bantashi da wata damuwaba balle bacin rai,Dan sosai nasami nutsuwa dana kwanta jikinshi.

Agaggauce ya wuce masallaci anata la'asar nikuma saida nai wanka Sannan nai sallar,Nai zaman shafa mai ne Saigashi ya shigo cikin d'akin.

Sannu nai mishi Amma batare dana kalli inda yakeba,Abinda yasa ban tsananta fishi dashiba shine,Nasihar da mama tai min na cewar kar in yadda in tsananta fishi,Lallai idan yaban hakuri to in hakura,Rashin yin hakurina shine zaisa ya daina bani hakurin sabida zaiga ai idan yabani ma ba hakura zaiyiba hakan zaisa yadaina baki daya,Saidai duk da na hakuran sainabashi lokaci na rashin walwalata tunda nasan bazaiso hakanba.


Zama yai gefena yana d'an lakato man be tsaya tambayataba yafara shafamin"Nagode babyna.


Kallon da akai me naimishi,Amma saidai naga yai murmushi,Dan harararshi nayi yayinda cikin raina nace gulmamme kawai me baki irin na mata,Dan dr.wani irin k'aramin baki gareshi zagayayye me matukar kyau shiyasa idan ya fara sumbatata ban sanin lokacinda nake biye mishi.


"Yanzu ina ke miki ciwo?

Girgizamishi kaina nai ina d'an juya idanuna.

. "Ki dinga min magana aysha kinji?

Doguwar riga 'yar kanti nasaka mara nauyi tare hula,Babu wanda zai ganni alokacin yai tunanin na isa aure dan rigar wata baby dol ta mayar dani gashi d'an zazzabin danayi nakuma k'ankancewa sai kirjina da yai wani das dashi gwanin sha'awa.


Hamdala yakeyima Allah cikin zuciyarshi yayinda idanunshi suke kaina saikace tsohon maye.

Harara nasakar mishi tare da ficewa wajan mama.




***

Bayan sati uku; KANO.
"Kema da yakamata ki kwantar mata da hankali Amma kece mekuma rurawa sai me idan batanan akai bikinki? Ke ko tausayinta bakiji ance bata da lafiya? Kumama idan kin kwantar da hankalinki ba can za a kaikiba inda take? Haba mana zainab da hankalinki.


Takurewa takumayi tasaki kuka,Wannan wane irin aurene yazo musu ita da aminiyarta? Ita anyishi cikin magagin mutuwa Sannan anbata mijin yayarta batare da anbata zabi ba,Dalilin dayasa babu wani sha'ani da akai na murnar aure,Itakuma yanzu ga nata ,Ta hakura zata auri tubabbe kuma hakan beyiba wai hidimar bikin ma baza'a bari aminiyar tata ta halartaba? Gaba daya auren yafice mata arai ta fadi tafasa yafi cikin carbi amma babu me saurarenta hidimarsu kawai suke haka zalika basu daina yimata duk gyaran da ya dace ba.

Tana kallon kiran wayarta da akeyi akai akai amma Tai biris hasalima wani irin haushin me kiran takeji,Yayinda shikuma yaketa nacin kira dan jin yanda take,Danshima anashi bangaren babu kalar lallashin da beyima shi Ahmad dinba Akan yakamata yai hakuri yabari ayshan ta halarcin bikin ,Amma ya rantse babu wanda zai jamishi asarar aikin da yayi tukuru yasamu dankuwa k'aramin cikine wanda ko sati biyar be cikaba.



"""***"""

Kwance nake idanuna duk sun tashi kuma sunyi ja,Yana zaune yana tacemin lemon zaki da kankana cikin cup.

Sam fuskarshi babu walwala Amma hakan besa ya daina kyautataminba.

"Anshinan taso kisha kinji bazakiji tashin zuciyarba yanzu.

Kwacewa nai nakuma komawa tare da furta"Bansha ko dole ne?

Fincikoni yayi na fado kanshi,Manyan idanunshi ya fiddomin"Tausayinki nakeji aysha wallahi da sai in makeki yanzu maza bude baki ki shanye kamin in cinyeki d'anya yanzu yanzu.

Bakina na bude ina hawaye dan atsawace yai maganar abinda becika yiminba.

Abaki ya dinga bani Saida yaga na shanye sannan ya jawo magungunan da nakesha yabaresu yabani.

"Tashi saka hijab dinki muje In kaiki kiga gari.

Turo bakina nai tare da cewa"Ni babu inda zani jira nake gani.

"You see ahaka kikeso inbarki kije gida jikinki babu wani kwari haka kawai kije ki kakkabar min da abinda nake kulafuci wajan shashanci irin naki ko?

Hararshi nai kamin nace da kaina zan kakkabar dashi din danni banso karatu zanyi.

Ihu nasaki jin wani mugun dalli da yaima bakina.
Kuka nasaka saikuma ya rungumeni yana lallashi tsabar ya rainani.



Hausawa sukace biki wan shagali,Gidan namu tuni ya cike da 'yan biki dan mama da abba sune iyayen ango.

Duk hidimar nan idanun Dr. Na kaina idan zaiyi shigowa goma saiya lek'ani kokuma yataba jikina yaji yanayin zazzabin dan kwanakinnan shike wahal dani.

Dangin abban kusan dasu ake komai.duk da cewa kusan gulmarsu tafi yawa,Dan mutanene masu matukar sa ido da hassada.

Tsananin kulawar da Dr. Ke nunawa akaina itace takuma tashin hankalin 'yammatan dake sonshi tare da iyayensu dan kowanne beki ace diyarshice tasami Wannan kulawar ba.

Ita kanta mama yawan mutane besa ta kauda idanunta daga kainaba balle da yanda yaita binta kamin su wuce d'aurin auren akan ta kula dan Allah, Kadda wani ya lababo yasami mafaka.


Daga k'arshema saita sa yaya halima tace ta kamani ta kaini can d'akinta in kwanta sabida hayaniya dan yau dawani zazzafan zazxabi natashi.



***
ya kira wayata yafi a kirga Amma ko sau d'aya ban dagaba ,Shiyasa duk beda wata nutsuwar kirki har aka kammala d'aura auren.



Ba k'aramin dadi yajiba da yaga hadda mama cikin masu kai zainab din duk da cewa dama bawata gayya sukayoba tunda wuri ba kusa ba.


Su malam abubakar baki har keya anzama.ango betaba tunanin riskar farincikiba kwatan kwacin wannan Saigashi Allah me ni'imomi kala kala yaimishi ta musulunci yaukuma ga daruruwan mutane sun shaida anbashi auren zainab halak malak, Shiyasa lokacinda yaji sautin ihunta wajan shiga kota jiyai kamar yafita ya lallashi abarshi.



"Mama kintaho mana da tsaraba kuwa? Dan wallahi baby kwadayi gareta yanzu.

Kauda kanta tai gefe tana d'an mirmushi sam bataso hawa motarshiba,To ya zatai tunda shine ya d'auko amaryar kuma itace rike da amarya.
Sam bejin kunyarta Saita tuno randa ya kirata yanamata albishr tasami jika bakatsine.


"Kai yaran zamani Allah ya shirya.

"Mama bakice komaiba,Wallahi duk ta rame,Kumafa da kullun sai naimata Addua Allah yasa karta sami me wahala ashe ashe me wuyar ne.


"Waikai baka iya yin shirune Ahmad? Haba ka kalli gabanka mana.


Murmushi yasaki kawai yacigaba da tukinshi ba tun yau yasan cewa maman kunyarshi takejiba sosai.

Wanda ke gefen Dr.dinne da mamaki ya hanashi motsin kirki dan kowa yasanshi da rashin magana Amma kuma yaga anan harwani kalo zance yake.

Kasa hakuri yai ya turama Salim message wanda ke motar baya"Wai wacece ke rike da Amarya?


Babu jimawa salim din ya turomishi da amsar"surukar Dr. Ce itace maman matarshi baby meya faru?


Ajiyar zuciya kawai ya sauke yacigaba da kallon hanya.





Labarin jaruma na kudine.



Haske writer's association
12/10/20, 9:46 PM - Naffy Aliyu Umar: 62




"Wai mama ankaita asbt kuwa?

"To gaskiya be kaitaba Amman naga yana kokarin dubata yace wai cikine,To kuwa kinga idan shi dinne ai dole sai hakuri.

"Hakane mama Amma gaskiya tausayi takebani wallahi duk ta zabge ta kuma komawa shiru shiru da ita.

"Hakane Amma hadda bakincikin hanata zuwa gida da yayine yakuma kwantar da ita kinsan aminiyarta ce yarinyar shiyasa duk ta kuma zabgewa nifa tunanima nake anya banda mahaifiyarta za azo Kuwa bazanso ta gantaba cikin wannan yanayin.



***


Duk yAdda yaso yajata da hira Amma tai biris dashi dan harwani shagwaba yake mata wanda yasa hajiya ladi k'anwar mamar zainab din dakuma zainab din dariya,Balle kuma abokinshi hashim wanda yake ganin abun sabo.

Dariya maman tasaki ganin zainab me kuka yanzu takoma dariya,Allah ya shiryaku dai.


"Amin mamammu ammadai nan zakimana kwana biyu ko?

Banza tai dashi tare da kauda kanta gefe duk cikin srukanta shine kawai bejin kunyarta har garama lokacinda yana auren fatiman akan yanzu.



** **

Baiwar Allah tashi zan d'an kwanta nan gefe.

Idanuna wa inda sukai d'an ja na bude ahankali na saukesu kan yarinyar da take dasuna ummi itace mama taban labarin son da takeyima Dr. Dan dai kawai iyayenta na hanatane.

Gyara kwanciyata nai tare da juyamata baya.Wata irin masifa ke yunkoromin dama tun safe nake neman wanda zan saukewa Amma ban samuba.

Kamin nakuma daidaita inda nake naji tawani kwashemin k'afafu tana neman saukesu.dayake dama daga gefe nake.

Wata irin muguwar hambara naimata da k'afafuna,Saida ta hantsila kanta ya bugu da miro dan sam bata zaci zanyimata hakanba.

Hakan be minba nabita daga kwancen nafara fallamata mari kota ina.
Shigowar ya hannatu yasata saka salati Amma tagaza banbareni jikinta.
da gudu tafita saigata da mutane.

Dakyar mama ta yakiceni jikinta,Kamin ta rungumeni sai lokacin tafara k'okarin kawomin bugu yayinda taketa k'unduma min zagi kala kala tana kawo hannu jikina duk da cewa mutane na rike da ita,Yayinda mahaifiyarta keta sakin maganganu wai asakeni itama ta rama bugunta indai ba zalinci aka shiryaba.


Cikin wannan yanayin motocin amarya suka dira gidan,Babu wanda yaji sabida hautsunewar da d'akin yayi kowa na kokarin fadin albarkacin bakinshi.


"Gaskiya hajiya kibar ummi ta rama bugunta sabida Allah shikenan ta bugi banza? Hakan ma bazata sabuba wallahi.Cewar matar k'anin Abban mesuna musa.

Mamace tafara magana cikin damuwa da bacin rai"Haba ladidi sabida Allah anaso a kashe wuta amma kina k'okarin rurata wannan wane kalar abune haka? Yarinyar da ko lafiya bata da ita,Na tabbata idan da ummi bata shiga hanyartaba wallahi bazata kulataba dan aysha babu ruwanta da abinda be shafetaba.

Dayake kusan duk sune shiyasa duk sai sukafara fadin maganganu sunabin bayan ummin da mahaifiyarta wadda keta kumfar baki.

Yaya halimace ta jawoni daga jikin mama ta turani gaban ummin"Gatanan bigeta tunda abinda kikeso kenan,Ke kuma kicimin uban shegiya dan Allah.

Daidai shigowar Dr. Da Abubakar haddama salim dan tuni suna falo tsaitsaye jin hayaniyar tai yawane yasa suka shigo.

Manyan idanunshi waje yake kallonmu,Kotai tunanin zai kyaletane kawai takawomin mari dan abinda innarta keta sata kenan.

Hannun na rike tare da yarfa mata nawa mari kamin tai wani yunkuri Dr. Yabata wani marin"Dan uwarki matar tawa da ciki zaki daka wani marin yakuma saukemata duk da cewa innarta tashiga tsakiyarsu.

"Waima Dakata ubanwa ya gayyaceku wannan bikin? Munce kuzo ne?

Wayarshi ya zaro ya fara neman lamba kamin yasa akunne.

"Lafiya lau,Cewa nai kana office ne?

"Yauwa turomin mota biyu ko uku da ma'aikata dan Allah yanzu pls.


Fahimtar idan ya dosa yasa kamin wani lokaci d'akin yakoma babu kowa sai imu imu,Sai lokacin mama kecemin aysha ya akai?


Cikin siririyar muryata wadda takuma dishewa sabida bacin rai ga zazzabi nafara magana"Mama barci nakeyi sainajita wai intashi zata kwanta sai banyimata maganaba kawai naji ta zubomin kafafu k'asa.


"Hakan shine daidai gara da kikaima hegiya duka haba ina amfanin jaraba,Cewar inna suwaiba k'anwar mama.


Kwanciya nai sukuma suka fice tarar baki.

Bansan hadda mamana aka zoba shiyasa sainai kwanciyata,Shima Dr. Rufa kawai ya gyaramin ya fice yanajin yanda ranshi kewani mai suya.



Barcine ya kwasheni yayinda falon ya kuma dinkewa da baki.


Akunyace take Amma duk da haka taso kwarai ace tafara tozali da diyar tata Amma shiru takeji gashi babu halin yin tambaya.

Saida suka shiga alwalar magriba Sannan ta ganni kwance ina barci ga zainab zaune gefena zazzabine ringis jikina shiyasa ita kanta takasa tashina tunda aka kawota cikin d'akin.


Maganar danaji sama sama yasani bude idanuna.
da mama nafara hada ido kamin zainab,Dawani irin sauri na dire gadon dan saida nai wani taga taga ya safiyya ta taroni kamin na isa jikin mama.

Kankameta nai ina hawaye dan jinai wata tabata ta sakkomin gaba daya.
Ita ma matseni tai jikinta tanajin yanda jikina yake rau dashi.


Shigowar Dr. Yasa duk muka kalleshi.

Can ya tsallake har inda nake tare da taba jikina,Cikin damuwa yace"Sorry muje ki wanka saikisha magani.

Kunyace ta kama mama yayinda su ya maryam ke dariya.

Da tsiya yajani yayinda nasaka ihu shiko ko a jikinshi,Kallon zainab yai tare da cewa muje.


Waro idanunta tai kamin ta sadda kanta k'asa.

"Ke muje mana mijinki ke kira.

Dole ta biyo bayanmu.

Da yatsanshi ya nunamata inda zata sami dr.din yayinda yai ciki dani yana fad'in"Kincika rigima baby kodai wannan cikin shine ke kuma tunzuraki ne?

Banza nai dashi bakin nan nawa d'ane.

Saida yagama tubeni tas kamin ya lashe libs dinshi"baby bari nafara sauke miki da zazzabinnan tukunna.




Haske writer's association.
12/10/20, 9:46 PM - Naffy Aliyu Umar: 63




Ko alama ban nuna bansoba dan na san yanda yakemin matukar yaso biyan buk'atarshi nikuma naki yadda.

Saida yagama wajagalgani Saigashi kuma sai zufa nake alamun zazzabin ya Sauka.nan nabarshi kwance naje nai wanka.Saida yaji kwanciyata Sannan yatashi shima ya wuce bayan ya sumbaci goshina.



""""

Tunda tashigo yake rike da tattausan hannunta yana aikin murza gani yakeyi kamar ba'a ne ita din ba mallakinshi bace.

Duk kunya tagama dabaibayeta Amma shi ko ajikinshi,Gabadaya yagama maida hankalinshi akanta.

"Muje in nubamiki wajan da zamu zauna ko?

Da sauri ta girgizamishi kai"A a basaika nunaminba anjima.kadan za a kaini can.

"Ok injiraki kenan?

Kanta takuma amsamishi dashi.

Mikewa yai da ita tsaye ya rungumeta gaba daya cikin jikinshi,Dan dama abinda yaketa kwadayi kenan Amma ya rasa ta ina yakamata yafara,wani irin k'amshi yakeji tanayi me matukar kwantar da hankali da tada sha'awa.
Sabanin 'yammatansu wa inda basu damu da k'amshi ba.

Da kyar yasamu ya danne kanshi ya rakata falo ta koma d'akin maman dan lokacin gidan babu kowa daga yayin Dr. Din saikuma bak'in da suka kawo amarya.



***

A,daddafe nasamu nai magriba da isha'i,kan sallayar na kwanta ina rike da cikina wata irin murdawa yakemin wanda nasan yunwace bawani abuba ga tashin zuciya wanda ya hanani sakat,Har ji nake inama zanyi aman inhuta.

Zuwa yai ya zauna tare da ubamin ido babu zazzabi jikina. Amma kallo daya mutun zaimin lokacin zai tabbatar da banda lafiya Kokuma banjin dadin jikina.

Damuwace k'arara kwance fuskarshi yanason cikin fiye daduk yadda zai fad'a Amma kuma yafi son babyn akan cikin so dubu,Besan yanda zaiyiba Amma beson wannan yanayin na damuwa da ciwo wanda yake gani.

Tallaboni yai jikinshi yana gyara zamanshi,Duk jikina ya mutu nifa araina ji nake kawai bansan cikin dan nakai wata daya kenan da fara jin yanayina ya sauya memakon kuma inji sauki a a saima gaba da ciwon yakeyi kullin.

Wayarshi ya zaro ya danna kira.

"Dan kashiga wajansu usman zan rubutomaka magunguna ka amsomin yau Baby saitasha drip dole.

Ajiye wayar yayi bayan yagama rubutu ya tura.



***
"Gaskiya hajiya na kokari haka yarannan kemata rashin kunya? Kallifa tunda ya janye matarshi bamu kuma jin motsin kowaba cikinsu!!!

Yo mama ai ita mama babu ruwanta aiko haka suke yini like da juna damma yanzu naga hankalinshi tashe yake sabida rashin lafiyarta,Cewar yaya hannatu tana bawa maman labari suna dariya.



Fuskar nan sam babu walwala haka yagama sakamin drip din.



***

Lafiya Ahmad? Cewar ya halima.

Zama yai wajan k'afar mama kamin yace"Humm ni wallahi ciwon baby yafara Isata tamafa daina jin sauki yanzu.


Duk dariya aka sakamishi kamin mamanshi tace"To ya zakuyi ai dole sai hakuri,Yanzu tana ina?


"Drip na sakamata yanzu Amma tafara barci mama kizo muje ki ganta,Yai maganar yana kallon mamana duk da irin yanda take kauda kai da daurewa saida tai murmushi ganin yanda yake kuma karya wuya Saikace wani baby.


Zainab dai tai zuru tana kallon ikon Allah,Wai namiji na shagwaba.

Shigowar Abba cikin falon yasa duk aka maida kai gareshi baki na gaisheshi.


"Wai halima duk baku wuceba me kuka tsaya jira haka?

ko wacce kauda kai tai tana dan murmushi dama sunsan saiyayi magana kam.

Girgiza kai yai kamin ya ce"Kudai naga randa zaku girma wallahi,Kuma ai yakamata a nunama baki makwanci ko?

"Eh dama yanzu muke niyyar komawa can bangaren idan mundibo aysha,Cewar maman tana kallon abban wanda ke niyyar juyawa.

"Ah wai jikin matsa mata yai kenan?Kai Ahmad muje in ganta niyau gajiye nake jina.



***

Sama sama naji sautin magana kamar saman kaina shiyasa saina bude idanuna ahankali na saukesu akan Dr. Dake gyaramin rufar"Baby kintashi? Ga abba zaimiki Sannu.


Niyyar tashi nafara Amma yai saurin mayar dani"Sorry karki goce allurar,Yai maganar yana kuma maidani kwance.

Cike da jimami Abban ya gaisheni kamin ya fice.


Kusan gaba dayansu suka shigo dubani.

Yana like kusa dani yana waya ganin mama besa ya matsa daga jikinaba saima hannuna da yake murza,wata matace ya ciroma baby da safe shine yanzu bata da lafiya Amma bazai iya fitaba.


Idona nakan mama Amma ita saiwani shashsharewa takeyi,Hannun ya safiiya na riko ina kallonsu duk nawani yamutse Saikace bani ba.

Kowa dake d'akin saida ya tausayamin sabida yanda nagama ficewa hayyacina.

Sunjima cikin d'akin kamin a rugind'uma inda za a aje amarya zainab.

.kallon dr nai tare da marairacewa dannma sonake inbisu.


Kwanciya yai gefena tare da rungumeni yanda bazan goce hannunaba"Kiyi kwanciyarki idan ruwan ya k'are zan kaiki kinji ko? Ya idasa maganar yana shafar gashin kaina.
Nan da nan barci yai awon gaba dani.



Wata irin guguwace tataso sosai ta tirnike ko ina ganin tana neman lulluneni ne yasani fara wani irin gudu dan ganin na tseremata.

Saidai ga mamakina shine saina ashema ni takebi aiko muka dasa tsere ina gaba tana biye dani Saida nai gudu nai gudu har k'arfina yafara neman k'arewa Sannan nanemeta na rasa.


Saida nai wani uban gudun Sannan na tsaya wani wuri ina hutawa.

Marata naji tacika da fitsari danhaka ina dubawa naga babu kowa kawai Saina duka gabana da niyyar yin fitsarin.

Saidai me a memakon inga ruwan fitsari sai kawai naga jinine ke fita amatsayin fitsarin.





haske writer's association
12/10/20, 9:47 PM - Naffy Aliyu Umar: 64




Yawan mutsu mutsun da nakeyi cikin barcin yasashi farkawa batare da yaso ba dan wani irin matsanancin barci ne ke janshi shima,To kowa yagaji sabida yawan zirga zirgar hidimar biki,Tashi yai Zaune tare da haskeni da wayarshi.


Ruwan yafara zaremin kamin yatashi dani gaba daya jikinshi,Tar na bude idanuna akanshi ina sauke numfashin wahala kamin in dafe marata dake wani murdamin.



Please Login or Register in order to submit comment